Skip to content

Akan So | Babi Na Talatin Da Biyu

0
(0)

<< Previous

Da sallama ya tura ƙofar, yana shiga ɗakin gefen gadon Nana ya zauna. Idanuwan nan nata ta ware akan fuskarshi.

Ya yi mata murmushi tare da faɗin,

“Ruwan nan kawai zai ƙare mu tafi gida.”

Safiyya da ke gefe ta ja numfashi tare da cewa,

“Me ka je ka yi?”

Cikin fuska ya kalleta. Ya wani yi narai-narai da idanuwa.

“Ni kam me zan yi?  Roƙonta na yi kawai.”

Taɓe baki Safiyya ta yi, don ta san roƙo yana ƙarshen littafin Fu’ad da ba kowane ya ke gani ba. Da fara’a Nana ta ce,

“Thank you M.”

Da confusion yake kallonta.

“M?”

Ya maimata da alamar tambaya. Puppy eyes Nana ta yi ta na faɗin,

“Oh-oh…”

Ɗaga mata gira Fu’ad ya yi yana ɗan daƙuna fuska alamar ita ya ke jira ta yi masa bayani. Kallon Safiyya ta yi ta ɗan ɗaga mata kafaɗa da ke nufin ita ta fara sai ta ƙarasa.

Sauke numfashi Nana tayi. Cikin sanyin murya ta ce,

“Mumny ta faɗa min kana stunts da, and ana kiranka da Moh. Ina tsoron kar in yi claiming wani dangantaka tsakanin mu kaƙi dawowa.

Shi ne na ke kiranka M. M koda yaushe.”

Wani abu ya ji ya yi squeezing a Kjirjinshi. Safiyya ya zuba ma idanuwa yana tunanin me ye abinda ta gaya ma Nana dazaie saka ta wannan tunanin.

Tambayar shi ta ke karanta cikin idanuwanshi ba tare da ya furta ba. Haɗe fuska ta yi don ba ta san me ya ke so da ita ba. Bayan ya watsar da ita tsawon shekarun nan.

Tun dawowarshi Safiyya ke ɓata mishi rai. Kamar duk tsawon shekarun nan da ta ja mishi nisanta da ita bai ishe shi ba. Sai ta ƙara da saka wa ‘yarshi wannan tunanin.

Bai san lokacin da ya ce,

“Shekararta nawa?”

Yana jin wani zafi a ƙirjinshi. Ba tare da fahimtar dalilin tambayarshi ba Safiyya ta ce,

“Eleven…”

Lumshe idanuwanshi Fu’ad ya yi yana dafe goshin shi da ya ke jin wasu abubuwa na mishi yawo. Shekaru sha ɗaya na rayuwar Nana ya rasa.

Miƙewa ya yi. Yana son fita ya ɗan sha iska kafin ya faɗi wata maganar da ba ya so Nana ta ji. Ji ya yi an riƙo hannun shi. Juyowa ya yi ya kalli Nana da idanuwanta suke cike da hawaye.

Girgiza mishi kai ta yi.

“I am sorry na kiraka M. Ban san wane suna kake so ba. Please karka tafi.”

Wani irin rauni zuciyarshi ta yi. Numfashi ya ke fitarwa da sauri-sauri saboda yadda ya ke jin gara a ce asibitin nan ne ya baje da hawayen da ke cikin idanuwan Nana.

Da sauri ya samu waje gefenta ya zauna. Hannuwanshi ya sa ya tallabi fuskarta. Muryarshi a dakushe ya ce,

“Babu inda za ni Princess. Ina nan tare da ke…”

“Ummmm.”

Safiyya ta faɗi alamar ba ta kama zancen ba. Yana jinta hakan kuma ya mishi ciwo ba kaɗan ba. Zai sauke mata in ba sa gaban Nana.

Zai iya ɗaukar duk rashin kunyarta da ta koya yanzu. Banda gaban Nana. Ƙarshen abinda zai so shi ne ta sa wa ‘yarshi yi mishi wani kallo na daban.

Miƙewa Safiyya ta yi ta fice ta na ɗan doko ƙofar da ƙarfi. Ya bi ta da kallo kafin ya mayar da kallonshi kan Nana da ta yi murmushi ta ce,

“Karka damu. Na yarda da kai.”

Ware idanuwa ya yi. Kafin ya yi’ yar dariya. She is smart. Ya faɗi a cikin zuciyarshi. Kafin ya ce wani abu Nana ta ce,

“Za ka zauna da mu?”

Dariya ya yi.

“Kina son mumynki ta yankani ko?”

Dariya ta ke sosai. Inda rayuwa za ta tsaya a haka zai iya cewa farin cikin da ta miƙo mishi mai ɗorewa ne.

*****

Dr. Jana na hango Safiyya ta ƙarasa wajenta tare da faɗin,

“Na so mu riƙe Nana sai zuwa gobe. Ba zan iya da masifar babanta ba.”

Sauke ajiyar zuciya safiyya ta yi.

“Don Allah ki yi haƙuri…”

Murmushi Dr. Jana ta yi mata tare da faɗin,

“Karki damu. Ko zazzaɓi kika ji jikinta ku dawo. Abin na spreading da sauri fiye da yadda mu ke zato.”

Wasu hawaye suka ciko idanuwan Safiyya. Addu’a ta ke Allah ya sa Fu’ad ya zo dai dai da abinda ake buƙata. Dafa mata kafaɗa Dr. Jana ta yi sannan ta wuce.

Mayafinta ta janyo ta na goge idanuwanta. Sannan ta wuce ta koma. Zaune ta same su Fu’ad yana ba Nana labari.

Kallonsu ta ke. Ta kasa nutsuwa da shi. Tana tsoron kar tarihi ya maimaita kanshi. Wata zuciyar ta ce koma menene ya zo ai. Kuma yana nan yana son taimakon Nana.

Za ta maida hankali  akan wannan kawai. Za ta danne son shaƙe shin da ke taso mata. Za ta yi ƙoƙarin ɓoye abinda ya faru tsakaninsu inda ya ke duk shekarun nan.

Gyara zama ta yi ta na kallonsu. Da yadda suka yi kama ba ‘yar kaɗan ba. Ko mintina goma ba a yi ba ruwan da ke jikin Nana ya ƙarasa ƙarewa.

Tasowa Safiyya ta yi ta kashe. A tsorace Fu’ad ya kalleta.

“Me kike yi?  No, kirawo Doctor su zo su cire mata.”

Kallon da gaske kake? Safiyya ta yi mishi kafin ta koma kan abinda ta ke ƙoƙarin yi.

Miƙewa ya yi a dake ya ke faɗin,

“Da gaske nake. Ba aikinki ba ne, ba za ki taɓa min yarinya ba…”

Wata dariyar takaici ta ɗan ƙwace mata. Ƙarfin hali ta ke kallo ƙiri- ƙiri. Yana son nuna mata ya fi ta damuwa da Nana ne.

Riƙo hannunshi Nana ta yi tare da faɗin,

“It’s ok. Ta na cire min wani lokaci.”

Girgiza ma Nana kai ya yi idanuwanshi na kafe kan Safiyya tare da faɗin,

“Lokacin ba na nan ne…”

Buɗe baki ta yi za ta amsa shi. Dr. Jana ta shigo ɗakin. Hankalinshi Fu’ad ya mayar kan ta da cewa,

“Wane doka ya ba ku damar barin wanda ba Doctor ko nurse ba taɓa marar lafiya?”

Safiyya ta kalla. Don ba ta ma gane kan tambayarshi ba.

“Ignore him. Yana jin daɗin magana shi kaɗai wasu lokutan.”

“WTF Sofi.”

Idanuwanta ta ware mishi da ke nuna a shirye ta ke ta biye mishi su kwashi ‘yan kallo a gaban Nana. Mayar da maganar da ya ke shirin yi ya yi.

Dr. Jana ta wuce ta zare ma Nana ruwan. Ta cire abin daga hannunta ta sa auduga ta na danne wajen kafij ta sakarwa Nana.

Da sauri Fu’ad ya kamo hannun yana saka audugar ya danne mata.

“Sannu.”

Murmushi Nana ta yi. Tana kallon yadda ya ke daƙuna fuska kamar abin a hannunshi ya ke. Hakan kuwa ya ke ji har ranshi.

Dr. Jana ta ce,

“Please ko ciwon kai ta ke ji ku dawo da ita.”

Kai suka jinjina mata su duka biyun ta kalli Nana ta ce,

“Allah ya ƙara sauƙi.”

Da murmushi a fuskarta ta amsa da,

“Amin Anty Jana. Me ke damunki?”

Da mamaki sosai Dr. Jana ta kalli Nana. Sosai ta ke jin mamakin tambayarta. Hakan ya sa Nana faɗin,

“Ko yaushe kina min hira har ki gama dubani. Banda yau da safe da yanzun kuma.

Kina kawomun milkshake ko zuwa muka yi ban kwana ba. So kawai wani abu na damunki.”

Lumshe idanuwa Dr. Jana ta yi. Tana buɗe su kan Safiyya. Allah ya ba ta yarinya mai tattare da baiwa kala-kala.

Safiyya ta ce,

“Nana…”

Hannu Dr. Jana ta ɗaga mata alamar babu komai. Tsakaninsu ne. Hankalinta akan Nana ta ce,

“Yeah wani abu na damuna. Karki damu i will be ok. Sorry ban kawo miki milkshake ɗin ba. Kina bina, ok?”

Murmushi ta yi har haƙoranta suka fito.

“Alright na gode Anty Jana. Kiyi addu’a komai mai wucewa ne tunda kina da lafiya.”

Wannan karon Fu’ad ne ya ware idanuwanshi kan Safiyya da tambayar ‘haka Nana ta ke so smart ko kuma shi kaɗai ne ya kula.’

Kai ta ɗan rausayar gefe da nufin ‘Haka na ke fama.’ Murmushi ya yi da ya kai har zuciyarshi. Raɗa ya yi wa Safiyya da,

“She is my daughter.”

Dake nuna dole ta zama smart. Wato ta biyoshi. Dariya Safiyya ta yi da ta janyo hankalin Nana da Dr. Jana kanta. Ta ɗan haɗe fuska.

Miƙewa Dr. Jana ta yi ba ta ce musu komai ba ta fice. Rankwafawa Fu’ad ya yi ya kama Nana yana ɗorata kan kafaɗarshi.

Dariya ta kama yi ta na faɗin,

“Ka sauke ni zan iya tafiya da kaina fa…”

Girgiza mata kai ya yi. Yana ƙara gyara mata zama a kafaɗarshi.

“Princess ba sa tafiya da Kafarsu.”

Dariya ta ke yi sosai. Safiyya ya ke kallo ta na tattara kayyakinsu cikin wata jaka. karasawa ya yi yana ƙoƙarin ɗaukar jakar.

Ta janye tare da watsa mishi wani kallo.

“Ba na so.”

Ɗan ɗaga kafaɗa ya yi alamar matsalarta ce. Ya wuce ya buɗe ƙofar ya fita da Nana da ke ta mishi surutunta.

Sauke ajiyar zuciya Safiyya ta yi. Lokaci ɗaya ya shigo rayuwar Nana ya sace zuciyarta. Yadda ‘yan uwanshi sukai mishi ɗazun bai ba ta mamaki ba.

Son shi ba ya bari a ga laifinshi. Wannan a jininshi ya ke. Ɗaukar jakar ta yi da mukullin motarta da ya ajiye gefen gadon Nana ta bi bayansu.

Tsaye ta samu Fu’ad Nana na kan kafaɗarshi. Buɗe musu motar ta yi. Baya ya buɗe ya saka Nana shima ya shiga.

Kallonshi ta yi. Ya wani kauda ido. Ita za ta tuƙa. Inda ya ke zaune nan Nana za ta zauna. In tsarin bai mata ba ta dawo baya su koma gaba.

Ta karance shi tsaf don haka ta zagaya ta buɗe motar ta shiga ta tayar ta ɗauki titi.

*****

Tana shiga cikin gidan ta ga motar Nawaf. Lumshe idanuwanta ta yi ta na sauke ajiyar zuciya. Tsayawa ta yi na wajen mintina biyar tana ƙoƙarin mayar da fuskarta dai-dai.

Ganin Farhan ba ƙaramin girgiza ya zo mata da shi ba. Ta kuma san Nawaf kamar yunwar cikinta. Yana karantar komai a fuskarta. A hankali ta taka zuwa cikin gidan ta tura ƙofar da sallama.

Yana jingine da bango a tsaye. Ya ɗago idanuwan nan ya sauke su akanta. Yanayin su ta gani ta yi tsaye ta ƙi ƙarasawa ciki.

Takowa Nawaf ya yi ya zo daf da ita yana fitar da numfashi da sauri da sauri. Muryarshi a dakushe ya ce,

“Waye kuke tsaye da shi a bakin saloon?”

Wani irin dumm ta ji cikin kunnuwanta kafin zuciyarta ta ɗauki duka. Tambayarshi ta girgiza ta. Abinda ta tsaya tana ƙoƙarin boyewa ne.

A tsawace ya ce,

“Tambayarki nake Nuri.”

Ja ta yi da baya kaɗan. Ya damƙo hannunta kamar zai karyata. Ƙoƙarin Kwace hannunta take yi ta kasa. Jijjigata ya yi yana faɗin,

“Da wa ki ke magana Nuri? Waye shi?”

Cikin kuka ta ce,

“Ka sake min hannu…”

Mari ya ɗauke ta da shi yana ƙara jijjigata.

“Ki faɗa min waye kike tsaye dashi?”

Ba ta san lokacin da wani ƙarfi ya zo mata ba. Ture shi ta yi gefe tana sakin wani irin kuka.

“Farhan ne! Sai ka ƙyale ni yanzu ko?”

Ta ƙarasa maganar ta na goge fuskarta. Wani irin abu zuciyarshi take yi. Duhun nan ya cika mishi kai. Janyota ya yi ya haɗata da bangon ɗakin.

Ya ci gaba da dukanta kunnuwanshi ba sa jin ihun da Nuri ke yi. Maigadin gidan ya ji ihun ya yi yawa daga inda yake ya shigo ya ga ko lafiya.

Salati ya saka yana ƙoƙarin janye Nawaf. Amma kamar ma sake tunzura shi ya ke. Tun Nuri na ihu har ta daina saboda ta yi laushi ba kaɗan ba.

Da ƙyar maigadi ya janye Nawaf da ya fice daga gidan don in yana ganin Nuri bai san abinda zai iya faruwa ba. Girgiza kai kawai maigadi yayi da ya ga Nuri ta motsa ya fice.

Don shigowar da ya yi ma ba huruminshi ba ne. Ji ya yi abin sai addu’a. Da wani irin ƙarfin hali ta na hawaye ta ja jiki ta janyo jakarta da ke gefe.

Kuka ta ke sosai. Ta tabbatar nan gaba Nawaf kasheta zai yi. Ta na jure komai ne saboda ba ta da inda za ta juya ma.

Mamanta ce. Ita kuma da ta koma gidan karuwai gara ta mutu a gidan Nawaf. Ganin Farhan. Ganin Farhan ya sa ta ji tana da zaɓi.

Rayuwa a gidan Nawaf da ya ke tunanin zai jibgeta a duk sanda ya yi niyya saboda ya mata alfarma ta aurenta.

Yanzun ta ke ganin komai a saman farar takarda. Baƙin rubutun ƙaddarar auren Nawaf daro-daro. Yanzu ta sake tabbatar da ‘yan uwan Nawaf da sunsan ɗan uwansu mai lafiya ne ba za su taɓa bari ya auri’ yar gidan karuwa da ba asan asalinta ba irinta.

Ko da kuwa liman ne rataye a saman kanta saboda kamun kai. Hakan da ƙarin ba ta da inda za ta ya sa take shanye duk dukan Nawaf.

Ya yi mata alfarma mai girma. Amma ita ma ta mishi. Ta na tare da shi a duk cutar shaye-shayen da ke damunshi. Ta na tare da shi a duk wannan stage ɗin.

Ita ta ba shi ƙwarin gwiwa ta zame mishi mudubi a lokacin da ba shi da inda zai duba fuskarshi. Ita ta zame mishi titin da ya hau ya gane hanya lokacin da ya ɓace.

Ita ce silar shi zuwa rehab.  Har aka shawo matsalar shi ta shaye-shaye sannan suka yi aure. Sannan ‘yan uwanshi suka kauda kai daga mugun gidan da ta fito domin sun san in babu ita zai iya komawa inda babu wanda zai iya taro shi.

Dafa ƙasa ta yi da niyyar tashi wani irin ihun azaba ta saki jin wani zogi da ta yi har cikin ranta. Hannunta ta riƙe da ɗayan tana juyi saboda azaba.

Kuka take sosai. Ɗayan hannun mai lafiyar ta dafa da shi ta miƙe zaune hawaye na zubo mata. Ko ina na jikinta ciwo ya ke.

Mayafinta da ke gefe ta janyo ta goge bakinta inda ya fashe sannan ta mayar gefen fuskarta tana flinching saboda zogin da wajen yake mata.

Jakar ta janyo ta fito da wayarta. Lambar da Farhan ya ba ta tun a napep ta haddaceta ta yaga takardar. Hannunta na rawa take shigar da lambar ta kira ta kara a kunne tana wani irin kuka..!

****

Hamma ya ga Nana na yi. Ya ce mata,

“Bacci ko?”

Ta ɗaga mishi kai. Janta ya yi ya kwantar da kanta a cinyarshi yana jin wata irin kaunarta na shigarshi.

Can ƙasan zuciyarshi wani abu na daban yana tafasa. Abinda ya kamata ace yana yi ne shekaru sha ɗaya. Sai yau ya samu dama kawai saboda Safiyya ta zaɓi ta ɓoye mishi ita.

*****

Sanda suka ƙarasa gida Nana har ta yi bacci. A hankali Fu’ad ya daaukota daga motar. Safiyya ta karasa ta buɗe musu gidan.

Kan kujera ya kwantar da Nana. Har ya miƙe da sauri ya ce ma Safiyya,

“Ba zata faɗo ba?”

Bata kalle shi ba ta amsa da,

“Damuwata ce wannan.”

A ƙufule Fu’ad ya ke kallonta.

“Me kike nufi?”

“Duk abinda ka fassara.”

Motsi ya ga Nana ta yi. Da sauri ya kai hannu ya ɗan tallabeta.

“Damn it sofi. Karta faɗo fa.”

Sauke numfashi ta yi. Ya soma isarta kuma.

“Kana ina shekara goma sha ɗaya. Sai yau ne za ka damu da faɗowarta? Kana ina ka tallabeta lokacin da ta faɗo duniya?

So please ba ka da wajenta a rayuwarka. Ba ka da lokacin asara a sonta. Karka dame ni.”

Tafasa zuciyarshi take yi.

“Karki fara. Karki fara ɗora lefin akaina. Bana nan saboda ba ki neme ni ba.

Bana nan saboda kin zaɓi ki ɓoye min ita…”

Dakatar da shi ta yi tana jin yadda ya ke taso mata da ɓacin ran da ta jima ta na binnewa. Cikin idanuwa ta kalle shi.

“Ba kama ka na yi na turaka waje ba. Ƙafafuwanka ka ɗauka ka fice.

Me kake tunani?  Duk abinda na yi Akan sonka bai isheka ba? Ko a lokacin ina da sauran abinda ya rage in ba ka?

Na ba ka zuciyata Fu’ad. Na bar duniyata na shigo taka. Na bar kowa nawa saboda kai…”

Tana jin wasu hawaye masu ɗumi na zubo mata. Kallonta ya ke yana jin zuciyarshi na auna nauyin maganganunta.

Wani murmushi ya yi da bai kai zuciyarshi ba.

“Sofi ba sai kin jefo min abinda ki ka yi akaina a fuska ba. Ina sane dashi. Saboda me ni ba za ki duba abinda na yi akanki ba?  Ba za ki duba girman abinda na yi miki ba?”

Ba ta son ganin shi sam. Saboda yadda take tunanin ɗazun tsanarshi na gogewa daga zuciyarta shirme ne. Tana nan daram.

“Ka fice min daga gida please. Don Allah ka tafi.”

Nana ya kalla. Sannan ya sake kallon Safiyya. Bai sake ce mata komai ba ya fice daga ɗakin. Son kai. Son kan Sofi ya yi yawa.

Da wannan tunanin a zuciyarshi har ya kai titi ya tari taxi zuwa hotel ɗin da ya sauka.

*****

Kwance yake kan kujera cikin falon gidan nashi. Kallon ko’ina na ɗakin ya ke da irin kayan ƙawa na duniya da ke ciki.

Wanda sam ba su da amfani a wajenshi. Ƙirjinshi zafi ya ke mishi sosai. Tunda ya dawo numfashi ya ke yana tafiyar da komai yadda ya kamata a yi bawai don yana jin daɗin shi ba.

Daɗin me za ka ji na duniya in babu kowa da ya rage maka wanda ka damu da shi? Nuriyya ce last hope ɗin shi na jin daɗin rayuwa.

Ita kaɗai ta rage mishi da yake jinta kamar family. Komai ya tarwatse mishi da ya ji ta yi aure. Ya yi yunƙurin nemanta ya fasa saboda yana gudun kar ganinshi ya ja mata matsala.

Yasan ba kowane zai iya auren Nuriyya ba duba da inda ta fito. Wanda duk ya aureta dole yana sonta. Soboda yasan Akan sonta dole ya yi rikici da ‘yan uwanshi akan asalinta.

Waɗannan dalilan su ya riƙe. Su suke tare shi daga neman Nuriyya sai yau. Da ya ganta inda bai taɓa zato ba. Ya kasa jurewa sai da ya yi mata magana.

Sai dai ga mamakinshi duk abinda ya hanashi nemota ƙarya ne. Ba haka abin ya ke ba. Daga yanayinta kawai ya san meke faruwa a rayuwarta.

Saboda ba baƙon abu bane a tashi rayuwar. Cikinshi ya taso tun wayonshi har ya zuwa yanzun. Ya kuma jima da sanin matan da suke cikin irin halin da Nuriyya ta ke ba ƙaramar matsala ba ne.

Ba ka da yadda za ka yi ka taimaka musu in har ba su suka ba ka dama ba.  Ya gani akan mahaifiyarshi har rasuwa ta risketa.

Wayarshi da ta yi ringing ba ƙaramin taimaka mishi ta yi ba don har ya soma saka wuƙa yana tona ciwukanshi. Wayar ya ɗauka da ta ke ajiye kusa da kanshi. Baƙuwar lamba ce.

Ɗagawa ya yi tare da faɗin,

“Hello?”

Murya a sarƙe ya ji an ce,

“Yaya Farhan…”

Da sauri ya miƙe daga kwanciyar da yake yana tattara dukkan hankalin shi kan wayar. Ya sa hannu biyu ya riƙe ta.

“Nuri. Nuriyya kina lafiya?”

Yana jin yadda kuka ke sarƙeta ta cikin wayar da yake ƙona mishi rai.

“Nuri ki minmagana. Dukanki ya yi ko?”

Da kyar ta iya cewa,

“Eh.”

Wani abu da ya ji ya taso mishi tun daga ɗan yatsan ƙafarshi ya yi tsaye a ƙirjinshi yana tafasa. In aka ba shi bindiga maza masu dukan matansu zai fara harbewa.

Saboda babu zalincin da ya kai wannan. Har wani huci yake. Muryarshi a dake ya ce,

“Calm down Nuri. Ba ke kaɗai bace. I am here. Faɗa min address ɗin gidan.”

Da ƙyar ta iya karanto mishi. Miƙewa ya yi da wayar a kunnenshi ya ɗauki mukullin mota. Ko gidan bai ja ba. Ya ƙarasa wajen motarshi yana faɗin,

“Zan zo yanzun kina jina. Ki kulle ɗakinki. Karki buɗe mishi sai kin ji na kira ki.”

Ba ta amsa ba ta kashe wayar. Ya shiga mota ya yi baya da ita. Maigadi ya buɗe mishi ya fice daga gidan yana addu’a ya samu sanyi ko ya yake a zuciyarshi kafin ya ƙarasa.

*****

Yana zuwa alwala kawai ya yi. Anan ya yi sallar azahar. Don kafin ya fito ya nemi masallaci lokacin sallar ya ja sosai.

Tunawa ya yi ya kamata ya sa ma cikinshi wani abu duk da bakinshi ba ya so. Sawa ya yi a kawo mishi fried rice da farfesu. Da ƙyar ya iya cin rabi. Ya kira room service suka fita da kayan.

Wanka ya sake yi ya fito ya kwanta. Idanuwanshi ya rufe babu komai a cikinsu banda Nana. Dariyarta. Murmushinta zai iya rantsewa sautin muryarta har cikin zuciyarshi yake jinta.

Bacci ya ɗauke shi cike da mafarkin Nana.

*****

Sanda ya tashi har anyi la’asar. Don haka sallah ya yi. Yana zaune a inda ya yisallah wayarshi ta hau ruri. Ɗagawa ya yi ya ga lambar Lukman.

Ya amsa da faɗin,

“Hello…”

“Kuna asibitin ne har yanzun?”

A sanyaye ya ce,

“A’a an sallame su. Suna gida. Ni ina hotel ɗin da na sauka.”

Tambaya Lukman ya yi ko a ina ne. Ya faɗa mishi ya ce ya jira shi ga shi nan zuwa.

Ko mintina talatin ba a yi ba ya sake kiran Fu’ad cewar yana wajen hotel ɗin. Wayarshi ya ɗauka da mukullan ɗakin ya fito.

*****

A mota ya samu Lukman zaune. Ya buɗe ya shiga. Shiru suka yi su duka kowa ya rasa me zaice ma kowa kafin Fu’ad ya ce,

“This is awkward.”

Dariya Lukman ya yi.

“Ban san ta inda zan fara ba.”

Murmushi Fu’ad ya yi tare da faɗin,

“Banda abin faɗa. Daga lokacin da na tafi babu komai a rayuwata banda ball. So banda abin faɗi.”

Nisawa Lukman ya yi.

“Ina da zainab. Da Junior da wani yana hanya mace ko namiji.”

Da mamaki Fu’ad ya kalle shi.

“Kana da mata da yaro Lukman?”

Kai ya ɗaga mishi. Wani nauyi zuciyarshi ta yi. Bai san ta inda zai fara kamo abubuwan da ya saki ba.

“Ina jin nauyin in ce ka kaini in gansu Lukman.”

Shi kanshi wani iri ya ke ji. Sun rasa abubuwa da yawa a tsakaninsu. Da wani yanayi a muryarshi ya ce,

“Kiran da za ka yi shegen taurin kai ya hana ka.”

Dariya Fu’ad ya yi.

“Irin wanda ya hanaka kirana ko?”

“Shut up.”

Lukman ya faɗi yana tayar da motar. Fu’ad bai ce komai ba har suka nufi hanyar da ya ke tunanin gidan Lukman ne.

Yadda rayuwa ta tafi da sauri haka yake mamaki. Ba shi da komai da yake kallo balle ya ga gudunta!

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×