Hannun Inna Safiyya ta ƙara kamawa ta riƙe cikin nata. Don gani take kamar za ta ɓace a kowanne lokaci. Ɗayan hannun ta kamo mayafinta tana goge hawayen da suke zubo mata.
Muryarta a dishe saboda kukan da take yi ta ce,
“Inna kun yafe min da gaske?”
Ƙwalla Inna ta share tana ɗaga ma Safiyya kai. Ta mayar da kallonta zuwa wajen Baba da ke zaune yana kallonta ciki da wani yanayi.
“Baba!”
Girgiza mata kai yayi alamar ta yi shiru.
“Mun yafe miki Safiyya. Duniya da lahira. Kema ki yafe mana ɓacin rai ne ya sa muka ko…”
Da sauri Safiyya ta ce,
“Baba ka bari. Ba ku yi min komai ba. Wallahi baku min komai ba…”
Kasa ƙarasa maganar ta yi saboda wani abu da ya tsaya mata a wuya. Ƙoƙarin haɗiye shi ta yi ta kasa.
Muryarta ƙasa-ƙasa ta ce,
“Ina yaya?”
Wani murmushi Inna ta yi da Safiyya ta ji tana son ace ita ce sanadin bayyanarshi. Murmushi ne da ke cike da alfahari.
Irin murmushin da kowanne da zai yi farin ciki ace shi ne sanadin bayyanarshi a fuskar mahaifanshi kafin ta ce mata,
“Yana nan lafiya Safiyya. Yana aiki a gidan Radio. Da matarshi da ‘ya’ya biyu.”
Murmushi Safiyya ta yi kafin lokaci ɗaya wani abu na daban ya maye gurbinshi. Har ranta take jin shekarun da ta rasa tare da su da ba za su taɓa dawowa ba.
“Zan so in gansu.”
Ta faɗi a sanyaye komai na dawo mata.
“Zai zo ya kawo su anjima da yamma.”
Baba ya faɗi da kalar murmushin dake fuskar Inna. Haɗe hannayenta Safiyya ta yi tana son taga sun kalleta da irin alfaharin nan.
“Kin bar mijinki a waje. Ba Za ki ce ya shigo ba?”
Inna ta faɗi. Kallonta Safiyya ta yi da sauri hawaye na sake taruwa cikin idanuwanta. Girgiza ma Inna kai take, wani kukan na ƙwace mata. Ranar da Fu’ad ya barta na dawo mata kamar lokacin abin ya faru.
*****
Kofa take kallo tana son ta gasgata da gaske Fu’ad ya sa ƙafa ya fice bayan furta mata kalmar da ta wargaza duniyar da suka gina.
Kalmar da ke barazanar tsayar mata da bugun zuciyarta. Miƙewa ta yi hannuwanta na rawa take kallonsu. Kafin ta mayar da kallonta zuwa ko’ina na ɗakin.
Da sauri ta ƙarasa wajen ƙofa ta kama handle ɗin ta buɗe jikinta na rawa. Kallon hanyar waje ta yi ta ga ko alamar Fu’ad bata gani ba.
Ya tafin da gaske. Zame jikinta ta yi wajen ƙofar tana zama. Wani irin kuka ta saki da ya fito tun daga zuciyarta da take jin tana tarwatsewa. Sautin kukanta ne ya shigo da Mama Indo da ta zo wucewa ta ji ta. Ganinta durƙushe tana wani irin kuka ya sa Mama Indo ƙarasowa inda take da sauri.
“Subahanallahi. Safiyya lafiya?”
Kamata mama Indo ta yi. Safiyya ta maƙale jikinta tana wani irin kuka mai taɓa zuciya.
“Safiyya mene ne? Ko wani ya rasu?”
Ta kasa magana jikinta ɓari kawai yake da ƙarfin kukan da take. Da wani ya rasu zai fi mata sauƙi, saboda wannan abu ne da ka riga da ka san zai faru.
Abinda Fu’ad ya yi mata ko da wasa bata taɓa hango shi ba. Ɗago kai ta yi muryarta na rawa ta ce,
“Ya sakeni…ya tafi. Komai ya… Komai ya ƙare…bani da kowa.”
Faɗar da ta yi ya sake tabbatar da abinda ya ke faruwa. Da gaske ba ta da kowa. Babu su Inna. Fu’ad kaɗai ya rage mata, shi ma ya tafi abinshi. Numfashinta ta ji yana wani irin ɗaukewa saboda tashin hankali. Bata da kowa. Bata da inda za ta je a wannan duniyar da bata san kanta ba. Tana jin yadda Mama Indo ke girgiza ta. Sai dai sam ta kasa daidaita numfashinta da ke ɗaukewa. Wani irin duhu ta ji ya mamaye kanta kafin daga bisani duhun ya zo har cikin idanuwanta!
*****
“Safiyya!”
Inna ta faɗi tana girgizata da katse mata tunaninta.
“Safiyyaa!”
Da sauri tana ware idanuwanta kan Inna ta ce,
“Na’am.”
“Lafiyarki kuwa?”
Ta girgiza kai. Ita kaɗai ta san abinda zuciyarta ke mata. Nauyin da ta ke ji a ciki. Wasu zafafan hawaye na sake biyo fuskarta ta ce wa Inna.
“Alhaki bai barmu mun samu farin ciki ba. Rashin albarkar iyaye a auren mu ya sa bai yi nisa ba. Ya sakeni shekaru sha ɗaya da suka wuce.”
Daga Inna har Baba wani shocked Expression ne ɗauke a fuskarsu. Safiyya ta yi wani murmushi cike da takaici.
“Kar ku yi mamaki Inna. Babu ɗan da zai ga dai dai babu albarkar iyaye a rayuwarshi.”
Cikin nutsuwa take ba su labarin yadda komai ya faru. Ta ke basu labarin Nana. Yadda Inna ta riƙo ta jikinta cike da ƙauna da tausayawa ba ƙaramin taɓa zuciyar Safiyya ya yi ba.
Cikin kuka take faɗin,
“Nana ɗin ma ba mai tsahon kwana bace ba Inna.”
Baba ne ya jinjina kai ya ce,
“Haƙiƙa rayuwa wani abu ce mai cike da darussa kala-kala. Dabara ɗaya ce mai rai zai yi. Shi ne ƙoƙarin gyara lahirarshi.”
Cike da yarda da abinda Baba ya ce Inna ta karɓe da faɗin,
“Babu komai da ya ke da tabbas a zaman duniya. Dawamammen farinciki na tare da wanda ya cika da imani.”
Sake kwanciya Safiyya ta yi jikin Inna. Ɗumi da ƙaunar mahaifiyarta na saukar mata da wata nutsuwa ta daban. Kafin Baba ya ce,
“Da kun maida aurenku Safiyya. ƙaddarar da ta haɗa ku mai girma ce. Allah ne kaɗai ya bar wa kanshi sanin abinda ke tattare da rayuwarka.”
Miƙewa zaune Safiyya ta yi zuciyarta cike da nauyin maganganun da Baba yayi. Ba auren Fu’ad ba ne matsalarta. Ba rashin haihuwarshi ba ne damuwarta. Don daga ranar da ta san tana da cikin Nana ta fahimci haihuwa kyauta ce ta Allah. In ya rubuta maka samu baka isa ka canza hakan ba ko min ƙinka kuwa. Da nisantaccen yanayi a muryarta ta ce,
“Baba bana son sake rasaku. Na ɗanɗana hakan ya fi komai ciwo da ɗaci. Tunanin rasa Nana bai kai tashin hankalin tunanin ƙin sake ganinku ba.”
Sauke numfashi Baba ya yi.
“Ba za ki rasa mu ba Safiyya. Mutuwa ce kawai za ta raba mu in shaa Allah. Muma mun ji rashinki wallahi.”
Ta rasa daga inda sabbin hawaye ke sake zubo mata. Muryarta na rawa tacee,
“Bazan sake abinda babu albarkarku a ciki ba. Komenene.”
Jinjina kai Baba ya yi. Ya miƙe da faɗin,
“Ina zuwa.”
*****
Zaune yake cikin mota ya lumshe idanuwanshi. Bai san iya lokacin da ya ɗauka ba a haka. Babu tunanin komai a ranshi banda na Safiyya da Nana. Su kaɗai ya ke gani cikin zuciyarshi da idanuwanshi. Haɗata da iyayenta shi ne abu na farko da ya ke alfahari da ba ta shi.
Ko ba komai ya dawo mata da wani ɓangare na rayuwarta da ya yi silar salwantar da shi. Ya samu nutsuwa da ya kasa samu na tsayin lokaci.
Ba zai taɓa manta abinda ya gani cikin idanuwanta da kan fuskarta ba lokacin da ta yi tozali da su Inna. Kamar yadda ba zai manta yanayin da ya ji ba lokacin da ya riƙe hannuwan Abba bayan lokaci mai tsayi. Ƙauna kenan.
Wannan ita ce ƙaunar da ke tsakanin mahaifa da ‘ya’yansu. Ƙaunar da Allah ne ya dasata shi kaɗai ya san girma da nauyinta.
Abinda ya ke ji akan Nana babu kalaman da zai yi amfani da su wajen fassarawa. Ya san zafin ƙaunar iyaye. Ya san darajarsu ba zai taɓa bari su sake kuɓce masa ba. Ji ya yi an ƙwanƙwasa glass ɗin murfin motar. A nutse ya ɗago daga jinginar da ya yi da kujera. Ganin Baba ne ya sa shi buɗe wa ya fito da sauri. Zuciyarshi na wani irin dokawa don ya ɗauka wani abu ne ya samu Safiyya ya ce,
“Baba lafiya dai ko?”
Murmushi Baba ya yi ya ce mishi,
“Ba abinda ya sameta.”
Wata kunyace ta lulluɓe Fu’ad ya sadda kanshi ƙasa ganin Baba ya karanci manufar tambayarshi.
“Mu je ciki sai mu yi magana a nutse.”
Ba musu Fu’ad ya rufe motar ya bi bayan Baba har cikin gidan. Ɗaki suka nufa. Kan Safiyya da ke lafe jikin Inna Fu’ad ya sauke idanuwanshi. Nutsuwar da ke kan fuskarta ya saukar mishi da wani nishaɗi na daban. Waje ya samu ƙasa ya zauna duk da kujerun da ke cikin ɗakin. Wata kunyace ta kamashi da ya ke tuna girman laifukan da ya aikata musu. Bai san ta inda zai fara ba.
Kanshi a ƙasa ya ce,
“Wallahi ban san ta inda zan fara ba. Ni mai laifi ne a gareku Inna. Ina jin nauyin roƙar yafiyarku saboda laifina mai girma ne.”
Shiru Fu’ad ya yi kanshi a ƙasa yana jin yadda laifukanshi ke danne shi. Baba ya ce,
“Allah ma ana mishi laifi ya yafe ballantana ɗan Adamu. Mu suwaye da za mu riƙe ka da abinda kai nadama akai? Abinda ya faru ya riga da ya faru. Bai kamata muna duba baya ba. Mu kam mun yafe duniya da lahira. Allah ya yafe mana gaba ɗaya.”
Inna ce ta amsa da amin. Don Fu’ad ya kasa magana. Yana jinjina ma karamcin su Baba ne. A nutse Baba ya ce,
“Safiyya ta faɗa mana komai. Kamar yadda na faɗa mata zan sake faɗa maka. Ina tunanin ƙaddarar da ta haɗa ku tana da girma. Da kun yafi juna kun maida aurenku ko don yarinyar da ke tsakaninku. Ku kula da ita a tare zai fi.”
Da sauri Fu’ad ya ɗago ya kalli Safiyya. Sosai yake duba idanuwanta ya ga ko zai ga tsanar shi ko ƙin yarda da maganar Baba.
Ya kasa karantar komai. A tsorace ya ce,
“Baba ban san me zance ba. Bana son sake yi ma kowa laifi.”
Ya ƙarasa maganar yana ware idanuwanshi kan Baba. Murmushi ya yi.
“Babu damuwa. Ku yi shawara a tsakaninku. Kar ku ɗauki lokaci. Rayuwar ba mai tsayi bace ba. ‘Yarku na buƙatarku.”
Cikin sanyin murya Fu’ad ya ce,
“Banda shawara ni kam. Ina son yin komai dai dai ne. Ina son gyara komai saboda ban samu na yi daga farko ba. Zan yi magana da Abba yau in shaa Allah.”
Kai safiyya ta sadda ƙasa hawaye na zubo mata. Oh rayuwa kenan. Albarka Inna da Baba suka saka musu hakan ya musu daɗi sosai.
Shiru ya ɗan gifta na wani lokaci cikin ɗakin. Kowa da abinda ya ke saƙawa cikin zuciyarshi. Fu’ad hamdala ya ke ta jerowa.
Yasan bai cancanta a sake ba shi auren Safiyya ba. Saboda ba shi da abinda zai bata. Sai dai ba zai iya hana zuciyarshi son sake aurenta ba. Ya sake tabbatar da sonta da yake yana nan daram. Babu inda ya je. Muryarshi ya sauke ƙasa sosai ya ce,
“Baba zan tafi. Zan kirata in faɗa mata idan mun yi magana da su Abba.”
“Allah ya ba da iko ya tabbatar mana da alkhairi.”
Fu’ad yana miƙewa ya amsa da.
“Amin baba. Inna na gode sosai. Allah ya ƙara girma.”
Safiyya ya kalla. Yana jin nauyin ya yi mata magana gabansu Inna ya sa kai ya fice daga ɗakin. Inna ta ce wa Safiyya.
“Ki je ko za ku yi magana.”
Da ƙyar ta iya miƙewa jikinta ya mata wani irin nauyi. Yanajin takunta ya juyo da sauri. Tsayawa ya yi har ta ƙaraso inda ya ke bakin ƙofar da za ta fitar da shi soron gidan. Ta rasa ta inda za ta fara mishi magana. Ko me za ta ce. Abubuwan da take ji suna da yawa yau. Ganin ta yi shiru yasa shi faɗin,
“Tunda Nana na gida. Sai ki kwana wajen su Inna kema ko?”
Ta ji daɗi sosai. Don ko bai faɗa ba bata yi niyyar binshi su koma ba. Saidai yaune rana ta farko da ta rabu da Nana. Da za ta kwana a wani waje ba tare da ‘yar tata ba. Ba za ta yi ma kanta ƙarya ba. Har kewar Nana ta fara damunta. Ga tsoron kar a ƙi kula da ita yadda ya kamata. Gani take kamar wani abin zai faru. Idanuwanta cike da tsoro ta ce wa Fu’ad,
“Kar a bata madara da yawa. Na bata magungunanta duka da za ta yi amfani da su. Karka barta ta je wajen ruwa. Ko tashai abu mai sanyi sosai. Ka taɓa jikinta duk minti sha biyar ka ji ko da zazzaɓi.
Da ka ga ta yi shiru ka tambayeta. Bata son faɗa in wani abu na mata ciwo. Karta kwana ita kaɗai and kuma da ka ga matsala dai ka kira ni please…”
Murmushi Fu’ad ya yi. Wani burge shi ta ke yadda duk ta daburce sai lissafo mishi ƙa’idoji take. Ganin kallon da ya ke mata ya sa ta ɗan yi murmushi itama.
“Ka kula da ita sosai dan Allah.”
“Karki damu. Babu abinda zai same ta in shaa Allah. How bouh’ in kira ku yi magana lokaci-lokaci.”
Ta ji daɗi sosai. Ta ɗaga mishi kai alamar hakan ya mata. Har ta juya ya ce,
“Sofi…”
Juyowa ta yi ta zuba mishi ido. A raunane ya ce mata,
“Banda abinda zan baki Sofi. Kin sani ko?”
Bata ce komai ba. Shiru ta yi tana son fahimtar maganarshi. Ya ɗora da faɗin,
“Zan fahimta idan ba kya son sake aurena. Wallahi zan fahimta duk da zuciyata ba za ta so ba.”
Gaba daya ya ƙarasa kashe mata jiki. Ita yanzun burinta ya gama cika. Ta ga su Inna ta samu yafiyarsu. Shi kanshi haushin da ya ke bata ta neme shi ta rasa.
Duk da ba za ta iya tsayar da abinda ta ke ji a kanshi ba.
“In har Baba ya hango ƙaddararmu mai girma ce bani da bakin musu.”
Da sauri ya ce,
“Farin ciki nake so ki samu. Ko da ba tare da ni bane ba.”
Sauke numfashi tayi.
“Na same shi a yau Fu’ad. Na gode da cika min alƙawarin nan.”
Wani kasalallen murmushi ya yi mata.
“Hmm sofi. Alƙawarin da ya ɗaukeni shekaru.”
Kallonshi ta yi.
“Bance ga ranar da zan cika miki alƙawarin nan ba. Amma komin daɗewa zan gyara komai.
Wannan shi ne kalamanka a gareni. Ko har ka manta?”
Wannan karon murmushin da ya yi har cikin zuciyarshi ya kai.
“Ban manta ba. Ban manta komai ba.”
Jinjina mishi kai ta yi. Ta juya tana jin shi ya furta.
“Na gode. Na gode sosai Sofi.”
Bata juyo ba. Da murmushi a fuskarshi ya fice daga gidan.
*****
Ɗaki Safiyya ta koma ta zauna gefen Inna. Sai yanzun abinda ke manne a ranta ya faɗo mata.
“Inna ina Usman?”
Ta buƙata. Ƙaninta mai sonta. Usman da lokuta da dama in nana tayi wani abin takan tuna mata da shi. Haɗa ido ta ga Inna da Baba sun yi kafin su yi shiru kowa na sadda kanshi kasa. Wani irin bugawa ta ji zuciyarta ta yi.
Lokaci ɗaya tsoron da ta kasa faɗar kalarshi ya rufeta har tsigar jikinta ta tashi. Muryarta a sarƙe ta ce,
“Innaa…”
Kauda kai gefe Inna ta yi. Safiyya ta mayar da shi kan baba.
“Baba ina ƙanina? Ina Usman? Don Allah ku faɗa min.”
Cikin wani yanayi Baba ya ce,
“Ya rasu Safiyya. Shekara huɗu kenan. Ciwon ciki na yini ɗaya.”
Kanta ke juya mata. Girgiza kai take yi tana jin zufar da ke keto mata ta ko’ina. Inna ta kama hannunta.
“Sai haƙuri Safiyya. Allah bai yi za ku sake haɗa fuska a duniya ba. Ya fi kowa jajenki. Babu inda bai nemeki ba.”
Wani irin kuka ya ƙwace ma Safiyya marar sauti. Zuciyarta ta ke ji kamar ta ciro ta ajiye gefe ta ɗan samu sa’ida saboda zafin da take mata. Usman ya rasu. Rufe idanuwanta take tana jin yadda suke mata wani yaji-yaji amma hawaye ko ɗaya ya ƙi fitowa.
Tana tuna shi. Tana tuna komai nashi. Yanayin maganarshi. Riƙota Inna ta yi jikinta amma sam Safiyya ta ƙi. Matsawa ta yi ta haɗe kanta da gwiwa, so take kar su lallasheta. Su bar ta ta ji mutuwar Usman. Ta ji rashin ƙaninta da bata samu ta mishi sallama ba. Ƙaninta da zai ji ta manta da shi saboda ko sau ɗaya bata taɓa aika mishi da saƙon addu’a ba tunda bata san ya rasu ba. Mutuwa na da ɗaci. Ɗacinta ba zai fahimtu ga wanda bai san yadda take ba. Wanda bai taɓa rasa wani makusancin shi ba.
Allah sarki Usman yaron kirki. Yaro mai cike da ƙauna da fahimtar kowa!
*****
Bai yi ƙoƙarin hana zuciyarshi tsalle-tsallen da take ba. Yana cikin mota ya kira Lukman. Bugu ɗaya ya ɗaga.
“Bazawari.”
Bai san lokacin da ya kwashe da dariya ba. Ya manta rabon da ya yi kalarta haka. Wai bazawari. Lukman ɗin ma dariya ya ke yi.
“Ni yanzun na girma na kusan aurar da Junior. So ba ni da lokacin ka don ka ji.”
Cewar Fu’ad ɗin yana dariya. Shima Lukman ɗin dariya ya ke.
“Amma Lukman baka da mutunci wallahi. Wai bazawari.”
Yana dariya shi ma ya ce,
“Gaskiya ce baka so na sani. Yane? Ya su Nana?”
Komai da ya faru ya juyema Lukman da ya sauke ajiyar zuciya ya na faɗin,
“Na yarda kam Fu’ad. Ƙaddararku da Safiyya babu mai fahimtarta idan ka duba.”
“Hmm. Hakane kam. Yanzun zan tsaya masallaci inyi sallar juma’a in kana free mu haɗu gidan Yaya Babba mana. Banje ba fa tunda na dawo.”
Lukman ya amsa da,
“Babu damuwa to. Ni ma yanzun wanka kawai zan yi in fito sallar. Zan dai kiraka idan na fito.”
“Alright. Godiya.”
Fu’ad ya amsa yana kashe wayar.
*****
Yana fitowa daga masallacin sarki kanshi tsaye Kundila ya wuce gidan babban yaya. Ya kira Lukman shi ma ya ce mishi yana hanya ya ma kusa kaiwa. Bakin ƙofar gidan ya samu Lukman, Maigadi ya buɗe musu suka shiga suka yi parking motocinsu.
Sunci sa’a Babban Yaya na gida. Sosai Anty sa’a matarshi ta yi mamakin ganinsu. Musamman Fu’ad, don gara Lukman wani lokaci sukan zo da Haneef.
Bayan sun gaisa ta shiga ciki ta kira musu Babban Yaya. Yana fitowa ya ware idanuwanshi da mamaki. Duk da Momma ta faɗa mishi Fu’ad ɗin ya dawo bai hanashi mamaki ba.
Waje ya samu ya zauna. Suka gaisa da su Fu’ad.
“Dama na ce zanzo in gaishe da kai ne.”
Fu’ad ya faɗi yana murmushi. Babban Yaya ya harare shi.
“Ai kam kai ba ka da kirki ko kaɗan Fu’ad.”
Ɗan sosa kai Fu’ad ya yi a kunyace.
“A yi haƙuri Babban Yaya. Ba zai sake faruwa ba in shaa Allah.”
“Allah ya ƙara shirya mana kai. Don kam ba ka jin magana. Ya jikin Nana ɗin?”
A sanyaye ya ce,
“Da sauki tana gidan Momma ma.”
Jinjina kai Babban yaya yayi.
“Momma ta faɗa min komai. Ina jiranka ne daman. Muma mun haɗa jini da ita ai. Saboda me ba za a auna mu ba? Ko don bamu da mutunci a idonka har yanzun?”
Da sauri Fu’ad ya ce,
“Haba mana. Wallahi sam ba haka bane ba. Ko ɗaya wannan tunanin bai zo min ba. Saboda abu ne mai girma da haɗarin gaske. Don Allah karkace haka. Nagane kuskurena.”
Kallon shi Babban Yaya ya yi sosai. Lukman da ke zaune ya ce,
“A yi haƙuri Babban Yaya.”
Jinjina kai ya yi.
“Bakomai. Komai ya wuce. Zan yi magana da kowa tun daga kan su Hassan ina son kowa ya je a auna shi ranar Monday.”
Fu’ad shiru ya yi. Ya rasa abinda zai ce. Ya rasa kalar ƙaunar ‘yan uwanshi a gare shi. Jiki a sanyaye ya miƙe. Din tsaf zuciyarshi za ta iya karyewa. Wani irin yanayi yake ji da yake buƙatar ya zauna shi kaɗai ya jinyace shi.
“Na gode.”
Bai jira amsarshi ba da sauri ya fice daga falon. Lukman ya kalli Babban yaya ya ce,
“Abubuwan ne sun mishi yawa. Yana ganin kamar bai cancanci dukkan karamcin da ake mishi ba.”
“Menene amfanin ‘yan uwantaka idan babu taimako a tsakani? Zumunci abu ne mai girman gaske Lukman. Ba mu haɗa jini da kai ba. Iya abinda zan ma Fu’ad shi zan maka. Za ku min laifi. Zan yi fushi da ku. Za ku gane kuskurenku zan kuma yafe muku.
Wanna shi ne zama na haƙiƙa. Wannan ita ce ƙauna ta gaskiya.”
Maganganun Babban yaya sun shigi Lukman ba kaɗan ba. Ya ƙara daraja girma na zumunci. Godiya ya sake yi ma Babban Yaya kafin su yi sallama. Sanda ya fito babu motar Fu’ad. Tashi ya shiga ya yi gida abinshi. Ya san zai neme shi in yana buƙatarshi. *****
Ya daɗe cikin mota bayan ya yi parking bai fito ba. Ya haɗe kanshi da gaban motar kawai yana jinjina kalar ƙaunar da Babban Yaya ya nuna mishi yau. Haka ya kamata ace ‘yan uwantaka ta kasance. Haka ya kamata ace an girmama zumunci. Idan ya tuna ranar da ya sa ƙafa ya yi watsi da wannan ƙaunar yakan ji ciwo marar misaltuwa. Yakan yi da na sani da shi kaɗai zai fahimce shi. Buɗe motar yayi ya fito saboda yadda yake jin iskar da ke ciki ta mishi kaɗan.
Yana kaiwa ƙofa Haneef na fitowa. Da fara’a ya ce,
“Yanzun nake shirin kiranka. Momma ta ce min kun je wani waje da Safiyya.”
Jajayen idanuwanshi Fu’ad ya sauke kan Haneef da ya sa shi saurin ƙarasowa ya na dafa kafaɗar Fu’ad ɗin.
“Lafiya? Fu’ad me ya sameka?”
Dafe kai Fu’ad ya ɗan yi. Ga abinda ya same shi nan. Muryarshi a dakushe ya ce,
“Ion’ deserve dukkanku. Dukkan ƙaunarku ban…”
Katse shi Haneef ya yi i da faɗin,
“Daga ina wanna shirmen ya ke fitowa? Kar in sake ji Fu’ad. In ba so kake ranka ya ɓaci ba.”
Kama hannuwan Haneef ɗin ya yi yana tsugunnawa kan gwiwoyinshi. Bai damu da yadda Haneef ɗin ke faɗin,
“Fu’ad ka tashi. Wai meye haka?”
Hawayen da yake riƙewa ne suka zubo mishi. Hawayen farin ciki ne da samun ‘yan uwa irin su. Murya na sarƙewa Fu’ad ke faɗin,
“Haɗa jini da ku alfahari ne a wajena Haneef. Ƙaunarku mai girma ce a gareni.”
Riƙe da hannayen Fu’ad cikin nashi Haneef ya kama shi yana ɗago shi. Sai da ya saki hannunshi ɗaya sannan ya zaro hanky daga aljihunshi ya miƙa wa Fu’ad.
“Saboda Allah ka shiga cikin gida ka gani. Su Khadee duk suna nan. In kana hawaye haka ai anyi abin kunya. Bakasan ka girma bane yanzun?”
Langaɓe kai Fu’ad ya yi, yasa hanky ɗin yana goge fuskarshi. Daƙuna fuska ya yi.
“Na girma ai. Na kusan aurar da Ya’Ya.”
Sosai Haneef ke dariya. Shekaru kam sun ja. Amma akwai ɓangare na Fu’ad da ya san da wahala ya girma. Yanzun haka yadda ya daƙuna fuska cike yake da yarinta.
Halittace ta Fu’ad wannan. Yana buƙatar dukkan kulawarsu duk girman da zai yi.
“Ni kam ina da wajen zuwa. Sai mun yi waya, ok?”
Kai Fu’ad ya ɗaga mishi yana faɗin,
“Hanky ɗinka.”
Girgiza mishi kai ya yi.
“Ewww waye zai karɓa? Na bar maka.”
Ware idanuwa Fu’ad ya yi kafin ya kwashe da dariya.
“That is gross Haneef.”
Dariya kawai ya yi ya wuce. Shi ma hanky ɗin ya kalla. Sai dai bazai iya cillar da shi ba. Da murmushi a fuskarshi ya shiga gida. Kamar yadda Haneef ya faɗa gidan a cike yake da yara da suka saka murmushin shi ya ƙara faɗaɗa. Ƙarasawa ya yi wajen su. Yana ganin su Yassar ya gane su. Kamarsu ɗaya sak da Fa’iza.
Gaishe da shi suka yi. Nana na zaune ita da wata yarinya mai kyau da yake son gane ko ‘yar wacece. Nana ta kalle shi tana murmushi.
Ɗayar yarinyar da bai san sunanta ba ta ce,
“Kai ne Uncle Fu’ad?”
Dariya ya yi ya ɗaga mata kai.
“Zo mu gaisa mana.”
Ba musu ta taso ta zo wajenshi. Ya tallabi kumatunta duk ƙaunarsu ta cika mishi zuciya. Bai taɓa sanin haka ƙaunar yara take ba sai ranar da ya ɗora idanuwanshi kan Nana. Kamar ta buɗe mishi wani waje ne da bai san da shi ba. Yanzun duk inda ya ga yara sai murmushi ya ƙwace mishi. Biye su ya yi suna ta shiririta har Momma ta fito.
“Fu’ad yaushe ka dawo?”
Kallonta ya yi a gajiye.
“Ban daɗe ba Momma. Sannu da hidima. Wallahi yunwa nake ji sosai.”
Momma ta ɗaga mishi kai. Miƙewa ya yi ya ƙarasa inda Nana take zaune ta yi wani shiru.
“Lafiya dai ko Nana?”
Murmushi ta yi ta ɗaga mishi kai.
“Na sha magani ne. So yana sani bacci kuma shi yasa. Ina mumy?”
Ɗan daƙuna fuska ya yi.
“Zan baki labari anjima.”
Da ido ta nuna mishi ta fahimta. Ya wuce inda Momma ta bi ya bar su nan. Yana cin abinci yake ba Momma labarin komai.
Taji daɗi. Tuni take son mishi magana kan auren su da Safiyya ɗin sai dai batason ƙara mishi tension.
Ya dora da faɗin,
“Na je gidan Babban Yaya ma.”
Kai ta ɗaga ta amsa shi da,
“Eh ya kirani kuna fita ya ke faɗa min yadda kuka yi. Ya kamata ka je gidan Antynku ma.”
Sai da ya haɗiye abincin da ke bakinshi sannan ya ce,
“Aikam wallahi. In shaa Allah anjima. Da na gama cin abinci wanka zan yi in ɗan huta sannan.”
Miƙewa Momma ta yi da cewar,
“Allah ya kaimu. Bari in je. Na san yanzun Abbanku zai zo sai in mishi magana aji yadda za a yi.”
“Ba damuwa Momma. Allah ya ƙara girma ya tabbatar mana da alkhairi.”
Ta amsa da amin tana wucewa. Sosai ya ci abincin sanna ya tashi ya nufi ɗakinshi.