“A miƙo min towel ɗina.”
Fu’ad ya faɗi yana daga cikin toilet ɗin.
“Wa ya hanaka shiga da shi?”
Lukman ya faɗi. Haneef kam taɓe baki kawai ya yi.
“Wallahi zan fito haka.”
Da sauri Lukman ya ɗauki towel ɗin ya ƙwanƙwasa banɗakin. Ya miƙa masa. Yana yin dariyar da yake. Yasan halin Fu’ad, babu kunya a idanunshi tsaf zai fito in ba su miƙa mishi towel ɗin ba.
Yana fitowa Lukman ya shiga. Jakar shi ya ɗauka. Banda comb da man gashi bai ɗauko komai ba. Sai kayan sawa da takalma.
“Ba ni manka in ɗan shafa ma hannuwana.”
Vaseline Haneef ya miƙa mishi. Don shi ma bai ɗauko mai ba yace:
“Ga dai na masu ɗakin”
Ai da sauri ya janye jikinshi kamar ya miƙo masa miciji. Ajiye robar Haneef ya yi yacie gaba da latsa wayar shi. Kaya ya ɗauka ya sake ya gyara gashin shi da yake ta ɗaukar ido. Kallon shi Haneef ya yi ya ga crazy jeans ɗin da ke jikin shi. Ya ga duk a gwiwar zuwa ƙwauri, har jikin cinya yaga ne. Sai riga fara data bala’in kama shi, shi da ma ba wani jikin kirki ba.
Ya san in ya masa magana ma fitsara zai sha ranshi ya ɓaci a banza don haka ya yi masa fatan shiriya kawai a ranshi.
Dai dai sallamar Khalid. Haneef ya amsa da fara’a a fuskarshi.
“Ina kwanan ku.”
Khalid ya faɗi yana ajiye kwanan shan da ya shigo da shi a hannu.
“Khalid ka tashi lafiya? Ya hidima kuma?”
Haneef ke tambaya yana miƙewa daga kwanciyar da ya yi. Khalid ya amsa shi da:
“Alhamdulillah.”
Ya juya tare da ficewa da sauri. Ya sake dawowa da leda a hannunshi. Ƙamshin ƙosai ya cika ɗakin.
Fu’ad da ke tsaye ya wani yamutsa fuska. Don ƙamshin koma menene aka shigo da shi yana shirin saka shi amai.
“Ga abin kari.”
Haneef ya yi masa godiya ya sauko ya buɗe ledar ƙosan. Ga su manya-manya ya ɗauki ɗaya ya gutsura. Rabon shi da ƙosai tun wani azumi da Atika ta yi musu shi. Haɗa idanuwa suka yi da Fu’ad da ke masa kallon ‘Me kake yi haka?’
Share shi ya yi ya ci gaba da cin ƙosan shi suna ɗan hira da khalid ɗin da ke kallon Fu’ad lokaci-lokaci.
Kayan da ya cire ya ɗaga a ƙyamace yace:
“Ina za a yar da wannan?”
Idanuwa khalid ya zaro yana kallon kayan da Fu’ad ke kira da a zubda.
“Me ya same su?”
Ya tambaya, sanin Fu’ad ba zai kula khalid ba balle har ya amsa mishi tambayar da ya yi ya sa Haneef saurin cewa.
“Ya ɗan fita ne wata ta watso ruwa ya same shi.”
“Ayya, bari sai na wanke masa su.”
Cewar khalid. Rolling idanuwanshi Fu’ad ya yi. Ko ance ma wannan ɗan ƙauyen zai iya saka kayan da aka tsoma a bokiti ya sa ƙazamun hannun shi ya wanke.
“Germs.”
Ya faɗi ƙasa-ƙasa. Don bai shirya dogon surutun Haneef ba. Zai yi magana Lukman ya fito daga wanka.
“Naji ƙamshin ƙosai.”
Ya faɗi yana dariya. Wani mugun kallo Fu’ad ya yi masa da ko kula da shi bai yi ba ya zauna a gefen Haneef suka ci tare.
“Ka kawo kayan sai in wanke maka.”
Kallon Khalid Lukman ya yi. Mutanen karkara akwai karamci da sanin darajar mutane.
A shekaru zai girmi Fu’ad amma yana offering ya wanke masa kaya. Ba ruwansu da girman kai.
Da Haneef da Lukman suka zuba masa ido yadda yake tsaye yana yamutsa fuska. Ya san kallon da suke masa. Kamar wanda aka shaƙe.
Can ƙasa-ƙasa yace:
“Babu abinda zan yi da kayan ne. A zubar kawai. “
Tashi khalid ya yi ya karɓa yana fadin:
“Kai ni kam ina so.”
Ya dawo ya zauna. Wani kallo Fu’ad yake mishi. Ya rasa me ke damun talakawan nan. Har ka iya kasa kayan da wani ya yi using.
Girgiza kai kawai ya yi. Ya ɗauko jakar shi. Ya duba. Kuɗin da ya ɗbo ba su shige dubu goma ba don in ba amfani zai da kuɗi ba, ba yawo yake yi da su ba.
“Wa yake da cash a jikinshi? Like 20k or more.”
Ya tambaya yana kallonsu. Lukman ya miƙe ya ɗauko wallet ɗin shi. Dubu takwas ne. Ya girgiza ma Fu’ad kai.
“Haneef?”
Ya kira da alamar tambaya a muryarshi.
“Aikin me nake yi da zan yi yawo da 20k?”
Haneef ya bashi amsa tare komawa kan katifa. Girgiza kai Fu’ad ya yi, ya tuna Haneef bai fara aiki ba. Kuma ba ya karɓar kuɗi a hannunshi sam. Ko ya tura masa maida mai yake yi. Gara ma mota itama sai da ya nuna masa mugun ɓacin rai tukunna ya karɓa.
“ko 5k tam kafin mu shiga gari. Lukman ban na hannunka.”
Miƙa mishi suka yi Haneef ya ba shi 5k ɗin. Ya ƙirga dubu ashirin. Khalid dai kanshi ƙasa yana sauraransu.
Lukman ya miƙa wa yace:
“Give him, I don’t want him wearing the ones I’ve used.”
Dariya Lukman ya yi ya karɓi kuɗin yace wa khalid:
“Ga shi Fu’ad ya baka ka siya kaya.”
Ya karɓi kuɗin da mamaki a fuskarshi. Allah kenan rabonka ba ya wuceka.
Godiya ya fara wa Fu’ad da ko kallon shi bai yi ba ya ƙarasa ɗaura takalman shi ya ɗauki key ɗin mota ya fice.
Da Khalid bai ji ya yi hausa ba zai iya rantsewa yadda Fu’ad ya basar da shi bai gane me yake cewa bane.
A sanyaye yace ma Haneef.
“Ina ta godiya ko bai ji ba ne?”
Wata kunya ta rufe Haneef ya ce masa:
“Ka yi haƙuri. Bai cika son godiya ba shi ya sa ka ga ya yi shiru.”
Jinjina kai Khalid ya yi kawai bai ce komai ba.
*****
Cake ɗin shi ya zauna a mota ya ci ya sha fresh milk da sun wani ɗauki ɗumi. AC ya kunna. Ya zame kujerar ya kwanta. Kanshi wani ciwo yake ya kuma san baccin da bai samu bane. Dama ya sani cikin mota ya kwana. Ya fiye mishi alkhairi da sauro da zafin shagon nan. Wata kewar ɗakin shi na gida ya ji. Ajiyar zuciya ya yi. Ya sake gyara kwanciyarshi kan kujerar motar ya lumshe idanuwanshi.
Bacci mai ƙarfi ya ɗauke shi da wani nauyi a zuciyarshi da ya kasa fahimta.
*****
Safiyya ce tsaye da kayan jikinta na ɗazun. Wata koƙaƙƙiyar atamfa. Fuskarta duk ɗige-ɗigen kwalli na alamar kwalliyar ƙauyen da ke fuskar ta. Ba ta cika haske ba sosai. Ba ta da tsawo. Banda idanuwanta da suke manya tubarkalla babu wani kyau a fuskar ta. Hancinta kamar daga baya aka ɗan ɗora mata shi. Ba zaka kirata mummuna kai tsaye ba. Saboda jikinta na da kyau sosai. Tana da ƙira da dirin da mata da yawa za su yi hassada da.
“Fu’ad………..”
Ta kira shi. Mamaki yake don bai san ya akai ta san sunan shi ba. Bai ma san me yake tsaye a wajen yana kallonta ba. Yamutsa fuska ya yi saboda yanayin yadda ta kirashin ba ya so. Ba ya son yadda zuciyarshi ta wani matse. Haɗe fuska ya yi. Ba ya son wata alaƙa tsakaninsu. Shi ba mata yake kulawa ba. Mazan ma ba kula su yake ba. Ball ce masoyiyarshi. Ita ya runguma. Amanarshi na tare da ita. Ba kuma ya tunanin zai iya haɗa sonta da na mace shi ya sa ba sa gaban shi.
Beside a shekaru ashirin da biyu wane shiririta zai kai shi soyayya. Don haka ya zo wucewa ta gabanta.
Ta riƙo mishi riga.
“Nima wulaƙancin za ka yi min?”
Ta buƙata.
A fusace ya juya ya sauke idanuwanshi cikin nata. Lokaci ɗaya ƙanƙarar da ke cikin idanuwanta suka soma kashe duk wata wuta da ke cikin nashi.
Dukkanin ginin da ke kare zuciyarshi suka soma girgiza. Foundation ɗin su na barazanar rugujewa.
*****
A firgice ya buɗe ido yana jan wani irin numfashi. AC ɗin motar bai hanashi zufa ba. Zaune ya tashi dirshan. Ya dafe kanshi cikin hannuwanshi. Yana maida numfashi da sauri-sauri. Glass ɗin motar ya sauke. Ɗan iskar da ke ciki ta masa kaɗan. Ruwa ya ɗauko ya buɗe motar. Ya kurkure bakinshi ya wanke fuskarshi sannan ya sha. Ya koma cikin motar ya haɗa kanshi da sitiyari yana jin yadda numfashin shi ya samu dai-dai ta. Wannan wane irin mafarki ne. Safiyyar da maganganunta ne kawai mafarki. Amman yanayin da yake ji a cikin mafarkin shi yake ji a yanzun. Rawar da zuciyarshi take yi sai ma abin da ya yi gaba. Wane irin bala’i ne wannan? Yake tambayar kanshi.
Bai ga haɗin sa da ‘yar ƙauye kucaka ba.’Yar gidan talakawa da za ta kutso masa kai cikin mafarki.
Wani tsaki ya ja. Yana miƙewa ya ji muryar Lukman kamar daga sama.
“Ɗan banza ashe kana nan. Anata kiran wayarka ka ƙi ka ɗauka.”
Wayarshi a silent take. Shiru ya yi wa Lukman ɗin har ya zagaya ya buɗe motar ya shigo. Bai ma kula tare suke da Haneef ba sai da ya ji an buɗe gidan baya an shiga.
“Lukman karɓi tuƙin nan please.”
Bayajin ‘yan gardamar don haka ya buɗe motar ya fita. Lukman ya koma inda ya tashi. Baya ya buɗe ya shiga. Haneef yace:
“Me ye haka ɗin?”
A kasalance yace.
“Em noh’ in the mood.”
Fita Haneef ya yi ya koma gaba. Fu’ad ya yi luf da shi a cikin kujera. Yana jin Lukman na maimaita yanayin turancin shi.
Ya rasa me yasa in dai zai yi turanci sai Lukman ya maimaita yana mai dariya wai ya zama masu jar fuskar nan. Yanayin da yake ji bana rigima bane. Suka ɗauki hanya. Wayar shi Lukman ya jona ya sa kiɗa yana dannawa waƙoƙin suna wucewa.
Wata waƙa ta shigo ta justin Bieber (Purpose) har ya danna ya canza dan ya san yadda Fu’ad ya tsani slow waƙoƙi. Wai sai kace marasa rai. Da hanzari Fu’ad yace masa:
“Bar ta please. Mayar mana.”
Mayarwa ya yi yana kallonshi ta cikin mudubi. Ya fahimci bai son surutun yau. Yakuma san akwai abinda yake damun shi.
Yasan da kanshi zai faɗa mishi don haka ya bar waƙar kawai. Fu’ad kam waƙar na shigar shi ya kuma rasa dalili. Ba son slow music yake yi ba. Sai dai kawai ya ji waƙar ta yi dai dai da yanayin da bai san ta inda ya fito ba.
Wani mai machine ne ya shigo musu kamar daga sama. Ba don a hankali Lukman ke tuƙin ba da munin abin zai fi yadda ya faru.
Parking ya yi suka fito su duka. Fu’ad ya riƙe baki yana kallon gefen gaban motar shi ya tashi aiki. Benz ɗin shi da yana da wanda suka fi ta kuɗi amma yake mugun ji da. Fuskar shi horrified yake faɗin:
“Oh no…..oh my God”
Yana girgiza kai. Bai ma kula dasu Haneef da ke magana da yaron ba. Juyawa ya yi rai a ɓace ya ture Lukman ya cakumi wuyan yaron.
Mutane harsun fara haɗuwa. Tsayi kawai Fu’ad zai nuna mishi. Amman ya fishi girma wani wawan mari ya kwaɗa wa saurayin yana ƙara mishi wani.
Haneef da Lukman suka riƙe shi suna faɗin.
“Fu’ad control yourself please ya bada haƙuri fa. Machine ɗin shi ne ba brake.”
Cikin hargowa Fu’ad ya ture su yana fadin:
“Ciyawa ce a kanshi? Da akace ya hau machine ba brake? Kana tunanin ko gidaje da gonakin danginsu za a siyar za su biya kuɗin motata ne?”
Cike da takaici yaron yace:
“Allah ya baka haƙuri.”
Kallon shi Fu’ad ya yi yanajin kamar ya rufe shi da duka yace:
“Aikin talaka kenan. Ba da haƙuri. Tunda ka gama min ɓarna dole ka bani haƙuri. Daƙiƙin banza.”
Har ya juya yana sake kallon motar shi. Matashin saurayin yace:
“Arziƙi dai ba hauka bane ba. Allah da ya baka muma talakawan zai iya bamu.”
Tunda ya bude bakinshi Haneef da Lukman suka karanci kuskuren hakan. A hankali Fu’ad ya juya muryarshi can ƙasa kamar mai magana da kanshi yace:
“Me kace?”
Haneef ne ya dafa kafaɗarshi yace:
“Forget it Fu’ad muje please.”
Ture hannun Haneef ya yi ya ƙarasa daf da saurayin. Muryarshi very controlled da abinda yake ji yace:
“No, ya maimaita abinda yace.”
Shiru saurayin ya yi. Cikin jama’ar wajen Fu’ad yace ma:
“Akwai Police Station a kusa?”
Haƙuri suka shiga ba shi yace wallahi sai ya maimaita maganar da ya faɗa. Sai ya sa an kulle shi.
Bai gama balbalin ba. Ashe tun farkon rikicin wani yaga abin zai wuce gona da iri ya yi saurin ƙarasawa Police Station ɗin da ke nan kusa-kusa ya kai report.
Nan suka rankaya zuwa Police Station ɗin. Haneef da Lukman na ƙoƙarin shawo kan Fu’ad ɗin da ko saurararsu ya ƙi yi.
Filing report ya yi yace yana son a biyashi ɓarnar da akai masa a jikin mota. Don ya san basu da kuɗin biyan shin. Wulaƙanta yaron yake so ayi. Saboda babu wanda ya isa ya gaya masa magana ko ya fishi kuɗi ba su yi shari’a ba ballantana wannan ƙazamin talaka. Dukan shi ‘yan sanda suka shiga yi za ka rantse da Allah kayan wani ya sata. Wani abu sai ƙasata Nigeria.
Gefe Haneef ya ja Fu’ad.
“Wai me ke damunka ne? Wallahi kasa su ƙyale shi ko na kira Abbah na faɗa mishi.”
Lukman na gefe don ya gaji. Fu’ad ba saurarsu zai yi ba. Wani dattijo ne ya shigo Police Station ɗin a rikice. ‘Yan sandan suka kira Fu’ad ya ƙarasa inda suke. Kallon dattijon ya ke yi, akwai inda ya taɓa ganin shi.
Lokaci ɗaya abin ya yi clicking masa. Shi ne tsohon da Anty Fatima ta mare shi saboda. Wannan ƙazamin tsohon.
Shima kallon Fu’ad ɗin yake yi. Ya gane shi sarai. Ya rausayar da kai gefe kawai. Nan ‘Yansanda suke ƙara wa zancen Fu’ad gishiri.
Ya buɗe baki zai yi magana Haneef yace:
“Fu’ad na taɓa roƙon alfarma a wajenka?”
Ya yi shiru kawai. Haneef ya ci gaba;
“Fine ban taɓa roƙon wani abu a wajenka ba. In dai har ina da wata daraja a wajenka. In jini ɗaya ne yake a jikinmu za kai dropping case ɗin nan yanzun.”
Shiru ya yi kamar bai ji abinda Haneef ɗin ya ce ba. Harma ya ɗauko waya zai kira Abba ya ji fu’ad ya ce:
“Fine. Ina son babanshi ya bani haƙuri.”
Ya faɗi yana kafe idanuwanshi akan dattijon. Haneef ya yi masa kallon kana cikin hankalinka kuwa.
“Allah ya baka haƙuri ya huci zuciyarka da kuskuren da yarona ya yi maka.”
Cewar dattijon muryarshi na rawa. Haneef fita ya yi daga Police Station ɗin Lukman na rufa mishi baya. Saboda kunya yake ji. Ya ji ya muzanta da abinda Fu’ad ya yi. Shikam wani murmushi ya ƙwace masa. Sauran kuɗin aljihun shi ya zaro ya ba ‘Yansandan sannan ya fita wajen su Haneef. Su duka babu wanda ya ce masa uffan har suka tsallaka wajen motarsu suka shiga Lukman ya tuƙa su zuwa gida.
I want to start reading