Skip to content
Part 2 of 2 in the Series Al-Mustapha by Asmau Abubakar Musa

Da wannan tunanin ya kammala alwalar ya shige ɗaki ya tada kabbarar sallah, sallar ma ba da cikakkiyar nutsuwa ya gabatar da ita ba. Yana nan zaune a inda ya idar da sallar Larai ta farka daga bacci tana miƙa daga zaunen da ta yi a kan gadon, ba hamdala ba salati bare kuma gaida miji, ta fara kwala kiran Al’mustapha.

Malam Jibrin ya kalle ta ya girgiza kai tare da faɗin, “Ya tafi makaranta.”

Cike da hargagi kuwa ta fara masifa, “Kai wane irin mutum ne? Ya za ka bar shi ya tafi bayan ka san bai gama ayyukan da zai yi ba.”

“Ya gama komai kafin ya tafi.”

“Komai fa kace? Kashin da Nafisa ta yi kuma wa zai wanke iyee.”

Miƙewa ya yi daga inda ya ke zaune ya nufi ƙofar fita daga ɗakin yana faɗin, “Larai idan ba za ki iya wankewa ba ki bar ta a wurin har sai ya dawo.”

Zaro ido ta yi cikin firgici da jin furucin da ya fito daga bakinsa, ba za ta iya tuna ranar ƙarshe da mijin nata ya kira sunanta haka ba, yau ita ce ke yi masa magana yana fice mata a ɗaki, lallai al’amura su na son lalace mata, dole ta farka daga bacci me nauyin da ta kwanta har abubuwa suka zama haka.

Tana nan a zaune tana tufka da warwara ya sake shigowa ɗakin yana tsane ruwan jikinsa da ya yi wanka. Ko uffan bai ce mata ba, ya yi shirinsa na fita ya gama. Ɗari biyar ya ajiye a gefen ta ya ce, “Ga kuɗin cefane ni zan tafi wurin nema.”

Daga haka ya fice ba tare da ya jira abin da za ta ce ba. 

Hannu Larai ta ɗaura a ka bayan fitar shi baki buɗe tamkar wacce mummunan labari ya iske, hannunta na dama ta sauke ta ɗaga kuɗin da ya ajiye tana jujjuyawa, da gaske dai ɗari biyar ce yau ya ajiye mata a matsayin kuɗin cefane. Duk da ba wani abu za ta siya da kuɗin ba sai ɗan abin da ba a rasa ba, don akwai komai na dafawa a gidan har ma da ƙananun abubuwan buƙata na girki irin su magi, manja, gishiri, mangyaɗa da sauransu.

Don Malam Jibrin na da rufin asiri sosai bayan harkar noma, kiwo da kasuwancin da yake yi, yana da matsayin Principal a makarantar sakandire ta Gwamnati da ke cikin garin Dukku, a jihar Gombe. 

Kasancewar shi cikin waɗanda suka jajirce wajen neman ilimi a waccan zamanin, a ƙasar waje ya yi digirinsa wanda gwamnati ce ta ɗauki nauyin tura su a waccan lokacin.

Ganin zaman ba shi da wani amfani a gare ta ya sa ta miƙe tana gyara ɗaurin zanin ƙirjinta ta fito tsakar gidan, buta ta ɗauka ta kuskure baki sannan ta ɗauraye fuska, babu batun alwala bare sallah. Daidai lokacin aka bude ƙofar ɗakin yaranta, babban ɗanta Abdulsamad ne ya fito wanda suke sa’a da Al-mustapha, babu batun gaisuwa ya fara tambayar, “Mama an hada abin kari kuwa?.”

Harara ta aika masa sannan ta ce, “Ɗan kutumar uba! Daga tashi ne za ka fara tambayar abin kari, shegen yaro da baisan komai ba sai ci. Ka wuce ka taso Ridwan da Ahmad ku zo ku wanke baki da jiki ku yi shirin tafiya makaranta. Ni fita ma zan yi ga ruwan zafi a fulas ku haɗa shayi, akwai biredin da Babanku ya dawo da shi jiya da dare sai ku haɗa.”

Baki ya turo yace, “Haba Mama, shayi da biredi kawai za mu ci? yaushe zai ƙosar da mu. Ga komai amma ba za a dafa mana ba, ni dai ki soya mana kwai mu haɗa da shi.”

“Don ubanka ba zan soya ba, idan kwan kake son ci me ya sa ba za ka je ka soya da kanka ba iyee?.”

Kukan da ta jiyo daga ɗaki ne ya sa ta tsagaitawa da masifar ta nufi cikin ɗakin, ba jimawa ta sake fitowa riƙe da yarinyarta da ba za ta kai shekara biyu ba tana sake bambami.

“Ƴar banzar yarinya kawai, sai kace mai sakakken ɗuwawu, ba dama ki kwanta sai kin yi wa mutum kashi. Mantawa ma nayi da ubanki zai fita ban bada sallahun siyo miki famfas ba don wanna ya ƙare.”

Bakin famfo ta isa da ita, cire mata wandon kashin tayi sannan ta ɗauraye mata jiki suka bar wajen, ba batun wanke wurin bare kuma wandon kashin.

A lokacin yaran sun fito duk sun nufi ƙofar kitchen sun tsaya, tsaki ta yi sannan ta shiga kitchen ɗin, fulas ɗin ruwan zafi ta ɗauko sannan ta tsiyaya a wata madaidaiciyar roba. Ta ɗauko robobin madara, suga da milo ta ɗebi kowanne ta zuba, cikin hanzari take komai har ta gama hada shayin.

Daga can gefe ta isa ga wata robar plastic da ke cike da ƙwayayen kaji da na zabbin da Malam ke kiwo a bayan gidan. Guda goma ta ciro ta fasa su a wata robar daban sannan ta zuba magi da gishiri ta kada, harara ta banka wa yaran da suka tsugunna suna jiran ta gama tayi tace, “Mayunwata ne ku da ba za ku wuce ku fara shirin makaranta kafin na gama ba? Shi ma Al-Mustapha zai dawo ya same ni, yau sai nayi masa dukan ajali.”

Sum-sum suka miƙe don yin abin da ta ce, sun san halinta sarai, duk da soyayyar da take nuna musu ba ƙyale su take yi ba idan sun tunzurata.

Cikin mintuna ƙalilan ta kammala, rabawa tayi ta ajiye wa kowa a plate sannan ta ɗauki sauranbbayan ta tsiyayi Tea, ta koma ɗakinta. Zaman dirshan ta yi a ƙasa bayan ta sauke yarinyar dake bayanta, ledar biredi ta janyo ta gutsiri babba kafin ta ƙwala wa Abdulsamad kira.

Cikin shirin shi na makaranta ya shigo ɗakin, kayansa a wanke sun sha guga, wannan kuwa ba aikin kowa bane face Al-Mustapha don kullum idan ya dawo sai ya wanke kayan makarantar ƙannensa ya goge, ko da babu wutar lantarki yana amfani da dutsen guga.

“Ɗauki biredin ka je ku ci, ku yi sauri ku gama ka ja hannunsu ku tafi, kun yi latti sosai.” Ta faɗa tana saka ƙwan da ta gutsiro a baki.

Har ya kusa fita daga ɗakin ta dawo da shi, ɗari biyu ta miƙa masa tace, “Gashi ku siya abinci idan an fita tara.”

Da to kawai ya amsa ya fice a ɗakin.

Ɗakinsu ya koma ya tarar yaran har sun sun ɗauko musu shayi da soyayyen kwan, zama ya yi ya ajiye biredin kowa ya fara ci. Ba su jima ba duk suka mike bayan sun bar sauran abin karin a wurin. Jaka kowa ya ɗauka suka fice a gidan.

Sai da ta gama karyawa sannan ta ɗauki zani ta goya Ƴarta, kulle gidan tayi da kwaɗo sannan ta nufi gidan aminiyarta Hansai.

Shi kuwa Al-mustapha yau yana cikin farin ciki da kyautar da mahaifinsa ya yi masa, cikin ɗoki yake tafiya don ya isa makaranta ya labartawa Umma abinda ya faru, don ita ma tana koyarwa a makarantar Gwamnatin da yake zuwa. Wannan dalilin ya sa sam ba ya zama da yunwa idan ba ranakun mako ba, don kullum sai ta dafo abinci ta taho da shi, da safe kafin ya shiga aji zai ci sannan bayan an tashi ma zai ci, watarana kuma idan akwai saura ta ƙulla masa a leda ya tafi da shi gida, idan dare ya yi sai ya ci. Idan babu kuma saura kuma tana siya masa garin rogo da suga ko kuma su je gida ta debar masa Nono a gora ko a leda, ko wani abu na ci da take da shi, a jaka yake ɓoyewa gudun kada Inna Larai ta gani ta haramta masa ci.

Daidai wurin wata mai sayar da fanke ya tsaya ganin yara ƴan makaranta sun taru kowa na son siya. Tsayawa ya yi a gefe yana jiran layi ya zo kan shi ya siya.

Koda mak fanken ta ɗago ta gan shi murmushi ta yi kana tace, “Yaro mai babban suna Al-mustapha, har an shiryo za a tafi makarantar ne?.”

“Eh.” ya faɗa a taƙaice sannan ya gaishe ta.

Cikin fara’a ta amsa mishi sannan ta ɗebo fanke guda biyar ta saka a leda ta mika mishi, kallonta ya yi sannan ya girgiza kai alamar a’a ya ce, ”Ki fara sallamar waɗannan ai sun riga ni zuwa, ni zan jira a soya wani.”

Murmushi ta yi duk da ba ta ji daɗin gwasale ta da ya yi ba amma gaskiyarsa ya faɗa, ko da na kan wutan ya soyu sallamar yaran ta fara yi tana ba wa kowa na kuɗin shi har ta gama da su, kamar ɗazu yanzu ma guda biyar ta saka a ledar a maimakon guda uku na goman da zai siya ta miƙa masa, kallonta ya yi sannan ya ce, “Inna Shatu ai guda biyar ne a nan kuma ni na goma zan siya.”

“A’a dai ɗan nan wannan na ba ka ne kyauta, ka bar kuɗin ka sayi alawa da shi a makaranta.”

“Na gode amma ki karɓi kuɗin.”

“Ban san ka da gardama ba mai babban suna, ka karɓa kawai ka tafi makaranta. Allah ya yi maka albarka.”

“Amin, Na gode.” ya faɗa sannan ya karɓi ledar fanken ya saka a cikin jakarsa ya nufi hanyar makarantar cike da mamakin wannan abu, a lokuta da dama idan Umman ta ba shi kuɗin ɓatarwa ya je siyan abu sai a ƙi karɓar kuɗin, wani lokaci ma har da ƙari ake masa a kan abindia ya je siya ɗin kamar yadda Inna Shatu tayi yanzu, koda ya tambayi Umma sai ta ce masa baiwa ce yake da ita na farin jini.

Kamar koyaushe a bakin ƙofar makarantar ya hango Umman tsaye tana jiran isowar shi, da ɗan hanzari ya ƙarasa ya durkusa yana gaishe ta.

“Ba ni labarin abinda ya saka farin ciki haka har ya kasa ɓoyuwa a fuskarka.”

“Umma har kin gane?.”

“Sosai ma Baɗɗo, ina iya karantar ko wani yanayi da kake ciki. Mu ƙarasa ciki sai ka ba ni labarin abinda ya saka nishaɗi yau.”

Jakar hannunta ya yi niyyar karɓa amma ta hana shi duk yadda ya so hakan, dole ya haƙura suka shiga cikin makarantar, ba’a fara taruwa sosai ba saboda makarantar Gwamnati a wannan zamanin ba ko’ina bane za ka ga ɗalibai ko malamai su na zuwa a kan lokaci.

Ajin da ta ke koyarwa suka nufa, zama tayi a kujerarta ta malamai shi kuma ya zauna a wacce ke fuskantar ta inda teburin littafai ya zama a tsakiyar su.

Hannu ya saka cikin jakarsa ya ciro ledar fanken ya miƙa mata, kallon da ta ke masa ne ya sa ya ba ta labarin abinda ya faru kafin ya fito a gidan. Murmushi kawai tayi da ya kasa fahimtar ma’anar shi.

“Ka manta yau Litinin Umma na azumi?.”

Haɓa ya riƙe sannan ya kyabe fuska yace, “Umma daɗin abinda ya faru ne ya mantar da ni.”

“Kar ka damu, watarana har kaza za ka siyawa Umma.”

Murmushi ya yi sosai kafin yace, “In sha Allah Umma.”

“Bari na zuba maka abinci ka karya.”

Kunun Nono ta zuba masa a kofi da alala guda biyu a plate ɗin, bismillah ya yi sannan ya fara cin abincin hankali kwance kamar yadda ya saba.

Ruwa ta ba shi a gora bayan ya gama karin kumallon ya je ya wanko hannayensa da suka ɓaci, zama ya yi a kujerar sannan ya ciro kudin da Babansa ya ba shi ya miƙa mata.

Karɓa ta yi tana faɗin, “Babu abin da za ka siya ne kake so a ajiye?.”

“A’a Umma, nima na ba ki ne ki siya dabino, idan kin buɗe baki sai ki ci.”

“Na gode yaron kirki, aikuwa yau da dabinonka zan fara buɗe baki. Tashi ka tafi aji an taru sosai, idan aka fita tara sai ka ci fanken, a yi karatu sosai ban da wasa.”

“To Umma, na tafi.”

Jakarsa ya ɗauka ya fice daga ajin yana waiwayen ta, wasu hawaye ne suka zubo mata na tausayin yaron, ko a ina mahaifiyarsa take? Tana raye ko a mace?Me ya sa har yanzu iyayenta ba su zo nemanta ba? Ko zaton su tana lafiya ne shi ya sa har yanzu ba su daina fushin da suke yi da ita ba? Shekaru sun ja sosai, amma babu wani sauyi daga ɗabi’un da ɗan’uwanta Jibrin ya bijiro da su tun a waccan lokacin bare ta samu ƙwarin gwiwar binciko inda take.

“Ya Allah kai ne masanin fili da ɓoye, Ka yaye mana matsalolinmu na zahiri da baɗini.”

Ta faɗa a fili tana share hawayen da ke ƙokarin zubo mata don a lokacin har yaran ajinta sun fara shigowa.

JASMINE🌸

 

<< Al-Mustapha 1

1 thought on “Al-Mustapha 2”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×