Skip to content
Part 36 of 48 in the Series Akan So by Lubna Sufyan

Juyawa Fu’ad ya yi safiyya ta dakatar da shi da faɗin,

“Please ka ɗauki mukullin motata kuje gida da Nana. Ba zan iya ganinta ba yanzun…”

Ta ƙarasa maganar muryarta na rawa. Kai ya ɗaga mata alamar ya ji, ya ɗan kalli Haneef da yake masa wani kallo da ke ƙara karya mishi da zuciya.

Sannan ya wuce. Shi kaɗai ya san yadda ya ke jin zuciyarshi. Ya kai mintina biyar tsaye riƙe da handle ɗin ƙofar yana maida numfashi.

Addu’a yake Allah ya ba shi ƙarfin gwiwar fuskantar Nana ba tare da zuciyarshi ta sake karyewa ba. A hankali ya tura ƙofar yana jin sallamar da yake sonyi tsaye a ranshi ta ƙi fitowa.

Idanuwanshi ya sauke kan Momma. Muryarshi a dakushe ya ce,

“Gida za mu tafi. An sallameta.”

Da fara’a momma ta ce,

“Alhamdulillah. Aikam ni ma bari na tashi…”

Kai ya ɗan ɗaga mata. Nazarin shi take, kwata-kwata a birkice yake, hankalinshi kamar ba ya jikinshi.

“Fu’ad?”

Ta kira cike da alamun tambaya. Kallonta ya yi sosai yana roƙonta da idanuwanshi da karta tambaye shi komai. A hankali ya girgiza mata kai.

Shiru ta yi tana miƙewa ta ce wa Nana,

“To ‘yar tsohuwa, ni kam zan wuce sai na zo duba ki ko?”

Dariya Nana ta yi da sautinta yasa Fu’ad jin zuciyarshi ta wani matse kamar za ta fashe. Baya son tuna ƙarancin lokacin da yake da shi na jin wannan sautin.

“Ni zan zo ai. Mummy za ta kawo ni in kwana gidan ki.”

Murmushi Momma ta yi mata.

“Allah ya kawo ku lafiya. Ya ƙara sauƙi.”

Ta amsa da,

“Amin. Allah ya tsare hanya.”

Momma na tafiya ta amsa ta da,

“Amin thumma amin.”

Raɓa Fu’ad ta yi ta wuce ba tare da ta ce mishi komai ba. Ya ji daɗin hakan, don baya jin zai iya wata magana a yadda yake jin shi.

Kayan su ya fara tattarawa don baya son ko kallon inda Nana take. Saukowa ta yi daga kan gadon ta zo inda Fu’ad ya saka warmers ɗinsu a babbar leda ta kamo hannunshi tana ja.

Sai da ya ja wani numfashi ya sauke shi ba tare daya kalle ta ba ya ce,

“Princess ina jinki…”

Sake jan hannun shi tayi. Ba ta son yanda yake ƙin kallonta ɗin nan sam. Ta san me hakan yake nufi. In tun yanzun za su fara mata irin hakan nan gaba ba ta san me zai faru ba.

A hankali ya juyo ya sauke idanuwanshi da suka sake launi kan fuskarta.

“Ina Mummy?”

Ta tambaya tanajin komai baya mata daɗi. Ba ta son ganinsu cikin damuwa ko kaɗan. Da da yadda za ta yi ta cire musu da ta yi. Da ƙyar ya ce mata.

“Sun yi gaba da su Lukman ni da ke za mu tafi.”

“Hmmm.”

Nana ta faɗi ta saki hannunshi ta je tana saka takalminta da hijab. Sannan ta dawo ta kama hannunshi suka fita tare.

Sai da ya buɗe bayan motar ya zuba kayayyakin ciki sannan ya buɗe wa Nana ta shiga ya zagaya shi ma ya shiga.

*****

“What is wrong?”

Nana ta tambaye shi kamar daga sama. Ɗan kallonta ya yi sannan ya maida hankalinshi kan tuƙi da faɗin,

“Bakomai, me kika gani?”

Sake lafewa ta yi cikin kujerar motar ta ce,

“Ka yi shiru tun ɗazun.”

Shi kanshi bai kula da cewar tunda ya soma tuƙin bai ce komai ba. Yana jin yadda hannuwanshi ke wata zufa duk da AC ɗin motar a kunne yake.

“Bako…”

Da sauri ta katse shi da cewa,

“Please kar kamun ƙarya. Na tsani ai min ƙarya.”

Sauke numfashi ya yi.

“Tsana is not a nice word Princess.”

Sauke murya ta yi ta ce,

“Ka yi haƙuri.”

Kai ya ɗan ɗaga.

“Yau ɗin ne babu daɗi shi ne kawai.”

Ba ƙarya ya faɗi ba. Gaba ɗaya ranar ba ta mishi daɗi. Tun kafin a faɗa mishi wannan mummunan labarin.

Hankalinta ta mayar kan titi sosai tana kallo hanya. Da wani irin yanayi mai nauyi da bai taɓa ji a muryar yarinya mai shekarunta ba ta ce,

“You are not a match ko?”

Motar ya ji tana ƙoƙarin kwace mishi. Kafin ya samu ya ɗan daidaitata yana rage gudun da yake. Wani irin yawo zuciyarshi take yi cikin ƙirjinshi.

Wani abu da ya tsaya mishi a wuya ya haɗiye. Zufa ya ke ji ta wajaje da dama ta na fito mishi. Baya son mata ƙarya ko kaɗan.

Sai dai bai san ta inda zai fara gaya mata gaskiya ba. Tsoro ne cike fal a zuciyarshi. Ko da Nana zata sani bai so daga shi sai ita ba.

Tafi sabawa da Sofi. Za ta so kasancewa da ita a wannan lokacin ba shi ba. Duk da faɗar hakan a kanshi kawai ba ƙaramin ciwo abin yake mishi ba.

“Princess…”

Ga mamakinshi gyara zama ta yi ta zuba mishi idanuwan nan nata iri ɗaya da na shi.

“Ya Mummy take? Ya ta ɗauki hakan? Ba ta ji daɗi ba ko?”

Nana ta jero mishi tambayoyin lokaci ɗaya. Damtse steering wheel ɗin ya yi kamar zai karya shi. Ta gane. Ta san bai yi matching ba.

Muryarshi a sarƙe ya amsa ta da,

“Pretty bad.”

Shiru ya yi, don bai san kalaman da zai ɗora yanayin Safiyya akai ba. Da shi kanshi. Don har yanzun ji yake gaba ɗaya duniyar shi ta yi wata irin girgiza da komawarta dai dai abune mai wahala.

Ko yanzun da yake tuƙi kokawa yake da zuciyarshi da duk wani abu nashi ya yarda cewar babu abinda zai iya yi wa Nana.

Shiru ta yi na lokaci mai tsayi. Tuƙin yake amma ji yake kamar garin za su bari. Kwatakwata ya ƙi masa sauri. Ya ma manta da ya rage gudun motar sosai.

Ta gefen idanuwanshi ya ga ta cire hijabinta. Ya ɗan kalleta ya maida hankalinshi kan tuƙi yana jin wani irin yanayi da ba shi da kalaman misaltawa.

Hular da ke kanta da tunda ya ganta irin su ne a kan ko yaushe ba ta taɓa cirewa ba ta sa hannu ta fitar.

Kanta ta shafa da babu gashi ko ƙwara ɗaya. Ya sake juyowa ya kalleta. Ji yake kamar wani abu na matse mishi zuciya. Ƙirjinshi zafi yake sosai.

“In faɗa maka wani abu ba zaka faɗa wa kowa ba? Ka yi alƙawari?”

Kai ya ɗaga mata ya kasa magana. Wannan wacce irin rayuwa ce. Shekararta sha ɗaya. Kamata ya yi ace tana can tana wasanta tana tunanin wanne Disney movie ne ya fi wani kyau.

Wacce riga ta fi burgeta. Bawai zaune anan ba da kanta babu gashi ko kaɗan. Ji yake zai iya bayar da komai don ta samu hakan ciki har da tashi rayuwar.

“Ina tsoron in mutu.”

Ji ya yi wani abu ya tsane a fuskarshi. Da yake da tabbacin duka jinin dake jikinta ne ya koma wani waje. Kafin lokaci ɗaya wani abu mai yaji ya mamaye mishi idanuwa.

Hannunta ya kamo da nashi guda ɗaya ya dumtse gam ɗayan na kan steering motar. Ya san shi ba mai yawan kuka bane. Amma wannan yarinyar ta zaune kusa dashi ta taɓa mishi zuciya.

Yarinyar shi. Jininshi. Yarinya ƙwal ɗaya da ƙaddara ta miƙo mishi kuma yanzun za ta sake karɓewa. Wasu hawaye ne yana jin taruwar su da ke da wani irin ciwo.

Yana jin ‘yan ƙananan yatsunta sun matse mishi hannu gam kafin ta ce,

“Kar ka yi kuka. Please. Kawai ina son in samu wanda zan faɗa wa ne. Ba zan iya faɗa ma mumy ba. Tana cikin damuwa mai yawa ba na so in kara mata… nasan da ka zo ta ƙara sama ranta zan ji sauƙi kuma…”

Shiru ta yi. Sai da ya ɗan yi gyaran murya ya haɗiye wani yawu yana maida hawayen da ke son zubo mishi kafin ya ce,

“Kuma me?”

Sauke ajiyar zuciya ta yi.

“Kawai ina so in faɗa ma wani ina jin tsoro ne ba tare da ya ce min komai zai yi dai dai ba.”

Kai ya ɗan ɗaga mata cikin fahimtar abinda take faɗa ɗin. Shi kanshi a tsorace yake saboda me zai kasa fahimtar nata tsoron.

Sauke murya ta yi ta ce,

“Kawai ina son kowa ya zama daidai ne.”

Da sauri ya fara faɗin abinda ya san ƙarya ne.

“Za mu zama dai dai. Kina iya faɗa min ko me kike so Nana… Za mu zama dai dai… Duk da…”

Sai da ya ja numfashi a jere yafi sau uku yana fitarwa kafin ya iya ƙarasawa cikin rawar murya.

“Duk da hakan baya na nufin ba zamu yi kewar ki duk rana ba.”

Ya juyo ya ɗan kalleta yana jin yadda zuciyarshi ta rabe gidaje da dama. Murmushin da ta yi mishi sam bai rage masa raɗaɗin da ke ƙirjin shi ba.

Da gudu in aka ba shi zaɓi zai karɓi cancer ɗinta. Ya riga da ya yi rayuwa. Wannan lokacin daya kamata ace ta yi tata ne.

Sai dai zuwa yanzun idan akwai abinda rayuwa ta koya mishi shi ne bai da iko da tsari na rayuwarshi. alƙalamin ƙaddara ya riga da ya daɗe da rubuta mishi tashi.

Da wannan tunanin ya karya kwana har suka ƙarasa gida. Maigadi ya buɗe musu. Suna yin parking ɗin motar Safiyya na fitowa ta yi tsaye bakin ƙofar shiga gidan.

Kama murfin motar Nana ta yi tana sauke wani irin numfashi me nauyi tare da faɗin,

“Daren yau mai tsayine…”

*****

Kwance take tana juya text ɗin da Jabir ya yi mata tun da yammaci kan maganar Aina. Rayuwa take dubawa.

Ta lumshe idanuwanta. Ta san yana wajen Aina zance ya faɗa mata. Sai dai maimakon ta hango shi babu komai cikin kanta sai fuskar Nana.

Babu abinda take tunawa sai yanayin tashin hankalin da iyayenta suke ciki. Sai take ganin rayuwa babu wanda ta zo ma da adalci irinta.

Babu wanda ke da kwanciyar hankali irin nata tunda har tana da nutsuwar da za ta zauna tana kishi. Godiya ta shiga jeroma Ubangiji da kalar ni’imar da ya yi mata.

Ba ta san iya lokacin da ta ɗauka a haka ba. Sam ba ta ji shigowar Jabir ba sai da ya hawo kan gadon inda take ya sumbaci kuncinta.

“Honey J.”

Ta furta a sanyaye tana buɗe idanuwanta kan fuskarshi. Murmushi ta yi mishi. Ya mayar mata.

“Na ji kana Kamshi. Ko Aina ta feso maka turaren angonci tun yanzun.”

Tana kallon yadda sonta ke yawo cikin idanuwanshi. Mamakinta Jabir yake sosai. Yana kuma jin tsoro can ƙasan zuciyarshi kar sai an yi auren ta birkice masa.

Sauke murya ya yi,

“Jana. Are you okay kuwa?”

Saida ta mintsinar mishi kunci sannan ta ce,

“Me yasa kake tambaya?”

Gyara zamanshi ya yi kan gadon sosai ya kwanta rigingine kamar yadda take. Kanshi ya ja ya haɗa da nata sannan ya soma magana cikin sanyin murya,

“Na kasa yarda cewar ba kya bani matsala don zan ƙara aure. Ina jin kamar kina ɓoye komai ne a ƙasan ranki. Ina jin kamar za ki iya birkice min in anyi auren nan.”

Kanta ta juyo ta sa idanuwanta cikin nashi. Takai hannu ta kamo nashi hannun, sosai take kallonshi.

“Honey J yau na sake ganin abinda ya ƙara karya min zuciya. Yau na ga abinda rayuwa take tattare da shi mai muni da ƙunci.

Ko kafin in gani kishi na ɗawainiya da ni. Kuma har yanzun bai daina ba. Sai dai ba ni da dalilin damuwa in har ina ganin wannan soyayyar cikin idanuwanka.

Fatana ɗaya, kar wani abu ya canza ta.”

Sauke numfashi ya yi.

“Ina sonki sosai Jana. Na gode da kalar ƙaunar da kika nunamun. Allah ya sa ke ce matata har a Aljannah.”

Sosai ta ji daɗin addu’ar shi. Ita ma tata takeyi musu. Allah ya ba su zama na fahimta ya ba shi zuciyar yi musu adalci.

Hannunta ta ɗora kan cikinshi sannan ta ce,

“Ka ci abinci?”

Hannunshi ya ɗora kan nata.

“Ina zan ci abinci naki yana jirana?”

Dariya ta yi ta na miƙewa. Ta sauka daga kan gadon. Ta zagayo.  Sai da ta ranwafa sannan ta sumbaci gefen fuskarshi.

Hannu ya sa ya kama kanta ya sumbace ta a laɓɓa sannan ya yi mata raɗa a cikin kunnenta. Dariya ta yi sosai tana girgiza kai.

“Ka tashi nikam mu je mu ci abinci.”

“Duk abinda uwargida take so.”

Ya faɗi da murmushi. Girgiza kai kawai ta yi ta wuce da wata ƙaunar shi mai nauyi a zuciyarta!

*****

Ya rasa abinda yake masa daɗi a zuciyarshi. Sam tunda ya koma gida Ummi ma da ta zo tana tambaya ce mata ya yi bakomai.

Karantar da ta yi baya son surutun yasa ta ba shi waje. Ya kuma ji daɗin hakan ba kaɗan ba. Wayarshi ya ɗauko ya nemo lambar Fa’iza ya kira.

Ringing ɗin farko ta ɗaga tare da yi mishi sallama ya amsa mata ta ɗora da faɗin,

“Kowa lafiya dai ko yaya Haneef?”

“Hmm Fa’iza ya muka yi dake?”

Ya buƙata yana tuna maganar da ya yi mata tun jiya. Don sai da ya fara kiran Abdulƙadir mijinta ya roƙe shi da ya barta ta zo asibitin yau kafin ma ya yi mata magana.

Shiru ta ɗan yi kafin a ciki-ciki ta amsa shi da,

“Ka yi haƙuri yaya Haneef. In shaa Allah zan samu lokaci in zo. Kawai zuciyata ce ta kasa haƙura wallahi.”

Dafe kai Haneef ya yi. Yau ya ga rayuwa ba komai bace ba. ‘Yar yarinya ma kenan da ba ta da wani zunubi mai yawa Allah ya ɗora mata wannan ina ga su.

“Fa’iza ki ji ni. Gaba ɗaya rayuwar nan ba ta da tsawo. Mu dukanmu munyi kuskure da muka zaɓi mu share Fu’ad kamar yadda ya yi mana. Da ya mutu fa? Ban faɗa miki ‘yarshi bata da lafiya ba?’ Yar ƙarama ce. In kika ganta za ki sota sai dai cancer take fama da.

Allah bai yi rayuwarta za ta yi tsayi ba. Fu’ad na buƙatar soyayyarmu ne ba fushin mu ba Fa’iza.

Don Allah ku yafe mishi ya ji da abu ɗaya.”

Yana jin yadda ta amsa da,

“In shaa Allah.”

Da ƙyar sannan ta kashe wayar ya san kuka take. Sauke wayar ya yi yana tunanin yadda rayuwa za ta iya birkice maka cikin ƙanƙanin lokaci.

*****

Tunda Ansar ya zo suke zaune su duka huɗun a falon an rasa wanda zai fara magana.

Nufin Safiyya su dukansu in Nana tana ganin su za su iya comforting ɗinta. Amma abin ya gagara. Rashin iyayenta zafin shi daban ne a zuciyarta.

Ba ta san asalin ciwon da zuciya zata iya ji ba sai yanzun. Ta san babu wanda zai fahimce ta sai wadda tasan daɗin haihuwa.

Sai wadda ta san me rayuwa da ɗa yake nufi. Ɗan da ka raina har tsawon shekara goma sha ɗaya. Ko jariri ne ka rasa hakan naday ciwo sosai balle wanda irin wannan shaƙuwar ta shiga tsakaninku.

Miƙewa daga kan kujera Nana ta yi inda take zaune kusa da Fu’ad. Yana kallonta ta taka har ta ƙarasa inda Sofi ke zaune kan kafet ta yi shiru.

Zama Nana ta yi ta na matsawa sosai kusa da Safiyya. Hannuwanta ta buɗe ta rungume ta. Sosai ta matse Sofi a jikinta.

Wani irin kuka marar sauti ne ya ƙwace ma sofi. Ita ya kamata ta yi wa Nana wannan ba wai ita ta lallashe ta ba.

Tissue ɗin da ke hannun Ansar ya sa yana goge idanuwanshi da yake jin sun kawo hawaye.

Ba zai manta shekaru huɗu kenan da ƙaddara ta haɗa shi da Safiyya ba. Ta je neman aiki a kamfanin da yake aiki.

Tun daga ranar ta shiga zuciyarshi. Hakan bai ƙaru ba sai lokacin da ya ga Nana. Ita ce sanadin shaƙuwar su da Safiyya har ya ji labarinta.

Nana ta haɗasu. Ba zai manta yarinyar ba da lafiyarta. Yarinyar da duk wanda zai ganta sau ɗaya zai jima bai mantata ba.

Ba zai manta shekaru biyu da sanin su da ya yi ba Nana ta fara wannan rashin lafiyar. Yana tare da su a duk lokacin nan.

Duk da bai yi aure da wuri ba. Kuma matarshi har yanzun Allah bai azurta su da samun haihuwa ba tun bayan ɓarin da ta yi bai hana shi jin Nana kamar ‘yarshi ba.

Yana ƙaunar yarinyar har ranshi. Kuma ko shi ya sa rai da samun lafiyarta. Sai yau ɗin nan da Safiyya ta faɗa mishi.

Sosai abin ya taɓa shi. Yanzun kam ganin yadda suke manne da juna da Safiyya ya ƙara karyar mishi da zuciya sosai.

Fu’ad kallon su yake. Yana ƙoƙarin tarbe nashi hawayen. Zai zama strong for Nana. Ta roƙi hakan daga wajen shi. Bai taɓa ganin yarinya mai ƙarancin shekaru irinta ba tunda yake.

Duk da dai ba wai ya ga yara da yawa bane. Yana jin ita ɗin ta dabance ba kuma don tana jininshi ba. Ansar yake kallo yadda gaba ɗaya ya birkice.

Sai yanzun ya ga tsantsar ƙaunar da yake wa Nana. Kuma zuciyarshi ba za ta taɓa manta wannan ba. A hankali Nana ta janye jikinta daga na Safiyya.

Ta sa hannu tana goge mata fuska. Kafin ta miƙe. Wajen Ansar ta nufa da yake kan kujera a zaune. A tsayen da take ta buɗe hannuwanta shi ma ta yi hugging ɗin shi.

“I love you. I love you so much Uncle Ansar.”

Take faɗi cikin kunnuwanshi. Kai kawai yake ɗagawa yana riƙe ta a jikinshi a hankali.

Saboda yana jin kalar ramar da ta yi ta cikin rigarta. Ji yake da ya matse ta sosai zai iya karyata. Ɗagota ya yi ya sumbaci goshinta da kuncinta kafin ya sake riƙe ta a jikinshi.

Magana ta yimishi cikin kunne yadda shi kaɗai zai ji.

“Can you do me a favour?”

Muryarshi a dakushe shi ma cikin raɗa ya ce,

“Ko mene ne ki faɗa Nana.”

Sai da ta sauke ajiyar zuciya yana ji kafin ta ce,

“Ba ni da lokaci mai yawa. Ina son maida aurensu mummy. Kana son mumy kai ma ko?

Na san ba za ka ji daɗi ba.”

‘Yar dariya Ansar ya yi. Tabbas Nana ta koyar da shi abubuwa da yawa. Ciki har da ƙarfin hali. A hankali ya amsa ta da,

“Umm Nana ba zan iya da dadynkin nan ba. Na bar mishi.”

Dariya ta yi cikin kunnenshi da ya sa shi dariya shi ma. Tun daga sanda ya san Safiyya ya karanci wajen mutum ɗaya take da shi a zuciyarta.

Ko da yana sonta dole zai haƙura. Ƙaunar da yake mata yana jinta kamar ‘yar uwarshi ne. Nana ta katse mishi tunaninshi da faɗin,

“You are the best Uncle Ansar. I love you.”

Lumshe idanuwanshi ya yi. Rashinta zai bar wani waje mai girma a zuciyarshi.

“I love you more Princess ɗin mumynta.”

Fu’ad kam ji yake dama shi aka runguma haka. Ko ta ina buƙatar lallashi yake. So yake wani ya lallashe shi har sai ya fitar da dukkan ciwon nan da yake cikin zuciyarshi.

Sai yanzun ya fahimci abin da Nana ta ce da ta faɗa mishi tana tsoron mutuwa. Ba tsoro take ji wa kanta ba.

Tana tsoron abinda mutuwarta za ta yi wa wanda take ƙauna. Zai iya rantsewa Nana ta dabance. Komai nata. Maganganunta da hankalinta ya girmi shekarunta nesa ba kusa ba.

Tana tsoron abinda mutuwarta za ta yi wa mamanta. She is the strongest girl da ya taɓa gani a rayuwarshi.

Yana kallo tana takowa zuwa inda yake. Sai dai yasan ko zuciyar da take da ƙwari irin tata tana buƙatar tallabi.

Ƙoƙarin saka kanshi yake a matsayinta ya kasa gane me zai ji ace yau yasan a hankali a hankali komai nashi na lalacewa.

A lokaci ɗaya kuma yana jin ya kamata ya zama strong saboda halin da zai saka wanda yake ƙauna a ciki amma ya kasa fahimta.

Harta ƙaraso kusa da shi ƙirjinshi kamar an kunna mishi wuta saboda zafin da yake masa. Goshinta ta haɗa da nashi tana tallabar fuskarshi da hannuwanta.

Yasan ƙwarin gwiwa take son samu daga wajen shi. Duk yadda yake jin kamar numfashin shi zai tsaya bai hana shi yin alƙawarin zai zamar mata abinda take buƙata ba.

Bashi da wani abu da zai ba ta. Yana jin hucin numfashinta da take fitarwa akan fuskarshi ya ƙi yarda su haɗa idanuwa saboda baya son taga raunin da yake da shi.

“Na gaji sosai. Bacci nake ji.”

Ta faɗi muryarta na wani irin sauka ƙasa sosai. Bashi bane a matsayinta amma a gajiye yake. Sai da ya sa hannuwanshi ya ɗorata kan kafaɗarshi sannan ya miƙe da ita.

Ɗakin da ya kaita rannan ya nufa. Bai ajiyeta ko ina ba sai kan gadon a hankali. Ya gyara mata kwanciya. Ya zauna gefen gadon.

Idanuwanta ta lumshe ta ɗora hannunta kan cinyarshi tare da faɗin,

“Dady!”

Sai da kalmar ta amsa yafi a ƙirga a cikin kunnuwanshi sannan ta samu wajen zama a zuciyarshi. Wani irin abu ya ke ji da bazai faɗu ba.

Sai maimaita kalmar yake yi. Cikin kanshi yana jin tana zama wajaje da yawa. Bai san yana buƙatar jin ta kira shi haka ba sai yanzun.

Da sauri yasa hannu yana goge hawayen da yake jin kamar su fito mishi don baya son ta buɗe ido ta gani. Jin ya yi shiru yasa ta faɗin,

“Zan iya kiranka dady?”

Da sauri ya ce,

“Zan fi kowa sa’a in kika kirani haka Princess.”

Murmushi ta yi tare da yin hamma. Ta yi shiru yana kallon yanda numfashinta ya canza alamar bacci ya ɗauketa. Gyara mata hannunta ya yi.

Ya miƙe ya zuba mata idanuwa na wani lokaci. Baya son fita daga ɗakin, yana son ya kalleta sosai. Ya yi ta kallonta kafin ta bar shi.

Sai dai a yanzun yana buƙatar ya ɗan jinyaci ciwukan da ke ƙirjinshi ko da na ‘yan awanni ne. A hankali ya fice daga ɗakin yana ja mata ƙofar.

Bai san yana riƙe da wani numfashi ba sai yanzun da ya sauke shi. Inda ya bar su Safiyya nan ya same su. Kanshi a ƙasa ya nufi ƙofa sannan ya ce musu,

“Ta yi bacci.”

Bai jira amsar da za su bashi ba ya fice daga ɗakin!

<< Akan So 35Akan So 37 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×