Skip to content
Part 7 of 48 in the Series Akan So by Lubna Sufyan

“Fuad yaushe ka ƙara lalacewa haka? Wancan mutumin bai isa ya haifeka ba har za ka iya ɗaga hannu ka mareshi?”

Anty Fatima ke faɗi rai a ɓace.

Wani numfashi ya ja da alamun relief. Yace:

“Thank God ba shi ya haifeni ba. And karki sake ɗaga min hannu ba yaro bane ni.”

Wani abu ya tokare mata a wuya. Anty maryam tace:

“Fu’ad rashin kunya ko?”

Juyowa ya yi daga inda yake zaune ya watsa mata wani kallo tare da faɗin:

“Mind your own fucking business.”

Fu’ad ke rashin kunyar amma Lukman da ke zaune shi yake jin kunya. Gaba ɗaya ji yake da ma motar su Fa’iza ya shiga da bai ga wannan ɓacin ran ba.

“Ka wuce muje Fu’ad. And do us a favour ka yi shiru mu ji da abu ɗaya.”

Lukman ya faɗi. Ya juya ya kalli anty Fatima da ke sharar hawaye. Anty maryam kuma tayi tsuru-tsuru a gefe yace:

“Don Allah anty ku yi haƙuri. Abar maganar nan. Mu ji da abu ɗaya.”

Kai kawai Anty Fatima ta ɗaga. Fu’ad ya wani fizgi motar duk yana gwara su da jikin motar.

“Maza kashe mu to.”

Lukman ya ce rai ɓace. Ko kula shi bai yi ba. Kawai tafarfasa yake a ciki. Kamar shi Anty Fatima za ta ɗaga hannu ta mara akan wani tsohon daƙiƙin talaka. Ya tabbata da ba su haɗa jini ba sai ya rama marin shi. Kuma sai ya sa an kulle masa ita. Suna ƙarasawa ya samu waje ya yi parking. Mutane ne cike a unguwar kamar za ta fashe.

Ana ta alwala kasancewar yamma ta yi sosai. Don a hanzarta a kaita makwancinta.

“Ku nemi wani ride ɗin home.”

Fu’ad ya faɗi bai jira amsarsu ba ya fice ya doka murfin motar da ƙarfi har wasu dake gefe suka juyo suka kalle shi.

“What?”

Ya buƙata a tsawace. Suka sadda kansu ƙasa. Ya ce ‘yan sa idon banza kawai a ranshi.

Fitowa su anty maryam suka yi suna ta kuka. Don yanzun mutuwar ke ƙara shigarsu da wani sabon yanayi. Ba su bi takan Fu’ad ba suka wuce abinsu. Lukman ya zo ya raɓa zai wuce shima Fu’ad yace:

“Ina kuma za ka je? Ai ka jira ni ko?”

Cikin idanuwa Lukman ya kalle shi.

“After abinda ka yi wallahi kunya nake ji ace tare muke.”

Yana gama magana ya wuce abin shi. Wani mutum ya yi wa sallama suka gaisa ya karɓi butar hannunshi da Fu’ad ke jin ai ko wajen zai haɗe ba zai iya wanke ko takalmi da ruwan ciki ba.

Ballantana har azo ga jikinshi. Allah kaɗai ya san daga inda butar ta fito da kuma kalar germs ɗin da ke jiki. Motarshi ya buɗe ya ɗauko robar faro ɗaya sabuwa. Ya rufe motar. Wajen ya ƙare wa kallo don bai ga inda zai tsaya ya yi alwala ba.

Da alamar tsantsar takura a fuskarshi ya hango wani dutse. Ya ƙarasa wajen ya zauna ya kwance takalmin ƙafar shi. Alwala ya yi sannan ya mayar da komai ya ɗaure takalmin. Haneef ya hango ya ƙarasa wajen shi.

Wani kallo Haneef ya yi masa daga sama har zuwa ƙasa.

“Ka cire wannan glass ɗin.”

Haneef yace yana ɗauko mukullin motarshi daga aljihu. Ya miƙa masa.

“Motata na bayan can. Kaje ka ɗauko takalmi ka cire na ƙafarka.”

Karɓar mukullin motar ya yi daga hannun Haneef muryashi can ƙasa yace:

“Bana so ana faɗa min abinda zan yi. And menene matsalar takalmina?”

Wucewa Haneef ya yi ya ƙyale shi. Gaba ɗaya gidansu Haneef ne ba ya jurar rashin kunyar Fu’ad.

Ba shi bane babba amma har su Anty Fatima suna ganin girmanshi.

Saboda yana da hankali. Magana ma sai dole yake yinta. Ba ya shiga harkar kowa. Kuma sun fi shaƙuwa da Fu’ad. Ko a yarinta in Fu’ad ya janyo rigimar da ta fi ƙarfin shi Haneef ɗin ke shigar masa dole.

Shi da kanshi yakan rasa ta ina Haneef yake ɓullowa sanda yake buƙatar shi. Wucewa ya yi ya & ɗauko takalman Haneef ɗin ‘yan zire. Ya saka da alƙawarin suna dawowa jana’izar zai sake su.

Don sun bala’in ɓata mishi shiga. Ba don Haneef bane ma ba zai saka ba.

*****

Suna dawowa ya je ya sake takalmanshi. Bai nemi Lukman ba. Shima ya yi zuciyar kowa ya yi harkar shi. Haneef ya lalubo da ƙyar saboda taron mutane. Ya miƙa mishi mukulli yana faɗin:

“Saikun taho.”

Da mamaki haneef yace:

“Meaning?”

“Gida zan tafi. Yunwa nake ji like sosai fa.”

Jinjina kai Haneef ya yi.

“Wai yaushe za ka yi hankali? Will you go and remove that shoe ka dawo a zauna dakai. Kama ga Abba?  Ka mishi gaisuwa?”

Kaman Fu’ad zai sa ihu yake kallon Haneef.

“Abba gaisuwan me zan mishi? Ba na zo ba anyi jana’iza and dare yana yi fa.”

Wani murmushin takaici Haneef ya yi. Muryarshi da alamun gajiya yace:

“Anan za mu kwana har sai an yi sadakar uku.”

Wani pale fuskar Fu’ad ta yi. Ya kwana uku a ina?  Wannan garin da tun da ya mallaki hankalin shi zai iya ƙirga zuwansa. Ya buɗe baki ya tabbatar wa Haneef da cewan ya samu matsala in har yana tunanin zai kwana ɗaya ma ba uku ba a wannan ƙauyen. Kamar daga sama suka ji muryar Abba yace:

“Yawwa Fu’ad ka kira Lukman ku zo zan aike ku.”

Juyawa ya yi da fara’a a fuskarshi yace:

“Abbah…”

Fu’ad ya faɗi da farin cikin ganin mahaifin nashi. Don tun da yazo yau sati ɗaya kenan bai saka shi a ido ba. Da sassafe ya tafi wajen training kafin ya dawo kuma ya fita.

“Fu.ad lemuka za ku siyo da ruwa. Sai nama, ka dai samu mamanku ko ka kirata a waya sai ta lissafa maka.”

ATM Abba ke ƙoƙarin ɗaukowa a aljihu Fu’ad yace:

“No abba. Zan siyo komai ake buƙata. Ka bar shi kawai.”

“Allah ya yi maka albarka. Ya ƙara daukaka ka ji.”

Ya amsa da amin. Abbah ya maida hankalinshi kan Haneef.

“To kai muje ko da za a yi wani abun.”

Lukman ya kira har ta yanke bai ɗauka ba ya yi mishi text.

“Idiot. Abbah ne ya aikemu to mu haɗu a mota.”

Momma ya kira ta faɗa mishi abubuwan da suke buƙata.

*****

Har suka gama siyayyarsu tas Lukman bai kula shi ba. Suka koma gida din su ɗauko kayan sakewa. Gaba ɗaya Fu’ad ji yake an takura wa rayuwarshi. A ina zai kwanta ma?  Me zai ci a ina zai yi wanka? Cake ya kwasa leda biyu ciccike ya ɗebi cincin da yoghurt da yawa.

Zaka rantse sati biyu zai yi. Yawan training din da yake yi yana burning mishi energy da wuri.

Ya san abinda ya ɗiba ya masa kaɗan. Balle ba wani abincin kirki bane. Ko kaya kala takwas ya ɗiba din ba ya iya wuni da kaya ɗaya a jikinshi. A mota ya samu Lukman zaune. Lokacin ana ta kiran sallar Isha’i.

“Ko muyi sallah mu sauke nauyi?”

Fu’ad ya buƙata. Kallon shi Lukman ya yi ya fito daga mota sannan yace:

“Da ace yadda kake kyautata sallah haka halayyarka take da ka ji daɗi.”

Dariya abin ya ba Fu’ad sosai.

“Halina is just fine ɗan rainin hankali. Ka gama fushin kenan.”

Yamutsa fuska Lukman ya yi.

“You disgust me. Ewww”

Da gudu Fu’ad ya bishi ya ruga yana dariya.

*****

Waje suke zaune har wajen tara da wani abu na dare. Haneef na kallon yadda Fu’ad ke sosa hannuwa alaman sauro ya ishe shi. Dariya ya yi ƙasa-ƙasa. Taɓararren banza ya faɗi a ranshi. Gani ya yi abun ya yi yawa don shi kanshi sauron ya dame shi.

Balle kuma Fu’ad da kwata-kwata bai saba shiga irin wannan wurin ba. Kallon shi ya yi shi da Lukman yace:

“Ku tashi mu je in kai ku inda zamu kwana ko?”

Ba musu suka tashi. Gidan wani ɗan uwan Abban suka je bayan gidan Hajiya Babba. Saboda cikin gidan Hajiya Babba mata ne kawai. Kasancewar daga ita sai ‘yan aikinta da take da rai. Sai wasu ‘ya’yan dangi da take riƙewa.

Gidan ba wani babba bane can.

“Taɓɗi”

Fu’ad ya faɗa ganin gidan da suka tunkara. Wani saurayi da zai kai tsaran Haneef da sai lokacin Fu’ad ya kula da shi, ya ƙarasa ya buɗe wani shago jikin gidan da ƙyauren langa-langa. Hannun Haneef ya ja gefe. Kamar za yii kuka.

“Ka san ba zan iya kwana anan ba ko?”

Ya ƙarasa yana nuna shagon da hannu. Hannun Haneef ya kama ya sauke ƙasa yace:

“Last i check ba ka da wani option. In kuma za ka je ka ce ma Abba ba za ka kwana bane sai ka dawo.”

Ƙasa ya ƙara yi da muryar da yakan yi amfani da ita ya samu abinda yake so wajen Haneef ɗin da suna yara.

“In tafi gida. Da sassafe in dawo.”

Kallon baka da hankali Haneef ya yi masa.

“Please…”

Yadda Haneef ya zaro ido zai tabbatar maka da Fu’ad faɗin please ɗin nan da Fu’ad ya yi abu ne mai bala’in wahala a wajen shi.

Numfashi ya sauke.

“Ka haƙura Fu’ad dare ya yi wallahi. Gobe in Allah ya kai mu sai ka koma gida.”

Yadda ya yi da fuska ya ba Haneef tausayi. Don ya san bai saba ba sam. Kama hannunshi ya yi kamar yaro. Ya ja shi zuwa cikin shagon.

Ko’ina a share yake tsaf. Da leda a shimfiɗe sai katifa an lailayeta da zanin gado. Kusurwar ɗakin jakunkuna ne da wasu kaya a rataye jikin ƙusa. Sai takalmansu can gefen wani bango akan siminti wajen da alamu ledar ɗakin ba ta kai ba. Haneef ya ƙarasa ya cire takalminshi ya ajiye inda yagae masu shagon na ajiye nasu.

Ya koma kan katifar kusa da Lukman ya zauna. Fu’ad suka kalla tsaye a ƙofar ɗakin .

Idanuwan nan nashi kalar na turawa sun yi wani haske. Suka bushe da dariya.

Bai ce musu komai ba don gab yake da ya fara kuka. Ya fara takawa da takalmin bai ko kula Haneef da ke mishi magana ba.

Wani farin hanky ya ɗauko daga aljihunshi ƙato ya shimfiɗa akan zanin gadon dake jikin katifar sannan ya zauna kamar wanda zai hau ƙaya.

“Kai da za ka yi birkiɗa akan katifar. Meye na saka hanky kuma? Ko kan leda za ka kwana?”

Cewar Lukman da ya sake bushewa da wata irin dariya.

“Fuck you and damn your mouth.”

Fu’ad ya faɗi yana kai mishi duka.

“Manners Fu’ad. Kamata ya yi ace momma na wanke maka bakinka da sabulu.”

Haneef da yake dariya shi ma ya faɗi. Pillow ɗin dake gefe Fu’ad ya ɗauka ya jefa masa a fuska ya kauce pillow ɗin ya samu Lukman.

Ɗauka ya yi ya rama suka soma hauka cikin ɗakin Haneef yana musu ihu.

“Dan ƙaniyarku mutuwa aka yi mana fa. Kuma ba a gida kuke ba. Ku nutsu please.”

Da ƙyar Haneef ya samu Fu’ad ya cire takalmin shi ya bar socks.

Ga katifa ɗaya su uku. Ga sauro. Tashi Fu’ad ya yi ya haɗa kanshi da gwiwa kawai yana jira gari ya waye.

<< Akan So 6Akan So 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×