Skip to content

Akan So | Babi Na Talatin Da Daya

0
(0)

<< Previous

Wani sama-sama ya ke jinshi. Ƙarar motocin da ke wucewa can ya ke jinsu a nesa. Saboda abu ɗaya ne ƙwaƙwalwarshi ke iya processing a yanzu.

‘Yar shi na da cancer’. Can sama-sama ya ke jin kamar muryar Sofi na kiranshi. Bai ko bi takanta ba saboda ba ta gabanshi a yanzun.

Komai na rayuwarshi a gefenshi ya ke a ajiye. Nana ce kawai ya riƙe gam tun da ya sauke idanuwanshi akanta.

Da gudu Safiyya ta ƙarasa ba ta damu da mutanen da ke wurwucewa ba. Ta sha gabanshi. Kallonta ya ke ya dauna fuska alamar bai fahimci me ta ke yi ba.

“Ba don na damu ba. Nana ta farka ta na tambayarka…”

Jin sunan Nana ya sa shi ware idanuwanshi akanta sosai. A tsorace ya ce,

“No ba zan iya ba. Ba zan iya facing ɗinta ba…”

Kallonshi Safiyya ta ke yadda ya ke girgiza kai yana ɗaga hannuwa. Lokaci ɗaya ta ga girman da Fu’ad ya yi a jikine kawai da fuska.

Har yanzu zuciyarshi akwai yarinta fal a cikinta. Sosai ta kalle shi.

“Shi ya sa na ce kar ta sake ta saka a zuciya don ba ka da wajenta…”

Wani abu ya ji tun daga yatsan ƙafarshi ya taso mishi har cikin ƙirji. Safiyya na son kule shi ya kula. Bai ce mata komai ba ya juya ya na komawa hanyar asibitin.

Ɗan karamin murmushi ta yi ta bi bayanshi. Har suka shiga cikin asibitin. Yana zuwa bakin ƙofar ɗakin da Nana ta ke ya riƙe hannun ƙofar ya yi tsaye.

Gabanshi faɗuwa ya ke sosai. Nan Safiyya ta ƙaraso ta same shi. Kallonta ya yi kamar zai yi kuka.

“Em’ scared Sofi…”

Sauke ajiyar zuciya ta yi. Ta na jin yadda duk inda ta cika da tsanarshi a zuciyarta ya fara gogewa. Sauke idanuwanta ta yi.

Ta ƙarasa ta raɓa gefenshi ta tura ƙofar ta shiga ta bar shi anan tsaye. Kamar mai ciwon wuya ya ɗan zira kai ya leƙa.

Nana na zaune kan gadon suna hira da Ansar da ke gefenta.

“Mai ƙaton kan nan bai tafi ba kenan…”

Ya faɗi ƙasa-ƙasa. Shiga ya yi a ciki. Sai lokacin Nana ta ganshi. Wani murmushi da ta yi mishi bai san lokacin da ya mayar mata da martani ba.

Ƙarasawa ya yi har inda Ansar ya ke zaune kan kujera. Hannuwa ya sa bayan kujerar ya ja ta baya ji kake wani ƙiiiiiii.

Dariya ce ta kusan kufce ma Safiyya ganin yafda Ansar ke ware idanuwa. Da alama ya tsorata sosai da jin yadda Fu’ad ya ja shi.

Yarinta na cin Fu’ad har yanzun. Ba ta kuma san ranar da zai girma ba. Ko kallon su Fu’ad bai yi ba ya zauna gefen gadon Nana.

Hannu ya sa ya tallabi fuskarta  yana kallon ta da murmushi a fuskarshi.

“Na ɗauka ka tafi. Mum ta ce mun kana nan. Na kasa yarda ne kawai. Ka yi haƙuri ba ni da lafiya ranar da ka zo….”

Da sauri ya girgiza mata kai tare da faɗin,

“Shhhhh Nana. Wani abu na miki ciwo? Em’ here now. Komai zai yi dai dai. Ni da ke zamu yaƙi ko mene ne kina jina ko?”

Wani irin tsalle zuciyar Safiyya ta yi jin kalmar nan ta ‘ni da ke’. Miƙewa ta yi da sauri ta ƙaraso inda Fu’ad ya ke. Cikin idanuwa ta kalle shi.

“Ina son magana da kai.”

Ta buƙata. Wani yatsina fuska ya yi.

“Ina jinki.”

Hanyar waje ta nuna masa da ɗan yatsanta idanuwanta cike da masifa. Kallon Nana yayi ya ce,

“Yanzun zan dawo…”

Ya ƙarasa yana miƙewa tare  da watsa wa Ansar kallon karka soma matsowa kusa da ita. Sannan suka fice shi da safiyya.

Tana jan ƙofar a hasale ta ce mishi,

“Karka sake yi mata alƙawurranka da babu komai a cikinsu sai ƙarya.

Zan iya yin komai akan yarinyata. Ko da hakan na nufin nisantata da kai.”

Kallon da ya ke mata zai tsorata duk wani wanda bai san shi ba. Kafin ya ce,

“Kin ji me kike faɗa kuwa? Nisantata da ni ai kin riga da kin gama. Ba zan yafe miki ba in har wani abu ya sameta.

Akan me za ki ɓoye min ita?”

Kallon shi ta ke da mamaki. Har yana da bakin tambayarta dalili kenan.

“I don’t do happily ever after. Daga ranar da kika yarda da soyayyata ya kamata ki san ban yi kalar wanda zai dinga zarya da yara da pampers ba…!

Ka tuna ko sai na ƙarasa maka?”

Ta faɗi ta na jin wasu hawaye na son zubo mata. Dafe kai ya yi.

“Damn it sofi. Za ki riƙe ni akan maganar da na yi shekaru goma sha ɗaya?

Me kike ɗauka? em’ noh’ gonna accept her. Sofi me kika sha ne?”

Kallon fuskarta ya ke yi. Yanzun kan wannan maganar da ya yi ne zai sa ta ɓoye masa yarinyarshi. Ji ya ke in bai bar ganinta ba komai zai iya faruwa.

Tambaya ɗaya ce a ranshi yanzu. Da ya ji zai bar mata wajen nan. Zai bar kallonta ya na jin yadda zuciyarshi ke yi kamar ta kama da wuta.

“Akwai hope?”

A hankali ta ɗaga mishi kai. Bai jira komai ba ya juya ya shiga ɗakin. Yana shiga Ansar ya miƙe domin ana kiran magriba.

A wajen ya samu Safiyya ya ce mata zai wuce gida. Ta yi mishi godiya sosai sannan ta shiga ta samu Fu’ad zaune gefe yana magana da Nana ta na ta ƙyalƙyalar dariya.

“Bari in yo Sallah in dawo.”

Miƙewa ya yi, sai da ya watsa ma Safiyya hararar da ta zaɓi ta yi biris da ita sannan ya fice. Ajiyar zuciya ta sauke.

Cikin sanyin murya Nana ta ce,

“Ko me ya shiga tsakaninku yana da kirki sosai Mummy.”

Shiru ta yi ta ƙyale Nana don wasu maganganun in ta na yi hankalinta ya girmi shekarunta.

Ita ma alwala ta yo ta dawo ta shimfiɗa ɗankwalinta ta tada sallah don ba su ɗauko komai ba garin sauri.

*****

Tunda ya idar da sallah gaba ɗaya addu’ar shi ta yau babu kowa a cikinta banda Nana. Allah ya ke roƙo da ya hukunta duk laifikanshi ta wata hanyar ya ba wa Nana lafiya.

Yana nan akai sallar isha’i sannan ya bar masallacin ya koma asibitin. Nana ta na bacci. Bai ko kalli Safiyya ba balle ta yi tunanin zai ce mata wani abu.

A hankali ta ce,

“Don Allah ka duba min ita in je gida in dawo….”

Ba tare da ya kalleta ba ya amsa da,

“Ba sai kin tambaya ba.”

Ba ta ce komai ba ta wuce ta tafi. Hannun Nana ya sa cikin nashi ya haɗa kanshi da gadon zuciyarshi na mishi wani irin nauyi.

Tun ranar da ya cika shekaru ashirin da biyu a duniya kamar wata takarda ce ya sa hannu akai. A duk lokacin da ya yi tunanin ya samu farin ciki sai wani abu ya gifta mishi.

Yana nan zaune har Safiyya ta dawo. Ko sallamar da ta yi bai amsa ba. Kanshi na haɗe da gadon Nana. Don zatonta ma bacci ya ke.

Abinci ta zuba ta ɗan ci. A hankali ta ga ya ɗago. Wani plate ɗin ta samu daban ta zuba mishi tare da faɗin,

“Ka sakko ka ci abinci.”

Sai lokacin ya kalleta. Kai ya girgiza mata. Tunanin saka ma cikinshi wani abu a halin da ya ke ciki ma neman saka shi amai ya ke.

Kamar wadda ta yi mishi dole ya ƙara daƙuna fuska ya girgiza kai.

“Na ji ka da farko ai.”

Ta faɗi ta na maida abincin cikin warmer. Matsalarshi ce ko ya ci ko kar ya ci bawai don ta damu ba ne ta ba shi.

“Da ka tafi dare yana yi…”

Kallon da ke fassara kin samu taɓin hankali ya yi ma Safiyya ya kauda kai gefe. Ba shi da lokacin asara akanta yanzu.

“Ka na ji na fa.”

Runtse idanuwa ya yi alamar ta takura shi sosai sosai kafin ya ce,

“Karki sake ɓata min rai Sofi. Ba zai mana kyau ba wannan karon. Ba don ke na ke zaune anan ba.

Saboda yarinyata ne.”

Shiru ta yi ta ƙyale shi kawai. Ya mayar da kanshi jikin gadon ya kwantar hannun Nana na riƙe da nashi.

Ba ta san ko ya yi bacci ba ko bai yi ba. shimfiɗa ta gyara ta kwanta da mayafinta. A karo na farko da bacci ya dauketa in har suna asibiti da Nana.

Don zuciyarta a nutse ta ke ta wani fanni da ya ba ta mamaki.

*****

Sai da ta gama haɗa musu breakfast sannan ta dafa ma Umar indomie ta soya mishi ƙwai ta sa mishi a warmer ɗinshi ta haɗa komai a basket ta ajiye mishi.

Wucewa ta yi ta shiga wanka ta bar Atika ta shirya mata Umar ɗin. Sanda ta fito Jabir na zaune yana danne-danne da wayarshi.

Ba ta bi takanshi ba ta cigaba da shirinta. Gaisuwa ce sun yi ta tun ɗazun. Sai da ta gama shiri tsaf sannan ta ƙarasa inda ya ke zaune.

Fuskarshi ta riƙe cikin hannuwanta ta sumbace shi a gefen fuska tare da faɗin,

“Ka kula da kanka please.”

A sanyaye ya ce mata,

“Ke ma haka. Ina sonki, ki riƙe wannan.”

Murmushi ta yi ta na wucewa. Sai da ta kai ƙofa sannan ta ce,

“Allah ya bada sa’a ya tabbar da alkhairi…”

Kasa jiran amsar Jabir ta yi ta fita da sauri ta ja ƙofar. Bakin ƙofar ta tsaya hawaye suna siraro mata. Hannu ta sa ta goge su tana karanto duk addu’ar da ta zo mata.

Sannan ta sa gilashinta ta fice.

*****

Kitso akai mata bayan an wanke kan. Ba ta son wani ƙananan kitso duk da wadatar gashi da Allah ya yi mata.

Guda sha biyu aka yi mai kyau sosai. Ta rasa me ke damun Nawaf. Yadda ya birkice jiya ba ta taɓa ganin hakan ba.

Duk abinda ya ke bai taɓa zaginta ba. Amma yana yin bacci jiyan ma ya tashi shikenan. Kamar mai Aljanu haka ya tashi garas.

Sauke ajiyar zuciya ta yi. Ta buɗe purse ɗinta ta biya kuɗin wankin kai da kitson da akai mata ta fito.

Gicci ta gani ta ji zuciyarta ta wani irin dokawa. Tsayawa ta yi ta rufe idanuwa tana karanto addu’o’i sannan ta buɗe su ta ci gaba da tafiya.

Wannan ba shi ba ne karo na farko da ta ke tunanin ta ga Farhan ba. Sai kuma ta zo ta ga tunaninta ne ke wasa da ita.

“Nuriyya..!”

Wannan karon ba da wasa zuciyarta ta ke ba wajen dokawa. Yau abin ya yi yawa. Ci gaba ta yi da tafiya.

“Nuriyya…”

Ta ji an sake kira a karo na farko. Da sauri ta juya tako sauke idanuwanta kan kyakkyawar fuskar Farhan. Girgiza kai ta ke cike da rashin yarda. Babu ta yadda za a yi ace Farhan ne a gabanta. Yadda ya ga tana kallonshi ya tabbatar mishi da cewar ba ta yarda shi bane ba. Ta ƙara girma sosai.

“Nuriyya…”

Da hawaye a idanuwanta ta dafe haɓa da hannayenta biyu tana kallonshi. Muryarta na rawa ta ce,

“Yaya Farhan…”

Sauke ajiyar zuciya ya yi. Yana gaya ma zuciyarshi da auren wani akan Nuriyya. Lokaci ɗaya ya fara jero neman gafarar Ubangiji.

Sauke murya ya yi ya ce,

“Kina lafiya? Ba ki da matsalar komai dai ko?”

Hawayen da ta ke tarbewa ne suka zubo mata.

“Yaya Farhan yaushe ka dawo? Yaushe ka dawo ni ban sani ba?”

Da wani yanayi a zuciyarshi mai nauyi da ya ke ƙoƙarin dannewa ya ce,

“Watana bakwai da dawowa. An ce min kin yi aure shi ya sa ban neme ki ba. Ba ki da matsala dai ko?”

Ya ƙarasa tambayar da damuwa sosai a muryarshi na son jin ko ta na lafiya. Kai ta ke ɗaga masa, alamar eh. Lokaci ɗaya ta ga ya sauke ajiyar zuciya kamar wanda aka sauke ma wani nauyi mai girma.

“Ki zauna cikin farin ciki. Shi ne kawai burina. Bai kamata mu tsaya anan ba. Na ganki ne ba zan iya jure ƙin miki magana ba…”

Ta kasa cewa komai banda hawayen da ta ke yi wani na bin wani. Ganin farhan ya mata daɗi. Don tana yawan tunanin ko yana raye ko akasin hakan.

Murmushi ta yi mishi ta sa hannu ta na goge fuskarta. Kamar an ce idonshi ya kai kan gefen fuskarta da har lokacin yatsun Nawaf na kwance ruɗu-ruɗu a wajen.

Ga wani jini da ya ke kwance a saman goshinta. Cike da tashin hankali Farhan ya ce,

“Dukanki ya yi Nuri?”

Cikin hanzari ta girgiza kai. Ƙarshen abinda za ta so shi ne Nawaf ya ma ji ta ga Farhan.

Idanuwa a ƙanƙance Farhan ya ce,

“Ki faɗa min idan yana dukanki. Karki ji tsoron komai.”

Kai ta sake girgiza masa idanuwanta cike da hawaye. Dubawa yake gefe gefe ya hango wani kanti.

“Ki jirani anan. Ina zuwa…”

Da gudu ya ƙarasa wajen shagon ya siyo biro da littafi. Ya yagi takarda ya rubuta mata lambar wayarshi sannan ya dawo.

Miƙa mata ya yi ta karɓa. Ya kalleta sosai cikin fuska ya ce,

“Ban damu da ko ɗan waye ba. Ko waye shi. In ya taɓa ki ki kira ni.”

Kai ta ɗaga mishi. Da kyar ya iya juyawa ba tare da ya sake ce mata komai ba saboda in har zai tsaya ya ƙara ganin wannan kwanciyar jinin a fuskarta za a iya samun matsala.

*****

Ganin ya dawo da wuri ya sa shi son suprising Nuriyya ya je ya ɗaukota a saloon. Ya hangota tsaye da wani da bai san ko waye ba.

Wani irin duhun kishi ya lulluɓe shi. Nuriyya tashi ce shi kaɗai ba ta kowa ba. Yana cikin mota ya ga wancanmn ya wuce.

Ita kuma ta ƙarasa bakin titi ta tare napep ta shiga. Jan motar ya yi da gudun gaske ya wuce…!

*****

Shiryawa ta ke maganganun Abba na mata yawo.

“Kina son saka yaron nan a ranki. In muna ranshi ai da ya waiwaye mu. Kin san ba zan hanaki ba idan kina son zuwa ki je. Allah shi kyauta.”

Sauke numfashi ta yi. Ta saka hijabinta. Haneef ta kira a waya, ringing ɗin farko ya ɗaga tare da yin sallama. Ta amsa mishi ta ɗora da.

“Haneef ka sake faɗa min address ɗin gidan Fu’ad yanzun zan tafi….”

“Ba ni da wani aiki sosai Momma. Ki jirani sai in zo in kai ki.”

Ta amsa da,

“To shikenan Allah ya kawoka.”

Ta kashe wayar bayan ya amsa ta da amin. Ta zauna tana jiranshi.

*****

Lukman na zuwa office ya kira Hamza a waya. Don Haneef ya faɗa mishi duk abinda ya faru.

“Hello….”

Hamza ya faɗi ta ɗayan ɓangaren.

“Hamza ya gidan da iyali duka?”

“Alhamdulillah, ya naka?”

“Duk suna lafiya. Dama abin nan ne da ka turomun. Ban samu na kira ba sai yau…”

Da hanzari Hamza ya ce,

“Wallahi abin yana raina. Ina son ka tabbatar min ne tukunna.”

Ɗan gyara zama Lukman ya yi kafin ya ce,

“Yar shi ce da gaske Hamza. Yanzu haka maganar da muke yana gari.”

Yanajin numfashin da Hamza ya ja kafin ya ce,

“Akwai damuwa. Ni ta yadda zan faɗa ma Hussaina ne matsalar. Na fi son ta ji daga wajena.”

‘Yar dariya Lukman ya yi. Rigimar Hussaina da Fu’ad banbancinsu kaɗan ne.

“Kun fi kusa. Dama abinda zan faɗa maka kenan.”

Sake sauke numfashi Hamza ya yi.

“Ba damuwa. Na gode….”

Wayar ya ajiye. Shi kanshi in ba ganin yarinyar nan ya yi ba hankalinshi ba wani kwanciya zai yi ba.

Wasu ‘yan ayyuka ya ƙarasa da suke gabanshi sannan ya tashi ya je ya yi report cewar ba ya jin daɗi zai tafi gida.

Haneef ya kira ya ke faɗa masa shi ma yanzu ya ɗauko Momma gidan za su je. Suka tsayar da magana cewar su haɗu acan ɗin.

*****

Tun da safe yana yin sallar Asuba ya dawo bai ce wa Safiyya komai ba ya ɗauki mukullin motarta da ya ke ajiye a gefe ya fice.

Hotel ɗin ya koma ya yi wanka ya sake kaya. Ko awa ɗaya bai yi ba ya gama komai ya fito. Rasa me zai siyawa Nana ya yi.

Hakan ya sa shi siyo mata gasasshiyar kaza da fresh milk da alƙawarin zai tambayeta abin da ta fi so.

Hakan kawai ya wani tokare masa a wuya. A ce wai ‘yarshi ce bai san me tafi so ba. Kawai don Safiyya ta ɓoye mishi ita duk shekarun nan.

Haka ya koma asibitin da saƙe -saƙe da yawa a zuciyarshi. Likitar Nana ya samu tazo. Ta ce musu za ta duba wasu marasa lafiyan.

Za ta yi magana da su nan da awa ɗaya. Safiyya ta yi mata godiya ta fice. Idanuwa Fu’ad ya sauke a kan Safiyya tare da faɗin,

“Ba ta tashi ba har yanzun?”

Kai ta ɗaga mishi ta amsa tambayarshi da,

“Allurar da akai mata ne. Za ta tashi da sun sake ta.”

Waje ya samu ya ajiye ledojin da ke hannunshi. Ya zauna kan kujera ya zuba wa Nana idanuwa.

Safiyya ba ta san lokacin da ta tsinci kanta da ce mishi,

“Ka karya?”

Kai ya girgiza mata alamar a’a kafin ya ce,

“Ba na jin yunwa ko kaɗan.”

Lumshe idanuwanta ta yi ta ware su akan fuskarshi da take kan Nana kamar kallon da ya ke mata ne zai sa ta buɗe ido ta ce,

“In har kana son kula da ita kana buƙatar lafiyarka. Ka ci wani abu saboda ita.”

Kai ya girgiza mata. Kanshi ciwo ya ke mishi. Ba ya son cin komai. Ba ta bi ta kanshi ba. Haka ta zuciyarta da ke son ja mata matsala.

Shayi ta haɗa mishi mai kauri. Ta miƙe tsam ta je ta ajiye a gabanshi. Ta koma ta zauna. Bin ta ya yi da kallo sannan ya maida hankalinshi kan kofin din shayin.

Ya ɗauka ya soma kurɓa a hankali. Ɗakin ya yi shiru kafin wayar Sofi ta ɗauki ruri. Yana kallonta ta ɗaga tare da yin sallama.

“Wallahi ba ma gida. Muna asibitin Imzad….”

Shiru ya ji ta yi kafin ta sake cewa,

“Eh shi….”

“To ba damuwa. Allah ya kawo ku.”

Ta sauke wayar. Ta kalli Fu’ad da ya zuba mata idanuwa. Duk da bai tambaya ba ta san bayani ya ke jira ta yi mishi.

“Momma da su Haneef ne. Suna hanya.”

Lumshe idanuwa Fu’ad ya yi yana ajiye kofin shayin a gefe tare da faɗin,

“Fuck…”

Kallonshi sosai Safiyya ta yi ta na jin wani sabon mamaki na kamata.

“Fu’ad..”

Ta kira a hankali. Kallonta ya yi yana ɗaga girarshi duka biyun.

“Karka cemun su ma…”

Kasa ƙarasa tambayar ta yi ma don ba ta san ta ina zata fara ba. Ya fahimci so ta ke ta ji in har su Momma ya bari duk shekarun nan.

Cike da takaici ya ce,

“Me kike tsammani? Ba kwa son ganina ku dukanku.”

Dafe kai tayi tana salati a ranta. Tun zuwan Haneef ta karanci hakan ta dai ƙi yarda ne kawai da zarginta sai yanzun.

To meye na damuwa tunda ma kowa nashi ya bari. Har ‘yan uwanshi don ita ya bar ta ba tare da juyowa ba sai me.

Ba ta jin komai game da shi sai kuɗin da ya ke turowa account dinta lokaci-lokaci. Wanda tunda ta samu aiki ba ta ƙara taɓawa ba sai da Nana ta soma rashin lafiya.

*****

Ta wani fannin Fu’ad ya ji daɗi sosai. Saboda tun jiya su ya ke buƙata. Shi bai saba kalar wannan tashin hankalin ba.

Daurewa kawai ya ke yi yana dannewa a zuciyarshi. Ƙarin abin jiya Sofi ta ce mishi akwai hope. Suna nan zaune Doctor Jana ta leƙo ta ce su bi ta office.

Ganin Safiyya ta wuce ya sa shi miƙewa tare da faɗin,

“Ita kaɗai za mu bari?”

Ya ƙarasa maganar yana kallon Nana. Doctor Jana ta yi murmushi tace mishi,

“Karka damu. Ba za ta farka yanzun ba.”

Shi kam duk da haka ba ya son barin wajen Nana ko na minti biyar. A haka ya bi su har office ɗin Doctor Jana.

Suna zama ya kalleta ya ce,

“Ba na son all nasihar nan da dogon zance. Kawai ki faɗa min abinda ake buƙatar yi. Koma mene ne.”

Kallon Safiyya ta yi ta ɗan ɗaga mata kai alamar babu damuwa kawai ta yi mishi magana.

Cikin nutsuwa ta ke mishi bayani da kuma stage ɗin da cutar Nana ta kai. Ji yake har wani zafi-zafi jikinshi yake yi mishi.

Ba ya son bayanin nan. Muryarshi can ƙasa ya katse Doctor Jana da faɗin,

“Do mi’ a favour. Mu je wajen maganar solution…”

Sauke ajiyar zuciya Doctor Jana ta yi sannan ta ce,

“Hemotopoietic stem cell transplantation (HSCT) sai dai yana da haɗarin gaske ga wanda zai yi donating ɗin.

Sannan a stage ɗin…”

Hannu ya ɗaga mata tare da faɗin.

“Kawai a yi komenene. Ko me kuke son cirewa a jikina. Kawai ta warke shi ne buƙatata.”

Kallonshi Safiyya ke yi zuciyarta na wani irin yawatawa. Komai na kwance mata. Ba ta taɓa zaton Fu’ad zai damu ba ma da har zai baro duk inda ya tafi ya zo.

Da ya zo ba ta taɓa zaton zai kalli Nana ba ballantana ta yi tunanin zai ba da haɗin kai.

Muryar Doctor Jana ta katse ta da faɗin,

“Za mu je da kai yanzun. Za a yi running wasu tests mu gani ko za ka zama match.”

Ba wani ɓata lokaci Fu’ad ya bi Doctor Jana suka bar Safiyya nan da mamaki matuƙa a fuskarta da zuciyarta duka.

Ta na sake jin yanayin nan na jiya da ke goge mata tsanarshi a wasu ɓangarori da ta adana na zuciyarta.

Miƙewa ta yi, ta fito daga office ɗin kenan wayarta ta kama ruri. Ta na dubawa ta ga Haneef ne.

Fita ta yi waje ba tare da ta yi picking ba don ta san sun iso ne shi ya sa suke kiranta. A waje ta gansu su uku.

Momma da Haneef da Lukman. Da fara’a a fuskarta ta ƙarasa inda suke ta gaishe da su.

Momma ta amsa ta da,

“Safiyya dama kina nan?”

Shiru Safiyya ta yi ta na sadda kanta ƙasa. Sai yanzun ta ke ganin rashin kyautarwa abinda ta yi. Ko ba komai Momma ta nuna mata ƙauna da karamci.

Amma a lokacin ba ta son ganin su ne. Gaba ɗaya laifin Fu’ad ya shafesu. Tuna hakan kawai ta ji tsanar shi na sake dawo mata.

Dafata Momma ta yi ta ce,

“Abinda ya wuce ya wuce. Mu je in ga jikata.”

Babu musu ta yi gaba suna bin ta a baya har ɗakin da Nana take. Momma ta zauna zuru tana kallon Nana da yadda kamaninsu suka ɓaci da Fu’ad.

Ta rasa me za ta ce. Addu’a ta yi mata ta miƙe ta kalli Haneef ta ce,

“Haneef ka mayar da ni gida. Mun dawo anjima…”

Ta ƙarasa muryarta na rawa. Don ganin Nana ya karya mata zuciya sosai. Ga kewar ɗan nata da ta addabeta.

Lukman ne ya ce,

“Ina Fu’ad ɗin?”

Sannan ya zo ma Momma da ta tambaya. Suka zuba mata idanuwa su duka ukun.

“Yana wajen…”

Ba ta ƙarasa ba ya turo ƙofar da sallama. Idanuwanshi suka tsaya kan Momma da ita ma ta zuba mishi ido.

Wata irin kewarta da muryarta kawai da ya ke ji lokaci lokaci ba ta cike mishi ta taso. Wani irin abu ya ke ji da bai da kalmomin da zai ɗora shi akai.

A hankali ƙafarshi ke takawa har ya ƙarasa inda ta ke. Hannuwanta ya kama ya dumtse cikin nashi. Ya kasa magana saboda yadda ya ke jin wani abu na shaƙe mishi wuya.

“Fu’ad.”

Momma ta furta a hankali ta na jin yadda wasu hawaye ke taruwa a idanuwanta. Ya ƙara girma ya zama babban mutum.

Hannunta ya kai bakinshi ya sumbata har lokacin ya kasa magana. Sai dai idanuwanshi da ke faɗa mata yadda ya yi kewarta.

Yadda rashinta ya fi taɓa shi fiye da na komai. Idanuwanshi suka bar fuskarta zuwa cikin ɗakin. Haneef yagani tsaye ya jingina da bangon ɗakin yana kallonshi.

Wani irin dokawa zuciyar Fu’ad ta ke yi. Hannuwan Momma ya saki ya taka ƙafafuwanshi kamar an yi su da dutse saboda nauyin da suka yi masa.

Gaban Haneef ya ƙarasa. Duk yadda ya ke gaya wa kanshi bai yi kewar ɗan uwanshi ba ya ƙaryata a yanzun.

Kauda kai Haneef ya yi gefe. Fu’ad ɗin ya matsa inda ya mayar da fuskarshi. Ya sake kauda ta gefe alamar ba ya son ganinshi.

“Haneef…”

Ya faɗi kamar zai yi kuka. Sai lokacin ya ware idanuwanshi kan Fu’ad ɗin. Yana neman duk wani haushin shi da yake ji yana rasawa.

Hannuwanshi ya kai ya kama kunnuwanshi yadda yakan yi lokacin da suna yara sosai in ya wa Haneef ɗin laifi.

Ganin ya yi ƙasa yana shirin tsugunnawa ya sa Haneef saurin ɗago shi. Da sauri Fu’ad ya kalle shi.

“Please….”

Ya faɗi da ta ke tattare da wata irin ƙauna da ban haƙuri da ya ke ji har ranshi. Rungume shi Haneef ya yi suna sake ajiyar zuciya.

Lukman kallonsu ya ke yi kawai. Yanzu ya tabbatar ko ɗan uwanshi da suka haɗa jini iya ƙaunar da zai mishi kenan. Ba kaɗan ya yii kewar abokantakarsu da ƙaunarsu ba.

Ƙarasowa ya yi kusa da Lukman da wannan murmushin yana ɗaga mishi gira duka biyun. Wani irin naushi Lukman ya kai mishi ya tare da hannu.

Yarfe hannunshi ya shiga yi yana daƙuna fuska.

“Wannan na rashin bawa kowa zaɓi ne….”

Haneef ne ya fara dariya kafin Fu’ad ɗin sannan Lukman. Ba ƙaramar kewarshi suke yi ba.

Muryarshi na rawa ya ce,

“Kuncika son kanku. Shi ne ko sau ɗaya ba ku taɓa kirana ba.”

Wannan karon har Haneef ne ya taho da niyar kawo ma Fu’ad ɗin naushi ya ruga ya ɓoye bayan Momma.

Girgiza kai ta yi ta ce.

“Ku ƙyale min yaro mana.”

Zama suka yi su dukansu. Sai yanzun ya ke jin shi wani iri. Kamar an rage mishi wani irin nauyi a zuciyarshi.

Faɗa musu ya ke Nana za ta ji sauƙi dan Doctor ta ce mishi jibi za su dawo su karɓi result ɗin. Safiyya dai na gefe ta na ta kallonsu.

Karo na farko tun da Nana ta fara rashin lafiya da ba ta ji ta ita kaɗai ba. Hamdala ta ke yi a zuciyarta. Muryar Nana suka ji ta ce,

“Mummy…”

Gaba ɗayansu suka tashi suka zagayeta. Ɗaya bayan ɗaya ta ke kallonsu. Haneef ta yi ma murmushin nan nata.

“Na sanka.”

Dariya Haneef ya yi. Ya ja mata hanci a hankali.

“Inye, ashe kina gane mutane haka. Kin san sunana?”

Kai ta ɗan girgiza.

“Uncle Haneef.”

Ya kalli Lukman da ke gefe ya ce,

“Wannan kuma Uncle Lukman.”

Wani gagging sound Fu’ad ya yi da ya sa Haneef harararshi. Ta ya za a ce Fu’ad na da yarinya bayan shi kanshi yarinta na cikinshi.

Kallon Haneef Momma ta yi ta ce,

“Kanku kawai ku ka sani ko?”

Dariya suka yi. Nana na kallon momma ta ce,

“Granny…”

Fu’ad ya yi dariya tare da faɗin,

“Momma an tsufa. Kin ga tagane ki babu wani introduction.”

Safiyya bata san lokacin da hawaye suka zubo mata ba. Ta yi kuskure sosai da ta ɓoye musu Nana.

Jibi yadda suke nuna mata ƙauna kamar su karɓe mata ciwon da ke jikinta. Son kanta ne ya sa ta ɓoye musu ita.

Cewa suka yi za su tafi da alƙawarin za su dawo da yamma in ba a sallame su ba. In an sallamesu za su zo gida.

Iya ƙofa Fu’ad ya raka su don yadda Nana ta farka ba ya jin zai iya matsawa ko ina. Safiyya ce ta tafi ta raka su.

Fu’ad ya koma gefen Nana ya zauna yana ce mata,

“Sannu. Ban son me ki ke so ba ina son siyo miki ɗazun da na fita.”

Dariya Nana ta yi da ya ji sautinta har zuciyarshi.

“Ni komai ina ci fa. Ka ba ni labari.”

Ya ɗan yi shiru kamar yana tunani kafin ya ce,

“Wanne iri?”

Yadda ta daƙuna fuska ya ji zuciyarshi har wani tsalle-tsalle ta ke yi.

“She is so damn cute.”

Ya faɗi a zuciyarshi kafin Nana ta ce,

“Kowanne iri. About you and mum.”

Ware idanuwa ya yi sannan ya yi ƙasa da muryarshi ya ce,

“Amma sirrine fa.”

Dariyar ta sake yi. Ta miƙa mishi ƙaramin yatsanta tare da faɗin,

“Ba zan faɗi mata ba, i promise.”

Dariya suka yi su duka suka ji Safiyya ta turo ƙofar. Su dukansu suka ware idanuwansu akan ta iri ɗaya.

Haɗe fuska ta yi.

“Gulmata ku ke yi ko?”

Kallon juna suka yi sannan suka girgiza kai. Wani irin sama ta ji numfashinta ya yi. Komai nasu iri ɗaya ne.

Ƙarasawa ta yi ta zauna daga ɗayan gefen gadon. Ta sumbaci goshin Nana. Dariya Nana ta yi kaɗan don ta san so take ta ji ko da zazzaɓi a jikinta.

“Za ki ci wani abu?”

Kai Nana ta ɗaga mata alamar eh. Ta ɗora da faɗin,

“Na gaji sosai. Ina Anty Jana mu tafi gida.”

Kai Safiyya ta girgiza mata tana haɗe rai. Fu’ad ya kalleta ya ce,

“Wace ce Anty Jana?”

A dake Safiyya ta amsa shi da,

“Likitarta.”

Miƙewa ya yi, har ya kai bakin ƙofa ƙofa Safiyya ta ce,

“Ina zaka?”

Kallonta ya yi da ya ke fassara da gaske tambayata ki ke. Kafin ya ce,

“Ba ki ji me Nana ta ce ba ne? Gida ta ke son zuwa.”

Da mamaki Safiyya ta ce,

“Sai kuma aka ce abinda ta ke so shi za a yi mata. In lokaci ya yi za su sallameta ai. Rigima ce kawai.”

Taɓe baki ya yi alamar wannan bai dameshi ba.

“Gida ta ke son zuwa. Ban damu ba ko da hakan na nufin a kwashi duk abinda ke cikin asibitin zuwa gida.”

Bai jira me za ta ce ba ya fice abinshi. Nana tai mata wani murmushi har haƙoranta suka fito tare da faɗin,

“I love him…”

Harararta Safiyya ta yi.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×