Kanta a ƙasa tun zamanta wajen. Idan ta ce ba ta jin zuciyarta kamar za ta faɗo saboda ƙuna ƙarya take. In da wani fraction na zuciyarta na tunanin auren Jabir zai fasu yau ga tabbatarshi nan a gaban idanuwanta.
“Fatan za ku bani haɗin kai wajen ganin mun zauna lafiya cikin amana da aminci da juna?”
Cewar Jabir da idanuwanshi ke yawo akan su duka biyun. Nisawa Jana ta yi, sai lokacin ta ɗago da kanta ta kuwa sauke idanuwanta cikin na Jabir.Tana karantar farin cikin da ke cikinsu da yau ba ita ba ce sanadin bayyanar shi. Ɗan murmushi ta yi mishi ya mayar mata nan take kafin ta maida dubanta ga Aina da kanta ya ke lulluɓe ta na ta wasa da hannayenta. Sauke numfashi Jana ta yi saboda yadda wani kishi na ban mamaki ya ke ɗibarta. Ganin ga ƙugun Aina ga na Jabir.
Muryarta a sanyaye ta ce,
“Ba zan maka alƙawarin komai ba Honey J. Fatana Allah ya ba mu haƙurin zama da juna, ya tabbatar mana da alkhairin da ke cikin aurenku.”
“Amin.”
Jabir ya amsa yana tabbatar da ya nuna mata godiyarshi a kan fuskarshi. Murmushin dai ta sake mishi tana ɗorawa da faɗin,
“Amarya ga amanar mijina. Allah ya ba shi ikon yi mana adalci.”
Shiru Aina ta yi amma har ranta tana jinjina ƙoƙari irin na Jana. Bata jin za ta iya wannan ƙarfin halin. Miƙewa Jana ta yi tana faɗin,
“Ango ni kam zan barku sai da safe ko? Na baku sati huɗu a ci amarci lafiya.”
Ware mata idanuwa Jabir ya yi da ya sa ta juya tana nufar hanyar fita daga ɓangaren Aina ɗin. Muryarshi can ƙasa ya ce wa Aina,
“Bari in rakata in dawo. “
Kai kawai ta ɗaga mishi. Sosai ta sake ganin ƙoƙarin Jana, yadda ta ji wani kishi ya turnuƙe ta da jin maganar raka Jana kawai.
Tana fita daga ɓangaren ta dafa kujerar da ke falo tana jin duk jikinta ko ina ɓari ya ke yi. Wasu siraran hawaye suka zubo mata.
Hannu ta sa ta goge su a fili take furta,
“Allah ka bani juriya. Allah ka bani haƙuri. Allah kai ka ɗora mana kishin nan Allah ka bani mai sauƙi…”
Ta baya ta ji Jabir ya rungumeta. Ta lumshe idanuwanta tana sauke numfashi tare da shaƙar ƙamshin turarukan da ke jikinshi.
Ƙamshin na mata baƙunta a hancinta saboda bata saba jinshi a jikinshi ba sam. Komai na mata wani iri. Sumba ya manna mata gefen kuncinta cikin kunnenta ya ce,
“Jana sati huɗu. Ya yi yawa. In ke ba za ki yi kewata ba ni zan yi taki. Saboda me za ki mana haka.”
Hawayenta take ƙoƙarin mayarwa. Ta sa hannu tana cire nashi da ke ƙugunta. Kamar ta tunzura shi da ya sake matse ta dam.
“Please you are making this hard Honey J. Ka bar yarinya ita kaɗai ka je abinka sai da safe.”
Juyo da ita ya yi suka fuskanci juna ya ɗora hannunshi ɗaya kan kafaɗarta yasa ɗayan yana ɗago da haɓarta idanuwanshi cikin nata.
“Ina sonki. Ina sonki sosai ki riƙe wannan.”
Kai ta ɗaga mishi. Ta manna mishi sumba ‘yar ƙarama a kumatunshi tare da rungumar shi. Har ranta take jin wata irin kewarshi ta ban mamaki. A hankali ta zame jikinta tare da faɗin,
“Saida safe.”
Bata jira amsarshi ba ta juya ta tafi. Dafe kai ya yi ta wani ɓangare daban yana jin zuciyarshi ta yi nauyi kafin ya juya ya koma ɓangaren Aina.
*****
Tana ƙarasawa ɗakinta kan gado ta faɗa ta saki wani irin kuka zuciyarta na yi kamar za ta fashe. Lumshe idanuwanta ta yi abinda zuciyarta ke hango mata ya sa ta miƙewa babu shiri.
Banɗaki ta shiga ta ɗauro alwala. Salloli ta fara jerowa na farko in za a yankata bata san me take ba saboda wani irin duhun kishi da take ji. Wani irin ƙunci ne marar misaltuwa. Haka ta ci gaba tana yi hawaye na zubo mata har wata nutsuwa ta soma shigarta.
Yanzun kam a nutse take sallolinta da bata san iya lokacin da ta ɗauka tana yi ba. Tana idarwa ta zauna kan daddumar tana sauke ajiyar zuciya.
A hankali ta ji an turo ƙofar. Da mamaki ta ɗago kai tana kallon ƙofar. Kai Ikram ta zuro tana leƙowa.
Ido biyu suka yi da Jana. Hakan ya sa ta dane tsayawa ganin Janar na kallonta.
“Kawai zan duba ki ne mummy.”
Ikram ta faɗi. Wani abu na daban Jana ta ji a zuciyarta. Da hannu ta yi mata alama ta shigo. Ƙarasowa ta yi cikin ɗakin ta zauna gaf da Jana. Hannunta ta kama. Don ɗazun ta leƙo ta sameta kife kan gado tana kuka.
“Are you okay?”
Kai Jana ta ɗaga mata. Muryarta a dakushe ta ce,
“Ba ki yi bacci ba?”
Kai Ikram ta girgiza mata.
“Na leƙo na ga kina kuka. Na kasa bacci ne. Dady yana wajenta ko?”
Ganin Jana ta yi shiru ya sa Ikram taɓe baki.
“Na tsane ta wall…”
Bata ƙarasa ba Jana ta bige mata laɓɓa da ya sa ta saurin kai hannu tana kallon maman nata cike da mamaki.
“Kar in sake jin wannan maganganun a bakinki. Kina jina? Me ta yi miki? Ba ki san Pa ɗinki na sonta ba? Za ki yi respecting ɗinta, ki koyi sonta kema kina jina? Babu inda za ta je, she is here to stay, you deal with it.”
Turo baki Ikram ta yi, don tana taya mamanta kishi har ranta. Tana kuma mamakin me yasa mumynta za ta ce ta so matar nan da ta turo musu kai cikin rayuwa.
Kallonta Jana take yi. Ga kanta na wani irin ciwo ga Ikram za ta ƙara mata wani ciwon kan kuma. Bata son yarinyar ta taso da tsanar kishiya tun tana ‘yar mitsitsiyarta.
Beside, ita ba kalar matar da take son turama yaranta aƙidar tayata kishi bace ba. Tarbiyarsu da kasancewarsu masu nagarta ya fiye mata komai muhimmanci.
Kamo Ikram ɗin ta yi da ba musu ta kwanta kan cinyarta tana haɗe jikinta. Cikin taushin murya Jana ta ce,
“She is not our enemy Ikram. Ba a tsanar mutum babu dalili. Ba abu bane me kyau. Ki bata chance ki ga halinta. Za ki iya min wannan ƙoƙarin? Ki mata kirki?”
Kai Ikram ta ɗaga wa Jana.
“Promise?”
Kai ta sake ɗagawa. Jana ta ɗan yi murmushi.
“Tashi ki je ki kwanta. Dare ya yi sosai.”
Miƙewa Ikram ta yi ta kalli Jana tana shagwaɓe fuska.
“Mumy zan kwana a nan please.”
Nisawa Jana ta yi. Ta kalli gadon. Ba ɗakinta bane ita kaɗai, kusan gaba ɗaya rabi da kwatar rayuwarsu da Jabir anan suka yi ta.
“Mu je in kwana a ɗakinki.”
Ware idanuwanta Ikram ta yi sannan ta yi murmushi. Miƙewa Ikram tayie ta kamo hannun Jana suka miƙe tare. Ɗakin Ikram ɗin suka nufa. Ita ta gyara wa Jana waje ta kwanta sannan ta hau gadon ta kwanta ta kashe musu ƙwan dakine ta sake matsawa jikin Janar tana sauke numfashi.
Addu’a Jana ta yi musu. Tana jin Ikram ɗin tana sake numfashi alamar bacci ya ɗauketa. Hannun Ikram ɗin ta kama cikin nata ta dumtse wata nutsuwa na saukar mata.
Addu’o’i ta shiga jerowa duk kalar da suka zo kanta. Kafin bacci ya ɗauketa.
*****
“Wai menene daɗin wanna shirin da kika liƙe wa?”
Fu’ad ya tambayi Safiyya da gaba ɗaya ta mayar da hankalinta kan My Tv series suna maimaita shirin Bade Ache Lagte Hai.
Ba tare da ta juyo ba ta ce mishi,
“Ba za ka gane ba.”
Remote ɗin da ke kusa da shi ya ɗauka ya danna ya canza channel ɗin. Juyowa ta yi,
“Ohhhh please ka mayar min.”
Turo mata lips ɗinshi ya yi.
“Wanna shirin ya fi ni muhimmanci?”
Kamar za ta fashe da kuka ta ce mishi,
“Bai fi ka ba. Now please ka mayar min ana wuce wa fa.”
Remote ɗin ya miƙa mata yana daƙuna fuska. Miƙewa ya yi daga kwanciyar da yake tare da faɗin,
“Bari in duba Nana.”
Kai ta ɗaga mishi. Ta san bacci take. Da wahala magungunan da ta sha su saketa yanzun. Jikinta ya soma zafi kwana biyun nan.
Ya dafa hannayenshi kenan zai miƙe Nana ta fito daga ɗakin tana daƙuna fuska. Kallonta ya ke, ta ƙara ramewa fiye da sanda ya zo.
Wani abu ya soki zuciyarshi. Murmushi ya yi mata da ta kasa mayar mishi saboda yadda take ta kokawa da numfashinta.
Da ƙyar ta iya cewa,
“Mummy…”
Da sauri safiyyay ta juya ta kalleta. Wani irin jiri ke ɗibar Nana ɗin ta soma ganinsu bibbiyu saboda yadda numfashinta ya ƙi kaiwa.
Kanta ya yi wani irin zafi kafin ta ji gaba ɗaya duniyar tana juya mata. Fu’ad ya soma miƙewa da gudu ya ƙarasa wajenta ya sa hannu yana tallabeta saboda karta faɗi. Girgiza ta ya ke amma ko motsi bata yi. A rikice yake ce wa Safiyya,
“Sofi please ki yi wani abu. Bata numfashi…Wallahi bata numfashi!”
Wani yawu Safiyya ta haɗiya. Ba wannan bane na farko a wajenta shi ya sa take da ‘yar nutsuwa fiye data Fu’ad ɗin. Ɗaki ta shiga ta ɗauko hijabinta da mukullin mota.
“ɗauko ta mu tafi asibiti.”
Girgiza mata kai Fu’ad ya shiga yi yana sake riƙe Nana gam a jikinshi.
“Ta ƙi tashi Sofi.”
Dafa kafaɗarshi ta yi cikin taushin murya ta ce,
“Za ta tashi. Sai mun je asibiti. Please Fu’ad ka taso.”
Miƙewa ya yi yana saɓar Nana a kafaɗar shi suka fice tare. Bayan motar ya buɗe ya shiga yana kwantar da ita a jikinshi.
Wayarshi ya ɗauko bayan Safiyya ta tashi motar suna ficewa daga gidan. Momma ya kira ta ɗaga da yi mishi sallama.
Ko amsawa bai ba ya ce mata,
“Momma Nana… Muna hanyar asibiti yanzun.”
Bai jira amsarta ba ya kashe wayar. Yana sake jijjiga Nana ko za ta buɗe idanuwanta. Zuciyarshi ciwo take kamar ya cire ya ajiye.
*****
Ta window ɗin ya ke tsaye yana kallon yadda wajen likitoci huɗu suke kan Nana an saka mata oxygen mask ya juyo ya kalli Safiyya da take zaune ta haɗe kanta da gwiwa.
Kusa da ita ya koma ya zauna ya dafa kafaɗarta. Ɗagowa ta yi ta kalle shi. Muryarta da yanayi na damuwa ta ce,
“Zan kira su Inna ne. Ina so su ganta before you know…May be.”
Hannunshi ya zagaya yana kwanto da ita jikinshi. Kansu ya haɗa yana faɗin,
“No Sofi….ki daina cewa haka. This is not it. Wata nawa akace? Ba shida ba yanzun fa ake wata na huɗu. Muna da sauran time.”
Ita yake faɗa wa amma da ka ji yanayin yadda ya ke maganar kasan cewa yana ƙoƙarin convincing ɗin kanshi ne fiye da Safiyya ɗin. Bata ce mishi komai ba sai sake maƙalewa da ta yi a jikinshi. Tana jin kukan da zuciyarta take yi amma hawaye ko ɗaya sun ƙi zubo mata.
Suna nan zaune Momma ta zo. Tashi Fu’ad ya yi ya ƙarasa wajenta yana kallonta, so ya ke ta ce mishi komai zai yi dai dai. Ta faɗa mishi Nana za ta samu sauƙi.
Ta faɗa mishi komai bai zo ƙarshe ba. Kai Momma ta girgiza mishi. Hakan ya sa shi dafe goshi. Raɓa Momma ya yi yana ficewa daga wajen gaba ɗaya.
Kusa da Safiyya ta ƙarasa ta zauna. A hankali Safiyya ta ce mata,
“Ina wuni.”
Dafa ta Momma ta yi saboda bata san me za ta ce mata ba. Nana jikarta ce, idan har tana jin wanna fargabar bata san su kuma me suke ji ba.
“Fu’ad…”
Safiyya ta faɗi tana jin hawayen da suka ƙi fitowa tun ɗazun suna zubowa.
“Kin san halinshi Safiyya. Yana son zama shi kaɗai a yanzun. In ba Haneef ko Lukman ba ba zai saurari kowa ba.”
Wayarta Safiyya ta cire daga key ta yi wa Haneef text.
“Muna asibiti da Nana.”
Ko minti biyu ba aiba tsakani ya dawo mata da amsa.
“On my way.”
*****
Zaune ya ke bakin ƙofar asibitin saboda yadda ya ji iskar ciki ta mishi kaɗan. Baya son tunanin komai banda na lafiyar Nana. Ko kaɗan bai kula da motar Haneef ba. Saboda hankalinshi na wata duniya ta daban.
Tun shigowarshi asibitin ya hango Fu’ad ɗin zaune. Har ya yi parking ya fito. Hannayenshi ya haɗe waje ɗaya tare da murza su, lokaci ɗaya kuma ya ja iska yana fitarwa ta bakinshi. Sannan ya taka ya ƙarasa wajen Fu’ad ɗin ya dafa shi. Da sauri ya ɗago. Ganin Haneef ɗin ya bashi mamaki na ɗan lokaci.
“Haneef.”
Ya faɗi cikin alamar gaisuwa. Zama gefenshi Haneef ya yi tare da faɗin,
“Me kake yi a waje?”
“Iskar cikin ce nake jin ta min kaɗan na fito nan.”
Ya amsa shi. Dafa shi Haneef ya yi.
“Ba yaro bane kai Fu’ad. Ya kamata ka koyi tarbar matsalolinka. Gudunsu ba zai canza komai ba.”
Tauna maganganun Haneef ɗin ya ke yana jin gaskiyarsu na zaunawa tare da shi.
“I…i…Ni bansan me ya kamata in yi bane ba.”
Wani irin helplessness ya ke ji da tunda yake a rayuwarshi bai taɓa jin kalar shi ba. Me ya kai kana sane cewar da duk mintinan da ke wucewa rayuwar ‘yarka ya ke tafiya da shi tashin hankali?
Jinjina mishi kai Haneef ya yi. Ko bai fahimci kalar abin da Fu’ad ya ke ji ba yana kamantawa. Kuma yana tausaya mishi.
“Ka tashi mu je. Kana buƙatar spending duk wani lokaci tare da ita. Za ta so haka.”
Miƙewa Fu’ad ya yi yana jin zuciyarshi na wani irin dokawa. Hannunshi ya sa cikin na Haneef kamar ƙaramin yaro.
Ƙyale shi Haneef ɗin ya yi. Ya san yana buƙatar ƙwarin gwiwa ne, in riƙe hannunshi yana samar mishi da hakan saboda me zai hana shi?
Lokacin da suka ƙarasa ciki ba su ga su Momma a waiting area ɗin ba, don haka suka shiga cikin ɗakin. Suna zaune gefen Nana kamar yadda suka zuba mata idanuwa zai sa ta samu sauƙi.
Haneef gaisawa suka yi da Momma da Safiyya yana musu ya me jiki kafin ya samu waje ya zauna. Zagayawa Fu’ad ya yi ya koma saitin kan Nana.
Hannu ya sa ya shafi goshinta da alama bata ma san duniyar da take ba. Ɗan ranƙwafawa ya yi ya sumbaci goshinta yana sauke murya.
“Allah ya ba ki lafiya Princess. I love you so much. Kin sani ai ko?”
Dafe fuska Safiyya ta yi cikin hannayenta. Momma da Haneef suka haɗa idanuwa suna rasa ko me ya kamata su yi.
*****
Zuwa yamma gaba daya ɗakin ya cika. Tun daga kan Anty Fatima duk sun zo. Har Zainab don da Lukman ya ce ta zauna saboda cikin satin ake sa mata ran haihuwa kuka ta kama yi.
Dole ya taho da ita. Doctor ne ya shigo sake duba Nana ya gansu cikin ɗakin. Ware idanuwa ya yi tare da faɗin,
“Gaskiya ku fita. Ana so ta samu hutu wadatacce ne. Ba a son hayaniya ko kaɗan.”
Kallonshi Lukman ya yi ya ce,
“Kafin ka turo ɗakin nan ka sa ran za ka ganmu fiye da mu goma a ciki?”
Girgiza mishi kai Doctor ɗin ya yi.
“Ka ji magana ko ɗaya na fita daga ɗakin?”
Ya sake girgiza mishi kai. Rai a ɓace lukman ya ce,
“Do your damn job ka bar mu muji da abinda ya ke damun mu.”
Fu’ad da ke gefenshi ya riƙe hannunshi. Idan zai ƙirga wannan ne karo na biyar da ya taɓa ganin ran Lukman a ɓace.
“Lukman please. Ka barshi ya yi aikinshi. In yana ganin za mu takurata sai mu fita.”
Cikin idanuwa Lukman ya kalle shi ya ce,
“Ku fita ban hanaku ba. Ina nan ni kam.”
Kallon Doctor ɗin Fu’ad ya yi. Shi yanzun kam baya jin wani ƙarfi ko na sisi balle har energy ɗin rikici. Hakan Doctor ɗin ya kula da shi. Yanajin idanuwansu gaba ɗaya akanshi. Don haka ya bar su tunda da gaskiyar Lukman ba surutu suke ba. Wanda suke tsaye suna tsaye. Wanda suke zaune suna zaune abinsu. Bai ga matsala tare da kasancewarsu a ɗakin ba. Kalar ƙaunarsu ga Nana har mamaki ta ba shi. Dubata ya yi ya ga komai na tafiya yadda suke tsammani sannan ya ce,
“Ko motsi ta yi ku min magana.”
Kai kawai Fu’ad ya ɗaga mishi. Safiyya ce mai ƙarfin halin yi mishi godiya kafin ya fice daga ɗakin.
*****
A asibitin suka yi sallar magrib da isha’i, ganin babu wani canji yasa Momma ta tusa kowa ta ce ya tafi gida. Tunda sun ga Nana ɗin. Addu’a ta fi buƙata daga wajensu ba wannan zaman ba. Kan dole suka tattafi. Daga Safiyya sai Fu’ad aka bari a asibitin.
Kallon shi Safiyya ta yi yana zaune ya tusa Nana gaba yana jira ya ga ko motsi ta yi. Ta ce mishi,
“Ka ci wani abu.”
Girgiza mata kai ya yi saboda baya jin zai iya saka wa cikin shi wani abu. Da sauri ya ɗago kai ya ce wa Safiyya,
“Ba mu faɗa wa Ansar ba.”
Dafe kai ta yi ita ma tanajin rashin kyautawar hakan. Text ta yi mishi ta faɗa mishi tana bashi haƙuri.
Shi kanshi Fu’ad ɗin ya san Ansar na da haƙƙin sani. Ko ba komai ya yi ɗawainiya mai girma da Nana kuma ba zai manta ba.
Bayan haka ya san ita kanta Nana ba za ta yafe musu ba in ta ji ba su faɗa mishi ba. Ai kam kasa haƙura ya yi.
A daren sai da ya zo ya ga Nana duk da bai jima ba ya koma. Ansar na tafiya Safiyya ta sauka ƙasa don ƙafafuwanta sun gaji.
“Ka sauko ka ci abinci.”
Kai ya girgiza mata. Ko magana ba ya son yi. Gajiya ta yi ta haƙura ta ƙyale shi. Sai da ta kira su inna kamar yadda ta saba ta yi musu sai da safe take faɗa musu suna asibiti ma sannan ta kwanta.
Damuwar da ke zuciyarta bai hana ɓarawon bacci sace ta ba cike da mafarkai barkatai.
Hannunshi Fu’ad yasa cikin na Nana ya dumtse yadda ko ya ta yi zai ji, ɗayan kuma yana kan cikinta ya ɗora kanshi jikin gadon yadda da ta motsa zai ji.
A nan bacci ya ɗauke shi.
*****
A ɗakin Ikram ta yi sallar asuba sannan ta tashi Ikram ɗin itama ta shiga toilet ta yo alwala. Tun jiya sun san duk da monday ce ba za su je school ba saboda gajiyar hidimar biki. Fita Jana ta yi daga ɗakin ta tashi sauran yaran su yi sallah suma in ya so sai su koma baccinsu. Ta tashi Atika ma. Sannan ta yi ɗakinta.
Tana shiga ɗakinta wanka ta yi ta fito ta zira wa jikinta wata doguwar riga ta atamfa ɗinkin simple ta ɗaura ɗankwalinta sannan ta nufi kitchen.
Dankali ta fara ferewa tana so ta taya Atika don kar aikin ya yi mata yawa. Ta ɗora kenan ta dafa shi atika ta shigo kitchen ɗin.
Tare suka kama aikin. Zuwa bakwai da kusan rabi sun gama komai. Sauri-sauri Jana ta ƙara watsa ruwa ta fito tana shirin tafiya aiki. Don ta makara sosai yau. Tana ƙarasawa ta lalubo wayarta ta yi wa Jabir text ta faɗa mishi ta wuce office.
Ga mamakinta text ɗin shi har huɗu ta gani. Biyu jiya da dare ne yake mata godiya, ɗaya kuma sai da safe. Biyun da safen na ne yake tambaya ya ta kwana ya yara.
Ɗayan yanzun ne ba jimawa ya turo mata shi.
“Please reply.”
Murmushi ta yi. Har ranta ta ji daɗin kalar kulawar da ya nuna mata.
“Afuwan Honey J. Yanzun na ɗauki wayar. Duka mun kwana lafiya. Fatan kaima. Zan wuce office ne yanzun sai na dawo.
Love you.”
Ta tura. Har zata saka wayar cikin jaka wata zuciya daban da mai kishin da ta hanata tambayarshi ya kwanan Aina take ce mata bata kyauta ba. Ko ba don Aina ɗin ba Jabir zai ji daɗi. Kafin ta kasa ta yi saurin tura mishi wani saƙon,
“Ya amarya ta kwana?”
Ta ɗauko glass ɗinta kenan tana fesa turaruka masu sauƙin ƙamshi don ita kaɗai ke jin abinta in ba gab da ita mutum ya zo ba sosai.
Ta kama handle ɗin kofar za ta buɗe ta ji an turo. Hakan ya sa ta ɗan yin baya. Jabir ne. Idanuwanta take yawatawa kan shi. Sanye yake da jallabiya. Ya mata kyau murmushin da ya yi mata ya sa ta ji wani irin kishi ya rufeta. Musamman da ta tuna bata san adadin kalarshi da Aina ta samu ba a daren jiya.
Saurin rintse idanuwanta ta yi tana korar shaiɗan da zai haɗa mata fitina da sanyin safiyar nan.
“Ina kwana.”
Ta faɗi kanta a ƙasa. Hannunshi ta ji ya sa jikin haɓarta ya ɗago da ita.
“Jana kin san ba na so in anamun magana a ƙi kallon fuskata ko?”
Murmushin ƙarfin hali ta yi.
“Afuwan. Ya kuka tashi?”
“Alhamdulillah. Har kin gama shiryawa?”
Kai ta ɗaga mishi tana faɗin,
“Eh kam. Ga breakfast ɗinku can a kitchen sai kaima Atika magana ta shirya muku komai in kun tashi.
Zata iya haɗa muku lunch. Yara suna bacci yau ba za su je school ba.”
Kai ya ɗaga mata.
“Mun gode sosai Jana. Sai mun yi waya ko?”
Kafin ta amsa shi ya manna mata peck a laɓɓanta ya juya. Sauke numfashi ta yi ta fice tare da yin addu’a.
*****
Tana shiga asibitin ta yi signing ake faɗa mata Nana tana nan. Sai da ta ji zuciyarta ta doka. Yau ɗin nan ta yi niyyar kiran safiyya ta ji ya jikinta. Sai dai itama abubuwa sun mata yawa akai. Yanayin yarinyar kawai yana sa ta ji kamar bata da matsala a tata rayuwar ko kaɗan. Jakarta kawai ta ajiye office ta ɗauki abubuwan da take buƙata ta ɗauki file ɗin Nana da aka ajiye mata kan table ɗinta ta nufi ɗakin.
*****
Kamar yadda rayuwa ke tafiyarma su Fu’ad haka ma take a wajen Nuriyya. Washe garin da ta fita takaba kamar yadda Farhan ya yi alƙawari ya je suka yi magana. Ta yi kuka sosai da ya yi mata maganar aure, sai take ganin kamar hakan cin amana ne wajen Nawaf. Kamar ya yi kusa.
Sai dai shi kanshi Farhan ya yi mamakin yadda family ɗin Nawaf suka yi tsaye akan abin. Yadda tare da taimakonsu suke nuna ma Nuriyya auren da za ta yi ba komai bane a wajensu.
Ba za su ɗauka ta ci amanar Nawaf ba ko kuma hakan ya yi kusa ganin watanni ko biyar ba a cika ba da rasuwarshi.
Sun fahimci tana buƙatar kulawa kuma su ba za su iya bata ita ba. Gaba ɗaya abinda Nawaf ya mallaka tun kwana bakwai da rasuwar shi da akace za a raba ‘yan uwanshi suka yafe wa Nuriyya.
Don haka su suka shige gaba aka ɗaura auren Farhan da Nuriyya. Bata da wasu da za ta kira ‘yan uwanta balle ace za a yi wani shagali. Ɓangaren Farhan kuwa ya san yana da ‘yan uwa ba wai ba shi da su ba. Sai dai zumuncin da ke tsakanin su ya daɗe da yin nisa. Bai ma bi takansu ba tunda family ɗin Nawaf sun musu wakilci su duka biyun. Shi kanshi ya ji wani iri da ya ga daga shi sai ita a mota lokacin da ya zo ɗaukarta. Har suka kai gidanshi tana wani irin kuka da yake ji har zuciyarshi.
Suna shiga gidan ya kama hannuwanta yana ƙoƙarin riƙeta jikinshi. Kuka take sosai tana ture shi.
“Yaya Farhan ba zan iya ba wallahi. Don Allah ka yi haƙuri.”
Ganin yadda ta rikice yasa shi riƙo mta gam. Ƙarfi yasa ya riƙeta jikinshi gam yana ƙoƙarin nutsar da ita.
“Ba abinda zan miki nuriyya. Wallahi ba abinda zan miki. Ki nutsu zan zame miki duk abinda kike buƙata a yanzun har lokacin da za ki so fiye da hakan.
I promise kome kike so in zama.”
Ya sauke ajiyar zuciya jin ta yi luf da ita a jikinshi tana kuka a hankali. Da gaske yake mata zai zama duk abinda take so.
Son da yake mata mai girma ne. Ya san tana buƙatar lokaci mai yawa. Ya aureta ne da wuri haka saboda yana son ta san ko da bata da kowa a duniya tana da shi.
Yana son kula da ita irin kulawar da bata taɓa samu ba a rayuwarta. Tana jikinshi ya ja ta har zuwa kan kujera ya sa hannunshi ya goge mata fuskarta.
“Ki yi shiru kar kanki ya yi ciwo please Nuriyya.”
Kai ta ɗaga mishi tana ƙoƙarin haɗiye kukanta. Ya miƙe ya shiga kitchen ɗin shi ya ɗauko mata fresh milk ya ajiye sannan ya fice ya ɗauko naman da ya siya tun ɗazun. Da ƙyar ya samu Nuriyya ta ɗan ci. Ya tambayeta ko ta yi sallah. Ta ɗaga mishi kai. Miƙewa ya yi ya kama hannunta. Ɗakin shi ya kai ta ya tabbata ta kwanta bata buƙatar komai sannan ya yi mata sai da safe ya fice.
Sake shigewa cikin bargo Nuriyya ta yi tana ajiyar zuciya. A karo na farko na rayuwarta ta samu wata nutsuwa da bata taɓa sanin akwaita ba.
*****
Kwanansu huɗu a asibiti. Cikin kwanakin nan babu wanda bai zo ya ga Nana ba. Daga kan abokan arziƙi har ‘yan uwa. Cikin kwana huɗun nan tun tana buɗe idanuwanta ta yi magana har ta kai ga sai dai in ta ji muryarsu ta buɗe idanuwanta da ƙyar ta mayar da su ta lumshe.
Daga Fu’ad har Safiyya ba kuka suke ba amma kallo ɗaya za ka yi musu ka ga ramar da suka yi saboda tashin hankali.
Yauma kamar kullum wajen Nana suka kwana sai dai me, tun jiya rabon da ta buɗe idanuwanta. Fu’ad ya yi maganar duniya amma shiru kake ji.
Hannunta ya murza ya ga bata motsa shi ba. Miƙewa ya yi ya taɓa goshinta. Ya sake kama hannunta ya murza. “Da
mmit Nana wake up please…”
Tasowa Safiyya ta yi su duka suke ƙoƙari amma Nana ta ƙi ko motsi. Da gudu Safiyya ta fita don ta kira Jana.