Sosai ya riƙo Zee jikinshi.
"Na gode sweetheart. Ban taɓa zaton za ki fahimce ni ba."
Hawayen daya taru a idanuwanta ta ji ya zubo. Ta sa hannu ta goge su. Muryarta can ƙasa ta ce,
"Haba Dee. Da zuciya a ƙirjina fa. Waye zai ƙi fahimtar ka."
Har cikin ranshi Lukman yake jinta. Bai san wanne kalar so Zainab ke masa ba. Zai iya cewa ya fi kowa dace da mata irinta.
*****
Zaune yake ya haɗa kanshi da gwiwa. Ba zai ce ga iya abinda yake damun shi ba. Komai ciwo yake mishi. Tun daga zuciyarshi. . .