Skip to content
Part 22 of 48 in the Series Akan So by Lubna Sufyan

“Mama na da karamci sosai.”

Safiyya ta ce masa muryarta da wani sanyi. Wani murmushi ya yi. Yana so a yabi Momma.

“Momma ba ta da matsala Sofi. Ni na san za ta so ki da ma.”

Langaɓar da kai ta yi kawai. Tana tunanin ranar da nata iyayen za su so Fu’ad. Ita kanta a yanzu ba ta san matsayin nata son a wajen su ba ballantana ta yi tunanin za su so Fu’ad.

Hannunshi ta ji kan nata. Ya riƙo tare da dumtsewa. Ba ta san yadda ya ke gane tana buƙatar hakan ba.

Idanuwanshi na kan tuƙi ya ce mata,

“Muna cikin wannan tare. Ni da ke. Komai zai yi daidai.”

Nashi hannun ta sake dumtsewa tana jin laushin hannun da wani ɗumi da ke ratsa ko ina nata.

A hankali ya zame hannunta daga cikin nashi ya ci gaba da tuƙin da ya ke yi.

*****

Gidan take ta kallo. Bai kai na Hotoro girma ba. Daga wajen kawai za ta iya gane hakan. Amma ya fi shi kyau. Fu’ad ya ƙarasa ya je ya buɗe sannan ya dawo ya buɗe bayan motar yana fito da kayan abincin da Momma ta jibgo musu. Kwalin taliya Safiyya ta ɗauka. Fu’ad ya wani fito da idanuwa.

“Sofi ajiye da nauyi.”

Dariya ta yi ta ce mishi,

“Zan iya ɗauka ai.”

Kallonta ya ke har ta shiga da shi cikin gidan. Tsayawa ta yi tana jiran Fu’ad ya shigo ta ga inda za su kai kayan. Kitchen ya nufa ta bi bayanshi. Haka a tare suka dinga ɗiban kayan suna kaiwa. Sai da suka gama tsaf sannan ya buɗe lockers ɗin kitchen ɗin suka jera komai. Haka kayan kitchen ɗin da suka siyo da Fa’iza suka jera inda suke son su. Kallon Safiyya ya yi. Da hijabin jikinta take ta aiki. Ko zafi ba ta ji. Bai dai yi mata magana ba.

Wayarshi ya ɗauko cikin aljihu ya duba. Huɗu saura minti biyar. Ya ɗan ware idanuwanshi yana faɗin,

“Mu je mu yi Sallah Sofi. Lokaci ya yi.”

Ba ta ce komai ba suka wuce tare har bedroom ɗin. Shi ya fara shiga ya fito sannan ta shiga itama ta yo alwala. Fitowa ta yi ta same shi cikin ɗakin,

“Ba za ka je masallaci ba?”

Ta buƙata. Ya girgiza mata kai tare da fadin,

“Lokaci na tafiya. Gashi ban ma san inda zan gano masallacin ba.”

Kai ta ɗan ɗaga alamar ta fahimta. Kan kafet ɗin ɗakin ya ja musu sallar La’asar. Bayan sun idar suna zaune shiru. Can ya nisa ya ce,

“Gobe in Allah ya kai mu za mu je makaranta.”

Cikin idanuwanta ya fara ganin murmushin kafin ya bayyana a fuskarta. Wani irin squeezing ya ji zuciyarshi ta yi da rabon da ya ji shi tun farkon ganin shi da ita.

“Allah ya kaimu goben.”

“Amin Sofi.”

Shiru suka sake yi. Don kalamanta neman su ta ke ta rasa in ya zuba mata idanuwan nan nashi.

“Kin san yunwa na ke ji . Cikina kamar ban ci komai ba.”

Dariya Safiyya ta yi. Tana mamakin inda Fu’ad ke kai abinci. Hakan ya karanta a fuskarta ya sake cewa.

“Ki shirya girki da yawa Sofi. Ina cin abinci sosai sosai.”

Murmushi tayie ba za ta yi masa ƙarya ba don haka ta ce,

“Gashi ban iya abinci masu yawa ba.  Banma iya duk kalar wanda na ga ka ci ba.”

Jinjina kai ya yi tare da faɗin,

“Sai ki koya. Akwai makarantu na koyon girki. Sai in kai ki.”

Kallon shi ta ɗan yi . Yana son sauƙaƙa mata komai. Wani son shi ya cika mata zuciya.

“Na gode sosai.”

Girgiza mata kai ya yi.

“Ni da za a dafa ma ai ni ne da godiya.”

Tunawa ta yi tana son ya koya mata yadda ake tura saƙo a wayarta. Mikewa ta yi ta wuce falo yana binta da idanuwa.

Wayar ta ɗauko ta dawo ta zauna inda ta tashi.

“Ina so fa in ce ka koya min tura saƙo na manta.”

Da fara’a a fuskarshi ya ce,

“Dawo nan to.”

Yana nuna mata gefen shi. Matsawa ta yi ta zauna a inda ya nuna mata. Tana jin har ƙamshin turarukanshi cikin hancinta.

Wani numfashi ta ja ta fitar da shi. Kallonta ya yi sosai. Muryarshi na sauka ƙasa sosai ya ce,

“Ya dai?”

Kai ta girgiza masa. Wayar ya karɓa daga hannunta ya shiga nuna mata yadda za ta yi.

Sannan ya miƙa mata ya ce ta yi. Yadda take duba keypads ɗin kafin ta danna ya sa shi bushewa da dariya.

“Sofi…”

Dariya ya ke yi sosai.

“Awa nawa za ki yi kafin ki yi layi biyu?”

Ita ma dariyar ta yi. Ta miƙa masa wayar.

“Jera min ABCD ɗin su koma daidai.”

Dariya ya sake yi. Ganin fuskarta da gaske ta ke ya jera mata su koma daidai.

“Haka suke ai Sofi.”

Girgiza masa kai ta yi tana sake duba keypads ɗin wayar sannan ta kalle shi tana wani daƙuna fuska.

“Ba daidai suke ba. Duba ka gani.”

Kara matsawa ta yi sosai kusa da shi ba tare da ta kula ba ma.

“Ka ga A anan ko. To kalli inda B take fa. Na ce maka nawa ba daidai suke ba.”

Dariya ya ke.

“Sofi please. Sai cikina yayi ciwo?”

Dariya ta ɗan yi. Ita kam ba ta gane wannan malatsai ba. Karɓar wayar ya yi daga hannunta.

“Haka suke na kowanne waya sunan su qwerty…”

Jinjina kai ta yi. Ba ta dai ga dalilin da zai sa a jirkita abu ba ga yadda ya ke ba.

Hannu ta miƙa tan karɓi wayarta daga hannunshi. Ya riƙe hannunta. Tsayawa ta yi tana kallonshi.

Wayar ya karɓa ya ajiye gefe ya kamo ɗayan hannunta ya saka nashi yana ware tafin hannunta.

Dogayen yatsunta sun masa kyau sosai. Hannu ɗaya ya kama da nashi duk biyun yana kallon ƙunshin ta.

Bai taɓa sanin yana son ƙunshi ba sai da ya ganshi a hannunta.

Gaba ɗaya jikinta ya yi wani ɗumi. Idanuwanta na kan nashi hannayen. Zoben da ke jikin hannunshi na hagu ta ke kallo.

Fuskarta ya kalla kafin ya bi inda idanuwanta suke kafe.

“Haneef ya siya min…”

Maganar da ya yi ta sa Safiyya ɗago da kai ta kalle shi.

“Zoben da kike kallo. Shi ya ba ni gift da na cika shekara sha takwas.”

Kallon zoben ta sake yi kafin a hankali ta furta.

“Yana da kyau sosai.”

Zoben ya sake kallo ya sa ɗayan ɗan yatsan shi yana murza shi.

“Ban taɓa cirewa ba tunda na saka.”

Ta kula akwai ƙauna mai girman gaske tsakanin shi da Haneef da Lukman. Duk da ya faɗa mata ba su haɗa jini da Lukman ba.

Za ta iya ganin ba ya banbanta su da Haneef. Kusan waje ɗaya suke a zuciyarshi. Cikinshi ya ji ya yi ƙara alamar yunwar da ya ke ji.

Hannunta ya ja zuwa cikinshi yana daƙuna fuska. Dariya ta yi jikinta da wani nauyi na daban.

Sakin hannunta ya yi yana miƙewa.

“Tashi mu siyo abinda za mu ci. Mun huta kin gani.”

“Da ka barni ka je ka dawo.”

Tunda ta buɗe baki yake girgiza kai.

“Tashi. Ina zan barki babu mai gadi babu komai. Tashi mana.”

Miƙewa ta yi dole suka fita tare ya kulle gidan. Ba ma su yi nisa ba ya ga wani ƙaramin bakery ya tsaya suka yi siyayyarsu anan suka koma gida. Suna shiga ya ji kamar kiran sallar magrib. Saurarawa ya yi ledojin ya miƙa wa Safiyya ya fita harabar gidan da sauri.

Kiran sallah ne kuwa. Ciki ya koma ya yo alwala ya fito falo ya sameta a zaune.

“Taso ki kulle kofar. Karki bude in ba ki ji muryata ba.”

Kai ta ɗaga masa da murmushi a fuskarta. Yadda yake mata bayanin za ka rantse ‘yar shekara takwas ce ko ƙasa da haka zai bari cikin gidan. Ita ma alwala ta je ta yi. Falo ta dawo ta yi sallar anan don kar Fu’ad ya dawo ya yi ta ƙwanƙwasawa ba ta ji ba.

Nan ta yi zamanta tana danne danne a waya. Ta shiga nan ta fito. Gani ta yi ya daɗe sosai bai dawo ba. Ganin ƙarfe takwas har da kwata ya sa ta tashi ta yi sallar isha’i, tana idarwa ta ji ƙwanƙwasa ƙofa.

Da sauri ta je ta buɗe. Fuskarshi a haɗe ya ce,

“Haka na ce fa in ba ki ji muryata ba karki buɗe.”

Dariya ta ɗan yi.

“Ai na san babu wanda zai ƙwanƙwasa sai kai shi ya sa.”

Sake ɓata fuska ya yi tare da faɗin,

“Still. Ki tambaya waye kafin ki buɗe.”

Ta amsa da,

“In shaa Allah. Ka zo ka ci abincin tun ɗazu ka ke kiran yunwa.”

Ƙarasawa ya yi. Ta ɗauko ledojin ta ajiye su a gabanshi. Buɗe musu ya yi. Shawarma ya fara ci.

“Kici Sofi.”

Kai ta girgiza masa tana ɗaukar burger. Abinda za ta iya ci tun daga idanuwanta za ta iya gane shi ba ma sai ta wahalar da harshenta ba.

Ɗibowa ya yi da cokali.

“Sai kin ɗanɗana fa. Ina kallon ki shekaranjiya ma…”

Janye fuska ta yi tana girgiza masa kai.

“Ba zan iya ci bane.”

“In baki ɗanɗana ba ya za a yi ki gane ko da daɗi ko babu?”

Hannunshi ta kama ta karɓi cokalin. Da ƙyar ta haɗiye tana wani yamutsa fuska da ya bashi dariya. Sosai ya ci komai ya sha exotic. Ya yi hamdala ya sake komawa kan kujera.

Da ƙyar ta cinye burger ɗin hannunta. Ruwa ta ɗauka ta buɗe ta sha. Fita Fu’ad ya yi ya yo addu’a ya sa ma gate ɗin mukulli.

Sannan ya dawo cikin gidan ma ya yi addu’a a ko’ina tana kallonshi sannan ya sa mukulli ya kulle ya zaro shi ya ƙaraso ya ajiye kan kujera.

“Taso mu je mu yi wanka mu kwanta. Na gaji ko banyi bacci ba so na ke in ji ni a kwance.”

Binshi ta yi har bedroom ɗin. Sai da ya buɗe jakarshi ya ɗauki wata T-shirt marar nauyi da gajeren wando sannan ya shiga wanka.

Bai wani daɗe ba ya fito sanye da kayan da ya ɗauka. Kallo ɗaya Safiyya ta yi masa ba ta ƙara na biyu ba. Wata kunya ta lulluɓeta ga wani bugawa da zuciyarta ke mata. Wucewa ta yi ta shiga wanka ita ma.  Ta fito yana zaune kan gado ya kalleta.

“Rigar nan ta yi girma. Ya za ki iya bacci a ciki. Ki ɗauko wata marar nauyi.”

Ita kanta tana jinjina kwanciya cikin rigar. Jakarta ta buɗe ta ɗauko atamfarta da ta zo da ita.

Fu’ad ya lumshe idanuwanshi ya buɗe su. Tana buƙatar abubuwa da yawa. Saukowa ya yi. Ya budee jakarshi ya ɗauko mata wata riga loose ya miƙa mata. Karɓa ta yi ta koma banɗakin ta ɗaura zaninta.

Ta saka rigar da ya ba ta. Tsawon ne kawai ya zo mata wajen cinya. Amman rigar ta ɗan kamata.

Kunya sosai ta ke ji tun kafin ma ta fito daga banɗakin. Daɗi ta ji da ta fito hankalinshi na kan wayarshi.

Da sauri ta samu waje kan gadon ta ɗayan gefen ta hau. Shikam Fu’ad text ya yi wa Fa’iza na list ɗin abubuwan da za ta ƙara a cikin wanda Safiyya ke buƙata.

Ƙafafuwanshi ya hawo da su kan gadon. Wani shagwaɓe fuska ya yi kamar zai yi kuka. Ɗazun da suka siya zannuwan gado shaf ya manta da blanket.

Safiyya ya kalla fuskarshi a shagwaɓe.

“Babu abin lulluɓa. Ko mu je gida mu ɗauko?”

Kallonshi ta yi sosai.

“Dare ya yi fa.”

Sake shagwaɓe fuska ya yi tare da faɗin,

“Bana iya bacci in ban lulluɓe  ƙafafuwana ba.”

Sauke numfashi Safiyya ta yi. Mutane kala kala.

“A kware zanin gadon mana. Saikae lulluɓe da shi.”

Kai ya girgiza.

“In ba shimfiɗa ma haka ba zan iya bacci akan gadon ba.”

Lumshe idanuwa Safiyya ta yi ta buɗe su kan fuskarshi da ya bi ya shagwaɓe cike da rikici.

Saukowa ta yi daga kan gadon.

“Bari in ɗauko zanin gadon wani ɗakin in akwai.”

Kallo ya bi ta da shi har ta fice. Yana tunanin gaskiya haɗa gida ya fi komai wahala.

Dawowa ta yi da zanin gado a hannunta ta miƙa masa. Ya karɓa ya na yatsine fuska.

“Wannan fa na shimfiɗa ne Sofi. Abin lulluɓa na ke so ba shi ba.”

Kallon shi ta ke. Rigimarshi na da yawa sosai. Yanzu take ganinta.

“Ka yi haƙuri da wannan ɗin iya yau kawai. Kawo ka gani in linka maka ya ƙara kauri.”

Miƙa mata ya yi. Ta karɓa ta gyara zanin gadon ta linka shi gida biyu. In ba rigima ba ma da kaurinshi sosai. Miƙa masa ta yi. Maimakon ya karɓa sai ya ja jiki ya kwanta yana faɗin,

“Ke ki ka ce zai yi. Sai ki rufa min ai.”

Dariya ma ya ba ta. Lilliɓa mishi ta yi ta ja masa har zuwa ciki sannan ta zagaya ta kwanta gefe.

Addu’a ta yi ta tofa. Tana gyara kwanciya. Juyowa ya yi fuskarshi na kallon na ta. Duk da da ‘yar tazara a tsakaninsu.

“Shi ne ni ba ki yi min addu’ar ba Sofi.”

Dariya ta sake yi.

“Na ga ka yi kaima ai.”

Wani shagwaɓe fuska ya yi.

“Ni dai ki min. Kuma kin matsa can ƙarshen gado sai kin faɗi. Ki matso kamar zan cije ki.”

Shiru ta yi masa. Inda ta ke ɗin ma duk jikinta a sanyaye ya ke da kusancin shi balle ta matsa.

Kaɗan ta ɗan ƙara jan jiki. Addu’a ta yi ta ɗan tofa mishi iskar.

Son jinta ya ke a kusa da shi kamar ya yi me. Ganin ba ta da niyyar matsowa ya sashi matsawa sosai gab da ita yana share yadda ta wani rintse idanuwa.

Peck mai taushi ya manna mata a goshi tare da faɗin,

“Sai da safe.”

Ba ta buɗe idanuwanta ba. Zuciyarta wani irin bugawa ta ke. Ta na ji ya kamo hannunta ya riƙe cikin nashi. A haka bacci ya ɗauke su dukansu.

*****

Ta na idar da sallar Asuba ta shiga banɗaki ta yi wanka. Tunawa ta yi Fu’ad ya ce karta ƙara wanki.

Don haka ta cire kayan jikinta ta linke su ta ɗauko wata doguwar riga light purple ta saka. Ta koma kan gado ta yi zamanta.

Ba ta damu da jimawar Fu’ad ba don ya gaya mata zai motsa jiki ko da ta ga ya daɗe bai dawo ba.

Kiranshi ta ji a wayarta. Ba ta ɗauka ba don ya ce da ya zo zai kirata. Tashi ta yi ta fita ta buɗe masa gidan.

Duk ya haɗa zufa. Yana wani maida numfashi yake kallonta ta masa kyau. Kanta ɗaure da ɗankwalin rigar.

Yana son ganin fuskartan nan fayau haka.

“Sannu.”

Ta ce masa. Kai kawai ya iya ɗaga mata ya wuce ciki. Kan kujera ya zauna yana ƙoƙarin daidaita numfashin shi saboda gudun da ya yi. Hannunshi ya kai ya bayan kanshi ya taɓa. Runtse idanuwanshi ya yi yana cire hannunshi. Ciwon na mishi zafi har yanzu. Sai lokacin ma ya tuna da wasu su Ado da abinda ya faru. Murmushi kawai ya yi, don ya gama rama abinda suka yi mishi tunda ga Safiyyar nan zaune a gabanshi.

Sai da bugun zuciyarshi ya koma dai dai tukunna ya miƙe ya tafi bedroom. Wanka ya yi ya sako kaya ya fito. Kallonshi Safiyya ta ke. Wandon jikinshi yaga ce a jiki kusan daga gwiwarshi har ƙwauri.

Blue ne mai haske sai riga ja a jikinshi. Ya yi kyau matuƙa, waje ya samu ya zauna.

Tunda ya tashi cikinshi ya ke ji wayam ga gudun da ya yi ya ƙara ƙona calories. Wata yunwa ke cinshi. So ya ke bakwai da rabi ta yi su fita gaba ɗaya.

Bai ma san makarantar da ya kamata ya kai ta ba. Da ya yi tunanin ya kai ta FAAN inda su Hussaina suke. Sai kuma ya fasa.

Tunani ya zo masa. Yakai ta Crescent kawai inda Fa’iza ta gama. Ya yarda da makarantar tana da kyau sosai.

“Sofi ɗauko hijabinki mu tafi. Sai mu ci wani abu a hanya ko?”

Tashi tayi ta nufi ɗaki. Cikinta a wani ƙulle. Tunanin komawa makaranta na mata daɗi ta wani fannin kuma yana ba ta tsoro.

Ba ta san ya za ta tsinci kanta a makaranta ba. Gashi ko turanci ba ta ji. Sai dai ita ba mai girman kai ba ce ta wannan fannin.

Tunda ta ɗauko hijabinta take wa kanta alƙawarin za ta tsaya sosai ta maida hankali kan karatunta.

*****

A hanya ya siya musu takeaway na dankalin turawa da ƙwai da fresh milk. Ya samu waje ya yi parking suka ci. Sannan suka wuce.

Tun daga gate ɗin makarantar ta ji ta karaya. Duk ƙwarin gwiwar da ta fito da shi ya ƙara wargajewa da suka shiga cikin makarantar.

Ga wani irin girma ta na da shi. Kayan makarantar kansu abin kallo ne. Sai ɗalibai ko ina suna kai kawo.

Da ka gansu ka san ‘ya’ yan masu hannu da shuni ne. Tsaf da su. Ba ta san lokacin da ta kama hannun Fu’ad ta dumtse gam cikin na ta ba. Ya san a tsorace ta ke. Hannunta ya riƙe sosai cikin na shi suka wuce office ɗin principal ɗin.

Sai da suka samu wajen zama sannan ya saki hannun Safiyya ya maida hankalinshi kan principal ɗin. Safiyya na zaune tana ta zare idanuwa. Kanta a ƙasa tana jin yadda Fu’ad ɗin suke magana cikin harshen turanci.

Bayanin komai ya yi masa. Da matakin da ta tsaya a karatu da kuma cewar ba ta jin turanci ga shi ba ta da takardu ko ɗaya sai dai ya siya mata na nan.

Shawara principal ɗin ta ba shi cewar Safiyya ta fara daga JSS1 Fu’ad ya ce bai san wannan ba. Ba ya so ko kaɗan matarshi ta ji kamar an rainata.

Kuɗi shi zai biya. Daga SS1 yake so ta fara. A samu malamar da zai biya ta dinga zuwa gida tana koya mata extra lesson komai da ake bukata don a taimaka mata. Amman ba za a nuna an raina karatunta ba.

Shawara ce ta ba Fu’ad ya ƙi ji. Makaranta ce ta kuɗi. Kuma su ne suke magana. Nan take akai masa lissafin komai daga kan kuɗin makaranta zuwa na uniform zuwa litattafai. Nan ya biya komai. Da sun ce sai ya je banki. Ya bada dubu ɗaya ya ce su aiki wani ya kai.

Uniform aka duba kala biyu aka ba Safiyya. Ta sa wata malama ta rakata inda za ta cire na jikinta ta gwada waɗannan.

Kallo ɗaya za ka yemata ka san a tsorace ta ke. Sai da ta kalli idanuwan Fu’ad ya ɗan ɗaga mata kai da cewar babu matsala sannan tabie matar.

Kamar an aunata haka uniform ɗin ya zauna mata. Ta sako hijabin ta fito. Da kayan da ta cire a leda malamar ta sako mata.

Kallonta ya ke da murmushi a fuskarshi ta yi kyau sosai. Ya ce a ƙara mata kala biyu uniform ɗin. Suka ce ya bar Safiyya sai ƙarfe huɗu ya dawo ya ɗauke ta.

In ya so za su yi magana kan wadda zatae dinga zuwa gida tana koya mata. A gaban su ya kama hannun Safiyya ya ja ta gefe.

Kallonta ya yi sosai.

“Na san za ki iya sofi. Kar ki ji tsoron komai ki na ji na ko? Ga dubu ɗaya ki ci wani abu. Ina wayarki?”

Miƙa masa ta yi. Ya karɓa ya kashe ya sa a aljihu ya ba ta dubun.

“Anjima zan zo in ɗauke ki. Ki yi karatu sosai kin ji?”

Kai kawai ta ɗaga mishi tanajin kamar kar ya tafi ya barta. Hannu ya sa ya ɗan yi cupping fuskarta ya ce mata.

“I love you.”

Murmushi ta yi ta sadda kanta ƙasa a kunyace kafin ta wuce ta koma inda malamar ke jiranta.

Ƙara kallonta ya yi sannan ya fice daga office ɗin.

Yana mota ya kira Lukman ya ce masa yana makaranta su haɗu a can. BUK ya wuce sai da ma ya ɗan jira Lukman ɗin ya fito lecture ƙarfe goma.

Mota ya buɗe ya shiga. Kallon Fu’ad ɗin yake ya masa wani haske.

“Ya Na ga ka yi wani fresh?”

Lukman ya tambaya. Dariya Fu’ad ya yi.

“Ba na son iskanci lukman. Sofi na kai makaranta shi ne na biyo ta nan.”

Wani murmushi ne a fuskar Lukman.

“Did you?”

Naushi Fu’ad ya kai masa a kafaɗa fuskarshi na yin wani ja. Girgiza kai Fu’ad ya ke yi.

“Inalillahi Lukman. Kai bakinka ba shi da tsarki. Idan na yi ne ma faɗa maka zan…”

Dariya sosai Lukman ya yi ganin yadda fuskar Fu’ad ɗin ke ƙara yin ja.

“Ashe akwai abinda ka ke jin kunya?”

Dariya shi ma ya ke yi.

“You are gross Lukman.”

Tashin motar ya yi yana juyata. Lukman da ke dariya ya ce,

“Kai ina da lectures fa ƙarfe sha ɗayan nan.”

Ai kamar ma Fu’ad bai ji shi ba ya ci gaba da jan motar.

“Da gaske nake maka.”

“You are skipping tunda ba test bane. Yawo zamu.”

Dariya kawai Lukman ya yi. Fu’ad sarkin rikici.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Akan So 21Akan So 23 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×