20 February 2017
Wani irin ciwo kanta yake mata da take da tabbacin yana da alaƙa da kukan da ta yi. Sai yau ta tabbatar rashin sanin ranar mutuwarka ba ƙaramar rahma bace. Ba ranar mutuwar Nana aka gaya mata ba, amma ji take yi kamar an yi yaƙin duniya na farko da zuciyarta.
Ko'ina a jikinta ciwuka ne da take da tabbacin ko da sun warke, tabonsu zai kasance da raɗaɗi har ƙarshen rayuwarta. Tana nan falo kwance, Nana ta dawo daga makaranta. Ita take ɗauko ta. Text ɗin da Ansar ya. . .