"Kai fa ka ce za ka barni, ko bikin Yaya Rafiq banje ba... Haba don Allah."
Zafira ta ƙarasa maganar tana jin hawayen baƙin ciki na cika mata idanuwa. Musamman yadda Omeed ɗin ke ɗaura agogo a hannun shi kamar bai tarwatsa mata farin cikin da ta yi wata ɗaya da kwanaki tana tarawa ba.
"Yanzun kuma na fasa, ko ban isa ba?"
Ya buƙata ba tare da ya juyo ba, asali ma hular shi ya ɗauka yana karyawa. Sannan ya zo ta gaban Zafira da ke zaune a bakin tanƙamemen gadon ɗakin ya ɗauki daya daga. . .