Skip to content
Part 45 of 48 in the Series Akan So by Lubna Sufyan

Dr. Jana na shigowa ɗakin na’u’rorin da ke manne jikin Nana ta shiga dubawa. Kallonta Fu’ad ya ke cike da tashin hankali.

Da gudu ya ga ta fita ba su fi mintina biyar ba suka dawo su huɗu. Kama hannun Safiyya ya yi tana tirjewa tana ce mishi,

“Ka sakeni. Ka barni babu inda zan tafi…”

Gam ya riƙe ta jikinshi tana wani irin kuka. Tashi zuciyar ta bushe. Wani iri yake jinta yadda babu kalaman da zai bayyana ta da shi.

Bakin ƙofar ɗakin da Nana take ciki suka tsaya, har lokacin Safiyya da ke kuka tana jikinshi. Haɓarshi ya ɗora saman kanta ya lumshe idanuwanshi yana faɗin,

“Allah ka bamu juriya. Allah duk yadda ka yi damu dai dai ne…”

Bai san iya lokacin da suka ɗauka a haka ba sai da ya ji buɗe ƙofar. Da sauri Safiyya ta zame daga jikinshi tana kallon Dr. Jana.

Ta gabansu sauran likitocin suka fito suka wuce. Safiyya bata jira komai ba ta wuce cikin ɗakin. Shi kam Fu’ad tsayawa ya yi ya zuba mata idanuwa.

Nata idanuwan ta ji sun cika taf da hawaye. Daga kan Nana ta yi alƙawarin ba za ta sake karɓar wani cancer patient ba. Zuciyarta ba za ta iya ɗauka ba.

Muryarshi a dakushe ya ce,

“How many days?”

Sai da ta kai mintina biyu tana ƙoƙarin controlling emotions ɗinta sannan ta ce mishi,

“A few hours max…”

Tana rufe bakinta ta juya da gudu tana barin wajen saboda bata son Fu’ad ya ga hawayen da ke zubar mata. Bata son ya ga yadda take ji, ita da bata haɗa jini da Nana ba kenan. Bangon wajen ya sa hannu ya laluba jikinshi na ɓari. Kalmomi huɗu ta faɗa, amma shi a wajenshi gaba ɗaya farin cikinsu ta tarwatsa. Cikin kunnuwanshi yake jin amsa kuwwar da kalmominta suke mishi. Ya san yana cikin shock sai dai bai san yadda zai iya fita ba. Wata dariya ce ya ji ta kuɓce masa da bai san ta inda ta fito ba. Wayarshi ya ɗauko ya kira Haneef ya ɗaga da faɗin,

“Fu’ad ya Nana din?”

Cikin muryar da bai gane ko tashi bace ya ce,

“Kuzo ku mata bankwana Haneef. Awanni kaɗan take da shi.”

Yanajin yadda Haneef ya ja numfashi ta cikin wayar ya sauketa daga kunnenshi bai damu da ya kashe ba ya sata a aljihunshi. Handle ɗin ɗakin ya kama zuciyarshi na wani irin yawo da zai iya rantsewa yana jin bugun da take har cikin kunnuwanshi. Turawa ya yi a hankali. Safiyya na riƙe da hannun Nana tana tsugunne ƙasan gadon tana wani irin kuka da ya ji ya tsaya mishi a wuya.

Gefen gadon ya zauna ta ɗayan ɓangaren yana kama hannun Nana da ya ya riƙe shi ma. Ji ya yi kamar ta yi motsi hakan yasa shi faɗin,

“Princess…”

“Daadyyy…”

Ta faɗa. Da sauri Safiyya ta ɗago ta na zama kan kujera. Hannunta ɗaya ta sa tana goge hawayenta.

“Nana kina jina?”

Idanuwanta a rufe ta ce,

“Mumy ya aljanna take?”

Ta tambaya muryarta na rawa tana wata irin kokawa da numfashinta. Kuka ya hana Safiyya magana. Fu’ad ya haɗiye wani miyau ya ce,

“Princess babu wanda ya san exact yadda take. Waje ne mai cike da ni’imomi fiye da zaton ɗan Adam. Wajene da ya ke da farin ciki. Kwanciyar hankali da natsuwa ta har abada.”

Murmushin da Nana ta yi har cikin ranshi ya ji shi.

“Babu rashin lafiya?”

Kai Fu’ad ya girgiza duk da bata ganin shi.

“Babu ko ƙishin ruwa Nana. Babu komai banda farin ciki…”

Yana kallon yadda ƙirjinta ke ɗagawa da ƙyar saboda yadda take kokawa da shigar iska abin na mishi wani iri.
“Duk ciwon nan zai tafi?”

Wannan karon kasa amsata ya yi. Saboda wani abu ya riƙe kalamanshi. Bakinshi ya bushe tas.

Muryar Safiyya na rawa wasu sabbin hawayen na zubo mata ta ce,

“Zai tafi Nana. Babu ƙunci ko kaɗan a cikinta. Wajene da mai laifi da marassa laifi ke da burin shiga.”

Murmushin Nana ya sake faɗaɗa. Hannayensu da ke riƙe a cikin nata da ɗan sauran ƙarfin da take ji ta dumtse.
“This is not a goodbye. Wannan na nufin sai kun taho. Yana nufin ina jiranku a aljanna…”

Lumshe idanuwanshi Fu’ad ya yi. Safiyya ta kife kanta jikin gadon, in tana zaton ta ji mutuwar Usman abinda ta ke ji na yanzun ya linka wancan fiye da zatonta. Wani irin ɗaci ne har cikin naman jikinta. Wani ciwo ne marar misaltuwa.

“Ya Allah…”

Nana ta faɗi kafin Fu’ad ya ji ta saki hannunshi. Buɗe idanuwanshi ya yi lokaci ɗaya da ɗagowar Safiyya. Jikinta na ɓari da wata irin fargaba marar misaltuwa take kallon Nana.

Kaman tana bacci da murmushi a fuskarta.

“Nana…”

Ta kira a hankali muryarta ɗauke da fargabar da ta ke ji. Idanuwanta cike taf da hawaye ta ɗago ta kalli Fu’ad da tashi zuciyar ke son fitowa daga ƙirjinshi.

Sam ba su ji turo ƙofar Haneef  da Lukman ba ballantana sallamarsu. Idanuwansu na kafe da juna. Kafin Safiyya ta sake maida hankalinta kan Nana. Wani irin abu Fu’ad ya haɗiye da ya tsaya mishi a wuyanshi. Haneef na kallon Nana ya kai hannunshi ya dafe kanshi.

Lukman ya kalla ya girgiza mishi kai yana son gaya mishi ba abinda suke zato bane ba. Ba shi bane sam. Ƙarasawa Lukman ya yi ya dafa Fu’ad. Ya juyo ya kalle shi ya sake maida hankalinshi kan Nana daga shi har Safiyya tsoron taɓata suke ji.

“Nana!”

Safiyya ta sake kira muryarta na karyewa. Lukman ya kai hannu ya taɓa ƙafarta. Dumtse ƙafar ya yi cikin hannunshi. Ya ji tayi sanyi. Da sauri ya saki ƙafar Nana yana goge hannunshi sosai jikin kayan jikinshi yana son cire yanayin da ya ke ji manne jiki har lokacin.

“Bari in kira doc.”

Haneef ya faɗi a tsorace yana fita daga ɗakin. Ko mintina biyar bai yi ba ya dawo da wani Dr.

Aune-aunen shi ya shiga yi. Kafin ya ɗan runtsa idanuwa ya dafa kafaɗar Lukman da ke tsaye sannan ya girgiza wa Haneef kai.

Yana ficewa daga ɗakin. Miƙewa tsaye Safiyya take tana ja da baya tana girgiza kanta.

“Don Allah ku ce min lafiyarta ƙalau. Don Allah ku ce min wani abu bai sami Nanata ba!

Kar ku ce min ta barni. Kar ku ce main wannan shi ne bankwana! Wallahi ban shirya ba. Ban shirya ba.”

Hannu Fu’ad ya kai a tsorace ya ɗora kan ƙirjin Nana dai dai zuciyarta. Wani irin shiru ya ji. Ya ɗago idanuwanshi ya kalli Lukman. Hawaye ya ga sun zubo daga idanuwan Lukman ɗin. Cike da wani yanayi ya ce wa Lukman,

“Ta rasu ko?”

Juya baya Lukman ya yi. Haneef ne ya ƙaraso yana dafa Fu’ad ɗin. Ture hannunshi ya yi still ɗayan nakan kirjin Nana.

“Em okay. Kawai ku faɗa min. Ina so wani ya tabbatar mun ne. Ta rasu?”

Da ƙyar Haneef ya ce,

“Ta rasu Fu’ad.”

Hannunshi ya ɗauke daga ƙirjinta ya miƙe daga kujerar da ya ke zaune ya koma gefen gadon ya zauna. Hannunta da ya ke ƙarara ya kamo ya sumbata. Sannan ya tsugunna ya sumbaci goshinta yana jin wani yanayi da bai taɓa ji a jikinta ba.

Batare da ya ɗago ba ya ce,

“Allah ya sa mutuwa hutu ce a gareki Nana. Allah yai miki Rahma. Allah ya sadaki da fiye da abinda kike zaton Aljannarki ta ƙunsa.”

Yana ƙarasawa ya miƙe tsaye. Wajen Safiyya da ke girgiza mishi kai ya nufa. Hannuwanta ya kama yana kallonta.

“Safiyya zo ki mata addu’a.”

Wasu hawaye masu ciwo da ɗumi suka zubo mata.

“Ku duba sosai. Don Allah ka duba. Bata rasu ba.”

Kamata ya yi ya rungume tsam a jikinshi yana rocking ɗinsu. Ya san shirun nan da yake ji cikin kanshi da zuciyarshi ba na lafiya bane. Yasan dole ne koma ina ya adana ciwon da ya kamata ace yana ji zai dawo mishi. Zai dawo mishi ba tare da shiri ba.

Wani yawu ya haɗiya. A hankali yake ce ma Safiyya,

“Dukkan mai rai mamaci ne Sofi. Ba ki ji me Nana ta ce ba? Wannan ba bankwana bane ba. Ki zo ki mata addu’a.”

Kai take ɗaga mishi tana jin zuciyarta na wani irin tsaitsayawa da ciwon da take ji.

“Inalillahi wa inna ilaihir raji’un…”

Fu’ad ya faɗi cikin kunnenta. Ai kamar ya tuna mata abinda ya kamata ta yi ta shiga jero wa jikinta na wani irin ɓari.

Wani ƙwarin gwiwa ta ji ta samu wanda bata ma san daga inda ya fito ba. Tare da Fu’ad suka taka wajen da Nana take kwance.

Kallonshi ta yi ya ɗaga mata kai alamar za ta iya.

“Ki mata addu’a tana jinki Sofi. Ta ji yadda kike kuaunarta.”

Muryarta na rawa ta ce,

“Allah ya sadaki da rahmarshi Nana. Allah ya baki hutun da kike ta nema. Za mu yi kewarki.

Allah ya haskaka kabarinki kafin ki ƙarasa mishi…”

Yadda ta ƙarasa maganar ya sa Fu’ad kamota yana janyeta daga wajen Nana.  

“Ban gama ba Fu’ad, ban gama mata bankwana ba.”
Kanta ya kama ya kwantar a ƙirjinshi yana janta a hankali yana faɗin,

“Za ki ƙara wani in mun je gida.”

Da kanshi ya fita da ita ya buɗe mota ya sakata a baya ya kullo sannan da gudu ya dawo.

Lukman na jingine da bango idanuwanshi kafe kan Nana da take kwance kan gado. Fuskarshi ta wani irin kumbura.

Fu’ad ya sauke numfashi.

“Lukman taho ku tafi gida da Safiyya.”

Girgiza mishi kai Lukman ya yi yana kasa magana. Kama hannunshi Fu’ad ya yi kamar ƙaramin yaro har lokacin idanuwanshi na kafe kan Nana.

Yana sake ganin yadda duniya ba komai bace ba. ‘Yar yarinya kenan da bata da wasu tarin zunubai. Ballantana kai babba da gulmar wasu ma kaɗai ta isheka tashin hankali. Buɗe mishi gaban motar Fu’ad ya yi ya shiga ya miƙa mishi mukullin motar.

“Can you drive?”

Ya tambaya. Kai Lukman ya ɗaga mishi. Ya sauke numfashi yana kallon Safiyya da ta haɗe kanta da gwiwa a bayan motar.

“ka kaita wajen Momma gamu nan zuwa.”

Sake komawa Fu’ad ya yi yana mamakin kanshi. Ya kamata ace yana jin wani abu amma kawai dai ya rasa ko me ya ke ji. Inda ya bar Haneef nan ya same shi. Bai bi ta kanshi ba ya shiga tattara kayayyakinsu yana zubawa cikin jakar da suka fito.

Sai da ya gama tas sannan ya miƙa wa Haneef da ya karɓa yana kallon Fu’ad ɗin da mamaki.

“Fu’ad?”

Ya kira cike da shakku yana son tabbatar da ko yana lafiya. Sai da ya ɗauki takalman Nana da ke ajiye a ƙasa ya haɗa su waje ɗaya sannan ya amsa da,

“Na’am…sa takalman Nana a ciki kar a barsu.”

Jinjina kai Haneef ya yi ya karɓi takalman, ya san akwai matsala tare da Fu’ad ɗin. Yana kuma tsoron sanda mutuwar za ta gama zauna mishi. Ƙarasawa kan gadon da Nana take Fu’ad ya yi ya ɗagota a hankali kamar tana bacci ya saɓeta a kafaɗarshi. Ya kalli Haneef tare da faɗin,

“Mu je ko?”

Ba musu Haneef ya kama hanya jikinshi a sanyaye. Suna fita daga ɗakin suna cin karo da Dr. Jana. Kallo ɗaya ta yi musu ta yi baya.

Fu’ad ya ce mata,

“Doc!”

Dawowa baya ta yi . Kallonta ya yi.

“Ki mata bankwana. Kina da muhimmanci a wajenta.”

Sai da ta lumshe idanuwa sannan ta ce,

“Allah ya jiƙanta, ya baku haƙurin rashin ta.”

“Amin mun gode. Sai wata rana.”

Ya fadi suna wucewa. Mamakin shi Haneef yake. Akwai babbar matsala.

*****

Ƙofar gida Haneef ya yi parking saboda mutane har sun fara taruwa a ƙofar gidan. Ya zagayo ya buɗe wa Fu’ad bayan motar.

Ya fito sannan ya tallabo Nana ya sake saɓata a kafaɗarshi. Haneef kaɗai ya tsaya gaisawa da mutane suna mishi gaisuwa. Cikin gida Fu’ad ya wuce. Saboda ba ya son yadda kowa ke kallonshi ɗin nan. Lokaci ɗaya maganar Nana ta faɗo mishi. Haka suke kallonta cike da wannan yanayin a idanuwansu kenan?

Sake tallabeta ya yi jikinsa yana rasa menene ya yi mishi daban cikin hakan. Yana sallama ya sa ƙafarshi cikin gidan Anty Fatima na sakin wani irin kuka.

Momma ma fuskarta har ta kumbura. Tasowa ta yi ta karɓi Nana daga hannun Fu’ad ɗin tana nazarin fuskarshi.

“Fu’ad…”

“Em okay Momma. Ku yi mata wanka bari mu siyo abinda ya kamata.

“Hassan ya tafi.”

Momma ta faɗi tana goge fuskarta da ɗayan hannunta.  Kai Fu’ad ya ɗaga mata.

“Abba fa?”

“Yana waje. Bai jima da fita ba.”

Kai ya sake ɗaga mata ya juya. Yana shirin fita Inna na shigowa tana goge fuska. Kaucewa ya yi gefe don ya ga yadda tana ganinshi wasu hawaye suka sake zubo mata. Da sauri ya bar ɗakin.

*****

Su Haneef ya samu suna alwala. Ƙofar gidan ya cika mail da mutane. Shi ma alwala ya yi ya ce wa Haneef,

“Ina Lukman?”

A sanyaye Haneef ya ce,

“Ya je ya taho da Zainab.”

Kai ya ɗaga mishi kawai yana miƙewa. Ansar ya hango ya nufo su. Tsayawa ya yi ya ƙaraso ya miƙa wa Haneef hannu sannan Fu’ad ɗin.

Muryarshi na rawa ya ce,

“Yanzun na je asibiti ake faɗa min. Na kira Safiyya sai wata ta ɗaga taban address ɗin nan. Ya Allah. Oh Nana…”

Kasa ƙarasawa Ansar ya yi, sai fuskarshi da ya sa cikin hannayenshi yana wani irin jan iska. Mutuwar Nana ya ke ji har cikin zuciyarshi. Dafa shi ya ji an yi, ya buɗe fuskar ya sauke idanuwanshi kan Fu’ad.

“Sai haƙuri. Kai mata addu’a, shi ta fi buƙata.”

Kai kawai Ansar ya ɗaga wa Fu’ad ɗin. Sai kuma ya sake kallonshi sosai wannan karon. Girgiza kai ya ke kafin ya maida dubanshi kan Haneef. Abba Fu’ad ya hango ya bar su Haneef nan tsaye. Ansar yace wa Haneef,

“Is he okay?”

Ɗan ɗaga kafaɗa Haneef ya yi tare da girgiza kai.

“Allah dai ya rufa asiri.”

“Amin. Oh Allah!”

Cewar Ansar yana samun waje ya tsugunna, don rasuwar na taɓa shi ba kaɗan.

30 Minutes Later

Su huɗu suka shigo cikin gidan. Da shi da Lukman, Haneef sai Babban Yaya don su ɗauko gawar Nana.

Ai nan tashin hankalin yake. Suna nufo inda take kwance an haɗata. Safiyya ta taso da gudu ta riƙe Nana jikinta.

“Don Allah ku tsaya. Ku tsaya ban gama ganinta ba.”

Momma da ke wani irin kuka ta taso ta kama Safiyya.

“Ki yi haƙuri Safiyya. Ki yi haƙuri.”

“Momma don Allah ki ce su ƙara tsayawa. Kar su tafi da ita…”

Riƙeta Momma ta yi a jikinta. Kafin Anty Fatima ta taso ta tayata. Fu’ad da kanshi yasa hannu ya ɗago Nana yana jin shiru cikin kanshi da ko’ina na jikinshi.

Sosai gidan ya sake rikicewa banda, “Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…” Babu abinda suke faɗi. Haneef ya runtse idanuwanshi yana buɗe su. Yana jin daɗin yadda ba su saki Allah ba.

Yana kuma da tabbacin zai sauƙaƙa musu ɗacin rashin Nana. Haƙiƙa sabo ake yi wa kuka. Safiyya na kallon sun nufi ƙofa da Nana ta rarrafa don ta kasa tashi.

Ta ƙarasa wajen Inna tana ɓoye kanta cikin cinyar Inna tare da sakin wani kuka da take jin fitowarshi daga wani waje na zuciyarta da ba ta san yana nan ba ma.

Shikenan ita da Nana har abada!

Inna ta riƙeta ita ma kukan take, saboda yadda mutuwar Nana ta sake fama mata ciwon mutuwar Usman. Ta san me ‘yarta take ji. Tasan halin da take ciki.

Abu ɗaya Inna take da yaƙini akai. Allah da ya ɗora musu ya san da su. In har suka riƙe shi zai ba su mafita.

*****

Da ƙyar ta iya kai kanta gida. Don lokacin tashi bai yi ba ma ta ce gida za ta je bata da lafiya.

Ko sallama bata yi ba ta zauna falon ta na ajiye komai anan. Dafe kanta ta yi cikin hannayenta.

Tun mutuwar mahaifinta rabon da a yi mata wata mutuwa da ta taɓata. Sai yau, rasuwar Nana ta girgizata sosai. Hawaye ke zubo mata. Wani na bin wani. Bata ji fitowar Aina ba sai maganarta ta ji,

“Anty? Yaushe kika dawo? Sannu.”

Ɗagowa ta yi wasu hawaye na sake zubo mata da ta sa hannu ta goge su. Ware idanuwa Aina ta yi ta ƙarasa inda Jana take ta zauna.

Kusan sati ɗaya kenan da zuwanta gidan nan. Banda gaisuwa babu abinda yake haɗa su da Jana ɗin. Haka ma yaranta za su gaishe da Aina ɗin kullum.

Ko bata fito ba sanda za su je school za su yi sallama ɓangarenta su gaishe da ita sannan su wuce. Kuma hakan ya mata daɗi, yadda Jana ta sa suke bata girma.

“Anty lafiya dai ko? Ko wani ya rasu?”

Kai Jana ta ɗaga mata. Ba za ta ce ta tsani Aina ba. More like tana kishi da ita ko ta ce tana kishin Jabir da soyayyarshi.

Cikin sanyin murya ta ce,

“Wata ‘yar yarinya ce. Nana sunanta patient ɗina ce kusan shekaru uku. Mun saba sosai yau ta rasu.”

Dafa ta Aina ta yi tana jin duk babu daɗi. Ita mutuwar yara na mata wani iri. Jikinta sanyi yake yi.

“Allah sarki. Allah ya jiƙanta, ya ba iyayenta haƙurin rashi.”

“Amin Aina, na gode.”

Kayan da Jana ta cillar tsakar ɗakin Aina ta tattara mata waje ɗaya tare da kauda mata gefe tana wucewa. Dawowa ta yi da ruwa da kofi. Ta buɗe ta zuba ta miƙa wa Janar. Ta karɓa ta sha. Sosai ta ji daɗin karamcin da aina ta yi mata.

“Na gode Aina.”

“Bakomai Anty. Ki yi haƙuri, ki mata addu’a sai ta san kin damu da ita sosai. Ko ki je ki ɗan watsa ruwa ko za ki samu natsuwa.”

Miƙewa Jana ta yi ta kalli Aina ta ce,

“Na gode fa. Bari in shiga daga ciki.”

Kai Aina ta ɗaga mata tare da murmushi. Jakarta ta ɗauka ta wuce ciki. Aina ta bi ta da kallo.

Tana fatan wannan zaman lafiyar da suke yi da Jana da ganin girman juna ya ɗore. Yadda bata shiga harkarta bata damu da harkarta ba kawai yana burgeta.

Bata son tashin hankali sam. Ta kuma kula Jana bata da matsala. Sai yanzun ta ga dalilin da ya sa kullum sai Jabir ya yabi halayyarta. Ta yi wa kanta alƙawari za ta sa ido ta karanci Jana tsaf ko ita ma za ta dinga samun ko da rabin yabon da Jabir yake mata ne.

*****

Tun daga hanyar dawowa daga maƙabarta Lukman ke kallon yadda Fu’ad ke ta duba hannayenshi kamar yana son ya tabbatar da su na nan ne ko yana mamakin ganinsu a jikinshi.

Haneef ya taɓo ya nuna mishi Fu’ad ɗin da ke ta jujjuya hannunshi, sauri suka yi suka ƙarasawa wajenshi suka jera tare.

Lukman ya kira sunanshi a hankali. Bai ko juyo ba balle su yi zaton ya ji. Kawai tafiya ya ke yi yana kallon hannuwa shi da ya ɗago su.

Haneef ya kai nashi hannun ya kama ɗaya na Fu’ad. Sai lokacin ya ɗago ya kalli Haneef idanuwanshi cike da wani irin ciwo da ya ke ji a ƙirjinshi.

“She is gone Haneef. Da hannuwana na kamata na sata a kabarinta. Da hannuwana na ɗibi ƙasa na taya aka zuba mata.

Haneef wannan shine soyayyar ko? Da kaina na dinga duba ko an manta ba a rufe wani waje da kyau ba. Iya ƙaunar da zan nuna mata kenan ko?”

Lumshe idanuwa Haneef ya yi.

“Ya Allah…”

“Ita ma haka ta ce kafin Allah ya ɗauki abinshi…”

Fu’ad ya faɗi yana juyawa ya kalli Lukman.

“Dama aronta aka bamu ko Lukman? Ka ga Allah ya ɗauki abinshi tunda ya fi mu sonta.”

Hannunshi ɗayan Lukman ya riƙe yana matsewa dam. Da ya yi magana hawayen da ya ke ji zubo mishi za su yi. Fu’ad na buƙatar dukkan strength ɗin da zai samu daga gare su. Haneef addu’a ya ke su ƙarasa gida lafiya kar Fu’ad ya samu break down a hanya. Hankalinshi bai kwanta ba sai da ya gansu a ƙofar gidansu.

Sai da ya ga sun shiga harabar gidan tukunna. Fu’ad da ke tsaye idanuwanshi kafe a ƙasa ya kalla ya sauke numfashi. Sai da ya dafa kafaɗarshi sannan ya ce,

“Fu’ad ka yi haƙuri. Dukkanmu babu mai tabbacin ba zai bi Nana yanzun nan ba. Ita mutuwa ba sallama take ba. Ba kuma jira take ka shirya ba. Idan bata zo kanka ba ka sa a ranka a kullum kai ne ko wani makusancinka ko wani wanda baka sani ba.

Ba zan ce na san ciwon da kake ji ba. Amma ka yi haƙuri don Allah.”

Girgiza kai Fu’ad ya ke yi.
“Haneef ta rasu. Shikenan ko?”

Har ranshi ciwo ya ke ji marar misaltuwa. Ganin Fu’ad ɗin cikin yanayin da ya ke yanzu. Amma ya san gara yanzun da ɗazun.

Ɗazun sam ba cikin hankalinshi ya ke komai ba.

“Ta rasu Fu’ad da gaske ta rasu. Allah ya ba ku juriya.”

Hannunshi ya sa ya ture na Haneef. Yana jin kiran shi da suke shi da Lukman bai ko juyo ba balle ya kalle su. Lukman ne zai bi shi Haneef ya riƙe mishi hannu.

“Ka barshi ya ji ta lokaci ɗaya ya huta.”

Kai Lukman ya ɗaga wa Haneef yana ƙarasawa cikin rumfunan da aka kafa a harabar gidan ya zauna ya haɗe kanshi da gwiwa.

*****

Cikin gidan ya shiga bai damu da yawan matan da ke ciki ba. Asali ma ba ya ganinsu, abu ɗaya ne ke yawo cikin idanuwanshi.

Yadda suka binne Nana. Hoto ne da ya san ya zauna zuciyarshi na har abada. Hanyar ɗakin shi ya nufa. Ƙafarshi ta taka benen farko ya ji an riƙe hannunshi.

Juyowa ya yi ya sauke idanuwanshi kan fuskar Momma.

“She is gone momma. Ta rasu.”

Ya faɗi yana wani irin fitar da numfashi. Momma ba za ta iya ganin shi hakan ba. Sakin hannunshi ta yi ta juya.

Ba mutuwar Nana take tsoro ba dama. Wannan tana kan kowa. Abinda mutuwarta za ta haifar shi take gudu. Safiyya ta kalla da ke zaune can gefe. Suna haɗa ido Momma ta juya ta kalli Fu’ad sannan ta sake kallon Safiyya tana son nuna mata suna buƙatar juna.

Shi kam Fu’ad da gudu ya ƙarasa hawa benen. Kawai so ya ke ya ƙarasa ɗakinshi. Jikinshi na rawa ya murza handle ɗin ya ko ci sa’a babu key a jiki, ɗakin ya buɗe.

Ƙafafuwanshi suka kasa ɗaukarshi a tsakiyar ɗakin. Durƙushewa ya yi yana dafe kanshi cikin hannayenshi. Jikinshi ko’ina ɓari yake yi.

Da sauri-sauri yake faɗin,

“Allah na karɓi jarabawarka da hannu bibbiyu. Allah ka kawo min ɗauki. Allah ka kawo min ɗauki…”

Ji ya yi an dafa shi. Hakan ya sa ya ɗago da kanshi daga cikin hannayenshi sannan ya juyo, Safiyya ce fuskarta a kumbure.

Wasu hawaye suka zubo mata. Kama hannayenta ya yi yana gogasu kan fuskarshi.

“Sofi ta rasu. Nana ta bar mu har abada.”

Kai take ɗaga mishi tana wani irin kuka. Ta kwantar da kanta a cinyarshi. Nashi kan ya ɗora a bayanta yana jin hawayen shi na zubowa. Kuka suke sosai. Kukan rashin ‘yarsu. Kukan tausayin kansu, domin ita dai tata ta yi kyau ba ita bace abin tausayi. Su da ta bari cikin duniyar da babu tabbas su ne abin tausayi.

<< Akan So 44Akan So 46 >>

1 thought on “Akan So 45”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×