Skip to content

Akan So | Babi Na Talatin Da Hudu

0
(0)

<< Previous

Yana so ya buɗe idanuwanshi ya kasa. So ya ke ya ƙwace daga inda tunanin shi ke son janshi.

Ya gwammace ya ziyarci ko’ina banda nan. Banda ranar farko da ya karɓi abinda ya rusa mishi rayuwa. Sai dai ya zamana bashi da karfin komai.

Bashi da ƙarfin fisgewa daga riƙon da koma menene ya yi mishi. A hankali ya bayar dakai. Ya daina ƙoƙarin kokawar da yake yi.

Ya bari koma menene ya ɗauke shi ya ja shi inda ya ke son kaishi.

*****

Nawaf A SS3

“Nawaf ka cika tsoro wallahi. Wannan ya fi komai da ka taɓa trying ba da kalan charge ɗin da ake buƙata.”

Girgiza kai Nawaf ya yi yana kallon Awwal haɗi da faɗin,

“Ni fa Codien ɗin nan ma ina so in bari ne. Na kasa kar a gane a gida.”

Dariya sosai Awwal da Haroon suke mishi. Kafin Haroon ya ce,

“Ka bani dariya maza. Sai ka ce wani ƙaramin yaro. In za ka ja kaya ka ja kaya kawai.”

Ajiyar zuciya Nawaf ya sauke. Yana tsoron karɓar ƙwayoyin da ke hannun Awwal, don bai san kalar ƙarfinsu ba. Codien ɗin ma don ya zamana kowa a ajinsu yana sha ne. Kullum kallon ƙaramin yaro suke mishi. Shi ne abinda ya fara jan hankalinshi. Shekara ɗaya kenan ya kasa dainawa. Sam ba ya jin daɗi in har bai sha ba. Dafa kafaɗarshi Awwal ya yi. Yana miƙa masa ƙwayoyin da ke hannun shi.

“Ka karɓa. Ba Za kai da na sani ba. Duka kwana nawa ya rage mana mu ƙarasa jarabawar mu?  Wannan ne lokacin holewa.”

Dariya Haroon ya yi.

“Kamar kasan yau akwai clubbing ba.”

Karɓar Kjwayar Nawaf ya yi. Yasa a aljihu ya wuce ya bar su nan. Don ya ga lokacin sallah ya yi. Ba damuwa suka yi da su yi ta ba.

Shi kam in akwai abinda ya tsana bai wuce wasa da sallah ba. Ko da lokacin sallah bai ba shi ba zai zauna ya saurari shirmensu kan mata ba. Har addu’a yakanyi. Allah ya kare mishi zuciyarshi daga zina. Shan codien wani abune daban. Amma zina na ɗaya daga cikin manyan laifukan da baya so ya haɗa shi da Ubangijinsa.

*****

Wannan ranar ita ce ta farko da Nawaf ya fara shan Kjwaya. Abin bai tsaya iya nan ba. Kafin su gama makaranta sai da ya zamana har cocaine suna sha.

Alh. Haladu shine mahaifin Nawaf. Ɗan kasuwane da yaranshi huɗu duk maza da suka haifa da matarshi Hajiya Asiya.

Kabir, Khamis, Ibraheem sai autansu Nawaf. Tarbiya dai dai misali sun yi ƙoƙarin ba wa yaran nasu. Nawaf ne kawai ƙaddara ya rubuta musu.

Ibrahim shi ya fara gane Nawaf ɗin na shaye-shaye. Kuma shi ya sanar da mahaifiyarsu. Lokacin ya gama jarabawarshi ta WAEC da NECO. Babu iya ƙoƙarin da ba su yi ba na ganin sun raba shi da su Haroon.

Amma ina, hakan ya sa su yanke hukuncin su turashi karatu England. Haka kuwa akai. Sai dai wannan ya zamana babban kuskuren su.

Don abin har ya so ya taɓa mishi ƙwaƙwalwa. Lokaci da dama zai dinga abubuwa kamar marar hankali.

Maimakon ya zama silar shiriyar Nawaf kamar yadda suke tunani, sai ya ƙara zama sanadin lalacewarshi. Da ƙyar ya kammala karatun shi ya dawo gida Nigeria.

Rayuwa ta ci gaba da tafiyar musu. Saboda Alh. Haladu ya san mutane da dama. Ya sa Nawaf samun aiki a wani kamfani da suke atamfofi.

Yana zuwa aiki. Ga biyayya kamar me. Sai dai shaye-shayen kawai. Duk da dawowarshi Nigeria ya sa sun sake jonewa da su Haroon bai sauke mishi aƙidarshi ta ƙin son kusantar zina ba.

Har lokacin da ya haɗu da Nuriyya. Ita ta soma ɗauke hankalinshi daga shaye-shaye. Kafin daga bisani wata irin soyayyarta ta shige shi.

Ta san matsalarshi. Hakan bai sa ta ƙyamatarshi ba. Domin shi yana da asali koda kuwa a cikin rijiyar giya yake kwana ya wuce gori.

Nuriyya ta soma zama silar shiriyar Nawaf. A hankali har iyayenshi suka san da ita. Da gudu suka karɓeta. Babu ƙyamata babu komai.

*****

“Nawaf…”

Yanajin muryar Ibrahim yana kiranshi sama sama. Ba ma tashi kaɗai ba. Ta mutane da yawa.

Muryarsu ya ke ji cikin kunnuwanshi amma Nuriyya yake gani a zuciyarshi.

“Nuri…”

Ya faɗi. Ibrahim da ke bakin gadon ganin bakin Nawaf ya yi motsi ya sa shi ƙara matsawa da sauri yana kasa kunne.

Su Mama kam banda kuka babu abinda sukeyi. Don har sun riga sun haƙura da Nawaf. Yakai awa biyu da kawowa asibiti kafin a samu zuciyarshi ta ci gaba da bugawa.

“Nuri…”

Ya sake faɗa wannan karon da ɗan ƙarfi. Khamis da ke tsaye Ibrahim ya yi wa nuni da su kira likita. Da saurin shi ya je ya taho da shi.

Zuwa ya yi ya sake duba Nawaf. Suna tsaye cirko cirko. Bai buɗe idonshi ba. Banda Nuri da bakinshi ke kira babu inda ke motsi a jikinshi.

Dr ɗin ne ya ke tambayarsu ko wacece Nuri. Ibrahim ya amsa shi da cewar matarshi ce,

“Ku kirata. Ku kirata da sauri…”

Cewar likitan yana ma Nawaf ɗin wata allura kafin ya fita. Su dukansu Ibrahim suka zuba ma idanuwa.

Tashi ya yi jiki a sanyaye ya fice daga ɗakin yana ja musu ƙofar. Wayarshi ya ɗauko ya lalubo lambar Nuri ya yi dialing…

*****

Yana zaune ya zuba wa sarautar Allah ido Dr. da Nurse ɗin suka fito. Dr. ɗin ya dafa Farhan ya ce ya biyo shi. Babu musu ya tashi ya bishi har office ɗin. Sosai ya ke kallon Farhan.

“Na san wannan ba hurumina ba ne. Saboda Allah me matarka za ta yi maka kai mata wannan dukan?”

Wani ɗaci Farhan ya ji cikin zuciyarshi. Cike da ƙunan rai ya ce,

“Hakane kam. Ya take?”

Bai son kallon da likitan ya ke masa. Duk da yana son faɗa mishi ba shi bane ba. Gara Allah ya ɗauki rayuwarsa da ya gwada masa ranar dazai ɗaga hannu akan mace.

Kamar yadda ya faɗa. Ba huruminshi bane ba. ‘Yan rubuce-rubuce ya yi a takarda sannan ya miƙa wa Farhan ɗin hadi da fadin.

“Ka siyo waɗannan magungunan yanzun. In ka shiga dubata ta ci wani abu sannan a bata.”

Karɓa ya yi ya miƙe tare da faɗin,

“Na gode.”

Bai kula shi ba. Shi ma bai damu ba ya fice. Kai tsaye Pharmacy ya wuce ya siyi magungunan da aka ba shi sannan ya koma zuwa ɗakin da aka kwantar da Nuri.

Duk da gadaje uku ne cikin ɗakin, ba kowa sai ita kaɗai. Da ɗori a hannunta da ya karye. Kallo ɗaya Farhan ya yi mata ya sauke idanuwanshi.

Baya son sake kallonta saboda ji yake yana son shaƙare Nawaf. A hankali ya ƙarasa inda take ya ja kujera ya zauna.

“Sannu.”

Idanuwanta ta ɗago da ƙyar saboda nauyin da ta ke jin sun mata. Cike suke da hawayen da su ba su zubo ba. Su ba su koma ba. Cikin sanyin murya ta ce,

“Inajin kamar wani abu ya faru da ni da ban sani ba.”

Kallonta ya yi. A tausashe ya ce,

“Banda wannan akwai wani abu da zai faru dake?”

Ɗaga kafaɗa ta yi alamar ita ma ba ta sani ba. Ta kai hannunta mai lafiya ta na goge hawayen da suka tarar mata cikin idanuwa.

“Koma menene yana da girma. Saboda ina jin shi har raina.”

Sauke numfashi Farhan ya yi. Bai san amsar daya kamata ya ba ta ba. Saboda haka ya ce,

“Me zakici? An ce ki ci wani abu sannan ki sha magani.”

Ita kam ba ta jin tana son cin wani abu. Banda jin da take wani abu ya faru da ita. Ga Nawaf ya mata tsaye a zuciya.

Ta so Nawaf. Tana son Nawaf. Sai dai tana jin tsoronshi sosai. Bayan abinda ya faru yau. Bai barta da wani zaɓi ba.

Wayarta da ke hannun Farhan ta soma ringing. Kallon juna suke. Ya zaro wayar daga aljihunshi ya miƙa mata.

Gani ta yi yaya Ibrahim ne. Gabanta ya yanke ya faɗi. Allah kaɗai yasan abinda zai faru yanzu kuma. Ta san wajen shi Nawaf yaje. Wani irin tsoro ya cika mata zuciya. Idan Nawaf ya ji tabiyo Farhan ba ta san me zai faru ba. Hawayen da suka zubo mata ta sa bayan hannu ta goge.

Wayar ta yanke. Kafij ta sake ɗaukar wani ringing ɗin . Kallon ta Farhan yake. Shi bai isa ya tayata yanke hukunci ba. Duk kuwa yadda yake so.

Sakata ta yi silent. Tana jujjuya wayar a hanunta kanta a ƙasa ta ce,

“Shekarar mu ɗaya da wani abu da aure. Babu wanda ya min dole. Ina son shi saboda ya taimake ni kamar yadda kaimin.

A ƙasan duk wannan dukan Nawaf na da halayya me kyau. Yana da zuciyar da kowacce mace za ta so…”

Shiru ta ɗan yi. Don ba ta ma san dalilin da ya sa ta ke wannan maganganun ba. Kawai ta na jin ya kamata ta yi wa Farhan ɗin bayani ne. Ta so shi shi ma. Son shi dabanne da na Nawaf.

Tana son ya fahimci tana son mijinta har yanzun. Tsoron shi ne ya ke son girmar son. Wasu hawayen suka sake zubo mata da ta ga kiran yaya Ibrahim na sake shigowa kafin ta ce,

“Yana da matsala. Yana shaye-shayen manyan ƙwayoyi kafin aurenmu.

Ya bari na wani lokaci kafin sati biyu da suka wuce. Ban tabbatar ba amman na ga alamu ne kawai.

Yana buƙatar taimako. Yana buƙata ta ni kuma……ni kuma ka ganni anan.”.

Murya a dake Farhan ya ce,

“Kalle ni nan Nuri. Ba ina son yanke hukunci ba ne. Ko in nuna na fi ƙarfin ƙaddara ko makamancin hakan.

Komenene dalilinshi. Ko menene naki. Babu amfanin zama da namijin da yake miki wannan dukan. Shi ya baki rayuwar?”

A hankali ta girgiza mishi kai.

“Saboda me zaki miƙa mishi ita ya yi yadda ya ga dama? Saboda kina jin cewa ya miki taimako?”

Sai lokacin ta ɗago kai ta kalli Farhan.

“Ina zanje? Gidan magajiyar karuwai da abin dariya ita ce mahaifiyata?”

Dafe kai Farhan ya yi cikin hannuwanshi yana girgiza kai. Bai san ta inda zai fara mata bayani ba. Sai yanzun da ta yi wannan maganar abin ya faɗo mishi. Ta ina zai fara gaya mata lokacin da ya je aka faɗa mishi tayi aure ba shi bane kawai labarin daya samu?

Wayarta ta sake kallo. Message ne ya shigo. Hannunta na rawa ta cire wayar daga key. Ta bude message ɗin.

“Na san abinda zaisa ki tafi ba ƙarami bane Nuri. Ban san me zance ba. Ko ta ina zan fara. Don Allah ki zo…”

Bata ƙarasa karantawa ba farhanu ya ce mata,

“Ba ita ta haifeki ba Nuri. Ba ki da alaƙa ta jini da ita ko kaɗan…”

Cikin kunnuwanta ta ke jin maganar na mata wani irin yawo. Tana son fahimtar abinda maganganunshinke nufi. Idanuwanta kafe kan screen ɗin wayar.

“Accident da Nawaf.”

Tagani cikin jumla ɗaya da su ma ta kasa fahimtarsu. Sosai ta buɗe idanuwanta kan screen ɗin wayar. Kalma uku kacal take ganewa.

Sunan asibitin. Nawaf da kuma haɗari. Kafin wani abu ya yamutsa cikin cikinta. Jiri ta ke ji yana ɗibarta daga zaune. Ɗakin na wani irin juyawa.

Hannu ta kai ta na dafe kanta haɗi da rintse idanuwa. A razane Farhan ya ce,

“Nuri!!!”

Sama-sama take jinta. Wani irin yanayi ne da wanda ya san tashin hankali kaɗai ne zai iya fahimtarshi. Yanayi ne da ba kowa ne zai gane ba.

Ƙafafuwanta ta sakko daga kan gadon. Ta ɗan yi jim tana jin garin ya ɗan saitu sannan ta diro tana miƙewa. Kalle-kalle take.

Ta hango mayafinta. Tana kallon bakin Farhan na motsi sai dai kunnuwanta ba sa jin me ya ke faɗi. Nawaf kawai.

Wajen Nawaf ta ke son zuwa. Takalmanta ta janyo ta saka a ƙafarta. Ihun magana Farhan ke mata amman ya ga alama ba ta ganewa.

Cikin wata irin murya ta ce,

“Ka kaini wajen Nawaf. Yaya Farhan ka kaini wajenshi…”

Ya kasa gane me take nufi ko meye sanadin faruwar wannan abin. Ko maganar da ya faɗa mata ne?

Gani ta yi kamar ba ya ganewa. Wayarta ta ɗauko da ke kan gado ta miƙa mishi ya karanta text ɗin. Ware idanuwa ya yi. Ba tare da tunanin komai ba ya ce mata,

“Mu je…”

****

Zame jikinshi ya yi a hankali zuwa Kjasa. Ya zauna ba tare da damuwa da cewar kan tile bane ba. Ya dafe kanshi da dukkan hannuwanshi biyu.

Addu’ar duk da ta zo bakinshi ya ke karantawa ko zai samu sauƙin abinda ya ke ji. Bai taɓa sanin haka ake jin mutuwa ba sai da ya yi tunanin babu numfashi a tattare da Nawaf.

Bai taɓa sanin haka ɗaci da raɗaɗin rabuwa da wanda ka shaƙu da shi kake ƙauna yake ba sai yau ya ɗanɗana kaɗan daga ciki.

Sai dai ya ɗauki wancan yanayin da mayewar gurbin shi da wani sabo. Fargaba da tashin hankali. Tunanin zai iya rasa ƙaninshi a kowanne lokaci.

Fatanshi Nuriyya ta buɗe text ɗin da ya tura mata. Ko da Nawaf rasuwa ya yi ba zai ji bai yi wani ƙoƙarin komai ba. Rawa ya ji zuciyarshi na yi.

Wayarshi ya ji tana ringing. Ya ɗaga ganin Nuriyya ce ya sa shi saurin ɗagawa da sauri. Sai dai ba muryarta ya ji ba.

Wata murya ya ji daban an mishi sallama. Ya amsa gabanshi na wani irin faɗuwa. Roƙon Allah yake kar ya haɗa musu abu biyu lokaci ɗaya.

Can yaji an ɗora da,

“Muna cikin asibitin. Daga farko. Kuna ina?”

Da Kjyar ya iya cewa,

“Bari in zo.”

*****

Daga nesa yake hango wata kamar Nuriyya. In ka ɗauke raunukan da ke fuskarta da kuma hannunta da yake a karye.

Tsaye take da wani matashi da in bai girmi Nawaf ba za su zo shekaru ɗaya. Da sauri ya Kjarasa inda suke. Kallon Nuriyya yake.

Kar dai ace Nawaf ne ya yi mata wannan dukan. Girgiza kai Ibrahim yake yana rikee baki. Idanuwa Nuriyya ta ware a kanshi.

Idanuwanta a bushe suke. Babu alamar komai a ciki. Bai taɓa ganin idanuwa haka ba sai yau. Muryarta a dakee ta ce,

“Yana ina?”

Ko sallamar Farhan Ibrahim bai tsaya amsawa ba balle ya karɓi hannun da ya miƙo masa ya juya. Ba wai don wani abu ba. Sam bai kula ba ne.

Suka bishi a baya.

****

Ba ta jin komai. Kamar an rufe mata duk wata ƙofa da kafa ta jin wani tashin hankali tun ɗazun. Komai ya tsaya mata cik.

Har lokacin da ta tura ƙofar ɗakin da Nawaf yake. Ba ta hango shi daga inda take tsaye saboda su Mama da suke zagaye dashi.

Ƙafafuwanta da wani irin nauyi ta ƙarasa cikin ɗakin. Suna jin takun tafiyarta suka juyo. Ganinta yasa suka matsa daga jikin gadon.

Tana sauke idanuwanta kan Nawaf zuciyarta ta yi wata irin dokawa da ta ke ji har cikin kanta. Kallonshi take. Kanshi naɗe yake da bandeji. Gefen fuskarshi ma haka.

In har baka sanshi ba ba za ka gane shi ba. Inda ba shida bandejin  ɗinkine ya kai huɗu. Da duk takun da take da ƙarin ƙarfin bugun zuciyarta.

Gaba ɗaya jikinshi na’urori ne har da abin abinci ta hancinshi. Gani ta yi tafiyar daga inda take zuwa gadonshi ta mata wani irin tsawo.

Kamar so ake ta ƙare mishi kallo. Ta ga yadda ya koma kafin nan ta ƙarasa inda yake. Hakan kuwa take.

Ƙafafuwanshi duka biyun a naɗe suke da irin abinda hannunta ke ciki. Bata taɓa sanin zaka iya jin tarwatsewar zuciyarka ba sai a wannan lokacin.

Bata taɓa sanin haka tashin hankali yake ba sai a yanzun nan. Bata taɓa gane rayuwa ba abakin komai take ba sai da ta ƙarasa bakin gadon da Nawaf yake kwance.

Hannunta na rawa sosai ta yi ƙoƙarin kaishi kan fuskar Nawaf. Sai dai ta rasa inda za ta ajiye shi.

Ko ina ciwuka ne. Ƙafafuwanta ta ji suna wata irin rawa. Ta dafa gadon da ƙyar tana zama. Bakinta ta buɗe sai dai kalma ko ɗaya ta kasa fitowa.

Banda wani irin ihu da ta ke jinshi cikin zuciyarta da kanta amma sautin shi ya ƙi fita.

Hannunta ta sauke kan ƙirjin shi. Kai take girgizawa. Fata take ta farka daga wannan mafarkin da take yi. Su koma gida abinsu da Nawaf ɗinta.

Ko da kuwa markaata zai dinga yi ƙarewar duka in har za ta ga fuskarshi babu wannan abin.

Yanayin Nuriyya da Nawaf ɗin ya sake karya zuciyar duk wani wanda ke cikin ɗakin. Su kansu mazan daurewa kawai suke.

Can Allah ya taimaketa muryarta ta ɗan dawo.

“Nawaf…”

Ta fadi. Baiko motsa ba ballanta na ta yi tunanin ya ji ta ko zai buɗe ido.

“Nawaf…!”

Ta sake kira wannan karon da ƙarfi.

*****

Ji ya yi kamar muryar Nuriyya. So yake ya buɗe idanuwanshi amma sun masa wani irin nauyi. Yana ji da wata irin murya ta sake faɗin,

“Nawaf ka tashi…!”

Ƙoƙarin buɗe idanuwanshi yake yi daga duhun dake riƙe da su. Nuriyya ce. So yake ya tashi ya ba ta haƙuri. So yake ta yafe mishi. Yana jin yafiyarta ce kawai za ta yaye wannan duhun.

Da wani irin ƙarfin hali ya samu ya soma motsa idanuwanshi. Ji yake komai ya mishi nauyi. Kafin a hankali ya buɗe idanuwanshi. Ya daɗe sosai kafin ya fara ganin alamu haske haske.

“Nawaf…”

Ta sake faɗi. Baya son yanayin da yake ji cikin muryarta. Raunin da yake ji fiye dana kowanne lokaci ne. Sake kiran sunanshi ta yi.

Sai lokacin ya fara ganinta dishi dishi. Yana ji daga can gefe wani kamar yaya Khamis na faɗin,

“Call the Dr.”

Sai dai baya ganinsu. Nuriyya ɗin ma dishi-dishi ya ke ganinta. Kanshi yake ji kamar ana doka mishi wasu irin ƙarafa a ciki. Ya rasa a ina ma yake jin ciwon a jikinshi.

Har cikin tsokarshi ciwo yake ji mai tsanani. A hankali fuskar Nuriyya ke washe mishi. Da ƙyar muryarshi can ƙasa ya ce,

“Nuri…”

*****

Buɗe idanuwanta ta yi ta sauke su kan Fu’ad da ke zaune yana riƙe da hannunta. Wani murmushi ya yi mata da yau ta kasa mayar mishi.

Kafin ta kalli gefenta. Sofi ce zaune.  Sake maida kallonta tai kan Fu’ad.

“M….”

Ta kira shi a hankali. Hannunta ya sake dumtsewa cikin nashi yana jin yadda zuciyarshi ke buƙatar suna mabanbancin wanda take kiranshi da shi.

Sumbatar hannun yayi tare da faɗin,

“Princess. Sannu.”

“Ku kaini wajen shi.”

Wani numfashi Fu’ad ya ja saboda Safiyya ta mishi bayanin komai tun ɗazun. Har ta gama faɗa mishi bai ce komai ba.

Saboda baya son zuciyarshi ta fara tauna dukkan maganganun. Komai zai iya faruwa. Nana ta fi buƙatarshi. Komai da na shi lokacin.

Ba Nana kaɗai ke son ganin wannan bawan Allah ba. Har shi ma yana son ganinshi. Yana son yi mishi godiya akan karamcin da ya yi wa Nana.

Yana son yi mishi godiya duk da ta yi kaɗan akan abinda shi ya yi mishi. Bai da wani abin da zai iya bayarwa banda wannan.

“Za ki ganshi. Yanzu ki huta sosai. Ki ci abinci ki sha magani sannan.”

Kai ta girgiza mishi tana daƙuna fuska.

“Yanzu na ke son ganin shi.”

Sauke numfashi Fu’ad ya yi yana kallon Sofi da ta kawo mishi ɗauki. Kauda kanta ta yi gefe. Ta san halin Nana. Ba ta cika nacewa kan abu ba.

Saidai duk lokacin da ta yi haka ɗin, lanƙwasata abu ne mai wahala. Kawai sai dai a yi mata abinda take so shi ne kwanciyar hankalin kowa.

Hannunta ya sake dumtsewa cikin taushin murya ya ce,

“Baki yarda da ni ba? Na ce miki za mu je. Ki ci abinci ki sha magani tukunna…”

Ƙwace hannunta Nana ta yi. Ta kauda kai gefe idanuwanta na cikowa da hawaye. Ba za su gane ba. Ta jima tana son sake ganin shi ta yi mishi godiya.

Ko sunanshi ba ta sani ba. Ranar ta ɗauka za su fito su same shi a waje. Sanda suka fito baya nan. Tun ranar duk fitar da za ta yi tana duba fuskarshi a fuskokin mutane da dama.

Dawowar Fu’ad ya sa ta sake son ganinshi. Sai dai ta na mishi addu’a. Tana mishi addu’ar samun wadatacciyar lafiya a rayuwarshi.

Don a wajenta tana jin banda mumynta da babanta babu abinda yafi mata lafiya muhimmanci. Yanzu da ta ganshi cikin jini. Tana so ta ga halin da yake ciki. Hawayen dake idanuwanta suka zubo.

“Ba zaku kaini inganshi ba sai na mutu ko shi ya mutu tukunna ba…”

Da sauri Fu’ad ya kai hannu ya rufe mata baki. Fuskarshi babu walwala ko kaɗan ya ce,

“Shhhhhhhh za mu je. Za mu je Nana ki daina wannan maganar. Ta girmi shekarun ki.”

Hannunshi ta kama da ya je bakinta ta sauke shi. Mayarwa ya yi yana goge mata hawayen da ke fuskarta. Kafin ya miƙe.

Safiyya na kallonshi ya fice daga ɗakin sannan ta taso daga inda take ta zauna kan kujerar da ya tashi.

“Kinsan ba…”

Da sauri Nana ta ce,

“Mummy please. Ina son ganinshi. Kuma ina son magana da ‘yan jaridar nan.”

Da mamaki Safiyya take kallonta. Ta ɗauka ta manta da maganar tunda Fu’ad ɗin ya dawo. Duk da bawai haƙura suka yi su da son magana da Nana ɗin ba.

“I thought M ya dawo. Shikenan.”

Girgiza kai Nana tayi.

“Ina son magana da su har yanzun. You promise Mummy.”

Jan numfashi Safiyya ta yi ta fitar kafin ta ce,

“Zan kira su. Da mun bar asibiti in shaa Allah.”

Sai lokacin ta yi murmushi.

“I love you mumy.”

Dariya Safiyya ta yi ta kai hannu ta taɓa ɗan jan hancin Nana ɗin.

“Sarkin rigima. I love you more.”

Girgiza kai ta yi ba ta yarda ba. Za ta yi magana Fu’ad ya turo ɗakin da sallama. Suka amsa mishi.

“Na gano ɗakin da yake. Sai dai family kawai ake bari ganin shi.”

Da sauri Nana ta ce,

“Ku je da ni. Za su bar ni.”

Girgiza kai Fu’ad ya yi. Baya son sake ganin hawaye a fuskarta. Kai ya sake zurawa waje ya hango likitan da sukai magana dashi ya taho.

Hanya ya bashi ya shiga cikin ɗakin. Ya cire wa Nana ƙarin ruwan da ke jikinta yana barin abin a jiki don in sun dawo a mayar mata.

Da idanuwa Fu’ad ya yi mishi godiyar fahimtarshi da ya yi. Tahowa ya yi inda Nana ke ƙoƙarin sakkowa daga kan gado yana son kamata.

Hannunshi ta dafa ta kalle shi ta ce,

“Zan iya fa.”

Tana saukowa. Takalmanta ta saka. Ta ɗauki ɗan  hijabinta ta saka a kanta. Sai ya ga ta yi wani irin kyau kamar ya sace ta.

Ɗaukarta ya zo yi ta matsa baya. Da murmushi ta ce,

“Um um. Zan iya.”

Girgiza mata kai Fu’ad ya yi yana kawo hannuwa zai ɗauke ta. Ta riƙe su duka biyun. Idanuwanta take yawatawa cikin fuskarshi kamin ta furta,

“Ina son yin komai da kaina yanzun da zan iya. Za ku yi min amma da ɗan saura.”

Runtse Idanuwanshi ya yi yana jin nauyin da zuciyarshi ta yi a ƙirjinshi. Ya ma kasa cewa komai sai hannunta kawai da ya kama cikin nashi.

Kallon Safiyya yake da wani irin yanayi da shi kanshi ya kasa fassarawa. Kafin ya ja Nana a hankali suna takawa zuwa ƙofa.

Bin su Safiyya ta yi tana jin wani irin abu na daban. Ta kasa fassara kallon da Fu’ad ya yi mata. Sai dai ta gwammace hararar da ta kan samu lokaci-lokaci a wajenshi da wannan kallon mai cike da fassarori da yanayi kala-kala.

*****

Kamar yadda Fu’ad ɗin ya faɗa. Family ne kawai za su iya ganin Nawaf. Fu’ad na ta fama amma sun ƙi saurarenshi.

Nana ta ja mishi hannu. Nuna mishi ta yi da ya ɗaga ta. Don ba sa hangota saboda counter ɗin da ta ɓoye su. Ɗaga ta ya yi.

Likitocin da ke wajen ta kalla idanuwanta cike da hawaye.

“Please please ku bar ni inganshi. Ba zan yi wani hayaniya ba. I promise. Ya min taimako a rayuwata. Shi ya tayani gano babana. Ina so in ganshi please please.”

Kallon Nana suke su dukansu. Ɗaya daga cikin likitocin ya gane Nana. Murmushi ya yi. Koma bai ganeta ba ba zai iya hanata ba.

Cewa ya UK su jira yaje ya yi magana da wani cikin family ɗin Nawaf ɗin. Yakai mintina goma kafin ya dawo ya ce za su iya wucewa.

Sosai suka yi mishi godiya. Wannan karon Fu’ad bai sauke Nana ba. Shi ya ɗauke ta har suka ƙarasa ɗakin da aka faɗa musu.

*****

Sam allurarar baccin da sukai ma Nawaf ta ƙi kama shi. Wani irin kuka Nuriyya ke yi mai taɓa zuciya. Tana kallon murmushin da Nawaf ke son mata cikin idanuwanshi.

“Ki yafe min Nuri. Ki yafe min duk abinda na yi miki.”

Hannunshi ta sake damtsewa gam. Bata son wannan kalaman da yake ta maimaita mata tun ɗazun.

“Ki faɗa kin yafe min inji da kunnuwa na.”

Da ƙyar cikin kuka ta ce,

“Na yafe maka Nawaf. Ka yafe min nima.”

Da ƙyar ya ɗan gyara kanshi da alama hakan ba ƙaramin wahala ya yi mishi ba.

“Na gode Nuriyya. Ina sonki. Zuciyata ke kaɗai ta ke so. Kece ta farko a cikinta kuma ke zaki zama ta ƙarshe.

Ina Farhan?”

Tambayarshi ta mata wani iri. Ɗago ido ta yi ta sauke su kan Farhan da ke gefe. Ya ji tambayar da Nawaf ɗin ya yi.

Don haka ya ɗan ƙarasa. Sai lokacin family ɗin Nawaf suka gane wanene shi ɗin. Don ba ma ta shi suke ba.

“Ka kula da ita. Ka so ta fiye da yadda na sota. Karka bar hawaye ya zuba a idanuwanta kamar yadda na yi.

Karka ɗaga hannunka akanta kamar yadda na yi. Ka zama farin cikinta tunda na kasa. Ka kula da Nuri Farhan.”

Duk wani haushin Nawaf da yake ji ya nema ya rasa. Don yanzun ya tabbatar da Nawaf da babanshi mutanene ne mabanbanta.

Duk abinda ya faru da ya masa fahimta ya fahimci Nawaf na son Nuriyya. Son da ya ke tunanin ko shi ba zai iya mata ba.

Sai yanzun ya fahimci taimakon da Nuriyya ke faɗin Nawaf na buƙata. Muryarshi a dakushe ya ce,

“Kai za ka kula da Nuriyya. Kai za ka zama farin cikinta. Saboda duk muna tare da kai.

Zamu taimaka maka.”

Baice komai ba. Saboda yadda ya ke jin a jikinshi sun gama taimaka mishi. Idanuwanshi ya kai kan mamanshi da babanshi da suke tsaye sun zuba mishi idanuwa.

Kallon da yake musu ya sa ya suka ƙarasa inda yake da sauri. Farhan ya matsa musu ya na komawa gefe.

Cikin sanyin murya ya ce,

“Ku yafe min . Na saka ku ɓacin rai da yawa a rayuwata. Ku taya ni roƙon Allah ya yafe min …”

Kuka sosai Mama take yi. Yana jin kukansu har cikin zuciyarshi.

“Ina su yaya Khamis.”

Dukkansu suka ƙaraso inda yake. Suma yafiyarsu ya nema. Ibrahim ne ƙarshe. Shaƙuwarsu daban ce ko a cikin ‘yan uwanshi.

Kallonshi Ibrahim ya ke yi da wani irin yanayi.

“Karka fara Nawaf. Muna tare. Babu inda za ka je. In ka tafi dawa zan kula?”

Da ƙarfin hali ya yi masa murmushi saboda ciwukan da ke fuskar shi.

“Za ka kula min da su mama. Za ka kula min da duk wanda na damu da su. Za ka kula min da kanka.

Yaya na gaji sosai.”

Dafa shi Ibrahim ya yi. Ya miƙe yana fita daga ɗakin . Dai dai zuwan wani likita da ke tambayarshi wasu abubuwa da bai fahimta ba. Ya dai amsa shi da to ne kawai.

Yana nan tsaye ya hango wasu su biyu suna ƙarasowa inda yake tare da wata yarinya kyakkyawa a sabe a kafaɗar namijin.

Ƙarasowa suka yi wajen shi suka yi mishi sallama ya amsa musu. Fu.ad ya ce,

“Nan ne ɗakin da Nawaf yake?”

Kallonsu yake don bai gane su ba sam. Zai iya rantsewa bai taɓa ganin su ba. Hakan Fu’ad ya fahimta ya ce,

“Muma ba mu sanshi ba. Ka ga wadda ta sanshi nan. Ya mana karamcin da ba zai mantu ba.

Shi ya sa muke son ganinshi in ba damuwa.”

Yadda Nana ke ƙoƙarin ya sauketa ne yasa shi sakkota a hankali. Ƙarasawa ta yi ta kama hannun Ibrahim.

“Don Allah ka bari in ganshi. Zan mishi godiya ne kawai.”

Ɗan dafe kai Ibrahim yayi. Inhar sunce Nawaf ya musu karamci waye shi da zai hana su ganshi. Da kanshi ya kama hannun Nana zuwa ɗakin.

Su Fu’ad na biye da su. Kallo ɗaya Safiyya ta yi mishi ta yi baya idanuwanta na kawo hawaye. Bata da juriya irin wannan don haka ta dakata.

Ko shi Fu’ad daga gefe ya tsaya. Kallon ahalin Nawaf yake. Yadda suke a hargitse yana jin zuciyarshi na cika da wani irin tsoro.

A hankali Nana take takawa har inda Nawaf yake kwance da wata a gefenshi tana wani irin kuka. Su dukansu kallon Nana suke.

Dai dai fuskarshi ta tsaya tana kallon shi.

“Ya jikinka?”

Ta tambaya. Sosai Nawaf yake kallonta yana son gane inda ya taɓa ganinta. Ga zuciyarshi na wani irin zafi. Yana jin yanda yake kokawa da numfashin shi.

“Da sauƙi.”

Ya faɗi a hankali.

“Na ga babana.”

Tace mishi. Sai lokacin ya tunata. Oh rayuwa kenan. Cike da taushin murya yace mata.

” Naji daɗi. Ya jikinki.”

Ɗan daga kafaɗa ta yi alamar yana nan kafin ta ce,

“Zan maka godiya ne. Da banga Babana ba ba don kai ba. Ba haka naso in ganka ba.

Na kasa ganewa ni fa. Na rasa me yasa mutuwa ta zaɓe ni. Kuma ka ganka yanzun.”

Murmushi Nawaf ya yi mata kafin ya ce,

“Lokaci da dama mutuwa tana da ruɗani. Sai dai hutu ce ga mumini.

Ina son in huta. Ina son in samu nutsuwa.”

Jinjina kai Nana ta yi kamar ta gane me yake nufi. Fu’ad ya ɗan dafa kanta. Ya kalli Nawaf.

“Mun gode sosai Nawaf. Allah ya ba ka lafiya.”

Sai yake jin wata nutsuwa ta daban. Ko ba komai sanadin shi wannan yar yarinyar ta gane babanta. Da idanuwa ya amsa saboda ya gaji sosai. Sosai nana ta matsa kusa da kunnen shi yadda ba mai iya ji ta ce,

“Kana jin tsoro?”

Shi ma da raɗa ta kai kunnenta ya ce mata,

“Sosai. Amma ganinki ya sa na daina.”

Wani murmushi tayi kafin ta sake ce mishi cikin kunnenshi,

“Na gode. Allah ya baka aljanna. Sai mu zama abokai acan.”

Lumshe idanuwanshi ya yi yana jin ƙaunar Nana har ranshi. Kama hannunta Fu’ad ya yi. Ta ce,

“Zan dawo…”

Bai ce mata komai ba. Har sunkai ƙofa ya ce,

“Ya sunanki?”

Juyowa ta yi da murmushin nan sannan ta ce,

“Nana Safiyya.”

Kai ya yi ƙoƙarin ɗaga mata wani irin tari ya sarƙe shi. Da gudu Nana ta yi niyyar ƙarasawa ganin yadda jini ke fitowa daga bakinshi Fu’ad ya ɗauke ta.

Kwantar da ita ya yi a ƙirjinshi tana wani irin ihun kuka ya fita da ita daga ɗakin da gudu.

Gaba ɗaya family ɗin Nawaf suna kanshi. Sun rikice sosai kowa ƙwala mishi kira yake.

Nuriyya tana riƙe dashi da hannunta tana jijjigashi.

“Nawaf ina za ka tafi ka bar ni?”

Sosai ta ke kuka. Shi kanshi Farhan wasu hawaye ya ji sun cika mishi idanuwa. Mama kuka take kamar za ta shi&e.

Yaya Khamis ya kasa ko da motsawa daga inda yake. Baba ne ya ga yadda numfashin Nawaf ke sama ya soma karanto mishi kalmar shahada da ƙarfi.

Aikam kaman Nawaf ya na saurarenshi. Yana karanto mishi muryarshi na rawa. Nawaf ɗin na maimaitawa ɗaya bayan ɗaya.

Dagaji harshen shi har ya karye. Kuka suke sosai. Ibrahim na riƙe da hannunshi ɗaya yana kallon yadda numfashin shi ke sarƙewa.

Muryarshi ba ta fita sosai. Kafin komai ya tsaya!

Fita Mama ta yi daga ɗakin. Yaya Khamis ne ya ƙaraso yasa hannu ya rufe mishi idanuwanshi yana zubda hawaye.

Kallonshi Nuriyya take yi. Tana jinta kamar ba a duniya take ba. Ibrahim miƙewa ya yi yana ja da baya. Ya kasa yarda Nawaf ya bar su.

Ya kasa yarda da abinda yake gani. Mama na miƙewa ta yanke jiki ta faɗi. Da gudu sukai kanta. Nuriyya kuwa ta  zuba ma Nawaf idanuwa.

Tana kallon murmushin dake kan fuskarshi. Hannu ta sa a hankali ta taɓa jikinshi. Sanyi ta ji ya yi ƙarara.

Girgiza kai take yi. Sake taɓa shi ta yi kafin a hankali ta jijjigashi. Gani ta yi yaƙi motsi. Gaba ɗaya yanayinshi ba iri ɗaya bane da nata.

Miƙewa ta yi tana girgiza kai. Wata irin gigitacciyar kara ta saki tana faɗuwa ƙasa!

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×