Skip to content

Akan So | Babi Na Ashirin Da Uku

0
(0)

<< Previous

Karfe uku da rabi a Crescent ta yi mishi. Sai da ya fara shiga suka yi magana da matar da za ta dinga zuwa gida tana koya wa Safiyya karatu. Ba wata babba ba ce ba can. Yoruba ce sai dai ta ji Hausa kamar ba gobe. Duka ba za ta shige shekaru ashirin da huɗu ba.

Magana suka yi ta fahimta. Fu’ad ya yi mata kwatancen gidansu. Kusan unguwarsu dayae ma. Layi uku ne tsakaninsu.

Suna gamawa ya fita waje ya tsaya a jikin motarshi ya na jiran Safiyya ta fito. Sai ware idanuwa yake yagae ta inda za ta ɓullo.

Hango ta ya yi rungume da litattafai. Wani murmushi ya ƙwace masa. Hango shi ta yi ita ma lokaci ɗaya ya ga murmushi ya bayyana a fuskarta.

Jinshi ya ke wani iri. Kamar da duk takun da take ta ƙaraso wajenshi har iskar wajen canzawa ta ke yi.

Kamar ya ruga ya rungumeta. Tana ƙarasowa ta yi masa kyautar wani murmushi da ya taɓa mishi zuciya.

“Ina wuni.”

“Sofi ‘yan makaranta. Sannu da ƙoƙari.”

Ya amsa. Dariya ta yi. Ya buɗe motar ta shiga. Ya zagaya shi ma ya shiga yajae motar.

“Ya makarantar? Ba dai wata matsala ko?

Girgiza masa kai ta yi.

“Dukkansu suna da kirki sosai. Wasu ma sun karɓi litattafaina za su tayani rubutun da aka wuce ni.”

Ya ji daɗin hakan. Yadda suka karɓar masa Safiyya.

“Babu wanda ya yi miki wulaƙanci dai ko? Daga ɗaliban zuwa malamai.”

Kai ta girgiza masa. Don ita kanta ta yi mamakin yadda suka yi mata karamci. Da sun fara mata turanci. A kunyace ta ce musu ba ta ji.

Mamaki kawai ta ga sun yi maimakon raini. Da alama dukkansu ‘yan manyan gida ne. Don haka ta amsa Fu’ad da,

“Haka ma suka ce zasue taimaka min . Gaskiya suna da karamci.”

Jinjina kai ya yi. Don Allah ne kaɗai zai raba shi da duk wanda ya nemi ya raina masa Safiyya ko ya wulaƙantata.

Suna isa gida ta yi mamakin ganin an buɗe musu gate. Kallon Fu’ad da ta yi ya gane tambayarta tun kafin ta buɗe baki.

“Ɗazu ya zo. An samo mana mai aiki ma.”

Ta ɗan ji daɗi. Ko ba komai ta ji motsin mutum banda su a cikin gidan. Taya ta ɗaukar litattafan ya yi yana faɗin,

“Anjima sai mu je a siyo jakar makaranta.”

Tare suka shiga ciki. Tun daga bakin ƙofa ya cire takalmin da socks ɗin da ya siya mata a makarantar.

Kauda su ta yi waje ɗaya. Sannan ta shiga ciki. Fu’ad ya bi bayanta. Kan kujera ya ajiye litattafan na ta.

Zuciyarta ta ji ta wani doka da su Inna suka faɗo mata. Ta na tuna yadda Baba ya so ta ci gaba da makaranta da ta nuna tana so sai dai bashi da ƙarfi.

Za ta so a ce sun ganta a yanzu. Sun ga yadda ta ke makaranta da ta tabbatar ta na da tsada sosai.

Ta san za su ji daɗi su ga ta samu ci gaba a rayuwa. Ita ta na nan ba ta san halin da suke ciki ba.

Ba ta san wasu hawaye sun zubo mata ba saboda wani nauyi da zuciyarta ta yi.

Ya ga tunani ta ke yi. Hawayen da ya ga ni a fuskarta ya sa shi tashi da sauri ya koma kan kujerar da ta ke.

Hannuwanshi ya sa ya tallabo kafaɗunta. Jinshi da ɗuminshi ya sa ta ji ta ƙarasa karaya. Cikin kuka tace masa,

“Ka kalleni. Cikin kwana huɗu rayuwata ta sauya. Ban san halin da iyayena suke ciki ba…ban san… Kawai…”

Riƙe ta ya yi gam. Kukanta na taɓa mishi zuciya. Ji ya ke ya na wani ci masa rai.

“Shhhhh”

Luf ta yi a jikinshi ta na sauke ajiyar zuciya. Riƙe ta ya yi ya sa hannunshi ɗaya ya na goge mata fuska.

“Laifi na ne Sofi. Ki ɗora shi a kaina. Ni na shiga rayuwarki na hargitsa komai. Ƙila da ban ganki sanda na ganki ba da ban jefa ki cikin halin nan ba. Da…”

Da sauri ta sa hannu ta rufe masa baki ta na girgiza masa kai idanuwanta cike da hawaye.

Karantar maganganunshi ta ke ta na jin wani irin yanayi. Muryarta kamar ba ta ta ba ta ce,

“Da baka ganni a sanda ka ganni ba da hakan na nufin da ban san ka ba..”

Lumshe idanuwanshi ya yi ya na sake riƙe ta gam. Don duk kalaman da ya yi zuciyarshi karyetawa ta ke.

Sumbatar goshinta ya yi yana jin kamar ya mayar da ita cikin cikinshi don kar wata ƙaddara ta zo ta ko da gifta ta tsakaninsu ne balle kuma a zo maganar ta raba su.

Hannu ya kai kan cikinta ya dafa.

“Me ki ka saka min a cikinki?”

Dariya ta ɗan yi ta na ɗora hannunta kan na shi saboda wasu abubuwa da ta ji suna mata yawo a cikin da ta san suna da alaƙa da hannunshi.

Mamakin yadda ta ke jin kamar shekara huɗu suka yi ba kwana huɗu ba.

Wani irin sabo ta ke jin sun yi da Fu’ad da ta tabbata ba aikinta bane na zuciyarta ne.

Yadda ya samu karɓuwa a yanzu ta ke jin numfashi daidaitacce ma da wahala ta iya yinshi in ba ya kusa mamaki ya ke ba ta.

Ba ta san sanda ta dumtse hannunshi gam ba. Hakan ya sa shi saurin ce mata,

“Sofi mene ne?”

Cikin idanuwanshi ta ke kallo. Kalarsu ta ke ƙare wa kallo yau. Ruwan ƙasar nan masu wani ratsin haske haske.

Wani abu ke fisgarta da ya sa ta ke son manta yadda ake numfashi.

Shi ma kallon na ta idanuwan ya ke. Yana karantar roƙon sa da ke cikin su.

“Ina nan sofi. Muna tare. Ba na ce miki ni da ke ne ba?”

Kai ta ɗaga mishi. Ta na sauke idanuwanta zuwa kan fuskarshi.

“Me kika ci?”

Fuskarta ta kai hannu tana gogewa tare da faɗin,

“Ban san sunan shi ba. A makaranta dai muka siya da su Khadija.”

Dariya ya yi.

“Ki ce har kin yi ƙawaye ma.”

Ita ma dariyar ta yi. Ta saka hannu a aljihun wandonta. Darie shidan da ya rage ta ɗauko masa.

“Ga canjin. Na kashe sosai dai. Ban san da tsada ba.”

Ware idanuwa ya yi ya na dariyar mamaki. Ɗari huɗu ta taɓa a ciki. Ganin ya tsaya kallonta ya satae jin duk babu daɗi.

Ta san ta kashe masa kuɗi sosai kuma har ranta batai san abinda suka siya da tsada ba da ba ta fara ba.

Muryarshi ta ji ya na faɗin,

“Sofi Allah ya shirya min ke.”

Dariya ya ba ta sosai sosai.

“Amin. Nima ana miƙo min canji sai da gabana ya faɗi.”

Wannan karon shi ya yi dariya.

“Kinga ke ɗin nan ko. Daga yanzu in na ba ki kuɗin makaranta. Duka ne na ba ki. In kin kashe fine. In ba ki kashe ba ki riƙe canjin.”

Riƙe baki ta yi. Ba ta san waccei kalar godiya za ta yi masa ba. Sai dai addu’a.

“Allah ya ba ka aljanna.”

Da sauri ya amsa da,

“Amin. Tare da ke mu yi zaman mu.”

Miƙewa ya yi ya riƙo hannunta.

“Kin ɓata min fuskarki da hawaye. Tashi mu je a wanke.”

Wata ‘yar kunya ta ji ta rufe ta. Ta yi masa murmushin nan da ya ke masa wani abu a zuciya da ba shi da kalaman ɗora shi akai.

Bin shi ta yi ya raka ta har bedroom ɗin ta wanke fuskarta. Tayi la’asar tun a makaranta.

Kallonshi ta yi.

“Bari in watsa ruwa. An bamu aikin gida ban iya ba sai ka duba min.”

Wani ɗaga mata girarshi ya yi duk biyun yana ciza leɓe. Sannan ya fice daga banɗakin ya bar zuciyarta da waƙar yadda kyawun shi ya ke.

*****

Falo ya koma ya zauna abinshi. Ji ya yi ana ƙwanƙwasa ƙofa. Ya tashi ya je ya buɗe.

Fa’iza ce an ci uban gayu. Sallama ta yi masa tare da faɗin,

“Ina wuni.”

Wucewa ta yi cikin falon. Ba ta ma jira amsar shi ba. Ya maida ƙofar ya kulle.

Ya dawo ya zauna. Sai lokacin ya kula da ledar da ke hannunta.

“Momma ta ce in kawo muku abinci. Sai kuma mu je wajen tela da matarka.”

Yadda muryarta ta yi a kalmar matarka ya mishi wani iri.

“Sunanta Safiyya. Thank you da ki ka gane matata ce. In ba za ki taya ni sonta ba. Ki bar abin a ranki.”

Sauke ajiyar zuciya Fa’iza ta yi a sanyaye ta ce,

“Ka yi haƙuri. Kawai zuciyata ta kasa nutsuwa da ita ne. I have this hunch…”

Katse ta ya yiyda faɗin,

“Spare me mana. Na ɗauka kin girmi wannan Fa’iza.”

Ɗan ɗaga kafaɗa ta yi.

“Fine. Allah ya ba ku zaman lafiya.”

Murmushi ya yi. Ya amsa da,

“Amin.”

Ya fi so dukansu su tayashi son Sofi. Kamar ta ji ambatonta da ya yi a zuciya ta fito daga ɗaki.

Jikinta sanye da doguwar riga ta ɗauro ɗankwalin. Ɗan tsayawa ta yi saboda ganin Fa’iza a falon.

Fuskar Fa’iza ba yabo ba fallasa ta ce,

“Ina wuni.”

A kunyace Safiyya ta ɗan ƙaraso ta zauna a gefen Fu’ad tare da faɗin,

“Ina wuni. Ya su mama.”

“Suna lafiya. Ta na gaishe ku. Ina jin bama sai mun je da ke ba. Ina da tape kawai sai in auna ki.”

Hakan ma ya fi wa Safiyya daɗi. Tape ɗin Fa’iza  ta ɗauko da ‘yar takarda da biro. Ta auna Safiyya ta rubuta.

Ta na gamawa ta kalle su ta ce,

“Ni kam dai na wuce. Sai anjiman ku.”

A hankali Safiyya ta ce,

“Sai anjima. Mun gode.”

Yadda ta yamutsa fuska sai ta yi mata yanayi da Fu’ad sosai sosai. Irin abu ɗaya hancinsu ya ke yi.

“Bro ka ji ta. Wai kun gode.”

Dariya Fu’ad ya yi ya ɗora da,

“Fa’iza ki kawo mata sauran kayan da mu ka yi magana fa.”

Ɗan dukan goshinta ta yi.

“Ka ganni ko. Suna mota fa. Bari in ɗauko.”

Fita ta yi daga ɗakin. Ba ta fi minti biyar ba ta dawo da ledoji har huɗu ta ajiye musu a tsakiyar falon ta juya da faɗin,

“Na wuce…”

Ɗaukar ledojin Fu’ad ya yi ya miƙa wa Safiyya. Ta buɗe su. Ɗaya kayan bacci ne sai under wears.

Da sauri ta rufe don tunanin ta Fu’ad ya gansu kawai ya sa ta jin kunya. Ɗayan kuma takalma ne. Ta ɗauko guda ɗaya ta gwada. Kamar Fa’iza ta auna ƙafarta sun zauna cif.

“Sun miki kyau.”

Fu’ad ya faɗi ya na kallon ‘yar ƙafarta da ta burge shi. Kallon shi ta yi sosai.

“Na gode. Na gode sosai…”

“Shhhhhh”

Ya faɗi ya na mata murmushi. Shi ya tayata suka ɗauki kayan zuwa bedroom ɗin da ya soma kira na ta. Ya buɗe wardrobe ya zuba mata kayan a ciki. Sannan suka dawo falo.

Assignment ɗin English ɗin da ta yi masa magana ta ɗauko. Ya yi mamaki sosai da ganin rubunta. Ko da ya ke ba wai a karatu ba ne abun. Iya rubutu baiwa ce. Ko shi bai da handwriting me kyau haka. Wannan sai su Haneef. Kamar ya sace lokacin da suke makaranta.

Bayani ya ke mata ya ga dai ba iya yi za ta yi ba. Dole komai sai a hankali. Rubuta mata answers ɗin ya fara yi.

Ya yi layi biyu ya ji ta ce,

“Kai kai kai.”

Shi kanshi rubutunshi ya kalla ya kalli na ta. Sai ya kwashe da dariya. Ya manta when last ya yi rubutu in ba a system ba.

Daƙuna fuska ta yi. Alamar rubutun bai mata ba. Idanuwanshi ya sa cikin na ta ya na mata wani cute eyes.

“Allah sai na rubuta.”

Dariya ta yi.

“Ka min a wata takarda sai in kwafa.”

Ɗauke littafin ya yi yana maƙe kafaɗa.

“Na ƙi. A ciki na ke son yi.”

“In ya ga rubutun ba iri ɗaya ba fa? Sai ka ja min bulala.”

Zaro idanuwa ya yi fuskarshi na yin wani serious lokaci ɗaya.

“Na faɗa musu matar aure ce ke. Za mu hau bene mu faɗo da duk wanda ya taɓa min jikinki.”

Dariya kawai ta yi.

“Ni kam ka ba ni littafina.”

Ɗaga hannunshi ya yi sama da littafin ya na girgiza mata kai.

“Na sani ai. Rubutuna ba shi da kyau ko? A haka zan miki. In an ce na waye ki ce na mijinki ne.”

Dariya take sosai. Hakan na mishi daɗi. Miƙewa ta i kan gwiwoyinta tana ƙoƙarin kai hannu ta kamo na shi da ke riƙe da littafin.

“Ka ga kana daƙuna min ko?”

Dariya ya ke mata. Sosai ta miƙa hannunta ta kamo na shi ya janye. Jikinshi ta faɗa. Bin ta ya yi da kallo. Ita ma kallonshi ta ke sosai. A hankali ya sauke hannunshi, idanuwanshi na cikin na ta. Har wata iska ya ke ji shuuu mai wani irin nutsuwa. A hankali ya ke ranƙwafowa ya na kai fuskarshi dai dai ta ta . Kusan numfashi ɗaya suke shaƙa ita da shi.

Ƙara matsawa ya ke sosai ya na jin yadda numfashinta ke fita da sauri. Ƙwanƙwasa ƙofar aka yi.

Ya lumshe idanuwanshi. Da sauri Safiyya ta tashi daga jikinshi ta na wani maida numfashi.

“Fuck…”

Ya faɗi da alamar kowaye ya ɓata musu yanayi. Miƙewa ya yi da irritation a muryarshi ya na faɗin,

“Waye?”

“Ni ce.”

Aka faɗi. Bai gane muryar ba. Don haka ya ƙarasa kawai ya buɗe ƙofar. Wata mata ce mai matsakaicin shekaru.

Ƙare wa shigarta kallo ya ke.

“Lafiya?”

Ya buƙata muryarshi a daƙile. Cikin taushin murya ta ce,

“Indo ce. Malam Isah ya turo ni.”

So yake ya tuna waye ma Malam Isah? Ganin kamar bai gane ba yasa sa ta faɗin,

“Wadda za ta yi muku aiki ce.”

Sake tamke fuska Fu’ad ya yi ya na faɗin,

“Oh. Shigo.”

Matsa mata ya yi. Ta raɓa shi ta wuce. Da fara’a Safiyya ta tarbe ta.

“Ina wuni.”

Ta gaishe da ita. Wani daƙuna fuska ta ga Fu’ad ya yi. A ƙiyasce matar za ta yi shekara talatin.

Ƙasa ta zauna. Safiyya ta ce mata,

“Ki hau sama mana.”

Ɗan murmushi ta yi.

“Nan ma ya yi.”

Shiru suka ɗan yi kafin Fu’ad ya ce mata,

“Ba wani aiki ba ne mai yawa. Na san ya ba ki kuɗin aikinki na wata biyu. Shara ce. Sai duk aikin dai da ta ke so. Za ki iya dafa abincin da za ku ci da mai gadi.

Yadda ki ka ga zai fi miki. In kwana za ki dinga yi. Akwai BQ, in kuma gida za ki dinga komawa to.”

Kallon Fu’ad Safiyya ta ke yi. Yadda ya haɗe fuska kamar bai taɓa dariya ba. Yanayin muryarshi kamar ranar farko da ta fara ganinshi. Sai ba ta ji daɗin yadda ya yi wa matar nan magana babu wani tausasawa ba.

“Ba kusa nake ba. Cikin Dawanau na ke da zama. Zan dinga kwana anan ɗin. Sai dai zan koma duk ranar Juma’a in dawo ran Asabar in Allah ya yarda.”

Wani kallo Fu’ad ya yi mata. Ya ce,

“Wa zai yi aikin gidan na ranar Juma’a ɗin kenan?”

Sake saukar da murya ta yi.

“Sai na gama tukunna. Ran Asabar ɗin in shaa Allah da wuri zan dawo.”

Ganin ya na girgiza kai ya sa Safiyya faɗin,

“Allah ya kaimu. Babu komai ai. Ko ni sai in yi.”

Miƙewa Fu’ad ya yi. Ya ɗauki mukullan da ke gefenshi ya zari wasu ciki ya ajiye kan teburin  tsakiyar ɗakin ya na faɗin,

“Ga mukullan in da za ki dinga kwana. Ya na nan baya da kin zagaya.”

Bai ko tsaya dubanta ba ya ƙarasa inda Safiyya ta ke ya kama hannunta ya miƙar da ita ya ja ta zuwa bedroom ɗin. Suna shiga ya tura ƙofar ya saki hannunta ya na mayar da nashi kan ƙugunshi.

“Idan ina magana da masu aikin nan ki daina saka baki. Kuɗi na biya ta ba wai kyauta na ce ta zo ba. Saboda me za ki yi mata aikinta?”

Yanayin shi ma tsoro ya ba ta. Ya wani tamke fuska. A daddaure ta ce.

“Ka yi haƙuri.”

Lumshe idanuwanshi ya yi ya sa hannu yana murza goshi. Kamota ya yi ya rungume a jikinshi.

Ba ya son tsoron shi da ya gani a cikin idanuwanta. Kamar yadda ba ya son kowa ya raina mishi ita.

Bayan Sati Biyu

Komai na tafiyar musu da ci gaba. Da wata irin shaƙuwa mai ƙarfi da ta ke ƙara shiga tsakanin su.

Don Safiyya ji ta ke ba ta da sauran kowa a wannan sabuwar duniyar da ba ta san gabas ɗin ta ba sai Fu’ad. Cikin satin farko kwana uku ta jera kullum ta dawo daga makaranta sai ta yi kuka.

Amma yanzu ta haƙura. A duk rana da kewar su Inna ta ke tashi da ita kuma take kwana.

Sai dai a hankali ta ke sabawa da ita. Ranar makaranta ƙarfe biyar Anti Laurat ke zuwa gida ta koya wa Safiyya karatu.

A sati biyun nan sun fara sabawa da ita sosai. Safiyya ta fara sakewa da ita. Haka ma Mama Indo kamar yadda ta ke kiranta.

Tare suke share sharensu in Fu’ad ba ya nan. Mama Indo ta dafa musu abinci. Ita ta ke koya wa Safiyya amfani da kayan kitchen ɗin.

Don ta yi aiki gidajen masu kuɗi bayan rasuwar mijinta ya bar ta da yara har shida da suke hannunta.

Fu’ad ba ya ci. Wai ƙazanta sai dai ya siyo musu abincin waje. Ita ma Safiyyar in ya na gida ba ta isa ta ci ba. Ta na gudun faɗan shi.

Ba ta kuma son a ce ga ta ya na fita waje siyen abinci. Ta masa magana ya kai ta inda za ta koyi kalan girkin da ya ke so ya ce aikin zai mata yawa ba yanzu ba tukunna.

A makaranta kuwa suna gaisawa da duk ‘yan ajin. Haka mazan suna ganin girmanta da aka ce musu tana da aure.

Za su gaisa a mutunce. A matan kuwa Khadija da Aisha ne suka zama kamar ƙawayenta. Suna ƙoƙarin koya mata karatun turanci da kuma gane yaren.

****

Zaune ya ke a ɗakin Lukman. Kallo ɗaya za kai wa fuskarshi ka san ya na cikin ɓacin rai.

“Ka share kawai. Zai sakko with time.”

Cewar Lukman. Sake ɓata rai Fu’ad ya yi tare da faɗin,

“Haba lukman? Nan da yaushe. Kullum fa sai na kira Abba a waya ba ya ɗagawa. Na ɗauka in ya ganni ido da ido yau zai haƙura. Amman ina gaishe da shi ko kallo na bai yi ba.”

Jinjina kai Lukman ya yi.

“To ita kuma Safiyya ta ce me? Kai kullum sai ka ga Momma da su Fa’iza.”

Tauna maganar Lukman ya yi. Ya nisa ya ce,

“Hakane, with time. Ita ma in shaa Allah zan shirya ta da na ta family ɗin tunda ni ne silar ɓata su.”

“Ko kai fa? Ashe ka fara hankali.”

Dariya Fu’ad ya yi kafin ya ce,

“Jibi fa zan tafi. Ni ban ma san ta inda zan gaya wa Sofi ba.”

Fito da idanuwa Lukman ya yi.

“Wai ba ta san jibi za ka tafi ba?”

Sauke numfashi Fu’ad ya yi.

“Ba ma ta san zan tafi ɗin ba at all. Maganar ba ta taɓa haɗa mu ba.”

Kallon shi Lukman ya ke yi.

“Ai kuwa ba ka kyauta ba. Yanzu tafiyar za ta yi mata wani iri.”

Langaɓe kai Fu’ad ya yi.

“Ai ba ita kaɗai ba.”

Harararshi Lukman ya yi.

“Dalla kauce da ga nan. Abin ma haushi.”

Dariya Fu’ad  ya yi ya taɓare fuska tare da faɗin,

“Em gonna miss her.”

Riƙe hanci Lukman ya yi.

“You are disgusting Fu’ad.”

Dariya suka yi gaba ɗayan su kafin Fu’ad ya miƙe.

“Bari in koma wajen matata. Zama ɗakin gwauro yana min somehow.”

Pillow Lukman ya ɗauka ya jefa mishi. Ya kauce ya fice daga ɗakin ya na dariya.

*****

Tunda ya koma gida ya samu Safiyya da Anti Laurat zaune a falo sun baje litattafai. Sannu da zuwan Anti laurat ma da ta yi mishi da ƙyar ya amsa ya shige cikin bedroom.

Kallon Safiyya ta yi.

“Ki je ko yana buƙatar wani abu.”

A iya sanin halin Fu’ad da ta yi ya sa ta girgiza kai.

“Idan yana son wani abun zai kira ni.”

Ta amsa ta na ƙarasa rubuta abinda ta ke yi. Kallonta Anti Laurat ta yi.

“Look at you. Oya tashi ki je. Ko ba ya buƙatar wani abin ki masa sannu da zuwa properly.”

A kunyace ta miƙe ta nufi bedroom ɗin. Ya na zaune gefen gado ya na danna waya Safiyya ta shiga da sallama.

Wani numfashi ya sauke. Atamfar da ke jikinta ta karɓe ta . Ga ɗinki ya zauna mata cif. Wani sonta ya ke ji ya na yawata masa.

Hannunshi ya miƙa mata da ta ƙarasa. Ƙarasawa ta yi ta sa hannunta cikin na shi ta zauna. A taɓare ya ce,

“Ki sallame ta Sofi. Ina buƙatar ki a kusa da ni.”

Murmushin nan ya samu mai cike da kunya. Ba ta ce komai ba ta miƙe ta fita falo. Murmushi ta yi ba ta san ta yadda za ta ce ma Anti Laurat ta tafi ba tunda yau weekend ne. In ta zo ƙarfe huɗun nan sai magriba. Suna da sauran mintina talatin kafin lokacin tafiyarta ya yi. Kallonta Anti Laurat ta yi tare da yin ɗan murmushi.

“Sai Allah ya kaimu gobe. Ki duba abinda mu ka yi yau.”

A kunyace ta ce,

“Allah ya kaimu. Na gode sosai.”

Har bakin ƙofa ta rakata ta kulle gidan sannan ta koma. Yana zaune inda ta bar shi. Agogon wayar shi ya duba. Ya miƙe tsaye ya taka zuwa inda ta ke. Hannuwan shi ya sa kan kafaɗunta ya ja ta zuwa jikinshi. Rungumeta ya yi ya na ɗan jujjuya su. Sun kai mintina biyar a haka. Bai san yadda zai fara gaya mata zai koma Europe ba. Sai ya yi sati shida in ya koma kafin ya samu ya zo yai kwana biyu. Da ace waje ɗaya zai zauna in ya je ba abinda zai hana ya ƙi tafiya da ita.

Da ƙyar ya iya janye jikin shi daga na ta tare da faɗin,

“Bari in yi alwala…”

Kai kawai ta iya ɗaga mishi. Ta ƙarasa gefen gadon ta zauna. Alwala ya yi ya fito. Ya tafi masallaci. Ta san ba dawowa zai yi ba sai ya yi Isha’i. Don haka ta shiga banɗaki ta yo alwalar ita ma ta fito ta yi Sallah.

Sanda ya dawo masallaci. Mama indo ta shigo ta yi musu sai da safe. Ya kulle na su side ɗin. Suka ci abincin da ya siyo.

Ɗakin shi ya wuce can ya yi wanka. Ita ma ta yi. Rigar bacci ta saka ta ɗaura Ɗankwali. Ta ji daɗin yadda Fa’iza ta samo mata wadatacciya. Duk da haka har yanzun kunya ta ke ji Fu’ad na kallon ta a ciki.

Suna kwance ta ji ya ƙarasa haɗe sauran wajen da ke tsakaninsu. Sannan ya ja blanket ɗin ya gyara musu rufa. Hannu ɗaya ya ɗora kan fuskarta ya na ƙare mata kallo cikin wutar ɗakin da ba ta da hasken kirki.

“Sofi ban san ta ina zan fara ba.”

Murmushi ta yi mishi. A sanyaye saboda yadda kallon da ya ke mata da kusancinsu ke kashe mata jiki ta ce,

“Ka fara ko ta ina.”

Numfashi ya sauke.

“Kin tuna na ce miki ball na ke ko?”

Ta ɗaga mishi kai alamar ta tuna. Don ba ta manta komai da yake faɗa mata game da shi ba.

“Tam kwanakin nan da ki ka ga na yi. Wani ɗan hutu ne na samu. Yanzun kuma zan koma.”

Hannunta ta dora kan na shi da ke fuskarta. Don ba ta ga abin kasa bayani a maganarshi ba. Tunda ya fara ta karanci damuwa a muryarshi.

“Allah yasa a koma lafiya ya kuma bada sa’a.”

Ya san ba ta gane ba.

“Amin…..”

Ya rasa ta yanda zai gaya mata. Shi kanshi har ya soma kewarta tun kafin ya tafin. Muryarshi can ƙasa ya ce,

“Ba a nan ƙasar ba. Tafiya zan yi jibi. Sai nan da sati shida zan dawo…”

Mikewa zaune ta yi ba shiri. Lokaci ɗaya idanuwanta suka ciko da hawaye. Shi ma zaune ya miƙe ya na faɗin,

“Haba Sofi. Za mu yi waya kullum zan kiraki. Kuma…”

Kuka ta sa. Kuka sosai hawaye wani na bin wani. Tafiya zai yi ya bar ta har sati shida. Kamo ta ya yi ya na lallashi cikin kuka ta ce,

“Wa zai kai ni makaranta?”

Kama hakan kawai ya isa dalilin da zai sa ya fasa tafiya.

“Zan samo driver. Kuma zan ma Laurat magana kullum ta biyo ta nan a kai ku tare. A ɗauko ku tare.”

Kukan ta ci gaba da yi ta na girgiza masa kai alamar ba ta yarda ba. Sake riƙe ta ya yi a jikinshi ya na jin yadda ta wani ƙanƙame shi.

“Ba na so ka tafi.”

Lumshe idanuwanshi ya yi. Shi kanshi da hawayen za su zubo da ya ɗan ji sauƙin abinda ya ke ji.

Kamo fuskarta ya yi. Ɗaya bayan ɗaya ya sumbaci idanuwanta. Da duk fuskarta. Hannu ya sa ya goge mata hawayen.

Kallonta ya ke sosai. Kafin ya haɗa bakin shi i da na ta. Ya na jin yadda ta riƙe jikinta kafin ta saki a hankali. Saboda ita ce rana ta farko da bakinshi ya haɗu da na ta. Ya rasa yadda zai mata ne kawai. Sai da ya tabbatar ba ta da wani ƙarfin ƙara mishi damuwa tukunna.

Janta ya yi kan ƙirjinshi ya kwantar da ita. A hankali cikin muryar da kunnenta ne kaɗai ke ji ya ke kwantar mata da hankali da kalamai masu taushi.

A haka ya yi musu addu’a ya na lallaɓata har bacci ya ɗauke su.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×