Skip to content
Part 20 of 52 in the Series Alkalamin Kaddara by Lubna Sufyan

Banda ruwa babu abinda Rafiq yake cewa yana so duk ranar har washegari, da ya farka ruwa kawai sai ya sake komawa bacci, likita ne ma yace a samu ko Tea a bashi. Ba yadda Nuri bata yi ba, daƙuna fuska ya yi yana lumshe ido kamar zai mata kuka, bacci yake ji, dole ta ƙyale shi ya sake komawa baccin ta shiga wanka ita kuma. A banɗakin ta shirya har kaya ta sake tana ninke wanda ta don ta fito da su. Akwai masu aiki da ta san za su shigo su take ba su wanke mata ta biya su. 

Fitowa ta yi daga banɗakin da kayan a hannunta, kanta a ƙasa yake don ko kaɗan bata kawo ma ranta kowa ba, ta gefen idonta taga kamar mutum a tsaye, da sauri ta ware idanuwanta tana juyawa, zuciyarta ta yi wata irin dokawa saboda tsoron da ta ji. Dariya Aroob take yi tana takawa inda Nuri take tsaye tare da rungume ta. 

“Nuri…”

Numfashi kawai Nuri take yi tana tattaro duk wata nutsuwarta da ta rasa. Tukunna ta ture Aroob ɗin. 

“In zuciyata ta buga sai ku huta ku dukkan ku.”

Ta ƙarasa maganar tana kallon Fawzan da Daddy da suke tsaye suna mata dariya. Kafin Fawzan ya ce, 

“Nuri…”

Cikin sigar gaisuwa. Kallon su take yi. 

“Fawzan.”

Ta kira tana mayar da hankalinta kan Daddy kafin ta ce, 

“Sannun ku da zuwa.”

“Sannunki da ƙoƙari.”

Daddy ya amsa, yana jan kujera ya zauna. Fawzan kuwa zagayawa ya yi yana zama gefen gadon Rafiq ɗin a hankali don kar ya tashe shi. 

“Fawzan karka tasar min yaro.”

Zuciyarshi Fawzan ya dafe yana kallon Daddy tare da faɗin, 

“Yanzun in wani ya shigo sai ya ɗauka shi kaɗai ne yaronka Daddy.” 

Aroob ce ta ƙarasa ita ma tana zama kusa da Fawzan ɗin da ya harareta. 

“Ku tashi karku karya gadon.. Kuna jin har ƙara ya fara.” 

Cewar Nuri da take jan kujera zuwa kusa da Daddy ta zauna. Sai lokacin ta kula da jakar kayansu a kusa da Daddy ɗin. 

“Ba dai mijina kuka bari ya ɗauko muku kaya ba.” 

Ta faɗi tana nuna Fawzan da Aroob da ɗan yatsa. 

“Daddy ne zai ɗaukar mana kaya Nuri?”

Aroob ta tambaya tana jinjina kanta, duk da tasan don ya ɗaukar musu kaya ba wani abu bane ba a wajenshi. Akwai abubuwa da yawa da basu samu ba ta ɓangaren Daddy, kalar ƙaunarshi ta sha banban da sauran iyaye, a wani ɓangaren kuma suna samun kulawar da ba kowanne mahaifi da ya taka matsayin Daddy bane zai damu ya ba yaranshi ba. 

“Aroob kina cika min kunne fa.”

Fawzan ya ce yana ɗan matsawa, juyawa ta yi tana hararar shi, kallon su Nuri take, ba ita take binshi ba, amma faɗan su baya ƙarewa, tunda Zafira mai sanyi ce ita, hayaniya ma bata dameta ba, sai Aroob. Ɗauke idanuwanta ta yi daga kansu tana mayarwa kan Daddy da ta ji ya riƙo hannunta yana dumtsewa cikin nashi. 

“Kin rame sosai.”

Ya faɗi muryarshi ɗauke da wani yanayi. Ɗan murmushi ta yi. 

“Kaima ka rame ai.”

Ɗan jinjina kai ya yi. 

“Damuwa ce da tunanin ku.”

Hannunshi da ke cikin nata ta kalla tana ganin yanda yayi kamar an halitta shine kawai don Daddy ya riƙe. 

“Nima damuwar ce da kewarka.”

‘Yar dariya Daddy ya yi. 

“Kina magana kamar ke kaɗai ke fama da kewa.”

Muryarta da wani sanyi ta ce, 

“Kasan na fika rauni ta wannan ɓangaren.”

Murmushi kawai ya yi, bai taɓa mamakin yadda ya kawo yanzun da soyayyarta daram a zuciyarshi ba, bata taɓa bashi dalilin da hakan zai faru ba. Shi ne na farko daya rage a duniyarta yanzun, ko da ta raba soyayyarshi da ta yaransu yana da tabbacin ba zata tsaya tunani ba in aka bata zaɓi akan biyun. Don haka ya ce, 

“Rafiq fa?”

“Gashi nan Alhamdulillah, kalma ɗaya ya faɗa dai har yanzun.” 

“Nuri…”

Daddy ya faɗa, daƙuna mishi fuska ta yi cikin rashin fahimta. 

“Ina nufin kalmar da ya faɗa. Ke ya kira ko?”

Murmushi ta yi tana ɗaga mishi kai. Shi ma murmushin yake yi don ƙaunar da ke tsakanin su ta daina bashi mamaki. 

“Nuriiiii.”

Fawzan ya kira da alama bashi bane karo na farko da ya yi kiran, hankalinta gaba ɗaya na kan Daddy, ba ko yaushe take sanin abinda yake faruwa a wajen duniyar ba in suna cikin tasu. Kallon Fawzan ɗin ta yi. 

“Yunwa muke ji fa.”

Ya faɗi, Aroob na ɗorawa da, 

“Mu fita mu nemi wani abu?”

Kai Nuri ta ɗan ɗaga musu, tasan yawo kawai suke son yi fiye da yunwar. Miƙewa suka yi suna kallon Daddy da yasa hannu a aljihu yana ciro kuɗin da yasa aka yi mishi canji, ya ɗiba ya miƙa musu. Ficewa suka yi suna barin Daddy da Nuri a ɗakin. Basu jima ba Rafiq ya farka, wannan karon da kanshi ya dafa gadon yana miƙewa zaune tare da kwantar da bayanshi jikin abin gadon. 

“Rafiq…”

Daddy ya fara, Nuri ta dumtsa hannunshi alamar ya yi shiru, tunda likita ya ce a barshi duk in ya farka ya fara yin magana da kanshi tukunna a yi mishi. Kallon su Rafiq yake yi yana jin ƙwari a jikinshi fiye da jiya, maƙoshin shi duk da yana jin kamar akwai raunuka a ciki yana mishi kamar zai iya fito da sauti ba tare da wahala ba. Kawai kanshi har lokacin yanajin nauyin shi har cikin wuya. Likita ne ya shigo yana ma su Nuri sannu tukunna ya ƙarasa wajen Rafiq ɗin. 

Duba shi yake yana mishi magana da turanci, da kai Rafiq yake amsa Eh ko Aa na tambayoyin da likitan yake mishi. File ɗin Rafiq ɗin da ke ajiye jikin wani ɗan abin sakawa da ke haɗe da gadon ya ɗauka yana yin ‘yan rubuce-rubuce tukunna ya mayar ya ajiye yana faɗa wa Rafiq ɗin cewar ya ci wani abu don ya samu ƙarfin jikinshi kafin ya ɗan ɗaga ma su Nuri kai yana ficewa daga ɗakin. Kallon su Rafiq ya yi yana murza hannunshi da yake jin yana ciwo. 

“Nuri…Daddy yana nan dama?”

Kujeru suka ja suna matsawa kusa da Rafiq ɗin don maganarshi can ƙasa take sosai. Ba su ji me ya ce ba. Hakan ya kula da shi yasa shi sake maimaitawa. 

“Aa yau suka zo.”

Bai yi ƙoƙarin ɗaga mata kai cewar ya gane ba saboda nauyin kan da yake ji, sake ƙarewa ɗakin kallo yake yi yana son tuna abinda ya faru amma ya kasa. 

“A ina nake?”

Ya tambaya, don tun jiya ya kula likita ko ɗaya baƙar fata bai gani ba. 

“India.”

Daddy ya amsa mishi, ɗan jim ya yi yana tunanin rashin lafiyar da zai yi da zata saka a kawo shi har India, duk asibitocin da ke Abuja. 

“Me ya same ni? Nuri me yake damuna haka?”

Ya ƙarasa maganar a gajiye. Yana runtsa idanuwanshi tare da sake buɗe su. Kallon Daddy Nuri ta yi zuciyarta na wata irin dokawa da tambayar Rafiq ɗin, fuskar Samira ta cika zuciyarta kafin ta Imaan ta bayyana. Daddy take kallo da ya yi magana. Shi ma kallonta yake yi a tsorace don ta fishi sanin yadda zata gaya wa yaran abubuwa. Baisan yadda zai yi magana irin wannan dasu ba. 

Ganin yanayin su yasa Rafiq faɗin, 

“Nuri… Me ya same ni?”

Kallonshi ta yi tana ƙoƙarin tarbe hawayen da suka fara cika mata idanuwa. Ta buɗe baki ya fi sau uku tana rasa kalaman da zata yi magana da su, jin turo ƙofa ya sa ta sauke wani numfashi mai nauyi. Aroob ce ta shigo da sallama hannunta riƙe da ledoji, Fawzan na biye da ita shima riƙe yake da ledojin. Ganin Rafiq a zaune yasa su duka sakin ledojin dake hannunsu. 

“Yayaa…”

Aroob ta faɗi muryarta na rawa, idanuwan ta cike da hawaye. Ta kasa ƙarasawa inda Rafiq ɗin yake, tsaye take tana kallonshi hawaye na zubar mata, ta kasa motsa ƙafafuwanta, sai yanzun take jin tashin hankalin da take ciki na rabuwa da ita, tare da hawayenta akwai taya Rafiq ɗin jimamin rashin da yake shirin fuskanta. Fawzan kanshi da rawar jiki ya ƙarasa yana zama kusa da Rafiq ɗin. Wani irin numfashi ya sauke. 

“Yaya….Yayaa karka ƙara bamu tsoro haka…” 

Ya ƙarasa yana maida numfashi, jikinshi gaba ɗaya ya yi wani irin sanyi, kanshi ya kwantar a jikin Rafiq ɗin, ko ina jikinshi ɓari yake yi, duk wani tsoro, wani tashin hankali da raɗaɗin rashin su Samira daya ke zaton ya gama dealing da su ashe ƙarya ne, komai ɓoyewa ya yi a wani waje daban sai yanzun yake danne shi ta ko’ina. Hawaye ke zubar mishi kamar an buɗe su. Wani irin tsoro ke shigarshi da bai taɓa sanin akwai irin shi ba a duniya. 

Basu rasa Rafiq ɗin ba kenan, amma ɗanɗana musu cewar rayuwar duka ta aro ce ya isa ya ƙara musu imani. Kuka yake kamar ƙaramin yaro, kallon shi Rafiq yake, ya kasa ko ɗaga hannunshi ballanta ya lallashe shi, inya kalle shi sai ya kalli Aroob da ke tsaye tana saka hannu tana goge hawayen da sun ƙi daina zubar mata. Gaba ɗaya sun sa zuciyarshi na dokawa don ya fara tunanin wani abu ne babba ya same shi da ya kasa tunawa. Hannu ya miƙa wa Aroob, kamar hakan take jira ta tako zuwa inda yake tana kama hannun nashi. 

Zaunar da ita ya yi a gefenshi yana girgiza mata kai alamar ya isa haka ta daina kukan, kai take ɗaga mishi tana goge hawayenta, kamar sake buɗe su ake yi, kukan da suke yi ne ya ba hawayen Nuri damar zuba. Sosai take kuka da abinda ya faru da su, da kuma abinda yake shirin faruwa, watanni suka yi suna jinyar zuciyoyin su, sun fara sauƙi, na Rafiq ɗin ne yanzun za su fara, tana kuma tausayawa halin da zai shiga. 

Sun jima suna kukan kafin su nutsu, Fawzan idanuwanshi sun kumbura, haka Aroob ma. 

“Sannu Yayaa…”

Ta faɗi muryarta a dakushe, ɗan murmushi Rafiq ya yi mata. 

“Ki sha ruwa, ki miƙo wa Fawzan ma.”

Ruwan ta tashi ta ɗauko, ƙananun robobi ne don haka ta ɗauki biyu, tana riƙe ɗaya ta miƙa wa Fawzan ɗaya, kurɓa ta yi ta mayar ta rufe, shikam ya kusan shanyewa duka ya yi. Numfashi Rafiq ya sauke yana kallon su. 

“Ku faɗa min abinda ya same ni kawai, meye ya lalace a cikina? Ƙoda? Hanta?” 

Kallonshi suke kamar ya samu taɓin hankali, da sauri ya saka hannunshi cikin rigarshi yana laluba cikinshi ko zai ji ɗinki, aikam ɗinkin ya ji ta gefen cikinshi da sauri ya ɗaga rigar yana dubawa yaga wani irin ciwo ne har ta haƙarƙarin shi. Jinin da yake tunanin ya zuba ta sanadin ciwon na saka hanjinshi yamutsawa, hankalinshi ya tsayar kan Nuri da ke mishi wani irin kallo daya kasa fassarawa. Hakan na saka shi danna haƙarƙarin shi a hankali, sai ya ji kamar ƙasusuwan sun yi laushi. 

“Ƙashin haƙarƙarina aka sake, na roba ne ko?” 

Ya ƙarasa tambayar muryarshi na sauka can ƙasa saboda tashin hankali. Daddy ne ya fara dariya kafin su Aroob, Fawzan har da ƙwalla, taya za a saka wa mutum haƙarƙarin roba. Dariya suke mishi sosai, da murmushi a fuskarshi ya ce, 

“Ku faɗa min don Allah. Me ya faru wai? Na kasa tuna komai wallahi.” 

“Ba abinda ya sami ƙasusuwanka, ko kayan cikinka.” 

Cewar Daddy, Nuri na ɗorawa da, 

“Hatsarin mota ka yi.”

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un.”

Rafiq ya faɗi, yana sake duba ƙwaƙwalwar shi ko zai tuna abinda ya faru, daƙuna fuska yake yi saboda baya ganin komai banda fili, baya tuna komai. 

“Mu ga wayarka.”

Ya ce wa Fawzan, wayar Fawzan ya miƙa wa Rafiq ɗin yana duba kwanan watan ranar, sannan yaba Fawzan wayarshi. Har cikin ƙasusuwan jikinshi yake jin akwai abinda ya rasa amma ya kasa tuna ko menene. Aroob idanuwanta ta sauke cikin na Fawzan tana ware mishi su cike da alamar tambaya, nashi Fawzan ya ware mata shima don tambayoyin yake da su. Ga kuma wani tsoro da yake ji a gefen zuciyarshi. 

“Na kasa tunawa. Na kasa tuna komai.”

Rafiq yake faɗi da wani nisantancen yanayi a muryarshi. Miƙewa Daddy ya yi ya fita zuwa office ɗin likitan ya ƙwanƙwasa yana shiga. Waje ya samu ya zauna ya soma magana da likitan cikin harshen turanci yana faɗa mishi Rafiq ya kasa tuna yadda akai ya yi haɗari. A nutse likitan ya soma yima Daddy bayani yadda zai fahimta. 

“Ya samu buguwa ne sosai a kanshi. Mun ji tsoro daga farko kar a ce raunukan zai iya bashi matsalar da tafi wannan. Zai iya yiwuwa mantuwar tashi gajera ce, wahalar daya sha ce, ƙwaƙwalwar shi yanzun take dawowa. Tunanin shi zai iya dawo mishi ko da yaushe. Karku matsa mishi da maganganu, kar kuma ku faɗa mishi abinda bai tuna da kanshi ba, zai iya bashi matsala mai girma in har bada kanshi ya tuna ba…gab yake da faɗawa cutar mantuwa akai-akai, ƙwaƙwalwar shi bata buƙatar tashin hankali koya yake.” 

Bayanin likitan ya tsorata Daddy sosai, da ƙyar ya iya komawa ɗakin yana jan Nuri suka fito yai mata bayani. Ita kanta zuciyarta bugawa take cike da tashin hankali. 

“In bai tuna bafa gaba ɗaya?”

Ta tambayi Daddy muryarta na rawa. 

“Zai tuna a hankali.”

“Saimun faɗa wa su Fawzan kar wani yai suɓutar baki.” 

Nuri ta ce. Girgiza mata kai Daddy ya yi. 

“Tsorata zasu yi in suka ji.”

“Sun ga tashin hankalin kusan rasa ɗan uwansu, wannan ba komai bane ba, ya kamata su sani.” 

Jinjina kai Daddy ya yi yana yarda da maganar Nurin, baya tunanin abinda za su ji zai tsorata su fiye da hatsarin Rafiq ɗin. 

***** 

Har aka sallamesu babu abinda Rafiq ya tuna game da haɗarin da ya yi, yana tuna duk wani abu daban amma banda wanda ya danganci Samira. Likitocin sun tabbatar musu da cewar memory ɗinshi na Samira ya mishi tsauri da yawa, shi yasa wani ɓangare na ƙwaƙwalwar shi ya ɓoye mishi shi, yana faruwa sosai a yanayi irin nashi. Zai iya tunawa, zai kuma iya ƙin tunawa gaba ɗaya, amma a shawarce kar wanda yai ƙoƙarin tuna mishi don gudun samun matsala. Yana tare da abinda a likitance ake kira PTSD (post traumatic stress disorder). 

Dama Rafiq a ƙagauce yake da ya koma gida, duk wata kulawa zai iya ƙarasa samunta a Nigeria yake tunani, duk da haka sai da suka ga babu wata matsala za’a iya sallamar shi tukunna suka sallame su, bakinshi ya ƙi rufuwa lokacin da suka fito daga asibitin su, shi, Fawzan, Aroob, Nuri da Daddy. Naadir bai samu zuwa ba sai dai waya da suke yawan yi haka ma Zafira. 

“Allah so nake kawai in jini a gida.”

Rafiq yake faɗi. Murmushi Fawzan ya yi. 

“Ai an kusa…”

Taxi ɗin da suka kira ta iso don ƙarasawa da su Airport, duka kayansu anyi loading, Daddy ya shiga gaba don yabar Nuri da yaranta a baya. Sai dai me Rafiq tsaye yake ya ƙura wa motar idanuwa, zuciyarshi na wata irin dokawa kamar zata fito daga ƙirjinshi. 

“Rafiq ka shiga.”

Nuri da ke tsaye ta faɗi, sai da ya ɗan kalleta tukunna a tsorace ya kama murfin motar ya runtsa idanuwanshi da sauri saboda wani irin haske da ya gilma mishi ta cikin idanuwa yana sa kanshi sarawa kamar zai rabe gida biyu. Baya son su gane don ba zai koma asibitin nan ba gida yake son komawa, da ƙyar ya shiga motar yana zama kusa da Fawzan. 

“Lafiyarka dai ko?”

Fawzan ya tambaya cike da kulawa. 

“Lafiya.”

Rafiq ya amsa da ƙyar saboda kanshi da yake ji kamar zai rabe biyu, cikin kujerar ya kwanta sosai yana runtsa idanuwanshi gam, yanajin Aroob da Nuri suka shigo motar, ana tayarwa ya ji ƙarar kamar cikin ranshi, sake runtsa idanuwanshi ya yi gam. Ana fara tafiya kanshi ya ci gaba da sarawa, bai san ya riƙo hannun Fawzan dam ba, har zufa yake ji tana tsattsafo mishi. Fawzan na jin riƙon da Rafiq ɗin yai mishi kamar zai karyashi, zai yi ƙarya in yace matsalar Rafiq ɗin bata tsaya mishi ba. 

Ya fi kowa fahimtar me yake damunshi, bai taɓa cin karo da marar lafiya mai fama da matsalar ba, hakan baya nufin baisan haɗarinta ba, gaba ɗaya rayuwar Rafiq ta canja, zai ji sauƙi amma ba’a warke ma PTSD, zai ta fama da rashin tabbaci, rashin wadataccen bacci, yawan tunani marasa kan gado, fushi da kuunci lokaci zuwa lokaci da abubuwa barkatai da baya son tunawa. 

Cikin yanayoyin da Rafiq ɗin zai iya tsintar kanshi a ciki ya haɗa da irin wannan, da wahala ya ƙara dawowa dai-dai duk in ya shiga mota. Addu’ar duk da ta zo zuciyar Fawzan ɗin ita yake yi ma Rafiq har suka ƙarasa Airport ɗin. Rafiq kuwa duk wani ƙoƙari yake yi don jure sarawar kan da yake fama da ita, amma suna lura da shi , har Daddy da ba zaune yake da su koda yaushe ba ya fahimci Rafiq ɗin na cikin wani yanayi dauriya kawai yake yi. 

Nigeria

Tunda suka dawo yake jin canjin daya samu a rayuwarshi. Yana jin akwai wani fili a zuciyarshi daya kamata ace akwai gini a wajen, amma babu komai yanzun, ya rasa abinda ya sameshi haka, in yai ƙoƙarin tunawa kanshi sarawa yake yi. Ga su Nuri kowa so yake ya ga ya koma dai-dai shi yasa yake ta daurewa. Sai da ya shiga ɗakin shi yaga komai ya canza tukunna ya ƙara tabbatar da abinda ya faru ba ƙarami bane ba. Akwai abubuwa da yawa da babu a cikin ɗakin, duk da in ba shi da yasan ɗakinshi ba, kowa zai ce akwai komai na buƙata. 

Yana buƙatar waya, sai zuwa gobe zai yi duk wannan, ruwa ya shiga ya watsa ya fito yayi sallar Asr tukunna ya kwanta kan gadon. Yana lumshe idanuwanshi ya ji ana ƙwanƙwasa ƙofar. Numfashi ya sauke. 

“Ko menene ya jira Fawzan. Hutawa zan ɗan yi.”

Rafiq ya faɗi don ya ji yanayin ƙwanƙwasa ƙofar, in Aroob ce sai ciwon kanshi ya ƙaru. 

“Ni ne Rafiq…”

Ya ji muryar Muneeb.

“Shigo.”

A hankali Muneeb ya turo ƙofar yana shigowa ɗakin tare da yin sallama. Dama Fawzan ke faɗa mishi yadda jikin Rafiq ɗin yake. Da yana da wasu kuɗine babu abinda zai hanashi zuwa har India ya dubashi lokacin, don Rafiq ya mishi komai a rayuwarshi, ya cancanci dukkan karamci daga wajen Muneeb ɗin. Shi yasa Fawzan na kira ya ce mishi sun dawo ya taho, a falo Nuri take faɗa mishi halin da ake ciki. Sosai jikinshi ya yi sanyi. Kan kujera ya zauna yana hango Rafiq ɗin da ke kwance. 

“Rafiq…”

Muneeb ya kira a tausashe. Tashi zaune Rafiq ɗin ya yi yana dafe kanshi da duka hannuwanshi biyun. 

“Ka koma ka kwanta abinka. Sannu. Ya jikin? Fawzan ne yake faɗa min kun dawo.” 

Ɗan ɗagowa Rafiq ya yi, sai lokacin Muneeb ya ga ramewar da ya yi, da kuma tabon yankan da ke gefen wuyanshi ya shiga har wajen kafaɗarshi da alama. Jikinshi ne ya ƙara yin sanyi, lokaci ɗaya in Allah ya tashi hautsina maka duniyar zaka gane kai ɗin ba komai bane ba, yanzun Rafiq bai ma san ya rasa matarshi da ‘yarshi ba, yana cikin wani ruɗani da Allah ne kawai zai fitar da shi. 

“Alhamdulillah. Ya aikin?”

Rafiq ya amsa da ƙyar. Hakan yasa Muneeb miƙewa. 

“Ka kwanta ka huta, dama na zo in ga ya jikin naka ne. Gobe in sha Allah mun dawo da su Faruk mu ƙara duba ka.” 

Kai kawai ya iya ɗaga wa Muneeb ɗin da ya juya yana ficewa daga ɗakin. Komawa Rafiq ya yi ya kwanta, kamar amai yake ji, duniyar duka ta mishi cunkus. Komai baya jin daɗin shi, bacci yake so ya yi ko zai samu sauƙi amma abin ya gagara. Sai juye juye da yake faman yi da tunanin da ba zai ce ga kalarshi ba. Har aka kira sallar Magrib, alwala ya yi ya nufi masallaci, da yake sabon shi ne acan yai zamanshi har akai isha’i tukunna ya fara tunanin tasowa ya dawo gida. 

Amma yana tsoron suɓucewar da nutsuwarshi zata yi. A masallacin ƙuncin da yake ciki ya ji ya yaye, har wani sanyi-sanyi ke ratsa zuciyarshi. Yanayin shirun na sanyaya wani ɓangare a tare da shi. Da ƙyar ya iya tashi ya fito, tunda babu waya a hannunshi, Nuri zata damu da sanin inda yake. Yana shiga gida ya samu su dukansu a falo, Daddy ne kawai baya nan. 

Sannu da zuwa Aroob da Fawzan sukai mishi yana amsa da, 

“Yawwa. Sannunku da gida. Nuri nikam kwanciya zan yi.” 

“Karka kwanta baka ci komai ba Rafiq. Ko Tea ne ka daure ka sha.” 

Nuri ta faɗi cike da kulawa. Ɗan daƙuna fuska Rafiq ya yi, baya jin shan shayi, a kwanakin nan ya sha shi harya fara fita daga kanshi. 

“Me kuka ci?”

“Dankali Aroob ta soya mana da ƙwai.”

Fawzan ya faɗi. Girgiza kai ya yi yana maida hankalinshi kan Aroob. Gara mishi shayin, 

“Aroob haɗa min Tea ɗin, karki samin Sugar amma.” 

“Kar a saka Sugar? Ko kaɗan?”

Ta tambaya tana kallon shi, kai ya girgiza mata yana samun waje ya zauna kusa da Nuri. 

“Kin manta harshen su yana da matsala shi da Naadir.” 

Fawzan yace, wuce Aroob ta yi tana haɗo mishi Tea ɗin ta kawo. Karɓa ya yi ya kurɓa, zaƙin Milo ɗin yana neman mishi yawa.

“Zaka rakani in siyo waya gobe in Allah ya kaimu Fawzan, ko da yake za ka fita aiki ko? Sai mu je da Aroob.” 

Rafiq ɗin yake faɗi yana ci gaba da kurɓar Tea ɗin shi. Da sauri Aroob ta ce, 

“Eh mu je tare, ni ba zan je makaranta ba dama.” 

“Nima ai sai Monday fa in Allah ya kaimu zan je aiki…” 

“Da ni za’a je ko Yaya. Tare zamu fita.”

Cup ɗin Rafiq ya ajiye yana miƙewa. 

“Sai mu je mu duka.”

Ya faɗi fuskarshi babu walwala yana wucewa yabar falon, ko sai da safe bai musu ba, bai ma zo a ranshi ba kuma. Ɗaki ya wuce, yana shiga kayan jikinshi kawai ya sake don yana jin sun mishi nauyi ya ɗauki magungunan shi da kala biyu ne kawai ya sha tukunna ya kwanta, yasan da taimakonsu ne ma bacci ya ɗauke shi. 

***** 

Da ƙyar yai Subhi don magungunan basu sake shi ba har lokacin. Daya koma bacci sai wajen sha ɗaya saura tukunna ya tashi, kafin ya yi wanka ya shirya sha biyu ta kusa. Yunwa yake ji sosai, yana sauka ƙasa kitchen ya wuce yana buɗe-buɗe kenan Aroob ta shigo. 

“Aroob bani wani abu in ci. Yunwa nake ji.”

Dariya ta yi. 

“To. Ina kwana.”

“Lafiya ƙalau.”

Ya amsa a taƙaice. 

“Ya jikin ka?”

Numfashi ya sauke

“Ki bani abinci nikam. Jikin zai dawo in baki bani wani abu na ci ba.” 

Rafiq ya faɗi don hanjinshi har ɗaurewa suke yi. Dariya Aroob take mishi, farfesun kayan ciki ne, Nuri ce ta yi wa Daddy, sanin halin Rafiq ɗin ba nama yake iya ci ba tasa aka yi mishi pancake. Duk da haka sai da Aroob ta zuba mishi farfesun, ya ɗan ci, ya ci pancake ɗin ya haɗa da Tea. Sai da ya ɗan nutsu tukunna ya ce wa Aroob, 

“Ina Fawzan ɗin? Ku zo mu fita ko? Rana na yi.”

“Saidai in kirashi a waya, ya fita amma yace ba nisa zai yi ba.” 

Kai Rafiq ɗin ya jinjina mata. 

“Ki kirashi to, tunda ɗaya ta kusa in mukai sallah sai mu fita.” 

“Uhm. Sai mu ci abinci a waje ma, muje indian cuisine Yaya ko Southern fried chicken.” 

Harararta Rafiq ya yi. 

“Bana jin yunwa ni, yanzun na ci abinci.”

Daƙuna mishi fuska Aroob ta yi. Don ita bata ƙi kullum a fita waje a ci abinci ba, tana bala’in son fita kamar me, Rafiq baya barinsu da kullum tana hanya tana zaga gari abinta, ta shiga duk wasu eateries da ke Abuja ta ci abinda take so. Bata son jin bakinta shiru ko kaɗan.

“Ni ai ina jin yunwa… Tun ɗazun muka karya fa.” 

Ta ƙarasa tana turo laɓɓanta. 

“Ki ci wani abu kafin mu fita.”

Rafiq ya faɗi yana miƙewa. 

“Yaya mana… Don Allah ni dai.”

Ɗan kallonta ya yi a kasalance. 

“In zaki dameni ne kiyi zamanki.”

Ya faɗi bai jira amsarta ba ya wuce. Alwala ya ɗaura ya fito yana tafiya masallaci abinshi, karatun Qur’an ya yi har lokacin Sallah ya cika, aka yi tukunna ya fito yana wucewa gida. Fawzan da Aroob ya samu har sun fito, aljihunshi ya laluba ko zai ji credit cards ɗinshi saboda ya saba yawo dasu duk inda za shi. 

“Me kake nema?”

Fawzan ya tambaya.

“Sai mun cire kuɗi. Banda credit card ko ɗaya a jikina.” 

Ya faɗi a sanyaye. Yana tunanin abubuwan da ya rasa sai a nutse zai gane su. 

“Duka suna wajen Nuri har da Id card ɗinka ma da aka tattaro. Akwai wani a jikina muje kawai.” 

Fawzan yace yana wucewa don bayason maganar tayi nisa. Binshi a baya suka yi, sabo yasa Rafiq buɗe gidan gaba mazaunin driver ɗin ya shiga yana jan murfin motar ya rufe. Ganin haka yasa Fawzan zagayawa, yana shiga ya miƙa wa Rafiq mukullin motar. Sai dai me yana karɓarsu a hannunshi ya ji wani irin yanayi da ba zai misaltu ba, yanayin da bai taɓa sanin akwaishi a duniya ba. Zufa ce ta fara tsattsafo mishi ta ko ina har yana jin numfashin shi baya kaiwa inda yake buƙata. 

Bai ƙara shiga tashin hankali ba sai da ya saka mukullin jikin motar ya murza, ƙarar tana dira kunnenshi tana aika wa ƙwaƙwalwar shi da wani irin saƙon firgici. Steering ɗin yake kallo, tunanin murza shi na saka hanjinshi yamutsawa, wani irin jan numfashi yake yi kamar wanda asthma ta tasarma. Girgiza shi Fawzan yake yi yana kiran sunanshi amma bai ma san yana yi ba. Wani irin haske yake gani yana gilma mishi ga kanshi ya soma sarawa kamar zai rabe biyu. Ji yake kamar motar na haɗewa da shi a ciki. 

“Yaya…. Yaya ka yi numfashi don Allah… Yayaaa.”

Fawzan yake faɗi yana girgiza Rafiq ɗin cikin firgici ganin yadda gaba ɗaya ya shiga yanayi kamar zai sume. Aroob ce ma ta yi dabarar fita tana buɗe murfin motar daga ɓangaren Rafiq ɗin tare da kama hannunshi da dukkan ƙarfinta tana janyo shi, gaba ɗaya ya taho kuwa, yana dafa jikin motar ta taimaka mishi ya sakko, tukunna ya ja wani irin numfashi yana saukewa a hankali, zufa yake yi ko ina na jikinshi na ɓari. 

“Yaya sannu.”

Aroob ta faɗi a tausashe. Fawzan ne ya zagayo shima suka zuba ma Rafiq ɗin idanuwa, kafin ya dawo da hankalinshi kansu yana faɗin, 

“Na kasa tuƙi, saboda me na kasa tuƙi? Me ya sameni wai? Me ya sameni Fawzan? Aroob ku faɗa 

min abinda ya same ni.” 

Yake faɗi kamar wanda ya samu taɓin hankali, saboda hakan yake ji, yana tuna lokutta da dama da yake ɗaukar mota yana zuwa duk inda zai je, ba zai yiwu rana ɗaya don ya gwada tuƙi ya ji kamar ana shirin zare mishi rai ba. Wani abu babba ya faru da ya kasa tunawa su kuma sun ƙi faɗa mishi. Da sauri Fawzan ya ce, 

“Dama baka tuƙi, ka manta ne, kai ka ake yi duk inda zaka je.” 

Aroob ce ta fara sakin baki tana kallon Fawzan da ya ɗan ware mata ido da yake fassara ‘me kike so in yi? Ƙaryar da ta fara zuwa kaina kenan’. Hankalinta ta mayar kan Rafiq da yake wa Fawzan kallon ‘Baka da hankali ko?’ 

“Eh Yaya, baka tuƙi dama.”

Aroob ta ce muryarta na rawa. Dariya Rafiq yake yi da babu nishaɗi a cikinta, in shi bai samu taɓin hankali ba, tabbas Fawzan da Aroob sun samu in suna tunanin zai yarda da ƙaryar nan da suka yi mishi. 

“Bana tuƙi kana kallo na shiga mazaunin driver, har kana miƙo min mukullin da hannunka…” 

Rafiq ya ce yana ci gaba da dariya. 

“Da gaske baka tuƙi dama na ɗauka wasa kake yi shi yasa ka zauna a wajen.” 

Fawzan ya faɗi shi kanshi baisan me yake faɗa ba ma balle Rafiq ɗin ya fahimta. Girgiza kai Rafiq yake yana fara tafiya da baya-baya kafin ya juya da gudu yana yin cikin gida, rufa mishi baya suka yi suna kiran sunanshi amma bai sauraresu ba. Nuri ce kaɗai zata faɗa mishi gaskiya, ita kaɗai ce zata tabbatar mishi bai samu taɓin hankali ba, tun daga falon yake ƙwalla mata kira a gigice yana sakata sakkowa babu shiri, buɗe bakinshi ya yi Fawzan ya rigashi da faɗin,

“Nuri mun faɗa wa Yaya tunda can baya iya tuƙi, driver yake da shi ko mu mukai shi ya ƙi yarda.” 

Juyawa Rafiq yayi yana kallon Fawzan ɗin, kafin ya mayar da hankali kan fuskar Nuri da ke kallonsu idanuwanta cike da tsoro da wani yanayi da ba zai iya fassarawa ba. Zuciyarta ke dokawa, tana son tsaida tunaninta akan fahimtar Rafiq ya kasa tuƙi, rasa abin cewa yasa ta faɗin, 

“Da gaskiyar Fawzan, driver kake da shi.”

Kallonta Rafiq yake cike da rashin yarda, muryarshi ɗauke da hakan ya ce, 

“Nuri…”

Yana bari ta ji yadda yake son sanin gaskiya ko ya take, yadda yake neman tabbaci a wajenta, yadda yake son ta haska mishi duhun da yake cikin rayuwarshi a yanzun. 

“Ba haɗari kawai nayi ba, wani abin daban ya faru ko?” 

Ya tambaya muryarshi na karyewa. Da sauri Nuri ta girgiza mishi kai. 

“Kana tunani da yawa. Kuma baka gama samun sauƙi ba, ka bar duk wani tunani, komai zai yi dai-dai a hankali, karka gaggauta don Allah.” 

Nuri take faɗi tana ƙarasowa inda Rafiq ɗin yake tana kama fuskarshi cikin hannunta. Tana ganin ruɗanin da ke tattare da shi da yake ƙaryar mata da zuciya. 

“Komai zai yi dai-dai. Ka yarda da ni.”

Kai yake daga mata a hankali, ko duniyar zata hargitse duka, Nuri zata riƙe mishi wani ɓangare ya sani. In ta ce komai zai yi dai-dai zai yi, in ta ce dama can baya tuƙi duk da yana tuna lokutan da yake yi ɗin, zai barsu akan cewar a tunaninshi suke kawai. Basu faru ba, numfashi yake mayarwa, gaba ɗaya garin Abuja ya mishi baƙiƙirin. 

“Inason barin garin nan, na wani lokaci Nuri…ina son shaƙar wata iskar ta daban. Komai zai iya faruwa in ban bar garin nan ba.” 

Kai Nuri take ɗaga mishi. In iska yake buƙatar shaƙa daban suna da halin ba shi hakan. Muryarta can kasa ta ce, 

“Ina kake son zuwa?”

Hannunta ta kama yana saukewa daga fuskarshi. 

“Kano… Zan koma Kano na wani lokaci.”

Ya faɗi. Kai take ɗaga mishi, bai jira komai ba ya wuce yana kama hannun benen ya soma takawa zuwa sama, da duk takun da zai yi da yadda yake ƙara jin son barin garin. Don ya kasa cire tunanin wani abu mai girma ya faru da shi. In ya ɗan bar garin ƙila ya samu nutsuwar da yake ji ya rasa ko ya take.

<< Alkalamin Kaddara 19Alkalamin Kaddara 21 >>

1 thought on “Alkalamin Kaddara 20 ”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×