Skip to content
Part 41 of 48 in the Series Akan So by Lubna Sufyan

“Fu’ad idanuwanka kenan?”

Ɗan sosa kai ya yi yana murmushi. Anty Fatima ta sauke numfashi tare da faɗin,

“Ka kyauta.”

Sai lokacin tun zamanshi falon ya ɗago idanuwanshi ya sauke su kan Anty Fatima da duk wata nadama da ke cikinsu. Saukowa ya yi daga kan kujerar da ya ke zaune ya saka gwiwoyinshi kan kafet ɗin ɗakin ya haɗe hannayenshi waje ɗaya. Muryarshi a dakushe ya ce,

“Na yi laifi Anty. A yafe min don Allah. Ƙaunarku a gareni ta fi min komai muhimmanci a yanzun. Ba zan taɓa iya dawo da shekarun nan ba. Amma zan iya gyara na gaba. Ki yafe min.”

Kallon shi take. Tabbas Fu’ad ya musu laifi su dukansu. Ta na kallonshi ya sa hannu a aljihunshi ya ciro wani abu. Kallonta ya yi yana miƙa mata hannunshi da ke dumtse kafin daga baya ya buɗe shi. Agogo ne na hannu. A ko’ina ta ganshi za ta gane shi. Idanuwanshi ya saka cikin nata. Da wani irin yanayi a muryarshi ya ce,

“I want mi’ sister back. Ina son sister ɗina da ta koya min yadda zan gane wannan agogon na hannuna. Ina son sister na da muke shiga kitchen haɗa salad tare. Ina son sister na da take tare da ni lokacin da nake sneaking zuwa ball.

Anty fatima please…”

Ya ƙarasa maganar yana sauke muryarshi ƙasa idanuwanshi cike da hawayen da ya ke riƙe da su. Komai na dawo mishi kamar lokacin ya faru.

*****

Kitchen suke da Anty Fatima ta na yanka ƙwan da ta dafa za ta haɗa musu salad. Yana tsaye gefe ta ce mishi,
“Fu’ad ƙarfe nawa. Ga agogona nan kusa da kai.”

Ɗaukar agogon ya yi. Ya tsura mishi idanuwa. Babu lamba ko ɗaya a jiki. Daƙuna fuska ya yi ya ɗan ɗaga girarshi tare da faɗin,

“Ya zan yi in gane? Babu number ko ɗaya a jiki.”

Dariya Anty Fatima ta yi tare da faɗin,

“Karka ce min ba ka iya reading wannan agogon ba Fu’ad.”

Cije leɓenshi na ƙasa ya yi yana ware mata idanuwanshi. A kunyace ya ce,

“karki faɗa wa Haneef. Zai ta tsokanata.”

Fuskarta babu alamar wasa ta ce mishi,

“Ba zai ji ba. Zan koya maka.”

Murmushi ya yi.

“Really?”

Kai ta ɗaga mishi.

“You are the best sis kin sani ko?”

Dariya kawai Anty Fatima ta yi tare da faɗin,

“Gashi na matane da na bar maka.”

Da sauri ya ce,

“Ban damu ba. Ina so sai in sa a aljihuna.”

Kallon fuskarshi ta yi. Da gaske ya ke son agogon in ta bar mishi.

“You can have it. Karka zo wajena in wani ya tsokane ka da agogon mata.”

“Zan fasa bakin duk wanda ya min dariya saboda ke kika ba ni.”

*****

Hawayen da ya ke idanuwan Anty Fatima suka zubo. Hannu ta sa ta karɓi agogon ta na juya shi.

Bata taɓa zaton Fu’ad na da shi ba har lokacin. Bata sake ganinshi da shi ba, bata kuma tambaya ba. Hannu ta sa ta goge idanuwanta muryarta na rawa ta ce,

“Kana da shi har yanzu daman?”

Kallonta ya yi da murmushi ya ce,

“Ina mantawa na ɗaura a hannuna. Saina ɗauko na duba na ga ya dainayi na ke tunawa.”

Dariya ta ɗan yi.

“Fu’ad.”

Katse mta ya yi da faɗin,

“Please. Please i want her back.”

“Ka tashi Fu’ad. Komai ya wuce. Your sister is here and always will be.”

Murmushi ya yi cike da jin daɗi ya miƙe ya zauna kan kujerar.
“Har yanzun watermelon eyes ne da ke Anty Fatima.”

Daƙuwa ta yi mishi ya kwashe da dariya. Yana jinshi wani light. Miƙewa ya yi yana faɗin,

“Ba ni agogo mna ni kam in wuce. Yamma na yi sosai.”

Miƙa mishi ta yi tare  da faɗin,

“Saura mu sake nemanka mu rasa.”

Dariya kawai ya yi yana wucewa.

“Ni kam sai mun yi waya.”

“Ka gaishe min da su momma.”

Ya amsata sannan ya fice.

*****

A hanya ya yi sallar magrib sannan ya koma gida ya samu Hassan zai maida su Khadee gida saboda washe gari duk yaran suna da Islamiyya. Kiran Hassan ya yi ya zaro credit card ɗinshi ya ba Hassan tare da faɗin,

“Ka biya da su ka siya musu ko chocolate. Ice cream. Ko me dai suke so.”

Karɓa Hassan ya yi. Har ya juya Fu’ad ya ce mishi.

“Ka siya duk abinda kake so.”

Girgiza kai Hassan ya yi.

“Ina aiki bro. Ka manta.”

Dariya Fu’ad ya yi.

“Ka girma ko?”

Ɗan ɗaga mishi kafaɗa Hassan ya yi sannan ya wuce abinshi. Falon ya ƙarasa ya samu Nana na kwance kan kujera ta yi pillow da cinyar Momma tana bacci.

Ya samu waje ya zauna yana sauke ajiyar numfashi. Gaba ɗaya jinshi ya ke a gajiye. Ba irin gajiya ta ciwon jiki ba. Jinshi ya ke emotionally drained. Kallon Momma ya yi ta yi mishi murmushi.

“Mun gama magana da abbanku. Da ya ce ku je yau ma. Na ce a bari zuwa gobe tukunna da safe in Allah ya kaimu. Sai ka kira Safiyya ka faɗa mata ko?”

Jinjina kai ya yi.

“Allah ya kaimu. Bari in je sallar isha’i in dawo.”

Ya ƙarasa maganar yana miƙewa.

“Allah ya karɓa mana.”

Ya amsa da amin yana ficewa.

*****

Yana dawowa daga sallar isha’i abinci ya ci ya wuce ɗakinshi ya watsa ruwa sannan ya sake kaya. Ya sa wata T-shirt marar nauyi da three quarter loose. Ƙasa ya sauko zuwa falo. Yana shirin kiran Momma ya ji ya Nana sai gata ta fito jikinta sanye da rigar bacci pink sai hular dake kanta ma pink.
Wani irin dokawa zuciyarshi take yi da ƙaunarta. Murmushi ta yi mishi ta ƙarasa inda yake ta kama hannunshi. Kujera suka samu suka zauna. Nana ta kalle shi tana ware idanuwanta kan fuskarshi. Tun kafin ta furta ya karanci tambayarta cikin idanuwanta.

Don haka ya hutar da ita ta hanyar amsa ta da faɗin,

“Ni da Mumynki. Za mu koma da aurenmu gobe in Allah ya…”

Bai ƙarasa maganarshi ba ya ji ihun murnar Nana ta faɗa jikinshi ta zagaya hannuwanta kan bayanshi ta ƙanƙame shi.

Yanajin dariyar da take yi. Shi ma dariya ya yi. Farin cikinta na ƙara mishi wanda ya ke ji. Da ƙyar ya samu ya ɓanɓareta daga riƙon da ta yi mishi.

Ta maƙe kafaɗarta tana sake komawa ta ƙanƙame shi. Ƙyaleta ya yi sai da ta gama murnar da kanta sannan ta ɗago daga jikinshi ta gyara zamanta kan kujerar.

Kanshi ta tallabo da hannuwanta duka biyun ta haɗa goshinsu tare. Ji take ya gama mata komai na duniya.

“Na gode dady. I love you so much. Na gode sosai.”

Cikin idanuwa ya ke kallon ‘yar tashi yana jin ƙaunarta har cikin jininshi. Yanajin ƙaunarta ta yadda ba zai iya fassarawa ba. Wannan son is priceless. Kalar ƙaunar dabance da wadda yake ji akan Safiyya.

“Ina Mummy yanzun?”

Muryashi can ƙasa ya ce mata,

“Tare da mummynta da dadynta.”

Sake ware mishi idanuwa Nana ta yi. Ta sauke murya ta ce,

“Suna nan?. Sauran grannies na suna nan? Mummy ba ita kaɗai bace yanzun?”

Kanshi da ke jikin nata ya ɗan ɗaga. Yana kallon yadda ta lumshe idanuwa wata nutsuwa na sauka kan fuskarta. Idanuwanta a lumshe har lokacin goshinta na haɗe da nashi ta ce,

“Na taɓa tambayarsu. Mummy ta yi ta kuka ban sake ba. Me ya faru dasu?”

Raba goshin su yayi ya tallabi fuskar Nana cikin hannuwanshi. Wani irin nauyi yake ji cikin zuciyarshi. Amman ya fi son wannan gaskiyar ta fito daga bakinshi. Ya fi so ya faɗawa Nana da kanshi. Sai dai wane irin bayani zai wa yarinya ‘yar shekara sha ɗaya.

Cikin sanyin murya ta ce,
“Ba saika faɗa min ba in baka so. Na ji daɗi da mummy take tare da su. Shi kaɗai ya isheni.”

Wani abu ne ya yi masa tsaye a wuya. ‘She is so fucking matured’ ya faɗi a ranshi a fili kuma ya ce mata,

“No zan faɗa miki. Ban san ta ina zan fara ba.”

Ɗaga mishi gira ta yi da ke nuna ita ma ba ta san ta inda ya kamata ya fara ba. Ya sauke ajiyar zuciya.

“Ina da shekaru ashirin da biyu Nana. So young and stupid. Na yi wani kuskure da bai kamata in yi ba.Bazan iya faɗa miki kuskuren ba. Amma abu ne marar kyau sosai. Hakan ya ɓata komai. Ni da mummynki da kowa namu.”

Kai ta jinjina mishi alamar ta fahimta. Bata son ganin yadda idanuwanshi suke. Kamar abinda yake faɗa yana mishi tsananin wahala da ciwo. Hannunshi da ke fuskarta ta ture tana kama shi cikin nata ta dumtse. Muryarta a tausashe ta ce,

“Ba na son ji dady.”

“Why?”

Ya buƙata yana tsare ta da idanuwana.

“It is hurting you. Ni kuma ba na so.”

Hugging ɗinta ya yi. Yanayin na karya mishi zuciya. Wannan yarinyar daban take a cikin mutane. Bai taɓa ganin irinta ba.

Muryarta cike da ƙaunarshi ta ce,

“Ka gyara komai ko dady? Komai ya wuce yanzun?”

Muryarshi a dakushe da yanayin da yake ji ya ce mata,

“Yeah. Komai ya wuce thanks to you.”

Dariya ta yi tana ɗagowa daga jikinshi.

“Kira mummy in mata good night.”

Ba musu ya ɗauko wayarshi ya duba. Tunawa ya yi ba shi da lambar ɗin Safiyya ma. Ya yi wiƙi-wiƙi da idanuwa yana jin wata yar kunya ta kamashi. Sosai Nana ta ke dariya. Ya daƙuna mata fuska.

“Ka faɗa in ji dady.”

Kai hannu ya yi ya ja mata hanci ta ture hannunshi tana dariya sosai. Karanto mishi lambar Safiyya ɗin ta yi. Ya kira bugu ɗaya ta ɗauka da sallama. Nana ya miƙa wa. Ta karɓa suka gaisa.

“Mumny bani su mu gaisa please please please.”

Dariya Safiyya ta yi daga ɗayan ɓangaren ta ce,

“Sun kwanta Nana. Kema ki kwanta ki ce dadynki ya kawoki gobe sai ki gansu ok.”

Turo baki Nana ta yi ta kalli Fu’ad da ya ɗaga mata gira da tambayar lafiya?

“Wai sun yi bacci, gobe ka kai ni.”

Tace ma Fu’ad ya ɗaga mata kai. Safiyya da ke ɗayan ɓangaren ta ce,

“Kika ce me Nana?”

“Ni da dady ne.”

Bata jira amsar Safiyya ba ta miƙa wa Fu’ad wayar. A ɗan daburce ya ce,

“Hello.”

Shiru ta ɗan yi da alama ita ma ta ra sa abinda za ta ce mishi. Kafin ta ce,

“Komai lafiya dai ko?”

“Lafiya ƙalau. Tana lafiya.”

Shiru suka sake yi kafin ta ce,

“Saida safe kenan?”

Da sauri ya ce,

“No. Za mu zo da su Abba gobe.”

“Allah ya kaimu. Ka kula da ita.”

Ya ɗan ɗaga kai kamar ta na ganinshi ya miƙa wa Nana.

“Good night mum. Take care. Love you.”

“Love you too Princess.”
Ta faɗi ta na kashe wayar.

Kallon Fu’ad Nana ta yi.

“That is awkward.”

Ware idanuwa ya yi yana mamakin yadda Nana ta ji turanci haka. Sai kuma ya yi tunanin JSS1 aka ce mishi take kuma da alama makarantarsu na da kyau sosai.

Kuma gaskiya ta faɗa. Wayarsu da Safiyya is kinda of awkward. Dariya ya yi. Hamma Nana ta fara ta kalle shi.

“Na gudu wajen granny dady bacci nake ji.”

Kai ya ɗaga mata.

“Sleep well. Banda snoring.”

Ta wani daƙuna fuska kamar ya faɗi ƙazanta.

“Ewww dadyyyyy!”

Dariya sosai Fu’ad ya ke yi. Nana ta soma dire ƙafafuwa.

“Ni ba na snoring. Ka tambayi mummy.”

Dariya ya ke yi. Sai da ya ga yadda Nana ta daƙuna fuska ya samu ya tsayar da dariyarshi.

“Go and sleep.”

“Bana snoring.”

Ta faɗi ta na ɗora hannuwanta kan ƙugunta. Dariya Fu’ad ya yi.

“Ba kya snoring. Na yarda.”

Murmushi ta yi ta matsa kusa da shi ta sumbaci kumatunshi.

“Good night dady. Love you.”

“Love you more.”

Wucewa tayi. Yana jin tana faɗin,

“Nooooo i love you moreee.”

Ya yi dariya kawai yana sake shigewa kan kujerar. Da ƙyar ya iya miƙewa ya tafi ɗakinshi. Yana addu’a bacci mai nauyi ya ɗauke shi cike da mafarkin Sofinshi.

*****

Tana zaune gaban mudubi tana shafa powder a fuskarta. Hannuwanshi ta fara ji kan kafaɗarta sannan ta sauke idanuwanta cikin nashi ta mudubin da ke gabanta. Murmushi ya yi yana sumbatar gefen fuskarta. Lumshe idanuwa ya yi.

“Ina son ƙamshin turarukan nan naki Jana. Ba na gajiya da jin su.”

Dariya ta yi ta ɗora hannuwanta kan nashi tare da ture su.

“Ni kam ka bar ni in shirya.”

Daƙuna fuska Jabir ya yi.

“Ke yanzun sai ki bar ni gidan nan shiru? Yara duk sun tafi Islamiyya”

Ɗankunnenta ta ke ƙoƙarin sakawa ya karɓe daga hannunta yana maƙala mata ta amsa shi da,

“In ban je ba yau banda lokaci sosai. Rabona da gidan Hajiya an fi sati huɗu fa Honey J.”

Langaɓe fuska ya yi yana ɗaukar ɗayan ɗankunnenta ya saka mata tare da jan kunnen. Dukan hannunshi ta yi tana faɗin,

“Wayyo. Da zafi fa!”

Ɗaga mata gira ya yi.

“Nikam bana jin zama ni kaɗai.”
Juyowa ta yi ta fuskance shi. Idanuwan shi cike suke da rikici. Yau kwana uku kenan da faɗa mishi za ta je gidan Hajiya, yanzun kuma zai rigime mata.

“Kai ɗan zaman majalissar da maza suke ba ka yi balle in ce ka fita.”

Hannu ya sa ya mintsinan mata kumatu yana matsewa. Ta ture shi tana shafa wajen.

“Kin san babu abinda na tsana banda zaman majalissa. Me suke banda gulma da kallon matan mutane.”

Ta shagwaɓe fuska. Hannunta na kan kumatunta inda ya mintsina.

“Shi ne sai ka mintsine ni?”

Ya ɗaga mata kai.

“Kisan yadda za ki yi da ni. Mu je in kai ki gidan Hajiyar ma ko? Sai mu gaisa.”

Girgiza kai ta ke yi.

“No. I mean in caps. Wallahi na gode. Ni sai bayan Azahar zan dawo idan na je.”

Ta san halinshi da wuya ya bari su yi minti sha biyar.

“Honey J. Ka ga ka ƙyale ni in shirya.”

Hannuwanshi ya haɗe kan ƙirjinshi ya zuba mata idanuwanshi masu rikita mata lissafi. Da sauri ta ce,

“Ka je wajen Aina.”

Din ba ta son yadda faɗar hakan kawai ya ke saka zuciyarta wani irin tafasa. Ya karance ta tsaf. Ƙarasawa ya yi inda take ya sa hannuwanshi ya tallabi fuskarta. Cikin idanuwa ya kalleta kafin ya manna mata sumba mai taushi.

“Sai kin dawo. Babu inda zan je. Zan kwanta in yi bacci.”

“I mean it Honey J. Ka…”

Kallon da ya yi mata ya sa ta rufe bakinta ya jinjina kai.

“You are doing enough. Nasan me kike dannewa Akan sona Jana. Ba sai kin ƙara da abinda zai cutar min da ke ba. Bana so, kina jina. Karki ƙure haƙurinki.”

Kai ta ɗaga mishi a sanyaye ta ce,

“Thank you.”

Da hannuwanshi da ke fuskarta yake nuna mata yadda muhimmancinta ya ke a wajenshi.

“Ki kulamin da kanki.”

Ta ɗaga mishi kai tana sa hannunta ta cire nashi da ke fuskarta saboda yanda yanayin kallon da yake mata da komai da take karanta cikin idanuwanshi suke saukar mata da kasala.

Cikin kanta take ƙirga satikan da suka rage musu. A ƙasan zuciyarta tana addu’a kar komai ya canza musu. Kar soyayyarsu ta girgiza.

Da wannan tunanin a ranta ta ƙarasa shiryawa. Sai da ta ƙarasa inda yake zaune kan gado ta sumbace shi sannan ta fice.

*****

Zaune take a ƙasa. Ta ɗora kanta kan cinyar Hajiyarsu da ke zaune ƙasa. Kuka take mai cin rai.

Gaba ɗaya abinda take dannewa ne a zuciyarta a kwanakin nan take ture shi gefe ya buɗe mata daganin Hajiyarsu.

Hannu Hajiya ta ɗora kan Jana da tana shigowa falon ta ƙaraso ta zauna gabanta ta ɗora kanta a cinyarta tana wani irin kuka.

Da Jabir bai zo har gida ya faɗa mata ba. Da yanayin kukan Janar ya ɗaga mata hankali. Bata yi ƙoƙarin hanata ba. Kawai ta ɗora hannunta a kanta ne cikin son nuna ma ‘yar tata tana tare da ita a koda yaushe. Ɗago fuska Jana ta yi da harta kumbura ta kama hannuwan Hajiya tana wani gogasu kan fuskarta.

Cikin kuka take faɗin,

“Bana baƙin ciki da auren da Jabir zai yi Hajiya, duk da na kasa hana zuciyata zafin kishin shi.

Babu wanda zan gaya ma inajiny tsoron auren na sai ke. Babu wanda zan nunama rauni na ya fahimta Hajiya. What if ta zo ta tarwatsa mana komai?”

Cikin idanuwa Hajiya ta kalli Jana murya a tausashe ta ce,

“Na fahimci tsoranki Murjanatu. Na fahimta wallahi. Na kuma jinjija ma ƙoƙarinki. Ina alfahari da ƙarfin halin da kika nuna.

Ko ni bance zan iya irinshi ba. Ki godema Allah wannan baiwa ce da ba kowacce mace ya yi wa ba.

Na ji daɗi da yafda ba ki yi wa ƙaddara gardama ba duk da kina tsoranta. Abu biyu zuwa uku zan faɗa miki.”

Kai Jana ta ɗaga tana sauraren Hajiya kamar gaba ɗaya duniya bata da wani aiki da ya wuce hakan. Har ranta tanajin yadda ruwan da take ciki ya kawo har bakinta. Bata da abin kamawa ta fito daga cikinshi da ya wuce shawarwarin mahaifiyarta.

Hajiya ta ci gaba da fadin,

“Karki yarda zafin kishi ya canza ƙauna da tausayin da ke tsakaninki da mijinki.

Karki bari addu’a ta kufce miki a kowanne hali da kika tsinci kanki.

Ki zauna da ita da zuciya ɗaya. Ko za ta cuce ki Allah zai zamana yana tare da ke saboda babu mugun abu a zuciyarki.

Ki koma gidanki ba tare da tsoron nan a zuciyarki ba Murjanatu. Ƙaddararki ta jima da bushewa. Tsoro ko rashin hakan ba zai canzata ba.

Hanyoyi na Ubangiji suna da girma. Ki yi addu’ar alkhairi. Ki miƙa wa marubucin ƙaddararki komai naki. Zai nuna miki hanya idan kin rasa ta.”

Wata irin nutsuwata daban Jana ta ke ji a cikin zuciyarta. Hannu ta sa ta goge fuskarta. Ta sake kwantar da kanta kan cinyar Hajiya. Muryarta a dishe saboda kukan da ta yi ta ce,

“Madallah da mahaifiya irinki Hajiya. Madallah da mahaifiyar da ta ke kama hannuna a koda yaushe zuwa hanyar gaskiya.

Ina ƙaunarki Hajiya. Allah ya bar min ke.”

Dariya Hajiya ta yi.

“Ke dai ki ce Allah ya haɗa ni da mahaifinku a Aljanna. Ita na fi buƙata.”

Murmushi Jana ta yi tana wa mahaifinta addu’ar samun rahma a zuciyarta. Kafin ta sauke numfashi.

*****

Da safe wajen ƙarfe goma duk sun gama shiryawa daga shi har Abba. Lukman da Haneef ma sun zo gidan. Nana da camera a hannunta su Haneef sun biye mata sai shiririta suke. Kar Lukman ya ji labari. Fu’ad ya kalle su ya girgiza kai. Gaba ɗaya Nana ta mayar da su ‘yan yara. Har ya juya ya maida hankalinshi wajen Abba ya sake juyowa da sauri.

Kallonsu ya ke sai yake tunanin shi ma kenan haka yake zama yaro in yana tare da ita kenan?

Ya buɗe baki zai yi magana Yaya Babba ya shigo. Su duka gaishe da shi suka yi, shikuma ya gaishe da Abba da Momma.

Fu’ad ya kalla. Jeans ne blue a jikinshi da riga fara sal da ita. Ya girgiza kai tare da faɗin,

“Kai haka za mu je gidan surukai da kai da ƙananan kaya?”

Sosa kai Fu’ad ya yi yana ware idanuwa tare da faɗin,

“Banda ko ɗaya ne.”

Haneef Babban Yaya ya kalla.

“Kayanka ba za su yi ma Fu’ad ba?”

Girgiza kai Haneef ya yi. Don Fu’ad ya fi shi tsayi yanzun kam. Na Lukman kuma daga tsayin har girman ya mishi kaɗan. Sauke ajiyar zuciya Babban Yaya ya yi.  

“Allah ya rufa asiri to.”

Abba da Momma kam dariya suke musu. A hankali Nana ta miƙe ta taka har inda Babban Yaya yake. Kallonshi ta ke yi.

Sai lokacin ya kula da ita.

“Ina kwana Baba Babban Yaya.”

Ta ce mishi don haka ta ji suna kiranshi Babban Yaya. Lukman ya fara kwashewa da dariya kafin su Haneef su ɗauka. Har Babban Yaya sai da ya murmusa. Kallonsu Nana take cikin rashin fahimtar me suke ma dariya. Kamo hannunta Babban yaya ya yi.

“Rabu da su Nana. Kina lafiya?”

“Lafiya ƙalau, na gode.”

Ware idanuwa ya yi da ɗan mamakin wayon yarinyar. Kafin ya kalli su Haneef ya ce,

“Mu je ko?”

Ba musu suka miƙe. Lukman ne ya kama hannun Nana suka fice. Momma na musu Allah ya bada sa’a. Mota ɗaya suka shiga da Babban Yaya da Abba. Su kuma su Haneef suka shiga mota ɗaya. Fu’ad ke tuƙin don shi ya san gidan.

*****

Ƙofar gida suka tsaya Fu’ad ya sake kiran Safiyya ya ce musu suna ƙofar gida.  Ko mintina biyar ba a yi ba tsakani ta kira ta ce su shiga. Ƙwace hannunta Nana ta yi daga na Lukman ta ruga da gudu cikin gidan Lukman ya ce,

“Au Nana don mun zo ko? Za ki fito ki same ni.”

Bata juyo ba dariya kawai ta yi. Suka shiga ciki su dukansu. A falon da suka shiga jiya aka tare su. Ware idanuwa Fu’ad yake ko zai ga Safiyya, amma babu alamar ko Nana ma balle ya yi tunanin zai ga Safiyya.

Inna ma suna gaisawa da su Abba ta  kawo musu lemuka da ruwa ta fice daga ɗakin. Su dukansu ruwan kawai suka sha. Babban Yaya ne kawai ya fasa lemon exotic guda ɗaya ya sha. A nutse suke magana tsakanin Abba da Baba.

Fu’ad kam ba ya jin me suke faɗa kwata-kwata saboda hankalinshi ba akansu yake ba. Zuciyarshi bata tare da su.Tana wajen Safiyya a yanzun. Mamakin yadda rayuwa ta canza musu lokaci ɗaya yake. Canji ta yi musu me kyau.

Ƙaddararsu ta sauya su daga duhun da ta jefa su zuwa haske mai ban mamaki. Lukman ya zungure shi. Da sauri ya ɗago kai ya kalle shi. Ware mishi idanuwa ya yi alamar ya dawo da hankalinshin kan maganar da ake yi don ya kula ba ya tare da su.

Yanajin su Abba suka tsayar da magana cewa ranar za a ɗaura aure ƙarfe huɗu. Saboda a samu damar sanarma mutane.

Babu ma yadda ba su yi da Baba ba akan ya karɓi sadakin ya riƙe ya ce a’a kawun Safiyya ne zai amsa sai an kira shi tukunna.

Miƙewa suka yi aka yi sallama gaba daya. Su Abba suka fara ficewa. Fu’ad ya kalli Haneef da ya zare mishi idanuwa alamar ya wuce su tafi.

“Bari in kira Safiyya ta turo Nana.”

Tura shi haneef ya yi . Ƙasa-ƙasa ya ke faɗin,

“Ba wata Nana. Ka barta anjima in mun dawo mun tafi da ita.”

Haƙoranshi Fu’ad ya buɗe wa Haneef gaba ɗaya sai ka ce mai tallar abin goge haƙori tare da faɗin,

“To ko nima in zauna anjima in kun zo sai ku tafi da ni?”

“Fu’ad!”

Lukman ya faɗi. Ɗaga kafaɗa Fu’ad ya yi yana ware idanuwa ya ce ma Lukman,

“What? Meye don kun barni?”

Swatting ɗinshi Haneef ya yi a bayan kai ya tsugunna yana faɗin,

“Ouchhhh me na yi ne wai ku?”

“Wuce mu tafi.”

Haneef ya faɗi yana haɗe fuska. Turo baki Fu’ad ya yi kamar yaron da aka ƙwace ma sweet. Ya wuce yana faɗin,

“I so don’t like ku biyun nan.”

Dariya sukai suna tusa shi gaba haneef na faɗin,

“We so don’t care!”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Akan So 40Akan So 42 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×