Skip to content

Akan So | Babi Na Talatin Da Tara

0
(0)

<< Previous

Three-piece suit ya saka baƙi da fari. Bai sha wahalar ɗora ta saman ba, don baya son takura ko kaɗan. Yanzun ma don inda za shi baya son a mishi kallon ƙaramin yaro ne, kuma ba shi da wasu manyan kaya ko ɗaya.

Da can ma ba sakawa yake ba. Ballantana yaushe rabonshi da Nigeria. Turaruka ya feshe jikinshi da su sannan ya fito.

A falo ya samu su Momma suna karyawa. Ya gaishe da su a ladabce sannan ya zauna. Wata irin yunwa yake ji.

Sosai ya ci dankali da ƙwan da Momma ta zuba mishi ya haɗa da tea sannan ya miƙe yana faɗin,

“Momma bari in je in kawo Nana ɗin. Amman ina so in biya ta gidan lukman dan kar ya fita aiki kafin in wuce in ɗauko ta.”

“A dawo lafiya. Ka gaishe da Lukman ɗin. Na ce kwana biyu bai kawomun Junior ba.”

Murmushi Fu’ad ya yi tare da ɗaga mata kai. Ya maida hankalinshi kan Abba.

“Abbah ba kai min addu’a ba.”

Murmushi Abba ya mayar mishi.

“Allah ya tsare ya kuma sanya albarka.”

“Amin. Hassan bai tashi bane?”

Fu’ad ya buƙata. Momma ta amsa shi da,

“Ai ya tsufa wajen aiki. Yana riga kowa tashi.”

Wucewa Fu’ad ya yi yana faɗin,

“Alright. Sai na dawo.”

*****

“Mummy don Allah in kwana?”

Ɗan jim Safiyya ta yi tana jinjina maganar Nana. Bawai ba ta so ta kwana bane. Ta san kewa zata dame ta. Amma tana buƙatar sanin dangin babanta. Su ma su santa. Ko ba komai sun nuna mata ƙauna lokaci ɗaya.

“Sai dai zaki tafi da magungunanki. Ki ba wa Momma su duka.”

Da sauri Nana ta ce,

“I promise zan sha duka. Na gode Mummy.”

Murmushi kawai Safiyya ta yi mata. Ta ɗauko mata kayan da za ta saka da kuma wasu kala biyu sai na bacci sa takalma guda biyu.

“Mummy ki bani cikin wanda dady ya siyo min jiya.”

Ɗan dafe kai Safiyya ta yi. Ta manta da kayan shaf. Miƙewa ta yi taje ta ɗauko mata su. Ta zazzage waɗancan daga leda ta saka mata sababbin.

Purple hijab ɗin data ɗauko mata za ta mayar. Ta riƙe da faɗin,

“Zan sa wannan.”

Sakar mata Safiyya ta yi. Ta barta anan tana ɗaukar wani riga da pencil trouser cikin wanda Fu’ad ya siyo mata. Ta san Nana ba ta son a tayata shiryawa in ba bata da lafiya sosai ba.
Don haka ta shiga wanka ta barta anan tana shiryawa abinta.

*****

Fu’ad bai samu Junior a gida ba. Kasancewar juma’a ce ya tafi makaranta. Yau dai sai da Lukman ya ja shi har cikin gidan suka gaisa da Zainab.

Yanayin karamcin Zainab ya burge Fu’ad. Suna gama gaisawa ta yi mishi godiyar mashin ɗin da ya siya wa Junior ta bar musu wajen.

Lukman ya ce mishi,

“Allah ya bar zumunci.”

Daƙuna fuska Fu’ad ya yi yana hararar Lukman.

“Bana son iskanci Lukman.”

Dariya ya yi.

“Daga na maka godiya.”

Juya idanuwanshi ya yi. Sarai yasan Lukman ɗin neman magana ne. Don haka ya share. Numfashi ya sauke ya ce,

“Na gano iyayen Sofi Lukman. Ga address ɗin nan ma.”

“Ma shaa Allah. Kai amma na ji daɗi sosai wallahi. Allah kenan. Gaskiya na ji daɗi. Ka faɗa mata ne?”

Girgiza ma Lukman kai ya yi.

“Na ce ta shirya dai za mu je wani waje amma ban faɗa mata ba. Na fi son in yi surprising ɗinta.”

Ɗan ɗaga kafaɗa Lukman ya yi.

“Da ka faɗa mata dai.”

Sake girgiza kai Fu’ad ya yi.

“Ni ba ma wannan ba, kasan me?”

“Sai ka faɗa….”

Kaf yadda suka yi da Nana Fu’ad ya fada wa Lukman ya ɗora da cewa,

“Ba zai zama adalci wa Sofi ba Lukman. Banda abinda zan ba ta. Na barta shekarun nan don ta samu farin ciki.

In…. In har aka ce babu Nana zai zama kamar zamu raba zunubaina ne da ita bayan ba ta yi komai ba…”

Dafa kafaɗarshi Lukman ya yi.

“Idan ka duba rayuwar Fu’ad ba komai bane a cikinta sai tarin wahala. Jin dadin da ke cikinta ƙalilan ne.

Na san tabbas ba zai zama adalci wa Safiyya ba. Rashin yara ba ƙaramin abu bane ko ga matar da ba ta san daɗin su ba ballantana.

Amma na yarda da Nana. Ba fata nake ba. In babu ita kana buƙatar Safiyya. Haka duk yadda Safiyya za ta nuna akwai soyayyarka a tattare da ita.

Tana buƙatarka… In har za ta aureka ina bayan Nana.”

Dafe kai Fu’ad ya yi. Zai iya jure rashin Safiyya in har za ta yi farin ciki,

“Banda abinda zan ba ta…”

Katse shi Lukman ya yi.

“Bance kana da shi ba. Amma akwai soyayyarka ko? Za ka ce min ba ka sonta ne?”

Ɗaga girarshi ya yi sama duka biyun tare da faɗin,

“Ina jin haushinta. Ta ɓoye min Nana.”

“Really? Da gaske kana jin haushinta ta ɓoye maka Nana?”

Lukman ya tambaya cike da jin haushin rashin adalcin dake cikin maganganun Fu’ad ɗin.

Cikin ɗacin rai ya ce,

“Sosai ma. Ba ta da right ɗin da za ta ɓoye min ita. Ba ta da shi…”

Gyara zama Lukman ya yi. Yasa hannu ya ɗan daki goshin Fu’ad ɗin. Da ya ture hannun Lukman yana fadin,

“Meye haka?”

Wani murmushin takaici Lukman ya yi.

“Ina so in gani ko kana bacci ne in tasheka?”

Ɗaga mishi gira Fu’ad ya cike da alamun cewar bai fahimci me ya kawo wannan cikin maganar da ya yi ba.

“Me kake so Safiyya ta yi Fu’ad? Ka sa ƙafa ka tafi? Ta je filin jirgi ta sa musu kuka su kai ta ƙasar da ka ke? Bayan bata sani ba?”

Magana Fu’ad zai yi lukman ya katse shi.

“Ka bari in gama please. A halin da ka barta ɗan sauran hankalin da ke jikinta kake so shi ma ta miƙa maka? Ka taɓa tunanin bari ka dawo saboda bata da kowa a garin Kano sai kai? Ka taɓa tsayawa ka ce me za ta yi ta ci abinci? Ka taɓa tunanin ita kaɗai za ta dinga kwana a ƙarancin shekarunta? Ko ka manta Akan so ta bar komai da kowa nata?

Fu’ad ka manta kai ne komai nata kafin ka yanke hukuncin sakinta lokacin da ta fi buƙatarka?

Rannan a asibiti bata faɗa maka ta yi ƙoƙarin nemoka lokacin da ta gane tana da ciki ba?

Allah kaɗai yasan ruɗanin da ta shiga da ɗimauta na renon cikin Nana ita kaɗai ba tare da mataimaki ba.

Ina tare da Zainab daga ranar da ta samu cikin junior har haihuwarshi. Wallahi sai da na ƙara ganin darajar Hajiya ba kaɗan ba. Don Allah in har za ka ga laifin Safiyya ka daina furta shi a gabana. Saboda raina ɓaci ya ke sosai. Kana tunamin abubuwan da na zaɓi na manta.”

Maganganun Lukman yawo suke masa cikin kai suna sanyaya mishi duk wata gaɓa da ke jikinshi.

Lokaci ɗaya wani irin laifi mai girma yake mishi mayafi. Cikin son kauda yanayin ya ce,

“Na sa ana turo mata kuɗi. Ana turo mata kaso biyu cikin duk wani abu da zan samu.”

Girgiza kai Lukman ya yi yana faɗin,

“Hmm. Babu abinda zai ma laifinka adalci Fu’ad. Kuɗi bakomai ba ne in har babu kulawa.”

Lumshe idanuwa Fu’ad ya yi. Lokacin da ya ke jin komai ya kusan daidaita sai kuma komai ya dawo mishi baya. Ajiyar zuciya ya sauke. Ya miƙe tsaye yana saka hannayenshi duka biyun ya goge fuskarshi da ya ke jin alamar zufa.

“Zan gyara komai.”

Miƙewa Lukman ya yi.

“Karka ce zaka ɗora sabon gini akan foundation ɗin da ka bari. Ya riga da ya lalace Fu’ad.

Ka sake komai daga farko. Ka tabbata ka yi shi da ƙwari.”

A sanyaye ya amsa da,

“In shaa Allah. Na gode Lukman. Na gode da komai.”

Jinjina mishi kai ya yi suka yi sallama. Da wani irin nauyin jiki Fu’ad ya buɗe mota ya shiga.

*****

Handle ɗin ƙofar ya kama ya murɗa. A hankali ya tura tare da yin sallama. Bai rufe bakin shi ba ya ji Nana a jikinshi ta maƙale shi.

Bai san lokacin da murmushi ya ƙwace mishi ba. Duk yanayin da ya ke ji bai hana wani farin cikin ganin Nana da bai san daga inda ya fito ba ziyartarshi. Tsugunnawa ya yi don tsayinsu ya zo daidai ya ce mata,

“Princess ta yi kyau.”

Dariya ta yi a kunyace tare da faɗin,

“Ka yi kyau sosai kaima. Ina kwana.”

“Kin tashi lafiya? Yanzun da na shigo ne kika shafa min kyanki.”

Dariya Nana ta sake yi.

“Ni ina lafiya. Kai mana pictures…”

Kafin ya amsa ta ce,

“Kai!  Na manta. Bari ɗauko camera ɗina…”

Ya buɗe baki ta bar jikinshi tana rugawa da gudu.

“Oh. Nana!  Kibi a hankali.”

Ai bata ma jishi ba ta shige ɗaki da gudu. Ita take gudun shi zuciyarshi ke dokawa karta faɗi. Safiyya ta fito sanye da Atamfa. Ɗinkin simple ne sai dai ya karɓeta sosai.

Fuskarta babu yabo ba fallasa ta ce mishi,

“Ina kwana.”

Idanuwanshi kafe akanta, zuciyarshi na karanta mishi kyawun da ta yi ya amsa da faɗin,

“Kin tashi lafiya? Su Momma na gaishe da ke.”

“Alhamdulillah. Ina amsawa. Na gode. Ka ce ina gaishe da su nima.”

Zai amsa Nana ta fito da gudu da camera ɗin a hannunta. Gaban Fu’ad ta tsaya tana danne-danne a jiki. Kafin ta ɗaga camera ɗin saitin shi tana faɗin,

“Dady me ka fi so?”

Dariya ya yi. Ya kalli Safiyya yana buɗe mata idanuwa yana son tambayarta me zai ce?

Taɓe baki ta yi. Tana sake tamke fuska. Ganin da Nana ta yi ya kalli Safiyya ya sa ta taɓare fuska tana turo baki ta ce,

“Dady na ɗauka ka fi sona.”

Sai lokacin ya dawo da hankalin shi kan Nana yana mata kallon ‘Me ki ka ce?’

Sake turo baki ta yi.

“Haka nace me ka fi so. Ka kalli Mummy.”

Safiyya dake tsaye ta ce,

“Nana!”

Dariya ta yi ta juya camera ɗin saitin Safiyya.

“Ke me kika fi so?”

Fu’ad Safiyya ta kalla da ya amsa tambayar Nana da hankalinta na kanshi.

“Mummy!  Kema?”

Da sauri Safiyya ta ce,

“Ke Princess. Na fi sonki.”

Shagwaɓe fuska Nana ta yi.

“Dady kika fara kallo kema. Zan je wajen granny na san ita ta fi sona.”

Dariya Fu’ad ya yi ya kamo Nana jikinshi.

“In ji waye. Ina son Princess fiye da kowa.”

Murmushi Nana ta yi tana ɗaga camera ɗin saitinsu ita da Fu’ad tare da faɗin,

“Hello. Ga M. Shi ne Dadyna. Dady say Hi.”

Dariya Fu’ad ya ke sosai. Yadda take ma camera ɗin magana kamar wata mutum.

“Nana camera ne fa.”

Dire ƙafafuwa Nana ta yi.

“Dady be nice. Ina son camera ɗin nan sosai fa.”

Dariya Fu’ad ya sake yi. Nana ta daƙuna mishi fuska sannan ya soma ƙoƙarin controlling dariyar.

Yadda kome Nana ta yi ya ke sa shi dariya har mamaki ya ke bashi. Da dariyar a muryarshi ya ce,

“Hi camera”

Yana daga hannu. Gaba ɗaya yadda ya biyewa Nana suka zama wasu ‘yan yara ya ba Safiyya dariya. Da sauri ya ɗaga idanuwa ya kalleta. Murmushi ya ke. Yana tuna yadda yake son dariyarta.  Yadda idanuwanta ke cika da wani abu da ba zai iya ɗora ma kalamai ba.

Camera ɗin Nana ta mayar saitin Safiyya tana faɗin,

“Mummy na dariya.”

Girgiza kai Safiyya ta yi. Ta san video Nana ke ɗaukar su.

“Ban iya shiririta ba Nana. Wuce ki ɗauko kayanki ku tafi.”

Sai lokacin Nana ta juyo cike da jin daɗi ta ce wa Fu’ad,

“Mumy ta ce in kwana wajen granny.”

Shi ma ya ji daɗi. Nana ta wuce za ta ɗauko kayanta. Da idanuwa yake nuna ma Safiyya godiyarshi can gefen zuciyarshi girman laifin shi da Lukman ya nuna mishi na nan manne.

“Kin shirya? In mun sauke Nana kuka gaisa da Momma sai mu wuce ko?”

Sauke numfashi Safiyya ta yi.

“Na ɗauka tun jiya na ce maka ba zan je ba?”

Miƙewa tsaye Fu’ad ya yi. Ya tabbata ya sauke idanuwanshi cikin nata kafin ya ce,

“Ki yarda da ni. In bai da muhimmanci ba zan tambaye ki ba.”

“Kamar yarda da kai a baya ya min wani amfani.”

Ta faɗi muryarta cike da takaici. Ya ji zafin maganar da ta yaɓa mishi har ranshi. Sai dai wannan ba lokaci bane da zai tsaya yana mata bayani tunda ya san ko me ta faɗa shi ya janyo.

“Sofi please…”

Wani murmushi ta yi da haƙoranta kawai ta buɗe mishi. Kafin ta haɗe fuska.

“Ka iya wannan ka tsaya kana bani umarni kamar ‘yarka?”

Shirun dai ya yi. Don ba shi da bakin magana yau.  Yana kallon hararar da ta watsa mishi kafin ta wuce cikin bedroom ɗin. Sauke ajiyar zuciya ya yi.

Bata san ina Fu’ad ya ke so su je ba. Sai dai ta rasa me yasa gabanta yake ta faɗuwa tunda safe. Bata kuma san dalilin da ya sa take son ta bishi ba.

Koma ina ne, koma mene ne za ta iya tarar Napep ta dawo in bai mata ba. Mayafinta ta ɗauka ta yafa. Ta kamo hannun Nana suka fito. Murmushi ya ƙwace ma Fu’ad saboda yadda suka yi mishi kyau kamar ya sace su. Wayar shi ya ɗauko ya buɗe camera ya ƙarasa inda suke ya tsaya gefen Nana.

“Me za ka yi?”

Safiyya ta tambaya. Bai kulata ba ya ɗaga camera ɗin yana musu hotuna kala biyu sannan ya kama hannun Nana suka fice. Ta girgiza kai kawai. Ƙarfin halin shi na bata mamaki. Sam bata so ta tuno buƙatar Nana akanshi. Yadda ta kwana da abin a ranta kawai ya isheta ba sai ta tsokano shi da safiyar nan ba. Sai da ta kulle gidan sannan ta same su a mota.

Nana ta shiga gaba ita da Fu’ad. Safiyya kam bayan motar ta buɗe ta zauna. Tana jero addu’o’i a zuciyarta saboda bata san dalilin bugun zuciyarta ba.

*****

Ba ƙaramin daɗin ganinsu Momma ta ji ba. Suka gaisa da Safiyya. Su zauna Fu’ad ya ce,

“Momma sauri muke. Akwai inda za mu je ki mana addu’a.”

“Aika bari dai ta ɗan huta ko?”

Girgiza kai ya yi.

“Yau Juma’a fa. Gashi har sha ɗaya ta kusa. In muka dawo sai mu biyo.”

Jinjina kai Momma ta yi.

“A dai kula din Allah. Sai kun dawo. Allah ya bada sa’a.”

A sanyaye Safiyya ta ce,

“Amin. Mun gode Momma.”

Ɗan tsugunnawa Fu’ad ya yi ya sumbaci Nana a kumatu.

“Banda rashin ji okay?”

Kai ta ɗaga mishi tana murmushi.

“Love you kai da Mummy.”

Murmushi Safiyya ta yi sannan suka juya ita da Fu’ad ɗin suka fice. Bayan motar ta buɗe ta shiga tana wani ɗaure fuska.

“Ba magana zan miki ba. Ni bana son neman rigima ko kaɗan.

Cewar Fu’ad da ya shiga motar yana jan murfin. Ta ji shi sarai. Ta zaɓi ta yi shiru ne kawai saboda jin su ita kaɗai da shi cikin motar ya isheta. Yadda zuciyarta ke son ƙwacewa da gudu ta kaita ziyara lokuta da yawa ya isheta yaƙi da. Ba sai ta tsaya kula Fu’ad ba.

Ta mudubi ya kalleta. Yadda ta lafe jikin kujerar motar tana lumshe idanuwa. Addu’a ya yi ta neman sa’a kafin ya murza key ɗin motar.

*****

Ga mamakin Safiyya bakin wani gida suka yi parking. Fu’ad ne ya fito ya bar ta cikin motar. Tana kallonshi yana ɗaga kai yana kallon lambar gidan.

Tsaye ya yi yana ‘yan waige-waige kafin ya ga wata yarinya ta zo wucewa.

“Ke!  Zo don Allah.”

Kallon Fu’ad yarinyar ta ɗan yi a tsorace ta tsaya. Shi ya matsa inda take ya ce mata,

“Anan unguwar ki ke?”

Kai ta ɗaga mishi. Ya ɗan ja numfashi ya fitar tare da faɗin,

“Ko kinsan sunan mai gidan nan?”

Da mamaki bayyane a fuskar yarinyar ta amsa shi da faɗin,

“Malam Audu.”

Wani tsalle zuciyar Fu’ad ta yi.

“Matarshi fa?”

“Ni ban san sunanta ba. Kowa Inna yake ce mata.”

Ganin ta soma gajiya da tambayoyinshi ya sa shi faɗin,

“Na gode sosai. Don Allah ki ɗan shiga ki ce musu sun yi baƙi.”

Ba musu yarinyar ta shiga. Bata fi mintina uku ba ta fito ta ce,

“An ce ka shiga.”

Godiya ya yi mata. Ta jinjina mishi kai kawai ta wuce abinta. Ji ya yi jikinshi ya yi wani iri. Da ƙyar ya ƙarasa ya ce ma Safiyya,

“Fito mu je.”

Yanayin shi da ta ga ya sauya lokaci ɗaya yasa ta mayar da musun da take son mishi ta buɗe motar ta fita. Matsawa ya yi yasa hannu ya zare key ɗin motar shi ya kulle ta yasa a aljihu sannan ya kama hanya suka nufi gidan.

Tunda suka taka cikin soron gidan zuciyarta ta tsananta dokawar da take har Fu’ad ya yi sallama yana danna kai.

*****

“Ai da kin bari na leƙa na ga ko su waye.”

Jinjina kai Inna ta yi da ke zaune kan darduma. Shi kuma yana saman kujera.

“Ba zai shige yaron nan ya yake da suna ba. Abokin wannan ɗan da ya ce zai kawo matarshi ta gaishe damu yau.”

“Au, Na ma manta fa.”

Sallama suka ji.

“Wa alaikumussalam. Ku shigo.”

Inna ta fadi. Tana janyo hijabinta da ke ajiye gefe ta saka.

*****

Wani irin dokawa zuciyar Safiyya ta yi. Muryar da ta amsa sallamar. Shekaru sha biyu ba zai sa ta mantata ba. Sai dai gasgata cewar ba kunnenta bane yake mata gizo abu ne mai wahala. Ƙafafuwanta ta ji suna mata rawa. Ga wani irin tsoro da ya cika mata zuciya. Fu’ad ya soma sa kai cikin gidan yana sake yin sallama.

Sosai Inna ke kallon shi tana son tuna inda ta san fuskarshi. Baba da ke zaune ya dafa kujera ya miƙe saboda yanayin rauni na manyantaka da ya kama shi.

Duk da sajen da ke kwance fuskar Fu’ad bai hana shi gane shi ba. Babu yadda za a yi ya manta fuskar da ya ke kwana da ita a zuciyarshi ya tashi da ita.

Fuskar da ta yi sanadiyar salwantar ‘yarshi. Baki Baba ya buɗe yana kallon Fu’ad ya ɗaga hannu yana nuna shi sai dai kalma ko ɗaya ta ƙi fitowa daga bakin shi. Duk da zuciyarshi cike take da tambaya guda ɗaya,

“Ina ‘yata?”

Sai dai ya kasa furtawa saboda yadda yake jin wani jiri na ɗibar shi. Kallon su Fu’ad yake yana jero godiya wajen Ubangiji da ya tabbatar mishi da wannan nasarar. Matsawa ya yi gefe ya kasa ƙarasawa cikin gida. Sai lokacin Safiyya ta samu damar shigowa, don Fu’ad ya tare hanya.

A hankali idanuwanta suka sauka kan Inna da ke zaune. Sannan ta maida dubanta wajen Baba da ya ke tsaye idanuwan shi cike da rashin yarda cewa ita ce.

Wani abu take ji yana mata yawo tun daga ɗan yatsan ƙafarta har zuwa tsakiyar kanta. Lokaci ɗaya jikinta ya ɗauki kyarma.

Kafafuwanta take so ta matsar su ƙarasa da ita wajen su Inna da take hangowa ko sau ɗaya ne ta nemi gafararsu kafin su ɓace mata. Kafin ta farka daga mafarkin nan da take yi su sake suɓuce mata, amma ta kasa. Ta kasa saboda yadda babu ƙarfi ko kaɗan cikin ƙafafuwanta.

Tana kallo Baba yana takowa. Duk da tsufan da ya yi bai hanata ganin shi ba. Bai hanata gane shi ba. Tana jin raunin da take gani cikin tafiyarshi har zuciyarta.

Gani take ya fi awa ɗaya bai ƙaraso ba. Gani take wata ƙaddara za ta iya giftawa kafin ya ƙaraso gareta saboda ita ta kasa kaiwa inda ya ke. Numfashinta take kokawa da shi wajen fita saboda tashin hankalin da take ciki.

Gab da ita Baba ya ƙaraso ya ƙura mata idanuwa. Riƙe numfashi Safiyya ta yi tana tsoron kar ta sake shi Baba ya ɓace. Karta saki numfashin da ta ja ta farka daga mafarkin da take.

Tana jin yadda ƙirjinta ke zafi da neman iska. Kanta ke wani irin juyawa saboda ƙarancin iska amman ta ƙi sakin wadda take riƙe da ita ballantana ta shaƙi sabuwa.

Za ta iya jure kowace azaba a yanzu in har hakan na nufin ba za ta kuma kokawa azabar rashin su Inna ba. Cikin rawar murya Baba ya juya ya kalli Inna yace,

“Taso ki gani. Safiyya ce. Safiyya ce ta dawo!”

Da sauri Inna ta taso har tana sassarfa. Gefen Baba ta tsaya. Don ta ƙi tasowa ne kar ta zo ta ga ita kaɗai ce Safiyya ke ma gizo kamar yadda take mata lokuta da dama.

Hannu ta sa ta taɓa kuncin Safiyya tana son jin ko da gaske ita ɗin ce. Jin hannun Inna a kuncinta ya sa Safiyya sakin numfashin da take riƙe da shi. Muryarta na wani sama-sama ta riƙe hannun Inna gam tana faɗin,

“Innaaaaa!”

Idanuwanta ta mayar kan Baba da ke tsaye. Ɗayan hannunta ta kai ta kamo nashi tana dumtse wa sosai cikin nata zuciyarta na wani irin dokawa.

“Babaa!”

Tana jin yadda zuciyarta ke rage gudu alamar za ta iya samun matsala ko da yaushe. Tana jin yadda ɗan ƙarfin halin da take da shi saboda Nana yana rugujewa.

Tana jin yadda ko’ina na jikinta ke buɗewa da buƙatar iyayenta da ta dinga ɗinkewa a tsawon shekarun nan saboda Nana na buƙatarta.

Wani irin jiri na ɗibarta take faɗin,

“Ku yafe min Inna… Baba ka yafe min. Don Allah… ku yafe min…”

Tana jin yadda duniyar ke juya mata. Kafin ƙafafuwanta su ƙarasa mutuwa, da neman yafiyar su Inna a bakinta ta yi ƙasa. Tana wani irin fitar da numfashi kafin komai ya tsaya!

Su duka ukun kanta suka yi. Inna na tallabe da ita a jikinta tana jijjigata. “Safiyya ki tashi. Wallahi mun riga mun yafe miki da daɗewa. Don Allah ki tashi…”

Hannunta Baba ya kama.

“Safiyya tashi kin ji. Mun yafe miki ai tun tuni. Kin ji Innarki ma ta ce ta yafe miki. Ki tashi tunda Allah ya haɗa fuskokinmu da rayuwar mu.”

Fu’ad ya rasa me ya kamata ya yi. Buta ya hango da gudu ya ƙarasa ƙarshen gidan ya ɗauko butar. Ruwan ya zuba a hannunshi ya yayyyafa wa safiyya da ke jikin Inna. A hankali take motsawa kafin ta soma buɗe idanuwanta. Sama-sama take jin muryar Inna na faɗin,

“Safiyya… Safiyya ki tashi ki ga mun yafe miki…”

Ware idanuwanta ta yi jin muryar Inna. Ta ko sauke su kan fuskar Inna. Da sauri ta miƙe daga jikinta. Hannuwanta ta sa ta tallabi fuskar Inna. Tana so ta gani da gaske ba mafarki take ba su Inna ne a gabanta. Sannan ta maida dubanta wajen Baba da ke zaune kan siminti ba tare da ya damu ba.

Yadda take ji a zuciyarta ba zai taba faɗuwa ba. Allah kaɗai ya san yadda take jin rashinsu, domin shi ya rubuta mata ƙaddarar rabuwa da su. Kanta ta kifa jikin Inna tana sakin wani irin kuka mai tsuma zuciya. Inna ma kuka take sosai ta ɗora kanta a bayan safiyyar. Kuka suke sosai da ya sa Fu’ad da ya ke a tsaye jin wani abu na mishi yawo cikin idanuwa. Su duka sun ɗanɗana rashin iyaye sun ji yadda yake.

Gara shi akan Safiyya. Ba zai taɓa misalta yadda take ji ba a yanzun sai dai ya kwatanta. Kuka take sosai. Ba tare da sun kula ba Fu’ad ya fice ya ba su waje.

Ɗagowa Safiyya ta yi ta kama hannun Inna jikinta na wani irin ɓari hawaye na wanke mata fuska.

“Inna da gaske ku ne? Ba mafarki nake ba Inna?”

Kai Inna ta iya ɗaga mata. Wani irin kuka take da take jin fitowarshi na mata ciwo a zuciyarta da idanuwanta. Baba ta kalla muryarta na rawa.

“Baba don Allah ka yafe min. Wallahi na muku laifi mai girma na sani. Na kunyata ku a idon duniya. Na jefar da soyayyar da ku kai min akan wadda ta ziyarce ni daga baya. Baba na yi wauta mai girma.”

Ƙwallar da ta taru a idanuwanshi ya sa riga ya goge. Cikin rauni ya ce.

“Safiyya kin yi laifi kam. Sai dai ƙaddara ba ta wuce kan kowa. Ɓacin rai ne ya hanamu fahimtar ƙaddararki ce ta zo a haka.

Mun jima da yafe miki duk da baki sake waiwayarmu ba.”

Kallonsu take cikin tashin hankali take faɗin,

“Na je baba. Wallahi na je aka ce min kun tashi…ba wanda ya san inda kuka koma.”

Ta ƙarasa maganar wani irin kuka na ƙwace mata. Sosai Inna ta riƙe Safiyya a jikinta.

“Surutun mutane ya sa muka tashi. Maganganunsu ya sa muka baro Bichi.”

Kuka Safiyya take, yanzun kam kamar za ta shiɗe. Sanadinta sun jure ƙunci mai girma. Akan so ta ja ma iyayenta muzanci da tozarta mafi girma.

“Inna rayuwata ba za ta taɓa yin daidai ba idan ba ku yafe min ba.”

Riƙeta Inna ta yi ganin yadda jikinta ke kyarma tana faɗin,

“Mun yafe miki Safiyya. Mun yafe miki duniya da lahira. Kasancewarki tare da mu yanzun shine abu mafi girma da ya faru da mu a shekarun nan.”
Baba ya ɗauka da cewa,

“Laifinki bai sa mun daina ƙaunarki ba Safiyya.”

Kai kawai ta iya ɗaga ma Baba saboda tasan yadda girman wannan ƙaunar tasu take. Ta san yadda ciwonta yake. A haka Inna ta kama Safiyya ta ja ta suka shiga ɗaki. Baba da kanshi ya je ya ɗauko kofi ya zo ya fasa ruwa ya zuba ya miƙa wa Safiyya.

Hannuwa biyu ta sa ta karɓa ta shanye tas tana jinjina kalar ƙaunar da ke tsakanin da da mahaifanta!

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×