Skip to content

Akan So | Babi Na Talatin Da Biyar

0
(0)

<< Previous

Kallon Fu’ad take sai kai kawo yake da Nana akan kafaɗar shi yana ta bubbuga bayanta a hankali. Tunda suka dawo daga ganin Nawaf yake lallashinta har ta yi bacci.

“Ka kwantar da…”

“Shhhhhhh.”

Fu’ad ya katse ta yana daƙuna fuska. Shirun ta yi ta zuba masa idanuwa kawai. Da alama baya ji da ganin kowa banda Nana a yanzun.

A hankali take jin wani abu a zuciyarta yana dokawa a hankali. ‘Ina sonki Sofi’ kalamanshi suka faɗo mata.

Kowa ya turo ƙofar ya taimaka mata ba kaɗan ba. Murmushi ta ɗora kan fuskarta ganin Ansar ne. Shi ma murmushin ya mayar mata.

Fu’ad da ke tsaye yana kallon su ya ɗan runtse idanuwanshi yana jin kamar ya shaƙare Ansar ɗin nan. Ya ringimo ƙaton kanshi yazo.

Ƙarasawa ya yi ya miƙa wa Fu’ad hannu. Ya karɓa yana kauda kai gefe. Murmushi Ansar ya yi. Fu’ad ɗin nan na ba shi dariya ba kaɗan ba.

“Ya jikin, Nana?”

“Da sauƙi. Mun gode.”

Ya amsa da ƙyar. Ƙarasawa ya yi ya ja kujera ya zauna suna gaisawa da Safiyya. Wani irin abu ya ji ya tsaya mishi a wuya.

“Zan wuce Safiyya. Idan Nana ta tashi ki kirani a waya mu gaisa.”

Ƙasa-ƙasa Fu’ad ya ce,

“Kamar ka san ba ma buƙatarka.”

Harara Safiyya ta watsa mishi. Ya ɗan buɗe mata idanuwa da ke fassara ‘Gaskiya na faɗa’.  Murmushi Ansar ya yi ya miƙe ya ajiye ledar da ke hannunshi.

Miƙewa Safiyya ta yi.

“Ina za ki je?”

Fu’ad ya buƙata yana tsare ta da idanuwa. Wucewa ta yi ta bi bayan Ansar. Safiyya ta raina shi, yanzun shi ne tunanin da yake yi.

Ƙarasawa ya yi a hankali ya kwantar da Nana yana gyara mata kwanciya ya ji an ƙwanƙwasa ƙofar.

“Yes…”

Ya furta ba tare da ya juya ba. Sallama akai aka turo ƙofar. Duk daɗewar da ya yi bai ji muryar ba bai hana shi ganeta ba.

Da sauri ya juya don ya tabbatar da abinda kunnuwanshi suka ji. Aikam Hamza ne. Shi ma tsaye ya yi riƙe da ƙofar yana kallon Fu’ad ɗin.

A hankali ya saki handle ɗin ƙofar da yake riƙe da shi ya na shigowa cikin ɗakin sosai.

“Hamza…”

Fu’ad ya faɗi cikin sigar gaisuwa. Da ɗan guntun murmushi Hamza ya amsa da faɗin,

“Moh…”

Sosai ya ƙaraso cikin ɗakin. Sai lokacin ya ga da mutum a bayan Hamza.  Daga ƙasan ƙafafuwanta ya fara yawatawa da idanuwanshi. A hankali har ya kai kan fuskarta inda ya tsayar da su cak. Tsaye take tana wasa da hannayenta. Idanuwanta na yawo ko ina na ɗakin banda kan Fu’ad.

Wani abu ya ji zuciyarshi ta yi. Ga bakinshi ya wani bushe. Da Kjyar ya haɗiyi miyau ya furta,

“Hussaina. Little sis.”

Hannuwanshi yasae ya goge fuskarshi da yake jin kamar zufa a jiki. Miƙewa ya yi daga kan gadon ya ƙarasa inda take tsaye.

“Hussaina…”

Bata kalle shi ba. Asalima raɓa shi ta yi ta wuce inda Hamza yake tsaye ta tsaya kusa da shi sosai. Hannuwanta ta saki.

Takai ɗaya ta kama na Hamza ta dumtse gam. Idanuwanta na ƙasa. Kallonta sosai Fu’ad ya yi. Inda take tsaye. Sannan ya maida hankalinshi kan hannunta.

Hannun Hussaina cikin na hamza a dumtse. Lokaci ɗaya ya fahimci me hakan yake nufi. Sai sannan ya lura da yanayin Hussaina.

Ciki ne a jikinta har ya turo. Hussaina ta yi aure. Lumshe idanuwanshi ya yi. Yakai hannu yana murza goshin shi da yake jin wani abu na yawatawa.

Safiyya ce ta turo ɗakin da sallama ta shigo. Ta gansu tsaye cirko-cirko. Kallon Hussaina take yi. Sai lokacin ta gane ta.

“Hussaina?”

Ɗagowa ta yi ta sauke idanuwanta kan Safiyya.

“Anty na.”

Da sauri Fu’ad ya kalleta. Bai san yadda ya yi kewar muryarta ba sai yanzu. Bai san kewarta da ya yi ta yi girma haka ba sai yanzun da ya ganta.

Wani abu ya ke ji a dukkan jikinshi. Gaisawa Safiyya ta yi da Hamza sannan suka gaisa da Hussaina. Ta ja musu kujeru suka zauna.

“Ya jikinta?”

Hussaina ta buƙata. Safiyya ta amsa ta da,

“Da sauƙi. Bacci take yi.”

Kai Hussaina ta ɗan ɗaga mata tare da ɗorawa da.

“Dama munzo dubata ne. Za mu dawo gobe in shaa Allah.”

“Allah ya kaimu goben. Mun gode sosai.”

Da sauri Hussaina ta katse ta da faɗin,

“Saboda ita na zo. Ba don kowa ba.”

Kallonta Safiyya ta yi ta rasa me za ta ce. Miƙewa ta yi, Hamza ma haka. Gani ya yi sun nufi ƙofa. Da sauri ya ƙarasa inda suke.

“Hussaina…”

Buɗe ƙofar ta yi ta fice. Hamza ma haka. Da sauri Fu’ad ya bi bayansu. Gudu Hussaina take tana nufar hanyar da za ta fiddata daga asibitin. Tsayawa Hamza ya yi yana tare Fu’ad. Hannunshi da ke kan kafaɗarshi Fu’ad ya bi da kallo. Yana jin wani irin ɗaci a zuciyarshi.

“Me hakan ke nufi Hamza?”

Da wani yanayi a muryarshi Hamza ya ce,

“Please ka ƙyale ta kawai. Ba lafiya gareta ba sosai….”

Ture hannun hamza Fu’ad ya yi yana mishi wani irin kallo.

“Ka sake bani dalilin binta kenan.”

Dafe kai Hamza ya yi kafin ya ce,

“Look. Ba wai ina so in hanaka ba ne. Ƙanwarka ce. Amman ina da hurumin da zan damu da lafiyar ta.”

Kamar daga sama Fu’ad ya ce,

“Kana sonta?”

Kallon wannan wacce irin tambaya ce Hamza ya yi wa Fu’ad.

“Kawai ka amsa ni. Kana sonta?”

Wani ɗan murmushi Hamza ya yi.

“Baka ga shaida a jikinta ba.”

Duka Fu’ad ya kai mishi ya kauce yana dariya.

“That is disgusting Hamza. Ƙanwata ce.”

Dafa shi Hamza ya ɗan yi.

“Karka damu. Ina son Hussaina. Ina sonta sosai wallahi. Please za ta sauko. Right now space take buƙata ka ba ta.”

Sauke murya Fu’ad ya yi sosai.

“Ba damuwa. Just… Just take care of her.”

Kai ya ɗaga mishi. Yana kallo ya juya ya koma. Hanya ya nufa yana ficewa daga asibitin. Cikin mota ya samu Hussaina a zaune ta haɗa kanta da jikin motar tana wani irin kuka.

Sai da ya shiga motar ya kullo sannan ya matsa ya riƙo ta. Hannunshi ta riƙe cikin nata ta na ɗora fuskarta akai. Kuka take sosai da sosai.

“Shhhhh baby please. Kukan ya isa…”

Cikin shesshekar kuka ta ce,

“Duk….duk shekarun da nake son mishi magana…. Yanzun ban kula shi ba….. I…..i miss him sosai…”

Hannunshi ya zame daga nata. Ya tallabi fuskarta. Cikin idanuwa ya kalleta.

“Shi ma ya yi kewarki.”

Girgiza kai Hussaina ta yi.

“Da ya neme mu. Saboda me bai neme mu ba duk lokacin nan?”

Bashi da amsar tambayarta. Don haka ya sa hannunshi yana goge mata fuskarta.

“Saikin haifo mana baby rigimamme ko.”

Murmushi ta yi. Ya ɗan sumbaci gefen fuskarta.

“Ko kefa. Komai zai yi dai dai kin ji ni ko? Ba na son kukan nan.”

Gyara zamanta ta yi tana ƙara goge fuskarta.

“I love you.”

“I love you more.”

Ya faɗi yana kunna motar…

*****

Kwance take jikin mamansu Nawaf. Tun jiya bayan ankai Nawaf makwancin shi ta nemi hawaye ta rasa.

Sai dai zuciyarta da ta ke ji kamar an bi takanta da mota. Ga wani irin zafi da take ji tana mata. Ba wai ba ta yarda da cewar Nawaf ya rasu ba.

Ta dai kasa yarda da ta rasa shi har abada. Ta kasa yarda da cewar ya tafi ba ta gama faɗa mishi duk irin son da take mishi ba.

Ba ta gama faɗa mishi duk yadda take godiya da kalar taimakon da ya yi mata ba. Tunda ya san ta burin shi yaga ya tsameta daga rayuwar da take ciki.

Amma ita ta kasa janye shi daga tashi. Ƙirjinta tafasa kawai yake kamar an zuba mishi garwashi.  Maganar mutane sama-sama ta ke jinta.

Gaba ɗaya duniyar ta mata wani irin empty. Ji take ba tada kowa da ya rage mata a cikinta. Duk da Farhan da zuciyarta ke sane da zamanshi bai hanata jin ba ta da kowa ba.

Tana jin mazaunin Nawaf da ya bari a zuciyarta can wani gefe da take da yaƙinin har tata mutuwar ta same ta babu abinda zai cike shi.

*****

“Tun ɗazun ina ta maka magana ba ka ce komai ba?”

Ajiyar zuciya ya sauke.

“Banda abinda zan faɗa in dai kan Fu’ad ne saboda na jima da cire shi daga zuciyata ballantana ya dame ni.”

Dafe kai Momma ta yi. Wani lokacin sai ta ga da gangan ake cewa Fu’ad ɗin na da taurin kai.

“Ni dai zan je in sake dubo ‘yar yarinyar nan.”

“A dawo lafiya. Allah ya ba ta lafiya.”

A sanyaye ta amsa da,

“Amin thumma amin.”

*****

Bai je ko ina ba sai hotel ɗin da ya sauka, shi ma wanka ya yi ya sako kaya ya dawo. Safiyya ta je ta dawo.

Yana zaune kusa da Nana da tunda ta farka ba ta ce mishi komai ba ta yi shiru. Ya rasa me zai fara ce mata. Duk sai yake jin shi ya wani daburce.

“Ya rasu ko?”

Ta tambaya. Da sauri Fu’ad ya riƙo hannunta yana girgiza mata kai.

“Ki bar wannan maganar Nana. Mumynki ta je ta dawo. Za ta taho da abinda zamuci.

Ko kina son wani abin daban?”

Kai ta girgiza mishi ta yi shiru kawai. Tun jiya ya ƙi barin zuciyarshi ta zo mishi da zancen Nawaf saboda ba ƙaramin tsorata shi hakan yake ba.

Da dare bai yi bacci ba sam. Ya rasa me ya hana shi bacci sai yanzun ya tuna result ɗin test ɗin da akai mishi ne za su karɓa yau.

Zuciyarshi ya ji wasu abubuwa na tsinkewa a ciki suna barin mazaunin su. Matsawa ya yi wajen fuskar Nana ya sumbaci goshinta.

Wani kasalallen murmushi ta sakar mishi.

“Mummy ta koya maka ko?”

Murmushin ya mayar mata. Ya ɗan ɗaga kafaɗa alamar bai ma fahimci me take nufi ba.

“In Mummy tana son jin ko jikina da fever ba ta son tambaya haka take yi fa. Ba ta san na gane ba.”

Dariya Fu’ad ya yi.

“I love you…”

Da sauri ya ware idanuwanshi akanta. Yana jin yadda zuciyarshi ke ta tsalle-tsalle cikin ƙirjinshi. Bai san wanne abin arziƙi ya aikata ba a rayuwarshi da ya cancanci wannan kalaman da Nana ta faɗa mishi.

Wasu irin akwatina ya buɗe ya rufe su ciki don ba zai so ya ɓatar da su ba. Kallon shi Nana ta yi ta ci gaba da faɗin,

“Ina Kaunarka kamar yadda na ke ƙaunar Mummy tun kafin in sanka.”

Sake sumbatar ta ya yi a goshi yana riƙo hannunta. Bai san kalaman da zai yi amfani da su ba don ya gaya mata kalar yadda yake jin ƙaunarta daga ranar da ya ɗora idanuwanshi a kanta.

Hannun ya kamo ya ɗora kan ƙirjinshi. Wasu emotions ne yake ji ta ko ina suna danne shi. Muryarshi na ɗan rawa ya ce,

“ƙaunar da nake miki ta girmi abinda kenan ciki.”

Dariyar nan da yake jin sautinta ya fi na komai da ya taɓa ji cikin kunnuwanshi ta yi. Ƙasa ta yi da murya ta ce,

“Ta fi ta Mummy?”

Ware idanuwanshi Fu’ad ya ɗan sake yi akanta. Ita ma nata a ware suke cikin nashi kafin su bushe da dariya a tare.

Haka Safiyya ta turo ƙofar ta same su. Tun daga bakin ƙofar take jin sautin dariyarsu. Suna kallonta suka sake wata sabuwar dariyar.

Da mamaki take kallon su. Girgiza kai kawai ta yi ta ƙarasa gefe ta ajiye kayayyakin da ke hannunta.

“Nana tashi muje in miki wanka.”

Daƙuna fuska ta yi ta na turo baki.

“Na iya fa.”

Kallonta Safiyya take.

“Muje in taya ki to.”

Da ka kalli fuskarta ka san ba ta so. Kawai dai ta sakko ne daga kan gadon. Sai da ta sumbaci Fu’ad a kumatu sannan.

Kallon shi ta yi sosai.

“Ka je gidansu please. Ni ma zan mishi addu’a.”

Kai Fu’ad ya ɗaga mata tare da faɗin,

“I promise.”

“Thank you.”

Ta faɗi tana wucewa toilet ɗin.

*****

Ita kanta Safiyya tunda taga Dr. Jana ta zo ta dudduba Nana ba ta ce musu komai ba ta bita ta ji maganar result ɗin ta ce mata sai ƙarfe huɗu haka ta dawo ta zauna gabanta na wata irin faɗuwa.

A haka Fu’ad ya fita ya yi sallar Azahar ya karɓi key ɗin motarta ya fita ya siyo musu take away da lemuka ya dawo.

Amma daga shi har Safiyya sun ɗan taɓa ne kawai saboda Nana ta musu magana. Ba wai don suna jin daɗin abincin ba.

“Mummy ba ki kira min su ba fa har yanzun?”

Sauke numfashi Safiyya ta yi. Ta ɗauko wayarta da jakarta. Lalubo ɗan katin da Yusra Fari ta ba ta ta yi. Ta duba number ɗinta a jiki.

Text ta yi mata sannan ta ɗago ta kalli Nana.

“Na masu magana yanzun.”

Daga nan kan gadon inda take ta yi kissing tafin hannunta ta hura ma Safiyya tare da faɗin,

“You are the best Mom ever.”

Dariya ta ɗan yi. Fu’ad da ke gefe ya taɓare fuska.

“Princess Mumynki kawai kika sani ko?”

Dariya Nana ta yi. Ya sa hannu ya ɗan taɓa kuncin shi. Babu musu ta matsa kan gadon ta sumbaci kuncin shi. Ya ce,

“Ko ke fa.”

Wayarshi da ke gefe ta ɗauka. Bai hanata ba. Ta miƙa mishi saboda akwai key a jiki. Kallonta ya yi ya ɗan kalli Safiyya sannan ya ware mata idanuwa.

Hannu ta sa ta rufe bakinta tana danne dariyar da take ji. Sannan ta saka ‘Safiyya’ a jikin wayar sai dai ga mamakinta wrong password.

Kallon Fu’ad ta yi ta daƙuna fuska alamar baiba. Ya ɗan ɗaga mata kafaɗa yana murmushi da ke nuna ta sake guessing dai.

Ɗan daga idanuwa ta yi tana tunani. Can ta ce,

“Yes…”

A fili. Dariya ya yi. Safiyya ta kalle su. Su biyun nan ba ta gane yadda suke magana. Sai dai ko ta ji sunyi dariya.

‘Sofi’ ta rubuta sannan ta yi masa OK sign da hannu alamar ya buɗe. Images ta kai. Hotunanta ta fara gani duk tana bacci.

Ta ɗago ta kalle shi. Bai ce mata komai ba ta ci gaba da swiping gaba tana kallon hotunan da ke ciki. Yawanci duk shi da abokanshi ne da kayan ball.

Gaba ɗaya hotunan babu wanda ya yi fara.a a cikinsu. Fita ta yi ta shiga wata folder ɗin daban amman key ne a jiki. Sake kallon Fu’ad ta yi da tambaya a cikin idanuwanta.

Ta juya mishi wayar ya ga folder ɗin. Wani numfashi ya ja sannan ya ɗan yi gefe da kanshi cewar ta sake saka sunan ɗazun.

Ware mishi idanuwa ta yi ya san so take ta faɗi kalar son da ya ke ma Sofi. Ya girgiza mata kai yana daƙuna fuska.

Dariya ta kama yi ta buɗe folder ɗin. Hotunan sunei shi da Safiyya a ciki lodi guda. Ta sa hannu ta shafi screen ɗin tana kallon yadda suke dariya a tare.

Haka ta ci gaba da wucewa, sai dai duk hoton da za ta gani da ƙarin ƙarfin alkawarin da ta ke ɗaukarwa kanta na sai ta zama silar komawarsu ko da shi ne ƙarshen abinda za ta yi.

Sai da ta kai ƙarshe sannan ta koma ta buɗe video record ta soma ɗaukar Fu’ad da ke zaune yana kallonta.

“Me kike yi?”

Ya tambaya. Dariya ta kama yi. Ta juya wayar saitin Safiyya da ta ce mata,

“Nana ki bari fa.”

Sauke wayar ta yi tai saving video ɗin. Miƙewa Fu’ad ya yi yana miƙa da jikinshi ya ce wa Nana,

“Ƙarfe nawa?”

Duba wayar ta yi.

“Ƙarfe uku da minti arba’in.”

Da sauri ya fita bai ma san lokaci ya ja ba haka.

*****

Yana dawowa daga masallaci ya hango motar Lukman. Don haka suna gaisawa suka shiga ciki tare.

Da fara’a Nana ta ce,

“Uncle Lukman…”

Gefen gadon ya zauna ya shafa kanta. Sai da suka gaisa da Safiyya sannan ya maida hankalinshi kan Nana da faɗin,

“Ya jikinki?”

Ɗan ɗaga mishi kafaɗa ta yi da ya ga ta masa yanayi sosai da Fu’ad. Ba ta son ana ce mata ya jiki saboda ba ta son ganin yadda idanuwan mutane ke canzawa in za su mata tambayar.

“Ina uncle Haneef?”

Lukman ya amsa da,

“Na san zai zo.”

Yana rufe baki suna jin turo ƙofa da sallama. Miƙewa Lukman ya yi yana faɗin,

“Momma sannu da zuwa.”

Su dukansu gaishe da ita suka yi. Fu’ad ya janyo mata kujera ta zauna suna hira da Nana.

Dr. Jana ta shigo suka gaggaisa ta sake duba Nana tace wa Safiyya,

“Za ku iya tafiya gida ma. Inda wata matsala dai ku dawo.”

“In shaa Allah. Mun gode sosai.”

‘Yar ledar da ta shigo da ita ta miƙa wa Nana da ta karɓa ta yi hugging ɗinta tare da faɗin,

“Thank you, Anty Jana.”

Da murmushi ta amsa da,

“Don’t mention sweetheart.”

Hankalinta ta mayar kan Safiyya ta ce,

“Zan ganku yanzun kafin ku tafi.”

Wani irin dokawa Fu’ad ya ji zuciyarshi ta yi kamar za ta fito daga Kirjinshi. Binta Safiyya ta yi. Fu’ad ya kalli Lukman sannan ya fita shi ma.

Juyowa Safiyya ta yi idanuwanta cike taf da hawaye ta haɗe hannayenta duka biyun cikin sigar roƙo. Muryarta a sauke ta ce,

“Ina buƙatar yin wannan ni kaɗai. Please…”

Sai da ya ja numfashi ya fitar da shi sannan ya ce,

“Ki daina irin wannan maganar sofi. Ba na so wallahi.”

Kai ta ɗaga mishi.

“Na daina. Ba za ka gane ba. Ina son fara ganin result ɗin ni kaɗai…”

Juyawa ta yi tana goge hawayen da suka zubo mata. Bin ta zai yi yaji an riƙe mishi hannu.

Juyawa ya yi, Lukman ya sake shi yana faɗin,

“Ka ƙyale ta. A karo na farko a rayuwarka ka ji roƙon da akai maka mana.”

Jingina Fu’ad ya yi da bangon wajen bai ce komai ba. Ya ga ‘yarshi ce yana da right ɗin da zai ga result ɗin, bai san me yasa Safiyya za ta dage ita kaɗai za ta gani ba.

*****

Sanda ta shiga office ɗin Dr. Jana na zaune da takardun a babban envelop. Waje ta samu ta zauna jikinta babu ƙarfi ko kaɗan.

Ita kanta ba ta buɗe result ɗin ba tunda ta karɓo shi daga lab. Don har ranta tana ƙaunar Nana. A shekarun nan biyu yarinyar ta wani shiga ranta.

Gabanta na faɗuwa ta buɗe envelop ɗin ta zaro takardun da na Nana da na Fu’ad ɗin. Kallonta Safiyya take idanuwanta cike da buri.

Runtse idanuwa Dr. Jana ta yi. Lokaci ɗaya wata irin zufa ta karyo mata. Kallon Safiyya ta yi.

Da kallo ɗayan da ta yi mata komai ya tarwatse. Da wannan kallon ta ji dalilin rayuwarta ya ƙare. Da wannan kallon da ta yi mata ta ji ta ƙarasa rasa komai na duniya.

Cikin wata irin murya da ba ta gane tata bace ta ce,

“Wata nawa nake da?”

Buɗe baki Dr. Jana ta yi Safiyya ta ɗaga mata hannu tare da sake maimaita tambayarta.

Sauke numfashi Dr. Jana ta yi tana jin idanuwanta na cika da hawaye.

“Da yanayin yadda komai ke spreading, ƙasa da wata huɗu.”

Miƙewa safiyya ta yi. Tana jin yadda ƙafafuwanta ke takawa sai dai komai ta ke ji kamar ba nata bane ba. A haka ta fice daga office ɗin ba ta ko kula da cewar ba ta ja mata ƙofar ba.

*****

Tsaye suke nesa da office ɗin kaɗan shi da Lukman yana jin yadda yake faɗa mishi komai zai yi dai dai in shaa Allah.

Bai ce uffan ba. Shi kaɗai ya san halin da zuciyarshi take ciki. Ganin Safiyya ta fito ya sa daga shi har Lukman suka ƙarasa inda take.

“Sofi…”

Juyowa ta yi ta kalle shi kafin ta ci gaba da tafiya. Zuciyarshi ya ji ta ci gaba da dokawa. Ita kanta ba ta san inda za ta ba.

Wani waje take son zuwa inda ba kowa. Inda babu wanda ke ciki sai ita da halin da take ji. Da sauri Fu’ad ya bi ta.

Tare hanyar ya yi. Yana mata wani kallo cike da bincike. Idanuwanta ta ɗago ta sauke cikin nashi tana son ya ga yadda zuciyarta ke ciwo.

Girgiza mata kai yake yi.

“No, Sofi. Don Allah karki faɗa min. Please na roƙe ki banda sauran zuciyar da za ta ɗauki wani rashin.”

Ƙafafuwanta ta ji sun kasa ɗaukarta. Durƙushewa ta yi a wajen ta sa fuskarta cikin hannunta tana sakin wani irin kuka marar sauti.

Matsawa yake da baya. Ya kasa gane me ke shirin faruwa da shi. Babu abinda ya ke gani cikin idanuwanshi yana gilma mishi banda fuskar Nana.

Lukman ya dafashi a tsorace ya ce,

“Fu’ad ya akai?”

Ture hannunshi ya yi yana ci gaba da ja da baya a hankali kafin ya juya da gudu ya nufi hanyar office ɗin Dr. Jana, bai damu da yadda Lukman ke ƙwalla mishi kira ba.

Tura ƙofar ta ji ba na wasa ba ne. Da sauri ta ɗago kai ta sauke idanuwanta kan fuskar Fu’ad.

“Yes ko No?”

Ji take da da yadda za ta yi da ta yi. Sai dai babu. Ko da an yi transplant ɗin ma ba wai warkewa za ta yi ba. Lokaci ne ake sa ran zata ƙara samu.

Muryarta can ƙasa ta ce mishi,

“No.”

Lumshe idanuwanshi ya yi. Yana jin yadda zuciyarshi ke rugujewa kala daban da na lokacin barin shi Nigeria.

Juyawa ya yi hannuwanshi cikin aljihun wandon shi. Yana jin yadda girman kalmar da Jana ta faɗa ke samun waje cikin jikinshi.

A hankali komai ke tafiya kafin ya kai inda zai zauna daram. Iskar asibitin ta mishi kaɗan. Lukman ya ga ya sha gabanshi.

“Fu’ad…”

Kallon Lukman ya yi. Kallon shi yake da roƙo cike da idanuwanshi kamar hakan zai sa Lukman ya taimaka ya karɓi kaɗan daga cikin nauyin da zuciyarshi ta yi mishi.

“Fu’ad kai min magana please. Safiyya ma ta ƙi cemin komai. Wai mene ne?”

Yana jin yadda iskar ta yi mishi kaɗan. Don numfashin shi har ya soma samun matsala. Yana fitar da shi da sauri-sauri ya ce,

“Lukman my little girl. Yarinyata… Yarinyata Lukman…”

Yadda yake watsa hannaye yana jan numfashi ya sa Lukman kama shi ya ja shi gefe yana jingina shi da bangon wajen.

“Calm down. Me yake faruwa?”

Numfashin shi ya ƙi kaiwa inda yakamata har yanzun. Yana jin yadda komai yake amsa wa cikin kanshi.

“Mutuwa za ta yi Lukman…”

Ware idanuwa Lukman ya yi yana jin yadda tashi zuciyar ke karyewa. Kallon Fu’ad yake da ko:ina na jikinshi kyarma yake.

Haneef ya hango yana tahowa. A hankali ya ƙaraso inda suke. Kallo ɗaya ya hi musu ya san ba lafiya ba.

“Lukman?”

Ya tambaya a ɗan tsorace. Cike da wani irin yanayi Lukman ya ce,

“Nana…”

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un…”

Haneef ya faɗi yana kallon Fu’ad, don in shi yana jin zuciyarshi na mishi wannan zafin bai san yadda ta Fu’ad take ba a yanzun.

Hannu ya kai a hankali ya dafa kafaɗar Fu’ad ɗin sai lokacin ya ɗago. Hawaye ne suka biyo fuskarshi. Abinda rabon da Haneef ya gani tun suna ƙanana.

Zame jikin shi Fu’ad ya yi ya haɗa kanshi da gwiwa. Kuka yake kamar karamin yaro. Nana mutuwa za ta yi. Shine abinda yake ta masa yawo.

Dafa shi Lukman zaiyi Haneef ya riƙe shi yana girgiza masa kai. Wannan ba abu bane da kowa zai iya taimaka mishi.

Dole subar shi. Shi da kanshi zai yi accepting abinda ke faruwa. Fu’ad kam bai taɓa jin duniya ta mishi ƙunci ba sai yau.

‘Yar shi da ko damar saninta bai samu ba. Kuma wannan ba laifin kowa bane saina Safiyya. Sofi ta ɓoye mishi ita gashi yanzun mutuwa za ta yi.

Miƙewa ya yi ya sa hannu ya goge fuskar shi yana shaƙar iska mai nauyi kafin ya fitar da ita. Daga Haneef har Lukman kallo suka bishi da shi.

Hanya ya nufa da Lukman kaɗai ya san safiyya ce a wajen. Don haka ya bi bayansh. Haka ma Haneef. Tana nan zaune inda suka barta tana wani irin kuka.

Ƙarasawa Fu’ad ya yi dab da ita. Ta ɗago da jajayen idanuwanta da fuskarta da ta kumbura ta kalle shi. Wani irin abune cikin idanuwanshi.

Muryarshi a dakushe ya ce,

“Saboda ke ba zan san abubuwa da yawa ba akan Nana. Saboda ke na rasa shekaru goma sha ɗaya na rayuwa tare da ita. Ba ke ya kamata ki yi kuka ba Sofi. Saboda ko da ace yau babu Nana kina da shekaru goma sha ɗaya a cikin kanki da za ki dinga dubawa kina samun sauƙi. Bani da komai!!! Bani da abinda zan duba na ta banda watanni!!! Wallahi ban san yadda akai zuciyata ta yi kuskuren sonki ba!!!”

“Fu’ad…”

Haneef ya kira shi don ya san yanayin da yake ji zai iya saka shi faɗar abubuwan da zai zo yana nadama daga baya.

Miƙewa Safiyya ta yi ta na kallonshi cike da tsanar da take ji tashi da rashin adalcin da rayuwa take mata ta ko wanne fanni.

Ba – tare da ta kalli Haneef ba ta ce,

“Ka bar shi!  Ka bar shi ya faɗi duk abinda yake so ya faɗa. Ka bar shi ya faɗi son ranshi don bai san kowa ba sai kanshi. Kana da bakin da zaka ɗora min laifi Fu’ad?”

Ji yake kamar ya maƙareta. Ta ya za ta iya tsayawa a gabanshi tana masa wannan kallon kamar shi ne da laifi.

“Kai ka tafi. Ban kama ka na turaka waje ba!  Kai ka zaɓi ka bar ni. Saboda me za ka ga laifina?”

Sosai ya ke kallonta.

“Saboda me zaki kasa ganin a kowanne zaɓi da na yi kece a cikinshi? Kina son yara ni kuma ba zan iya baki ba. Sai na yi laifi don na barki ki auri wanda zai iya baki abinda na kasa?”

Girgiza kai safiyya ta ke tana jin wasu hawayen na zubo mata.

Kama shi Haneef ya yi yana faɗin,

“Wannan ba zai ba ku mafita ba Fu’ad…”

Ƙwacewa ya yi yana kallon shi da faɗin,

“Ni na yi mata laifi, in ma laifi ne Haneef saboda me za ta hukunta mu har da Nana? Saboda me za ta hanamun rayuwa da ‘yata?”

Ya ƙarasa maganar da wani sanyin murya da ya karyawa daga Haneef har Lukman zuciya. Muryarta can ƙasa Safiyya ta ce,

“Na nemeka. Na nemeka daga lokacin da na gane ina da cikin Nana. Na neme ka Fu’ad gaba ɗaya numbers ɗinka a kashe.”

Kallonta yake yana tuna yadda ya kashe wayoyinshi gaba ɗaya na tsayin watanni. Kafin cikin ɗaga murya da kuka Safiyya ta ce,

“Ya kake so in yi?! Meye ban yi Akan sonka ba? Saboda me za ka ɗauka kai kaɗai ne za ka rasa Nana? Ko ka ɗauka ka fini sonta ne?”

Kallon Lukman ya yi.

“Ka ji ta ko? Ka ji ta ko Lukman. Zan ɗauki yarinyata. Zan kaita ko wacce ƙasa ta duniya. Zan kashe komai da na mallaka don ta samu lafiya.”

Wata dariya Safiyya ta yi da ba ta san daga inda ta fito ba.

“Welcome to reality Fu’ad Muhammad Arabi. Inda tarin dukiya ba zai maka amfanin komai ba! Zunubanmu ne muke girba ta wannan hanyar. Wallahi fushin iyaye ne muke gani.”

Kuka take sosai. Kalamanta sun girgiza shi. In haka rasa ɗa yake me su Abba suka ji da ya tafi? In haka soyayyar yara take wacce iri su Momma ke masa da yake ɗauka a arha? Tabbas Safiyya ta faɗi gaskiya. Gaskiya Sofi ta faɗa. Barin iyayenshi ne ke bibiyarshi. Fushin Abba ne yake bibiyarshi.

Kallonta ya yi da wani irin nauyi.

“Za mu gyara komai. Babu wanda zai iya saving Nana. Allah daya ɗora mata ne kawai zai iya.

Sofi za mu gyara komai. Zamu ba kowa haƙuri. Inna da Baba. Su Abba. Zamu fara ganin dai dai in suka yafe mana.”

Hawayen da ke zubo mata ta sa mayafinta tana gogewa. Da wani sabon ƙwarin gwiwa ta kalli Fu’ad.

“Komai zai gyaru in suka yafe mana. Mun yi kuskure na ɗaukar zamu iya tsara rayuwarmu da kanmu.”

Jinjina kai Fu’ad ya yi. A karo na farko yana ganin laifukanshi a shimfiɗe. Haƙiƙa babu mai iko sai Allah. Babu wanda ke tsara komai sai Shi!

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×