Shopping Cart

Close

No products in the cart.

alkalamin kaddara 2 by lubna sufyan

Alkalamin Kaddara 2 | Babi Na Talatin Da Takwas 

<< Previous

“Ka yi haƙuri Rafiq…na biyewa son zuciyata, don Allah ka yafe min, bana so mu tsaya a gaban Ubangiji da kai, ka yafe min tun yanzun ko zan ji da sauran zunubai na…” 

Yafindo take faɗi tana jin ƙirjinta kamar zai buɗe saboda ciwon da yake mata. Kallon ta Rafiq yake yi, ya rasa abinda yake son ce mata, ko ya kamata yace mata, tunda yasan basu Nuri suka haife shi ba bai yi wani tunani kan asalin shi ba, bayajin ko yayi tunani zai hango fitowa ta fuskar da Yafindo ta zayyana mishi. Dauɗa yake ji a duka jikin shi, dauɗar da baya tunanin akwai sabulu da ruwan da zasu taɓa wanke mishi ita. 

“Yaya…”

Aroob ta kira shi cikin tashin hankalin, ganin yanda ko motsi baya yi, Fawzan da Zafira kuka suke tunda Yafindo ta fara magana, don Zafira ita ta koma lallashin Fawzan, ya rasa ta yadda zai tsaida hawayen shi. Duk addu’ar da tazo zuciyar shi yinta yake ko za su farka su samu abinda yake faruwa yanzun mafarkine mai muni, ba komai yake saka shi kuka ba sai Rafiq, tausayin Rafiq ɗin yake ji yana ratsa shi har cikin ƙasusuwan shi. Laifin da Yafindo taima Rafiq ɗin mai girma ne, tabo ne tai mishi da rashin laifin da bashi da shi akan hakan ba zai sa ya ɓace ba. 

“Idan na ce kin cuce shi kalaman sun yi kaɗan su ɗauki girman laifin da kika yi… da zan iya komawa in goge ranar daya ganki wallahi da na yi.”

Fawzan yake faɗi yana kallon Yafindo da kukan da take baya komai banda ƙara mishi haushin ta, ba ita ya kamata ta yi kuka ba, Rafiq ne ya kamata ya yi kuka sai dai yana zaune har lokacin ko motsi ma baiyi ba. 

“Fawzan…”

Daddy ya kira cike da kashedi, miƙewa Fawzan ya yi daga ɗakin ya wuce ya haura sama. Rafiq kam gyara zaman shi ya yi yana kwantar da kanshi a jikin Nuri sosai, yana jin in ya yi wani abu banda hakan zuciyar shi ta yi motsi fashewa zata yi. Baisan me suka ci gaba da faɗi ba, ya dai ga su Yafindo sun tashi daga falon don ta gefen shi suka wuce, kafin a hankali kowa da kowa ya bar wajen daga shi sai Nuri da ta ɗaga kanshi daga jikinta tana saukowa ƙasa kan kafet ɗin, zame jikin shi Rafiq yayi yana tayar da kanshi da cinyar Nuri tare da gyara kwanciyar shi sosai. 

“Idan na yi wani tunani zuciyata zata fashe Nuri, ina jin ta a ƙirjina… Me ya kamata in yi?” 

Ya tambaya muryar shi cike da wani irin rauni da bata taɓa ji ba, hawayen da ke son zubo mata ta mayar, ba zata yi kuka ba, don ba kukanta Rafiq yake buƙata ba. Kanshi ta shafa a hankali. 

“Karka yi tunanin komai, ina nan, zan kareka daga duk wani abu da yake ƙarƙashin iko na, Allah zai mana sauran…ina ƙaunarka, ka san hakan?” 

Wani irin numfashi ya sauke. 

“Kin ji asalina Nuri, bata hanyar kirki aka sameni ba, ni ba ɗan…” 

Hannu Nuri ta sa tana rufe mishi baki. 

“Kar in sake jin maganar nan a bakinka, in har baka so raina ya ɓaci kar in sake jin maganar nan a bakinka Rafiq… Ni da Daddy ne iyayenka, kai ɗa ne kamar yadda su Fawzan suke ‘ya’ya. Ina sonka fiye da yadda…” 

Shiru ya yi wasu hawaye na bin gefen fuskar shi, kuka yake har jikin shi ke ɓari duk da babu sauti ko ɗaya da ya fito daga bakin shi, amma kuka yake sosai sosai. 

“Kai ɗa ne kamar kowa Rafiq…ina ƙaunarka sosai, kai ɗa ne kamar kowa…” 

Nuri take maimaita mishi tana riƙe hannun shi, don kukan da yake yasa ta kuka itama, wani irin ciwo yake ji a zuciyar shi marar misaltuwa, zuwa yanzun ba kukan cewar su Nuri ba iyayen shi bane yake yi, don sun nuna mishi babu abinda ya isa ya canza hakan, kukan asalin shi yake, kukan dauɗar da Yafindo ta sa zata ci gaba da bin shi har ƙarshen rayuwar shi yake yi, kukan baƙin tabon da ta yi mishi yake yi, baisan iya lokacin da suka ɗauka a haka shi da Nuri ba, tun yana jin muryarta tana faɗa mishi yadda shi ɗa ne kamar kowa, yadda take son shi har ya daina ji saboda wani irin wahaltaccen bacci da ya ɗauke shi.

Kano

Tunda ya shiga gida yake jin zuciyar shi ta mishi nauyi, ko abinci da ya shiga kitchen ya zuba a nan ya tsakuri cokali huɗu ya mayar yana rufewa. Har ɗakin shi ya koma ya kwanta ko zai samu bacci amma hakan ya gagara. Zuciyar shi mintsinin shi take da ya je ya gaya ma Ammi abinda yake ranshi, saboda Nuwaira ta mishi tsaye, tausayin halin da rayuwarta take ciki ya hana shi sukuni tunda ya ji, baya son rashin adalci a rayuwar shi. Miƙewa yayi yana fita falon, Ammi ya gani kwance kan kujera idanuwanta a lumshe, gefen kujerar ya zauna yana faɗin, 

“Ammi zan auri Nuwaira…” 

Wata irin miƙewa ta yi baccin da take ji na sakinta gaba ɗaya. Aslam take kallo kamar ya samu taɓin hankali, kafin ta murza idanuwanta tana son tabbatar da ba mafarki take ba, wannan karon cikin idanuwa ya kalle ta. 

“Kin ji, zan aure ta…”

Ya sake faɗi, ƙafafuwan ta Ammi ta sauko da su daga kan kujerar tana gyara zamanta sosai. 

“Me kake ce min Aslam?”

Cikin idanuwa ya kalleta ya maimaita maganar yana sa ta girgiza mishi kai cikin wani tashin hankali. 

“Me yasa?”

Aslam ya buƙata, bata da wani ƙwaƙƙwaran dalili, kawai ba zai aureta ba ne, bata ga me zai da Nuwaira ga dubban ‘yan mata nan a gari ba. 

“In dai babu wani dalili zan ma Baba magana, in kun koma gobe in shaa Allah yai min maganar auren ta a wajen iyayen ta.” 

Runtsa idanuwan ta Ammi tayi tana buɗe su da faɗin, 

“Bansan me ya shiga kanka ba Aslam, amman ba zaka auri yarinyar nan ba. Ta maka tsufa, kuma bata dace da kai ba. Ga mata nan kala-kala ka zaɓi ɗaya ka kawo banda wannan yarinyar…” 

“Ammi ita ɗin dai nake so.”

Innalillahi wa inna ilaihir raji’un Ammi ta furta cikin zuciyarta, don batasan me ya shiga kan Aslam ɗin ba, duk cikin yaranta shi ne bai taɓa mata musu ba, ko me zata ce sai dai ya amsa ta da to, amma yau cikin idanuwa yake kallon ta yana mata musu akan wannan ‘yar ƙauyen. 

“Ba za ka aure ta ba. Na gama magana, ka tashi ka bani waje. Don ubanka kai baka da hankali ne? Meye za kai da wata Nuwaira ko bata girmeka ba shekarunku zai kusan zuwa ɗaya. Altaaf ma bai ce zai aure ta ba sai kai?” 

Numfashi Aslam ya ja yana sauke shi, da wani murmushi a fuskar shi yake kallon Ammi. 

“Inda Barrah ce a inda Nuwaira take yanzun fa Ammi?” 

Wani irin abu Ammi ta ji ya matse a zuciyarta, har yana sa duka jikinta ɓari. 

“Inda Barrah ce aka yi wa abinda Yaya yaima Nuwaira ko ba ace dole ya aure ta ba, mu duka zamu so ta auri wanda ba zai riƙe ta da laifin da ba nata ba, wanda zai riƙe ta saboda Allah. Kun musu rashin adalci mai yawa Ammi. 

Soyayyar Yaya ta rufe miki idanuwa, tun tasowar shi bakya jin maganar kowa indai akan shi ne, sosai yake kurakuran da kin sani kike kauda kanki, na ɗauka wannan kuskuren nashi zai canza ki kamar yadda ya canza shi Ammi, na ga nadama a idanuwan Yaya, inda zai koma ya canza abinda yayi wallahi da yayi. 

Me yasa wannan karon kawai ba zaki ga kuskuren da kukai mata ba? Yaran ta za ku rabata da su ba tare da tunanin ita ɗin wane hali zata shiga ba. Kiyi haƙuri Ammi zan yi magana da Baba, idan za su bani ita, idan girman laifinku bai hana su bani ita ba zan aure ta Ammi…zan yi ƙoƙarin gyara mata kuskuren da kuka aikata mata…” 

Aslam ya kuarashe yana miƙewa ya bar Ammi da zufa take tsatssafo mata ta ko’ina. Inda wani na waje ne ya faɗa mata maganganun da Aslam ya faɗa mata ko kaɗan ba za su dameta ba, amma yanzun jinsu take har cikin zuciyarta, sosai maganganun shi sun mata zafi, numfashi ta ja da niyyar fitar da shi ko zata samu sauƙin abinda take ji, muryar Barrah ta dirar mata cikin kunnuwanta da faɗin, 

“Bai tsaya ya ji amsarki ba Ammi. Ni ina son sani. Inda nice me za ki yi?” 

Juyawa Ammi ta yi tana kallon Barrah da take tsaye jikinta da doguwar riga ta material, sai hula fara a saman kanta. 

“Barrah…”

Ammi ta kira tana tunanin lokacin da rayuwa ta kawota wannan matsayin da yaranta za su tsareta da tambayoyi haka. 

“Don Allah ki faɗa min Ammi, tun jiya nake a tsora ce, nayi tunani kala-kala Ammi, idan zunuban Yaya suka bini fa? Bana jin haushin shi wallahi, ƙaunar da nake mishi ta hana min hakan, amma bata rabani da tsoron da nake ji ba. Idan ƙaddarar abinda ya yi ma yaran mutane ta faɗa min fa?” 

Sai da safen nan da kuka tafi nayi wani tunanin, da babu Yaya Aslam a rayuwata da na yi fiye da abinda Yaya yayi. Ammi baki taɓa korata Islamiyya ba, ko sallah baki taɓa ce min in tashi in yi ba. Yaya Aslam bai taɓa dukana ba sai akan Islamiyya, tun yana zane ni ya ja hannuna mu tafi tare har na fara zuwa da kaina. 

Ammi da na tashi banda addini fa? Da yafi komai muni akan lalacewar da zanyi. Allah ne ya dubi rayuwar mu, da ke da Baba kun cuce mu kamar yadda rashin tsawatar ma da Yaya da ba ku yi ba kuka cuce shi. A jikinki yai kuka shekaranjiya, da bai yi kuka a jikinki ba tunda ke ce sanadin kukan shi. Kamar yadda kike son Yaya haka yake son ki shi yasa ba zai taɓa faɗa miki ke ce sanadin duk wani hali da yake ciki yanzun ba. Ba shi kaɗai bane Ammi, har yaran shi da za ku karɓo kun ja musu, ina tausayin Yaya saboda wata rana zai kalli idanuwan su ya faɗa musu abinda yaima Maman su, in sanadin hakan yasa sun tsane shi duka laifin yana kanki ne, kin so Yaya, kin so mu dukkan mu, kin mana son da baki ga rayuwar mu zata naƙasa ba Ammi, bana so in so yarana da kalar son da kike mana, bana so wallahi, ina jin tsoro yanzun, ina jin tsoro sosai na rayuwar gaba ɗaya. Inata tunani kala-kala fa, kaina na min ciwo saboda tunanin da nake ta yi. Idan Yaya Aslam yana son auren Nuwaira ne ki bar 

shi ya aure ta, in ba za ki iya ganin su ba, zan faɗa mishi ya nemi aiki a wani gari su yi miki nisa Ammi… Amman karki hana shi gyara kuskuren da kika yi…” 

Barrah ta ƙarasa maganar tana jin kanta ya mata nauyi, ba don Aslam ba da bata san inda rayuwarta zata kasance ba, har sallah ta yi daren jiya tana gode ma Allah da ya kuɓutar da su daga kalar soyayyar da Ammi ta nuna musu, gara ma Anam, don shi magana ma ba damun shi ta yi ba, ko hayaniya yaron baya so, shi yasa da lokacin makaranta Islamiya ko boko yayi yake tafiya, duk wani abu da za ai mai faɗa baya so tun yana da ƙarancin shekarun shi. Ɗaki ta wuce, da tana tunanin ƙarasa makaranta tukunna ta fara maganar wani aure, don duk cikin wanda suke zuwa gurinta mutum ɗaya ne yake mata maganar aure, wani Ahmad, kuma shi ta fi kulawa, tun jiya ta gama yanke shawarar su nutsu da maganar Altaaf ɗin, itama aure zata yi kafin zunuban Altaaf su kamo ta. 

Ɗakinta ta wuce, dama ruwa ta fito ɗauka ta samu Aslam yana ma Ammi magana, yanayin yadda Ammin ta amsa shi yasa Barrah faɗin abinda yake ranta itama. Tunda ta faɗa kuma wucewa ɗaki ta yi tana barin Ammi da take jin duniyar ta haɗe mata waje ɗaya. Wasu hawaye masu ɗumi ta ji sun zubo mata, ko a mugun mafarki bata taɓa hango ranar da ɗaya daga cikin su zai faɗa mata magana ba, bata taɓa ɗora ayar tambaya kan kalar ƙaunar da take musu ba, don tana jin zata iya komai saboda su. 

Amma yau cikin idanuwa Barrah ta kalleta tana faɗa mata ta cuci Altaaf, cikin su ma ba kowa ba sai Altaaf, yaron ta da take jin in aka bata dama zata kwashe sauran shekarun da suka rage mata a duniya ta miƙa mishi, yau shi Barrah take faɗa mata ita ce sanadin duk wani abu mummuna da ya same shi, ba wannan ba ne yasa hawayenta suke zuba yau, gaskiyar maganar Barrah ɗin, miƙewa Ammi ta yi daga falon saboda zazzaɓin da take ji ya saukar mata, ɗakinta ta koma ta kwanta, har lokacin hawayen takaici ne suke zubar mata, a karo na farko a tsawon lokaci da take kuka da idanuwanta, a karo na farko a rayuwarta da da na sani ya kawo mata ziyara, yanayi ne baƙo a wajenta, rufe idanuwanta ta yi ko zata samu sauƙi, amma sai duk wani abu da ta yi ba dai-dai ba a farkon aurenta da duk wani abu akan tarbiyar yaranta suka soma kawo mata ziyara suma.

*****

Ƙamshin manja ta ji da yasa yawunta tsinkewa, da sauri ta miƙe duk da zazzaɓin da yakan kawo mata ziyara duk idan yamma ta yi. Beena ce ta shigo ɗakin, har yanzun tsayinta na ba Tasneem ɗin mamaki. 

“Me kuke yi ne a gidan wai?”

Tasneem ta buƙata. 

“Wainar filawa Hamna ke soyawa…”

Da sauri Tasneem ta ce,

“Don Allah ki ce ta zubo min, a saka min yaji sosai.” 

Juyawa Sabeena ta yi tana fita daga ɗakin da sauri, tunda ta dawo gida duk wani abu da suka san mai ciki zata iya so shi suke dafa mata, ta riga ta fawwalawa Allah lamurranta, daga ranar da ta dawo gidan bata sake zubar da hawayenta haka kawai ba. In ta yi kuka a sujjada ne, da ta kuma idar da sallolinta na farilla ko nafila ta gama kuka kenan. Yadda su Hamna suka damu kawai ya isa yasa ta ƙoƙarin ganin ta danne damuwar ta. Ballantana ma ta cire duk wani abu daga ranta, har Rafiq ta ajiye shi a gefe, wayarta ma kasheta ta yi duka ta saka cikin akwati, don in tana kusa da ita sai ta ga kamar zai kira, amma in bata kusa bata saka rai. 

Tana ƙoƙarin ganin har ɗakin Ummi ta je ta ɗan zauna, duk da ba wata hira suke ba, yanayin sanyin da Ummi ta yi yana taɓa ta sosai, gaba ɗaya kamar ba Ummin su ba, magana ma sai sun mata suke jin muryarta, wuni take a ɗaki sai sun ce an gama girki ko su sun shiga, Tasneem na kula yanzun har Hamna tana ɗan jan Ummi ɗin da hira, tsakanin ɗa da mahaifa sai Allah, ƙaunar su mai girma ce komin yadda ta samu tangarɗa. Ita yanzun Tasneem yaron da ke cikinta take riritawa kamar ranta, ko bakomai tana son taga dirowar shi duniya, saboda ɓangarene na Rafiq da ita a tare. 

Sai dai tana da tabbacin zuciyarta ta rufe da dokawa kowanne ɗa namiji, Rafiq ne kawai, in babu shi ta haƙura, ko takardar daya bata buɗe ba, cikin akwati duka ta saka ta rufe, ta san menene a ciki, buɗewar ba zai canza hakan ba. ATM ɗin daya bata takan aiki Azrah ko Hamna su ciro mata kuɗi in suna buƙata, da yake Azrah ita tana zuwa school of nursing da ke Aminu Kano, Hamna kuma a FCE ta samu gurbin karatu, duka kuɗin makarantar su da ma makarantar kacokan ɗinta Rafiq ne, har account shi ya buɗe musu yana tura musu kuɗaɗen da za su yi hidindimun karatu da su, bata san yadda zata fara son wani namiji bayan shi ba. 

Bayan kaunarr daya nuna mata, ya mata halaccin da ba zai mantu a wajenta ba. Sabeena ce ta shigo da kwano, ƙamshin wainar filawar da tasha albasa na dukan hancin Tasneem ɗin. 

“Don Allah ki miƙo min da sauri mana.”

Sabeena na dariya ta miƙa mata, cinyewa ta yi tas tana jin wata nutsuwa ta ban mamaki, tana shirin cewa a ƙaro mata Hamna ta shigo da gaba ɗaya robar wainar filawar. 

“Kayya Hamna kin taimaka min sosai…”

Saida ta ajiye robar tukunna ta ɗiba ta saka a wani plate ɗin daban tana faɗin, 

“Bari in miƙa ma Ummi dai in zo, ku ci, nima wallahi tun ina makaranta nake jin ci, jiya na ce ma Azrah ina so ta ce in ta riga ni dawowa yau zata yi, kin ganta shiru har yanzun.”

Ficewa Hamna ta yi daga ɗakin tana sallama a dakin Ummi tare da tura labulen, a hankali Ummi ta amsa mata. 

“Ummi wainar filawa na soya fa, ga taki.”

Binta da kallo Ummi ta yi, sosai take jin yaran nata har cikin ranta, ta basu haƙuri kan duk wani abu da ta yi musu, sai dai lokaci ya ƙure mata akan mahaifinsu, ƙasa ta rufe mishi idanuwa balle ta bashi haƙuri shi ma, don ta fi mishi laifi akan su. Sai dai yadda Hamna take mata magana yana mata daɗi, don duk cikin su ita ce gaisuwa kaɗai ke haɗa su. Bata shiga harkarta sam-sam. 

“Akwai manja ne daman?”

Ummi ta tambaya tana ɗaukar plate ɗin da Hamnan ta ajiye mata. 

“Yaya Tasneem ta bayar an siyo kwalba biyu ko shekaranjiya ne…” 

Kai Ummi ta jinjina musu. 

“Da kun zo kun tambayeni ai.”

Ta faɗi don itama akwai kuɗi a wajenta, tun auren Tasneem, kuɗaɗen da ta samu wanda Rafiq ya bata ta haɗa take siyan gwanjuna dila-dila, akwai ƙawarta da take siyar mata, kuma babu laifi akwai riba a harkar, musamman da Allah yasa musu albarka a ciki, kuma kuɗin na mata auki saboda Rafiq na sai musu kayan abinci, to yanzun kam bashida dalilin ci gaba da musu hidima. Indai abinda za su ci ne bata tunanin zai fi ƙarfin su da yanayin kuɗin da take samu ɗin, har hidimar makarantarsu in Allah ya taimaketa ba zata fi ƙarfin ta ba. Zata basu kulawar da ta kasa basu ko laifukanta za su ragu a gaban Ubangiji, ko zata samu ƙwarin gwiwar duban idanuwan mahaifinsu. 

“Ai an siyo, sai dai ko in ya ƙare, bari in je in ci tawa kar ta huce…” 

Cewar Hamna tana ficewa daga ɗakin, komawa ta yi suka ci tasu wainar filawar suna hira sama-sama. Azrah kam bata shigo gidan ba sai gab da Magriba, don jakarta ta ajiye a gefe tana cire farin takalminta da safarta ta ɗaura alwalar Magriba kafin ma ta ƙarasa cikin gidan da faɗin, 

“Na ji ƙamshin manja…Hamna ki miƙo min tawa don Allah. Da na idar da sallah zan ci…” 

Dariya Sabeena ta yi. 

“Mun cinye…”

Harara Azrah ta watsa mata. 

“Yaya Tasneem wai kun cinye?”

Da murmushi a fuskar Tasneem ɗin ta ɗaga ma Azrah kai, wani langaɓar da kai Azrah ta yi. 

“Ai shikenan…”

“Tun ɗazu muka yi ne Azrah, kar yai sanyi shi yasa.” 

A sanyaye Azrah ta ce, 

“Kinsan dai ko yayi sanyi ni ina ci ai. Ba ku dai kyauta min ba…” 

Ta ƙarasa tana wuce su ta shige ɗaki don an kira sallah, suma miƙewa sukai da niyyar ɗaura alwala, Hamna kuma da yake hutawa take saita shiga kitchen ta kunna risho tana fara soya wa Azrah tata wainar filawar tunda dama ta rage ƙullun. Tukunna ta kashe rishon tana shiga ɗaki da plate ɗin wainar ta ajiye wa Azrah da take Azkar a gabanta, harara Azrah ta bita da ita, don da gaske ta ɗauka sun cinye ɗin, har ma ta fitar da rai. 

“In ɗauke ba kya ci?”

Hamna ta buƙata tana kai hannunta, da sauri Azrah ta tureta tana faɗin, 

“Meye haka wai?”

Dariya Hamna ta yi tana sa Azrah faɗin. 

“Ke banza ce Allah, kinsa na yanke Azkar ɗina.” 

“Wainar filawa ta sa kin yanke Azkar dai.”

Tasneem ta faɗi, shiru Azrah ta yi ta ƙyale su, suna ta tsokanarta, wainar filawar take ci da sauri-sauri tana duba agogon wayarta da take ajiye kan dardumar. 

“Ki ci a hankali karki shaƙe…in ya zo ya jiraki ki ci abinci.” 

Hamna ta ƙarasa maganar tana ƙunshe dariyarta. Ɗayan hannunta da bata taɓa manja da shi ba ta kai dln ta daki Hamna da shi ta kauce da sauri tana dariya. Tasneem kuwa murmushi take yi, don Muhammad ɗin ta kula yana da hankali duk da bata ganshi ba, kuma ya samu wajen zama a zuciyar Azrah ɗin. Ta yarda da tarbiyarsu sosai da take da yaƙinin Allah zai musu zaɓin abokan zama na alkhairi. Kuma Azrah ɗin ta ce mata malamin makarantar gwamnati ne, yana da gidan shi na gado, wanda duk yayi ma Tasneem ɗin, tunda yana da sana’ar da zai iya riƙe mata ƙanwa, gashi ya ce zai barta ta ci gaba da karatunta in ya riga ta gama shirin aure. 

Hamna ce ma Tasneem ta kula da kwata-kwata bata fita hira, ko an aiko kiranta zata ce ace bata nan, wayarta banda Radio sai kallo bata komai da ita, idan tana gida wayar ma na iya yini a hannun Sabeena, ko an kirata ta kawo mata zata ce ta bari kiran ya yanke ta ci gaba da abinda take yi, batai mata magana ba ne don abubuwa sun mata yawa a kanta, amma hakan baya nufin bata kula ba. Sai dai ran nan da Tariq ya zo gidan ta kula da yadda yanayin Hamna ɗin ya canza gaba ɗaya. 

Yayi mamakin ganin Tasneem ɗin sosai, ita kanta ta ji daɗin ganin shi, da kuma yanda bai yardar da zumuncin ba, bata kuma ɓoye mishi halin da take ciki ba, don babu wannan a tsakanin su, ya kuma gaya mata Yasir ɗinsu na tare da su bai rasu ba. Kusan yini yai a gidan don nan ya ci abincin rana, sai da yamma sosai ya tafi. Sosai Tasneem ta so ta fahimci wani abu akan shi game da Hamna, sai dai Hamna mutum ce mai wahalar sha’ani, feelings ɗinta ɓoye suke sosai da sosai, tana da riƙe sirri ba kamar su Azrah da za ka fahimci yanayin su a cikin idanuwan su ba. 

Yau ɗin ma kamar ko yaushe bayan Azrah ta fita babu jimawa aka zo kiran Hamna ɗin, kuma kamar kullum haka ta ce yaron ya ce bata nan. Tasneem ta katse ta da faɗin, 

“Kai ka ce tana zuwa.”

Turo laɓɓa Hamna ta yi. 

“Ko waye ma Allah yai masa shegen naci, kusan kullum sai ya aiko, ko fita kika yiykuka gaisa ai kin mutunta shi, bana son irin haka, kin fi kowa sanin mutum ba abin wulaƙantawa ba ne ba.” 

Muryar Hamna can ƙasa ta ce, 

“Ni bai min bane ba, da in ɓata mishi lokaci in ɓata nawa gara ban fita ba, kuma bacci nake ji Allah.” 

Ta ƙarashe maganar tana ƙin yarda su haɗa idanuwa da Tasneem ɗin. 

“Ki je dai ku gaisa, ko baka son mutum a zamanin nan lallaɓawa kake ku rabu lafiya babu wulaƙanci.” 

Hijab ta ɗauka tana ɗorawa kan kayan jikinta ta fita ɗin babu yadda zata yi, da ƙyar suka iya gaisawa da Najib ɗin da a nan ƙasan unguwar su yake, ta ce mishi kanta na ciwo zata je ta sha magani ta kwanta, sukai sallama ta koma cikin gida. In zata faɗi gaskiya ko kaɗan Najib ba shi da wata makusa, kuma kowa yasan gidansu da tarbiyyar gidan su, mutanen kirki ne na gaske. Kawai dai ba shi da wajene a zuciyarta, banda Tariq babu kowane namiji a zuciyarta. Tun tana ƙaryata abinda take ji a kanshi har ta daina. 

Ko da Rafiq ya siya musu wayoyi ta ji daɗi ne saboda sukan gaisa ko da bai zo ba, kuma kullum sai ta mishi text ɗin gaisuwa da safe, da dare kuma ta sake tura mishi wani, duk da ba kullum take samun amsa ba, bata damu ba, a kalar son da take ma Tariq bata jin wani sauran aji a tare da ita, wani lokaci cikin dare takan farka haka kawai da tunanin shi manne a zuciyarta da yake hanata sukuni, haka zata ƙare daren da yin salloli da neman mafita. A satikan nan abin yake ƙara mata yawa, ita kanta ta san ya kamata ta ba wasu dama, don ko da wasa Tariq bai taɓa nuna mata alamar soyayya ba. 

Ba zata manta ranar da wani ya biyota ba ta dawo makaranta, Tariq ɗin ya gansu, tsokanarta ya dinga yi da cewar ya kamata ya fara tari kar aurenta ya zo mishi da bazata. Bata san me yasa yadda ya nuna bai damu don wani ya mata magana ba yasa ta kwana tana zubar da hawaye. Ta sha itama tsokanar shi in ya zo gidan ta ganshi da manyan kaya da faɗin ko ya je zance ne, murmushi yakan yi ya ce mata babu wajen nan a zuciyar shi, ba shi da sauran soyayyar da zai ba mace. Amma zata rantse da Allah da duk wayewar gari da yadda soyayyar shi take ƙara tsaya mata a rai. 

Ta yi addu’a, ta yi azumi, ta yi kuka a sujjadar ta, amma kamar hakan ƙara mata soyayyar shi yake yi, har ta rasa inda zata tsoma ranta ta ji sanyi-sanyi. Musamman yanzun da baya kwana uku bai zo gidan ba. Numfashin ta har barazanar tsaya mata yake duk idan yai mata murmushi, tana cikin wani irin yanayi da ta kasa faɗa ma kowa, har Tasneem ɗin, don bata san ta inda zata fara ba, kunya ma ba zai barta ta fada musu cewar Tariq din take so ba, bayan hakan bata asarar magana akan abinda ba zata iya canzawa ba tunda can, Tariq baya jinta kaman yadda take jin shi ta sani, ita kuma ta kasa daina jin abinda take ji akan shi, faɗa a fili ba zai canza musu yanayin su ba. 

Yanzun ma da ta shigo wucewa ta yi kan katifa ta kwanta tana jan mayafi ta rufe jikinta. 

“Abincin dare fa?”

Tasneem ta buƙata ganin Hamna ɗin na tofa ma jikinta addu’a alamun shirin bacci ta yi gaba ɗaya. 

“Yanzun da yammaci muka ci wainar filawa, nikam a ƙoshe nake Yaya Tasneem. Sai da safen ku.” 

Cikin sanyin murya Tasneem ta amsa ta da. 

“Allah ya tashe mu lafiya.” 

Gyara kwanciya Hamna ta yi, tana jan mayafin ta rufe har kanta, ta gode ma Allah da yanayin sanyi da ake a gari balle wani ya yi mata maganar abinda yasa ta rufe har kai, kuma babu wuta, amma ɗakin da hasken fitilar cajin da take kunne a ɗakin, batasan dalilin da hawaye masu zafin gaske suke zubar mata ba, sosai hawaye suke zubar mata, ga ƙirjinta da yai nauyi, a haka bacci ya ɗauke ta cike da mafarkin Tariq ɗin. 

Next >>

Leave a Reply

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.