Skip to content

Akan So | Babi Na Arba’in Da Takwas

5
(1)

<< Previous

Daga bedroom ya fito Zee na zaune a falo kan kafet da plantain chips a gabanta tana ci tana danne-danne da wayar Lukman ɗin. Kusa da ita ya tako ya zauna. Hannu ya kai zai ɗibi chips ɗin ta janye. Daƙuna fuska ya yi.

“Bani wayata nima. Wai meye ma amfanin wayarki? Kullum sai kin cinye min charge.”

Dariya ta yi tana janye wayar gefe.

“Taka ta fi daɗin amfani.”

Kallonta ya yi yana ɗaga mata gira. Don wayarta ta fi tashi tsada da komai.

“Mu yi musanya to.”

Maƙale kafaɗa ta yi.

“Ni dai ka ƙyale ni ina karatuna.”

Kwanciya ya yi yai filo da cinyarta ta ture kanshi. Ya sake komawa.

“Dee ka ɗaga ni. Duk ka moƙale min cinya.”

Dariya ta bashi sosai.

“Ɗan kan nawa guda nawa yake? Na fi jin daɗin kwanciya anan ɗin ne kawai.”

Cikinta ya kalla.

“Nifa na ƙagu in ga ajiyata ta nuna.”

Murmushi Zee ta yi.

“Kwanan shi nawa da zai fito? Don ba a jikinka yake girma bako?”

Gyara kwanciyarshi ya yi.

“Da kinga yadda ake laulayin ciki kuwa.”

“Allah ko? Me za ka yi?”

Juya kwanciyar ya yi yana kallon fuskarta.

“Ai ko wanka sai kin min. In na zauna waje ɗaya sai dai ki ɗauke ni ki mayar wani waje in na gaji.

Ke abinci ma inba a baki ba kuka zansa. Rikici kala-kala.”

Jinjina kai Zee take da wani murmushi a fuskarta. Miƙewa Lukman ya yi daga kan cinyarta yana kallonta muryarshi babu wasa ya ce,

“Wallahi wasa nake miki.”

“Aifa. Ashe ni wahala nake sha. Ga yadda ya kamata ace ina yi.”

Katse mata magana ya yi da faɗin,

“A’a wallahi. Yadda kike yin nan ma ya isheni.”

Girgiza kai ta yi. Za ta yi magana kenan suka ji sallamar su Fu’ad. Da fara’a suka tarbesu.

Zee ta kawo musu ruwa da lemo. Bama su sha ba. Mimi na hannun Fu’ad tana bacci. Yanayin sanyin jikinsu Lukman ya kalla.

Yasan akwai damuwa a tattare da su.

“Lafiya dai ko?”

Ya tambaya cike da kulawa. Takardar da ke hannun Safiyya Fu’ad ya karɓa ya miƙa wa Lukman. Cike da rashin fahimta ya karɓi takardar ya duba. Ta asibiti ce. Sunan Safiyya ne rubuce a jiki. Wani irin dokawa zuciyarshi ta yi ya soma dubawa babu wata nutsuwar kirki a jikinshi.

Idanuwa ya ware. Yana sake ɗaga takardar yana dubawa. Mamaki ƙarara a fuskarshi. Fu’ad ya kalla da ya zuba mishi idanuwa da wani irin yanayi.

Sakkowa Fu’ad ya yi i daga kan kujerar gwiwoyinshi a kasay gaban Lukman. Safiyya ma sakkowa ta yi hawayenta har sun soma zuba.

Kan Fu’ad na ƙasa ya ce,

“Daga asibiti nan muka zo. Ba mu je ko’ina ba. We have to know. We need to know ko hakan zai sa ku karɓeta.”

Da rashin fahimta Zainab take kallon su duka ukun. Don ta ga alama ita kaɗai ce bata fahimci me ke faruwa ba. Takardar da ke hannun lukmanu ta karɓa ta na dubawa.

“Please don’t take her away. Please lukman wallahi..”

Kasa ƙarasawa Fu’ad ya yi saboda yadda wani abu ya tsaya mishi a wuya. Ga ƙirjinshi na wani irin zafi. Kallon Mimi yake da ke baccinta a jikinshi. Hannunta ɗaya riƙe gam da rigarshi. Wani zafi yake ji a ƙirjinshi kamar wuta.

Tunanin raba shi da yarinyar nan kawai ji yake zuciyarshi na neman bugawa. Wasu hawaye masu zafi suka zubo mishi.

Safiyya dake gefen Fu’ad ta ja hijabinta ta goge idanuwanta muryata na sarƙewa ta ce,

“Za mu… Za mu haƙura da babyn jikina…don Allah ku bar mana ita.”

Kallon Zainab Lukman ya yi. Muryarshi ɗauke da wani emotions da ya kasa tsayarwa akan komai ya ce mata,

“Kin gansu ko Zee?”

Ita har sun sakata hawaye ma. Ta sa hannu ta goge su. Har ranta tana musu murnar kyautar nan da Allah ya yi musu.

Kuma zuciyarta na mata wani irin yawo kan ƙaunar da take karanta suna wa Mimi. Ƙaunar da ta ɗauka jininka ne kawai za ka yi wa. Ko tsakanin Fu’ad da Lukman ta fahimci akwai yiwuwar bare ya yi maka ƙaunar da ɗan uwanka ne zai maka.

“Allah sai na faɗa wa Abba abinda kai min. Taya ma wannan banzan tunanin zai zo maka? Safiyya kema ya shafa miki yarinta ko? Allah za ku sani idan na faɗa ku da Abba.”

Ɗago kai Fu’ad ya yi ya kalle shi. Ya sa hannu ya goge fuskarshi. Muryarshi a dakushe ya ce,

“You are not a fucking kid Lukman.”

Harararshi Lukman ya yi.

“Kasan Fu’ad ai ko? To ka kalle shi za ka san na girma sosai. Marar hankali kawai. Wallahi da ba gaban ‘yarka bane sai na kwaɗa maka mari ko za ka dawo cikin hankalinka.”

Zainab ta fara dariya. Kafin Safiyya ta ɗauka. Fu’ad kanshi murmushi yake yi.

Lukman kam ya kasa ganin abin dariya har yanzun.

“Ku bar min gida please. Ku tafi kafin ku ƙara ɓata min rai.”
“Sorry…”

Fu’ad ya faɗi. Sake daƙuna fuska Lukman ya yi.

“Please…”

Kallonshi Lukman ya yi ya ware idanuwa.

“Ɗan sake cewa please mu ji?”

Dariya Fu’ad ya yi.

“Fucking grow up!”

Dariya suka yi a tare. Kafin in a serious murya Fu’ad ya ce,

“Na gode. Ka yi min abinda ko Haneef bai min shi ba Lukman. Ƙaunarka a gareni mai girma ce.

Taya zan iya biyanka?”

Dafa kafaɗarshi Lukman ya yi.

“Ka kasance ɗan uwana har ƙarshen rayuwata. Ka kasance cikin farin ciki gwargwadon iyawar ka. We are even.”

Wasu hawayen Fu’ad ya ji sun cika mishi idanuwa. Bai san me ya same shi da kuka ba kwanakin nan. Sai dai kawai ya ji suna fitowa.

“Haƙiƙa hanyoyin Ubangiji Masu Girma ne. A kanku na yarda ko asibiti ka haɗiye in Allah ya yi niyyar baka kyauta baka isa ka kauce mata ba. Akanku na yarda da cewa a dukkan haƙuri akwai riba. A dukkan tsanani akwai sauƙi sai dai jinkiri zai iya samuwa.”

Allah ya dawwamar muku da farin ciki.”

Cewar Zainab da take jin wata nutsuwa ta daban. Ko da family ɗinta ba su damu da ita ba. Ga wasu da bata haɗa jini dasu ba tana jinsu har cikin jininta.

A kasalance Safiyya ta ce,

“Hmm Zainab. Amin. Amma Allah ya bamu zuciyar karɓar jarabawarshi shi ne addu’ar da muka fi buƙata. Da yawan farin ciki da yawan jarabta. Wannan shi ne asalin usancin mu da mahaliccinmu.”

Kai suka jinjina cike da jin maganganunta. Ganin yadda jikin kowa ya yi sanyi yasa Lukman cewa,

“Kun san da Nana ta ga fuskokin ku me za ta ce? Na yi laifi ko? Uncle ya naga kowa is looking so serious?”

Yanayin muryarshi da tuna Nana ya sa su dariya su dukansu.

Nana ta musu nisa amma memories ɗin da ta bar musu na sa su farin ciki. Har bakin mota su Lukman suka rakasu.

*****

Sai da suka biya gidansu Inna. Babu wata kunya Fu’ad ya faɗa wa su Inna kyautar da Allah ya yi musu. Addu’a suka yi musu gaba ɗaya kafin su wuce gidan su Fu’ad. Yana parking ɗin motarshi suka fito suna cin karo da Haneef.

Gaisawa ya yi da su yana tambayar ya Mimi. Miƙa mishi ita Safiyya ta yi ya ga bacci take ya ce ta barta kar su motsata ta tashi.

Wucewa cikin gida Safiyya ta yi abinta. Ta bar su nan. Hugging ɗin Haneef Fu’ad ya yi cike da farin ciki. Har ya sake shi da mamaki a fuskar haneef. Kafin Fu’ad ya ce,

“Allah heal me Haneef. Sofi ciki gareta.”

Ware idanuwa Haneef ya yi kafin jikinshi ya yi sanyi.

“Allahu Akbar. Allah kenan Fu’ad. Oh! Alhamdulillah.”

Sosai Haneef ya yi murna da mamaki da kuma jinjina lamari na ƙaddara. Kafin su yi sallama Fu’ad ya shiga cikin gidan.

Safiyya ya samu da Momma a zaune. Sallama ya yi, ko jira Momma ta amsa bai yi ba ya ƙarasa tsakiyar falon ya zauna ƙasa.

Ƙafafuwanta ya kama da hannayenshi yana ɗora kanshi a cinyarta. Wai sai da yazo gabanta girman abinda ya samu ya sake lulluɓe shi. Hawaye ke zubo mishi. Ya rasa bakin da zai faɗa wa Momma wannan labarin.

“Fu’ad lafiya? Subahanallah. Safiyya me ya faru?”

Sadda kanta ƙasa ta yi. Kukan da Fu’ad ke yi na sa hawayenta sake zuba. Jin yadda Momma ta ɗaga hankalinta yasa shi cikin kuka faɗin,

“Momma Sofi ciki take da shi. Zan sake haihuwa. Momma addu’ar ku a kanmu da albarkarku ta yi tasiri.”

Hamdala Momma take. Addu’ar ta kullum bai wuce Allah ya basu rabo ba.

“Fu’ad ai abin farinciki ne bana kuka ba.”

Ɗagowa ya yi yana goge fuskarshi.

“Kukan farin ciki ne Momma.”

Murmushi ta yi musu. Basu jima gidan ba suka wuce.

*****

Tsakiyar ɗakin suka tsaya. Mimi na hannun Safiyya. Mayafinta ta cire ta ajiye. Tana kallon Mimi sannan ta kalli Fu’ad.

“Allah ya jiƙan Nana. Za ta so ganin wannan ranar.”

Ƙarasowa Fu’ad ya yi kusa da ita yana haɗe sauran space ɗin da ke tsakaninsu. Yasa hannu ya ɗago da haɓarta.

“Tana inda ya fiye mata nan sau dubu. Sai mu cika aikin da za mu sameta.”

“Allahumma Amin.”

Safiyya ta faɗi da murmushi. Riƙota ya yi ita da Mimi jikinshi yana kissing goshinta.

 “Alhamdulillah da rayuwarmu ta baya ta koya mana darussa da dama. Alhamdulillah da rayuwar da muka samu yanzun.

Alhamdulillah da duk tsarin da Allah ya yi mana nan gaba.”

Riƙoshi ta yi da ɗayan hannunta tana jin wata ƙaunarshi ta daban tana ratsa ta.

“Ina sonka sosai. ƙaddarar da ta haɗa mu ta koya mana darussa da dama. Alhamdulillah.”

Murmushi ya yi.

“Ta ƙara mana imani. Alhamdulillah. Ina sonki sosai.”

Ya faɗi yana lumshe idanuwanshi. Wata nutsuwa na ratsa shi. Tabbas duk wanda ya riƙe Allah ya yarda da ƙaddara mai kyau ko marar kyau yana tare da nasara.

Epilogue

“I feel ridiculous cikin kayan nan wallahi.”

Daƙuna fuska Safiyya ta yi tana ɓalle mishi maɓallin rigar. Ta kalle shi sosai. Kalar shaddar ruwan ƙasa ne mai haske sai ya yi shige da idanuwanshi.

“Ka ga yadda ka yi kyau?”

Tamke fuska ya yi yana jin gaba ɗaya manyan kayan sun takurashi. Duk ya shaƙe.

“Ni kam da kin barni na sa riga da wando abuna.”

Ɗaure fuska Safiyya ta yi.

“Ka kalli luku da Mimi sun girma. Ko Affa (Mai sunan baban safiyya) ya girma. Yaushe za ka fara saka manyan kaya? Oya mu je.”

Fuska a daƙune da alamar takura ya fita falon. Mimi ce a zaune da litattafan Islamiyya baje a ƙasa tana assignment. Jin tafiya ya sa ta ɗago. Sauke idanuwanta ta yi kan Fu’ad lokaci ɗaya ta yamutsa fuska. Kallonta Safiyya ta yi. Gaba ɗaya expressions ɗin nan irin na Fu’ad ne. Duk ya koya mata.

“Menene wannan ka sa dady?”

Ta tambaya fuska a yatsine. Harararta Safiyya ta yi. Fu’ad ya kalli Safiyya da ke fassara ‘Bana gaya miki ba.’

“Kaya sunan su. Manyan kaya.”

Safiyya ta amsa wa Mimi.

“You look different.”

Mimi ta faɗi tana maida kanta wajen assignment ɗin da take yi. Ƙarasawa Fu’ad ya yi, bai damu da zaman da ya yi a ƙasa zai squeezing mishi kyanshi ba.

“Daban in a good or bad way?”

Ya buƙata. Ɗagowa Mimi ta yi da ɗan murmushi ta rausayar da kanta gefe alamar tana tunani.

Daƙuna mata fuska Fu’ad ya yi. Hakan ya bata dariya.

“Kana sakawa koyaushe. In a good way.”

Murmushi ya yi.

“Ko me queen take so.”

Ware idanuwa Safiyya ta yi.

“Tunda ‘yarka ta ce kayi kyau ka yarda. Ni da na faɗa ai baka ɗauka ba.”

Kallonta Mimi ta yi da smug face.

“Yafi sona ko dady?”

Tsare shi da idanuwa Safiyya ta yi. Ya ɗan ware mata idanuwa. Miƙewa ya yi daga kusa da Mimi ya taka har inda take. Idanuwanshi ya sauke cikin nata. Godiyarshi da ƙaunarta yake nuna mata. Yake son tabbatar mata. A shekaru goman nan rayuwa ta musu wani irin sauyi na ban mamaki.

Allah ya musu kyautar yara har biyu bayan Mimi dukkansu maza. Yanayin kallon da yake mata ya kashe mata jiki.

“Ina sonki sosai.”

Ya faɗi ƙasa-kasa. Daƙuna mishi fuska ta yi alamar Mimi na falon. Ɗan juyawa ya yi ya ga ba ma ta su Mimi take ba.

Ranƙwafawa ya yi. Ta yi saurin matsawa. Da sauri ta juya ta yi bedroom ɗinsu. Ya bi bayanta. Yana shiga ta sa hannuwanta jikin wuyanshi.

“Kai ko?”

Tarin wasa ya fara. A dole ta shaƙe shi. Sauke hannayenta ta yi tana dariya.

“Ka ɓata min yarinya. Duk irin abinka ta ɗauka.”

Cute face ya yi mata.

“Like daughter like dady.”

Murmushi Safiyya ta yi. Tana kai hannu tare da ja mishi hanci.

“Allah ya raya min ku.”

“Amin. Tare da ke ma.”

Ya faɗi yana janyota jikinshi. Sumba ya manna mata mai taushi a lips.

“Alhamdulillah da kyautar iyalai irin ku.”

Ta amsa da,

“Alhamdulillah da ƙaddara irin tamu.”

Lumshe idanuwanshi ya yi. Yana hugging ɗinta jikinshi.

“Ina tunanin me Nana za ta ce ne da za ta ganni da wannan kayan.”

Dariya Safiyya ta yi. Cikin kwaikwayon muryar Nana ta ce,

“Dady me mumy ta baka ka sa haka?”

Sosai yake dariya da dukkan zuciyarshi. Yana jin daɗin yadda har yau memories ɗin Nana na saka su farin ciki irin wannan.

Ta wani fannin yana jinjina wa rayuwa. Yana ƙara ganin yadda take tamkar makaranta. Kowa da yadda zai fahimci tashi.

*****

Nikuma anan nake muku sallama. Da fatan alkhairi a rayuwa gabaki daya.

ALHAMDULILLAH

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×