Yana shigowa gidan da sallama ya ga bai ga Nuriyya ba. Ciki ya shiga ya duba bedroom ɗinta.
Don ya san bata cika zama falo ba. Ta fi gane ta yi kwance a bedroom ɗin in ba shi ya dawo ya zo ya fito da ita ba. Zuciyarshi ya ji tana dokawa babu dalili. A rikice ya fito yana faɗin,
"Nuriyyaaaa!"
Da saurinta ta fito daga cikin. Idanuwanta ta sauke cikin nashi. Wata ajiyar zuciya ya sauke yana tura hannunshi daya cikin sumar kanshi. Da mamakin ganin tsoron da har lokacin bai barshi ba ya sa ta faɗin. . .