Skip to content

Akan So | Babi Na Sha Shida

0
(0)

Karanta Babi Na Sha Biyar.

“Innalillahi wa inna ilahi raji.un…”

Momma ta faɗi bayan Haneef ya gama gaya mata ko me yake faruwa.

“Yanzun duka Fu’ad ɗin nawa yake? Hankalin kirki bashi da shi Haneef.”

Jinjina kai ya yi ya gyara zama yace,

“Na sani Momma. Amma ki kalli fa abinda yake yi. Wallahi zai iya samun matsala. Ni kam dai a taimaka aje a ji.”

“Hmm bayan tozarcin da ya yi musu kana zaton za su saurare mu ne?  Ka fi kowa sanin halin Abbanku. Da wahala yaje.”

Shiru Haneef ya ɗan yi kafin yace,

“In ya ga yadda Fu’ad ke shirin zaucewa zai je. Na san bashi da wani hankalin kirki. Amma wallahi yana sonta. Kema kin ga alama ai.”

“Kai. Oh Allah na!”

Momma ta faɗi tana sauke numfashi. Wannan wace irin ƙaddara ce. Ita tunda take in ba a fim ko a littafi ba. Ba ta taɓa ganin irin wannan abu ba. Ba ma ta san ta yadda za ta fara tunkarar Abba da wannan maganar ba.

“Bari in je in yi Sallah.”

Cewar Haneef yana miƙewa. Kai kawai Momma ta iya ɗaga masa.

*****

Da yammacin ranar Abba ya dawo daga Abuja. Sai da ya ci abinci ya yi wanka ya huta sannan Momma ke faɗa masa Fu’ad bashi da lafiya. Da yake zamansu babu ɓoye-ɓoye a ciki. Za ta iya tunkarar mijinta da kowacce irin damuwa. A nutse ta faɗa mishi komai da yake faruwa. Shi ma salatin yake yana mamakin lokacin da Fu’ad ya zama haka.

“To ni kam ya zanyi maman Fatima. Allah ne yake hora shi.”

Da yake uwa dabance, a tausashe tace,

“Alhaji na sani. Amma sai a duba halin da yake ciki. Ko neman auren yarinyar sai a je masa.”

Girgiza kai ya yi.

“Bayan abinda kika ce ya musu. Kina tunanin ko Fu’ad ya isa aure za su bashi ‘yarsu ne?  Ku rabu da shi kawai. In ya gaji zai haƙura.”

“Allah ya kyauta.”

Ta faɗi tana miƙewa ta fice daga ɗakin. Da alama ranta ya sosu da maganganunshi.

*****

Haneef da Lukman ne zaune a ɗakin Fu’ad. kallon shi kawai suke yi. Don Lukman ma da ba a yi a gabanshi ba a tsorace yake.

Gani suke da sunyi magana zai ƙara shiga matsala. Tunda ya tashi dai bai ce musu komai ba. Suna kallo ya sauko daga kan gado ya nufi hanyar ƙofa. Suka haɗa ido ba su ce masa komai ba. Ƙasa ya sauka ya nufi ɓangaren su Momma. Karo ya ci da ita ta fito ɗakin Abba.

“Momma kin masa magana?”

Ya tambaya. Ta kalli yadda ya wani faɗa ya ƙara haske.

“Na masa magana ka kwantar da hankalinka. Za su je gobe in shaa Allah.”

Wani murmushi ya ji ya ƙwace masa ya sosa kai ya wuce abinshi.

Momma wayarta ta ɗauko ta kira yaya Babba. Da yake dare ya yi ta waya ta yi masa bayanin komai.

Ta ce masa kome yi yake yazo da safe su ƙara tattaunawa.

*****

A gidan Lukman ya kwana. Baccin shi ya sha hankali kwance.

Fu’ad ma ya samu bacci da nutsuwa ta wani ɓangaren tunda Momma ta ce masa za a je a yi maganar auren shi da Safiyya.

Haka ya kwana yana mafarkinta.

*****

Babu yaddda yaya Babba bai yi ba ya fahimtar da mama cewar Fu’ad ɗin ma duka nawa yake. Amma ina, tsakanin ɗa da uwa sai Allah.

Cewa ta yi ma umarni ne ta bashi ba wai neman shawararshi take yi ba. Haka dole ya shirya suka ɗauki hanyar Bichi shi da Haneef.

 ****

Fu’ad ya kasa zaune ya kasa tsaye sai kai kawo yake yi. Ya ƙagu ya ga sun dawo ya ji ya ake ciki.

Gashi jibi zai koma. Lukman ya kalle shi yace,

“Ka soma sakani jiri. Ka zauna waje ɗaya don Allah.”

Dariya ya yi da tunda ya zo Lukman bai ganta ba.

“Ina ruwanka da ni. Wai su Haneef sun yi awa ɗaya da tafiya ko?”

“Ko minti goma ba su yi ba.”

Zaro idanu ya yi.

“Ni bana son ƙarya. Ka sani ko Lukman, Allah ina son ta sosai.”

Dariya Lukman ya yi. Tun jiya yake faɗa musu yana son Safiyya kamar wani cikinsu ya ce ƙarya yake yi.

*****

Lokacin da suka isa Bichi, sai suka aika a yi musu sallama da babansu Safiyya . Aka ce ya je gona. Jin da Inna ta yi sun aiko cewa daga nesa suke kuma magana ce mai muhimmanci ta aika Usman ya kira shi. Cikin soron gidan aka shimfiɗa musu tabarma suka zauna. Har da ruwa aka kawo musu.

Yadda babansu Safiyya ya karɓe su a mutunce za ka rantse dama can ya sansu.

A nutse Babban Yaya ya yi masa bayanin cewar ƙaninsu ya ga ‘yarshi yana so.

Cikin taushin murya yace.

“Allah sarki. Gaskiya mun gode ƙwarai da gaske. Saboda wanda ya nuna ma naka so har abada ya wuce wulaƙanci.

Sai dai kuɗin sadakinta ya kai wata biyu a hannunmu. Yanzun haka bai shige sati huɗu ya rage a ɗaura mata aure ba.

Kuma gashi ba ta da wata ƙanwa ballantana.”

Wani abu Haneef ya ji ya ƙulle a cikin shi. Murya a sake yace:

“Yanzun baba babu yadda za a ɗan duba mana. Wallahi yana sonta matuƙa.”

Murmushi ya yi.

“Ɗan nan ka taɓa ganin inda akai nema cikin nema?  Dama ace ba a amsa su bane.

Mun gode matuƙa.”

Baki Haneef ya buɗe zai sake magana Yaya Babba ya katse shi da faɗin.

“Mun gode muma. Ga wannan. Allah yasa hakan shi ya fi alkhairi.”

Sam Baban su Safiyya ya ƙi karɓar kuɗin da Yaya Babba ya bashi. Da ƙyar da ban baki ya samu ya karɓa. Suka tashi suka tafi.

*****

Tabarmar ya shiga da ita gida. A tsakar gida ya ke nuna ma Inna kuɗin yana labarta mata abinda ya faru. Safiyya da ke ɗaki tana jiyo su. Tana jin baba ya kira sunan Fu’ad zuciyarta ta wani doka. Haɗe kai ta yi da gwiwa. Ba ta san kuma me za ta yi ba. Kukane ta yi shi har ta gode wa Allah.

Wato sai da ya turo neman aurenta gidansu. Taya za ta samu ta manta da shi in har a duk rana yana aikata abinda zai sake zaunar mata da shi.

Kwanciya ta yi tanajin dama ace duk wannan abubuwan sun farune a wani yanayi na daban.

Saurin kulle shafin dake son hango mata rayuwarsu da Fu’ad ta yi. Ta shiga wani na daban.

****

Dama a tsaye yake. Tunda Yaya Babba ya fara wa Momma bayani yake matsawa. Kwata kwata babu wanda ya kula da fitar Fu’ad. Haneef ne yace,

“Ba Fu’ad nan yake tsaye ba.”

Sai lokacin kowa ya kula da ba ya nan. Kallon kallo suke. Da gudu Haneef ya haura sama ya tura ɗakin shi. Ba ya ciki. Sakkowa ya yi ya fita. Motarshi ba ta wajen. Baba mai gadi ya tambaya yace ya fita.

Dawowa ya yi yace musu,

“Mota ya ɗauka.”

“Fara kiran Lukman ka ji ko tare suka fita.”

Wayarshi ya ɗauko ya kira Lukman ya tambaye shi.

“Ina gida wallahi. Bai kuma ce min zai fita ba. Ya Salam!”

Kashe wayar Haneef ya yi ya girgiza wa Momma kai. Cikin tashin hankali tace,

“Oh Allah. Wannan wanne irin abu ne.”

Haneef ya ɗauki mukullin motarshi ya biya ya ɗauki Lukman ba tare da ya san inda za su je nemo shin ba.

Wayarshi yake ta kira sai ringing take ya ƙi ɗauka.

****

Hankalinshi ba ya tare da shi harya ƙarasa Bichi. Yana jin wayarshi na ihu ba shi da lokacinta. So yake yaje ya ga Safiyya ya faɗa mata ba fa za ta auri wani ba.

Inma ba zata aure shi bane ya ji. Inma ba ta sonshi ne duk zai ɗauka. Ba dai zai ɗauki ta auri wanin ba.

Parking ya yi nesa da gidansu ya fito. Ƙofar gidansu ya ƙarasa ya aika yaro a kira mishi ita.

****

Tana kwance abinta. Don ba ta jin za ta iya zuwa Islamiyya ranar. Yaro ya shigo wai ana sallama da ita. Ba ta kawo komai a ranta ba. Zatonta Ado ne. Don yace mata ta duba lambar takalminta ta faɗa mishi ya manta.

Ta ɗauka shi ne ya dawo. Hijabinta ta ɗauka ta zira takalmanta ta fita.

Wani bugawa zuciyarta ta yi ganin Fu’ad. Gefe da gefenta ta kalla ko wani ya taho. Ko ina na jikinta ɓari yake yi.

Muryarta na rawa tace masa,

“Ka tafi kar wani ya ganka. Don Allah ka taimaka ka tafi.”

Kallonta yake yana wani saukar da numfashi.

“In ba kya sona na yarda. In ba za ki aureni ba na yarda. Amma Sofi karki auri wani. Karki auri wani don Allah.”

Ba shi take sauraro ba. Hanya take kallo kar a ganta tsaye da shi.

Kai kawai ta ɗaga mishi…

“Na jika. Ka tafi.”

Ƙaramar wayar rannan ya zaro ya miƙa mata.

“Ki karɓa za muyi magana.”

Kai take girgiza masa alamar a’a.

“Wallahi in ba ki karɓa ba anan zan zauna. Babu inda zan je.”

Rufe idonta ta yi ta buɗe su. Wannan wanne iri ne shi cikin mutane. Ta san zai yi abinda ya faɗa. Jikinta na ɓari ta sa hannu ta karɓi wayar. Ba tare da ta san me za ta yi da ita ba.

“ka tafi to.”

Kallonta ya yi sosai. Wayarshi babba ya zaro daga aljihu. Bai ma tsaya duba yawan kiran da akai masa ba.

Safiyya na kallonshi idanuwa buɗe. Gaba ɗaya a tsorace take. Ba ta san me zai ba ya ɗago wayar idanuwanshi na kan wayar.

Hotuna yake ɗaukarta. Ya san zai buƙace su ko don kwanciyar hankalinshi. Ba ya son tsoron dake cikin idanuwanta sam.

Ji yake kamar ya ɗauketa ya kareta daga dukkan abubuwan dake bayyana wannan firgicin cikin idanuwanta.

Wayar ya damtse a hannunshi ya sauke idanuwanshi cikin nata.

“Ba wannan bane ƙarshe Sofi. Zan dawo. Zan haɗa duniyarmu waje ɗaya. Ban damu da rashin dacewarsu ba…”

Bude baki ta yi ya ɗaga mata hannu.

 “In har ba zaki faɗi abin da zai sama mun sauƙi ba ki yi shiru.

Akwai kalamanki cike da kaina da maganganun da suke mun ciwo. Ba sai kin ƙara musu abokan zama ba.”

Ta nutsu tana kallon fuskarshi. Yadda yake magana. Muryarshi da komai nashi.

Tana kallonshi ne saboda yadda zuciyarta ke mata ba ta son manta shi. Tana son ta ɗauki hotunan shi da za ta adana a zuciyarta.

Yanda take kallonshi yake kallo. Ɗige-ɗigen baƙin da ke fuskarta yake jin kamar ya sa hannu ya gogesu.

So yake ya ganta babu su. Ya ga fuskarta ita ɗin babu ƙari ko ragin komai. Da duk wani abu mai motsi a jikinshi yake jin ciwon tafiyar da zai yi ya barta.

Ya rasa ko menene ke faɗa mishi za ta zama tashi. Yanayi ne ko murya ya kasa fahimta.

Da ƙyar Safiyya ta iya ce masa

“Ka tafi.”

Kai ya ɗaga mata ya soma tafiya da baya a hankali.

 “Idan na kira ki ɗauka.”

Itama kai take ɗaga mishi idanuwanta kafe akanshi. Takunshi a kasa yake yi amma nauyin shi a zuciyarta take ji.

Tana kallonshi har ya juya. Ya sa hannuwanshi cikin aljihu ya tafi.

Jingina ta yi da bangon wajen. Wasu hawaye masu ɗumi suka zubo mata. Ta sa hannu ta goge su tana haɗiye kukanta.

Wayar ta kalla. Ba ta san ya za ta yi da ita ba. Don ma ‘yar ƙarama ce sosai. Za ta iya ɓoye ta a jikinta don ba ta da abinda za ta faɗa in Inna ta gani.

Cikin gida ta koma. Ta ji daɗin yanda Inna ba ta ko dubeta ba. Tana ta tankaɗen garin tuwo.

Ɗaki ta shiga. Ta ɓoye wayar cikin zaninta. Ta haɗa kai da gwiwa tana sauke wani irin numfashi.

*****

Murfin motar ya buɗe daidai ƙarasowar motar Haneef. Parking suka yi. Haneef ya fara fitowa. A fusace yake takowa inda Fu’ad yake.

“Babu hankali a jikinka ne? Inma tahowa za ka yi ba za ka iya gaya ma mutane ba? Haba Fu’ad?”

Tunda ya fara faɗan idanuwa kawai Fu’ad yake binshi da su. Don ba ya jin yana da ƙarfin amsa shi.

Da ya tabbatar ya gama mota kawai ya shiga. Ya rufe ya soma ƙoƙarin juyawa. Haneef ɗin wucewa kawai ya yi ya koma motarsu.

Lukman dama bai kai ga fitowa ba ma. Don bai san me zai ce wa Fu’ad ba. Damuwarshi ɗaya ko wani abu ya same shi a hanya.

Bin bayanshi kawai Haneef ya yi da motar. Amma da yake wani irin gudu yake yi, fintinkau ya yi musu.

“Da na sani na fito na karɓi tuƙin can.”

Cewar Lukman da alamun damuwa a muryarshi.

 “Allah ya kyauta. Dama ya lafiyar kura…..”

Shiru kawai Lukman ya yi.

*****

Duk ranar babu wanda ya yi wa magana. Ko me za ka ce mishi da idanuwa kawai zai bika.

Fuskar nan babu annuri sam. Gara ma Momma da ta tambaye shi ko lafiya yake ya amsa mata da babu abinda ke damun shi.

Sun dai ƙi su bar shi ya zauna shi kaɗai. Dole ya kwanta falo har aka dawo sallar isha’i.

Matsa masan da Momma ta yi da ƙarin ba ya son ko bakinshi ya buɗe ya yi magana ya sa ya tura wa cikinshi doya da ƙwai.

*****

Lukman ya zo gidan wajen ƙarfe tara. Sannan suka yi ɗakin Fu’ad ɗin tare. Kwanciyarshi ya yi yana karatu domin yanada test washegari. Fu’ad kam lambar wayar da ya ba Safiyya ya duba ya danna kira. Zuciyarshi na wani bugawa.

*****

Ƙarin Tauhid ɗin da akai musu ta zauna tana dubawa tunda ta yi sallar isha’i. Wani zu ta ji cikin ƙugunta daidai inda ta ɓoye wayar da Fu’ad ya bata. Da alaman tsarguwa a fuskarta ta ɗago ta sauke dubanta kan Inna.

Hira suke ta yi ita da Baba da alama ma ba su san me ke faruwa ba. Wani numfashi ta sauke ta miƙe.

“Inna sai da safenku. Allah ya bamu alkhairinsa. Usman da yaya sai da safe.”

Su usman suka amsata da amin da yi mata fatan tashi lafiya.

Inna ce tace,

“Ba ki ci abinci ba fa Safiyya. Haka za ki je ki kwanta?”

Girgiza kai ta yi.

“Ai da yammaci na ci abinci Inna. Kin manta. Bana jin yunwa yanzun.”

“To Allah ya tashemu lafiya. Adai yi addu’a.”

Ta amsa da,

“In sha Allah.”

Wayar ba ta daina zuu ɗin da takeyi ba. Ɗaki ta shiga. Ta saki labulen. Can ƙarshe ta koma. Ta ɗauko wayar.

Kallonta take yi . Irin wayar yayanta ce. Sai dai sabunta ta banbanta su. Zuu ɗin da take ta sake ɗauka. Cikin kanta take tunanin yadda ya nuna mata ko da zai tafi gona ko wajen express ɗin shi yabar wayar.

Green ta danna ta kara a kunnenta zuciyarta na wani yawo a wajajen da bai kamata ta je ba.

Za ta iya rantsewa har cikin kunnuwanta tanajin yadda zuciyarta ke bugawa.

*****

Karo na huɗu kenan daya sake dialing lambar. Hannuwanshi har zufa suke da bai san daga inda ta fito ba.

Ji ya yi an ɗaga. Ya sauke wani numfashi da yake riƙe dashi.

“Sofi………”

*****

Lumshe idanuwanta ta yi. Tana jin kamar yana gabanta. Ba ta san me ya sa yake ce mata Sofi ɗin nan ba.

Ba dai za ta ma kanta ƙarya ba. Sunan na mata wani irin abu da ta kasa fahimta. Muryarta can ƙasa tace,

“Sai da safe.”

Kai ya ɗaga kamar tana ganinshi kafin yace,

“Thank you. Thanks for picking. Zan sake kira amman ba da wannan lambar ba. Ki yi bacci mai daɗi, cike da mafarkina.”

Ba ta amsa shi ba ta sauke wayar daga kunnenta. Jikinta ko’ina ɓari yake yi. A hankali ta tashi ta zo wajen ƙofa . Labulen ɗakin ta ɗaga ta leƙa ta ga ko su Inna sun jiyota. Suna nan zaune inda ta bar su.

Komawa ta yi. Ta gyara shimfiɗarta ta kwanta. Cikin kanta take sake dawo da maganganun Fu’ad.

Bama saiya wahalar da kanshi na cewar tai mafarkin shi ba. Ta san abune da yake a ajiye.

*****

Yana nan kwance har Lukman ya fice don yana da test ƙarfe takwas na safiyar ranar. Don haka ya yi wa Fu’ad sallama. Ya san sanda zai dawo ya koma.

Lukman na fita ya yi wanka ya fito ya shirya tsaf. Son jin muryar safiyya na damunshi.

Waya ya ɗauka har ya kai kan lambarta ya fasa ba ya son ta ji kaman ya takurata.

Zai iya lallaɓa zuciyarshi na ɗan wani lokaci. Maimakon haka, sai hotunanta na wayarshi ya buɗe.

Murmushi ya ƙwace masa. Hannu ya sa ya shafi screen ɗin daidai fuskarta. Hakan kawai ya saukar masa da nishaɗi.

Jakarshi yar ta system ya ɗauka. Ya rigada ya zuba komai da yake buƙata a ciki.

Har ya sauka ƙasa da murmushi a fuskarshi. Haneef ya fara karo da shi.

“Wannan murmushin fa?”

Kawai sai ya ji wata ‘yar kunya ta ɗan kama shi.

“Ina kwana…. “

Ya faɗi maimakon amsa tambayar da Haneef ya yi masa. Zaro idanuwa Haneef ya yi.

Gaisuwar da Fu’ad ya yi masa baƙon abu ne a wajen shi. Banda su Momma ba ya gaida kowa.

Ko ya zo ya same su zaune maganarshi ba ta wuce ‘Hey guys’ ko ya kalle ka ya ɗaga maka kai.

Momma ce ta fito kafin ya samu damar tsokanar Fu’ad ɗin. Kallon shi ta yi tace,

“Ba dai tafiya ba?”

Ɗan sosa kai ya yi.

“Wallahi kam. Ina kwana.”

“Lafiya ƙalau… Amman dai ka tsaya ka karya ko? Kana lafiya dai?”

Murmushi ya ƙara faɗaɗawa.

“Lafiya ƙalau Momma. Bana jin yunwa. Zan yi grabbing ko burger ne. Abba fa?”

Kai ta jinjina tace,

“Yana ɗakin shi.”

“Bari in je mu gaisa mu yi sallama to…”

Bai jira amsarsu ba ya wuce. Suna nan tsaye ya fito sukai sallama da Momma. Fa’iza na bacci. Su Hassan kuwa sun tafi makaranta. Don haka Haneef ya tafi ya raka shi.

“I mean are you okay?  About….”

Katse Haneef ya yi da faɗin:

“Absolutely… Ion’ wanna talk bouh’ it.”

Bai sake masa maganar ba har suka kai airport. Sallama suka yi da cewar sai sun yi waya, Haneef ɗin ya juya da mota..!

Babi Na Sha Bakwai

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×