Skip to content
Part 5 of 48 in the Series Akan So by Lubna Sufyan

21 February 2017

Har ya gama bubbuga ƙofar ya tafi ba ta buɗe ba. Kuka kawai take yi. Sai da ta yi mai isarta sannan ta tashi ta shiga toilet. Ruwan ɗumi ta haɗa ta shiga ciki, saboda jikinta ko’ina ciwo yake yi. Yadda Nawaf ya janyota daga kan kujera ya jefar ƙasa. Ba ƙaramar buguwa ta yi ba. Za ta iya rantsewa wani lokaci Nawaf ba shi da hankali. Zaman lafiyarsu na wata biyu ne a shekara ɗaya da rabi da aurensu. In har sunan Farhan ya gifta cikin gidan sai an samu matsala. Ta rasa kalar soyayyar nan ta Nawaf. Ta san da gaske yana sonta sosai. In kuma ya dake ta yana yin duk abinda ya san zai faranta mata. Nawaf ya mata halacci. Ba zata manta abin da ya fara yi mata ranar farko ba.

*****

Ta dawo daga makaranta da yamma sakaliya. Tafiya kawai take, amma da tana da wani wurin da za ta je da ba ta koma inda ya zame mata dole ta kira gida ba.

Ta jima sosai tana tsaye a wajen ƙaton flat house ɗin da yake da bala’in jan hankali daga waje. Gidan da za ka iya rantsewa mutanen arziƙi ke rayuwa a ciki. Ajiyar zuciya Nuri ta yi sannan ta ƙwanƙwasa ƙofar, mai gadi ya buɗe mata. Ta gaishe da shi cike da ladabi, tsohon ya amsa cike da tausayinta a muryarshi da yanayin shi. Tun kafin ta ƙarasa cikin falon take jin shewa da hayaniyar maza da mata.Duk da hakan ba baƙon abu bane a wajenta, bai hanata jin sabuawar tsanarshi a ranta ba. Ba ta damu da ta yi sallama ba, kai tsaye ta ƙarasa falon. Addu’a kawai take yi ta wuce zuwa ɗakinta lafiya. Ba ta ƙi ace babu wanda zai kula da shigarta ba.

Kanta a ƙasa. Muryar Alhaji Baushe ta ji yace:

“Nuriyya kin taso daga makarantar?”

Ba ta ko nuna alamun ta ji shi ba. Zuciyarta sai bugawa take yi. Ta tsani mutumin nan, da za a ba ta damar kisa shi ne na farko da zai faɗo mata a rai. Jin takun shi ya sa ta ƙara sauri don wucewa ɗakinta. Caraf ya riƙe mata hannu da duk karfin shi. “Ke ina miki magana za ki wuce ni. Ko uwarki ba ta isa ta wulaƙanta ni ba balle ke banza.”

Idanuwan Nuriyya cike da hawaye take ƙoƙarin ƙwace hannunta. Amma sai ƙara janta zuwa jikin shi yake yi. Kokawa ta gaske suka shiga yi. Da yake Alhaji Baushe ba ƙarami bane. Irin manyan mutanen nan ne ya riga ya fi ƙarfin Nuriyya ta ko’ina.

Allah ne ya ba ta sa’a ta gatsa masa cizo a ƙirji wanda sai da ya gigita shi. Da gudu ta nufi hanyar waje tana ihun da ta san ba ta da mataimaki sai Allah. Sanin halin gidan da abinda ke faruwa ya sa baba Mai gadi buɗe wa Nuriyya ƙofa cikin hanzari don shi ne kaɗai taimakon da zai iya yi mata.

Wani matashin saurayi ta hango tsaye jikin wata farar mota. Banda shi ko kare babu a unguwar.

Juyawa ta yi ta hango Alhaji Baushe ya fito da gudu. Ta ƙarasa wajen saurayin tana wani irin kuka.

“Ke lafiya kuwa?”

Ya tambayeta.

Cikin kuka tace:

“Ka taimaka min, wallahi zai lalatamun rayuwa.”

Da mamaki a idanuwanshi yace:

“Bangane ba.”

Kafin ta yi masa bayani, tuni Alhaji Baushe ya ƙaraso inda suke yana wani huci kamar mayunwacin zakin da ya kwana bai ci ba. Ko kallon saurayin da ke tsaye bai yi ba ya kai hannu zai cafko Nuriyya da ta ɓoye a bayan saurayin. Ba tare da tunanin komai ba saurayin ya wanke Alhaji Baushe da wani irin mari.

Hakan ya ba Nuriyya damar sake laɓewa a bayan saurayin. A dake yace:

“Wallahi, in ka taɓa ta zan baka mamaki.”

Da alamun kallon da Alhaji Baushe yake wa saurayin ya ga babu alamar wasa a bayanin shi, kuma yanzu yake ji da ƙuruciya. Gashi in ya ja maganar har wani ya zo wucewa za a iya samun matsala. Kallon da yake fassara za ki dawo gidan ya yi wa Nuri sannan ya juya. Hankalin shi saurayin ya maida kan Nuri da ke wani irin kuka cike da tambayoyi da yawa yace:

“Menene haɗinki da wannan mutumin?”

Ta kasa ba shi amsa, sai wani irin kuka take da ya ji yana ci mishi rai. Hannunta ya kama ya buɗe motar shi ya saka ta. Zagayawa ya yi ya zauna. Ya ɗauko ruwa dake gefe ya miƙa mata tare da faɗin:

“Ungo ki sha.”

Ba ta yi musu ba ta karɓa ta sha sosai. Ta buɗe motar ta wanke fuskarta tana ta sauke ajiyar zuciya. A sanyaye yace mata:

“Sunana Nawaf.”

“Nuriyya.”

Ta amsa mishi, muryarta a dakushe.

*****

Sallama ta ji da ta dawo da ita daga tunanin da take yi. Kafin ta amsa an sake yin wata. Da sauri ta tsane jikinta ta fito daga ban ɗakin.Doguwar riga ta zura ta ɗauki ƙaramin hijab ta sa da sauri ta fito tana amsa sallamar.

A kunyace tace:

“Yaya sannu da zuwa. Wallahi ina wanka ne shi ya sa ka ji shiru. Ina kwana.”

Kallon ta T.J yake yi sosai. Wani jini ne ya taru a gefen fuskarta har ya soma baƙi-baƙi. Ya girgiza kanshi cike da takaici. Wuri ya samu ya zauna kawai. Nuriyya ta zauna nesa da shi tana faɗin:

“Ina Aunty Jidderh?”

Numfashi T.J ya sauke, sannan yace:

“Tana lafiya Nuriyya. Ya kike?”

“Alhamdulillah.”

Ta amsa, sannan ta ƙara ɗorawa da:

“Sai dai Nawaf ɗin ya fita.”

Kallonta T.J ya sake yii sosai a nutse yace:

“Gidana ya je Nuriyya. Me yasa ba ki taɓa ko da kirana kin faɗa min Nawaf na dukan ki ba?”

Kanta ta sunkuyar ƙasa. Ta yaya za ta fara kai ƙarar nawaf? Ta ce me? Gani ya yi ba ta da alamar  ba shi amsa, hakan ya sa shi ci gaba fadin:

“Nuriyya yadda ya yi min bayani kamar Farhan ne ke yawan kawo matsala tsakanin ku. Kin ga dai yadda Nawaf yake. Ke ce abu na farko a rayuwarshi da ta raba shi da addiction ɗin da mu munyi iya bakin ƙoƙarinmu mun kasa. Nuriyya Nawaf yana sonki. A kalar nasa haukan. Don Allah ki yi ƙoƙari sunan Farhan ya daina fitowa daga bakinki a gabanshi kin ji ko?”

Muryarta can ƙasa ta ce:

“In shaa Allah Yaya. Mungode sosai. Allah ya ƙara girma.”

Miƙewa T.J ya yi yana faɗin:

“Bakomai Nuriyya. In ya sake dukanki ko ki kirani ki faɗa min ko kuma ki kira Jidderh. Ko kizoe gidana kin ji ko?”

Kai Nuriyya ta ɗaga masa. Ya yi mata sallama ya fice. Ta sake lafewa cikin kujera. Ko don karamcin da ‘yan uwan Nawaf suka nuna mata kaɗai ya isa ta shanye duk wani abu. Ballantana son da shi kanshi Nawaf ɗin yake mata.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Akan So 4Akan So 6 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×