Skip to content

Akan So | Babi Na Goma

3
(1)

<< Previous

Bai ma yi ƙoƙarin kula su Lukman ba. Kamar yadda ba su ce masa uffan ba, haka shi ma bai ce musu komai ba har suka kai gida. Lukman ya ce ma Haneef zai je gida ya kira shi in za su koma.

“Haneef ka ban lambar mai gyara ma Abba mota.”

Ko in da yake Haneef bai kalla ba ya wuce ya shiga cikin gida. Wani abu Fu’ad ya ji ya tokare masa wuya. Already baya jin daɗin komai. Ga yunwa da ke damun shi, ɗan cake ɗin da ya ci har ya ƙone. Cikin gida ya shiga. Atika na hango shi ta rakuɓe a jikin bango. Kaf ‘yan aikin gidan ya kula dole ke sawa suna haɗuwa da shi.

Wucewa ya yi ɗakin shi ya yi wanka sosai. Sanda ya fito jin shi yake wani fresh. Crazy jeans ɗin dai ya sake maidawa blue. Da farar riga da ta matse shi. Ya feshe jikinshi da collection ɗin turarukan shi.

Ɗakin Haneef ya nufa. Bai damu da ya yi knocking ba ya shiga. Yana tsaye yana ɓalle links ɗin rigarshi. Jikin shi sanye da wani yadi ruwan toka. Ya matuƙar karɓar shi.

“Zan fita. Ba nisa zan yi ba, abinci zan siyo in dawo.”

Ko kallonshi Haneef bai yi ba. Za ka rantse ba da shi yake magana ba ma. Matsalolin Fu’ad yawa gare su. Ya san gulma ce wai shi ba ya cin abincin ‘yan aiki. Ƙara son taɓara shi ma Mummy ke shi ga kitchen ko su Fa’iza a dafa mishi.

Yau ba sa nan ya san hotel zashie ya kaso dubunnai kan abinci bayan ga shi a gida.

A ƙufule Fu’ad yace:

“What is with the attitude? Tun ɗazun nake maka magana ka share ni.”

Kallon shi Haneef ya yi cikin idanuwa sannan yace:

“Me kake so in ce maka? Abinda kake so ba shi kake yi ba? Meye na neman ra’ayina kuma?”

Kallon shi Fu’ad ya yi na wani lokaci kafin yace:

“Ka ce in yi dropping case ɗin kuma na yi. Me ka ke so inyi again?”

Wani numfashi Haneef ya ja. Ƙarasawa ya yi inda Fu’ad yake tsaye ya sa idanuwanshi cikin na Fu’ad.

“So nake ka san darajar mutane Fu’ad. Kai ma watarana uba za ka zama. Za ka so a girmama ka.”

Wani murmushin takaici Fu’ad ya yi.

“Ba na girmamaka?  Ba na girmama su Abba? And ban taɓa hango ni da yara ba. Ba na son damuwa.”

Girgiza kai Haneef ya yi. Rashin hankalin Fu’ad yawa gare shi.

“Just get out of my room!”

Lokaci ɗaya ya ji ɓacin ran da yake ta yawo a ƙasan zuciyarshi ya samu wajen zama.

“Haneef! Ni kake kora daga ɗakinka?”

Wucewa ya yi ya ci gaba da hidimar shi. Wuri Fu’ad ya samu kan ɗaya daga cikin kujerun ɗakin ya zauna. Wasa yake da zoben azurfar da ke hannunshi. Har Haneef ya gama shiryawa yana wajen a zaune.

“Ba yunwa ka ce ka na ji ba?”

Haneef ya tambaya. Shiru ya yi shi ma. Bai damu da yunwar shi ba ai. Ya fi damuwa da ‘yan ƙauyen nan da bai ga abinda suka yi mishi ba zai ɗora masa laifi.

Ajiyar zuciya Haneef ya sauke. Matsala ɗaya da ake samu kenan. Son Fu’ad yana hana shi nuna masa kuskurensa. Da ma duka’ yan gidan. Kan hannun kujerar ya zauna muryarshi a sanyaye yace.

“Ka tashi ka je ka siyo abincin. In kuma ba zaka koma ba mu tafi da Lukman.”

Ɗago fuska ya yi. Ya wani taɓare murya.

“Ka damu da yunwar da nake ji ne. Za ka kama min faɗa akan ‘yan ƙauyen nan.”

Murmushi Haneef ya yi.

“Sorry okay? Tashi ka wuce. Kai zamanka kawai za mu koma.”

Da sauri yace:

“No zan bi ku ni ma.”

Kawai ya ji yana son komawa ƙauyen. Ba kuma ya son amsa ma kanshi dalili. Miƙewa ya yi ya kalli Haneef yace:

“We’re good?”

Ɗaga masa kai ya yi tare da faɗin:

“Yeah, we are good.”

Murmushin shi da yakan jima bai yi ba ya yi wa Haneef sannan yace:

“Bari in je in yi settling da Lukman.”

“Kaje ka sa abu a cikinka tukunna.”

Girgiza kai ya yi yana buɗe ƙofar yace:

“He is more important.”

*****

Yana shiga gidan su Lukman kanshi tsaye ya wuce ɗakin su Lukman ɗin. Yana zaune yana cin indomie da soyayyen ƙwai.

Ko sallama bai mishi ba yace:

“Wa ya dafa?”

Ɗagowa Lukman ya yi ya kalle shi.

“Shi ne sallamar ka kenan?  To ban sani ba.”

Dariya kawai Fu’ad ya yi.

“Don’t be a jerk. ‘Mma hungry.”

Saida ya yi kamar ba zai amsa shi ba sannan yace:

“Ummie na sa ta ɗafa min.”

Bai cire takalmin ƙafarshi ba ya ƙarasa ya zauna a gefen gadon Lukman. Sanin halin shi ya sa Lukman ya miƙa mishi plate ɗin duka. Bai musu ba ya karɓa.

Saida ya cinye duka sannan ya sha orange juice ɗin da ke cikin kofin glass ɗin da Lukman ya zuba bai taɓa ba.

“I am still hungry.”

Ya fadi yana yamutsa fuska. Miƙewa ya yi yana faɗin:

“We’re good?”

Kai kawai ya ɗaga mishi. Ya san pointless ne ƙoƙarin saka Fu’ad a hanya. Yana kallon shi har ya fice daga ɗakin.

*****

Wannan karon Fu’ad bai manta komai ba. Za ka rantse wata tafiyar sati biyu zai yi in ka ga kayan da ya ɗauka. Har da toiletries gaba ɗaya. Ya je ya zuba cikin Range Rover ɗin shi ya kira Lukman a waya ya ce musu sun shirya. Haneef da Lukman suka zauna a gaba. Wannan karon Haneef ke tuƙin.

*****

Suna shiga Maman su ya kira a waya shi yana missing ɗinta.

“Fu’ad a nan ka kwana?”

Ta tambaya cike da mamaki. Da fara’a a muryarshi yace:

“Eh Momma muna tare har da Lukman fa. Haneef ya ce sai jibi za mu tafi gida har da ku.”

Ɗan jim ta yi da alama tana tauna maganar Fu’ad kafin tace:

“Please banda rigima. Ka zauna tare da Haneef throughout kana ji na?”

Sai da ya tabbatar mata zai kiyaye sannan suka yi sallama. A mota yake zaune yana cin burger.

Su Haneef na wajen zaman makokin. Ba ma su gayyace shi ba.

Wayar shi ta hau ruri. Fa’iza ce ya ɗaga yana faɗin:

“Sis… “

“Bro namu mu kaɗai. Ka ga white rice suke dafawa a cikin gidan nan….”

Kafin ta ƙarasa maganar yace:

“Ki fito ki duba za ki ga baƙar Range ɗina. Ina ciki.”

Bai jira amsarta ba ya kashe wayarshi. Yana nan zaune Fa’iza ta fito. Leda ɗaya ya bata. Ta juya abinta. Kulle motar ya yi ya fito ba tare da ya san inda za shi ba.

Headphones ɗin shi ya kunna waƙar Drake- child’s play. Ya ci gaba da tafiya zuciyarshi na masa jagora. Don ba ma ya kula da inda yake saka ƙafar shi. Gaba ɗaya tunaninshi yana wani waje da bai san ko ina bane. Kanshi a ƙasa; hannuwanshi na cikin aljihun hoodie ɗin da ya ɗora da za su fito bawai don kare sanyi ba. Don gayu kawai. Sai ganin shi ya yi tsaye a ƙofar gidan su Safiyya. Ya rasa yadda akai ya zo wajen da kuma abinda yake yi.

Kallon ƙofar gidan yake yi. Zuciyarshi na masa wani iri. Juyawa ya yi da niyyar tafiya.

Kamar daga sama ya ji muryar Safiyya tace:

“Usman ka ce Lami ta jira ni. Yanzun zan fito.”

Bai san lokacin da ya juya ba. Ita ce a tsaye. Banbancin ta da mafarkin shi hijab da take sanye da shi a jikin ta. Kwalliyar fuskarta na nan. Muryar iri ɗaya ce.

“WTF…….”

Ya faɗa sakamakon jin yadda zuciyarshi ta yi wani squeezing. Kallonta yake kamar ba shi da wani muhimmin abu da zai yi bayan hakan.

*****

Safiyya ta riga da ta san Lami na iya ƙin jiranta. Jin da ta yi jikinta cewar ana kallonta ya sa ta juyowa in da Fu’ad yake tsaye kamar an dasa shi. Idanuwanta ta sauke cikin nashin nan da suka yi mata tsaye a rai. Ta kasa manta komai nashi. Zuciyarta ta ji tana ta bugawa. Ta haɗiye wani abu da ta ji ya tsaya mata a maƙoshi.

Mai shanu ta hango yanata faman yi wa Fu’ad ihun ya kauce daga kan hanya amma ga dukkan alamu bai ma san yana yi ba.

“Kauce daga hanya zai wuce!”

Ta faɗi da ƙarfi. Fu’ad ya wani yamutsa fuska da dukkan alamu bai fahimta da shi take magana ko da wani ba.

Hannu ya ji a saman kafaɗar shi an ture shi gefe a fusace ana faɗin:

“Kurma ne kai ko me? Ana ta magana wa zaka kawo ma tsagerancin ku na zamani?”

Kafaɗar shi ya kalla. Sawun hannun mutumin ya fito da dauɗar da bai san ko ta mece ce ba a jikin farar hoodie ɗin shi. Headphones ɗin shi ya cire daga kunnuwa ya taka wajen mutumin da ya tabbata ya girmi Anty Fatima.

“Wawan ina ne kai da za ka ɗauki ƙazamin hannunka ka ɗora akan kafaɗata?”

Da bala’in mamaki mutumin yake kallon Fu’ad.

“Yaro rashin kunya za kai min?  Ɗan gidan uban waye kai da ba ka san…….. “

Fu’ad bai bari ya ƙarasa ba ya ɗauke shi da mari. Babu ƙaramin da zai zagi Abba. Saffiyya ba ta san sanda ta ƙaraso wajen ba da sauri. Hannu ta ɗaga ta wanke ma Fu’ad fuska da yatsunta biyar.

Kallon shi take tana gefen mutumin da ya mara.

“Safiyya?”

Mutumin ya kira da alamun tambaya a muryarshi.

Tata muryar na rawa tace:

“Kawu ka barni. Akan me shi ne da laifi bai ga girman ka ba zai ɗaga hannu ya mareka?”

*****

Fu’ad hannu ya sa ya taɓa kuncin shi. Ya sake shafawa ya dawo da hannun shi ya kalla. Sannan ya sake kallon Safiyya da ke tsaye a gefen mutumin da ya ji ta kira da kawu. Ƙwaƙwalwar shi ta kasa tauna abinda ya faru. Zuciyar shi ta kasa yarda da cewa abubuwa biyu ne suka faru dashi.

Wani ƙazamin talaka mai ɗauke da dauɗa ya zagi Abba. Wata kucakar ‘yar ƙauye ta ɗaga hannuwanta a mare shi.

“Marina ki ka yi?”

Yake tambayar kanshi fiye da yadda yake tambayar Safiyya. So yake wani ya tabbatar mishi da gaske abin ya faru. Can nesa yake jin muryar Safiyya da ke cike da rauni na faɗin:

“Eh marinka na yi.”

Kalar ashar ɗin da zai sa ko bamaguje yake wajen kunya ta lulluɓe shi ya yi. Lokaci ɗaya idanuwan shi suka rine saboda ɓacin rai. Ɗagowa ya yi ya sauke idanuwan shi cikin na Safiyya.

*****

Idanuwanshi take kallo. Lokaci ɗaya duk wani abinda ke motsi a jikinta yake fahimtar kuskuren da ta aikata. Bata san lokacin da ta matsa bayan kawunta ba. Har lokacin idanuwanta na cikin nashi.

Girgiza masa kai take. So take da wannan alamar kawai ya karanci yadda take da na sanin abinda ta aikata. Shi kanshi kawunta kallon Fu’ad yake. Ga dukkan alamu yaro ne mai ƙarancin shekaru.

Sai dai a yanzun akwai wani abu tattare da yanayin shi da shi kanshi ya tsorata. Akwai wata isa da tsayuwarshi da fuskarshi kawai ta nuna su.

*****

Takawa yake yi a hankali kamar mai tafiya akan ɓawon ƙwai. Yana kallon yadda jikin Safiyya ke kyarma. Ta riƙe rigar kawunta kamar za ta koma cikin shi.

Hannu kawunta ya ɗago yana shirin tare Fu’ad. Muryarshi a dake can ƙasa yace:

“Kuskure na uku da za ka aikata shi ne barin hannunka ya ƙaraso ya taɓa ko da rigata ne.”

Da alamu kawu ya karanci gaskiya a maganar Fu’ad, don haka ya maida hannunshi inda ya kamata ya tsaya. Ƙarasawa ya yi daf da Safiyya da ta kasa sauke idanuwanta daga cikin nashi.

Ko me yake ji akanta. Ko me yake tunanin akwai a cikin idanuwanta. Abinda ta aikata ya girme shi.

Ko wanda yake so yakan nuna masa kuskurensa in har ya mishi ballantana ita da basu haɗa komai ba. A’a, ganinshi na biyu kenan da ita akwai abinda suka haɗa da bai fahimta ba ba kuma ya son fahimta.

“You gonna’ regret this. Ba ke kaɗai ba, gaba ɗaya dangin ku…

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×