Skip to content

Akan So | Babi Na Talatin

1
(1)

<< Previous

Yana sauke Khadee a makaranta ya wuce gidansu. Tun daga yarinta shi Fu’ad ya ke bari da goge dauɗar ɓarnar da ya yi.

Ba baƙon abu bane wannan. Sai dai rabon da maganar Fu’ad ta gifta cikin gidansu ma an ɗauki shekaru. Momma na ƙoƙarin yi musu tun yana gidan.

Sai su yi shiru su dukansu. In abinci ake ci ba mai ƙara magana har a gama. Sai ta bari. To yanzu ɗin ma shi Fu’ad ya bari da zuwa yiwa Momma bayanin Safiyya na nan.

Ba ta bar garin ba kamar yadda suke ɗauka. Tana nan daram kuma har da yarinya. ‘Yar Fu’ad.

*****

Da sallama ya shiga gidan. Dai dai fitowar Hassan daga shi sai 3 quarter da singlet. Da fara’a ya amsa sallamar tare da faɗin,

“Yaya Haneef ina kwana.”

“Antashi lafiya? Babu aiki ne yau?”

Hassan ya ɗan sosa kai.

“Akwai fa. Yanzu nake ta shiri. Ya su Anty Ummi da Khadee?”

Kallonshi Haneef ya yi sosai.

“Khadee ai ta yi fushi. Ta na ta tambayarka.”

Dariya Hassan ya yi.

“In shaa Allah zan je in ɗauko ta ta yi mana weekend.”

“Allah ya sa. Momma ta tashi ne?”

Ɗan yamutsa fuska ya yi kafin ya amsa da,

“Tun Asuba da muka gaisa dai ba mu haɗu ba, ban san ko ta koma bacci ba. Ka kira wayarta mana.”

Kai Haneef ya ɗaga masa yana lalubo wayarshi daga aljihu. Wucewa Hassan ya yi abinshi.

Waje ya samu ya zauna ya kira Momma a waya ya ce mata yana babban falo. Ko mintina biyu ba a yi ba ta fito.

“Ina kwana.”

Haneef ɗin ya gaishe da ita a ladabce. Sai da ta ƙaraso inda ya ke sannan ta amsa shi da.

“Lafiya dai ko Haneef?”

Ɗago kai ya yi tare da faɗin,

“Lafiya ƙalau…”

Shiru ya ɗan yi yana tunanin ta inda zai fara mata maganar kafin cikin sanyin murya ya ce,

“Akan Fu’ad ne…”

Wani irin dokawa zuciyar Momma ta yi. Saboda yau kwana uku kenan ba ta samun wayar Fu’ad ɗin. Kuma bai kirata ba kamar yadda yakan yi.

Tana ta tunanin ko lafiya. Babu dai wanda za ta tunkara da maganar ne shi ya sa ta bar wa ranta abin. Jin sunanshi a bakin Haneef yau ba ƙaramin tayar mata da hankali ya yi ba.

A ƙagauce ta ce,

“Eh, me ya faru?”

Ganin yadda ta tsorata ya sa Haneef girgiza kai da saurin faɗin,

“Jiya ne Lukman ya zo min da wata wasiƙa da ta ke ta yawo a labarai da yanar gizo gaba ɗaya.

Akan wata yarinya Nana da take neman babanta. Cewar yana tunanin yarinyar ‘yar Fu’ad ce…”

Ware idanuwa Momma ta yi akan Haneef cike da ruɗanin jin maganar da ya ke yi kafin ya ci gaba da faɗin,

“Na yi kokwanto sosai ko da ya faɗa min ya je makarantarsu yarinyar ya ganta. Shi ne na yi tunanin ko Safiyya na garin nan.

Shi ne jiya da yamma bayan mun rabu da Lukman ɗin na je tsohon gidansu da Fu’ad ɗin. Momma tana nan.

Ta ɓoye mana ne saboda ba ta son alaƙa da duk wani wanda ya haɗa jini da Fu’ad bayan abinda ya faru.

Na kuma ga yarinyar. Nana ɗin. Yar Fu’ad ce babu ko musu a ciki….”

Cike da tashin hankali Momma ke kallon Haneef. Da ƙyar ta samu kanta da faɗin,

“Ta yaya? Nake jin Fu’ad ga abinda ya yi. Ba zai taɓa samun yara ba?”

Rausayar da kai gefe Haneef ya yi. Don shi kanshi bai san yadda akai ba. Koma dai ya akai yarinyar Fu’ad na nan. Sauke numfashi ya yi. Momma ta gyara zama sosai.

“Wallahi na rasa ta cewa ma. Yanzu ita Safiyyar ta kyauta mana kenan? Babu neman da ba mu yi mata ba…”

Da sauri Haneef ya ce,

“Banga laifinta ba Momma. Ta san ko gaba ɗayan mu irin halin Fu’ad ne da mu? Bama wannan ba. Duk mai sauƙi ne yanzun. Ita yarinyar…”

Katse shi ta yi da faɗin,

“In dai yar Fu’ad ce kamar yadda ka ce tana buƙatar dangin babanta. Tana kuma buƙatar babanta.

Oh Allah!”

A sanyaye ya ce,

“Tana buƙatar babanta ne fiye da mu ma. In har zai sauke son kanshi ya dawo. Saboda ba ta da lafiya. Bata da wani lokaci mai tsawo…”

Da wani sabon tashin hankali Momma ke kallonshi. ‘Yar murnar da zuciyarta ta fara yi ta na birbishewa.

“Ta na da cancer. Fu’ad ne ƙarshen hope ɗinsu akan rayuwar yarinyar…”

“Innalillahi wa ina ilaihir raji’un. Wai meke faruwa ne a rayuwar Fu’ad? Wannan yaro Allah kaɗai ya san abinda ya ɓoye kan ƙaddarar shi.”

Sauke numfashi Haneef ya yi.

“Wallahi da ƙyar na yi bacci jiya. Idan ki ka ga yarinyar…Ki ka ga Safiyya ɗin…”

Kasa ƙarasawa ya yi saboda yadda zuciyarshi ke karyewa da tunanin yanayin damuwar da ke cike da idanuwan Safiyya.

Da kuma yadda tunda yake a rayuwarshi bai taɓa ganin yarinya mai dauriyar Nana ba. Kalar ƙaunar da ya gani a tsakaninta da Safiyya bai taɓa ganin irinta ba.

Cikin wata nisantacciyar murya Momma ta ce,

“Yau zan yi magana da abbanku. Zan yi maganar da ya yi shekaru sha ɗaya yana kauce mata.

Zan kiraka anjima ko ya muka yi da shi. Ka tashi ka tafi aiki.”

Miƙewa ya yi. Don so ya ke ya ɗan fita ko iska ya sha ya ji sauƙin abinda ke zuciyarshi.

“Sai na dawo.”

“Allah ya bada sa’a…”

Har ya kai ƙofa ta kira sunanshi ya juya.

“Ka kira ƙaninka.”

Runtse mata idanuwa kawai ya yi ya buɗe su ya juya ya fice.

*****

Kwance ya ke kan kujera ta na zaune ƙasa dai dai kanshi suna kallon wani film a tablet ɗin Nawaf ɗin ‘wrong turn’.

A tsorace take saboda horror film ne. A hankali Nawaf ya lallaɓa hannu ya ja mata kunne. Ƙara ta saki tana neman yar mishi da tablet.

Dariya ya ke yi sosai.

“Nur tsoranki ya yi yawa wallahi.”

Hararar shi ta yi a cikin wasa. Hannunshi ya ɗora kan kafaɗarta yana dariya. Ya riƙota yana ɗoro kanshi gefen nata.

“Ina sonki sosai. Ki riƙe wannan ko da wata rana bana nan. Ki yafe min…”

Da sauri ta gyara zamanta ta fuskance shi. Kanta ta ɗora a jikin kujerar gaf da fuskarshi.

“Wace irin magana ka ke yi haka?”

Lumshe idanuwanshi ya yi.

“Kawai ina jin wani iri ne Nur. Ina jin kamar ba zan jima ba…”

Da sauri ta sa hannu ta rufe bakinshi don har idanuwanta sun kawo hawaye taf. Babu inda za shi ya bar ta. Zata iya tuna lokacin da ta fara sanin wani abu daɗin rayuwa.

*****

Bazata manta ranar farko da ta fara haɗuwa da Farhan ba. Ranar da yunwa ta isheta. Tun safe take jin yunwa amman Anty kamar yadda ta ke kiran mahaifiyarta ta hanata abinci.

Asalima cewa ta yi sai ta je unguwa da wani mutum da ba ta san shi ba tukunna. Ita kuma ta ce ba za ta je ba.

Akwai wani lokaci da Anty ta ce ta bi wani unguwa. Suka je tun cikin motarshi ya dinga taɓa ta. Ta yi ta zunduma ihu. Dole a hanya ya sauketa.

Hakan ya sha faruwa. Tun Anty na jibgarta kamar jaka har ta haƙura ta ƙyale ta. Reza gareta koyaushe a jikinta bata rabo da ita. Ko kusa.

Tunda ta illata mutum huɗu suke shakkar taɓa ta ko yaya. To yanzun saidai anty ta hanata abinci. Cewarta ba za ta zauna tana ci da ita a banza ba ta morarta da komai ba.

Ga makaranta ta na son komawa tun da suka yi jarabawar gama primary Kjawayenta duk sun ci gaba Anty ta ce ba za ta biya mata ba tunda ta rainata.

Tsaye take a ƙofar gida ta na ta kuka. Shi kuma ya zo wucewa ya ke tambayarta komenene. Yanayin shi lokaci ɗaya ta ji ta yarda da shi.

Kukan da take kamar ranta zai fita ya sa shi riƙe ta jikinshi yana lallashinta. A tsawon shekarunta tara a duniya Farhan ne mutum na farko da ya taɓa nuna mata irin wannan kulawar.

Ranar farko ta juye masa matsalarta tas. Tun a ranar ya tambayeta ko ta san inda ake siyar da abinci a unguwar ta ɗaga mishi kai.

Dubu uku ya ba ta ya ce ta ɓoye ta dinga siyan abinci. Haka kuwa aka yi ya yi tafiyarshi.

Ba afi sati biyu ba ba ta san ya aka yi ba ya sake dawowa. A haka rayuwar ta ci gaba da tafiyar musu. Har wata irin shaƙuwa ta shiga tsakaninsu da Farhan ɗin.

Ranar da ya kamata ya mayar da ita makaranta Anty ta fito za ta yi masa karnukanci suka ɗiibi ‘yan kallo. Farhan ya ce zai kwaso mata ‘Yan msanda ya tona mata asiri.

Dolenta ta ƙyale shi. Haka Farhan ya zamo wa Nuri wani haske cikin duhun da ke rayuwarta.

Ba ta taɓa sanin akwai wata rayuwa mai nutsuwa ba sai da ta haɗu da Farhan.

*****

Hannun Nawaf ta kamo ta dumtse cikin nata.

“Ba na son kana min irin wannan maganar sam. Ba na so.”

Miƙewa zaune ya yi tare Sumbatarta a goshi sannan ya miƙe.

“Zafi na ke ji bari in ɗan watsa ruwa…”

Bin shi ta yi da kallo saboda akwai AC a ɗakin ga fanka amma ya ce zafi ya ke ji. Sauke numfashi ta yi har ya shige bedroom ɗin ya bar ta nan falon a zaune.

Sallama ta ji. Da fara’a ta amsa. Maƙwafciyarsu ce Maimunatu. Ta ce ta shigo ta zauna sai dai a tsorace ta ke.

Saboda ta san yadda Nawaf ya tsani Maimunatu. Saboda wata rana daya kamata tana faɗa wa Nur ɗin cewar ya akai ta auri Nawaf.

Ai ta san ‘yan gidansu tun tuni. Mahaukaci ne ɗan shaye-shaye. Kaca-kaca ya yi mata ya koreta. Yanzun ma ba ta san wani tsautsayi ya shigo da ita ba.

Suna gama gaisawa sun zauna jim. Kawai Nawaf ya fito. Maimunatu ya kalla da ke zaune yana jin wannan duhun da ke rufe mishi kai ya bayyana.

Ƙarasowa ya yi ya ja hannun Nur ya yi bedroom da ita. Don ba zai manta warning ɗin da ya yi mata kan Maimunatu ba.

Wani irin mari ya ɗauke ta da shi.

“Jakar ina ce ke? Ban ce miki ba na son ƙara ganin waccan matar a gidana ba?”

Azabar marin da ta ke ji bai kai ta zuciyarta ba. Ga wani tsoro da ya rufe ta.

“Don girman Allah Nawaf ka yi haƙuri wallahi…”

Wani marin ya sake wanketa da shi da sai da ta ga wani haske ya gilma mata. Kunnenta ya ɗan daina jin iska sosai.

Wani mugun kallo ya watsa mata ya ce,

“Just twominute na baki ki fita ki sallameta ki dawo ina jiranki…”

Da gudu Nuri ta fice daga ɗakin. Tsayawa ta ɗan yi ta goge fuskarta sannan ta ƙarasa. A dake ta ce wa Maimunatu,

“Ki tafi don Allah. Ki tafi karki ja min matsala…”

Ba ta jira amsarta ba ta juya abinta. Inda ta bar Nawaf ta same shi a tsaye. Idanuwan nan sun sake launi.

Gefe ta kai kallonta. Wani gwangwani ne a ajiye sannan ta dawo da hankalinta kan Nawaf a tsorace ta ce,

“Nawaf me ka sha?”

Wani shaƙar iska ya yi.

“Ba na son yawan tambaya. Ki ƙyale ni! Kaina ciwo ya ke min!”

Ya faɗa a tsawace yana wani daddafe kanshi. Ja da baya Nuri ta yi don ta san ba cikin hankalinshi ya ke ba.

Allah kaɗai ya san abinda ya haɗa wa cikinshi. Ficewa ta yi daga ɗakin kafin ya illatata!

*****

Girgiza kai ya ke ya kasa ɗauke idanuwanshi daga kan Nana. Ta ya ya samu ‘ya? Ta ina? Neme-neme ya shiga yi cikin akwatunan da suke binne a kan shi. Possibilities ya ke nema na cewar Nana’ yarshi ce. Wata dariyar takaici Safiyya ta yi tana kallonshi. Tasan dole ya yi mamaki.

“Ka ɗauka za ka iya tsarawa kanka rayuwa ne? Saboda kai ka ke da iko da ita ko?”

Bai damu da yanayin muryarta ba. Da tambayar da ta ke masa da gayya. Ba ita ba ce a gabanshi. Yarinyar nan ita zuciyarshi ke ta ɗauka hotuna tana adanawa a wurare daban-daban.

A hankali yana sassarfa ya taka har inda Nana ke tsaye da manyan idanuwanta irin nashi tana kallonshi cike da wani irin abu a cikinsu.

Kamar ta na tsoron ƙarasawo inda ya ke kar ya ɓace. Zai iya karantar shekarun da ta yi ta na jiran irin wannan ranar cikin idanuwanta.

Kallonta ya ke yi. Bai san lokacin da ya tsugunna kan gwiwoyinshi ba. Hannunshi na rawa ya ɗaga shi ya taɓa kuncin Nana ya ji ko ta gaske ce.

Ya ji ba rayuwa ba ce ke son yin wasa da shi kamar yadda ta saba. Ba wani rubutun ƙaddarar ba ne da ya ke tunanin kan dutse ya ke sai daga ƙarshe gogewar shi ta zama tamkar akan ruwa.

Ba wani farantin cike da farin ciki ba ne ƙaddara ke son miƙo mishi sai ya kai hannuwa biyu ya karɓa ta fisge tare da mishi gwalo ba.

Ɗumi ya ji a hannunshi. Sosai ya ɗago ɗayan ya tallabi fuskar Nana. ‘Yan hannuwanta ta sa akan nashi ta na taɓawa.

Muryarshi a dushe can ƙasan maƙoshi ya ce mata,

“Em real…”

Saboda yadda ya ga ta na tsoron taɓa shi. ‘Yan yatsunshi ta kama cikin nata ta dumtse. Wata irin ajiyar zuciya ta saki. Kafin ta saki yatsun nashi ta kai hannunta kan fuskarshi ta tallaba kamar yadda nashi ya ke a fuskarta.

Ranƙwafawa ta yi ta haɗa goshinta da nashi tana kallonshi cikin idanuwa. Fu’ad zai iya rantsewa bai taɓa sanin wata nutsuwa kamar wannan ba.

Zai iya rantsewa an halicci zuciyarshi ne kawai don ta buga ta zo da shi wannan lokacin ya tsinci kanshi da ƙaunar wannan yarinyar.

Zai iya rantsewa babu farin cikin da ya kai na ka ɗora idanuwanka kan halittar da ta fita daga jikinka. Safiyya da ke tsaye gefe ta riƙe baki.

Wasu hawaye ne suka zubo mata. Abinda ta ke gudu kenan. Shi ne yake faruwa a gaban idanuwanta. Tana ganin yadda daga kallo ɗaya Fu’ad ya sace zuciyar Nana kamar yadda ya yi wa tata.

Tana tsoron abinda ya faru da ita ya faru da Nana. Domin iya wahalar duniya a shekarunta ta gansu. Bata son ta haɗa da ciwon zuciyar rashin ƙaunar Fu’ad.

Don ta fi kowa shaida yadda raɗaɗi da rashinta suke. Ta fi kowa sanin zafin abin. Ta kuma fi kowa sanin ba shi da zuciyar ƙaunar kowa banda kanshi.

Nana kuwa ta sha tunanin me ya sa za a ce ita ce za ta mutu bayan ga tsofaffi nan. Da duk wani hankali na ta ta yi tunani ta kasa gane kalar zaɓe na mutuwa.

Tsoronta ɗaya, kar ta ɗauke ta ba ta saka M a idonta ba ko da sau ɗaya ne. Ba ta san dalilinshi na barin rayuwar Mumynta ba. Ba kuma ta damu ba.

Abu ɗaya ne a zuciyarta a yanzun. Ƙaunar M wadda ta linka ta da da ganinshi. Sai ta ke jin duk abinda ta rasa ta samu yanzu.

Cikon ƙaunar da ba ta samu ba. Ba ta san lokacin da wata dariyar farin ciki ta ƙwace mata ba.

Fu’ad ji ya yi zuciyarshi ta buɗe tana maraba da jin sautin dariyar Nana. Bai san dalilin dariyarta ba amma ta saka shi farin ciki marar misaltuwa.

Shi ma bai san lokacin da dariya ta suɓuce masa ba. Sosai dariya suke su duka biyun kamar waɗanda suke cikin wani irin farin ciki. Girgiza kai Safiyya ta ke yi saboda ba ta san me Fu’ad ya ke nufi da wannan abin da ya ke yi ba. Za ta iya komai akan Nana ciki har da kareta daga Fu’ad in har zai zama barazana ga farin cikin yarinyar.

Duk da yadda zuciyarta ke mata wasi-wasi da kokwanto da yawa bai hana yanayin su Fu’ad saka zuciyarta wani matsewa ba.

Cikin kanta take faɗin,

“Don Allah karki min haka. Karki buɗe mumin ƙofar da na daɗe da rufewa.”

A hankali sautin dariyarsu ya ke ragewa. Suka ci gaba da kallon juna. Hannu Nana ta sa ta ƙara tallabar fuskarshi har lokacin goshinta na haɗe da nashi.

Muryarta ta saukar dai dai kunnenshi.

“Na ɗauka ba zan taɓa ganinka ba.”

Wata irin iska ya ji ta na fita daga zuciyarshi. Kafin wani irin ɗaci ya ziyarce ta. Janye goshin shi ya yi daga na Nana ya maida kallonshi kan Safiyya da ke tsaye ta zuba musu idanuwa.

Sannan ya sake kallon Nana. Lokaci ɗaya ya tuno ranar da rabon Nana ya gifta. Randa zai tafi da suka haɗa gado da Safiyya babu kariya.

Wani irin duhu-duhu ya ke ji na lulluɓe mishi zuciya da ɓacin rai. Shekaru goma sha ɗaya ta ɓoye mishi wannan abin.

Ya san ba ta san ganinshi. Ta tsane shi. Nana ya ke kallo sosai. Amma ta ɓoye mishi Nana abu ne da ba zai iya yafe mata ba.

Kula ya yi Nana na yamutsa fuska kamar wadda ta ke cikin wani mawuyacin yanayi. Kallon fuskarta ya ke yana manta damuwar komai banda abinda ke sa ta yamutsa fuska haka.

“Are you okay?”

Ya buƙata cikin taushin muryar da bai taɓa amfani da shi ga kowa ba sai ita.

Wani irin numfashi ta ke shaƙa da sauri-sauri kamfn jini ya fara biyo hancinta idanuwanta suka fara wani kakkafewa.

Ji ya yi zuciyarshi na shirin tsayawa. riƙeta ya yi dam a rikice ya kalli Safiyya da ta ƙaraso inda suke tsaye da gudu tana karɓar Nana daga hannunshi wacce har ta suma tun kafiin ƙarasowar Safiyya. Girgizata Safiyya ta ke tana kiran,

“Nana…”

Hannunta Fu’ad ya riƙo yana kallon Safiyya a rikice yana jin zuciyarshi na wani irin dokawa.

“Me ya same ta?”

Shiru ta yi ta ƙyale shi tana dube-dube. A tsawace ya ce,

“Damn it Sofi magana na ke miki. What the fuck is wrong with my daughter?”

Kallonshi ta ke tana jin yadda ya ke ƙure manejin haƙurinta. Akan Nana zai ce zai mata ihu? Ashe ma me yake damun ‘yarshi.

A kufule tana ƙara jan Nana jikinta ta ce,

“Da gaske kake? Ka ji me kake faɗi kuwa? ‘Yarka fa ka ce Fu’ad? Anya ba ka sha wani abu ba?”

Dai dai shigowar Ansar. Ganinsu tsugunne ya sa shi ƙarasowa da sauri. Ba su kula da shi ba suna watsama juna wani irin kallo da ke nuna mintina kaɗan suka rage su far wa juna.

Bai ko bi takansu ba ya janye Nana daga jikin Safiyya yana saɓa ta akan kafaɗarta.

“Me kika tsaya yi haka Safiyya. For goodness’s sake kin manta warning ɗin Dr. Jana ne. Mtswwww…”

Da gudu Ansar ya fice da Nana. Safiyya ta ɗauki mayafinta za ta bi bayanshi ta ji an riƙo mata riga an fizgota.

Kallon shi ta yi a fusace.

“Ba na son neman rigima. Ka bar ni ‘yata tana buƙata na….”

Miƙewa tsaye ya yi hannuwanshi kan ƙugu ya na kallon Safiyya cikin fuska. Har wani huci ya ke saboda ɓacin rai.

“Shekaru goma sha ɗaya. Komin tsanar da ki ka yi min ba za ki iya faɗa min ina da yarinya ba?”

Ba ta da lokacin yin wannan rigimar. Ta na juyawa ya sake shan gabanta.

“Me ke damunta da wancan mai ƙaton kan ya sani ni ban sani ba?”

Haɗe hannyenta ta yi waje ɗaya muryarta na rawa. Idanuwanta cike da hawaye ta ce,

“Please and please ba yanzun ba…”

Da gudu ta fice daga ɗakin ya bi bayanta. Ansar ya riga ya yi tafiyarshi. Buɗe motarta ta yi ta shiga. Fu’ad ya buɗe gefe ya shiga.

Ba ta da lokacin tsayawa masifar shi don ta san ita ya ke ji. Dukan sitiyarin motar tayi ta buɗe ta fice da gudu ta koma cikin gida ta ɗauko mukullin motar.

Ta dawo ta tasheta ta ja ta fita daga gidan. Can ƙasan maƙoshi ba tare da ya kalleta ba ya ce,

“A karo na uku zan sake tambayarki me ke damun yarinyata? And ba na son yadda wancan ya ɗauketa kamar yana da iko a kanta.”

Hankalinta na kan titi ta ce,

“Mintinanka nawa da bayyana cikin rayuwarmu da har ka ke tunanin ka na da wani muhimmanci a ciki? Ko ka ga alamar na damu da abinda ya yi maka da wanda bai maka ba?”

A fusace ya kalleta. Gaba ɗaya ta canza.

“Sofi kar ki ce za ki min rashin kunya. Ban ce mun gama maganar nan ba…”

Shiru ta yi ta ƙyale shi. Ba ta yi parking a ko’ina ba sai a bakin asibitin. Ba ta jira Fu’ad ba ta fice abinta. Bin ta ya yi shi ma.

Ansar suka samu a waiting area yana tsaye yana ta kai kawo. Ya ce ma Sofi,

“Dr. Jana ta tafi gida. But Dr. James ke dubata. Ba su ce min komai ba tukunna.”

Kallon su Fu’ad ya ke. Yadda Ansar ke yi za ka rantse shi ne baban Nana. Wani irin karyewa ya ji zuciyarshi na yi. Shi ya kamata ace yana abinda ya ke yi ba wannan mai ƙaton kan ba.

Duk laifin Safiyya ne. Ya ɗauka ƙara tabbatar da ta tsane shi zai masa ciwo sosai. Sai ya ji bai ji ciwon shi kamar yadda ya ke jin ciwon maye gurbinshi da wannan yayi ba.

Safiyya ta cuce shi da ta ɓoye mishi Nana. A hankali ya taka inda suke tsaye suna magana ita da Ansar. Tsakiyarsu ya shiga ya fuskanci Ansar.

“Excuse me. In ba za ta iya faɗa maka ba ni zan faɗa maka. Mun gode sosai da karamcinka da kawo Nana asibiti.

Family time ne yanzu. Ko zaka ɗan ba mu waje?”

Kallon shi Ansar ya ke. Daga yadda ya ji labarinshi bai yi mamakin maganganunshi ba. Ba don shi ya ke tsaye a nan ba. Ba kuma don Safiyya ba.

Ƙaunar da ya ke ma Nana Allah ne kaɗai ya sani domin shi ya halitta mishi ita. Murmushi ya yi wa Fu’ad ya ɗan dafa kafaɗarshi sannan ya kalli Safiyya ya ce,

“Bari in siyo wannan allurar in dawo….”

Kasa ce mishi komai ta yi har ya wuce. Wani kallo ta watsa wa Fu’ad tare da faɗin,

“Faɗanka da ni ne babu ruwan Ansar a ciki.”

Taɓe baki ya yi. Dr. James ta hango, da sauri ta ƙarasa wajenshi. Fu’ad na binta. Kallon Safiyya ya yi ya ce,

“Na ba dad ɗinta ya kawo wata allura. She is stable yanzun. Za mu riƙeta anan gaskiya.”

Da sauri Fu’ad ya ce,

“He is noh’ her dad. I am…”

Da mamaki Dr. James ke kallon Fu’ad. Kafin ya ce wani abu Safiyya ta harare shi ta ce wa likitan,

“Karka damu da shi. Zan iya shiga in ganta?”

Kai ya ɗaga mata ya ce,

“Eh amman banda hayaniya.”

“Na gode sosai…”

wucewa ya yi yana faɗin,

“Call me in an kawo allurar.”

Ɗakin da aka saba ajiye Nana Safiyya ta nufa. Juyowa ta yi ta ga Fu’ad na biye da ita. Tsayawa ta yi ta lumshe idanuwanta ta ware su akanshi.

“Ba ta buƙatar kowa a kusa da ita sai family ɗinta…”

Hannu Fu’ad ya ɗaga mata don in ta ci gaba da magana zai iya kwaɗa mata mari. Zagin da ta ke masa ya ishe shi haka.

“Wallahi a shirye na ke da in birkita asibitin nan da duk wanda ya ke son gaya min bazan iya ganin ‘yata ba.

Kamar yadda na ke a shirye mu hau sama mu faɗo ni da ke akan ɓoye min ita da kika yi…

Ki wuce mu je kafin in yi abinda za mu yi da na sani Sofi.”

Wani miyau ta haɗiye. Ta san zai iya yin fiye da abinda ya faɗa. A hankali ta tura ɗakin. Nana na kwance kan gado jikinta jone da Na’urori.

Da alamun bacci ta ke yi. Yanzun da idanuwanta suke a rufe ramar da ta yi ta sake fitowa sosai.

Tsaye Fu’ad ya yi a bakin ƙofar yana kallonta. Kamar ba ita ba ce ta gama dariya mintinan da suka wuce. Wani irin abu zuciyarshi ta ke mishi.

Ba ya sonta akan gadon nan. Ba ya son ganinta ko kaɗan. Ya fi son ganinta kamar yadda ya ganta ɗazun. Kamar mai ciwon ƙafafu haka ya ke takawa har ya ƙarasa bakin gadonta.

Zuciyarshi na rawa sosai. Tsugunnawa ya yi. Ya kama ɗan yatsanta guda ɗaya a hankali saboda ƙarin ruwan da ke jikin hannun.

Idanuwanshi ɗauke da wani yanayi mai nauyi ya kalli Safiyya. Abinda ta gani a fuskarshi ba ta taɓa ganin kalarshi ba a iya lokacin da ta san shi.

“Please Sofi….”

Lumshe idanuwanta ta yi ta na ƙoƙarin mayar da kukan da ke shirin ƙwace mata. Tun ɗazun ta ke daure yadda ganinshi ya karya mata zuciya.

“Leukemia take da shi…”

Girgiza kai Fu’ad ya ke yana so ta ce masa ba ta gaya mishi ‘yarshi na ɗauke da cancer ba. Ba ta gaya mishi ya makara ba.

“Akwai chemo Sofi…”

Hawayen da ta ke tarbewa ne suka zubo. Ta sa hannu ta goge su kafin cikin raunin murya ta ce,

“Sau uku ana mata chemo-therapy. Ta roƙeni saboda ba za ta iya ɗaukar wani ba…”

Ta ƙarasa maganar wasu hawayen na sake zubo mata. Miƙewa ya yi ya fice daga ɗakin bai damu da ya rufe ƙofar ba.

Tafiya kawai ya ke batare daya san inda yake saka ƙafarshi ba. Ba ya ganin komai a gabanshi sai ciwon da ke shirin raba shi da yarinyar da ko cikakkiyar awa ɗaya bai yi ba da saninta.
Mutanen da ke wucewa sai dai su su kauce masa don ba ya ganinsu. Ansar ne ya ganshi. Kafaɗarshi ya dafa yana faɗin,

“Lafiya…?”

Bai ko kalle shi ba ya cire hannunshi daga kafaɗarshi ya wuce. Ba ya buƙatar kowa. Ba ya buƙatar kowa sai Momma. Ba ya son gaya wa kowa damuwarshi sai Lukman.

Ba ya son kowa ya gaya mishi ya yi kuskure sai Haneef. Ba ya son kowa ya lallashe shi sai Momma!

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

1 thought on “Akan So | Babi Na Talatin”

  1. Avatar

    Book dinnan ya tabamin raida zuciya, na karanta shi a Wattpad Amman yanxun ma innajin shisabo a duniyar ta😢😰

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×