Imaan, kamar yadda suke kiranta saboda sunan Nuri da ta ci, in har jariri na fahimtar abubuwa zata fara gane yadda take da gata, take kuma zagaye da mutanen da ke ƙaunarta kamar rai, daga sutura da sai dai a bayar da wasu don ba ma za'a samu a saka mata ba tunda ba zata dawwama a jaririya ba zuwa kan kulawa.
Kyawun yarinyar da girman da take da shi kamar ba 'yar wata biyu ba yake sata shiga ran mutane da wuri, Nuri kullum sai ta aiko Aroob da driver an ɗauketa an kai mata ita, haka. . .