Skip to content

Akan So | Babi Na Sha Biyu

0
(0)

Karanta Babi Na Sha Daya.

“Wani ya sake trying mun lambar  Fu’ad please.”

Haneef ya faɗa muryarshi a gajiye. Sun kai mintina wajen talatin suna neman wayar Fu’ad a kashe. Lukman na shirin sake dialing kira ya shigo.

“Hamza ne…”

Yace yana ɗaga wa da faɗin, “Hello ina jinka Hamza.”

Wani numfashi Hamza ya sauke sannan yace, “Please kar ka faɗa wa Fu’ad, promise me sunana ba zai fito ba cikin maganar nan.”

A ƙagauce Lukman yace, “Wallahi ba zai taɓa jin daga bakinka maganar ta fito ba. Trust me nasan Fu’ad, ba zan so in saka ka cikin rikici da shi ba.”

Sai da ya ɗan tauna maganar jim sannan ya nisa yace,

“Ya sani na ɗauko masa ‘Yansanda har mota uku. To be frank ban san abinda zai yi da su kenan ba. Yasa an tattara wata yarinya da alhalin ta sun kai su sha biyu. Yanzun haka muna Dawanau. Mun kusan shiga cikin gari. Please ku zo abin is getting out of hand. Akwai yara ƙanana.”

Haneef Lukman ya kalla. Jikin shi ko ina ɓari yake yi.

“Wallahi Fu’ad ne Haneef…” Abinda Hamza ya faɗa masa ya maimaita musu. Daga Haneef har Fa’iza salati kawai suke yi.

“Wallahi ban san inda Fu’ad ya kwaso wannan halayyar tashi ba. Babban yaya na da zafi amma ba irin wannan ba.”

Cewar Haneef da yake jin kamar ya juya ya koma wajen zaman makokin shi. Ya gaji da halin Fu’ad da rigingimun shi. Shi ya sa har ba ya so yace zai zo. In yana can ƙasar waje hankalinsu kwance yake. Daga Fa’iza har Lukman sun kasa cewa komai. Mumynsu kawai ta yi wa text cewan tana tare dasu Haneef za su je gida su dawo.

*****

Suna zuwa Police Station ɗin ya tabbatar an tura su cell an kulle gaba ɗayan su. Aka ɗauki statement ɗin shi cewar yana filing charges akan assault. Ya shiga motarshi ya tafi gida abin shi.

Alwala ya ɗaura ya fito ya tafi masallaci ya yi sallar magriba sannan ya dawo. Bai bi takan wayarshi ba. Yana sane ya kashe ta don ba ya son su Haneef su dame shi. Mota ya koma ya ɗauko sauran burger ɗin shi da pizza ya dawo babban falo ya kunna T.V yana kallon Aljazeera Sport.

Kallo ɗaya za ka yi masa ka gane idanuwanshi ne kawai akan T.V ɗin. Sam hankalin shi na wani waje daban.

A lokuta da dama in ya yi rashin mutunci irin wannan yana ba shi wani satisfaction na daban.

Yana jin cewar ya isa. Yana jin cewar an masa ya rama. Sannan ɓacin ran yakan guje daga zuciyar shi. Da ƙyar ya ƙarasa tura burger ɗin ya bi da fresh milk saboda ya san jikin shi na buƙatar abinci.

Yana saurin burning calories. Amman yau bayajin yunwar sam. Ga zuciyarshi ta mishi wani iri.

Jikin kujerar ya koma ya kwanta sosai. Ya lumshe idanuwan shi. Ba abinda ke masa yawo sai fuskar Safiyya da kalar kukan da take yi.

Bai san dalilin da zai sa hakan ya dame shi ba. Kukan ya tsaya masa a rai. Yanayin da yake ji baƙon abune a wajen shi.

*****

Ba yadda Haneef bai yi ba da ‘Yansanda su saki su Safiyya amma suka ƙi sauraron shi.

Sun kuma tabbatar masa in ba Fu’ad bane ya janye case ɗin da kanshi ko beli ba za su bayar ba.

Kallon su Safiyya yake da suke rakuɓe cikin cell ɗin mata suna ta kuka. Ɗayan cell ɗin kuma maza ne ciki matasa guda biyu duk za su kai sa’annin Haneef ɗin. Sai  magidanta. Haneef ya gane ɗayan magidancin shi ne wanda suka yi karo da ɗan shi a safiyar ranar.

Ranshi ɓace yace ws Lukman, “Mu je gida kawai. Na san Fu’ad na can.”

Jiki a sanyaye Lukman ya bi shi suka samu Fa’iza zaune cikin mota inda suka bar ta.

*****

Suna parking motar Haneef ya buɗe ya fita. Ko rufe murfin motar bai yi ba saboda ran shi a ɓace yake. Ko sallama bai yi ba ya shiga gidan.  A falo ya ga Fu’ad a zaune jikin kujera ya rufe idanuwanshi.

Wani irin kallo yake masa mai cike da fassarori daban-daban. In akwai abinda ya tsana a duniya bai wuce wulaƙanta dan Adam ba.

“Fu’ad…”

Ya kira muryarshi can ƙasa. Sai a lokacin ya ɗago ya sauke idanuwanshi da suka yi wani duhu akan fuskar Haneef.

“Yanzun nan za ka kira ka sa a sake su. Ba na buƙatar jin me ya haɗaku. I want them out of that hell hole.”

Kallon Haneef kawai yake yi. Ya ɗauke idanuwanshi zuwa kan su Fa’iza da Lukman da suka shigo ɗakin da sallama. Lukman ya ƙarasa inda yake ya zauna. Muryarshi a sanyaye yace, “Fu’ad ban san me ke damunka ba. Me yake… “

Katse shi ya yi da faɗin, “Cut it please.”

Miƙewa tsaye ya yi ya kalli Haneef da har wani huci yake yi. A hankali ya ƙarasa dab da shi. Cikin fuska ya kalle shi yace,

“Ka fita daga maganar nan. Babu ruwanka. “

“Wallahi wannan karon Abba zan faɗa wa. Waɗannan mugayen halayen naka nagajiy da ɓoye su. Din kana da kuɗi sai ya zama mene ne? Abbah ba shi da kuɗi?  Wa ka ga ya taɓa wulakantawa?”

A tsawace Fu’ad yace, “Saboda me za ta sa hannu ta mareni?  Wallahi sai marina ya fita a jikin gaba ɗaya ‘yan gidansu.”

Fa’iza da ke gefe tace, “What? Mari?  Wa ya mare ka bro?”

Hankalin shi ya maida kan Fa’iza yace, “Wata kucakar ‘yar ƙauye. Ta ɗaga ƙazamin hannunta ta mare ni.”

Rai a ɓace Fa’iza tace, “Ashe ma su ne da laifi. Waye uban ta da za ta ɗaga hannu ta mare ka?”

Kallon Haneef ya yi da ke fassara ‘ka ga ita ta gane karatun. Saura kai.’

Muryar Haneef can ƙasa yace, “Ba na son jin me ya haɗa ku. Kawai ina son ka sa a sake su ne.”

Kai yake girgiza masa alamar abinda ba zai yiwu bane kafin yace, “Yadda ta mare ni sai na wulaƙanta su sai… “

Mari Haneef ya ɗauke shi da shi wanda ya sa iskar da ke ɗakin kanta ta tsaya. Hannu ya kai kan kumatun shi cike da mamaki. Fa’iza ta riƙe baki. Lukman kan shi bai taɓa zaton Haneef zai iya marin Fu’ad ba.

Cikin bacine rai yace, “Kai har ka isa ka wulaƙanta wani? Me kake da shi?  Nawa ne a account ɗinka?  Yaushe su Abba suka gama ɗaukar ɗawainiyarka? Fu’ad ka yi hankali da duniya wallahi.”

Idanuwan shi cike da wasu hawaye da ya ƙi bari su zubo. Hannun shi har lokacin yana kan kuncin shi. Tun yarinta ya fi shaƙuwa da Haneef fiye da kowa. Duk wata rashin kunya. Duk wata fitsara da zai yi Haneef na shanye wa. Babban hukuncin da zai masa shine ya ƙi kula shi. Ko faɗa ba ko yaushe Haneef yake iya mishi ba.

Haneef ya sha haɗa kuɗin break ɗin shi na makaranta ya bar wa Fu’ad saboda ya yi mita nashi sun mishi kaɗan.

Yau Haneef ɗin nan ne ya mare shi saboda wasu talakawa. Ba akan wani abu ba akan ‘yan ƙauye.

Wani ɗaci yake ji a zuciyar shi. Tunda yake duniya bai san ciwon wani abu ba irin na yanzun.

Bai ma taɓa zaton akwai ranar da zai ji son zubda hawaye akan ɓacin rai irin na yanzun ba.

Bai ce komai ba ya sa hannu ya zaro wayarshi daga aljihu. Ya kunna ta. Lambar Sifetan da ya yi saving ɗazun ya yi dialing. Ringing ɗaya ya ɗauka.

“Na yi dropping charges ɗin gaba ɗaya. A sake su.”

Bai ma jira amsar da zai bashi ba ya kashe wayar shi. Kusa da Haneef da ke tsaye yana kallon shi ya ƙarasa. Sai da ya sa idanuwanshi cikin nashi yace,

“Ba ka yi ƙarya ba. Ina alfahari da abinda na tara. Saboda ka fi kowa sanin baƙar wahalar da na sha kafin in je inda nake a yanzun.

Ka fi kowa sanin clubs da adadin wasannin da na yi playing. Kana tare dani a duk zaman asibitin da na yi in na samu ciwuka. Kana tare da ni lokacin da na fara wasa da Kano Pillars. Kana tare da ni lokacin da Mack ya fahimci zan iya zama wani abu. Kana tare da ni a duk wata wahala tawa. Yau kai ne ka ɗaga hannu ka mare ni akan wasu banzaye. Yau kai ne hannunka ya taɓa fuska ta saboda an ci zarafina na yi ƙoƙarin ramawa.”

Wani numfashi Fu’ad ya ɗauka kafin ya juya da gudu ya hau benen zuwa ɗakin shi. Suna jin ƙarar datso ƙofar da ya yi kamar mai son karyata. Lukman ya tashi ya bishi. Wani irin kallo Fa’iza take wa Haneef da ke nuna rashin jin daɗin abinda ya yi.

Muryarshi can ƙasa ya ce mata, “What is with the look?”

Kallon shi ta yi cikin fuska, “Wata ta mare shi ka bar shi ya ji da abu ɗaya. Ba sai ka ƙara mishi ba. Na yarda yana da halaye marasa kyau. But he is our brother. Na ɗauka ‘yan uwa suna goyon bayan ‘yan uwansu ne…”

Hannu Haneef ya ɗaga mata alamar ta yi masa shiru. Sai da ta kalle shi na tsawon mintina biyu sannan ta wuce abinta. Kujera ya samu ya zauna ya dafe kanshi da hannuwa biyu don bai san me ya kamata ya yi ba.

*****

“Kukan nan ya isa haka Safiyya.” Inna ke faɗi ta ɗora da, “Ki je ki kwanta kin ji. Komai ya zo ƙarshe ai.”

Cikin kuka Safiyya tace, “Duk ni na ja muku Inna duk… “

Baba ne ya katse ta da fadin, “Ba ki yi laifi ba safiyya. Nama ga haƙurin Yunusa da bai yi masa komai ba; Ko da yake duniya ce ta fi bagaruwa jima.”

Tashi Safiyya ta yi ta koma ɗakin su ta shimfiɗa tabarmar ta da zannuwa ta sa pillow ta kwanta.

Wani abu ya tsaya mata a wuya. A ɓangare daban tana jin tsanar Fu’ad. A wani ɓangare kuma ɗauke da yanayin da bata san fassarar shi ba.

Washegari

Jikinta babu ƙarfi ta gama ayyukan gidan tsaf. Ta ja ruwa ta yi wanka. Haka ta sha tsuran ruwan koko saboda sam ba ta jin daɗin komai. Jikinta sai ka ce wadda zazzaɓi ke shirin kamawa.

Usman ne ya shigo ya kalle ta yace, “Yaya Ado na kira. Yana waje.”

Ji ta yi yanayin da take ji ya ƙaru. Kallonta ta kai kan Inna da ta kafeta da idanuwa. Ta san fassarar kallon, ta sauke numfashi ta ce wa Usman, “Ka ce gani nan zuwa.”

Hijab ɗinta ta ɗauka. Fuskarta a daƙune ta fita. Da ƙyar ta iya mishi sallama. Yana ganinta ya wani wangale baki.

“Amarya ta nan da wata uku in shaa Allah.”

Ado ya faɗa yana ƙara faɗaɗa murmushin shi. Abinda ke tsaye wuyanta ta ji ya ƙara girma.

Ta san ko sauran kwanaki nawa aurensu ba sa ya tuna mata da bakin shi ba. Har yanzun tana jimamin yadda za ta zauna da ado a matsayin miji bayan ba ta son shi ko kaɗan. Ko fara’a take in ta ganshi sai ta ji ranta ya ɓaci. Babu yadda za ta yi ne kawai. Da ƙyar ta ce masa, “Lafiya dai ko?”

Ya girgiza kai yace, “Lafiya ƙalau. Baba ne yake faɗa min ashe wani tsautsayi ya faɗa gida kuma. Shi ne na ce bari kafin in wuce gona in biyo in muku jaje.”

“Allah Sarki. Ai kam mun gode sosai. Bari in shiga in faɗa wa Inna sai ka shigo ku gaisa ko?”

Safiyya ta faɗa sannan ta koma cikin gida ba tare da ta jira amsar shi ba. Ba ta jima ba ta fito ta ce masa ya shigo. Cikin fara’a da mutunci suka gaisa da Inna ya yi musu jaje. Da zai tafi ya kawo dubu ɗaya ya ba Inna wanda da ƙyar ma ta karɓa.

*****

Safiyya ita ce yarinya ta biyu cikin ‘yaya uku kacal da Malam Audu da Zainabu suka mallaka a duniya.

Kasancewar duk yaran da suka haifa har huɗu ba sa shige kwana arba’in a duniya Allah ke karɓar abinsa. Sai akan Saminu da shi ne babba a yanzun. Sai Safiyya sai Usman. Daga Malam Audu har Zainabu duk ‘yan nan asalin garin Bichi ne.  Mutanene masu karamci da gudun rikici. Talakawa ne sosai sai dai Allah ya azurta su da wadatar zuci. Duk ‘yan uwan Malam Audu sun ɗan fi shi ɗan abin hannu.

Don shi gonar shi ɗaya ‘yar ƙarama. Ita yake nomawa yake rufa wa kanshi asiri. Sai dai bai taɓa damuwa da halin rashi da yake fama da shi ba. Haka rayuwarsu take tafiya. Saminu kuwa, Yunusa ƙanin Malam Audu ya samu ‘yan kuɗi ya siya mishi babur na hannu yake acaɓa da shi. Hakan ba ƙaramin rage wa Malam Audu wahalhalu ya yi ba. Domin yanzun haka saminu shi ya biya wa kanshi kuɗin jarabawar aji shida ta sakandire. Kuma yake ɗaukar ɗawainiyar karatun Usman. Duk da saka mata a makarantar boko ba damuwar zuri’ar su Malam Audu ya yi ba. Hakan bai hana shi  saka Safiyya a makaranta ba. Lokacin da ta zo aji uku ta yi jarabawa ba ta ci ba.

Hakan ba ƙaramin damunta ya yi ba, don har ranta tana da kwaɗayin karatu. Lokacin Ado ɗan mai unguwar su ya fara zuwa wajenta. Kasancewar ya fito daga gida na mutunci ga shi yaro mai hankali da girmama mutane, kuma har ya fara ginin shi.

Manyan shi na zuwa da maganar neman auren Safiyya Malam Audu ya amince. Ba a wani saka abin da nisa ba. Wata huɗu kacal aka saka.

Abinda ba su sani ba shi ne, biyayya ce kawai ta saka Safiyya amsa su lokacin da Malam Audu ya zo da maganar da kuma ƙarin ba ta kula kowa sai ado ɗin. Amman ko kaɗan ba ta jin son shi a ranta. Duk da ba shi da makusa.

Babi Na Sha Uku

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×