Skip to content

Akan So | Babi Na Talatin Da Bakwai

0
(0)

<< Previous

Sosai ya riƙo Zee jikinshi.

“Na gode sweetheart. Ban taɓa zaton za ki fahimce ni ba.”

Hawayen daya taru a idanuwanta ta ji ya zubo. Ta sa hannu ta goge su. Muryarta can ƙasa ta ce,

“Haba Dee. Da zuciya a ƙirjina fa. Waye zai ƙi fahimtar ka.”

Har cikin ranshi Lukman yake jinta. Bai san wanne kalar so Zainab ke masa ba. Zai iya cewa ya fi kowa dace da mata irinta.

*****

Zaune yake ya haɗa kanshi da gwiwa. Ba zai ce ga iya abinda yake damun shi ba. Komai ciwo yake mishi. Tun daga zuciyarshi. Kanshi da koma ina na jikinshi. Yana jin kamar mota ta bi takanshi, sai dai babu wani ciwo a jikinshi daga waje. Daga ciki yake jin ciwon. Miƙewa ya yi. Zaman nan ba zai mishi ba. Zaman nan ba shi Nana take buƙata ba. Tana buƙatar ya yi setting komai. Ya roƙi yafiyar zunubansa da ta ke biya. Don haka ya miƙe ya ja iska ya fitar da ita ta bakinshi tare da ficewa ya kulle ɗakin yaysa key ɗin a aljihun shi.

*****

Tun da taxi ta ajiye shi a bakin ƙofar gidansu abinda ya yi saura daga zuciyarshi yake wani irin dokawa.

Ga wata zufa har cikin tafin hannun shi. Ko da maigadi ya buɗe masa yake tambayarshi wa ya ke nema. Kallonshi kawai ya yi. Ya rasa me zai ce. Yau shi ake tambaya wa yake nema cikin gidansu. Kalle-kalle yake kamar yaune rana ta farko da ya taɓa shigowa gidan. Komai na nan yadda ya san shi. Wata irin ajiyar zuciya ya sauke ya bar maigadin nan tsaye yana binshi da kallo. Da Alama ya mishi kama da ‘yan gidan shi ya sa ya ƙyale shi.

Da wani nauyi ƙafafuwanshi ke takawa har suka kai shi cikin gidan. Kamar a lokacin ranar da ya bar gidan ya faru haka abin ke masa yawo cikin idanuwa. Komai na ɗakin shi ne banda furnitures. Zai iya rantsewa yana kallon su wani lokaci can baya su duka zaune suna hira.

Wata irin kewar hakan ta saukar mishi. Cikin muryar dabai gane tashi ba ce ya yi sallama. Jin shiru ya sake sa shi ɗaga murya da sake yin sallamar.

*****

Tunda ta dawo gida ta kasa daina zubda ƙwalla. Nana ta tsaya mata a rai ba kaɗan ba. Da ƙyar ta iya samu ta watsa ruwa. Haka Abba ya dawo ya sameta. Shi ma ruwan ya watsa ya ci abinci suka zauna falonsu yana kallon tashar Nat geo. Yana kallon abubuwan al’ajabi. Remote control ɗin da ke hannunshi ya ajiye gefe ya fuskanci Momma da ta yi nisa cikin tunani. Sai da ya yi magana sau uku ba ta ji ba ya taɓa ta.

“Me ke damunki?”

Cikin sanyin murya ta ce,

“Ba ka son jin wannan matsalar na sani.”

Da mamaki ya ce,

“Wane irin magana ne wannan. Abinda ya ke damunki ai yana damuna ne.”

Sauke ajiyar zuciya Momma ta yi. Cikin nutsuwa ta faɗa mishi duk abinda yake faruwa. Lumshe idanuwanshi ya yi yana jin wani irin abu na mishi yawo a zuciya.

Tun ranar da Fu’ad ya sa ƙafa ya bar gidan abin yake manne da zuciyar shi. Ba ya nunawa ne kawai bawai don ba ya damun shi ba.

Ɓacin rai ya sa shi ya yi furucin da ya yiyba wani abu ba. Bai taɓa ɗauka Fu’ad zai tafi ya ƙi waiwayarsu ba. Ya ɗauka abune na ƙaramin lokaci. Zai gane ya yi laifi ya zo ya roƙi gafararsu komai ya wuce. Ya kasa ko da furta ma Momma cewar yana kewar ɗan nashi kamar yanda take yi.

Yana son sake ganin shi ko sau ɗaya ne domin mutuwa ba sallama take ba. Bacin rai duk shi ya hana. Yanzu da take faɗa mishi maganar Nana har ranshi yake jin ɗacin abin.

Ya san bakinshi ne ke ɗawainiya da Fu’ad. Fushin da ya ɗauka ne. Haƙiƙa fushin iyaye babbar musifa ce ga ‘ya’yansu.

“Ba ka ce komai ba.”

Momma ta faɗi muryarta na rawa. Ya kasa kallonta. Idanuwanshi a ƙasa ya ce,

“Ina Fu’ad ɗin yanzun?”

Girgiza mishi kai ta yi,

“Haneef ya ce ya sauka a hotel ne. Ban san kowannene ba.”

Buɗe baki Abba ya yi zai sake magana suka ji sallama. Saurarawa suka yi. Sallamar suka sake ji wannan karon da ɗan ƙarfi.

*****

Fitowa su Momma suka yi tare ita da Abba, don su dukansu sun ji kamar muryar Fu’ad ce. In da ya ɗauka zuciyarshi dokawa take ba komai bane akan yadda yake jinta yanzun. Zai iya cewa su Momma da ke tsaye suna ganin hakan ta cikin rigarshi.

Hannu ya kai wajen ya danna yana ƙoƙarin sai ta zuciyarshi daga dokawar da take yi. Bakin shi na rawa idanuwanshi kafe kan Abba ya ce,

“A…Abbah…”

Kallon shi Abba yake. Ya girma sosai kamar ba Fu’ad ɗin shin nan ba. Ɗan shi daya fi so fiye da kowanne cikin ‘ya’ yanshi ko da ba ya nunawa. Yana kallon Fu’ad ɗin na takowa zuwa inda yake. Ya kasa cewa komai. Kallon shi yake yana tuna tsawon shekarun da suka wuce bai neme su ba. Baisan yadda akai ƙafafuwanshi ke kaishi wajen Abba ba. Zai iya cewa tsantsar ƙaunar shi da yake yi ne a zuciyarshi ke janshi.

Saboda a shekarun nan ya ƙi barin zuciyarshi ta faɗa mishi yadda ya yi kewar Abba. Yana amfani da fushin da yake yi da shi ne yana danne komai. Inda Abba yake ya ƙarasa. Hannuwan Abba ya fara kamawa ya sumbata duka biyun. Wani irin abu ya ke ji yana masa yawo. Bai san lokacin da ƙafafuwanshi suka kasa ɗaukar shi ba. Tsugunnawa ya yi yana sakin hannun Abba. Da duk hannayenshi ya riƙe ƙafafuwan

Abba.

Duk abinda yake daurewa tun ɗazun ne yake dawo mishi. Ciwon da yake ji. Ɗacin da yake ji. Rashin adalcin da rayuwa ke mishi ta kowanne fanni. Bai san lokacin da hawaye suka fara zubar mishi ba. Kan gwiwoyin shi ya koma ya sake riƙe ƙafafuwan Abba dam yana wani irin kuka marar sauti. Gaba ɗaya jikinshi rawa yake. Ko ina na jikinshi ɓari yake. So yake yace Abba ya yafe mishi kalma ko ɗaya taƙi fitowa daga bakinshi. So yake ya faɗa wa Abba yau ya ga wautar da ta aikata. So ya ke ya faɗa mishi yau ya gane amfanin neman shawara. Ya gane irin ƙaunar da suke mishi. Ya gane ba takura mishi suke yi ba. Ya gane irin wannan ranar suke guje mishi. Yana jin Abba ya tsugunno yana riƙo shi da nufin ya ɗago shi daga jikinshi.

Girgiza mishi kai yake. Hawayen har da wanda ya ƙi bari ya zubar lokacin da ya tafi yau sun samu hanya.

Dole sai Abba ya tsugunna, hannuwan Fu’ad ya riƙo muryarshi ɗauke da yanayi na tausayawa da ƙaunar ɗan nashi ya ce,

“Fu’ad ka yi controlling kanka. Sai ka ce mace. Da ƙarfin hali aka san namiji.”

Girgiza kai Fu’ad ya yi. Yana kamo hannuwan Abba ya sa fuskar shi a cikin su. Yau lallashi yake buƙata. Mahaifin shi yake buƙata. Cikin kuka muryarshi na wani irin sarƙewa yake faɗin,

“Abbah na gane soyayyarku mai girma ce a gareni. Wallahi na gane duk wata soyayya ƙasa take da ta iyaye. Abbah ka yafe min. Ka yafe min ko zan samu in ga dai dai a rayuwata…”

Hawaye ya ci gaba da zubdawa yana damtse hannayen Abba kamar ƙaramin yaro. Momma da ke tsaye ita ma ta kasa tarbe nata hawayen. Kallonta Fu’ad ya yi da fuskar shi da har ta kumbura.

“Ku yafe min. Don Allah ku yafe min…”

Muryar Abba na rawa ya ce,

“Na yafe maka Fu’ad. Na yafe maka duniya da lahira.”

Wani irin sanyi ya ke ji yana ratsa shi na daban. Momma ya kalla. Kai kawai take iya ɗaga mishi alamar ita ma ta yafe mishi. Ta daɗe da yafe mishi.

Kallon Abba ya yi sosai. Idanuwanshi na sake cika da wasu hawayen.

“Abba mutuwa za ta yi. Nana za ta mutu. Abba ku taimaka min ita kaɗai nake da a duniya.

Na yi wautar da in ta tafi ba zan sake sanin meye daɗin ɗa ya kalleka cike da ƙauna a idanuwanshi ba.

Bazan sake sanin…Abba.”

Kasa ƙarasawa ya yi yadda yake jin numfashin shi har wani sama-sama yake yi. Da ƙyar Abba ya kamashi ya ja shi kan kujera ya zaunar da shi.

Nasiha ya shiga yi mishi da nuna mishi girman yarda da ƙaddara a musulunce. Jikin Fu’ad ya ƙara yin sanyi.

Momma ta kawo mishi ruwa ya sha. Suna nan zaune aka kira magrib. Ɓangaren Abba Fu’ad ɗin ya bi shi suka yi alwala suka fita masallaci tare.

*****

Tare suka ci abinci a plate ɗaya. Sai dai duk wani motsi da Fu’ad zai yi sai ya sake kallon Abba ya ce,

“Abbah ka yafe min.”

Sai da ya gaji ya ce mishi,

“Fu’ad komai ya wuce. Anan zaka kwana yau. Gobe ka je ka kwaso kayanka ka dawo gida…”

Kai ya jinjina ma Abba alamar ya ji. Wata irin girmamawa ta daban yake jin yana musu. Da wata irin ƙauna da ya san ko rabin wadda suke mishi ba ta kai ba.

Wanda ya haihu ya san meye ɗa ne kawai zai iya sanin girman ƙauna har haka.

Har suka je sallar isha’i da Abba suka dawo. Ɗakin shi tun na da Momma ta ba shi mukullin ya wuce.

Ya yi mamakin ganin ɗakin fes. Komai na nan babu abinda aka canza. Wani irin abu ya ji na daban na masa yawo.

Duk wanda ya ɗauki soyayyar iyaye abin wasa haƙiƙa yana ɗaya daga cikin marasa rabo.

Kwanciya ya yi yana jin sanannen yanayin da ke cikin ɗakin na nutsar da shi. Yau zai huta. Yau zai yi jinyar ciwukanshi. Zai tattara duk wani strength da ya san Nana na buƙata daga wajen shi.

*****

Tunda ta tashi ta zaɓi kayan Nana da ta san ta fi so. Wata doguwar riga ce ta atamfa purple.

Ta ɗauko mata takalmanta da hijab purple. Don sun yi da Yusra za ta zo ƙarfe goma na safiyar ranar don su yi magana da Nana.

Kitchen take tana soya ƙwai Nana ta shigo. Sanye take da riga da wando kanta da hula. Duk ramar da ta yi bai hana Safiyya ganin ta yi mata wani irin kyau da ya taɓa mata zuciya ba.

Kujera ta janyo ta hau sama. Safiyya ta lumshe idanuwa.

“Nana na hanaki tsayuwa kan kujerar nan. Sai kin faɗo ko?”

Dariya ta yi tana leƙa frying pan ɗin da Safiyyar ke soya ƙwai tare da faɗin,

“Na tsaya da kyau ba zan faɗo ba. Mummy in tambayeki?”

Sai da ta juya wainar ƙwan daker ciki sannan ta amsa da,

“Uhum ina jinki.”

Shiru ta ɗan yi na wani lokaci.

“Kin yi alƙawari ba za ki yi kuka ba in na tambaya?”

Wani miyau Safiyya ta haɗiye, don tun kafin ma ta tambaya ɗin ta ji hawaye na taruwa a idanuwanta. Muryarta a sarƙe ta ce,

“Ina jin ki.”

“Mene ne soyayya? Ya ake ji in ana soyayya?”

Cike da mamaki Safiyya ta ce,

“Me yasa kike tambaya?”

“Oh oh Mummy. Karki yi kuka please idan na faɗa miki.”

Jinjina mata kai ta yi. Idanuwa Nana ta ware kan fuskarta tare da faɗin,

“Saboda na san ba zan yi girman da zan san ya ake ji ba shi ya sa nake so ki faɗa min.”

Abun da ke tsaye wuyanta take ta so ta haɗiye ta kasa. Ɗan gyaran murya ta yi tana ƙifta idanuwanta cikin son maida hawayen da ke son zubo mata.

Kettle ta ɗauko ta ɗora musu ruwan zafi sannan ta fuskanci Nana ta ce,

“Soyayya wani abune mai girma Nana. Babu kalaman da za ka ɗora girmanta akai. Wani irin yanayi ne na daban.”

A nutse Nana ke kallonta tana son fahimtar me take faɗa. Kafin ta ci gaba da cewa.

“Lokacin da kake son wani za ka ji zuciyarka ta cika. Ba ta gane komai sai wannan yanayin.

Za ka ji kamar dama can an halitta maka zuciyarka ne domin mutum ɗayan nan.”

Tunawa take. Tana tuna yadda taji son Fu’ad. Yanayin soyayyar shi a zuciyarta. Komai dawo mata yake da wani irin bazata.

“Haka kika ji da dady?”

Nana ta tambaya muryarta da murmushi. Harararta Safiyya ta yi. Shagwaɓe fuska Nana ta yi.

“Mummy please. Waye zai faɗa min in ba ke ba?”

‘Yar dariya Safiyya ta yi. Ƙarya ita ce ƙarshen abinda za ta so ta yi ma Nana a wannan lokacin. Don haka ta zaɓi ta gaya mata gaskiya.

“Ya girmi hakan da dad ɗinki.”

Cike da jin daɗi Nana ta ce,

“Har yanzun?”

Wannan tambaya ce da ba ta son amsa ma kanta ita. Ba ta son ta fara wannan tunanin ko da wasa. Da wani rauni ta kalli Nana hakan ya sa ta faɗin,

“I’m sorry.”

Murmushi ta yi.

“Ɗaukar mana wannan kikai mana falo gani nan zuwa.”

Ba musu Nana ta ɗauki plate ɗin dankali da na wainar ƙwan ta wuce. Sauke numfashin da ta ke riƙe da shi ta yi.

*****

Suna gama breakfast ɗin Nana ta ce za ta je ta ƙara yin wanka. Ita ma Safiyyar wankan ta je ta yi.

Tana fitowa Yusra ta kirata suka gaisa. Ta ce mata za ta iya tahowa a shirye suke. Atamfa ta saka daviva ruwan hoda da ta matuƙar amsar jikinta.

Duk da babu wata kwalliya a fuskarta. Tana zuwa falo ta zauna Nana ta fito sanye da doguwar rigar da ya fito mata da ita da ɗan hijab.

Kallonta Safiyya take. Har da jan baki pink a leɓenta. Ɗan murmushi ta yi.

“Ba na so in yi kama da marasa lafiya. Ba na son mutane su kalle ni da irin abinda na ke gani cikin idanuwanku bayan ba su sanni ba.”

Sauke idanuwanta ta yi daga kallon da take ma Nana a sanyaye ta ce,

“Wane irin kallo ne muke miki Nana?”

Ƙarasowa ta yi kusa da Safiyya ta zauna.

“Tausayi da sona duka a tare. In kun min ba na jin kamae bani da lafiya. Amma in Anty Jana ta min ba na jin daɗi. Bana son ganin shi a idon kowa sai naku.”

Sauke ajiyar zuciya Safiyya ta yi tai shiru saboda ba ta san me za ta ce ba. Wasu maganganun idan Nana ta yi sai su sa ka rasa naka kalaman.

*****

Da motar Abba ya je hotel ɗin ya ɗauko komai nashi ya yi Check out ya dawo. A gida ya yi wanka suka yi breakfast gaba ɗaya.

Wata irin kewar Nana yake ji. So yake kawai ya je ya ganta. Shi ya fara miƙewa daga kan dining ɗin tare da faɗin,

“Momma ara min motarki.”

Kafin ta amsa Abba ya ce,

“Ka ɗauki mota ɗaya cikin nawa kawai.”

Sai da ya kalli Abba sosai sannan ya ce,

“Na gode Abbah. Allah ya ƙara girma.”

“Amin. Ka je ɗaki mukullan suna nan gefen gadona.”

Kai ya ɗan ɗaga alamar to. Har ya zo wucewa Abba ya ce,

“Fu’ad….”

Dawowa ya yi ya zauna. Yana ba wa Abba dukkan hankalin shi.

“Ka kawo min ita anjima in ganta.”

Cike da ƙaunar Abba cikin idanuwanshi ya ce,

“In shaa Allah.”

Sannan ya miƙe. 406 ya ɗauka, don shi yanzun duk wani ƙyale-ƙyalen duniya ya fice mishi a rai.

Da ya shiga ciki ya ja motar wani murmushi ya ƙwace mishi. Rayuwa ba komai bace ba. Wai yau shine kwata-kwata bai damu da mota ba.

Ta zame mishi wani abu da zai hau ya biya buƙatarshi. Bai kuma damu ba. Abin ya ba shi mamaki.

Cike da tunani barkatai ya hau titi.

*****

Ƙwanƙwasa ƙofa suka ji suna zaune suna hira ita da Nana. Ware idanuwa Nana ta yi kan Safiyya.

“Turo.”

Safiyya ta faɗi. Don ta ɗauka Yusra ce. Fu’ad ne ga mamakinta. Kallon shi take.

Sanye yake da jeans blue. Sai wata hoodie fara ƙal. Hular na kanshi. Ya ja hannun hoodie ɗin zuwa gwiwar hannun shi.

Ya yi wani irin kyau. Sallama ya yi. Ta amsa a sanyaye saboda hakan take jin jikinta ya mata wani irin sanyi.

Da gudu Nana ta tashi ta je ta ruƙunƙume Fu’ad ta na faɗin,

“Dady. Ina ta missing ɗinka.”

Ɗagota ya yi jikinshi. Ya sumbaci kuncinta duka biyun sannan ya ce,

“Princess ta sha kyau yau. Ina ta missing ɗinki nima.”

Wayarshi ya lalubo cikin aljihunshi da ɗayan hannun. Ɗayan na riƙe da Nana da ke faman murmushi bakinta ya ƙi rufuwa.

Camera ɗin ya buɗe ya daga ya ɗauke su. Sake riƙe shi Nana ta yi yana ta ɗaukarsu.

Sumbatarta ya yi a kunci yana ɗaukar su a haka. Hannunshi mai wayar yasa yana nuna mata alamar tai kissing ɗinshi a kumatu.

“Dady zan shafa maka lipstick.”

Daƙuna fuska ya yi da ke nuna bai damu ba tare da juya mata idanuwanshi. Dariya ta yi.

Ta zagaya hannayenta duka biyun a wuyanshi sannan ta sumbaci kumatunshi, ya ɗauke su wajen kala goma. Sannan ya kalli Safiyya.

Saurin kauda kai ta yi. Don ta fahimta sarai. Babu abinda zai ja mata ɗaukar hoto da shi. Nana ya kalla yana wani matse lips waje ɗaya.

“Mumy please ki zo mu yi.”

Ta faɗi. Ware mata idanuwa Safiyya ta yi alamar ba ta so. Nana ta ce,

“Dady za ka ɗauki pic da Mummy?”

“Banda matsala princess. Duk abinda ki ke so.”

Fu’ad ya faɗi yana Karasa maganar da kallon Safiyya. Harara ta watsa mishi wato ita ce take da matsala.

Miƙewa ta yi. Sai lokacin ya samu damar kallonta sosai. Numfashin shi ya ji yana masa wasa wajen fita da komawa.

Ta canza in all the good ways. Kyanta ya fito fiye da da. Kallon da yake mata yasa ta tuna babu mayafi a jikinta. Kallon shi ta yi ta ga idanuwan Nana basa kanta.

Yadda iya shi kaɗai zai gani ya fahimta ta ce,

“Bana son kallo.”

Ɗaga mata gira ya yi duka biyun. Ta taka ta ƙarasa inda yake. Duk da bayanshi ta tsaya bai hana ƙamshin da take ya cika mishi hanci ba.

Mamaki yake sosai saboda collection ɗin smart ɗin da ya daina amfani da su ne saboda suna tuna mishi ita. Shi ne a jikinta.

Sake baza hanci ya yi ƙamshin na tuna masa abubuwa da yawa. Da ƙyar ya iya ɗaga camera ɗin ya ɗauke su kala biyu duka Safiyya na bayanshi ta wani haɗe fuska.

Zai ɗauki na ukkun aka ƙwanƙwasa ƙofar. Ta san wannan karon Yusra ce. Da kanta ta je ta buɗe ƙofar. Aikam Yusra ce sanye da doguwar riga fara. Ta yi rolling farin mayafi. Hannunta ɗauke da wata jaka.

Da fara’a suka gaisa da Safiyya ta shigo ciki. Gaishe da Fu’ad ta yi ya amsa a daƙile. Sai da ta zauna sannan ta yi wa Nana murmushi tare da faɗin,

“Nana.”

Murmushin Nana ta mayar mata.

“Ina kwana.”

Ta faɗi Yusra ta amsa. Yarinyar ta mata kyau. Ba sai an faɗa mata ba tasan mutumin da ke riƙe da ita shi ne babanta. Don ga kamanni nan.

“Gata ta zo Nana.”

Fu’ad Nana ta kalla.

“Dady sauke ni.”

Kallonta ya yi ya ce,

“Wace ce?”

“‘Yar jarida.”

Lokaci daya idanuwanshi suka yi wani irin haske. Sake riƙe Nana ya yi gam. Baya son yarshi a TV balle duniya ta kalle masa yarinya.

Baya son labarinshi a kunnuwan kowa. Baya son duniya ta kalle shi da matsayin uban da ya kasa yi wa ‘yar shi komai. Sai da ya ji Nana na son sauka da kanta sannan ya ajiyeta.

Yusra ya kalla.

“Ba na son ki ɗauki komai nata…”

Ya maida hankalinshi kan Safiyya.

“Ina son magana da ke.”

A dake ta ce,

“Seriously Fu’ad? Ka bari mu gama tukunna.”

Ƙara ɓata mishi rai take.

“Ki taso ko mu yi a gaban ta.”

Miƙewa ta yi. Kitchen ya nufa, tsabar masifa ce fal a cikinshi. Abin ya so ya ba ta dariya.

Suna ƙarasawa ta ce,

“Sai ka ce min yunwa kake ji drama king.”

Dariya ta yi saboda yadda yake mata kallon rashin fahimta. Lokaci ɗaya ya ji ya sake ƙulewa. Ya ma zama wani game a wajenta.

“Kitchen ka kawo mu. Me kake tunanin zan ɗauka?”

Sai lokacin ya kula. Ya ɗan daƙuna fuska don ya kasa ganin abin dariya cikin lamarin.

“Ba na son yarinyata a TV. Ba na son kowa ya kalleta da kalar me zai faɗa. Saboda me ma za ki kira su?”

Hannunta ta ɗora kan ƙugu tana kallon ikon Allah.

“Na ɗauka tun a asibiti na faɗa maka tana son magana da su. Ka ce bakomai.”

Kallonta yake dake fassara ashe baki da hankali?

“Na ɗauka kin gane don a gabanta ne. Ba ki ga idanuwana ba?”

‘Yar dariya ta yi cike da takaici.

“Ka faɗa mata da kanka.”

“Ba na son in ce kar ta yi abinda take so.”

Ya faɗi. Ba ta san ranar da Fu’ad zai bar son kanshi ba. Ba ta ga ranar ba. Shi ba shi da zuciyar da zai ce wa Nana a’a sai ita kenan.

Kamar daga sama suka ji an ce,

“Dady.”

Da sauri suka kalli Nana a tare. Idanuwanta kan Fu’ad a kafe ta ce,

“Na haƙura tunda ba ka so.”

Tsugunnawa ya yi. Ya sa hannu ya tallabi fuskar Nana cikin hannuwanshi.

“Princess ba na son maganganun mutane ne. Ba na son ki zama abin kallo da magana.

Ba na son kowa ya miki kallon something weak and fragile. You are my daughter Nana. Zuciyata ba za ta iya ɗauka ba.”

Tallabar hannuwanshi da ke fuskarta ta yi da nata. Murmushi ta yi mishi.  

“Ba sai ka min bayani ba. Ban san me yasa nake son magana da ita ba. Na haƙura tunda ba ka so.”

Sunbatar goshinta ya yi.

“Thank you, Princess.”

Dariya ta yi mishi.

“Ku bar ni in faɗa mata da kaina.”

Kafin su ce wani abu da gudu ta fice daga kitchen ɗin. Suka kalli juna shi da Safiyya suna sauke numfashi a tare.

*****

Zama ta yi a gefen Yusra.

“Anty ba zan yi ba. Dady baya so. Na haƙura. Amman ki tambayeni ko me kike so zan amsa miki in dai ba za ki saka a TV ba.”

Murmushi Yusra ta yi mata. Duk yadda take son ta sa labarin yarinyar nan bai kai yadda ta fahimci babanta ba. Ko ita ce ba za ta so ‘yarta a TV ba sam.

Hira suka ɗan yi kaɗan da Yusra. Tana tambayarta ya akai ta ga babanta duk ta amsa ta. Roƙon Nana ta yi suka yi hoto tare. Sannan ta miƙe ta kalli su Fu’ad da ke bayansu.

“Na gode sosai. Allah ya ba ta lafiya.”

Suka amsa da amin. Har ƙofa Safiyya ta rakata sannan ta dawo. Fu’ad bai ce mata komai ba. Wajen Nana ya je ya zauna.

“Zan je unguwa. Idan na dawo za mu je tare da ke, okay?”

Kai ta ɗaga tare da faɗin,

“A dawo lafiya. Love you.”

Wani kumburi zuciyarshi ta yi. Sai da ya yi hugging Nana yana jin kamar ya mayar da ita cikinshi kar wani abu ya sameta sannan ya ce,

“Love you more.”

Dariyar nan da yake so ta yi mishi cikin kunnuwanshi sannan ya saketa. Miƙewa ya yi ya sauke idanuwanshi kan Safiyya.

Wani irin kallo yake wa safiyya da ta kasa fahimtarshi. Muryarshi ya saukar sosai. Idanuwanshi na cikin nata ya ce,

“Zan dai dai ta komai. Zan cika miki wannan alƙawarin.”

Lumshe idanuwanta ta yi. Tana jin yadda yake fama mata tsofin ciwukanta. Hular rigarshi ya cire daga kanshi ya kalli Nana ya yi mata murmushi sannan ya nufi hanyar ƙofa.

*****

Yana fita daga gidan Lukman na kiranshi a waya. Ɗagawa ya yi tare da faɗin,

“Lukman…”

“Fu’ad yane? Ya Nana?”

Sai da ya yi jim ya amsa da,

“Okay I guess.”

Yana jin yadda Lukman ya sauke numfashi kafin ya ce,

“Kana gidan ne?”

Girgiza kai ya yi kamar yana ganin shi.

“Ina hanyar bichi. Ban kai da fita daga cikin gari ba tukunna dai. Em’ gonna make it right. Duk abinda na ɓata.”

“About time Fu’ad. Da ka faɗa min da mun je tare.”

Murmushi ya yi. Har ranshi ya ji daɗin maganar Lukman ɗin, sai dai wannan abu ne da zai yi shi kaɗai. Baya son kowa ya taya shi.

Ya gaji da yadda tun yarinta Lukman da Haneef ke share hanyar da ya ɓata. Wannan karon zai yi komai. Laifin shi ne shi kaɗai, kuma shi kaɗai zai gyara.

“Na gode Lukman. Na gode fiye da yadda zan iya faɗa. Kuskurena ne. Ina son gyarawa da kaina.”

“Hmm. Be safe. Just be safe Fu’ad.”

‘Yar dariya ya yi.

“Yeah whatever. Ka shafa min kan Junior…”

Sai yanzun ya tuna. Ya ɗan daki steering motar tare da faɗin,

“Em such a bad Uncle. Na ea junior alƙawari Lukman ko ka tuna min.”

Dariya kawai Lukman ya yi ya kashe wayar. Ajiyeta ya yi gefe ya mayar da hankalin shi sosai kan tuƙin da yake yi.

Da ya dawo anjima zai cika alƙawarin nan.

*****

Tura ɗakin Ikram ya yi da sallama. Tana kwance kan gadonta tana karatun Ƙur’ani, Sai da ta kai ayar sannan ta amsa shi. Ƙur’anin da ke hannunta ta rufe ta ajiye gefe a hankali. Da ɗan murmushi ta ce,

“Pa?”

Don ta san ta musu sai da safe tun kafin isha’i, Ba kuma al’adarshi bane shigowa ɗakinta babu wani dalili. Gefen gadon ya zauna. Ya rasa ta inda zai fara.

“Lafiya dai ko? Ina Mummy?”

Ganin yadda duk ta rikice ya sa shi saurin cewa,

“Komai lafiya Ikram. Kawai ina son magana da ke ne.”

Gyara zama ta yi kan gadon.

“Alright. Ina ji.”

Saida ya sauke numfashi sannan ya ce,

“Zan ƙara aure Ikram. An sa rana yau. Nan da wata biyu.”

Shiru ta yi tana ƙara tauna maganar shi na tsayin mintina biyar kafin ta ce,

“Why?”

Ta tsare shi da idanuwa. Ɗan ɗaga kafaɗar shi ya yi.

“Just…”

“Kana son Mummy?”

Kai ya ɗaga mata. Don tana jin tsoro. Ta ga yadda kishiyar maman ƙawarta Jawahir take ba su wahala. In tana ba ta labari takan gode wa Allah da babansu bai ƙara mata ba.

Sosai ta kalle shi. Tsoro cike fal da idanuwanta. Hannunta ya kamo. Yana son ya fara zame ma ‘ya’yanshi aboki da za su iya magana ba tare da shakka ba.

“Kinsan za ki iya faɗa min komai ko? I am your dad. Your best friend Ikram.”

Kai ta jinjina.

“Kawai ina jin tsoro ne. I love Mum sosai. Kai ma haka. What if ta ƙwace mana kai?”

Da wani irin yanayi ya ce,

“Babu wanda zai ƙwace muku ni in shaa Allah. Babu abinda zai canza. You will be there for me da ke da Mum ɗin ki da su Umar. Ba za ku bari kowa ya ƙwace ni ba?”

Fuskarta babu wasa ta ce,

“Sosai ma. Promise komai ba zai canza ba?

Sai da ya yi jim sannan ya ce,

“In shaa Allah. Kumin addu’a Allah ya tabbar min da alkhairi. Shi nake buƙata.”

Sai lokacin ta yi mishi murmushi. Ya san da wuya ta sake cewa wani abu. Ikram ba mai yawan magana bace ba.

Har ya kai ƙofa ta ce,

“Pa…”

Ya juyo ya kalleta.

“Thank you.”

Murmushi Jabir ya yi. Ya jinjina mata kai kawai ya fita yana ja mata ƙofar. Numfashi ya sauke yana juya idanuwanshi.

“So awkward…”

Ya faɗi ƙasa-ƙasa. Ya na takawa zuwa ɗakinsu. Jana ya samu inda ya barta tana dudduba wasu takardu.

Idanuwanshi ta ji suna mata yawo ta ɗago ta kalle shi sai raba idanuwa yake. Dariya ya bata.

“Ya dai?”

Ɗan rausayar da kai ya yi.

“Kin bar ni da Ikram ni kaɗai ko?”

Dariya ta sake yi.

“Ba ga shi har ka gama ba. Na ce maka ba wani wahala.”

Ƙarasawa ya yi ya zauna kusa da ita. Takardun da ke hannunta ya karɓa ya ajiye gefe ɗaya.

“Lokacina ne yanzun. A taimakamin a ajiye office work ɗin nan Jana.”

Shagwaɓe fuska ta yi.

“Na bar wa Aina ai.”

Ware idanuwa ya yi.

“Tun yanzun?”

Ɗan murmushi ta yi cike da kishi. Har ɗaci take ji a wuyarta. Ya karance ta tsaf, don haka ya matsa daf da ita sosai.
“Naki ne ni jana. Kin san wannan ko?”

Ɗaga mishi kai ta iya yi kawai. Duk soyayyar nan a kwanaki sittin da wata za ta dinga raba ta. Addu’a ta ci gaba da yi a zuciyarta.

Sai da ta ji wata nutsuwa ta saukar mata sannan ta fara nuna ma Jabir kalar soyayyar da take mishi.

*****

Kanshi tsaye gidan su Safiyya ya wuce da wani irin yanayi na nasara da yake saka shi murmushi shi kaɗai.

Da sallama ya shiga. Nana na zaune tana kallon cartoon network. Ta ruga ta na mishi sannu da zuwa. Safiyya ta fito daga ɗaki.

“Sannu da dawowa.”

Ta faɗi. Kai ya ɗan ɗaga mata. Yana kallonta tare da yin murmushi. Komai nasu ya kusan gyaruwa. Zai ba ta mamaki ba da jimawa ba.

“Za mu fita da Nana.”

Ya fadi. Kai ta ɗaga mishi. Da gudu Nana ta ruga ɗaki ta ɗauko hijabinta da takalmi ta dawo.

Safiyya ta ce,

“Nana ko goodbye?”

Da sauri tana dariya ta ƙarasa wajen Safiyya ta rungumeta. Sakinta ta yi ta juya tana faɗin,

“Sai mun dawo.”

“Allah ya tsare hanya.”

Safiyya ta faɗi. Fu’ad ya kama hannun Nana cikin nashi suka fita. Wata ajiyar zuciya ta sauke gidan na mata wani irin shiru.

*****

Yana tuƙi ne Nana ta ce,

“Dady in roƙeka?”

Kai ya ɗaga mata. Don ba ya jin akwai abinda za ta nema in dai zai iya da zai kasa yi mata.

“Ka auri Mummy. Don Allah ku koma aurenku!”

Wani shiru ya ji cikin kanshi. Zuciyarshi na tsayuwar wucin gadi kafin ta ci gaba da aiki.

“Please. Tana buƙatarka in ba na nan. Kana buƙatarta in ba na nan. Tana sonka sosai. Don Allah karka ce no.”

Zufa ke keto mishi ta ko’ina. Nana na tambayarshi abu mai girma. Tana tambayarshi abinda baya jin zai iya.

Bashi da abinda zai ba Safiyya. Bashi da farin cikin da take buƙata. Parking ya yi gefe yana maida numfashi.

“Nana…”

Ya kira sunanta yana rasa me zai ce. Ta ina zai fara faɗa mata sakin Safiyya da ya yi ‘yanci ne ya ba ta. Farin cikin da ba zai iya ba ta bane ya barta ta samu da wani.

Idanuwan Nana cike da hawaye ta ce.

“Ka daina sonta ko?”

Da sauri ya girgiza kanshi. Son da yake ma Safiyya ba zai taɓa misaltuwa ba. Sonta ya sa yabarta. Akan son da yake mata ya zaɓi ya barta in har za ta samu farin cikin da shi ba zai iya bata ba. Hawayen da suka zubo mata ta sa hannu ta goge. Tana son ta gansu sun koma. Tana son hakan fiye da yadda take son lafiyarta.

“Please Dady. Bana so in bar Mummy ita kaɗai. Bana so… Ba ta da kowa….”

Kuka Nana take yi. Jinshi yake har cikin tsokarshi. Kamo Nana ya yi yana tallabar fuskarta yana goge mata hawayenta da sauri. Don shi kanshi da zai samu wanda zai wa kuka, yi zai yi.  

“Ina sonta Nana… I love your mum. Ita kaɗai zan so har abada…”

Cikin kuka Nana ta ce,

“To ka aure ta.”

Cikin rasa yadda zai ce wa Nana yasa shi faɗin,

“Banda abinda zan ba ta. Banda komai da zan ba ta.”

Riƙe hannuwanshi Nana ta yi.

“In tana sonka a haka fa? Za ka aure ta?”

Kai ya ɗaga wa Nana. Son da yake ma Safiyya mai girma ne. Ya san ba ta son shi, ta tsane shi yanzu. Ta kuma ƙara tunda ba shi da abinda zai ba ta.

Ya ji daɗi saboda zai ba ta mamaki zuwa gobe da safe in shaa Allah. Zai ba ta abinda ya san tana so. Abinda ya yi mata sanadin salwantarshi.

“Zan ma mum magana. Ka ji.”

Kai ya ɗaga mata. Ya goge mata fuska tare da faɗin

“Bana son kukanki. In kuma na sake gani zan fasa.

Da sauri ta sa hannu ta sake goge fuskarta.

“Na daina. Ka yi haƙuri ba zan sake ba.”

Murmushi ya yi.

“Good girl… Zauna sosai to.”

Gyara zamanta ta yi ya tayar da motar suna tafiya.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×