Skip to content
Part 50 of 52 in the Series Alkalamin Kaddara by Lubna Sufyan

A kwanaki biyun nan ciwo take da ba shi da alaƙa da asibiti, ta rame ta yi zuru-zuru da ita. Bata san me yasa son Tariq ɗin ya taso mata haka ba lokaci ɗaya, tunda abu ne da ya jima tare da ita, kusan da shi ta girma a zuciyarta. Da Tasneem ta tambaye ta ce mata ta yi gujumniyar makaranta ce, kuma tana jin kamar zazzaɓin dare take yi, ta ce mata ta je asibiti ta amsa da zata sha magani in zata kwanta in bai yi ba sai ta je, dole Tasneem ɗin ta ƙyale ta. Yau ma tun wajen ƙarfe ɗaya ta dawo daga makaranta, don ta riga Sabeena, Tasneem na kallon ta da ɗan abincin da ta zubo ta ci tana fara duba takardu har akai sallar Asr, su dukkan su suka yi Sallah, Sabeena ta wuce Islamiyya. 

Miƙewa Hamna ta yi tana faɗin, 

“Bari in siyo kati…”

Kai kawai Tasneem ta ɗaga mata, tana binta da ido ta fita daga ɗakin. Tana fitowa daga gida ta hango shi, idanuwanta na sauka kan yanayin takun tafiyar shi, zuciyarta na wani irin dokawa kamar zata fito waje, sosai yake ƙarasowa inda take tsaye a ƙofar gidan, tana jin kamar a cikin zuciyarta yake tafiyar da yake yi. Yana ƙarasowa inda take da murmushin nan manne a fuskar shi 

“Hamna…”

Ya faɗi yana ɗorawa da, 

“Kin yarda ni kwana biyu ko? Ɗan saƙon ma bana gani.” 

Magana take son yi mishi, amma babu abinda ya fito banda 

“Hmm…”

Hakan yasa Tariq faɗin, 

“Hamna lafiya? Me yake faruwa?”

Shirun ta sake yi tana sa hankalin shi ya tashi, kwana biyu bai ga saƙonta ba, duk da ba ko da yaushe yake amsawa ba, hakan baya nufin baya dubawa, yana ɗaukar wayar shi da safe saƙonta yake fara gani, haka komin dare sai ta turo mishi ya duba tukunna yake kwanciya, ƙaramin abu ne a wajenta, amma babba ne sosai a wajen shi, ya zo don ya ga Tasneem, amma a ƙasan zuciyar shi yasan don ya ga ko lafiyar ta ya zo, har da yai zaton bata da kati ne ya tura mata kati, rashin samun saƙon godiyarta ne yasa shi zuwa ma. 

Numfashi Hamna take ja tana fitarwa cike da ƙoƙarin danne abinda ya taso mata gabaki daya, so takeyi ma ta motsa ƙafafuwanta ko zata samu ta bar wajen amma ta kasa. 

“Hamna kina tsorata ni, ki min magana don Allah…” 

Tariq ya faɗi yana jin bugun zuciyar shi har cikin kunnuwan shi. Bata san meye ba, yanayin muryar shi, shi ɗin da yake tsaye a gaban idanuwan ta, ko kuma me yasa ta bude bakinta ta fito da duk wani abu da ta yi shekaru tana riƙewa ba, ta dai san ya taso mata ne kamar aman da ta kasa mayarwa, tana fatan fitar shi ya zo mata da dukkan wani sauƙi. 

“Bansan ko tun yaushe ba Yaya Tariq. Ina sonka, ba son da ke tsakanin ‘yan uwa ba. Ina son ka, ban kuma san ya zan yi ba, ban kuma san ko me yasa duk shekarun nan sai yanzun nake faɗa maka ba…” 

Kallon ta yake cikin tashin hankali yana girgiza mata kai. Ba baƙon abu ba ne a wajen shi don kalmomi ‘yan kaɗan sun birkita mishi komai cikin ƙanƙanin lokaci, amma wannan karan kalmomi ne da ya kamata su saka nutsuwa. Kallon shi take yi itama, idanuwanta ɗauke da wani irin yanayi da baya son gani, kafin a hankali hawaye su cika su taf suna maye gurbin yanayin. 

“Ba sai ka ce komai ba Yaya Tariq, nima ba na gaya maka bane don ina tsammanin za ka soni ko wani abu, na faɗa maka ne ko zuciyata zata barni in huta haka, ko zata haƙura ta fara kallon wani…” 

Ta ƙarasa tana sa hannuwa ta goge hawayen da ta ji sun zubo mata. Ƙirjinta ya mata nauyi kamar an ɗora dutse. Ji take kamar ƙasar wajen ta tsage ta nutse da ita. Ya buɗe bakin shi ya kai sau huɗu amma komai ya ƙi fitowa, muryarshi can ƙasan maƙoshi ya ce, 

“Hamna…”

Ganin ya kasa cewa komai ya sata raba bayanta daga jikin bangon tana juyawa ta bar mishi wajen. Har cikin ranshi ya so kiranta, ya ma kirata ɗin, muryarshi ce ta ƙi fitowa fili, akwai shaƙuwa ta daban a tsakanin shi da Hamna, ta fara sanin sirrikanshi da ko Ashfaq bai sani ba, amma bai taɓa kallon ta da abinda ya wuce ‘yar uwar da ta maye mishi gurbin Yasir ba. 

Duk lokacin da zai yi magana da ita, zai yi ba tare da tsoro ko fargabar dangantakar su zata canza bayan ta ji mugayen halayen shi ba, baisan ya akai ya sani ba, ya akai yake da tabbacin komai lalacewar da zai yi Hamna na cikin mutanen da ba za su gujeshi ba, sai dai bai taɓa wuce hakan a wajenshi ba. 

Ta yaya zai fara kallonta da wasu idanuwan bayan zuciyarshi na doka ma Tasneem? Ko da tai aure ba wai ya rage sonta ba ne ba, yana nan daram a zuciyarshi, burin mallakarta ne kawai ya ƙarasa dishewa. Amma yanzun, daga ranar da yasan ta dawo gida zuciyarshi ta saka shi a gaba. Wannan karan ba zai taɓa yin wasa da damar da ya samu ba. 

Shi ya kamata ya faɗa ma wani ba ko da yaushe rayuwa take sake baka dama ba, yanzun haka in akwai abinda kalaman Hamna sukai mishi bai wuce bashi ƙarfin gwiwa ta ɓangare da dama ba, a cikin yanayin da take ya samu ƙarfin zuciya, zai faɗa ma Tasneem yana sonta ko da zuciyarta ba zata iya doka mishi yadda yake so ba, kamar yadda Hamna a matsayin ta na mace ta faɗa mishi tana son shi duk da sanin ba lallai yana jin yadda take ji ba. 

Numfashi ya ja yana fitarwa a hankali, zai fara faɗa ma Tasneem, sannan zai fara ƙoƙarin ganin son da Hamna take mishi bai canza dangantakarsu ba.

‘Son kai Tariq, kana son kan ka da yawa.’

Wata murya ta faɗa mishi can cikin kanshi. Bai bi takanta ba, ba laifin shi ba ne ba, rayuwa ce bata barshi da wani zaɓi ba. Ba zai taɓa bari ya rasa Hamna ba, ya iya rayuwa da son Tasneem da rasa ta, zuciyarshi da ta tarwatse baisa ƙarshen duniyarshi zuwa ba, ya kuma san Hamna ta fishi ƙarfin zuciya. In hakan son kai ne, bai dame shi ba. 

***** 

Bin ta yayi cikin gidan yana samun Tasneem zaune akan kujera, sai dai ko alamun Hamna bai gani ba, murmushi Tasneem ta yi mishi, da sai lokacin ya tuna yai mata sallama. 

“Yaya Tariq kana zuwa duk sa’adda nake buƙatar ka…” 

Ta faɗi tana saka shi motsa laɓɓanshi da fatan murmushi ne ya bayyana a fuskar shi, amma Hamna yake son ya gani ba ita ba, a karo na farko da ganin ta bai rage mishi abinda yake ji a zuciyar shi ba. 

“Kuɗi nake so a ciro min wallahi. Hamna bata jin daɗi, ta ma fita ta siyo kati, Azrah kuma sa’adda zata dawo Magriba ta yi…” 

Muryar shi can ƙasan maƙoshi ya ce, 

“Ba matsala…”

Yana tunanin inda Hamna ɗin ta yi, don cikin gida ta koma, baisan Tasneem ta dawo ba saida ta miƙa mishi ATM ɗin tare da faɗa mishi lambobin sirrrin katin, karɓa yayi yanayin shi na sata faɗin, 

“Lafiya dai ko?”

Cikin idanuwa Tariq ya kalleta 

“Kina tunanin sake yin aure?”

Tambayar ta dirar mata kamar saukar ruwan saman da bai nuna alamun hadari ba, shi kanshi baisan me yasa ya tambayeta ba, zai rantse ba abinda yake cikin kanshi kenan ba. A hankali Tasneem ta girgiza mishi kai. 

“Banda wajen wani a zuciyata Yaya Tariq, ina jin kamar an halitta min ita ne a ƙirjina kawai don ta doka ma Rafiq, bazan iya rayuwa da wani namiji banda shi ba. Na miƙa ma Allah dukkan lamarina, yanzun ba shi bane ma a gabana…me yasa ka tambaya?”

Kai kawai ya girgiza mata yana juyawa ya fita daga gidan, a ƙofar gida ya tsugunna yana jin kanshi yayi mishi wani irin nauyi. Baisan me yasa ya tambayi Tasneem abinda ya tambayeta ba, amma ya samu tabbaci ɗaya, soyayyar da yake mata abu ne da ba zai taɓa wuce zuciyar shi ba, balle ya fito da shi kan harshen shi ya furta mata, a cikin idanuwanta ya ga kalar soyayyar da yake mata, amma ba akan shi ba, akan Rafiq, tun aurenta burin samunta ya dishe mishi, da ta ce mishi auren ya mutu ne yasa shi jin kamar wutar burin na son hasko mishi, amma yanzun ne yake da tabbacin ta yi mutuwar da babu abinda zai iya kunnata. 

Amma hakan baya nufin ya karɓi abinda Hamna ta faɗa mishi. A hargitse yake jin shi, da ƙyar ya iya zuwa banki ya ciro ma Tasneem ɗin kuɗin ya dawo, yana bata ya juya ya fice ba tare da ya ce komai ba. Gaba ɗaya a hargitse Tasneem ɗin take ganin shi, tana tunanin inda Hamna ta daɗe haka ta ga shigowarta ba tare da ta yi ko sallama ba. Gidan su Tariq ta shige tana zama a tsakar gida ba tare da ta damu da ƙurar da take cikin gidan ba. Kuka ta yi kamar zuciyarta zata faɗo, amma ko kaɗan babu dana sani a cikin zubar hawayenta, tana dai jin yadda maganganunta za su sa ta rasa Tariq ɗin da duk wani zumunci da ke tsakanin su. 

Amma hakan zai fi mata sauƙi, in tai jinya ta warke zata haƙura da shi ta fara kula wani, sauƙi ne ta nemarwa kanta, ganin yamma na yi sosai yasa ta goge fuskarta ta fito tana shigowa gida, sai dai me kallo ɗaya ta yi ma Tasneem ta ji wani sabon kukan na ƙwace mata. 

“Inbalillahi wa inna ilaihir raji’un… Hamna me ya faru?” 

Tasneem ta faɗi cikin tashin hankali, da sauri Hamna ta ƙarasa jikinta tana ƙara fashewa da wani irin kuka. Ummi da ke ɗaki na fitowa babu shiri. 

“Meya faru? Me akai mata?”

Rausayar da kai Tasneem ta yi tana riƙe Hamna da rabon da ta ga ta yi kuka haka tun rasuwar Abba. 

“Nima ban sani ba Ummi, kati ta ce min zata siyo kawai ta shigo tana kuka.” 

Ƙarasowa Ummi ta yi tana kamo Hamna ɗin da tun tana yarinya rabon da ta riƙe ta a jikinta haka, sai take jinta daban, tsugunnawa Ummi ta yi, Hamna na kwanciya a jikinta, wani irin numfashi da bata san tana riƙe da shi ba ta saki, wannan karan hawayen ta sun zuba ne da jin ɗumin Ummi da bata taɓa sani ba, don ta yi yarinta ta tuna ranar ƙarshe da Ummi ta riƙe ta haka. 

“Ummi…”

Ta kira da wani irin yanayi da ya karyar ma Ummi ɗin zuciya. Hamna ta fi kowa ƙarfin zuciya duk a cikin yaranta, abinda duk zai sata kuka haka mai girma ne. 

“Hamna me akai miki don Allah? Ki faɗa min kin ji? Menene?” 

Kai Hamna ta girgiza mata tana sata sake faɗin, 

“Na san ba kwa gaya min abubuwa, ki faɗa ma Tasneem to kin ji in ba za ki iya faɗa min ba.” 

Kai Hamna ta sake girgiza mata tana ƙara riƙeta, su dukkan su haka suka dinga lallashin Hamnar har suka samu ta yi shiru, tashi ta yi taje ta wanke fuskarta, bata ce musu komai ba ta wuce ɗakin Ummi, a tsorace Ummi ta kalli Tasneem. 

“Ko ki je wajen ta?”

Kai Tasneem ta girgiza mata tana share ƙwallar da ta zubo mata itama. 

“Tunda ta je ɗakinki bata buƙata ta Ummi, ki je wajenta babu komai, zata neme ni in tana buƙata ta.” 

Kai Ummi ta jinjina tana shiga ɗaki, a tsaye ta samu Hamna ɗin, ta ƙarasa kan gadonta ta zauna, a hankali Hamna ta taka tana hawa kan gadon, kwanciya ta yi gefen Ummi, basu ce wa juna komai ba, Ummi ɗin bata yi ƙoƙarin riƙe Hamna ba duk da hakan take son yi da duk wani abu na jikinta. A karo na farko tun tasowar Hamna da ta ji tana son zama kusa da Ummi ɗin ko da ba zata ce mata komai ba. Maraici take ji da ta jima bata ji irin shi ba yau. A hankali ta lumshe idanuwanta tana magana da Abbanta ta hanya ɗaya da ta rage mata wato addu’a. 

Kano

“Yasir!”

Ashfaq ya faɗi a firgice yana buɗe idanuwan shi. Har sai da ya tsorata Yasir ɗin da yake zaune a gefen shi  

“Gani nan Yaya, babu inda na je.”

Yasir ya faɗi, tashi zaune Ashfaq ya yi yana mayar da numfashi, tun dawowar Yasir ɗin duk wani tashin hankali da ya faru da rayuwar shi dawo mishi yake yi, ko bacci ya yi mugayen mafarkai ne suke tashin shi da ganin kamar zai sake rasa Yasir ɗin, sam baya so ya ga yayi nisa ko kaɗan. Yasir abokin shi ƙaddara ta haɗa su , don bayan mutuwar Arfa ne ya fara neman hanyar da zai samu kuɗi don baya jin zai bari rashin kuɗi yasa shi ya rasa Tariq, abu ne da ba zai bari ba. A haka ya haɗu da Manga ya fara bashi ƙwayoyi yana kai mishi unguwanni yana biyan shi kuɗi, a hankali sukai wani irin sabo har ya zama babban yaron Manga, babu lungu da saƙo a garin kano da ake siyar da kayan maye da Ashfaq ɗin bai sani ba. 

Musamman duk wasu yaran masu kuɗi da suke shaye-shaye, hakan bai taɓa sa Ashfaq ya sha wani abu ba, ko da wasa su duka abokan harkarshi sunsan baya shan wani abu, wannan dokar shi ce, ya raba hanya da komai, ciki har da burin shi, ba zai rabu da hankalin shi ba. Ba zai ce ya taɓa karɓar kayan kowa ba, duk da su Manga suna yi, baya son haƙƙin wani a kan shi, gara ya siyar da ƙwayoyin shi. Yana kuma samun kuɗin da bai taɓa tunani ba. Da haka ya kama musu haya a rijiyar zaki suka bar gidan da suke don ba zai iya zama a cikin shi ba. 

Yai tsaye ganin Tariq ya ci gaba da karatun shi, tunda nashi karatun ya samu tangarɗa, wajen sata aka kama Manga sun dira gidan wani Alhaji, hakan yasa Ashfaq ya maye gurbin Manga ya kuma yi sanadin fara zaman shi dila babba da ake damawa da shi a harkar safarar miyagun ƙwayoyi a garin Kano. Duk da bai taɓa barin Tariq yasan hanyar samun kuɗin shi ba, yakan ce mishi kasuwanci yake yi, Tariq ɗin ma ba magana yake mai ba. A hankali harkar shi ta ci gaba da bunƙasa yana fitar da ƙwayoyi har wajen Kano, zuwan shi garin Lagos ne suka haɗu da Yasir da shi kuma rasuwar iyayen shi ta sa aka kaishi almajiranci da ya gudu ya fara bin tasha, har ya zama yaron mota yana bin manyan motoci zuwa Lagos. 

Kallo ɗaya za kai ma Yasir kasan babu kalar rayuwar da bai gani ba, sunan shi yasa Ashfaq fara mishi magana, har suka zama abokai kafin ya baro Lagos suka kuma dawo garin Kano tare, akwai haɗarin gaske a zama ɗan safarar ƙwayoyi, ba jami’an tsaro ba ne kawai abokan gabarsu, har da sauran masu safarar ƙwaya ‘yan uwan su, don a irin hakan ne yai ciniki da su Seyi da suma manyan ‘yan siyar da miyagun ƙwayoyin ne, da niyyar zai kai musu cocaine, sun siya suka basu kuɗin da darajar ta kai dubu ɗari biyar, Seyi ya kuma sa aka biyo bayansu don a kashe su a kwashe kuɗin, Allah ya taimake su suna da rabon shan ruwa a gaba. 

Tun a washegari kuma ya faɗa ma Yasir abinda yake yi da rayuwar shi, ya faɗa mishi yadda Tariq yake shan ƙwayoyin da har gidan mahaukata suka kaishi, ƙwayoyin da har yanzun yake fama don ganin Tariq ɗin ya barsu. Shiru Yasir yayi yana jin shi har sai da ya gama tukunna ya amsa shi da faɗin, 

“Komai zai yi dai-dai Yaya… Mubar asibitin nan tukunna.” 

Basu sake maganar ba kuma har yau, likitan ya ce musu nan da kwana biyu ma zai iya sallamar su in dai Ashfaq ɗin zai kula da kan shi yadda ya kamata, su dujkan su suka kuma amsa da za su kiyaye duk wata doka, don Ashfaq ya gaji da zaman asibitin gaba ɗaya. Yanzun ma banɗaki ya shiga ya wanko fuskar shi ya fito. 

“Ka ci abinci, Yasir ya kawo kana bacci.”

Kai Ashfaq ya jinjina.

“Ina ya je kuma? Yasir akwai shegen yawo. “

Ɗan ɗaga kafaɗu Yasir yayi, ba zai tsare shi da tuhumar ina ya je ba tunda ba ƙaramin yaro bane ba. Magana Ashfaq ɗin zai yi Tariq ya turo ƙofar yana shigowa ɗakin tare da jan kujera ya zauna. 

“Tariq…”

Yasir ya kira cike da kulawa. “Meye ka shigo a firgice haka?”

Ashfaq ya buƙata yana kallon Tariq ɗin, kai Tariq ya girgiza musu, baya son magana, in suna magana suna ƙara mishi nauyin da kanshi yayi mishi, shiru yake son ji ko yaya ne, shirun da kayan mayen shi ne kawai sukan samar mishi da shi. 

“Karka ce min babu komai Tariq.”

Ashfaq ya faɗi muryar shi can ƙasa. 

“Bana son yin magana akai ne.”

Tariq ɗin ya amsa, yanayin kusancin su na sa Yasir yin shiru, ya rasa abubuwa da yawa tare da su, ciki harda rasa abinda ya kamata yayi in ya gansu cikin yanayi haka, ko shiru Tariq yayi Ashfaq yakan san fassarar shirun, haka shima Tariq ɗin ya kula da idanuwa kawai Ashfaq zai motsa yasan me yake cewa, sosai abin yake bashi mamaki tunda ya dawo cikin su, Tariq shi kaɗai zai dinga magana, sai dai ka ga yana dariya, in baka kula da yanayin Ashfaq dake motsi da fuskar shi ba za kai zaton Tariq ya samu taɓin hankali ne, amma yasan me yake cewa. 

Yanzun ma da idanuwa Ashfaq ɗin yake kallon shi. 

“Ba abinda zai faru karka da mu.”

Tariq ya faɗi, don ware mishi idanuwa Ashfaq yayi yana sa shi faɗin, 

“Yaya mana, da gaske nake.”

Jinjina kai Ashfaq ɗin yayi yana samun waje ya zauna. Kallon su Yasir yake kawai, yana jinsu har ƙasan zuciyar shi, duk da yasan za’a ɗauki lokaci kafin ya fara fahimtar su, sun canza sosai daga yadda yake iya tuna su, ‘yan uwan shi ne har yanzun, ko kallon su yayi yana ganin hakan, amma halayyar su da ra’ayoyin su, abubuwa ne da zai fara fahimta tare da lokaci, yana kuma gode ma Allah da ya sake bashi damar da zai sake sanin su. Ba sauri yake ba, a hankali komai zai zame musu dai-dai.

Kinkiba

Zuciyarta take jin kamar zata faɗo, tunda su Inna suka sameta da maganar su Altaaf take jin wani abu na buɗewa a cikin ƙirjinta, kwana ta yi tana kuka, don ko bacci da yake ɓarawo bai gwada lallaɓowa kusa da ita ba. Baba yai mata bayani, sosai yai mata bayani yadda zata fahimci tasowar yaran nata da Baban su ba zai hana tabon da yai musu binsu ba, balle kuma tasowar su a hannun ta, da kuma yadda rayuwar su zata fi samun inganci idan tare da Babansu suke, amma sun bata zaɓi, ba su yi mata maganar cikin yanke hukunci ba, sun dai nuna mata kalar zaɓukan da take da su da makomar kowanne a rayuwar yaran nata. 

Ta kuma san ba ma Altaaf ɗin su shi ne ya fi alkhairi a rayuwar su, zuciyarta ce kawai take mata wani irin ciwo na ban mamaki, Hassana da Hussain ne babban tabon rayuwarta, hakan bai taɓa hanata jinsu kamar ranta ba, ga dai duk wucewar da za su yi sai ta ji gabanta ya faɗi saboda suna ƙara girma kamannin da suke da fuskar da ba zata taɓa mantawa da ita ba suna ƙara fitowa. Yau ma da ta tashi da safe kukan dai take, fuskarta ta yi wani irin kumburi, hasken da take da shi ya ƙara taimakawa wajen nuna kalar kukan da ta sha. 

Tana zaune a ɗaki ta haɗa kanta da gwiwa ta ji sallamar Tawfiq, a sanyaye ta amsa, muryarta na fitowa a dakushe. Tukunna ya ɗaga labulen yana shiga ɗakin, wani abu na matsewa a zuciyar shi da ganin yanayinta, ba don ya fi son Nuwaira duk a cikin ƙannen shi ba, ƙaddararta ce take taba shi fiye da yanda kalamai zasu taba furtawa. 

“Don Allah ki daina kukan nan ƙar ya sa miki wani ciwo Nuwaira.” 

Hannu ta sa tana share hawayen da suka zubo mata wasu na biyo bayansu. 

“Hmm…”

Kawai ta iya furtawa tana ƙara karya mishi zuciya, duk da bayanin da Baba yai mishi ranshi a ɓace yake tun daren jiya, ko baccin kirki bai samu yayi ba saboda ɓacin rai, shi da yana gidan sai ya musu fata-fata, ba ma za su samu damar zama har su faɗi wasu maganganun rashin kunya ba. 

“Kinsan ina nan ko? Kar ki yi wani hukunci da za ki yi dana sani, ni nayi niyyar ɗaukar su Hussain idan na yi aure in riƙe su a wajena…banda kuɗi sosai Nuwaira, amma wallahi zan riƙe su iya ƙarfina ba zan taɓa bari a musguna musu ba.” 

Wani hawayen ta ji suna ƙara biyo mata da kalaman shi, ko kaɗan bata da haufin zai riƙe mata yara fiye da yadda zata riƙe su, sai dai nauyin gidan gaba ɗaya yana kan shi ne, hidimar su Hussain ɗin da tasu gaba ɗaya, in dubu ɗaya ya samu da wahalar gaske ya ci Naira ɗari a ciki, sauran duk a hidimarsu zata ƙare. Ko don nauyi ya rage mishi zata ba Altaaf su Hussain, tana jin lokaci yayi da zai ɗauki kaɗan cikin laifukan da ya aikata, ko da ta hidimar yaran ce kuwa. 

“Ya ɗauki yaran shi Yaya.”

Ta faɗi da wani yanayi a muryar ta 

“Kema yaranki ne ai, me yasa kuka yanke hukuncin nan bana nan? Ni ba ku yi tunani na ba ko?” 

Tawfiq ya ƙarasa maganar muryar shi a karye, don shima yana jin yaran har ƙasan ranshi, sun taso a hannun shi kamar yadda suka taso a hannun ta, zai ce shaƙuwar da yai dasu ko ita bata yi da su ba. Lokaci ɗaya ace za’a raba shi da su, abin na mishi zafi na gaske. 

“Ka yi haƙuri, kaima hidimar zatai maka sauƙi, kuma lokaci yayi da zai ɗauki ko kaɗan ne daga cikin laifukan da yayi.” 

Miƙewa Tawfiq yayi, idan ya tsaya a ɗakin kuka zai yi don yana jin hawaye na mishi barazana. Bai ce komai ba ya ɗaga labule yana ficewa daga ɗakin. Nuwaira kuwa kanta ta mayar tana haɗewa da gwiwar ta, wani irin kuka na sake ƙwace mata da ciwon da take ji. 

*****

Wajen ƙarfe goma su Ammi suka isa Kinkiba, Altaaf bai biyo su ba, daga ita sai Baba sai Aslam. Da safiyar ranar ne Baba yake faɗa mata zancen da Aslam ya same shi da shi bayan sun fito masallaci. 

“Allah ya kaimu lafiya.”

Kawai Ammi ta furta, don har yanzun zuciyarta na mata zafi da maganganun da suka yaɓa mata jiya, musamman maganganun Barrah da take ji suna mata yawo, musamman yanzun da suka ƙaraso Kinkiba. Yau ɗin har cikin gida aka shimfiɗa musu tabarma aka kawo musu ruwa a wani kwanon sha. Baba da Aslam suka ɗauka suka sha, wayar Aslam ɗin da take ƙara ta sa shi tashi ya zira takalma yana fita daga gidan. Ammi kuwa tasan sai dai in suma take a ɗibi ruwan a yayyafa mata, ko a ɗura mata shi, da hankalinta dai ba zata sha wannan ruwan ba. Duk da gidan a share yake tsaf-tsaf, jar ƙasa ce dai da babu ko shafen suminti, amma ba shi da da datti. Haka jikin su Inna ma. 

“Idan kuka ɗauki yaran, mahaifiyar su fa? Rabata da su lokaci ɗaya haka ba abu bane mai sauƙi.” 

Malam Bashari ya faɗi bayan sun natsa, yana sa Baba amsa shi da hanzari. 

“Duk ƙarshen wata za’a kawosu su kwana biyu in sha Allah…” 

Jinjina kai Malam Bashari ya yi, tausayin ‘yar tashi na cika zuciyar shi, a sanyaye yake jin shi tun tafiyar su jiya. Amma yayi addu’a fiye da wadda yake yi a koda yaushe, yana fatan Allah ya kawo mata sauƙi a rayuwarta. Gyara zama Baba ya yi yana jin nauyin maganar da yake son furtawa. 

“Bansan ya za ku ji maganar nan ba, amma yaron wajena Aslam na son auren ‘yar wajen ku Nuwaira…” 

Inna ce ta ɗago wannan karan, idanuwanta cike taf da hawaye ta ce, 

“Shin iya abinda zuri’arku ta yi wa yarinyar nan bai isa ba ne? Lokacin da zata huta bai yi ba har yanzun? Ganin yaran da take yana tuna mata abinda ta rasa da wanda ba zata taɓa samu ba har abada bai isheta ba? Wane irin mutane ne ku?” 

Ta ƙarasa wasu hawaye masu ɗumi na zubar mata, tana tunanin su ne ajalin Nuwairar, so suke su kashe mata yarinya sai hankalin su ya kwanta. Tana ganin kukan da take yi tun jiya har zuwa safiyar yau, batai ƙoƙarin hanata ba saboda ta wani fannin kukan ma rahma ne. Amma baya nufin bata jin abin har ƙasan ruhinta. Wannan karon Ammi ce ta buɗe bakin ta. 

“Jiya Aslam ya same ni da maganar yana so ya auri Nuwaira, yana so ya gyara ɓarnar da mukai mata a rayuwarta. Ki yarda da ni idan na ce miki a jiya maganar bata zauna min ba, saboda banda yaro kamar Aslam. 

Bana tunanin za ki samu yaro kamar Aslam a gidaje fiye da ɗari, ba ina faɗa ba ne don ya fito daga jikina, ina faɗa ne saboda shi ne gaskiya. A shekarun rayuwata na ga mutane kala-kala amma ban taɓa ganin mai irin zuciyar shi ba. Yarinyar ku ta cancanci samun dukkan farin ciki, ina kuma tabbatar muku da Aslam zai iya bata. Aslam ba zai taɓa musguna mata ba, akan ce ba’a shaidar mutum, ba kuma lallai ku ɗauki shaidata akan yaron da ya fito daga cikina ba, amma ku duba zuciyoyinku, idan akwai wajen da zai iya ture laifinmu gefe ya duba lamarin don Allah ku yi hakan. Kuma ku yi haƙuri da abinda Altaaf yayi, ku yi haƙuri da abinda na yi muku nima.” 

Kallon ta Inna take yi, batasan tana jiran haƙuri daga wajen Ammi ba sai yanzun da ta furta, akwai wani abu a ƙasan zuciyarta da yake jiran haƙuri irin wannan daga bakin Ammi ya dishe, wani numfashi ta sauke tana sa gefen zaninta ta share ƙwallar ta. 

“Zaɓin na Nuwaira ne, ba za mu taɓa yanke mata hukunci ba. Ɗan ku yayi magana da ita. Idan alkhairi ne shi a rayuwarta wallahi bazan ɗaga kai ba.” 

Baba ya faɗi da wani irin sanyin murya, yana jinjina yadda al’amarin yake son juyewa gaba ɗaya, ya ga yaron da suka kira da Aslam ɗin, akwai wata kamala da nutsuwa shimfiɗe a fuskar shi da ko a ta su iyayen shi Malam Bashari bai gani ba. Yanayin komai nashi da wani irin sanyi na ban mamaki. A wani yanayin ba wannan ba zaice Aslam ya fi ƙarfin ‘yar su, ba kalar namijin da zai dubi gidansu da neman aure ba ne ba. Amma yanzun shi kam ba shi da ta cewa. 

“Ba damuwa, Allah yai mana jagora, zai dawo in komai ya natsa, nasan yanzun dai ba lokacin da ya dace bane ba.” 

Baba ya faɗa, bazai yiwu a rabata da yaranta kuma ai mata zancen aure duk a rana ɗaya ba. Hargitsin zai mata yawa, Inna ce ta miƙe tana ɗauko wata ƙoƙaƙƙiyar jaka da zip ɗinta ya sha ɗinki tana dawowa. 

“Ga kayan su…”

Ta faɗi muryarta na rawa da alamun kuka. Tashi ta sake yi tana wucewa ɗaki, Nuwaira na zaune da yaran a jikinta, don ta faɗa musu za su je unguwa kuma za su shiga mota, abinka da ƙuruciya, murna suke tayi suna tambayarta yaushe zasu tafi. 

“Zasu tafi Nuwaira…”

Inna ta faɗi tana son yin ƙarfin hali, hannu Nuwaira ta sa tana share ƙwallar ta, sakar mata labulen Inna ta yi, don ta san kunya irin ta Nuwaira, kamar hakan take jira ta ɗago Hassana tana rungumeta a jikinta tare da sumbatar gefen fuskarta, Hussain ma ta ɗago shi. 

“Me yasa kike kuka?”

Hassana ta tambaya tana tsura mata ido. 

“Idona ke ciwo Hassana. Karku yi ƙiriniya da yawa kun ji?” 

Kai ta ɗaga tana mata murmushi, bayan su ta ɗan tura tana jin zuciyarta kamar zata faɗo saboda ciwon da take mata. Bata zata rabuwa da yaran zai mata wahala haka ba sai da suka fita. Wani abu ta ji yana mintsininta, zuciyarta na gaya mata zata ɗauki lokaci kafin ta sake ganin su, zata ɗauki lokaci kafin ta riƙe su a jikinta. Wataƙila fuskarta ta dishe musu tunda suna da ƙarancin shekaru, batasan ƙafafuwanta sun motsa ba, inda Allah ya taimaketa da hijab a jikinta. Da hanzari ta fito tsakar gidan ta sake ganinsu ko da sau ɗaya ne. 

Basa nan, da sauri kamar zata faɗi ta nufi hanyar fita daga gidan, su Inna suna waje tsaye kusa da mota, an saka su Hussain a baya, laɓewa ta yi daga cikin soron gidan tana kallon yaron wasu hawaye masu zafi na zubar mata, miƙa wuya take don ta hango su sosai ta sauke idanuwan ta cikin na Aslam, sanyin da ke cikin idanuwan shi na fizgar wani abu a zuciyarta. Murmushi yai mata, zata rantse ya ɗaga mata hannu. Yana sake faɗaɗa murmushin shi da yake bata tabbacin yaranta ba zasu wulaƙanta ba, batasan me yasa ta ji ta aminta da shi ba, idanuwan shi taga ya sauke daga cikin nata a hankali, yanayin yadda yake komai a nutse yana mata tsaye a wuya. 

Ta kasa ɗauke idanuwan ta daga kanshi har ya buɗe motar ya shiga. Tana kallo ya ja motar tare da ɓangarori da dama na zuciyarta, tukunna ta koma cikin gida da sauri ganin su Inna na shirin dawowa, kusan da gudu ta shiga ɗaki ta zauna. Tana gyara zamanta Inna na ɗago labulen da faɗin, 

“Sun tafi Nuwaira, sun tafi.”

Inna ta faɗi tana jin gidan yai mata wani shiru, kai Nuwaira ta iya jinjina ma Inna da ta shigo ɗakin. 

“Allah yasa hakan ne alkhairin ku gaba ɗaya. Allah ya dubi lamurranki kin ji.” 

Kai Nuwaira ta sauke ƙasa tana jin hawaye na tarar mata, yanayin Inna na ƙara karyar mata da zuciya. Haka sukai zaune a gidan kamar masu zaman makoki, Baba ma ɗaki ya koma ya kwanta don baya jin ƙarfin fita gona kwata-kwata. Ko karin safe babu wanda yayi shi a cikinsu. 

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Alkalamin Kaddara 49Alkalamin Kaddara 51 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×