Skip to content

Alkalamin Kaddara 1 | Babi Na Uku

4
(1)

<< Previous

ABUJA

Bayanta ne a riƙe kamar zai karye haka take jin shi, ga zazzaɓi tun na jiya da yake jikinta har safiyar yau.

“Sugar…”

Ta kira Rafiq da ke kwance akan cinyarta, din da alama a haka suka kwana, ganin bacci yake hankalin shi a kwance ya sa ta saka hannunta cikin sumarshi tana yamutsawa. Buɗe idanuwa ya yi da addu’ar tashi daga barci a bakin shi, ganin Tasneem ya sa shi miƙewa babu shiri. Kallonta yake da mamakin me yake yi a ɗakinta, kaf komai ya dawo mishi. Muryarshi da bacci a jikinta har lokacin yace,

“Neem?”

“Lokacin Sallah ya yi.”

Shi ne abinda ta ce tare da miƙewa, wani irin jiri ya kwashe ta, cikin zafin nama Rafiq ya riƙo ta.

“Me yasa ba ki da hankali ne wai? Ba ki san ba a so daga tashin ka daga bacci ka miƙe ba?”

Ya yi maganar yana ƙoƙarin saita bugun da zuciyar shi take yi har a lokacin. Ta hannunta da yake riƙe da shi ya ji zafin zazzaɓin da ke jikinta da ya tuna mishi cewar tana buƙatar ganin likita, yana riƙe da ita ya miƙar da su, hannunta riƙe cikin nashi yake janta zuwa toilet. Muryarta babu ƙwari ta ce,

“Zan iya zuwa da kaina…”

Don har a zuciyarta take jin kusancin shi da ta san don raunin da ya ga tana da shi ne yake nuna mata, a hankali take ƙoƙarin zame hannunta da Rafiq ya sake riƙewa dam ya ja ta zuwa hanyar toilet ɗin, da kanshi ya buɗe ya ja ta ciki tukunna ya sake ta, nazarin yanayinta yake y, sai da ya tabbatar za ta iya alwala ba tare da ta faɗi ba tukunna yace,

“In za ki iya ki yi wanka, zanje Sallah idan na dawo ni ma shiryawa zan yi sai mu tafi asibitin, Fawzan ma na can.”

Da mamaki Tasneem ta kalle shi, kafin ya juya zuwa wani yanayi daban, tun farko ma ba ta san me ya sa ta mamakin rashin faɗa mata cewar Fawzan na asibiti da Rafiq bai yi ba. Ganin ta yi shiru ya sa shi juyawa ya nufi hanyar da ta fita da shi daga ɗakin. Har lokacin kanshi da nauyi sosai, ya nufi ɗakin shi, banɗaki ya shiga, alwala yayi ya fito ya sake kayan jikinshi zuwa doguwar jallabiya ya fita masallaci, duk saurin da ya yi raka’a ɗaya ya samu. Ko da ya dawo sai da ya fito wanka tukunna ya ɗauki wayarshi. Yana shirin kiran Nuri ya ji ya suka kwana ne nata kiran ya shigo, ɗagawa ya yi tare da yin sallama.

“Yanzun nake shirin kiran ku.”

“Nasan hali ai, shi ya sa na ce bari in kira in faɗa maka da sauƙi, ya farka amma ko mintina goma bai yi ba ya sake komawa bacci, to har yanzun.”

Sauke numfashi Rafiq ya yi wata ‘yar nutsuwa na shigar shi.

“Alhamdulillah. Ina kwana…”

“Lafiya kalau, ya kuka tashi?”

Numfashi ya sake saukewa, yana jin yadda zuciyarshi ke son faɗa wa Nuri damuwar shi amma ba zai iya ba.

“Sai hamdala Nuri, Tasneem ma ba ta jin daɗi, za mu taho asibitin tare anjima kaɗan.”

“SubhanAllah… Allah ya ba ta lafiya ya kai mu.”

Nuri ta faɗi ta ɗayan ɓangaren. Rafiq ya amsa da,

“Amin thumma amin. Aroob fa?”

“Karatun Qur’an take yi.”

Ɗan murmushi Rafiq ya yi, Aroob ita ce ustazziyar gidan gaba ɗaya dama. “

Ki ce ta saka mu a addu’a.”

“In shaa Allah.”

Sallama suka yi da Nuri akan sai sun je asibitin tukunna, ya sauke wayar daga kunnen shi. Yana jin nauyin ranar akan kafaɗun shi tun kafin garin ya ƙarasa haske. Miƙewa ya yi ya nufi wardrobe, yadi ya fito da shi ruwan ƙasa mai haske ya saka a jikin shi, takalmi da hula ya fiddo yana ajiyewa.

Sai da ya fesa collection ɗin turarukan shi tukunna ya fita don ya ga ko Tasneem ta shirya.

*****

Da ƙyar ta iya yin alwala ta fito, a zaune ta yi Sallah don ko kaɗan jikinta babu ƙarfi, ko azkar ɗin safe ba ta yi ba, da dafa bango ta koma banɗaki, ruwa mai zafi ta haɗa ta samu ta watsa a jikinta, hakan bai hana wani irin sanyi ratsa ta ba, har cikin ƙasusuwanta. Tana fitowa kan gado ta faɗa ta jan bargo ta rufa. Amman ko’ina na jikinta kyarma yake yi, sanyin da take ji har cikin hanjinta. Tana jin haƙoranta na haɗuwa waje ɗaya. Ga numfashinta da take ta faman kokawa da shi yana sa kanta ɗaukar ɗumin gaske. Ba ta san lokacin da ta ɗauka a haka ba sai jin turo ƙofar Rafiq ta yi, ba za ta iya amsa mishi sallamar da ya yi ba.

Hango ta da ya yi akan gado rufe har kanta ya sa shi ƙarasawa da hanzari ya hau kan gadon gaba ɗaya tare da kama bargon ya buɗe fuskarta, idanuwanta a runtse suke sai rawa da duk jikinta yake yi.

“Yaa Rabb…”

Rafiq ya faɗa zuciyarshi na sake jagulewa, don yanayin Tasneem ɗin kawai za ka kalla ka san ta kwana biyu ba ta da lafiya. Ya ma rasa abinda ya kamata ya yi mata, kamota ya yi yana miƙar da ita zaune, hakan ya sa ta buɗe idanuwanta.

“Amai nake ji…”

Ta faɗa a galaɓaice, sauka Rafiq ya yi daga kan gadon ya taimaka mata ta sauko, yana riƙe da ita suka nufi banɗakin, sai dai banda yunƙurin aman babu abinda take yi.

“Me za ki amayar? Bayan cikin ki babu komai.”

Rafiq ya faɗa cike da damuwa, haka ya kama ta suka dawo ɗakin. Da kanshi ya ɗauko doguwar riga ta atamfa da hijab ya taya Tasneem ɗin ta saka rigar ya kwantar da ita ya

fita. Yoghurt ya samo a fridge ɗin kitchen da kofi ya dawo. Ajiyewa ya yi ya tashe ta ya jinginar da ita tukunna ya ɗauki kofin ya zuba, tun kafin ya miƙo mata ta ce,

“Ba zan iya sha ba…”

Don ganin yoghurt ɗin kawai ɗaga mata hankali yake ƙara yi. Girgiza kai Rafiq ya yi, Fawzan da Aroob sun sa zuwa asibiti ya zame musu jiki, ba ita da shi za su yi rashin hankalin nan ba, ya san dokokin King’s Hospital, dole ta sa ma cikinta wani abu. Shi Doctor ɗin zai wa magana.

“Ko za ki yi amai ki sha, wani zai zauna.”

Karɓa ta yi ta rufe ido ta kafa kai, tas ta shanye ta miƙa mishi kofin tana yamutsa fuska, nazarin ta yake yi. Sai da ya tabbatar ba ta yunƙurin amai tukunna ya sa hannu a aljihunshi ya kira direban shi ya faɗa mishi cewar yana gab da shigowa. Kasancewar ba su da nisa yasa Rafiq ɗin bai damu ba, don ko da cikin dare matsala ta tashi kiran shi kawai zai yi.

“Tun yaushe ne ba ki da lafiya?

Ya buƙata, ɗan jim Tasneem ta yi, tambayar shi na sa ta tunanin yaushe rabon da ta ji ta da lafiya, ko da gangar jikinta ba ta amsaba, zuciyarta akwai ciwo a cikinta. Muryarta a sanyaye ta ce,

“Kafin bikin mu…”

Ranshi ya ji ya ɓaci ba kaɗan ba.

“Hankalin ki bai faɗa miki yakamata ki je asibiti ko ki faɗa min ba? Damuwar da kika sani ciki ba ta isheki ba Neem?”

Idanuwanta ta ji sun ciko da hawaye, ko da taso gaya mishi ɗin yaushe ta samu dama, tun daren farkon su komai ya canza a tsakanin su, ta ina za ta fara faɗa mishi ba ta da lafiya, zai ma iya ɗauka don tana neman kulawarshi ne, buɗe baki ya yi zai sake magana sai wayar shi ta fara. Isah ne, miƙewa ya yi ya fita daga ɗakin. Bai fi mintina biyar ba ya dawo kanshi sanye da hula, hijab ɗin Tasneem ya ɗauka ya ba ta ta saka a jikinta tukunna. Hannu ya miƙa mata, yana kallon yadda motsi ma wahala yake mata amman ƙoƙarin tashi take yi da kanta.

“Na kusan ɗaukarki a kafaɗata in ba za ki bari in taimaka miki ba…”

Ta san zai iya, don haka ta kama hannun shi ta riƙe gam ya taimaka mata ta sakko, a haka suka fita har wajen motar, gaisawa suka yi da Isah tukunna suka shiga bayan motar ya ja su zuwa King’s hospital.

*****

Ƙauyen Kinkiba

Ganin Altaaf ya jima, ga kuma zaman shirun ita kaɗai ya soma isarta ya sa ta kunna wa’azin Mufti tana ji, kira ne ya shigo wayarta,  hakan ya sa ta ɗagowa daga jinginar da ta yi da kujerar ta ɗauka ta duba. Ganin Aslam ne ya sa ta ɗagawa tare da yin sallama.

“Anty ina wuni…”

Amsa gaisuwar ta yi, tun tana jin nauyin Antyn da Aslam yake kiranta da shi kasancewar ya girme ta har ta saba.

“Wayar yaya ba ta zuwa… Har kun ƙarasa ne? Ni yanzun nake shiga Zaria ma.”

Da mamaki Majida tace,

“Na aza da su Ammi kuka tahi.”

“No ni ina wajen aiki fa, kafin in dawo har sun wuce…”

Aslam ya amsata, jinjina kai Majida ta yi.

“Motar mu ta lalace bisa hanya wallahi, mun tsaya wani ƙauyene, Altaaf ya tahi nemo mai gyara.”

“SubhanAllah… Wane ƙauyen?”

Ɗan daƙuna fuska Majida ta yi don ba ta san ko wanne ƙauye bane.

“Ina zuwa in duba.”

Ta faɗa tana kashe wayar, data ta ta buɗe, sai dai network ɗin babu ƙarfin kirki, hakan ya sa ta sauke glass ɗin motar ta tambayi wani saurayi ya faɗa mata. Sake kiran Aslam ta yi tana gaya mishi sunan ƙauyen.

“Okay… In an wuce Zaria ne, ba zan fi mintina talatin ba zanzo wajen… Sai in duba motar mu wuce gaba daya.”

“Tau, Allah ya iso da kai lahiya.”

Ya amsa da amin yana kashewa. Ajiye wayar ta yi kan cinyarta ta sake komawa ta jingina da kujerar. Sosai take jin ta gaji ga yunwa da ta fara damunta.

*****

Marin da Tawfiq ya yi mishi na dawo da wani abu cikin kanshi. Da sauri samarin da suka rako Altaaf suka ƙaraso suna riƙe Tawfiq da faɗin,

“SubhanAllah… Tawfiq me ya yi zafi haka?”

Ture su ya yi, yana maida hannuwanshi baya yana sake ɓoye yaran a bayan ƙafafuwan shi. Idanuwan shi cike da wani irin yanayi don tsallen da zuciyarshi ta yi da ganin Altaaf har cikin wuyanshi ya ji ta. Yanzu kam kamar yana ɗanɗana ɗacin da take mishi akan harshen shi yace,

“Kuskure na biyu da za ka yi yau banda sake tako ƙafafuwanka Kinkiba shi ne shiga ta gida in fito in sameka…”

Hannu Altaaf yasa cikin sumar kanshi yana harmutsawa kafin ya sauke shi ya fara tafiya da baya taku biyu, ya ɗora hannuwanshi duka biyun akan ƙugunshi ya kuma sauke su, cikin shi da hanjin ciki suke yin kamar suna tsinkewa ya dafe. Dariya ta kuɓce mishi da ba ta da alaƙa da nishaɗi. Kai da kake nesa da Altaaf yanayin da ya shiga za ka iya cewa sabon hauka ne yake shirin kama shi, shi da kanshi yana jin kamar haukan ɗan lokaci ne ya same shi, don yadda kanshi yake cunkushe da rashin yiwuwar abinda ya ƙi yarda ko zuciyarshi ta furta mishi.

Wata dariyar ce ta sake kuɓce mishi da ya ga yadda Tawfiq ya ja yaran suna komawa ta ƙofar da suka fito, musamman da ya ji shigar su ta tafi da wani ɓangare na zuciyarshi da bai taɓa sanin yana da shi ba sai yau. Samarin da ba su san me ke faruwa ba suka ƙaraso inda Altaaf yake ɗaya daga cikin su cike da rashin jin daɗi yace,

“Kayi hakuri don Allah.”

Kallon shi Altaaf yayi kafin ya sake kwashewa da dariya, cikin shi na yamutsawa yana faɗa mishi ko da wanne lokaci abinda duk yaci da ya yi saura a cikinshi yana gab da fitowa. Juyawa Altaaf ya yi ya nufi hanyar da suka biyo wajen zuwa.

Kamar wanda ya sha wani abu haka yake haɗe hanya wajen tafiya. Ikon Allah ne kawai ya sa ya gane inda suka bi wajen zuwa, yadda jikin shi ba ya tare da nutsuwa ko kaɗan, ba zai ce ga yadda aka yi ya zo ba, motar Aslam yake gani kusa da tashi. Sai Majida a tsaye da alama hirar da suke da Aslam ɗin ta ɗauke musu hankali don babu wanda ya kula da ƙarasowar shi.

Ganin Majida ya ƙara hautsina mishi lissafi.

‘Ka san an yi hwaɗa sosai tsakanin dangin Innata da na Babana kan auren mu, sukai ta hiɗin Baba ya amince ne saboda kuɗi, ba ka da halin ƙwarai.’

Maganganun Majida suka dawo mishi, jikin shi ya ɗauki ɗumi kamar a lokacin ne ta zagaya hannuwanta tana sake kwantar da kanta a ƙirjinshi.

‘Yanzun kau da babbar murya zan hiɗi ma kowa mijina mutumin azziƙi ne, ba ni kaɗai nike alfahari da shi ba har yaran mu ma za su yi.’

Cikin shi ya sake jin ya yamutsa, zazzaɓi nan take yana kama shi.

‘A-Tafida kamata ya yi ace duk garin da za ka sauka a dinga sanarwa kowane gida su adana yaransu wallahi, ka soma ba ni tsoro, da gaske cikin ka Abida ta zubda last week?’

Maganar Jamal ba ta gama dawo mishi ba, Majida ta katse mishi da faɗin:

“Wai, har ina kukaje haka?

Wayarka ba ta zuwa kuma?”

Kallonta kawai Altaaf yake yi da wani irin yanayi a fuskarshi da ya sa ta ƙarasowa tana nazarin shi, hannu ta kai ta riƙe haɓarshi da juyo da gefen fuskarshi, abinka da farar fata, yatsun Tawfiq ne kwance kan kuncin shi. Ware idanuwa Majida ta yi, kafin ta yi magana Altaaf ya ture ta tare da matsawa gefe. Amai ya soma kwarawa, hakan ya sa ita da Aslam suka yi kanshi. A rikice take dafa shi tana faɗin,

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un…”

“Daman bashi da lafiya ne wai?”
Aslam ya tambaya ganin yadda Altaaf ɗin ke kwara amai kamar zai fiddo kayan cikin shi. Girgiza mishi kai Majida ta yi idanuwanta cike da hawaye, muryarta na rawa tace,

“Lahiyar shi ƙalau muka hito wallahi… Ban san MI ya same shi ba.”

Ruwa Aslam yaje ya ɗauko a cikin motarshi ya ba Majida. Altaaf ta miƙa wa ya karɓa ya kurkure bakin shi ya kuma wanke fuskarshi, da ƙyar ya iya miƙewa, Majida ta kama hannunshi, jin zafin ya wuce misali ya sa ta saurin kai hannu ta taɓa wuyanshi da fuskarshi, zazzaɓin da ta ji ya sa ta mantawa da shatin yatsun da ta gani kwance akan fuskarshi.
“Mi ya same ka wai? Jikinka da zahi ƙwarai.”

Ta tambayeshi, girgiza mata kai kawai ya yi, don ba ya jin zai iya magana, har lokacin cikin shi yamutsawa yake yi.

“Sannu…. Aslam ma ya duba motar hwa, mu tahi kawai sai muje asibiti.”

Majida ta faɗi.

“Gaskiya kam… Jiba yadda har fuskarshi ta kumbura.”

Aslam ya ce cike da damuwa. Buɗe mishi ƙofar motar Majida ta yi ya shiga. Ita ta zagaya mazaunin driver ta zauna tana wa Altaaf ɗin sannu, shi kam hannu yakai yana sake sauke kujerar ya kwanta a jiki sosai ya rufe idanuwanshi. Yana ji har Majida ta ja motar suka soma tafiya. Ba asibiti yake buƙata ba, ba magunguna yake so ba, rashin lafiyarshi ba ta da alaƙa da duk wannan, Alƙalamin Ƙaddara ne yake son buɗe mishi shafin rubutun da yake zaton ya disashe, rubutun da ya jima yana addu’ar kar ya gifta ko ta inuwar Majida balle ta ganshi. Da yaƙinin da bai taɓa sanin yana da shi ba a rayuwarshi, zuciyarshi na zubda hawaye masu ciwo yake jero Addu’o’i.

‘Allah karka tona min asiri a wannan lokacin, Allah karka sa abinda nake zato ne ya faru, Allah ka sa abinda ya faru yanzun nan ya zama mafarkin da zan farka daga shi ina mai sake neman gafarar zunubaina.’

Sai dai me, da kukan motar da yake ji a hankali dana sauran motocin dake wucewa kan titin da yawan tsoron dake sake cika mishi zuciya, ga fuskokin yaran da suke son hargitsa mishi duniyarshi lokaci ɗaya.

*****

Kano

“Nikam da an sa wuƙan yanka lemon nan Tariq.”

Ashfaq ya faɗa, yana jan jiki da gyara zamanshi da ƙyar, runtse idanuwa ya yi saboda azabar raɗaɗin da ya ratsa shi, ta baki yake jan numfashi yana ƙoƙarin daidaita shi.

“Saboda me?”

“Saboda wahala kake tayi tun ɗazun.”

Lemon da ke hannunshi Tariq ya kalla, da gaskiyar Ashfaq ɗin, ya fi mintina goma yana kokawa da ɓare lemon zaƙin, bai sa an yanka ba da ya siyo, don in dai Ashfaq zai sha lemo bai taɓa ganin ya yanka ba, ya fi son ya ɓare da hannun shi. Bai taɓa sanin abin da aiki ba sai yau.

“Ka ga, miƙo min nan.”

Girgiza kai Tariq ya yi yana daƙuna fuska.

“Ni zan ɓare fa.”

“Bance ba za ka ɓare ba ai nima, kawai cewa na yi ka miƙo min wani nima.”

Ashfaq ya faɗa yana ƙoƙarin ɓoye murmushin shi, don lemon da ke hannun Tariq ɗin ba ƙaramar wahala ya sha ba, duk kana ganin kayan cikin lemon. Jan kujerar shi Tariq ya yi yana matsawa sosai gab da gadon Ashfaq ɗin, ya ɗauki lemo ɗaya ya miƙa mishi.

Ɗan yatsan shi kawai yasa ya yi hanya, sai ga shi ya soma ɓare lemon, ko mintina uku bai ɗauka ba ya gama, yana gyara shi. Baki a sake Tariq yake kallon shi.

“This is so not fair.”

Dariya Ashfaq ya yi, yana miƙa wa Tariq lemon da ya gama ɓarewa.

“Miƙo min wani, sha wannan.”

“Kai ka fara sha…”

“Ba na son jan magana… Ka karɓa ka miƙo min wani.”

Karɓa ya yi, ya miƙa mishi wani lemon, dai-dai shigowar Yasir da sallama. Su duka biyun suka amsa, waje ya samu ya zauna.

“Kamar anyi wasan cikar shekara da kai a bakin sabon gari.”

Tariq ya faɗa yana kallon Yasir ɗin da ya yi duhu, idanuwanshi sun canza launi, gajiya tattare a fuskarshi. Ga gashin kanshi a cukurkuɗe. Hannu Yasir ya kai ya ɗauki lemo ɗaya.

“Ban ɗauka ma na kai haka yin kyau ba.”

“Kanka kamar dambun yara.”

Tari Ashfaq ya soma yi saboda lemon da ya shaƙe shi wajen dariya. Shi kanshi Yasir ɗin murmushi ne a fuskarshi.

“Ba abin dariya bane Yaya… Yana buƙatar taje kanshi.”

Tariq ya faɗa babu alamar wasa a fuskarshi. Ganin Ashfaq bai da niyyar daina dariyar da yake yi ya sa Tariq ɗin miƙewa.

“Kana nan? Ina son zuwa gida in ɗauko kayana.”

Ya yi maganar yana kallon Yasir. Kai ya ɗan ɗaga mishi a hankali.

“Da ka faɗa min da na ɗauko maka, daga gida nake yanzun.”

Tariq bai amsa shi ba ya mayar da hankalin shi kan Ashfaq, kafin ya yimi magana Ashfaq ɗin ya riga shi da faɗin:

“Ka je Tariq, ina nan, babu inda zan je.”

Sauke numfashi Tariq ya yi, ya wuce ya buɗe kofar ya fita ba tare da ya ce komai ba, kamar tura ƙofar shi kawai Ashfaq yake jira kafin ya ce wa Yasir:

“Ka je?”

Girgiza mishi kai ya yi a hankali.

“Na ɗauka har roƙonka na yi, ka fi kowa sanin muhimmancin cika alƙawari a wajena Yasir, me ya sa za ka yi min haka?”

Sosai Yasir yake kallon shi.

“Me yasa ba zaka faɗa min wacece ita ba? Me yasa ita ɗin? Mahaukaciya Faq?”

Kau da kai gefe Ashfaq ya yi, zai yi ƙarya idan ya ce ranshi bai ɓaci ba, ba ko da yaushe yake barin tunanin abubuwa na damun shi ba. Muryarshi can ƙasan maƙoshi yace,

“Ba mahaukaciya bace.”

Jinjina kai Yasir ya yi.

“Yeah, na gani ai, shi sa take rayuwa a gidan mahaukata, har da ɗaki ko?”

“Nudra…”

Ashfaq ya faɗa can ƙasa, daƙuna fuska Yasir ya yi.

“Nudra, sunanta Nudra, ba mahaukaciya bace ba…”

Shiru Yasir ya yi yana jiran wani ƙarin bayani. Ganin Ashfaq ɗin ba shi da niyyar sake cewa komai yasa shi faɗin:

“Me ka yi wannan karon? Ashfaq me ka yi?”

Juyowa yayii ya saka idanuwanshi cikin na Yasir.

“Me kake zaton zan yi?”

Kallon shi kawai Yasir yake. Sauke numfashi Ashfaq ya yi ranshi a ɓace:

“Ka san komai…”

“Nasan abinda ka zaɓi ka faɗa min, na gane wasu abubuwan da kaina, amman ita? Tun jiya da daddare kaina yake yawo na kasa zuwa ko’ina da tunani, me ya sa ita?”

“Tausayin ta nake ji…”

Yasir bai san lokacin da dariya ta ƙwace mishi ba, sosai yake dariya, idanuwan shi Ashfaq ya ɗauke daga kan Yasir, ya san me yake wa dariya, shi kanshi kalmar har lokacin nauyi take mishi akan harshe.

“Faq, tausayi? Tausayi fa ka ce, kai kake haɗa kanka da tausayi a jimla ɗaya. Allurar baccin da akai maka ce ba ta gama sakin ka ba ko me?”

“Idan ba za ka je ba ka faɗa min kawai…”

Hankalin shi Yasir ya nutsar kan Ashfaq.

“Da gaske ka damu da zuwan nan har haka? Ashfaq me yake faruwa ne wai?”

Tambayoyin da Yasir yake mishi yanzun ne dalilin farko da ya sa bai taɓa faɗa mishi ba. Bai kuma taɓa bari ya sani ba. Don ko za a sake yi mishi sabon harbi ba zai ce ga abinda yake faruwa ba.

“Da gaske ka damu da wani banda Tariq.”

Yasir yake faɗa da matuqar mamaki a muryarshi.

“Kana magana kamar hakan sabon abu ne.”

“Faɗa min wa ka damu da shi? Banda Tariq?”

“Kai…kuɗi…”

“Uhum… Ina jinka, sai me kuma?”

Yasir ya faɗa, sosai Ashfaq yake tunani, zuciyarshi yake dubawa, me ya yi saura banda su da ya damu da, me ya rage mishi kuma? Rayuwa ba ta barshi da wani zaɓi na damuwa da wasu bayan Tariq, Yasir da kuma kuɗin da ya faɗa ba, sai kuma kanshi. A yanzun in duniyar za ta jirkice da kowa ba matsalarshi bane, in har su kaɗai ɗin nan za su fita, wataƙila in ya samu dama zai fitar har da Nudra, inya samu dama kenan.

“Zan je…”

Yasir ya faɗa tare da miƙewa tsaye. Jinjina kanshi kawai ya yi, ya zame jikinshi ya kwanta kan gadon tare da lumshe idanuwan shi. Numfashi mai nauyi ya sauke, yana ganin yadda duniyar ta yi mishi duhu gaba ɗaya, babu komai cikin kanshi da zuciyarshi na tsawon lokaci banda duhu.

In ba idanuwanshi bane a buɗe, kuma ya nutsu kan duniyar da ke faruwa a wajen shi, mantawa yake akwai wani haske a duniya, komai baƙiƙirin yake a tare da shi. Balle kuma wani abu wai shi nutsuwa, ya ma manta ya ake jin abu mai kama da kalmar, ya kuma cire rai daga sake samun kusanci da kalmar. Kamar yadda ya cire rai da faruwar abubuwa da yawa a rayuwarshi, kamar yadda ya faɗa ne, Alƙalamin Ƙaddararshi bai bar shi da wani zaɓi ba.

*****

Jin ƙafafuwanshi sun yi nauyi yakuma san zama waje ɗaya ne ya sa bai nemi abin hawaba da ya fito bakin asibitin. Ya yanke hukunci takawa ko yaya ne. Ko ba komai doguwar tafiya kan rage mishi tunanin da yakan cika mishi kai a lokuta da dama. Wasu yara ya gani mace da namiji, da alama namijin ne babba, hannun shi riƙe da na ƙanwar da ke dariya, kallo ɗaya za ka wa fuskarta ka san tun daga zuciyarta take dariyar, harararta yayan ya yi yana jan hannunta ranshi a ɓace.

Tariq bai san murmushi ya ƙwace mishi ba, sai da yaji bakinshi ya motsa.

*****

“Yaya Tariq ni yaushe zan koma makaranta?”

Arfa ta tambaye shi tana turo bakinta cikin yanayin da ya ga kamananninta da Baba na ƙara fitowa, yana saka zuciyarshi matsewa. Ɗan murmushi ya yi mata.

“Mu da muke hutawa Arfa…. Za mu koma ai, amma sai mun ƙara hutu….ko ba kya son hutun?”

Idanuwanta ne suka ciko da hawaye.

“Ni ba na jin daɗin hutun nan, saboda Su Mama ba sa nan, kuma in da makaranta ana dafa min abinci in tafi da shi da biscuit.”

Lumshe idanuwanshi Tariq ya yi, ya rasa ta ina zai fara ba ta amsa, ko kuma me zai faɗa mata, ƙarancin shekarunta sunyi kaɗan ta fahimci halin da suke ciki, a lokaci ɗaya kuma shekarun sunyi ƙaranci ta dinga fuskantar abinda take fuskanta tare da su. Tashi ya yi ya miƙa mata hannu, ta kama tare da mikewa. Fitowa suka yi daga gidan suka nufi shagon Mahdi, akwai Naira ashirin a jikin shi, ita ya zaro ya siya mata biscuit ya bata. Wata irin dariya ta yi.

“Nawa ne?”

Kai ya ɗaga mata, wannan karon ya kasa ko da murmushi ne, jinta ya yi ta riƙe mishi ƙafafuwa tana dariyar jin daɗi.

*****

Birkin da mashin ɗin ya taka ne ya katse mishi tunanin shi, don duk da ƙoƙarin kauce mishin da ya yi sai da ya dakar masa hannu da hannun mashin ɗin. Azabar raɗaɗin da yake ji ya sa Tariq jin hannunshi gaba ɗaya kamar ba na shi ba.

“Wane irin marar hankali ne kai? Ba ka da kunnuwa ne?”

Mai mashin ɗin yake faɗa rai a ɓace, muryarshi ta sa Tariq sakin hannunshi da ya riƙe, ƙwaƙwalwarshi ta daina jin komai, lokaci ɗaya zuciyarshi ta soma bugawa da ƙarfin gaske. Cikin tashin hankali ya ɗago kanshi yana sauke idanuwanshi akan fuskar saurayin da ke kan mashin ɗin. Runtse su ya yi ya sake buɗewa, shekaru biyar, watannin cikin shekarun, ranakun cikin watanni, daƙiƙan da ke cikin ranakun, duhun da yanayin rayuwa ya sa shi yi, ƙasumbar da ke fuskarshi har ma da girman da ya ƙara bai hana Tariq gane shi ba. Gwiwoyin shi ya ji sun yi sanyi ƙafafuwanshi suka soma rawa.

Lokaci ɗaya ya runtse idanuwanshi yana ƙara buɗe su, zuciyarshi ta kasa yarda da abinda yake gabanshi.

“Ya… Ya… Yaya Yasir.”

Ya faɗa da nufin maganar ta fito fili sai dai ko laɓɓanshi basu motsa ba, iya zuciyarshi kalaman suka tsaya. Bai san me yake faruwa a duniyar dake wajen shi ba, don ta cikin shi a hargitse take da tashin hankali, sai da ya ga ya ja mashin ɗin ya yi gaba.

Zuciyar Tariq ta fara gudu tana bin bayan shi kafin ƙafafuwanshi su karɓa.

“Yaya Yasir!!!”

Yake kira yana bin bayan mashin ɗin da gudu, sai dai me, gudun mashin da shi da yake a ƙasa ba ɗaya bane, musamman yadda yake gudun ƙafafuwanshi na harɗewa kamar zai faɗi, ganin mashin ɗin ya mishi fintinkau ya sa shi tsugunnawa a ƙasa , ba tare da ya damu da mutanen da ke harkokin su na yau da kullum a wajen da kallon da suke mishi ba.

Sosai ya durƙushe cikin ƙasa yana maida numfashi, dafe kanshi ya yi da duka hannuwanshi yana girgiza kai cikin alamar rashin yarda da abinda ya faru kafin ya miƙe tsaye ya juya. Gudu da sassarfa yake haɗawa da shi har ya koma cikin asibitin, sama ya hau ya nufi inda ɗakin Ashfaq ɗin yake.

Ƙafafun wandon shi inda ya durƙusa cikin ƙasa sun yi buɗu-buɗu. Tunanin sallama bai zo mishi ba, hannu kawai ya sa ya bankaɗa ƙofar. Jin buɗe ƙofar ba na lafiya bane ya sa Yasir juyawa. Ashfaq da bacci ya soma ɗauka shi ma sai da ya buɗe idanuwanshi. Bin Tariq da yanayin shi da kallo suke su biyun, an rasa wanda zai fara magana. Har Tariq ɗin ya taka cikin ɗakin ya je ƙarshen bangon, jikin kusurwa ya haɗe fuskarshi da wajen kamar mai son shigewa cikin bangon ɗakin.

Numfashi yake mayarwa a hankali saboda kanshi da yake ji a hargitse, ga jikinshi da ya soma ɓari a hankali, maƙoshin shi ya bushe ba don ƙishin ruwa ba, hannuwanshi da ke ɓari ya kai kan bangon yana ɗora fuskarshi akai. Da duk wani abu dake da rai a jikinshi yake buƙatar ko da syrup ne. Wani abu ya taimaka mishi wajen dai-dai ta hargitsin da yake faruwa cikin kanshi da zuciyarshi.

“Tariq…”

Ashfaq ya kira can ƙasa, muryarshi cike da fargaba da son sanin me yake faruwa. Yasir kam bai ce komai ba, ya san magana ɗaya, muryarshi kawai za ta iya ƙara wa Tariq ɗin damuwa. Inda zai iya tashi zai yi ya fice ya bar musu ɗakin.

“Tariq mene ne?”

Ashfaq ya sake faɗa a karo na biyu. Yana jin shi din haka ya girgiza kan shi kawai, ƙoƙarin miƙewa zaune Ashfaq ya yi, sai dai kafaɗarshi ta ce ba ta san ya sauko daga kan gadon ba don ciwon da take na saka numfashin shi ɗaukewa na ɗan lokaci

“Ka min magana Tariq!”

Yanayin muryar Ashfaq ɗin ya sa Tariq raba jikinshi da bangon, yana juyowa a hankali, har idanuwanshi sun sake launi saboda ƙwayoyin da jikinshi suke buƙata.  Ga jikinshi da ke ɓari kamar mai jin sanyi, ƙarasowa ya yi gefen gadon Ashfaq tare da durƙusawa.

Duk da ƙarin ruwan da ke hannun Ashfaq ɗin da babu inda ba ya mishi ciwo, hakan bai hana shi riko kafaɗar Tariq da ya ɗago ba, gefen gadon ya zauna ya ɗora kanshi akan ƙafafuwan Ashfaq ɗin ko zai samu sauƙin abinda yake ji.

Sai dai yana rufe idanuwanshi Fuskar Yasir ya gani, muryarshi na rawa yake fadin:

“Naganshi…Yaya na ganshi wallahi…”

Girgiza kai Ashfaq yake yi.

“Ba yanzun ba Tariq… No… Ba za kai min haka ba wallahi…ba za kai min haka ba…”

Yake faɗa cikin tashin hankali, babu yafda za ai ciwon Tariq ya dawo, yana ganin yadda jikin shi ke kyarma, bubbuga bayanshi Ashfaq yake yi.

“Tashi ka kalle ni… Babu abinda zai sameka…. Babu abinda zai sake samun ka… Ka na jina ko? Babu abinda zai sake samun ka Tariq!”

Ya ƙarasa a tsawace, har ya sa Tariq din ɗagowa. Kamar zai yi kuka yake kallon Ashfaq, inda za su ba shi syrup, kwalba ɗaya kawai zai ɗan samu nutsuwa, sai dai zuciyarshi ba ta da ƙarfin rokar Ashfaq ɗin.

“Yaya Faq na ganshi… Na ga Yaya Yasir… Ba akaina bane wannan karon…Wallahi ba a tunanina yake ba… Shi na gani akan mashin…”

Sosai Ashfaq yake girgiza wa Tariq kai, yana amfani da hannunshi da ke kafaɗar Tariq ɗin shi ma yana girgiza shi.

“Babu abinda ka gani… Babu abinda zai sameka kuma…. Mun yi sadakar mutuwar Yasir tuntuni.”

Ture hannunshi Tariq yayi yana miƙewa tsaye.

“Na ganshi…. Wallahi na ganshi!”

Yake faɗa cikin hargowa yana jin kanshi na jujjuyawa kamar zai tarwatse saboda muryoyi yake ji a cikin kan da ba ya gane me suke nema, me suke so da shi, me suke buƙatar ya yi su yi shiru.

“Me yasa ba za ka yarda na ganshi ba?!”

Ya tambaya cikin hargowa, ba Ashfaq ɗin yake ɗaga wa murya din ya yarda da shi ba. Yana ɗaga murya ne ko sautinta zai sa ya ji sauƙin hargitsin da ke cikin kanshi. Girgiza kai kawai Ashfaq yake, yana jin yadda zuciyarshi take ƙaryata cewar ya gina bangwaye masu ƙarfin kare shi daga jin yanayi irin wannan. Muryarshi can ƙasan maƙoshi yace:

“Saboda mun yi mishi sadaka….Saboda ya rasu Tariq…. Ya rasu…”

“Bai rasu ba!”

Tariq ya amsa yana tsugunnawa, ya riƙe kanshi tare da kurma wani irin ihu da ya sa Ashfaq runtse idanuwanshi, Yasir kuma ya saka hannuwanshi babu shiri ya rufe kunnuwanshi, kafin ya miƙe tsaye ya nufi inda Tariq ɗin yake tsugunne yana riƙe da kanshi da yake jin kamar zai tarwatse.

Tsugunnawa ya yi ya kama shi, duk da ƙoƙarin ture shin da Tariq ɗin yake yi, sosai ya sa ƙarfi ya riƙe shi, jikinshi ko’ina kyarma yake yi, idanuwanshi na wani kakkafewa da yadda jikinshi ke buƙatar ƙwayoyin da suka yi mugun sabawa dasu. Ashfaq buɗe idanuwanshi ya yi yana kallon su, zuciyarshi ta tsaya mishi waje ɗaya, duhun da ke cikin kanshi na yawatawa zuwa duk wani sassa na jikinshi. Bai san lokacin da rayuwa za ta yi mishi haske ba, na rana ɗaya ya sake jin haske cikin rayuwarshi abin ya gagara.

Lagos

“Mummy…Mummy…”

Zafira take jin ana kiranta sama-sama, buɗe idanuwanta ta yi, motsin da ta yi ya sa jikinta gaba ɗaya ɗaukar ɗumi, babu shiri ta buɗe idanuwanta gaba daya.  Yusayrah tagani da uniform a jikinta.

“Mummy yunwa nake ji, pasta aka dafa mana a makaranta.”

Kai Zafira ta ɗaga tana kallon agogon ɗakin, shida saura, kallon ta ta mayar kan Yusayrah da ke turo bakinta irin na Omeed.

“Sayrah har kun tashi?”

Gani ta yi ta nutsa tana kallon hannuwanta, kafin ta kai ɗan yatsa ɗaya tana taɓa shatin belt ɗin da ke kwance kan hannun Zafirar.

“Papi ya dake ki ko?”

Yusayrah ta tambaya da wani yanayi a muryarta da Zafira ba ta so, idanuwanta cike da hawaye ta yi saurin miƙewa tana faɗin:

“Zo mu je in zuba miki abinci… Nayi meatpie kuma.”

Bin bayanta Yusayrah ta yi, sai dai maimakon ta bi ta kitchen hanyar ɗakinta ta nufa.

“Ina za ki je kuma Sayrah?”

“Zan sake uniform ne Mummy.”

Ta amsa ba tare da ta juyo ba. Sauke numfashi Zafira ta yi ta nufi kitchen ɗin. Sai da ta ɗago hannunta don ta yi amfani da shi taji ya mata mugun nauyi, gashi ya kumbure; musamman yatsunta na tsakiya da gefe, don har naso suke yi saboda kumburi. Hannun hagu ta yi amfani da shi ta zuba wa Yusayrah abincin, ta zuba mata Meatpie ɗin guda biyu a waje daban, duk da ta san ba iya cinye biyun za ta yi ba. Shigowa kitchen ɗin ta yi ta saka doguwar riga ta material a jikinta. Inda taga plate kawai ta ƙarasa ta ɗauka, ko ta kan Meatpie ɗin ba ta bi ba ta wuce ta bar kitchen ɗin. Zafira ta san shatin belt ɗin da Yusayrah ta gani ne ya ɓata mata rai. A shekarun yarinyar takwas da ‘yan watanni tana fahimtar abubuwan da suka girmi shekarunta. Ta gode wa Allah da ba ta gidan ɗazun. Omeed ba damuwar shi bane ya jibgeta gaban Yusayrah, in ranshi ya ɓaci hankalin shi barin jikin shi yake yi. Falo ta fito ta zauna don ta san halin Yusayrah in ta gama fushin za ta nemeta. Da agogon ɗakin ta yi amfani wajen gane lokacin Sallah, don ba masallaci suke da shi a kusa da su ba. Ɗaki ta koma ta yi Sallah, sai da ta nemi Panadol da ba ta rabuwa dashi ta haɗiya don tasan dukan da Omeed ya yi mata zai saka mata zazzaɓi tukunna ta sake dawowa falo ta zauna. Kallo take amma sam hankalinta ba akai yake ba, ta kuma rasa tunanin da ya kamata ta yi, da ta tuna son zuwan da take gida sai gabanta ya yi mummunan faɗuwa, don zuwan ya fice daga ranta, dukan da ta sha ya sa ta ji ta haƙura. Omeed bai dawo gidan ba sai takwas da wani abu, don lokacin ma ta yi Isha’i. Da sallama ya shigo falon, sai da zuciyarta ta doka. Da sauri ta miƙe ta tarbe shi, rungume shi tayi, tana ji ya sumbaci saman kanta, kafin ya zame ta daga jikin shi.

“Sannu da gida…”

Ya faɗa yana mata murmushi tare sa hannu da shafar kuncinta.

“Fuskarki a kumbure…”

Murmushin takaici ta yi, yana faɗa mata fuskarta a kumbure kamar ba shi da alaƙa da kumburin fuskar. Ba ta amsa mishi ba, sanin Omeed ba kowace maganarshi take buƙatar amsa ba. Cikinta ya kai hannu yana shafawa.

“Kin ci abinci?”

Girgiza mishi kai ta yi.

“Me yasa?”

Ya buƙata yana kama hannunta da ya sa ta ihu ta ƙwace tare da riƙe shi, idanuwanta ya cika da hawaye saboda zugin da yatsun suke mata. Da sauri Omeed ya kai hannu zai kama nata, ta matsa baya tana girgiza mishi kai, tare da ɓoye hannunta baya.

“Me ya samu hannun, kawo in gani.”

Ya faɗa yana ƙoƙarin haɗe space ɗin da ke tsakanin su, Zafira kam ƙara matsawa ta yi nesa da shi. Kallonta ya yi fuskarshi babu alamar wasa.

“Ki zo in gani.”

Kai ta sake girgizawa wannan karon hawayenta na zubowa. Takalma Omeed ya cire ya shiga cikin falon sosai ya samu kujera ya zauna ya cire hular kanshi ya ajiye.

“Zafira zo…”

Tsaye ta yi.

“Kizo na ce ko!”

Ya faɗa a tsawace, babu shiri tana hawaye ta ƙarasa inda yake, hannunta ɓoye a bayanta. Riƙo ta ya yi ya zaunar da ita kan ƙafarshi ɗaya tare da sa hannu ya kamo nata da take ɓoyewa. Ranshi ya ji ya baci ganin yadda yatsunta suke a kumbure. Muryarshi can ƙasan maƙoshi yace:

“Garin ya? Ta yaya kika ji ciwo haka?”

Shiru ta yi hawaye na zubar mata, ba zatae iya jure wani dukan ba, kaɗan daga aikin Omeed ne ya sake tusa mata wani sabo.

“Ban faɗa miki ki dinga bi min kanki a hankali ba?”

Da sauri ta amsa da:

“Ka faɗa min…”

“Ta ya akai kika ji ciwo to? In ina son ganin ciwo a jikin ki zanjie miki da kaina…”

Ware mishi idanuwanta ta yi tana ƙoƙarin tarbe hawayen da ke sake son zubo mata. Idan ta faɗa mishi lokacin da yake dukanta ne ta ji laifin kanta zai koma, intay faɗa mishi faɗuwa tayi ma ba tsira ta yi ba. Har yanzun batai gane kan Omeed ko asalin abinda yake so daga wajenta. Hannunta ya sa cikin nashi yana dubawa sosai.

“Targaɗe ne a yatsunki har ukku…”

Yadda akai ya gane bai bata mamaki ba, duk da babu abinda ya haɗa Pilot da aikin kanshi. A zamansu abubuwan da ya sani ya daina bata mamaki, ya kuma koya mata yarda da shi ta ƙarfi da yaji.

“Zan gyara miki, ba zaki mjn ihu ba saboda ban aike ki jin ciwo ba, ban san me ya sa kike son ɓata minn rai ba…”

“Ka yi haƙuri.”

Ta tsinci kanta da faɗi, sumbatar gefen fuskarta ya yi da take jiƙe da hawaye.

“Na sani…”

Ya amsa yana gyara mata zama a kan cinyarshi, ƙafarshi ɗaya ya ɗaga ya danne nata ƙafafuwan da su.

“Karki min ihu Zafira…”

Kafin ya rufe baki ya damƙe hannunta ya soma jan yatsun, wani fitsari tajie yana shirin zubo mata, ga mamakinta azabar ba ta sa ihu ya kuɓce mata ba, sai hawaye da zufa datae hada, har ya gama, tukunna ya miƙe da ita riƙe a jikinshi. Bedroom ɗinsu ya ja ta ya zaunar da ita akan gado.

Da kanshi ya shiga toilet ya ɗauko ruwan zafi da towel ya gasa mata hannun da shi, kumburin har ya fara ragewa, ta kuma soma jin daɗin hannu.

“Sannu, ba kya jin magana. In ba dukan ki na yi ba hankalin ki ba ya kwanciya.”

Omeed yake faɗa yayin da yake ƙarasa gasa mata yatsun. Sai da ya tabbatar ya isa tukunna ya je ya zubda ruwan dayae ɗebo yan shanya towel ɗin. Sake zuwa ya yi ya kamo hannunta, da kanshi ya zubo musu abinci a kitchen shi da ita. Ba don tanajin yunwa take ci ba, sai don gudun tashin hankali.

Laifin ƙin cin abinci babbane a wajen Omeed, zai ce ko ba ta jin yunwa jikinta na buƙatar abinci, sam ba ya wasa da abinci da kula da lafiya. Da suka gama shi ya ɗauke plate ɗin. Al’amuran shi na rikitar da ita. Platforms da yawa takan shiga, irin su Inside Arewa, Jaruma Magazine, Open Diaries, tana cin karo da labarai da dama.

Mazan dake dukan matansu suna da yawa, amma babu namijin da ta ji kalar Omeed, babu macen da ta ji in mijinta ya dake ta yake kula da ita haka, kuma ba sa faɗan laifin da suka yi wa mazan. Omeed na faɗa mata laifin da ta yi mishi ya daketa, kuma har a zuciyarta tana jin wasu lokutan kamar ta cancanci duk wani duka da yake mata.

Jin ya taɓa mata fuska ya sa ta kallon shi.

“Ba na son tunani mai zurfi haka.”

Ya faɗa yana daƙuna mata fuska. Don a irin tunanin nan ne take yin na rabuwa da shi. Ko kadan ba ya son ƙwaƙwalwarta ta samu hutu ko nutsuwar da za ta yi tunanin wani abu mai zurfi.

“Sayrah fa?”

“Tana ɗakinta.”

Ta amsa mishi a taƙaice, kama hannunta ya yi suka nufi ɗakin Sayrah tare, bakin kofa suka tsaya, sai da ya ƙwanƙwasa tukunna, sakewa ya yi har sau uku tukunna ya tura haɗe da sallama a hankali. Ya ja hannun Zafira ciki. Kwance suka samu Yusayrah kan gado, idanuwanta a rufe da alamun bacci, kunnenta da earpiece.

Gefen gadon Omeed ya zauna, ya ja abin rufa ya lulluɓe Yusayrah, kafin a hankali ya zare earpiece ɗin da ke kunnenta ya dane ɗaga ta ya ciro Tablet ɗin da ta danne rabinta. Dannawa ya yi, murmushi ya ƙwace mishi ganin Karatun Qur’ani take saurare har bacci ya ɗauketa.

Addu’a ya yi mata, da za su fita daga ɗakin ya kashe mata wutar ɗakin tare da jan ƙofa, Yusayrah na jin jan ƙofar su ta buɗe idanuwanta. A kwance take dama tana sauraren ƙarin karatun da akai musu a Islamiyya da yammaci. Ta ji ƙwanƙwasa ƙofa, ta san sune, tun ba ta iya baccin ƙarya ba har ta koya, in ba ta son magana da su haka take yi, cikin duhun ta lalubo wayarta ta mayar da karatun ta sake gyara kwanciyarta.

*****

Ƙauyen Kinkiba

Bai taɓa sanin duk wani abu da yake ji akan mutanen da saɓani yakan haɗa shi da su ba tsana bace ba, ko kusa da tsana bai taɓa ba, sai da A-Tafida ya shigo rayuwar su. Cikin shekara huɗu babu abinda ya canza na daga yadda yake ji akan shi.

In akwai bai wuce yadda tsanar take ƙaruwa a duk rana ba. Inda za a ba shi zaɓi cilla bomb a duniyar A-Tafida ya tabbatar bazaie tsaya tunanin ko su waye bomb ɗin zai shafa da suke kusa ko cikin duniyar shi ba, in har zai tarwatse da A-Tafida ba tare da da na sani ba zai amince.

Yana jin yadda zuciyarshi ke girgiza har lokacin da ganin A-Tafida, bai san bai yi sallama ba, sai da ya ji Inna tace,

“Waye nan?”

Muryarshi na fitowa a hargitse yace,

“Inna ni ne.”

“Tawfiq har ka dawo… Ban ji sallamar ka bane shi ya sa.”

Inna ta amsa daga can cikin ɗakin.

“Yan nema, wato duk kiran da na yi sai da kuka bishi ko?”

Take ce wa su Hussaina da tun shigarsu gidan suka ruga ɗakin Inna suka bar Tawfiq tsaye a nan. Yanayin da yake ciki ya sa ya rasa abinda ya kamata ya yi.

“Inna Kawu ya mari wani.”

Hassan ya faɗi, da mamaki Inna ke kallon shi, yaron na da surutu, amma da wahalar gaske ya faɗi abinda bai faru ba. Kuma ta san zafin zuciyar Tawfiq.

“A ina?”

Ta tambaya.

“A waje…”

Hussain ya ba ta amsa, babu shiri Inna ta miƙe ta bar su a ɗakin ta fito waje, ganin Tawfiq ɗin tayir a tsaye ya yi zurfi cikin tunani, don kira huɗu ta yi mishi bai ma san ta yi ba, sai da ta taɓa shi tukunna.

“Tunanin me kake yi haka?”

Sauke numfashi ya yi, ta ina zai faɗa wa Inna A-Tafida ne ya tako ƙafarshi ƙofar gidan su, shekara huɗu yana kallo tana kokawa da warkewar ciwon da A-Tafida ya ji mata, kullum yake kallon yadda take jinya da fama da tabon ciwon. Ba zai yi sanadin buɗe mata shi ya koma sabo ba.

“Bakomai Inna.”

“Hmm… Hassan yace mun ka mari wani a waje.”

Runtse idanuwanshi Tawfiq ya yi ya buɗe su, Hassan da ta kira na sa zuciyarshi bugawa da sanin A-Tafida ya gan su, daga Hassan har Hussaina, ba kuma zai manta yanayin da ya gani a idanuwan shi ba kan yaran. Zufa ya ji tana tarar mishi a goshi da tafukan hannuwan shi.

“Tawfiq…”

Inna ta kira da damuwa bayyane a muryarta.

“Surutun Hassan ne kawai Inna.”

Tawfiq ya faɗa, a kunnuwanshi ma yanajin yadda muryarshi ta fito da ƙarya ƙarara, balle kuma Inna da duk wani motsin su tana kula da shi, sai dai in ta ƙyale ka kawai.

“Hmm… Don Allah dai a dinga kai zuciya nesa Tawfiq… Ka dinga saka salama a ranka.”

“In shaa Allahu…”

Ya faɗa a sanyaye.

“Tuwonka na ɗaki na sa an kai maka tun ɗazu.” 

“Yanzu ma zan shiga ɗakin.”

Ya amsa tare da juyawa don bai son wata magana ta sake haɗa su da Inna. Sai dai bai kai da ƙarasawa ɗakin shi ba, Baba ya shigo gidan da sallamar da Tawfiq ɗin ya amsa.

“Tawfiq… Kai da wa kuka yi rigima?”

Lumshe idanuwanshi Tawfiq ya yi buɗe su, ba Kinkiba ya tsana ba, yana alfahari da asalin shi, yana kuma son ƙauyen shi, mutanen cikin shi ne suke da matsala, da yadda bakin su ba ya shiru musamman kan abinda bai shafe su ba. Yanzun haka idan akace su Salele zuwa suka yi har inda Baba yake suka faɗa mai ba a musu. Juyowa Tawfiq ya yi, sai da ya fara kallo yaga Inna ta koma ɗaki, tukunna muryarshi can ƙasa yace,

“Yanzu Baba har an faɗa maka…”

“Au damuwarka an faɗa min ne, ba zuciyarka da ba zaka sa ma salama ba.”

Ranshi Tawfiq ya ji ya sake jagulewa.

“Me yasa duk wani abu sai ku yanke min hukunci ba za ku tsaya ku ji nawa ɓangaren ba?”

Ɗan jim Baba ya yi yana tauna maganar Tawfiq ɗin, kafin cikin taushin murya yace,

“Saurin fushinka ne yake jawo hakan, sun ce rako shi suka yi yana neman mai gyara…”

Jingina bayanshi Tawfiq ya yi a jikin bangon ɗakin nashi, fuskarshi ɗauke da damuwa, muryarshi da yanayi mai nauyi yace,

“A-Tafida ne Baba…”

Kiran A-Tafida kawai da Tawfiq yayi yana jin yadda yanayin komai ya yi shiru, har iskar da ke buso shi ya ji ta bari, yana nazarin fuskar Baba da shekarun shi suka sake nunawa akan fuskarshi lokaci ɗaya, muryarshi da nisantaccen yanayi yace,

“A-Tafida ɗin ya zo ƙofar gidan nan? Ƙofar gidan nan fa Tawfiq? Me ya…”

Ƙarar faɗuwar abu da suka ji ne ya katse wa Baba abinda yake faɗa ya kuma sa su duka biyun juyawa inda suka ji ƙarar. Nuwaira suka gani tsaye, da alama daga banɗaki ta fito, manyan idanuwanta take warewa akan Baba da Tawfiq da suke kallonta cike da tashin hankali. Takowa ta yi tana zuwa inda suke, muryarta na rawa take kallon fuskokin su.

“Yaya…”

Nuwaira ta faɗa, Tawfiq na jin yadda a kalma ɗaya bugun da zuciyarta yake yi ya fito ta ciki, yana jin kamar ya koma mintinan da suka wuce ya goge abinda kunnuwanta suka ji, cikin idanuwa yake kallonta yana son buɗe mata zuciyarshi ba tare da ya furta komai ba. Yana son ta ga yadda yake da na sanin abinda ta ji, yadda yake roƙonta kar ta bari ya fama mata ciwon da ya san take fifitawa tsawon shekaru huɗu. Yana kuma ganin yadda itama take roƙon shi da nata idanuwan da hawaye ke taruwa ciki da ya faɗa mata ba ta ji A-Tafida a bakin shi ba.

Ganin ya yi shiru ya sa Nuwaira girgiza kanta.

“Bai tako ƙafarshi ƙofar gidan nan ba… Yaya ka ce min bai zo ba….”

Sadda kanshi ƙasa Tawfiq ya yi, ciwon da yake ji a muryarta ya sa zuciyarshi ɗaukar dumi. Cikin sabon tashin hankali Nuwaira ta maida dubanta kan Baba.

“Baba ka ce min ko kusa da Kinkiba bai zo ba…”

Shima shirun ya yi, wani irin numfashi Nuwaira ta ja, duniyar na taruwa tana danne ta waje ɗaya. Wani ƙaramin yakie ya soma faruwa a cikin zuciyarta, ɗan dai-daiton da ta samu yana hargitsewa.

‘A-Tafida…’

Wata murya ta faɗa cikin kanta da ta sa ta runtse idanuwanta tana jan wani wahaltaccen numfashi.

‘Kina da kyau… Idanuwanki sunfi komai jan hankali na. Yadda kike buɗe su duk idan za ki yi magana…’

Muryarshi ta diro mata, girgiza kai take yi, hawaye masu ɗumi na zubo mata, wani irin tashin hankali marar misaltuwa na ziyararta. Ganin yadda jikinta ke ɓari ya sa Tawfiq ƙarasawa inda take.

“Nuwaira ya tafi…Ya tafi wallahi…”

Wani irin kuka take tana girgiza kanta, ba ta son muryarshi da take ji cikin kanta, ganin fuskarshi a jikin ta su Hassan ya isheta tashin hankali har ƙarshen rayuwarta. Ba sai ta haɗa da jin muryarshi cikin kanta ba.

“Bai daɗe da daina mun kutse cikin mafarkina ba Yaya… Kacer min bai zo ba.”

Nuwaira take faɗa muryarta na karyewa da kukan da take yi. Hannunta Tawfiq ya kama ya nufi ɗakin Inna da ita, da ganin su da yanayin da suke ciki ya sa ta miƙewa, jikinta Nuwaira ta faɗa ta fashe da wani irin kuka. Sosai Inna ta riƙe Nuwaira ganin kukan da take yi da yadda jikinta ke ɓari. Tawfiq ta kalla da ido take tambayarshi ko me yake faruwa. Da tsanar A-Tafida dake taso mishi yace,

“Sallamar da aka yi da ni ɗazu, su Salele ne suka rako wani in mai gyaran mota… A-Tafida ne.”

“Auzubillahi…”

Inna ta faɗa da sauri tana sake riƙe Nuwaira kamar mai son ɓoye ga daga sunan A-Tafida ɗin da Tawfiq ya furta. Juyawa ya yi ba tare da ya sake cewa komai ba, haka ya bar Baba da yake tsaye ya shige ɗaki. Yana jin daɗin yadda ya samu ya yi Sallar Isha’i.

Ko ta kan tuwon da Inna ta ce mishi ta sa an kai mishi ɗaki bai yi ba, don ba shi bane a kanshi, ko yunwar ba ya ji. Kwanciya ya yi kan gadon ƙarfen da ke ɗakin. Zuciyarshi na ƙara girmama da tsanar A-Tafida, da yadda sunanshi kawai yake da tasirin hargitsa musu zaman lafiya har haka. Lumshe idanuwanshi ya yi.

‘Dukkan tashin hankali Allah ya haɗa rayuwarka da shi A-Tafida, yadda ka hargitsa mana rayuwar mu, Allah ya hargitsa maka taka.’

Itace addu’ar da Tawfiq yake maimaitawa har bacci ya ɗauke shi, cike da mafarkin A-Tafida.

Abuja

An yi wa Tasneem gwaje-gwaje da yawa, tun Rafiq na ƙirgawa har ya bari, in akwai abin so a asibiti yadda King’s ke kula da marassa lafiyar su yake so. Duka gidansu nan suke da kati, Tasneem ma a ƙasan sunan Mustafa Shettima ya buɗe mata kati. Yana jin nisan da ta yi wa zuciyar shi da kuma kusancin da take dashie a lokaci ɗaya. Faɗa musu da akai za su jira Awa ɗaya saboda wasu result ɗin ne ya sa Rafiq ce wa Tasneem,

“Zaki jira anan inje wajen su Nuri ko za ki iya mu tafi tare.”

“Zan iya.”

Ta amsa mishi da sauri, hannunshi ya miƙa mata, ba ta yi musu ba ta sa nata ya taimaka mata ta miƙe, ɓangaren suka bari gaba ɗaya suka nufi wani waje. Nazarin asibitin Tasneem take yi, tunda take a rayuwarta ba ta za ta a Nigeria akwai asibiti me kyau haka ba. Tana can tana kalle kalle sai gani tai Rafiq ya tsaya da su a bakin ƙofar wani ɗaki, ya tura da sallama. Ɗaki ne babba sosai, kuma gado ɗaya ne a ciki dake nuna alamar Fawzan ne kawai a ɗakin. Har da kujerun cushion manya manya. Sai kuma na robobi a ɗakin.

Hannunta da ta ji Rafiq ya saki ya sa ta maida hankalinta kan su Nuri. A hoto kawai take ganin matar, yaune ranar farko da ta fara ganinta. Sai ta tsinci kanta da jin kunyar Nuri sosai, kanta a ƙasa suka gaisa tana tambayar mai jiki.

Kujera Rafiq yaja mata, ta karɓa ta zauna.

“Mai jiki da sauqi… Ya naki jikin? Har kun ga likita?”

“Mun gani fa… Kin san gwaje-gwajen su, sai nan da awa ɗaya za mu koma.”

Rafiq ya amsa ya kuma ɗora da,

“Bai tashi ba har yanzu?”
Ya ƙarasa gefen gadon Fawzan ya zauna, yajie daɗin ganin yana numfashi da kanshi ba da taimakon inji ba. Kafin Nuri ta amsa Rafiq yace,

“Aroob bacci ake?”

Ya bi inda take kwance kan kujera da kallo.

“Ko runtse ba ta yi ba jiya…”

“Kema haka Nuri… Kina buƙatar hutawa. Da kinje gida sai in tsaya da shi.”

Girgiza kai Nuri ta yi.

“A’a fa, ga aikinka, ga kuma matarka kaima ba lafiya…”

Ɗan murmushi Rafiq ya yi yana sadda kanshi ƙasa. Duk da murmushin na ‘yan daƙiƙu ne, kafin ya ɓace Tasneem ta ganshi, ta ƙasan idonta take kallon Rafiq ɗin tunda ya zauna, muryarshi take sauraro, tana mamakin yadda za ka iya kewar muryar wani har haka. Ɗan giccin murmushin da ya yi yasa zuciyarta matsewa a ƙirjinta da yadda ta jima ba ta ga fara’ar shi ba. Zafi ƙirjinta ya soma yi, hakan ya sa tarin da ta soma gajiya da shi ya sarƙeta. Da sauri Nuri ta tashi ta ɗauko ruwa a roba ta buɗe ta miƙa wa Tasneem ɗin, don a zatonta ko sarƙewa ta yi.

Ina numfashinta da take kokawa da shi ya sa ko jinsu ba ta yi, so take ko yayane iskar da take shaƙa ta kai cikin ƙirjinta. Dafa mata kafaɗa Nuri ta yi tana ta mata sannu. Rafiq kam yana tsaye inda yake, duk da zuciyarshi na mishi ihu ya ƙarasa ya ga Tasneem ɗin, kunyar Nuri ba za ta barshi ba.

A hankali tarin ke tsagaita mata, riƙo hannunta Nuri ta yi tana faɗin,

“Zo ki ɗan kwanta kafin lokacin yayi, sannu…”

Kallonta Tasneem tayie idanuwanta cike da hawaye. Ta manta rabon da wani ya yi mata magana cike da kulawa haka. Kan ɗayan cushion ɗin Nuri ta ja ta ta kwanta, ta zauna a gefenta tana mata sannu, hannunta da ta ji da lema-lema da ta riƙe na Tasneem ɗin ne ya sa ta kallo. Cikin tashin hankali Nuri ta ware idanuwa ganin tsilli-tsillin abu kamar jini, sosai take duba hannun ta, kafin ta kamo na Tasneem ta ware tafin hannun, jini ne a jiki. Kallon Rafiq Nuri ta yi ta rasa me za ta ce, ko wata biyu ba su yi da ɗauko ‘yar mutane ba, tana tarin jini, abin ya tsorata ta.

“Rafiq…Wanda wuro gullami bikka dondiwona (Karka ce mun jiya ne ba ta da lafiya)”

Nuri ta faɗa da yanayi mai nauyi a muryarta. Ba ta son mishi faɗa a gaban Tasneem ɗin, shi ya sa ta sake yare take tambayar shi da Kanuri, da idanuwanta take tuhumar shi da me yake tuntuni bai kula da Tasneem ɗin ba ta da lafiya ba. Don ko yanayin rashin ƙarfinta ka kalla ka san ciwon ba na jiya bane. Ɗan daƙuna mata fuska ya yi yana turo laɓɓanshi a hankali da ke fassara shi fa bai yi komai ba.

“Bikko nungo (Jiya na sani).”

Ya amsa, da kanshi yana jin rashin kyautawarshi ba sai ya ƙara da na Nuri ba.

“Chistu halnum guyi Rafiq (Rashin kulawa ba halinka bane Rafiq).”

Nuri ta faɗa kafin ta miƙe zuwa toilet. Hannunta ta wanke da Dettol, ta jiƙo towel ta zo tana goge wa Tasneem nata hannuwan.

“Ciskukin (Zan kiyaye).”

Rafiq ya faɗa can ƙasa, bayan ta fito. Ko ta ji ba ta kula shi ba. Hankalinta duka na kan Tasneem.

“Na gode…”

Tasneem ɗin ta faɗa a raunane. Murmushi Nuri ta yi.

“Karki damu… Ki ɗauke ni kamar mamanki…”

Wannan karon Tasneem ce ta yi guntun murmushi mai cike da takaici, yanayin Nuri kawai banda kuɗin da gayun ya nuna akwai nisa mai tsayi tsakaninta da Ummi. A kirkin da ta mata na ‘yan mintinan nan ya nuna cewa ita da Ummi ba za su taɓa zama a inuwa ɗaya ba. Sannan Tasneem ba ta buƙatar Ummin da kanta balle ta ɗauki wata kamar ita, za ta ɗauki Nuri kamar Maman Rafiq. Sai da ta saka Mama take jinjina Nuri da suke kiranta da shi. Ta sha nufin ta tambayi Rafiq sai ta manta, yanzun kuwa ba ta jin zai amsa ta, ko za ta iya samun kuzarin tambayar shi kuwa.

*****

Baccin wahala ne ya ɗauke ta, can sai Nuri ta tashe ta cewar lokaci ya cika. Miƙewa Tasneem take shirin yi, Nuri ta sake taimaka mata ta tashi tana faɗin:

“Rafiq ka zo ka taimaka mata mana, kana gani ba ta da ƙwarin kirki.”

Kanshi a ƙasa ya ƙaraso ya kama hannun Tasneem, fuskarshi da ta yi ja ta ɗan kalla, kunyarshi ba za ta daina ba ta mamaki ba.

“In kun gama ku wuce gida ta huta…”

Buɗe baki Rafiq ya yi zai yi gardama, don yana son dawowa ya ga Fawzan, Nuri ta katse shi.

“Na sani… In ya tashi zan kiraka ka, ko kana gida sai ka dawo.”

Kai ya jinjina mata, ya kama Tasneem ɗin suka fita. Ƙarfin hali kawai take na tafiya, amma jikinta babu ƙarfi ko kaɗan , har suka ƙarasa office ɗin likitan da suka fita ɗazu. Sai da ta sauke numfashi da ta zauna saboda gajiyar da ta yi. Sosai likitan yake kallon Rafiq da yanayin da ba ya wa Rafiq ɗin daɗi, tukunna ya mayar da hankalin shi kan Tasneem.

“Tun yaushe kike jin tsaitsayawar numfashi? Da kasala?”

“Yafi wata uku.”

Ta amsa a sanyaye, ta sa Rafiq juyawa ya kalleta, duk da idanuwanshi dake mata yawo a jiki, hakan bai sa ta ɗago ba, tambayoyi ya ci gaba da mata tana amsa shi dai-dai saninta. Kafin ya tattara takardun da ke gabanshi ya buɗe wani file ya saka su. Kafin ya maida hankalin shi gaba ɗaya kan Rafiq.

“Matarka ce ko?”

Daƙuna fuska Rafiq ya yi kafin a hankali ya ɗaga mishi kai.

“To, cikin kashi ɗari, takai mataki casa’in na gab da kamuwa da abinda muke kira CHF, wato congestive heart failure…duka alamomi masu ƙarfi sun nuna, abubuwa da yawa kan jawo hakan, a nata case din jininta ya hau fiye da misali…”

Kallon shi kawai Rafiq yake tunda ya soma maganganun da yake ji suna shiga zuciyarshi da tafasa duk wani jini da yake yawo a jikinshi. Ta yaya za a ce heart failure na gab da kama Tasneem, hawan jini, a ina ta same shi? Bai gama tunanin da ƙwaƙwalwar shi take sonyi ba likitan ya sake jefa shi yanayi da faɗin:

“Kuma tana ɗauke da ciki sati huɗu…”

Daga nan bai sake jin abinda likitan yake faɗa ba, ya dai ga bakin shi na motsi, amma babu abinda yake isowa kunnuwan Rafiq. Ciki sati huɗu, baya son inda zuciyarshi take kai shi saboda yadda zuciyarshi ke tafasa. Dafe kai yayi da hannuwanshi duka biyun. Tasneem kuwa tunda ya fara magana babu abinda ya bata mamaki, daga hawan jinin har ciwon zuciyar, amma yana kiran kalmar ciki sai da ta ji zuciyarta ta yi wani irin tsalle kamar za ta fito waje. Da sauri ta kai hannu ta dafa cikinta tare da shafa shi ta lumshe ido.

Wata saƙa na ƙulluwa a zuciyarta da ba ta taɓa zaton akwai ta ba, wani irin kusanci take ji da cikinta ta fannin da ba ta zata ba. Akwai ɓangaren Rafiq a waje fiye da zuciyarta, akwai ɗan ƙaramin Rafiq a cikinta. Ko da ta ga period ɗinta ya wuce lokaci ba ta kawo komai a ranta ba, don sosai yakan mata haka. Rabonta da shi tun sati biyu kafin bikinsu da Rafiq ɗin.

Ba ta san hawaye sun zubo mata ba sai da ta ji saukar su akan kuncinta, hannu ta sa ta share hawayen, wasu na sake zubo mata haɗe da murmushi mai sauti, ta manta rabon da ta yi murmushin da ya fito daga zuciyarta haka. Sosai take shafa cikinta hawaye na zubar mata, ta sa ɗayan hannunta tana goge su.

Kallonta Rafiq yake yi, yana ganin farin ciki bayyane a fuskarta, sai dai duniya daban-daban suke a yanzu, yana akasin wadda take ciki, kokawa yake ta gaske da zuciyarshi kar shakku ya ɗarsu a ciki, kar ta ja mishi ƙarewar auren shi da Tasneem ba tare da shiri ba. Bai san lokacin da ya kamo hannunta yana sumbata ba.

Kusanci yake so da zai janye zuciyarshi daga inda take son kai shi, sosai yake dumtse hannu Tasneem ɗin. Ta kasa kallon shi, ba ta son abinda zai janye zuciyarta daga alaƙar da ke tsakanin ta da cikinta.

“Wai kuna jina kuwa?”

Likitan ya faɗa ganin sai surutu yake yi shi kaɗai, daga Rafiq ɗin har Tasneem sun ma manta da zaman shi a office ɗin, muryar Rafiq can ƙasan maƙoshi ba tare da ya kalle shi ba yace,

“Ka yi aikinka kawai…ka rubuta abinda za ka rubuta.”

Girgiza kai Likitan yayi kawai. Ya ɗauka shekarun da ya ɗauka yana aiki babu abinda zai ba shi mamaki, sai ga Rafiq da Tasneem a gabanshi.

“Dole sai kun saurare ni zanyi aiki na.”

Ba tare da su duka sun so ba suka maida hankulansu kan Likitan, bayanin dokokin magunguna da kuma wasu daban ya shiga shimfiɗa musu. Babu doka ɗaya da Rafiq bai riƙe ba. Nan office ɗin suka zauna, Likitan ya yi waya aka zo aka amshi takardar magungunan da aka rubuta musu.

Aka siyo aka kawo, ya basu zaɓi ko su riƙe Tasneem ɗin kwana ɗaya ko kuma gobe su dawo. Kafin Rafiq ya amsa ta ce ba za ta kwana ba. Ta samu babban dalili na kula da kanta yanzun. Hannunta riqe cikin na Rafiq suka fita daga asibitin. Tana jinshi ya yi waya da Nuri ya faɗa mata sun wuce.

*****

Suna shiga gida, a falo ta cire Hijab ɗinta ta zauna, tana jin wani sabon ƙarfi, tsaye Rafiq ya yi yana kai-kawo a falon, ya kasa zama, ƙarfin mulkin zuciyarshi na soma ƙwacewa daga hannun shi, kallon Tasneem ya yi, ya maida hankalin shi kan cikinta.

“Cikina ne a jikin ki ko ba nawa ba Tasneem?”

Rafiq ya jefe ta da tambayar da ta sa zuciyarta tsayuwar wucin gadi. Miƙewa tsaye ta yi a hankali tana takawa ta ƙarasa inda yake ta yi tsaye tana kallon shi da idanuwanta da suka bushe wannan karon, sun sa ta san zubar hawaye sauƙi ne a yanayoyi daban-daban. Hannuwanta tasa duk biyun ta hankaɗe ƙirjin Rafiq da ko motsi bai yi ba, ta ba wata irin ƙara da ta fito tun daga zuciyarta damar fitowa, wadda sautinta na raguwa kagin ta ƙaraso maƙoshinta zuwa kan harshenta, ko’ina ta samu a jikin Rafiq take kai wa duka, me yasa zai mata wannan tambayar?

Bai ko motsa ba, barinta ya yi ta ci gaba da kai mishi duka, tun tana yi da ƙarfi har ta soma rage ƙarfin dukan, tukunna ya kama hannuwanta yana ƙoƙarin riƙe ta a jikinshi tana ƙwacewa, ƙarfi ya sa ya matse ta yana son ta ji yadda zuciyarshi ke ciwo da tambayar da ya yi mata, da ta ba shi dalilin yi mata tambayar. Sai a lokacin hawayenta ya soma zuba, wani irin kuka take yi har jikinta ke kyarma.

“Me ya sa za kai min tambayar nan….laifina babbane a wajenka na sani… Na daɗe ban ji farin ciki a raina ba… Na manta yadda yake sai yau… Me yasa zaka ƙwace min? Hukuncin da kake min bai isa ba?”

Take tambaya tana ci gaba da wani irin kuka. Riƙe ta ya yi, ta zame daga jikinshi tare da durƙushewa ƙasa, binta ya yi ya riƙo ta.

“Neem…. Please…. Ina son sani ne… Ina son sani, zuciyata ba za ta nutsu ba in ba ki tabbatar min ba… Cikina ne?”

Ya sake tambaya yana sa ta sake rushewa da wani irin kuka, tana jin indai da haske ko yaya ne a lahirarta gara mutuwa da rayuwar da take ciki. Da komai da take da shi take jin dama tana da ikon komawa baya ta sake wasu cikin zaɓukan da ta yi.

“Kuskure… Kuskure ɗaya na yi… Shi ne zai zame min tabo har ƙarshen rayuwa… Shinee yasa kake min tambayar nan Sugar…”

Tasneem ta faɗa numfashin ta na sarƙewa. Da zai samu hawaye su zubar mishi da ya samu sauƙin abinda yake ji.

“Ba laifina bane Neem… Ke kika kawomu wajen nan.”

Jinjina mishi kai ta yi tana ɗagowa daga jikinshi tare da saka hannu ta goge fuskarta.

‘Ka yi ƙoƙari ta rage damuwa.’

Maganar Likita ta ɗazun ta dawo mishi, bai san yadda zai sa ta rage damuwa ba. Kallonta kawai shi yana jefa shi cikin damuwa. Gyara zaman shi ya yi yana kallon yadda take goge hawaye wasu na zubar mata.

“Ki faɗa min … Ya akai kika kawo mu nan… Ina son sani.”

Kallon Rafiq ta yi da rinannun idanuwanta. Da gaske yana son sani, ta gani a fuskarshi, yana son jin yadda akai rayuwa ta kawota inda take yanzu, da yadda akai ta janyo shi suke tsaye tare. Numfashi mai nauyi ta ja tana saukewa a hankali.

Next >>

How many stars will you give this story?

Click to rate it!

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Share the story on social media.

1 thought on “Alkalamin Kaddara 1 | Babi Na Uku”

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×