Yana zuwa gida ya ɗauko ɗaya wayarshi da ya kashe yana kunnawa, sabuwar ya kashe ya ajiye sai kuma ranar da amfaninta ya tashi. Yana buɗewa saƙonnin Samira ne suka fara shigowa sun fi talatin, sannan wasu saƙonnin daban, bai buɗe ko ɗaya ba. Lambar Daddy ya kira, bugun farko ya ɗaga da faɗin,
"Ka gama fushin kenan..."
Dariya Rafiq ya yi, yana ganin yarinta cikin abinda ya yi, akan Daddy zuciyarshi ta riga ta gama bushewa kuma, sai yanzun da ya kira shi yaga da wahala in akwai wani abu da zai ƙara. . .
Muna jin Dadi buk Dinan