Skip to content
Part 38 of 48 in the Series Akan So by Lubna Sufyan

Kwance yake shi kaɗai a ɗaki. Ya kira lambar Nuriyya a kashe. Yau kwana uku kenan da rasuwar Nawaf. Bai samu ya yi magana da ita ba. Yana son ya ji yadda take. Shi kanshi da ya ga Nawaf na mintina rasuwar ta tsaya mishi a rai sosai.

Lumshe idanuwanshi ya yi. Kamar hoton film rayuwarsu ta wani lokaci ta faɗo mishi.

Years Back

Kitson da ake mata ta ce a barshi haka, za ta zo gobe da Safe a ƙarasa mata.

Mai kitso ta ce,

“Maman Farhan da kin bari an gama, saura Kaɗan a gama.”

Ta ce,

“Aa, yanzu maigidana ya shaida min yana kan hanyar gida, kar ya zo gida ya iske ba na nan, zan dai dawo gobe.”

Da sauri ta saka mayafinta ta fito daga saloon ɗin ta ja Motarta ta nufi gidanta da ke ƙasan layi.

*****

Zaune yake kan Motarshi,  Fuskar shi ba annuri a ɗaure kamar zakin da ya kwana huɗu be ci abinci ba, tana shiga gidan gabanta ya yanke ya faɗi bisa ganin shi.

Ƙirƙiro Murmushi ta yi ta ƙarasa gunshi da,

“Welcome Dear you are home Already.”

Mugun kallon da ya jefeta da shi ne ya sa hanjin cikinta kururuwa.

“Daga gidan Uban wa kike?”

Ɗankwalin kanta ta zame, baki na rawa ta ce,

“Daga gidan kitso nake, kuma ai na maka text.”

Gashin kanta ya damƙa, ta tsandara ihu, zafi ya sa ta kiran sunanshi,

“Muhammad don Allah ka yi haƙuri, you are hurting me.”

Be saurareta ba ya ja ta har falo inda ya yasar da ita a ƙasa kamar shara.

Kuka take yi sosai, ga zafin kitson ga kuma na jan gashi. Belt ya shiga zarowa, ta san dawan garin, ta yi sauri tashi za ta gudu ya sa ƙafa ya taɗe ta, ta fadi ƙasa, wani ihu ta saka.
Muhammad be ji tausayin ta ba haka ya shiga lafta mata wannan belt ɗin kamar Allah ya aiko shi, sai da ya gaji don kanshi kafin ya bar ta.

*****

Straight Islamiyyar su Farhana ya nufa, ya ci sa’a ko sun tashi, dama abunda baya so ya zo ya yi ta jira, da gudu ta ƙaraso gunshi tana faɗin,

“YaYa Farhan, ina ta jiranka.”

Murmushi ya yi ya ce,

“Sorry mu je gida.”

*****

Tana jin dawowar su ta yi saurin tashi don shiga ɗakinta, ba ta kai ga shiga ɗakin ba ta ji Farhana a jikinta.

“Mummy, me ya sameki?”

Rasa abin da za ta ce mata ta yi, ta fara kame-kame.

Daga nesa Farhan ya ƙare mata kallo, fuskarta duk bruises ya matso kusa da ita a nutse yace da ƙanwarshi,

“Farhana je ki cire Uniform ɗinki.”

Ba gardama ta ɗauki jakarta ta yi ɗaki.

“Mummy, Daddy ya sake dukkan ki ko?”

Ta shiga girgiza kai ta rasa amsar da za ta bashi, a fusace ya ce,

“For how long za ki cigaba da jure dukkan da yake miki?”

Jiki a sanyaye ta ce,

“Ka yi haƙuri, zai bari.”

A fusace ya ce,

“Till when zai daina dukkanki? Sai kin aurar damu? Mummy shekaru na sha takwas, tun ina Shekara 4 nake ganin yana cin zarafinki, Allah kaɗai ya san tsawon lokacin da kika yi cikin wannan halin, Mummy put an end to this please.

Ki kai shi ƙara, bai fi ƙarfin hukuma ba, akwai Agency na Women Rights and Child Abuse, he’s been abusing us all for quite a long time, Mummy I hate seeing you like this.”

Murmushin takaicin ta yi ta ce,

“Farhan I cannot, ni ba kowa bace face marainiyar Allah, banda kowa, banda wanda zai tsaya min, Kai da ƙanwarka ne farincikina, I can endure all this for you, so everything is going to be fine.”

Takaici ya hana Farhan magana, ya saba jin wannan maganar daga gun mahaifiyarsa, haushi ya sa shi fita daga falon.

*****

Wayarshi da ta yi ringing ta katse mishi tunanin da yake yi. Ya ɗauko ya duba. Ɗan guntun tsaki ya ja ganin ba kowa bane MTN ne, sai ka ce za su bashi wata tsiyar.

Miƙewa ya yi da wani nauyi a zuciyarshi ganin lokacin sallah yayi. Yana son yin wani abu wa matan da ke cikin rayuwar domestic abuse sai dai bai san ta inda zai fara ba.

Da wannan tunanin a zuciyarshi ya fita masallaci.

****

Yana riƙe da hannun Nana da sallama suka shiga babban falon a tare. Momma ta amsa su.

Ƙwace hannunta Nana ta yi daga cikin na Fu’ad ta ruga da gudu tana faɗin,

“Granny…”

Da fara’a Momma ta riƙo Nana jikinta. Fu’ad kam yarinyar da ke zaune ƙasa tana wasa yake kallo. Ta mishi kyau ba kaɗan ba.

Karasawa ya yi yasa hannu ya ɗauketa ya kwantar da ita kan kafadarshi. Ya haɗa fuskarshi da ta yarinyar yana rocking ɗinsu a hankali.

Yadda ta yi luf yake jin abin har cikin zuciyarshi. Lumshe idanuwanshi ya yi yana jin ƙamshin ‘yar yarinyar da bai san na mene ne ba. Powder ce ko turare.

Muryarshi can ƙasa ya ce,

“Momma babyn wace ce?”

Kallon shi take yadda ya lumshe ido yana jijjigasu shi da babyn. Ta kalli Nana da ke jikinta. Gaba ɗaya sai tausayinshi ya cika mata zuciya.

Da sanyin murya ta ce,

“Arfat. ‘Yar Fa’iza ce.”

Buɗe idanuwanshi ya yi yana ware su kan Momma. Zuciyarshi ta yi wata irin dokawa. Sauko da yarinyar ya yi daga kafaɗarshi da ta soma bacci.

Hakan ya sa ta fara kuka. Kallonta yake sosai. ‘ Yar fara ga wasu kumatu. Jijjigata yake ta ƙi yin shiru. Ya buɗe baki zai yi magana.

Fa’iza ta fito daga hanyar da ya san ta kitchen ce hannunta ɗauke da feeder tana ɗaure murfin.

Tsayawa ta yi cak. Idanuwanta na kan Fu’ad. Shi ma kallonta yake. Wani miyau ya haɗiya. Za ka rantse Arfat ta san akwai wani abu da ke faruwa da ya fi kukan da take muhimmanci.

Shiru ta yi. Kallonta yake. Kamar ba Fa’izar da ya sani ba. Ta yi girma sosai. Buɗe baki ya yi,

“Fa’iza…”

Bai ma san maganar bata fito ba. Ita da ke tsaye daga nesa za ta iya karantar sunanta akan laɓɓan shi duk da bai fito ba. Shekaru sha ɗaya. Ya sa ƙafa ya fice ya bar su ba tare da ya juyo ba. Wani abu ya tsaya mata a wuya. Miƙewa Momma ta yi ta kama hannun Nana.

“Zo mu je…”

Ba musu Nana ta miƙe tana riƙe da hannun Momma. Don sam ba ta kula da Fa’iza ba, suka nufi sashin Momma a tare.

A hankali Fa’iza take takowa tana jin yadda idanuwanta ke cika da hawayen da ta ƙi bari su zubo. Ƙarasowa inda yake ta yi.

Hannu ta miƙa za ta karɓi Arfat. Ga mamakinsu yarinyar ƙara maƙale wa Fu’ad ta yi. Dariya ya yi yana buɗe idanuwanshi.

Kallon Arfat Fa’iza ta yi ta daƙuna fuska.

“Baki san Uncle ɗinki bai damu da mu ba kike maƙale shi ko?”

Wani abu ya ji a ƙirjinshi da maganarta.

“Faiza…”

Ya faɗi da wani irin yanayi. Cikin idanuwa ta kalle shi.

“Shekara sha ɗaya. Ko ka ɗauka weeks ne?”

Ya rasa me zai ce mata. Arfat ta karɓe daga hannunshi da ta soma kuka. Ta samu waje kan kujera ta zauna tana lallashinta.

Gabanta ya tsugunna yana wani dafe kai.

“Fa’iza. Please…”

Sai lokacin hawayen da take riƙewa suka zubo. Muryarta ɗauke da ɗacin da take ji ta ce,

“Da sai wani cikin mu ya rasu za ka dawo? Ba ka taɓa tunanin ka waiwaye mu ba ko sau ɗaya. Why? Laifin da muka yi maka ya yi girma har haka? Da bro Lukman bai kiraka ba ba za ka taɓa dawowa ba ko? Ka manta kana da ‘yan uwa? Ko baka son mu ba ka tunanin mu muna sonka? Bro ko…”

Hannunta ya kama da sauri yana katse mata abinda ta yi niyyar faɗi. Idanuwanshi ya sauke cikin nata. Yana so taga nadamar da ke cikinsu. Yana so ta ga yadda girman ƙaunarsu yake a zuciyarshi kafin ya ce,

“Ni mai kuskure ne Fa’iza, banda abinda zan faɗa. Ki yarda da ni, da ina da iko da na koma shekaru sha ɗaya na gyara komai.

Ina biyan kuskuren da na aikata da zuciyata Fa’iza…ki yafe min.”

Hannunta ta sa tana goge fuskarta. Ta riga ta yafe masa. Duk da za a ɗauki lokaci kafin ta daina jin ɗacin laifin shi.

Jin ta yi shiru ya sashi faɗin,

“Ki yafe min. Ban ce ki manta ba…”

Katse shi ta yi da faɗin,

“Na yafe maka bro. Ka yafe min nima. Da na kiraka. Dukkanmu muna da laifi. ‘Yan uwantaka abu ne mai girma. Zumunci abu ne da bai kamata ɓacin rai ya yi sanadin yankewarshi ba.

Ɗaya daga cikinmu ya kamata ya ajiye ɓacin rai ya nemi ɗaya. Duk ba mu yi hakan ba.

Yanzun sai mu duba gaba….”

Kai yake jinjina mata alamar duk ya ji abinda ta ce, don ya ji ɗin. Baya son ko tunanin abinda zai sa ya nisance su yanzun.

Komawa ya yi kan kujera gefen Fa’iza ya zauna. Arfat take kallo.

“She is so cute…”

Miƙa mishi ita ta yi. Ya karɓeta. Hannuwanta ta sa tana sake goge fuskarta. Da ɗan murmushi ta ce,

“Sauran will love to meet you.”

Dariya Fu’ad ya yi.

“Su nawa?”

“Su huɗu…”

Ware idanuwa ya yi suka yi dariya gaba ɗaya.

“Akwai Kabir da muke kira (Amir) yana da sunan in-law ɗina. Sai Yassar da Yasir, Ridwan sai Arfat gata nan.”
Da mamaki Fu’ad ke kallonta.

“Kina da twins?”

Ta ɗaga mishi kai. Lokaci ɗaya fuskarshi ta canza. Muryarshi can ƙasa ya ce,

“Na yi missing abubuwa da yawa…”

Yadda ya yi maganar ya taɓa mata zuciya ba kaɗan ba. Cikin taushin murya ta ce,

“Make sure bakai missing wani abu ba nan gaba, okay?”

“Damn right…”

Dariya suka yi gaba ɗaya. Lokacin da suka ji sallama. Su duka suka ɗaga kansu zuwa hanyar shigowa falon. Hassan ne. Yana ganin Fu’ad ya yi baya zai koma. Da sauri Fu’ad ya miƙa wa Fa’iza Arfat yana binshi da gudu.

“Hassan…”

Bai tsaya ba. Asalima ƙara sauri ya yi ba tare da ya juyo ba. Yana jin takun Fu’ad ɗin ya ƙaraso inda yake. Hannu ya sa kan kafaɗarshi yana juyo da shi.

Fuskar Hassan babu annuri ya ce,

“Sannunka.”

Yana sake juyawa. Lumshe idanuwa Fu’ad ya yi. Ya sake juyo da Hassan. A ƙufule ya ce,

“Hit me! Yell at me in kana so. Buh’ for goodness’ sake ka daina min kamar baka taɓa sani na ba.”

Ture shi Hassan ya yi da hannuwa duka biyun tare da faɗin,

“Da gaske ba ka so? Ba ka son ina yin kamar ban sanka ba? Ka sa ƙafa ka bar mu? Ko ance ba zuciya a ƙirjinmu kamar kai ne?

Saboda me za ka dawo ka san ba zama za ka yi ba. Ka tuna mana yadda muke ƙaunarka ka sake tafiya ko me?”

Har wani huci Hassan yake. Komai na rayuwarshi. Tun tasowarshi duk wani burinshi bai wuce na ya zama kamar Fu’ad ba.

Shi kaɗai yasan abinda tafiyar Fu’ad ta yi mishi. Ta yi musu gaba ɗaya. Sosai Fu’ad ya kalle shi.

“Babu inda za ni Hassan. Ba inda zan sake zuwa. Kaima ka yafe min mana ko zan ji sauƙi a rayuwata.”

Wani kallo Hassan yake mishi cike da rashin yarda kafin ya juya.

Hannunshi Fu’ad ya riƙo.

“Hassan…”

Juyowa ya yi yana zame hannunshi daga na Fu’ad, murya a gajiye ya ce,

“Ka ƙyale ni. Please ka bar ni kawai…”

Girgiza kai Fu’ad yake. Ya ga abinda ƙyaliya ta yi mishi a baya, baya fatan tarihi ya sake maimaita kanshi.

“Ba zaka iya yafe min ba Hassan? Zan fahimceka in ba za ka iya ba? Ka faɗa min cikin idanuwa sai in sani. Ka faɗa min ba za ka iya sake ba ni damar zama yayanka ba.”

Girgiza mishi kai Hassan yake fuskarshi ɗauke da wani yanayi mai wahalar fassarawa. Murya a sarƙe ya ce,

“Kullum har shekara biyu ni da Hussaina sai mun zauna. Mun yi tunanin laifin me muka yi maka mu. Saboda me baka neme mu ba? Laifin Abba ne ya shafemu ko me?

Mun kiraka daga farko bama samu. Muka gaji muka daina. Hirar ka ma muka bari kamar yadda kai ma ka watsar da mu.

Ka yi haƙuri idan ba na son ganinka yanzun. Ban ce ba zan yafe maka ba. Amma zai ɗauki lokaci.”

Haɗe hannayenshi Hassan ya yi waje ɗaya yana ɗorawa da,

“Please ka ɗan bar ni tukunna.”

Kai Fu’ad ya ɗaga mishi ba don ya so ba. Ba don bai ji ciwon maganganun Hassan ba. Sai don a kwana biyun nan ya fahimci mene ne asalin rayuwa. Ya soma koyan ɗora buƙatar wasu akan tashi. Cikin sanyin murya ya ce,

“Bakomai Hassan. Na fahimta ko da ban so hakan ba. Sai dai ina son ka ga Nana.

Ina da duk lokacin da nake buƙata. Ba ta dashi…”

Da mamaki Hassan ke kallonshi. Don sam ya ƙi zama ai mishi maganar Fu’ad ɗin. Momma ta fara ya bar mata wajen sai ta ƙyale shi.

“Wace ce Nana?”

Ɗan murmushin nasara Fu’ad ya yi tare da faɗin,

“Mu je cikin gida ka ganta…”

Ba musu Hassan ɗin ya bishi suka koma cikin gida. Tsaye ya yi bai zauna ba. Fu’ad ya nufi ɓangaren Momma ya taho da Nana.

“Ina su Amir?”

Ya tambayi Fa’iza.

“Suna gida. Za su zo muku hutu in sun gama exams Ai.”

A sanyaye ya ce,

“Allah ya kai mu.”

Ɗago kan da zai yi ya sauke idanuwanshi kan Nana. Kallonta yake sosai kafin ya maida kallonshi zuwa kan Fu’ad.

Kamanninsu yake gani ƙarara. Yana tunanin in bai manta ba ance Fu’ad ba zai iya haihuwa bane ko me? Sanadin hakan ne ma har ya bar gida.

Kallon Nana Fu’ad ya yi ya ce mata,

“Ga Uncle Hassan.”

Kallonshi Nana take. Ta kalli Fu’ad tana ware idanuwa a hankali ta ce,

“Kuna kama Daddy.”

Murmushi Fu’ad ya yi.

“He is ma’ lil bro.”

A hankali ta taka ta ƙarasa wajen Hassan. Fa’iza ma kallonta take don sai yanzun ta ganta. Labarinta kawai ta ji wajen su Haneef.

Kama hannun Nana Hassan ya yi da ta miƙo mishi.

“Ina wuni…”

Shafa kanta ya yi yana rasa me zai ce mata. Gaba ɗaya abubuwan sun masa yawa cikin kai. Da ƙyar ya iya ce mata.

“Nana. Zan zo mu gaisa sosai, okay?”

Kai ta ɗaga mishi.  Ya ɗan mata murmushi ya saki hannunta yana ficewa daga ɗakin. Wajen Fa’iza Nana ta koma ta gaishe da ita tana tallaban kumatun Arfat.

“Ina son ƙanwa nima. Amma banda ita. Duka ‘yan class ɗinmu suna da fa.”

Kallon Fu’ad Fa’iza ta yi ya ɗan ɗaga mata kafaɗa. In dai Nana ce yanzun ta fara jin maganar da ba ta da amsarta a bakinta.

Momma ce ta fito daga ɗaki. Fu’ad ya kalli agogon hannunshi ya kalli Momma tare

da faɗin,

“Yamma na yi Momma.  Za mu tafi. “

“Dady…”

Nana ta kirashi cike da alamun ba ta so a tafin. Daƙuna mata fuska ya yi ta maƙe mishi kafaɗa itama tana daƙuna tata fuskar alamar ba ta gaji bafa.

“Ba zaka bari abbanku ya dawo ba. Yana son su gaisa da Nana.”

“Zan dawo da ita gobe in Allah ya kaimu. Za ta wunin muku anan ma.”

Jinjina kai Momma ta yi.

“Allah ya kaimu. ‘Yar tsohuwa me an dafa miki?”

Dariya Nana ta yi ta ce wa Fa’iza,

“Anty don Allah ba granny bace tsohuwa? Kin ji wai ni ce tsohuwa.”

Dariya Fa’iza ta yi.

“Ki ƙyale granny ta ga kin fita kyau ne.”

Kallon Momma Nana ta yi tana jijjiga kai alamar kin gani, na fi ki kyau. Dariya ta basu gabaki daya kafin Fu’ad ya ce,

“Taso mu tafi.”

Sumbatar Arfat ta yi a goshi kafin ta miƙe da faɗin,

“Anty za ku zo gobe?”

Girgiza mata kai Fa’iza ta yi. Langaɓe fuska Nana ta yi.

“A kawo babyn nan to. Ya sunanta?”

“Arfat sunanta. Ai dole ma in kawo miki ita. Ƙanwarki ce. Kin ga in ‘yan class ɗinku sunce suna da ƙanwa kema ki ce ƙannenki da yawa. Su biyar ne.”

Riƙe baki Nana ta yi cike da jin daɗi.

“Su ma za a kawo su?”

Fa’iza ta amsata da,

“Eh su ma za su so su ga Anty Nana.”

Ƙarasawa ta yi wajen Fa’iza ta yi hugging ɗinta. Cikin kunne ta ce mata,

“Na gode Anty.”

Ta sake Fa’iza da ke cike da mamakin Nana. Bata taɓa ganin yarinya cike da ƙauna irinta ba.

Za ta iya rantsewa yarinyar ta dabance a cikin halittu. Dubi yadda ta manne mata a zuciya daga ganinta. Lumshe idanuwanta ta yi da ta tuna abinda ke tattare da Nana.

Tana kallonta har ta ƙarasa wajen Momma ta yi hugging ɗinta tare da faɗin,

“Sai gobe. Zan zo da camera ɗina mu yi video.”

Ta saki Momma ta ruga wajen Fu’ad da ke tsaye tasa hannunta cikin nashi. Ya kalli Momma da tace musu,

“Ka gaishe da Safiyya.”

Ya jinjina kai.

“Za ta ji. Fa’iza sai mun yi waya.”

Kai ta ɗaga mishi. Ya ja hannun Nana da ta ke waige tana ɗaga ma Arfat hannu suka fice.

*****

Baby dream ya biya da Nana ya shiga kwasar mata kayayyaki daga na sawa zuwa takalma.

Kamo hannunshi Nana tayi ya juyo ya kalleta yana mayar da hankalinshi kan wasu takalma da sukai mishi kyau. Sake janyo hannunshi ta yi.

“Daddy…”

Ɗauko takalman ya yi ya miƙo mata tare da faɗin,

“Na’am, sa wannan ki gani zai miki.”

Karɓa ta yi ta mayar inda ya ɗauko su. Ya daƙuna mata fuska. Ta ware mishi idanuwanta.

“Ya isa haka. Mu tafi gida…”

Girgiza kai ya yi.

“Sai mun ƙara…”

Yana tunanin yadda ya rasa shekaru goma sha ɗaya na siya mata abubuwa. Ya san ba zai iya biyansu ba amma yana so ya kamanta.

Sosai Nana ta shagwaɓe mishi fuska.

“Na gaji daddy. Na gaji sosai.”

Hannu ya sa ya riƙo fuskarta. Yana feeling goshinta da wuyanta ko da zazzaɓi. Sauke numfashi ya yi da ya ji babu. Babu shiri ya ja ta da kwandon da suka zuba kaya zuwa wajen biyan kuɗi.

Tunawa ya yi da alƙawarin da ya yi wa Junior ya ce ma Nana ta jira shi anan karta je ko’ina. Ya koma ciki ɓangaren kayan wasan yara ya ɗauko ma Junior mashin ya dawo.

Credit card ɗinshi ya bayar don ba shi da cash a hannunshi suka cire kuɗinsu aka ɗaukar musu zuwa bayan mota.

Kiran sallar magrib ya ji ya lumshe idanuwan shi. Buɗe motar ya yi Nana ta shiga. Ya ɗan tsugunna ya ce mata.

“Idan na barki na je na yi sallah ba komai?”

Kai ta ɗaga mishi tana lafewa jikin kujerar. Ɗazun da take ce ma Fu’ad ta gaji don ya bar siyayyar da yake yi ne.

Da gaske gajiyar take ji yanzun. Ko ina na jikinta ciwo yake. Ganin yana tsaye har lokacin yasa ta ce,

“Really. Ka je ka dawo. I will be okay.”

Sumbatar goshinta ya yi. Ya rufe murfin motar ya wuce masallaci. Acan ya samu buta ya yi alwala.

*****

Sanda ya dawo ya zagaya ya buɗe motar Nana ta yi bacci. Fasa zama ya yi ya zagayo ɓangaren ta ya ɗauketa.

Bayan motar ya mayar da ita ya kwantar sannan ya dawo ya shiga ya kunna motar. A hankali yake tuƙin don baya so ya shiga wani rami da zai sa ya yi tsalle ya tashe ta.

*****

A kafaɗa ya saɓi Nana tana ta bacci. Ya ƙwanƙwasa. Safiyya ta zo ta buɗe mishi jikinta sanye da shadda light blue ɗinkin doguwar riga da ya karɓi jikinta sosai.

Sauke ajiyar zuciya ya yi. A ɗan daburce ta ce mishi,

“Sannu. Bacci ta yi.”

Kai ya iya ɗaga mata a yanayin da yake jinshi. Nana ta zo karɓa ya girgiza mata kai.

“Sai kin yarda min da yarinya.”

Raɓa ta ya zo yi. Ta matsa mishi ya wuce tana bin bayanshi.

“Duka Nana ɗin nawa take da ba zan iya ɗaukarta ba?”

“Oh-Oh yaushe kikai ƙwarin ɗaukar Nana ɗin? Ke kanki kina buƙatar ɗaukar.”

Kallonshi take da mamaki. Fu’ad ya rainata. Ya wuce ya kwantar da Nana kan gadon ya cire mata takalma ya gyara mata kwanciya.

Zuwa ya yi ya wuce Safiyya ya fice daga gidan. Da kanshi ya shiga kwaso ledojin siyayyar da suka yi yana shigowa da su cikin falon.

Sai da ya gama tas. Sannan yace ma Safiyya,

“Ki shirya Nana gobe wajen ƙarfe goma zan kai ta wajen su Momma. Kema ki shirya za mu je wani waje.”

‘Yar dariya ta yi dake nuna wasa kake ko? Ganin fuskarshi ta yi ko murmushi babu. Hakan ya sa ta faɗin,

“Wai da gaske kake?”

“Yep”

Ya faɗi yana jan P ɗin. Haɗe fuska ta yi.

“Ina da abinyi. Beside banga me zai sa na bika wani waje ba. Nana ɗin dai zan fahimta saboda Momma. Ka zo ka ɗauketa.”

Idanuwa ya tsareta da su da yasa ta fara jin duk ta takura, a dake ya ce,

“Ki shirya ƙarfe goma.”

Bai jira amsarta ba ya juya.

“Fu’ad ba fa inda zan je.”

Ko saurarenta bai ba ya fice daga ɗakin. Ta juya idanuwanta. Ta ga alama yana jin daɗin ganin ranta ya ɓaci. Kayayyakin da ya ajiye ta zo ta shiga dubawa. Kayan sawa ne da takalma lodi guda. Tana mayar dasu kamar daga sama ta ji Nana na faɗin,

“Munmy…”

Juyawa ta yi ta kalli Nana da ke murza idanuwanta da hannu.

“Ina dady?”

A sanyaye ta ce,

“Ya tafi ba daɗewa.”

Dafa kafaɗar Safiyya ta yi ta zagayo tana zama.

“Bacci nake ji.”

Ta faɗi. Murmushi Safiyya ta yi.

“Baccin ki ke ai kika tashi Nana.”

Muryarta cike da baccin da take ji ta ce,

“Banyi sallar magrib ba fa. Kuma ga isha’i.”

Dan shiru Safiyya ta yi.

“Tam tashi maza. Ki yi sallah sai ki zo ki ci abinci ki sha magunguna ki kwanta.”

“Na ci dambun nama wajen granny. Bana jin yunwa.”

Jinjina mata kai Safiyya ta yi tana maida hankalinta kan kayan da ke baje a falon.

“Sun yi yawa ko?”

Nana ta tambaya a sanyaye. Shiru Safiyya ta yi, ba ta san amsar da za ta bata ba. Ta ɗora da faɗin,

“Wasu ma ba zan saba. Na kasa faɗa mishi ne saboda na ga yanata so ya siya min.

Wai zamu koma a ƙara. Mumy ko za ki faɗa mishi sun isa?”

Hannu safiyya ta kai ta ɗan ja mata hanci saboda yadda take jin idanuwanta na cika da hawaye da gaskiyar maganganun Nana ɗin.

“Oya tashi mu je tare. Nima ban yi sallar isha’i ba.”

Miƙewa Nana ta yi.

“I love you mum.”

Murmushi Safiyya ta yi mata. Suka shiga bedroom ɗin tare.

*****

Ja musu bargo Safiyya ta yi tare da yi musu addu’a cikin sanyin murya Nana ta ce,

“Mummy in roƙe ki wani abu?”

“Ko me Princess ke so.”

Cewar Safiyya. Sauke numfashi Nana ta yi.

“Bana so in ɓata miki rai. Ki min alƙawari za ki duba magana ta. Ba za ki ji haushina ba.”

Da mamaki Safiyya ta ce,

“Nana ki faɗa min. Komenene zan duba in shaa Allah.”

Juyawa Nana ta yi ta fuskanci Safiyya sosai.

“Ki auri dady. I mean ki sake auren shi please…”

Wata irin dokawa zuciyar Safiyya take yi. Ga kanta da ya sara. Bata taɓa tunanin wannan roƙon daga wajen Nana ba. Ta sake aurar Fu’ad?

“Na faɗa mishi. Ya ce ba shi da abinda zai baki. Ni bangane ba amma yana sonki sosai Mummy.

Please in dai za ki aure shi yace zai aureki…”

Katse ta Safiyya ta yi da faɗin,

“Nana!  Kin ma Fu’ad magana?”

A tsorace Nana ta ɗaga mata kai. Tana sake ware idanuwanta kan Safiyyar.

“Ki yi haƙuri mummy. Please kar ki yi fushi. Kawai bana so in tafi in barki ke kaɗai ne.

In da dady zai kula da ke. Bana so in barki ke kaɗai. Bana so…”

Kamota Safiyya ta yi jikinta ta rungume gam. Cikin kunnenta take faɗin,

“Shhhhhhh…waye ya ce za ki barni?”

Kuka nana take jikinta har rawa yake. Sai ƙoƙarin maida numfashi take.

“Please Mummy za ki aure shi?”

Ba za ta iya faɗin abinda take ji ba. Abinda tambayar Nana take mata. Yadda zuciyarta ke mata wani irin ciwo. Da ƙyar ta iya faɗin,
“Ki yi bacci Nana. I love you…”

“Mummy please.”

Cikin son Nana ta yi shiru Safiyya ta ce,

“Okay. Okay na ji zan duba okay?”

Dariya Nana ta yi ta sumbaci kumatun safiyyar kafin ta zame jikinta ta kwanta sosai.

Bata jima ba bacci ya ɗauketa. Safiyya kam juye-juye kawai take. Ta rasa kalar tunanin da ya kamata ta yi!

*****

Yana shiga gida ya ajiye mota bai ma ƙarasa ciki ba ya juya ya fice don yana ji ana kiran sallar isha’i.

Yana kan hanyar dawowa daga masallaci ne ya ji wayarshi ta yi ƙara alamar text ya shigo.

Ya buɗe,

“Kurna babban layi. Layin Birji gida mai number 85.”

Murmushi ya ƙwace mishi. Fita ya yi daga text ɗin ya sa wayar a key ya mayar aljihunshi. Hamdala yake ma Ubangiji da ya bashi wannan Nasarar har ya kai gida.

Ya taka ƙafarshi zuwa cikin falo ya ji an ce,

“Ka ji…”

Juyowa ya yi. Hassan ne a tsaye duk ya daburce.

“Hassan lafiya dai ko?”

Hannunshi yasa cikin sumar kanshi ya yamutsa. Kafin ya ɗauko wayarshi da ke cikin aljihu.

Fu’ad na tsaye yana kallonshi. Ɗan yatsa Hassan ya ɗaga mishi alamar minti ɗaya.

Ɗan ɗaga mishi kafaɗa Fu’ad ya yi. Yana kallonshi yana latsa wayar ya kara a kunne na ɗan wani lokaci kafin ya ce,

“Hussaina gashi nan…”

Wayar ya miƙa wa Fu’ad ya yi tsaye. Karɓa ya yi ya kara a kunne tare da faɗin,

“Hello…”

Cikin sauri ya ji muryar Hussaina na faɗin,

“Me yasa ka tafi bro. Na yi kewarka sosai. Ka yi haƙuri ban maka magana ba a asibiti. Ina fushi ne kawai shi yasa.

Amma zan zo. Zamu zo ni da Hamza ya ce zai kawo ni.”

‘Yar dariya Fu’ad ya yi tare da faɗin,

“Lil sis…… Breathe… Yanzun nan.”

Yana jin dariyarta kafin ta yi shiru tana maida numfashi. Har ranshi yake jin ƙaunar Hussaina.

Banda su Abba ya fi kewarta akan kowa. Ƙaunarta dabance a wajenshi. Cikin serious magana ya ce,

“Ki yafemun kanwata. Na yi kewarki da yawa. Na muku laifi babba. Ki yafe min don Allah ki…”

Katse shi Hussaina ta yi da faɗin,

“Na yafe maka bro. Tuni fa. Kawai ina ɗan yin fushi ne dama…”

Wani numfashi mai nauyi Fu’ad ya sauke yanajin kamar an sauke mishi ƙaton lodi da ke kanshi.

“Ki kula da kanki sosai kin ji?”

“In shaa Allah, kai ma haka.”

Katse wayar ta yi. Ya miƙa ma Hassan da wani irin yanayi cikin idanuwanshi. Tsaf Hassan ya karanci roƙon da Fu’ad ke mishi.

Ya ƙara tamke fuska ya karɓi wayarshi. Yana kallon yadda Fu’ad ya wani langaɓe fuska ya na juyawa.

“Bro…”

Hassan ya faɗi. Da sauri Fu’ad ya juyo fuskarshi na tambayar Hassan ko da gaske ya kira shi da bro. Kamar yana son amsa tambayar da ke fuskar Fu’ad ya ce,

“Bro…”

Riƙe fuska Fu’ad ya yi da Hannuwanshi duk biyun cike da jin daɗi.

“Na gode Hassan. Na gode sosai.”

Dariya Hassan ya yi tare da faɗin,

“We are good tun ɗazun. Kawai na barka ne ka ɗan ƙara sweating kaɗan.”

Ya ƙarasa maganar yana kashe ma Fu’ad ido. Duka Fu’ad ya kai mishi ya kauce yana dariya. Girgiza kai Fu’ad ya yi ya shige cikin gida.

****

Saida suka ci abinci da su Abba ya shiga ɗakinshi ya watsa ruwa ya fito. Ji yake gaba ɗaya ya gaji. Ya ɗan kwanta.

Da yana son zuwa yakai ma Junior mashin  ɗinshi, sai dai ba ya jin zai iya. Bacci kawai yake so ya yi.

Wayarshi ya ɗauko ya kira lukman suka gaisa.

“Da gidanka zanzo yanzun fa.”

Lukman ya amsa shi da faɗin,

“Yawwa ina jira.”

“Na fasa ai. Jikina ciwo fa. Zan kawo ma junior mashin ɗin shi ne dama. Ko za ka zo ka karɓar mishi?”

“Waye? Taɓ! Ba mai fito da ni da daren nan.”

Dariya Fu’ad ya yi.

“Sai ni ne zan fito ko? Hmm. Ka shafa min kan Junior. Ka gaishe da madam.”

“za su ji in shaa Allah…”

Lukman ya amsa kafin suka yi sallama ya kashe wayar. Gyara kwancia Fu’ad ya yi.

Addu’a ya yi ya lumshe idanuwanshi. Sai dai ga mamakinshi. Babu abinda ke mishi yawo banda fuskar Safiyya.

Hakan ba baƙon abu bane. Sai dai tun ranar da ya sauke idanuwanshi kan Nana ba shi da tunanin komai sai nata. Yauma yana tunanin Safiyya da ta addabe shi na da alaƙa da roƙon da Nana ta yi mishi.

A haka bacci ya ɗauke shi.

<< Akan So 37Akan So 39 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×