Skip to content
Part 1 of 1 in the Series Al'adarmu by Dielaibrahim

Bismillahir rahmanir rahim

ƘASAR HAUSA, DAURA.

Al’adarmu, al’ada ta kasance cikakkiyar hanyar rayuwar mutane a karkashin yarensu da mabambanta al’adu, addinin su, muhallin su da kuma zamantakewar su. Al’ada dai na da matukar muhimmanci musamman ma a cikin yaren mutane, ko wanne yare yana da na shi al’adan da kuma banbanci tsakanin wani yare da wani yaren, a hausan ce al’ada na nufin abin da aka gada daga kaka da kakanni.

Al”ummar hausa dai, al’umma ce dake zaune a arewa maso yammacin tarayyar Najeriya da kudu maso yammacin jamhuriyyar Nijar. a al’adance mutane ne masu matukar hazaka da baiwa iri da kala ta fannin al’adu da kirkire kirkiren abubuwan al’adu.

Daura jiha ce ta addini kuma ta taka muhimmiyar rawa a fannin gargajiya a arewacin Najeriya, kirarin da aka fi yima ta shine “Daura ta ABDU tushen hausa”

Gidan Daura haka kowa yake kiran gidan mu, mafi akasarin mutanen garin suna mana lakabi da Daurawa saboda zumunci da son ƴan uwan junan mu, Sunan ya samo asali ne tun daga kan Kaka da Kakanni kuma suka kafa tarihi mai karfi a cikin zuriyar gidan daura wanda tarihin ya jima yana tasiri a zuciyoyin al’ummar dake gidan.

Kakannin mu su suka kafa wannan zuri’ar sa’annan sun taɓa mulkan garin Daura a zamanin baya kafinnan mulkin ya fita daga hannun su, sai suka kafa nasu ahalin da tambarin sunan gidan wato Gidan Daura.

Babban estate ne wanda a kalla ba’a kasari ba ya kunshi gidaje ashirin koma fiye da haka, ban da yawan adadin filayen dake ajiye gefe guda ana noma idan damuna yazo, haka zalika duk wanda zai yi aure a zuri’ar gidan Daura anan ake yanka masa fili a ba shi kyauta shi kuma ya gina da gumin sa.

Alkasim Muhammad Daurawa shi ne Kakan mu na karshe wanda yai mulki a masarautar Daura, kuma daga kan sa mulkin ya fita a hannun sa, ba laifin sa bane amma da yawa ana kawo chechekuche akan cewa da haɗin bakin gwamnati aka fidda gidan mu daga cikin masarauta, Alkasim Muhammad Daurawa matar sa ƙwalli ɗaya_Murjanatu ta haifi yara uku, Namiji biyu, sai mace ɗaya.

Murjanatu ta haifi Bishir, Huraira sai Mustapha wato kakana, ma’ana mahaifin Babana shine ɗanta na uku, daga nan kuma Alkasim wanda ake masa lakabi da *Daurawa* Allah ya wadata shi da dukiya mai tarin yawa, shi ya siya estate ɗin da muke ciki sa’annan ya haɗa kan family guda har yar sa HURAIRA A estate ɗin ya basu gida ita da mijin ta kasancewar shi mijin nata ɗan uwa ne…abu dai a hankali ya fara yawa…..ya kashe ma ƴaƴan sa kuɗi sun yi makaranta boko da islamiyya sun yi jami’a, Bishir na aikin banki, aka haɗa sa aure da ƴar kanwar Maman su(Murjanatu), shi kuma kaka na, Mustapha shi yayi gadon sarauta, duk wani hali na ɗan sarki da gidan sarki to fa kakana Mustapha ya gada, kasaitaccen mutum ne mai faɗa aji, kuma ɗaya cikin dubu mai basirar haɗa kan mutane da taimakawa talakawa fa jama’ar sa, tun kuruciya har girman sa, duk da sarautar bata dawo gidan mu ba amma Kakana Mustapha ya fanshe duk wani cin mutunci da butulci da akayi wa mahaifin sa Alkasim Daurawa…..Mustapha ya karanta politics fannin siyasa hakan yasa yai fice yayi suna domin har honourable na garin ɗaura sai da yayi a wancen lokacin kuma yayi senater a garin katsina sa’annan shima Allah ya dafa masa, Allah ya sa ma hannun sa albarka dukkan abin da zai yi sai Allah ya albarkace shi….duk wani matashi babba da yaro mai neman shiga takara sai ya biyo ta hannun kakana Mustapha kafin ake samu.

Mahaifin su Alkasim Daurawa shi ya kafa Al’ada mai tsauri a gidan Daura wacce har yau har gobe da tsoffin al’adu ake anfani.

Ya sanya doka kuma al’ada mai tsanani akan cewa babu mai auran bare sai na gida daga kan maza har mata, bai yadda wani ko wata jika ya kawo mata miji ko mata daga waje ba idan ba na cikin gida ba.

Wannan Al’ada ko ince doka yayi tsauri amma hakanan kowa yake bin umarnin sa, saboda samar da zaman lafiya a Zuriyar Gidan Daura.

Mutapha ƴar sarkin Daura ya aura mai mulki a wannan zamanin, kuma dole aka basa, duk dama Daurawa ya so ya hana auran amma hakanan ya hakura kasancewar matar mutum kabarin sa kuma ƴar aminin sa ce babu yanda ya iya….amma tun daga kan Kakana babu wanda ya sake fita waje neman aure.

Bishir ya haifi yara bakwai, maza biyar mata biyu,

Huraira ta haifi yara goma maza shidda mata huɗu, duk suna estate ɗin mu.

Sai Kakana Mustapha da ƴar sarkin Ɗaura mai suna Maimunatu fulanin katsina ce ita, Allah ya azurta su da yara biyu Mahaifi na (Sulaiman) sai kanwar mahaifi na (Salima).

A lokacin da aka haifi mahaifi na, Alkasim Daurawa ya rasu ya bar wasiya mai karfi na kar wanda ya kuskura ya rusa al’adar Gidan Daura, haka suka tafiyar da rayuwar su kamar yana raye….in da Mahaifi na (Sulaiman) ya girma yayi karatu mai zurfi a ƙasar turkey ya zama kwararran likita sai da yayi shekaru goma sha biyar a ƙasar turkey kafin ya dawo Najeriya daga nan kuma asibitoci daban daban suka rinka tura masa appointment wannan ya bashi damar zama International doctor, yana zuwa gari daban daban, ƙasashe daban daban domin yin aikin sa, yayi fice a sako da lungu na garin Daura ko ince garin katsina babu wanda bai san Dr. Sulaiman Mustapha Daurawa ba.

*****

Istiklal Avenue

TURKEY

Ɗaya daga cikin rantsastsun gidajen dage jere a birnin tarayyar turkiye, gidane na alfarma kuma na gani na faɗa, gaban gate ɗin black color irin trasparent gate ɗinnan mai karafuna dogaye wanda kana iya hango kashi hamsin na dukkan abubuwan dake kunshe a barandar gidan , Sunan mai gidan ne ɓaro ɓaro wato DR.SM DAURAWA.

Cikin jerun ɗakunan hutawa na cikin shiyyar gidan muna zaune ne muna tattauna wa, gaba ɗayan mu mun dukufa mun mai da hankali akan abin da mu keyi.

Lallausan hannun Ammi na shi ya dawo dani daga trance ɗin dana shiga ina kara gyara littafin da nake rubutu akai ina rubuta daidai gwargwadon abin da Ammi take zayyana min akan labarin dangin mahaifi na wanda ban ma san su ba ina kwaɗayin haɗuwa da su, ina son ganin su, ina son sanin dangi na, ina son sanin yadda suke ɗabi’un su, da al’adar su kamar yadda Ammi ta zayyana min duk da itama bata taɓa ganin su ba, asalima babu wani daga cikin dangin mahaifi na da yasan da zaman mu a turkey, mu kaɗai muke rayuwar mu, sai Abhi idan yazo duba mu duk bayan sati uku yake zuwa wajan mu.

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×