Skip to content

Akan So | Babi Na Ashirin Da Daya

0
(0)

<< Previous

Ya riga safiyya tashi. Sai da ya yi wanka ya yi alwala ya fita mota ya ɗauko kayan da zai sake.

Ba ya son ya ajiye su cikin gidan sam. Don in son samun shi ne kar su wuce yau ba su koma gidansu ba. Komawa bedroom ɗin ya yi. Yadda Safiyya ke baccin ta hankali kwance yasa ya ji kamar kar ya tashe ta. Gefenta ya zauna ya zuba mata idanuwa. Ba ya son hannunshi ya kai jikinta saboda alwalar da ya ke da ita.

Gefen gadon ya ɗan bubbuga. Ta buɗe idanuwanta cike da bacci ta sauke su akanshi.

 “Sofi Sallah.”

Ya faɗi da murmushi yana miƙewa daga kan gadon. Sai da ta gama addu’ar tashi daga bacci sannan ta miƙe zaune.

Tana kallon Fu’ad har ya fice daga ɗakin. Dafe kai ta ɗan yi . Duk da yau zuciyarta a shirye take da tashi tare da Fu’ad, hakan bai hanata jin wani iri ba.

Ga kewar su Inna. Miƙewa ta yi ta shiga banɗaki. Sai da ta fara yin brush da Fu’ad ya ajiye mata sannan ta yi alwala.

Sallah ta gabatar. Addu’a sosai ta yi bayan ta idar na Allah ya ba wa su Inna zuciyar yafe mata ya kuma basu zama mai inganci da Fu’ad.

Don shi kaɗai ya san me ya ke shimfiɗe kan titin ƙaddarar dayya ɗora su. Tana nan zaune kan kafet Fu’ad ya dawo daga masallaci.

“Ina kwana.”

Ta gaishe da shi. Cikin fuska ya kalleta.

“Kin tashi lafiya?”

“Alhamdulillah. Kai fa?”

Dariya ya ɗan yi.

“Kina kusa da ni, komai dai dai Sofi.”

Kunya ta ji ta sadda kanta ƙasa. Fu’ad ya ɗora da fadin, “Yau ba wanka da ruwan sanyi ko?”

Dariya ta yi.

“Yanzu ma zan yi wankan ai.”

Kallonta ya yi yana wani ware idanuwa. ‘Yana da kyau’ zuciyarta ta faɗi. Sake daƙuna fuska ya yi alamar bai gane abinda ke sa ta murmushi ba.

Hakan da ta karanta ya sa ta miƙewa. Kafin ta yi wani abu maganar zuci ta kuɓce mata.

“Kana da kyau.”

Hannu ta sa ta rufe baki. Dariya ta bashi sosai. Da gudu ta nufi banɗaki ta rufo yana fadin, “Sofi dawo nan….za ki fito ki maimaita min in sake ji.”

Dariyarta ya jiyo daga banɗakin. Fita ya yi daga ɗakin saboda ba ya son abinda tunanin tana wanka yake mishi. Yau akwai abubuwa da yawa da yake son yi. Ga ball yana son zuwa amma ya san bashi da wani lokaci. Dole zai haƙura zuwa gobe in komai ya daidaita.

Yana nan kwance bacci ya ɗauke shi.

*****

Wata doguwar rigar ta sake mayarwa. So take ta wanke kayayyakinta amma ta rasa sabulun wanki. Wankan ma da wani abune cikin roba da ba ta san ko meye ba. Sai ƙamshi ga kumfa yana da shi. Fita falo ta yi ta duba Fu’ad ba ta ganshi ba. Ɗaya daga cikin bedroom ɗin ta tura. Don tana buƙatar sabulun wanki. Ganinshi ta yi kwance yana bacci. Har za ta fice ta ja masa ƙofar idanuwanta suka hango kayan kan wani tebur.

Ƙarasawa ta yi cikin ɗakin.

Kayanshi ne duk da ya cire daga zuwansu zuwa yau. Ɗauko su ta yi ta ja masa ƙofar a hankali.

Banɗakin bedroom ɗin ta koma. Dabara ta faɗo mata. Tunda dai babu bokiti. Ruwa ta tara a bathtub ɗin ta zuba shower gel ɗin ciki ta kaɗa ya yi kumfa.

Kayan Fu’ad ta soma wankewa. Duk rigunan ma fararene. Har da singlet ɗinshi da boxers. Sai da ta wankesu ta ɗauraye. Sannan ta wanke jeans ɗin da three quarter daban ta ɗauraye su. Nata ta wanke da ta zo da su da hijabinta sannan ta wanke dogayen rigunan da ta yi amfani da su.

Ƙarfen da ta gani cikin banɗakin ta shiga yarfe kayan tana shanyawa akai.

*****

Ya jima da tashi. Wata kasala dai ya ke ji ya sa shi ƙin sakkowa daga kan gadon. Wayarshi ya lalubo ya duba agogo. Takwas da rabi. Miƙewa ya yi Safiyya na manne a zuciyarshi. Bai san sanda bacci ya ɗauke shi ba. Daga ɗan hutawa kafin gari ya ɗan waye ya fita ya siyo musu abin da za su yi breakfast dashi.

A hankali kamar wanda ba ya so ya sakko daga kan gadon. Haka ya tako zuwa falo bai ganta ba.

Bedroom ɗin da ya san tana can ya nufa. Da sallama ya tura ƙofar ya shiga. Tana cikin banɗaki tsaye tana yarfe hijabinta. Da mamaki yace,

“Sofi? Me kike yi haka?”

Da sauri ta juyo. Ta lumshe idanuwanta ta buɗe su akanshi. Tsoro ya ɗan ba ta saboda ba ta ji shigowarshi ba.

A sanyaye ta ce,

“Allah ya sa dai ban yi ɓarna ba. Babu sabulun wanki da wannan ruwan na yi.”

Girgiza kai Fu’ad ya yi yana sauke numfashi sannan yace,

“Ɓarna ba ma ƙarama ba.”

Rau rau ta yi da idanuwa. Shi ya sa da kamar ta bari ya tashi daga bacci. Don dai tana zaune ba wani aikin yi ne kawai. Amma ta san wannan ruwan da tsada da ganinshi. Murya na rawa tace,

“Ka yi haƙuri don Allah. Wallahi babu sabulu shi ya sa. Bansan da tsada ba amma…”

Katse ta yai da faɗin,

“Damn the shower gel. Ɓarnar da kika min shi ne kin sa hannunki a ruwa. Kina so ki yi mura ne Sofi?  Duka yaushe zazzaɓi ya sake ki? Kin zo kina wani wanki.”

Ajiyar zuciya ta sauke. Ta ɗauka ɓarna ta yi.

“Ba abinda zai min. Wankin ma ba yawa.”

Ƙarasawa ya yi sosai cikin banɗakin. Zaro idanuwa ya yi ganin har da kayanshi.

“Haba mana Sofi. Har da kayana fa. Za a zo a wanke ai.”

Shiru ta yi don ba ta san me za ta ce masa ba. Ita a wajenta wannan ba wani aiki bane. Ko dauɗa kayan basu dashi. Yadda Fu’ad ɗin ya ke yi sai ka ce ta wanke kaya kala talatin ba ƙwarori ba. Hijabinta ta ƙarasa shanyawa.

Ƙarasawa ya yo gefen gado ya zauna yana wani ɓata fuska. Bai ji daɗin ganin ta yi wanki ba sam.

Kawai ji ya yi ba ya son ta yi ko wane aiki. Ya fi son komai a yi mata. Ta zauna ta huta kar ta wahala.

Fitowa ta yi daga banɗakin. Muryarshi can ƙasa yace,

“Ba na son ki ƙara yin wanki Sofi. Ba na so.”

A sanyaye ta ce,

“Na daina. Ka yi haƙuri.”

Kai ya ɗaga mata kawai ya miƙe yana faɗin,

“Bari in siyo mana abinda za mu ci.”

“Allah ya tsare hanya.”

Ta ce. Ya amsa da amin yana ficewa. Gyara zama ta yi ta sauke numfashi. Kawai yadda yanayinshi ya yi ba ta ji daɗi ba.

Duk ƙoƙarin da yake akanta. Ƙarshen abinda za ta yi shi ne ta ɓata mishi rai.

*****

Take away ne ya siyo musu na ƙwai da dankalin turawa sai yoghurt. A bedroom suka yi zamansu suka ci.

Sannan ya ce mata zai fita ya ƙarasa siyayyar komai. Sai da suka je falo ya kunna mata kallo sannan ya yi pecking ɗinta a goshi ya fice. Ganin maigadi ya buɗe masa gate ya tuna mishi da cewar yana bukatar maigadi shi ma. Da kuma ‘yar aiki.

Ƙasa ya yi da glass ɗin motar ya yi masa nuni da hannu da alamar ya zo. Da sauri ya ƙaraso.

Cike da ladabi duk da a haife ya haifi Fu’ad ɗin yake masa magana.

“Bawani abu bane. Ina son maigadi ne a gidana. Da kuma ‘yar aiki haka. Zuwa gobe ko jibi ma in an samu sai ka min magana.”

Da fara’a maigadin yace,

“In shaa Allah za a samo.”

Fu’ad bai amsa shi ba ya ja glass ɗin motarshi sama ya fice.  Yana hanya ne ya kira Fa’iza.

Ringing ɗaya ta ɗaga da faɗin,

“Bro. Ina kwana. Ko da ya ke ma fushi na ke yi. Hussaina kawai ka ke nema.”

Murmushi ya yi.

“Haba Sisto. Kina raina. Thank you da ba ki yi fushi ba.”

Yanajin dariyarta kafin ta ce,

“Oh no. Ni ban yi fushi ba. Abinda ka yi super cool bro. Allah kamar a Mumbai. So romantic irin…”

Katse ta ya yiyana dariya tare da faɗin,

“Gidanku Fa’iza…”

Dariya ta ke yi sosai. Muryarshi ya daidaita sannan ya ce,

“In Momma za ta barki. Ki shirya yanzun please. Flash me, za ki rakani yin abu ne.”

Ba ta ko tsaya jiranshi ta ji meye za ta taya shi ɗin ba tace,

“Be right back.”

Ta katse wayar. Ko minti biyar ba a yi ba a tsakani ta mishi text da,

“Done bro. Call me da ka zo kawai.”

*****

Kofar gida ya tsaya da motar, duk yanda yake so ya shiga su gaisa da Momma kuwa. Nan ya kira Fa’iza ta fito. Buɗe motar Fa’iza ta yi ta shiga tare da faɗin,

“Morning bro.”

Da ‘yar fara’a a fuskarshi ya amsa da,

“Fa’iza. Ya Momma?”

Kallonshi ta yitana rufe murfin motar sannan ta ce,

“Tana nan lafiya. Me ya sa ba za ka shiga ku gaisa ba?”

Girgiza kai ya yi yana tayar da motar.

“Um um fa. Ba yau ba.”

“Amma…”

Ɗaga mata hannu ya yi da ya sa ta yin shiru. Ya ja motar kawai suka nufi gidan da ya siya.

Dole shi ya sauka ya je ya sa key ya buɗe gate ɗin sannan ya koma ya shigo da motar. Suka fito shi da Fa’iza.Ya buɗe musu suka shiga cikin gidan sannan ya kalleta yace,

“Kinga gidana Fa’iza. Meye babu? Me ya rage in sa. Tun jiya muke tunani da Lukman mun rasa.”

Dariya Fa’iza ta yi. Tana ƙare wa gidan kallo. Ba wani babba bane ba amma ya yi kyau. Furnitures ɗin sun mata kyau sosai.

“Fa’iza ba dariya ba. Ki faɗa min.”

Dariyar ya ƙara ba ta kafin ta ce,

“Really bro? Yanzu ku ba ku ga babu labulaye bane ko yaya?”

Ware idanuwa ya yi kafin ya yi ‘yar dariya yace,

“Yeah. Kai wallahi sam fa. Munata tunani. Haba shi ya sa komai yake min wani iri.”

Tare suka zagaya da Fa’iza tana rubuta duk abinda ya ke buƙata a gidan a wayarta. Musamman kayan amfani na kitchen.

Sai da suka biya Banki ya ciri kuɗi tukunna suka wuce kasuwa. Shi kanshi mamakin kuɗin da ya kashe ya yi. Faiza ma ce mishi ta yi don furnitures ɗin ma na ƙarfe ne. Da na katako ne sun fi tsada sosai.

Duk wani abu da suke buƙata suka siyo. Har bayan mota shaƙe ya ke da kaya. Lokacin da suka dawo gidan suka zauna suna hutawa.

Wayarshi ya ɗauko ya kira Safiyya da ringing ɗaya ta ɗauka da sallama ya amsa yana ɗorawa da,

“Na barki ke kaɗai ko?”

“Ba komai fa. Ina ta kallo ne.”

Ta amsa. Zai rantse ya ji murmushin kunyar nan da ta ke cikin muryarta.

“Yanzu zan taho in shaa Allah. Ki haɗa kayanki na nan waje ɗaya. Da na zo za mu taho.”

Ta amsa shi da,

“Bari in tashi to. Allah ya dawo da kai lafiya.”

Ya amsa da amin yana sauke wayar. Fa’iza ke kallonshi tana wani murmushi. Dariya ya yi tare da da faɗin,

“Go away…”

Dariya ta kama yi ta ce,

“So cute. Mu je tare please ka ga ba mu gaisa ba.”

Kai ya ɗaga mata. Tare suka miƙe suka fita ya kulle gidan. A mota ne take ce masa,

“Bro kayan abinci kaɗai ya rage maka.”

Daƙuna fuska ya ɗan yi tare da faɗin,

“Zan siyo Fa’iza. Ita ma ban san meye na mata take buƙata ba. May be in ba ki kuɗi sai ku je tare.

Na siyo mata dogayen riguna dai. Ba ta faɗa min me take buƙata ba kuma.”

Jinjina kai Fa’iza ta yi alamar yarda da abinda Fu’ad ɗin ya faɗi.

*****

Kayan da ta wanke ta ɗauko. Nata da na Fu’ad ɗin ta linke su tsaf. Ta saka cikin ledojin da suka yo siyayya. Sai kayan wankansu duka a wata leda.Ta koma ɗayan ɗakin ta ɗauko jakar Fu’ad ta haɗa masa kayanshi a ciki. Ta tattara waje ɗaya. Ta koma ta zauna tana jiran dawowarshi. Har mamaki take wai kwana biyu ne kacal ya wuce rabon da ta saka Inna a idanuwanta. Wani nauyi ta ji ƙirjinta ya yi da tunaninsu.

Da ƙyar ta samu ta yakice tunanin gefe saboda ba ta son Fu’ad ya dawo ya ganta cikin damuwa.

Sallamar shi ta ji. Ta amsa tana ɗorawa da.

“Sannu da zuwa…”

Ƙarasawa ya yi falon, sai lokacin ta kula da Fa’iza da ta shigo da sallama ita ma. A sanyaye Safiyya ta amsa tare da ce wa Fa’iza,

“Ina wuni…”

Ɗan buɗe idanuwa Fa’iza ta yi tana kallon Safiyya. Tace,

“Anti ai ni zan gaishe da ke. Ina wuni. Ya gida?”

A kunyace Safiyya ta amsa da,

“Lafiya ƙalau.”

Wani ɗan shiru ya biyo baya. Zama Fa’iza ta yi kan kujerar da ke gefe. Ta ƙasan ido take kallon Safiyya. Ta kasa ganin ta inda ta dace da Fu’ad, don banda idanuwanta ba ta ga abu me kyau a jikinta ba. Hancinta dai ba wani dogo ba. Don Fa’iza ma gani ta yi doguwar rigar da ke jikinta daban. Safiyyar ma daban. Ga fuskarta wani tas.Safiyya kam duk jinta ta ke jin wani iri. Haka kawai ba ta son kallon da ta ke jin Fa’iza na mata. Sai ta ke jin ta duk ta bi ta tsargu.

Fu’ad da ke zaune jikin kujera yana ɗan hutawa saboda ranar da suka sha da Fa’iza ya ɗago kai ya sauke kan Fa’iza.

Lokaci ɗaya ranshi ya ɓaci. Ganin kallon rashin amincewa da Safiyya da ke kan fuskarta. Idanuwa suka haɗa ya yi narrowing mata nashi.

Ware nata ta yi tana son gaya masa yadda Safiyya ba ta yi mata ba sam sam. Ba ya son yin wata magana a gaban Safiyya don haka ya miƙe tsaye yace,

“Ku tashi mu tafi Fa’iza. Kin san fa akwai sauran aiki.”

Miƙewa Fa’iza ta yi da faɗin,

“Gida za ni bro. Kun ƙarasa aikinku ai na muku ƙoƙari ma.”.

Safiyya a sanyaye ta miƙe ta ɗauki hijabinta da ke gefe ta saka. Fa’iza tabi ƙoƙaƙƙen hijabin da kallo kawai. Rayuwa kenan. Da ta yi duba da yadda Fu’ad ko abincin da Atika ta girka ba ya ci sai abin duk ya sake ɗaure mata kai.

Nesa ba kusa ba Atika da ya ke wulaƙantawa ta fi Safiyya komai. Har kyau ta fita. Gashi yanzu yadda suka ja ta a jiki wayewa ta fara shigarta.

Fa’iza ta fara yin gaba tana kallon hararar da Fu’ad ya bi ta da ita. Ta daƙuna fuska tana son gaya mishi ai gaskiya ta faɗi ba ta ga inda suka dace da Safiyya ba.

Kayayyakinsu ya taya ta ɗauka suka nufi bakin ƙofa. Takalman da ta saka ya bi da kallo. Silifas ne duk sun ƙoƙe. Tana buƙatar takalmi zai faɗa wa Fa’iza.

Motar ya buɗe ya sassaka kayansu ciki. Ya zagaya ya buɗe gaba ya ce wa Safiyya ta shiga. Babu musu ta shiga ya maida ƙofar ya kulle ya ƙarasa wajen Fa’iza dake tsaye.

Idanuwanshi cike da masifa ya ce mata,

“What is with’ dah’ look da kike mata? Ba na so Fa’iza.”

Sauke numfashi Fa’iza ta yi.

“Ni na isa in ja ne da abinda Allah ya ƙaddara? Don ba ta yi min ba bro ba ya nufin ina riƙe da wani abu kan auren ku.”

Buɗe idanuwa ya yi. A ƙufule yace,

“Rashin kunya za ki min Fa’iza?”

Kai ta grigiza masa.

“Ni na isa bro. Yi haƙuri. Bari in wuce gida zan hau Napep.”

Dafe kai ya ɗan yi sannan yace,

“Muje in aje ki sai mu wuce.”

Ta buɗe baki za ta yi magana yace,

“Ba na son wata gardama. Ranki zai ɓaci.”

Wucewa ta yi ta buɗe bayan motar ta shiga. Shi ma ya zagaya ya shiga. Da ya ƙarasa gate sai da suka sake magana da maigadi sannan ya wuce.

Suna hanya ya kalli Safiyya da ta yi shiru cikin kujera ta haɗe hannayenta tana wasa dasu.

“Yunwa ko?”

A kunyace ta ɗan ɗaga mishi kai. Don tun dankalin safe sai ruwa da shi ma robar na jiya ta je banɗaki ta buɗe fanfo ta tarba ta sha.

Ya lumshe idanuwanshi ya buɗe su kan titin da ke gabanshi. Yace mata,

“Bari in sauke Fa’iza tukunna sai mu biya mu siya abin da za mu ci.”

Kai kawai ta ɗaga masa. Fa’iza dake zaune a baya tana jinsu. Text ta yi wa Momma ta faɗa mata duk abinda suka yi da Fu’ad ɗin.

Reply Momma ta yi mata. Sannan ta ce wa Fu’ad.

“Bro Momma ta ce ku shiga.”

Sitiyarin motar ya ɗan doka tare da faɗin,

“What dah’ fuck Fa’iza. Me kika yi? Ni bana son wani faɗa yanzu fa.”

Fa’iza ta amsa shi da faɗin,

“Abbah fa ba ya nan. Yau da sassafe ya tafi Abuja.”

Bai sake cewa komai ba har suka ƙarasa gidan. Shiga ya yi da motar ciki suka yi parking.

Da kanshi ya zagayo ya buɗe wa Safiyya. Fa’iza kam har ta wuce ciki abinta. Kallonshi Safiyya ta yi a tsorace. Tsayawa ya yi ya sha gabanta. Cikin idanuwa ya kalleta.

“Ki yarda da ni. Babu abinda zai faru kina ji na ko?”

Kai ta ɗaga mishi. Ya ce,

“Good…”

Sannan ya wuce gaba tana binshi a baya har cikin gidan. Tare suka yi sallama.Hussaina da ke zaune falon ta tashi da gudu ta ƙarasa inda yake ta riƙo hannunshi fuskar nan cike da fara’a.

“Ina ta missing ɗinka . Yanzun fa nake ce ma Momma ni kam zanje inda ka koma tunda ka ƙi zuwa”

Dariya ya yi sosai.

“Ni ma na yi missing ɗinki ai. Thank you for dah’ text lil sis.”

Ta amsa da,

“You are welcome…”

Tana sakin hannunshi ta ƙarasa wajen Safiyya ta riƙo nata hannun.

“Anti. Sannu da zuwa. Amma kwana za ku yi ko?”

Fu’ad Safiyya ta kalla. Ya ɗaga mata kai da ke nuna cewar kar ta ji komai za ta iya magana da Hussaina ba wata damuwa.

Da fara’a a fuskarta ta ce,

“Umm…”

Kaman tana tunani. Hussaina ta shagwaɓe fuska.

“Bro ba zai bari ba ko? Ni na sani.”

Cikin falon ya ƙarasa inda Momma ke zaune. Takalman ƙafarshi ya cire ya ajiye gefe sannan yaje gab da ita.

Tsugunnawa ya yi wajen ƙafafuwanta. Ya riƙe kunnuwanshi kamar wani ɗan ƙaramin yaro.

“Momma na yi laifi Babba. Don Allah a yafe min …”

Ajiyar zuciya ta sauke. Ta kalli Fu’ad. Allah sarki tsakanin ɗa da mahaifiya sai Allah.

Tun a shekaranjiya yana ranta. Ko abincin kirki ba ta sakawa cikinta ba tunanin halin da ɗan nata yake ciki ta ke yi.

Sai da Haneef ya je ya dawo ne ma jiya ya faɗa mata yana nan lafiya tukunna ta ɗan ji hankalinta ya kwanta.

Din shi kanshi Fu’ad ɗin har yanzu buƙatar kulawa yake ballantana a ce ya kula da kanshi ya kuma kula da Safiyya.

Za ta yi magana Safiyya suka ƙaraso da Hussaina. Har ƙasa Safiyya ta durƙusa a gefen Haneef. Zuciyarta na wani bugawa ta gaishe da Momma.

Da fara’a ta ce,

“Lafiya ƙalau. Kuna lafiya dai ko?”

“Alhamdulillah.”

Safiyya ta amsa a daddage. Momma ta maida hankalinta kan Hussaina.

“Ku je da ita dining. Ki haɗa mata abinci da komai ta ci.”

Hannunta Hussaina ta kama ta ja. Suka bari Fu’ad a nan.

“Momma ni ma yunwa fa.”

Ya faɗi. Ta ɗan harare shi. ‘Yar dariya ya yi don ya riga da ya san ta yafe mishi. Da wahala yake laifi a idanuwan Momma.

A nutse ta ce masa,

“Fu’ad ka yi kuskure babba. Ba kai nake ji ba. Yarinyar can na ke ji saboda yadda iyayenta suka yi fushi sosai. Na tabbata za su jima ba su sauko ba. Kuma ko ni ce iya abinda zan yi kenan. Don Allah ka riƙe ‘yar nan. Duk macen da za ta yi maka abinda ta yi to ba ƙaramin so take maka ba. Duk idan kuna da wata matsala ina nan. Sannan ka kira Abbanka ko ba zai ɗaga ba. Shi ma na san a hankali zai huce.”

Shiru ya yi yana jin nasihar da ta ke masa tana wani shigar shi. Da sanyin murya yace,

“In shaa Allah Momma ba zan baki kunya ba. Allah ya ƙara girma.”

Murmushi ta yi.

“Amin Fu’ad. Allah ya yi maka albarka.”

Da murna ya amsa da amin yana mikewa ta ce masa,

“Fa’iza ta ce min ka siya gida ko?”

Da sauri yace,

“Eh Mummy takardun suna wajen Haneef ma. Sauran kayan ne muka siyo da Fa’iza yau. Kayan abinci ne kawai ya rage yanzu.”

Jinjina kai ta yi.

“Shikenan. Allah ya sanya alkhairi. Yanzu sai insa a ɗiba muku kayan abincin a store. Abinda babu sai ku siya ko?”

Shi ya sa soyayyar Momma bai haɗa ta da komai ba a zuciyarshi. Ba dai ta faɗa amma yasan ƙaunar da take masa ta fi ta kowa a gidan.

Godiya ya yi mata sannan ya wuce dining inda Safiyya ke zaune Hussaina na ta cika ta da surutu. Sai juya cokalin take cikin abinci ya san kunya ce ta hana ta ci.

Hussaina ya kalla.

“em starving fa haɗa min komai. Kuma kin cika ta da surutu Hussaina ya za ta yi ta ci abincin?”

Dariya Hussaina ta yi tace,

“Hira mu ke yi ne…”

Ta miƙe tana zuba wa Fu’ad abinci. Haɗa idanuwa suka yi da Safiyya. Sai lokacin ta ɗan ji wata yar nutsuwa ganin fu.ad ɗin.

“Ki ci abincin kar ya yi sanyi.”

Ci ta soma yi a hankali. Dambun shinkafa ne ya ji kayan haɗi da miyar ganye. Sosai ta ci abincin don ya mata daɗi ba kaɗan ba.

Fu’ad plate biyu ya ci ya sha lemo. Sannan ya miƙe ya ce wa Safiyya ta tashi su tafi.

Ta miƙe, a falo suka sami Momma. Ta kalle su ta ce,

“Fu’ad Fa’iza za ta zo. Sai su je wajen mai mana ɗinki akwai wasu atamfofi suna nan. Sai a ɗinka mata.”

Sosai Fu’ad ya ji daɗi don kamar ta shiga zuciyarshi.

“You are dah’ best Momma.”

Murmushi kawai ta yi masa suka yi mata sallama. Safiyya ta yi mata godiya cike da ladabi. Momma ta amsa,

“Ku gaida gida. Don Allah a kula kun ji ko?”

Fu’ad ne ya amsa don Safiyya kunya ta ke ji sosai har suka fita.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×