Mutane da yawa da kanyi magana kan aure, suna mantawa su yi magana kan nutsuwar da ke tare da shi, da yadda kake jin kamar wani ɓangare ne da baka san baya tare da kai ba ka samu. Yanayin da yake jinshi a satika biyun nan ba zai misaltu ba, kusan komai tare suke yi da Samira, ko fita zai yi sai ya ce ta raka shi. Saidai me, abinda baisan yana da shi bane ya bayyana, wani irin zafin kishi daya saka shi fara addu'ar neman sauƙin shi.
Ranar da ta kasance safiyar Monday ce, zai. . .