Zaman shi yai a masallaci har yai isha'i tukunna, har tsoron fitowa yake daga masallacin don yasan zai rasa nutsuwar da ya samu a cikin shi. Dole ta sa shi fitowa don cikin shi wayam yake jin shi. Bai samu kowa a babban falon ba, don haka ya wuce kitchen ɗin ƙasan, don yasan nan ne yake da tabbacin zai samu abinda zai ci.
Shiga ya yi yana waige-waige, bai ga alamun komai ba, har leƙowa ya yi ko zai ga giccin ɗaya daga cikin masu aikin gidan, amma bai ga kowa ba. Don bai san. . .