Skip to content

Akan So | Babi Na Hudu

0
(0)

<< Previous

20 February 2017

Wani irin ciwo kanta yake mata da take da tabbacin yana da alaƙa da kukan da ta yi. Sai yau ta tabbatar rashin sanin ranar mutuwarka ba ƙaramar rahma bace. Ba ranar mutuwar Nana aka gaya mata ba, amma ji take yi kamar an yi yaƙin duniya na farko da zuciyarta.

Ko’ina a jikinta ciwuka ne da take da tabbacin ko da sun warke, tabonsu zai kasance da raɗaɗi har ƙarshen rayuwarta. Tana nan falo kwance, Nana ta dawo daga makaranta. Ita take ɗauko ta. Text ɗin da Ansar ya yi mata cewar ta huta zai je ya ɗauko Nana ɗin ne ya sa ta yi zamanta. Wani gajeren murmushi ta ɗora a saman fuskata sannan ta miƙe zaune tana amsa sallamar Nana. Tana kallonta ta cire takalminta sannan ta ƙaraso inda Sofi take zaune.

“Mummy kin ga Uncle Tunde wai a test ɗin Maths ne na ci 9.5 cikin 10. Kuma ni na san na cinye duka 10 ɗin.” Cewar Nana da ke cire Hijab ɗinta da jaka tana ajiyewa gefe. Wannan karon murmushin da Sofi ta yi ba iya fuskarta ya tsaya ba, har cikin zuciyarta. Kallon Nana take a ranta tana lissafa tsawon watannin da suke da shi tare. A fili kuma tace:

“Ban da abinki Nana, Ai kinci da, yawa.” Cikin idanuwa ta kalli Sofi hakan ya sa zuciyarta wani kai-kawo a ƙirjinta. Da wani yanayi a muryarta tace:

“Mummy me ke damunki?”

Murmushinta ta faɗaɗa, don ta san Nana. Yadda yarinyar ke karantarta har mamaki yake bata.

Maimakon ta amsa mata tambayarta sai ta ce: “Tashi ki sake uniform.” Babu musu ta miƙe. Har ta tafi ta dawo.

“Me Aunty Jana ta ce, Mummy?”

Kamar yadda take kiran likitar tata da a shekaru biyu da fara rashin lafiyarta suka yi wani irin shaƙuwa.

Wani abu Sofi ta ji ya zo ya tsaya mata a maƙoshi. Ta ina zata fara faɗa wa ‘yarta da ba ta ƙarasa ko cika shekaru goma sha ɗaya ba cewar babu tabbacin samun sauƙi a ciwonta? Wani kasalallen murmushi Nana ta yi, wanda ke fassara damuwa.

losing hope.

Koma me murmushin yake ɗauke da shi, ya taɓa zuciyar Sofi, don ba ta san lokacin da hawaye suka fara zubo mata ba. Ƙarasawa Nana ta yi ta zauna kusa da ita. riƙe ta Sofi ta yi tana wani kuka marar sauti. Hawaye Nana ta shiga goge mata tana faɗin:

“Mummy ki daina kuka. Ni bana jin tsoro. Kawai ina so in ga M ne.” Sake riƙeta ta yi. Tunda ta fara wayau take kiran sunan shi da M kawai. Sofi ta yi, ta yi, ta ce in ta yi ƙoƙarin claiming wani dangantaka tsakaninsu da shi zai ƙi dawowa.

Hakan kawai na sake tsaya wa Nana a rai. Saboda ta san laifinta wajen taimakon rashin babanta a kusa da ita. Don haka, ba ta sake ƙoƙarin hana ta kiranshi duk yanda take so ba.

Da ƙyar ta samu ta ɗan nutsu. Ta sa hannu tana goge fuskarta.

“Mumny please kada ki ce a’a, ba zan iya ba. Ina son magana da ‘yan jaridar da suke bakin school kullum.” Kai kawai Sofi ta iya ɗaga mata, alamar ta yarda. Don magana ta maƙale mata. Rungumeta Nana ta yi da wani murmushi a fuskarta tare da faɗin:

“I love you so much Mummy.”

Shirun dai shi Sofi ta yi, har Nana ta tashi daga jikinta ta ruga zuwa ɗakin ta. Ƙafafuwanta ta ɗora akan kujera ta haɗe kanta da gwiwa ta sake sakin wani irin sabon kuka. Nana ce kaɗai hope a gare ta, ita ce ƙwarin gwiwarta kuma dalilinta na farin ciki. Nana ce kaɗai adalcin da ta samu a rayuwarta. Ga ƙaddara da ba za ta kautu ba na shirin rabasu.

*****

21 February 2017

A irin tuƙin da yake yi Allah ne kaɗai ya kai shi ƙofar gidan yayan shi lafiya. Din shi kan shi Nawaf zai iya rantsewa ko hanya ba ya gani. Wani irin duhu yake gani cikin kanshi. Zaɓi ɗaya yake da shi ban da gidan yayan shi. Shi ne club. Sai dai duhun da yake ji bai fi ƙarfin alƙawarin da ya yi wa Nuri ba. Ya ga alama ita ce sanadin shiryuwarshi, kuma ita za ta sake zama sanadin komawarshi ruwa.

Matakan nutsuwarshi har yanzun kokawa suke ta gaske da na rashin nutsuwar. Fitowa ya yi ko motar bai rufe ba  da gudu-gudu ya ƙarasa shiga gidan yana kiran:

“Yaya!”

Jidderh da take kitchen tana girki ta ji kiran ba na lafiya bane ta fito a tsorace. Kallo ɗaya ta yi wa Nawaf da yake tsaye hannu ɗaya kan ƙugu ɗayan kuma cikin sumar shi, ta karanci damuwa ƙarara a tare da shi. Dn haka bata kula shi ba ta hau sama da hanzari. Ko sallama ba ta yi ba ta tura ɗakin Ibrahim da yake zaune yana ayyuka da laptop ɗin shi.

“Dear ga Nawaf ya… “

Bata karasa ba ya miƙe da hanzari. Ya san abin da zai kawo Nawaf gidan shi da wannan lokacin ba ƙarami bane. Hanyar waje ya nufa, Jidderh za ta bi bayanshi ya yi mata alama da hannu da ta dakata. Ba ta yi musu ba. Don in zata faɗi gaskiya, yanayin Nawaf kawai tsoro yake bata.

*****

Yana ganin saukowar T.J bai jira ba ya ƙarasa in da yake.

“Yaya Nuri. Nuri tana so ta kashe ni. Yaya ba zan iya ba fa.” Ganin yadda ko’ina na jikin Nawaf ke kyarma ya sa T.J kama shi ya ja shi zuwa tsakiyar falon. Kan kujera ya zaunar da shi kamar wani ƙaramin yaro. Ya koma da gudu kitchen ya ɗebo ruwa ya fito.

Nawaf ya miƙa wa tare da faɗin: “Calm down. Sha ruwa sai mu yi magana.”Cike da kulawa. Babu musu Nawaf ya karɓi ruwan ya shanye yana mayar da numfashi cikin ƙoƙarin son samun nutsuwa daga halin da yake ciki.

“Yaya hira fa muke. Ina ba ta labarin Mexico. Nine a gabanta. Amman Farhan ya zo mata a rai tana gayamun yana son garin…… “

Dafe kai T.J ya yi. Dole ya yi magana da Nuri yake tunani. Ya nutsar da hankalinshi kan Nawaf da cewa:

“Calm down, for goodness sake Nawaf. She is yours. Taka kai kaɗai. Din ta tuna Farhan ba wani abu bane da zaka ɗaga hankalinka and……… “

Bai jira ya ƙarasa ba ya miƙe da hanzari ya nufi hanyar waje. Bin shi T.J ya yi  ya riƙo hannun shi yana faɗin:

“Ina kuma za ka je?”

Lumshe idanuwanshi ya yi, ya buɗe su sannan yace:

“Na faɗa maka matsalata kana nunamun ba komai bane. I beat her up Yaya!”

Sakin shi T.J ya yi tare da alamun kaɗuwa a fuskarshi. Ya girgiza kai.

“No, Nawaf. Kar ka faɗa min ka daki Nuri.”

Zafin da zuciyar Nawaf ke yi ya ji ya ƙaru. Shi kan shi ya san baya kyautawa. A ranar da ya fara dukan Nuri mari ne kawai. Daga ɗaya zuwa biyu. Wani abu yake ji cikin kanshi da ba ya iya controlling. Yau ya dake ta sosai.

Da ba ta ruga ta kulle ɗaki ba. Zai mata wanda ya fi wannan. Muryarshi na rawa yace:

“Yaya, please help me. Ba zan iya rasa Nuri ba. Wallahi ba zan iya rasa ta ba yaya.” Hannunshi T.J ya ja yana fadin:

“Zo ka huta sai muje gidan tare.”

*****

Tunda ta koma aiki ta je ta duba Ikram a ɗakin ta, ta ganta zaune ma tana karatun Qur’ani. Ja mata ɗakin ta yi. Fushi suke mata daga ita har babanta. Da lafiya ma Ikram ba mai yawan magana bace. Shi kanshi Jabir ɗin share shi ta yi. Don sam bata son rikicin. Nana ce tsaye a ranta da tunanikan rayuwa da dama.

Tana yin sallar Isha’i ko takan abinci ba ta bi ba. Ta dai fita ne ta kammala yaranta ta sa sunyi addu’a itama ta yi musu. Tana dawowa ɗakinsu ta saka rigar bacci ta kwanta abinta. Tana jin Jabir ya hauro kan gadon. Riƙo ta ya yi jikinshi ta sauke wani numfashi.

Juyowa ta yi ta fuskance shi. Idanuwanshi kawai ta kalla taga gajiyar dake cikinsu. Wata gajeriyar sumba ya manna mata tare da faɗin:

“Na yi kewarki.”

Murmushi ta yi mishi.

“Nima haka. Na yi kewarka sosai, na kira ka ɗazu ba ka ɗauka ba.”

Ya wani langaɓar da kai.

“Ke da kika dawo aiki ba ki ko bi ta kaina ba. “

Ƙara matsawa ta yi jikinshi sosai. Ba ta da amsar tambayar shi, don haka ta yi shiru. Rungumeta ya yi sosai. Cikin kunnenta yace:

“Jana, ki bar aikin nan. Please, ki barshi.”

“Honey J, ba ka da matsala da aikina a duk shekarun nan.  Me ya canza a cikin wata ɗaya? Menene nake maka da, da bana maka yanzun?”

Sai da ya sumbace ta sosai sannan yace:

“Mubar maganar nan for now. Bana son yin faɗan.”

Ɗaga mishi kai ta yi tare da faɗin:

“I love you.”

“I love you more.”

Ya faɗi ya lalubi switch ɗin ɗakin ya kashe kafin ya janyota suka soma raya darensu cikin ƙauna da son juna.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×