Skip to content
Part 6 of 48 in the Series Akan So by Lubna Sufyan

Fu’ad Arabi shi ne yaro na huɗu cikin ‘ya’ ya bakwai da Alhaji Salman Arabi da Hajiya Aisha suka mallaka. Alhaji Salman dai ɗan asalin ƙauyen Bichi ne da ke garin Kano. Ita kuwa Hajiya Aisha Barumiya ce ‘yar asalin garin katsina. Anas shi ne ɗansu na farko, yana aiki da NNPC da matarshi da yaranshi biyu.

Fatima da nurse ce, itama da aurenta da yara guda biyu. Sai kuma Haneef da yake shekararshi ta ƙarshe a makaranta. Daga nan sai Fu’ad, da Fa’iza wadda ta gama secondary school ɗinta. Hassana da Hussain ‘yan biyunsu da suke aji huɗu kuma su ne ƙarshen haihuwa.

Alhaji Salman ba su da yawa a gidansu. Duka su uku ne, kuma shi ne babba sai ‘yan biyunsu duk maza. Babansu shahararren ɗan kasuwa ne kafin Allah ya yi masa rasuwa. Shi kaɗai ya gado babansu, wato harkar kasuwanci. Kuma Allah ya yi masa albarka. Don yana da gidaje da filayen da shi kanshi in ba takardu ka ɗauko ba ba zai ce ga yawansu ba.

Dai-dai gwargwado daga Alhaji har Hajiya sun yi iya bakin ƙoƙarinsu wajen ganin sun ba yaransu tarbiyya da ilimi na bokon da addini.

Fu’ad ya fita daban da sauran ‘yan gidansu. Tun tasowarshi ba shi da aiki sai buga wasan ƙwallon ƙafa.

Ya sha ƙin zuwa makaranta akan wasan ball. Tun suna duka da faɗa har suka gaji suka soma bashi goyon baya. Tun yana aji huɗu a Secondary ya soma jagorantar garin Kano fita ƙwallo zuwa sauran garuruwa. Nasarorin shi sun soma daga shekaru ƙasa da sha takwasa. Lokacin da ya shiga aji shida a Secondary ne ya samu ɗaukaka zuwa ƙasar Europe.

Dole su Alhaji Salman suka ƙyale Fu’ad ya tafi. Da ƙyar ya dawo ya zana jarabawar WAEC kaɗai.

Can ya nemi gurbin karatu. Classes ɗin shi ma online yake yinsu saboda rashin lokaci.

Yakan dawo gida da ya samu lokaci. Ya kasance da girman kai da tsanar talakawa wanda Hajiya Aisha da Alhaji Salman ke dangantawa da kuɗin da yake da su a shekaru ashirin da biyu.

Don su duk arziƙinsu mutanene masu sauƙin kai da girmama ɗan Adam. Labarin zai fara ne ranar da Fu’ad ya cika shekaru Ashirin da biyu a duniya.

*****

22 December 2005

“Kasan na kusa tafiya wallahi.”

Cewar Lukman da alamun ƙosawa a muryarshi. Dariya Fu’ad ya yi da ko gezau maganar Lukman ɗin ba ta shige shi ba. A nutse yake ɗaura takalmin shi. Wani tsaki Lukman yaja.

“Wani irin iskanci ne wannan? Ka tara mutane wajen minti talatin ka tsaya yanga. Banza kawai.”

Bai dai ce komai ba. Banda Lukman ɗin babu wanda ya isa ya tsaya saman kan shi yana mishi irin waɗannan maganganun.

Lukman abokinshi ne tun suna yara don maƙwafta ne. Abokantakarsu ta ƙara ƙarfafa zumunci tsakanin iyayensu.

Ko yanzun da Fu’ad ba cika zama ya yi ba. Ba shi da wani abokin da ya wuce Lukman. Ba ma mai iya jure zaman kwana biyu da halayyarshi.

Ɗagowa ya yi ya sauke idanuwanshi da suke ruwan ƙasa masu wani irin haske akan Lukman.

“If you will stop nagging for a minute za ka ga nagama shiryawa.”

Harara Lukman ya watsa mishi. Ya buɗe ƙofar ya fita Fu’ad ya bi bayanshi. Har sun kai ƙofa ya tuna ya bar wayoyinshi. Da gudu ya juya don ya ɗauko, dai-dai tahowar Atika mai aikinsu da sam ba ta kula da Fu’ad ɗin ba.

Karo suka yi har sai da ta faɗi . Jikinta na rawa ta miƙe tana ba shi haƙuri.

Wani irin mari ya ɗauke ta da shi .

“Daƙiƙiyar ina ce ke?”

Lukman ya ƙaraso da sauri ya ture shi.

“Atika je ki please.”

Idanuwan yarinyar cike da hawaye ta wuce da hanzari. Wani kallo Lukman ya yi masa.

“Tir da halinka wallahi. Kai fa ka tureta still ta baka ha…….”

Katse shi Fu’ad ya yi da faɗin:

“Kar ka sake ɓata min mood ranar birthday ɗina. Ka riƙe wa’azinka ba na so. Muje kawai na fasa ɗaukar wayar.”

Girgiza kai kawai Lukman ya yi suka fita. Ganin Benz ɗin da suka tunkara yasa Lukman yi wa Fu’ad kallon ba ka da hankali.

Dafe ƙirji ya yi.

“Na shiga uku ni Lukman. Don ubanka da wannan motar za kai stunt?  Rashin sanin darajar kuɗi ko?”

Fu’ad ya kwashe da dariya.

“chill mana. Birthday ɗina ne fa. Da ita dai za mu fita. Hamza na can da motar da zan yi amfani da ita. Ba na so momma ta yi faɗa ne.”

Lukman ya buɗe baki ya kai sau uku yana rufewa. Don ya tabbatar motar da zai ragargaza tafi miliyan biyar. Mota ya buɗe ya shiga da fatan shiriya wa Fu’ad a ranshi.

*****

Suna ƙarasawa wajen Fu’ad ya fito aka ruɗe da sowa da ihu.

“Moh!  Moh!! Moh namu!!!”

Kamar yanda suke kiranshi. Wani murmushi ya ƙwace masa. Sabon girman kai na ƙara ratsa shi.

Ko minti goma ba su yi ba. Lukman na gefe yana kallon yadda Fu’ad ɗin ke ta gaisawa da jama’a cikin yangar shi.

Wayar shi ta ɗau ruri. Ya fito da ita ya matsa nesa saboda hayaniya don ya ga Fa’iza ce.

Ɗauka ya yi da sallamarshi.

“Yaya Lukman in kuna tare da Yaya Fu’ad ku zo yanzun, Hajiya babba ce ta rasu, yanzun nan Abba yayo waya.”

Salati Lukman ya hau yi. Jikinshi ya yi sanyi sosai. Ya kasa ma amsawa Fa’iza  har ta kashe wayarta. Hajiya babba kakarsu Fu’ad ce, sukan je Bichi gaishe da ita da ‘yan gidansu Fu’ad.

Tsohuwar akwai kirki da karamci. Lokaci yayi. Ya kai mintina biyar a wajen yana tuno Hajiya Babba da kirkinta.

Jiki ba ƙwari ya ƙarasa wajen da Fu’ad yake da suke shirin fara wasan su da mota yace mishi yazo.

“Koma menene ya jira ni in gama abinda zanyi.”

Fu’ad ɗin ya amsa rabin hankalinshi kan Lukman.

“Hajiya babba ce fa Allah ya yi mata rasuwa shi ne momma ta ce muje yanzun.”

Fito da idanuwa waje Fu’ad ya yi tare da faɗin:

“Holy crap! Dammit. Bad timing Hajiya. Why yanzun?”

Lukman kamar ya kwaɗa mishi mari. Halayyar Fu’ad sai ka ce ƙara lalacewa take yi ma duk rana. Wato ba ma mutuwar bace ta shige shi. Yana kallo ya wuce ya yi magana da Hamza sannan ya dawo. Suna mota yana fadin:

“Tsohuwar nan ta yi min tsiya wallahi. Ran birthday ɗina.”

Lukman da yake ta ma Hajiya babba addu’a ya juya ya kalli Fu’ad kafin ya maida hankalinshi kan tuƙin da ya ke yi tare da faɗin:

“Shekaru nawa amma kana surprising ɗina wasu lokutan wallahi. Kakarka ce fa. Ita ta haifi Abba. Haba Fu’ad, mutuwa fa ta yi, amma kai tunanin banzan party ɗinka kake yi ko?  Addu’a ma baka san ka yi mata ba?

Kaima zaka mutu.”

Taɓe baki ya yi alamar bai shige shi ba juya idanuwanshi yace:

“Whatever. Allah ya jiƙanta. Ba ka da aiki sai wa’azi, saikace ɗan gidan limamai.”

Lukman bai ƙara kulashi ba har suka kai gida. Din ya san zasue iya yin rikici in ya biye masa.

*****

Da lukman ɗin suka tafi Bichin. Waya kaɗai ya yi wa mamanshi ya faɗa mata rasuwar. Itama ta ce za su biyo su a baya. Fu’ad ne ke tuƙin wannan karon. Lukman na gefe. Sai yayar Fu’ad ɗin Aunty Fatima da wata cousin ɗinsu Aunty maryam. Kukan da suke yi ya soma kular da Fu’ad. Don shi bai ga abin kuka ba. Shekarar Hajiya nawa a duniya. Ai ta sha miya a ganinsa. Ba su tsagaita da ‘yan koke-kokensu ba sai da suka ɗauki hanya sosai.

Banda Lukman da ya yi wa Fu’ad magana akan ya rage gudu su Aunty Fatima ko kula su ma bai yi ba, bai kuma rage gudun ba.

Har suka shiga garin Bichi duk lungun da suke bi Fu’ad bai rage gudu ba. Ba kuma ya horn in zai shiga kwana. Ido Lukman ya saka masa. Suna karya wata kwana sai ga wani babban mutum magidanci da itace akanshi. Rashin horn ɗin da Fu’ad bai yi ba ya sa bai kula da shigowarsu ba sai a ƙurarren lokaci.

Da hanzari yai ƙoƙarin kaucewa. Itacen kanshi ya watse akan motar su Fu’ad ɗin da ko’ina. Wani mugun birki Fu’ad ya taka da ya razana su Aunty Fati. Motar ya buɗe a fusace ya ƙarasa wajen mutumin da ya faɗi a ƙasa.

Ya tashi yana kakkaɓe jikinshi. Dai dai fitowar su Aunty Fati daga mota ji kake wani

Tas!

Fu’ad ya ɗauke mutumin da a haife ya haifi irin Fu’ad ɗin uku da mari.

“Ba ka ganin mota ne?  Wane irin jahilci ne wannan?”

Daga Aunty Fatima har su Lukman suka ƙaraso wajen da salati.

Marin Fu’ad Aunty fatima ta yi tana salati da girgiza kai da ɗanyen aikin da Fu’ad ya yi.

Mutumin ta kalla da yake riƙe da kunci yana kallon Fu’ad da mamaki a fuskarshi.

Hannu Fu’ad ya ɗaga Lukman ya riƙe shi a tsawace yace:

“Haba mana Fu’ad ya isa haka. Wane irin masifa ne wannan.”

“Lukman da ka ƙyale shi ya rama marin. Don wallahi ba wata rashin kunya da zai nuna minkuma.”

Kallonsu Fu’ad ya yi a ƙyamace ya wuce ya koma mota yana huci.

Har ƙasa anty fatima ta tsugunna tana ba mutumin haƙuri. Su duka suka haɗa baki har da Lukman.

Mutumin ya jinjina kai.

“Bakomai ‘yata. Kuje kawai, Allah ya shirya.”

Mota ta koma ta ɗauko kuɗi a jakarta ta dawo inda mutumin ke tattara itacen shi.

“Baba ga wannan.”

Ya dago ya kalleta. Ya girgiza kai yace.

“Nagode ‘ya ta amman bazan karɓa ba.”

Wasu hawayen takaici suka zubo wa Aunty Fatima. Ta goge su ta tsugunna murya na rawa tace.

“Ba don abinda ƙanina ya yi maka ba baba. Kyautatawa ce don girman Allah ka karɓa.”

Ya jima yana kallonta kafin ya sa hannu ya karɓa yace:

“Nagode”

Ta juya ta shiga mota.

<< Akan So 5Akan So 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×