Skip to content
Part 21 of 52 in the Series Alkalamin Kaddara by Lubna Sufyan

Lagos

Kai-kawo yake a ɗakin ya kasa zama, kanshi kamar zai tarwatse saboda tashin hankali. Har zazzaɓi yake ji ya rufe shi. Zafira da ke kwance kan gadon daya shimfiɗa ta yake kallo, har lokacin ko motsi bata yi ba, yana kula da yadda yake dukanta, duk kuwa zuciyar da zai yi yana kiyayewa sosai. Bata taɓa bashi dalilin kishinta ba sai yau da ta kira auren shi da na ƙaddara, da ta faɗa mishi da ba don rubutun ‘alƙalamin ƙaddara’ ba ita da shi ba za su taɓa faruwa ba balle ya dinga dukanta. 

Baisan hannunshi ya kai bayan wuyanta har ya haɗa mata kai da bangon ɗakin ba sai da ya ga ta faɗi a sume jini na bin kanta tukunna hankalin shi ya dawo jikinshi, ba zai taɓa raba zuciyarshi da firgicin da ta shiga ba, hannunshi na rawa ya samu ya ɗaure mata kanta ya goge wajen kar Yusayrah ta shigo gidan ta ga jini ya ɗauke ta ya kaita ɗaki tukunna ya ɗan samu nutsuwar daya ɗauko ɗan akwatin taimakon gaggawa ya dawo. 

Ta fasa kai sosai, zai yi ƙarya in ya ce hankalin shi bai tashi ba, bai taɓa ɗaukar diploma ɗin da ya yi a fannin kula da lafiya kafin a gama mishi komai na fita ƙasar waje don karantar tuƙin jirgin sama da muhimmanci ba sai yau, da kanshi ya yi mata ɗinki yana gode wa Allah da suman da ta yi tunda ba allurar kashe zafi ke akwai ba, yasa band aid yana liƙe wajen. So yake ta tashi amma ta ƙi ko da motsawa, wajen minti ashirin kenan da faruwar abun. 

In bata tashi ba yana nufin dole sai ya kaita asibiti, baisan asibitin da zai fara ɗaukarta ya kaita da shatin duka kwance ko’ina a jikinta ba. 

“Zafira ki tashi don Allah, ba za ki yi min haka ba… Don Allah ki tashi.” 

Yake faɗi kamar wanda ya samu taɓin hankali, bata ko motsa ba balle ta nuna alamar ta ji shi. Baisan me yake shiga kanshi ba lokuta da dama, duk idan ya ɗaga hannu ya dake ta yana shiga da na sani marar misaltuwa daga baya, zai iya rantsewa zafin da take ji a jikinta bai kai wanda yake ji a zuciyarshi ba. Abu ɗaya ya sani yana sonta, a hankali ya koyi sonta kuma saboda tana kyautata mishi ba kaɗan ba. Yana dukanta ne duk idan ta bashi dalilin hakan, ya faɗa mata tun farkon auren su yana da wata irin zuciya amma bata ji ba. 

Ƙarar wayarta ya ji da sauri ya ƙarasa inda wayar take yana ɗauka. Ganin Yaya Rafiq rubuce a jiki yasa shi kasa ɗauka. Don yana da tabbacin in ya ɗauka muryarshi zata bayar da shi. Tana yankewa ya ci gaba da kira, Omeed na kallon wayar. Ƙaramin tsaki ya ja yana faɗin, 

“Ka daina kira don Allah… Me zance maka idan na ɗaga? Don Allah ka daina kira.” 

Zafira kuwa ta jima da farkawa, azabar da take ji a goshinta ne yasa ta ƙin buɗe idanuwanta, kafin ta ji surutun Omeed ɗin da kuma ƙarar wayarta. Wani irin dokawa zuciyarta take yi saboda tsoron shi, muryarshi kawai ta isheta firgici. In da wani abu a zuciyarta na faɗa mata ta cancanci duk wani duka da yake mata tunda yana faɗa mata laifinta, to gawarta za’a fitar daga gidan ba da jimawa ba. Ba zata manta ranar farko da halinshi ya fara fitowa ba. Duka satinta uku a gidanshi, ranar ne kuma za su ɗauko ‘yarshi daga gidan Anty Umma yayarshi da take aure a nan Lagos ɗin ita ma. 

***** 

Hannu ta sa ta share siraran hawayen da suka zubo mata, zuciyarta ta mata nauyi a ƙirjinta kamar dutse. Kafin ta ɗauki eyeliner tana zanawa a idanuwanta, tunda ta zo gidan nan take fama da heavy makeup saboda ta ɓoye alamun rashin bacci da yawan kukan da take yi. Jikinta da yasha dirza wajen wanka ke mata raɗaɗi, duk da hakan bai hanata jin hannuwan shi a inda bai kamata su je ba, runtsa idanuwanta take yi tana buɗe su da sauri-sauri cikin son mayar da sabbin hawayen da suke son zubo mata. 

A hankali ta ji an turo ƙofar, sai da zuciyarta tai wani irin tsalle, ta cikin mudubin take ganin shi. Tun ranar da ta fara ganin shi girmanshi yake bata mamaki. ‘Mini giant’ Kamar yadda take kiranshi a zuciyarta. Ita kam akwai dogaye a zuri’arsu, amma babu masu girma haka. Ci gaba da dokawa zuciyarta ta yi ganin yana takowa cikin shirin ƙarasowa inda take. 

“Baki gama ba har yanzun?”

Ya buƙata cikin muryarshi da kunnuwanta sun kasa sabawa da buɗewarta ta. Sai da ta haɗiye wani abu da ya yi tsaye a maƙoshinta kafin ta amsa da. 

“Na kusa…”

Tana ƙarasa zana eyeliner ɗin a ɗayan idonta kafin ta miƙe, jikinta sanye da doguwar riga ta atamfa da tai matuƙar karɓar jikinta. Ɗankwalin kayan ta ɗauka da ke ajiye kan abin mudubin. Tana jin idanuwan Omeed na yawo akan ta. Yasa ta kasa ɗaura ɗankwalin yadda take son shi, dole sai simple ta yi tana soke shi ta gefe. Kafin ta juyo tana fuskantar Omeed ɗin da yake tsaye yana jiranta. Yau satin su uku yake cika da aure, yau da safe ne kuma yake faɗa mata za su je gidan su don su ɗauko yarinyar shi. 

Abu ɗaya da zuciyarta take so game da auren, abu ɗaya na alkhairi a cikin ƙaddarar auren shi da take ɗokin haɗuwa da. 

‘Yusayrah’

Ta maimata sunan yarinyar a zuciyarta, ya mata daɗi tun ranar da ya faɗa. Ta yi mamaki da bata ganta ba sa’adda aka kawota, bata kuma tambaye shi ba, don zata iya ƙirga yawan maganar da suke yi. In ba shi ya ce mata wani abu ba, daga gaisuwa bata sake ce mishi komai. Takowa yake har sai da ya ƙaraso inda take tsaye, kanta sadde a ƙasa, a duk jikinta take jin kusancin shi da yadda girman shi yai mata rumfa, duka-duka ko kafaɗarshi kanta bai kai ba, tana da yaƙinin za’a ɗibi irinta guda biyu a jikin Omeed batare da ya girgiza ba. 

Hannuwanshi yasa yana tallabar fuskarta cikin su, idanuwanshi yake yawo dasu kan fuskarta kafin ya tsayar da su cikin idanuwanta da yake ganin sun mishi fayau, kamar akwai abinda ya kamata ya gani a ciki da babu. 

“In baki shirya dawowar Yusayrah ba ki faɗa min. Zan jinkirta har baƙunta ta sake ki.” 

Da sauri Zafira ta girgiza mishi kai tana faɗin, 

“Na shirya…”

Sakin fuskarta ya yi yana kama hannunta ya jata zuwa kan gado ya zaunar da ita kafin ya zauna a gefenta. 

“Ni da ke mun faru babu wani shiri…kamar yadda na faɗa miki a farko, fahimta nake buƙata a tsakanin mu…zamu iya tolerating juna inda akwai fahimta tsakanin mu…” 

Wani abu taji ya tsaya mata a ƙirjinta mai zafin gaske. Inba ƙaddara ba me zai ƙulleta da Omeed? Har yana faɗa mata tolerating ɗinta zai yi. 

“In ba ƙaddara ba me zai kawo ni nan?”

Ta furta maganar da take son yi a fili ba tare da ta sani ba ma, cikin bazata ta ji iskar da ta shaƙa ta ƙi wucewa, kafin duka duniyar ta tsaya mata a wuyanta da wani yanayi marar daɗi, manyan idanuwanta na sake fitowa saboda rashin iska. 

Hannuwanta da take amfani da su wajen ƙoƙarin ture hannun Omeed ɗin da yake riƙe da wuyanta ne ya ba ƙwaƙwalwar ta damar gane cewa shi ne ya shaƙe ta. Tsikar jikinta gaba ɗaya ta miƙe cike da wani irin tsoro marar misaltuwa. 

Abinda take gani a fuskarshi da idanuwanshi na sa cikin ta ƙullewa. 

“Ba a mayar min da magana da gadara…idan ni ban ji komai in miki magana a mutunce ba me zai sa ke ki ji? Matsalar farko da zamu fara samu shi ne ina faɗa kina mayar min… Musamman da yanayin murya irin haka. Bana so… Are we clear?” 

Kanta da ya ɗauki ɗumi saboda rashin iska take ɗaga mishi cikin sauri, yana cire hannun shi daga wuyanta ta ja wata iska da ta sata tari, hannunta duka biyun na jikin wuyanta tana murzawa. Zuciyar ta na kokawa wajen yarda da abinda ya faru. Ko ina na jikinta ɓari yake cike da tsoro. Har lokacin tari take yi, hawaye masu zafi na taruwa cikin idanuwanta. Hannu Omeed ya kai zai taɓa ta a tsorace ta matsa, kamo ta ya yi yana matsowa da ita jikin shi. 

“Don Allah ka yi haƙuri…”

Ta faɗi muryarta na karyewa, hawayen da take ƙoƙarin tarbewa suka zubo, rungumeta ya yi a ƙirjinshi, hannun shi ɗaya na shafa wuyanta cike da kulawa. 

“Shhhh….I am sorry. Bazai sake faruwa ba…ina da zuciya ne sosai.” 

Muryarshi da yake mata magana a tausashe yasa wasu sabbin hawayen na zubo mata, tsoron da har lokacin bai sake ta ba yasa ta yin luf a jikin shi. Riƙe ta ya yi sosai, cikin kunnenta yake mata magana da wani yare da bata san ko na wacce ƙasa bane ba. Sam maganar da yake matan yasa ƙwaƙwalwar ta ta kasa samun damar yin tunanin abinda ya faru, muryarshi ta cika mata kunnuwa da kai. Har sai da ta ðago daga jikin shi ta sa hannu tana goge fuskarta. Miƙewa ya yi ya kamata zuwa toilet. 

Da kanshi ya zame mata ɗankwalin ta tare da wanke mata fuska, ya kuma kamo hannunta ya zaunar da ita gaban mudubin. Kafin ya ranƙwafa ya sumbaci gefen fuskarta. 

“Mintina goma… Ki fito muje ko mu fasa ðauko Yusayrah wannan satin.” 

Ya furta yana juyawa, tana jin ficewarshi daga ɗakin tare da ja mata ƙofar. Da sauri-sauri take gyara kwalliyar fuskarta, wannan karin ma ta kasa samun nutsuwar tauna abinda ya faru. Mayafinta da ke kan gado ta ɗauka tana zira ma ƙafarta takalma da sauri ta fita daga ɗakin zuwa falo inda Omeed yake tsaye. Yana ganin ta ya nufi hanyar waje. Binshi ta yi a baya har suka ƙarasa inda motarshi take, shi ya buɗe mata ta shiga, ya rufe ƙofar kafin ya zagaya ta ɗayan ɓangaren shima ya shiga, ya tayar da motar suka nufi inda bata sani ba. Ko a mafarki bata taɓa zaton aure zai kawo ta garin Lagos ba. 

***** 

Ƙarar rufe ƙofarshi ta dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi. A hankali ta buɗe idanuwanta ta samu ta miƙ da ƙyar. Wayarta da ya ajiye a gefe kan kujera ta ɗauka tana dubawa ta ga jerin kiran Rafiq, sai kuma saƙo. Buɗewa ta yi ta ga ya ce ta kirashi in ta zo. Wasu hawaye ta ji sun ciko mata idanuwa da ta yi saurin goge su don bata son Omeed ya shigo ya sameta tana kuka. Zai iya sake ja mata wata matsalar ta daban. 

‘Karki kunyatani a idanuwan duniya Zafira. Ki zauna gidanki kamar kowacce mace, kinsan bazan taɓa miki zaɓin abinda zai cutar da ke ba.’ 

Maganganun Daddy na ranar da za’a tafi da ita suka dawo mata. Wani abu daya yi mata tsaye a maƙoshi take ƙoƙarin haɗiyewa. Ta yi duk wani ƙoƙarinta, amma yanzun kam har bayan zuciyarta take jin gajiya da auren nan, sosai ta gaji da auren Omeed, ko da ba zai zo ƙarshe ba a yi mishi magana ya daina dukanta. Saƙon Rafiq take ta dubawa tana jin wani yanayi da ta manta da shi. Kafin yatsunta na rawa ta soma tura mai amsa. 

‘Karka kira in kaga sakon nan Yaya. Amma ka zo ka ɗauke ni. Don Allah ka zo da sauri.’ 

Ta tura mishi zuciyarta na wani irin dokawa da har jikinta ke kyarma, saƙon ta yi saurin gogewa dai-dai shigowar Omeed, da hanzari ta ajiye wayar da ya riga da ya gani, cikin sauri ya ƙaraso yana ɗaukar wayar idanuwanshi kafe a kanta. 

“Me kikayi?”

Ya tambaya yana karantar rashin gaskiyar da ke tattare da ita. Kai ta girgiza mishi tana ware idanuwanta. 

“Ƙarya kike. Me kika yi Zafira?”

Ya ce yana duba wajen kira ya ga bata kira kowa ba, saƙo ya duba shima bai ga ta tura ba, kafin ya tsura ta da idanuwa, ganin ta sadda kanta ƙasa ya sa shi zama kusa da ita yana riƙo hannunta, muryarshi ɗauke da kashedi yake faɗin, 

“Ba za ki barni ba….kin sani ko? Mutuwa ce kawai zata raba ni da ke.” 

Kai ta ɗaga mishi kawai. Kafin ya ɗago da hannunta yana sumbata. Batasan ya akayi ba, amma kallon shi take da wani ido na daban yau, tana kuma tsoron yadda zuciyarta ta nutsu akan cewa Omeed na da taɓin hankali. Sai ma da ya kwanta a jikinta yana maimaita kalma ɗaya ta ba zata barshi ba tukunna take ƙara tabbatar da maganar da zuciyarta take faɗa mata. Gyara zamanta ta yi tana lumshe idanuwanta da addu’ar Rafiq ya samu saƙonta. 

Kano

Tunda Jawda ta kirata ta baro asibitin, hankalinta gaba ɗaya yayo gida. In ba zuwa ta yi ta ga halin da Jawwad yake ciki ba hankalinta ba kwanciya zai yi ba. Da duk wani abu da take da shi take addu’ar Allah yasa ba Mama ya gani ba, don ita sosai ta sha ganinta tana bara a titi in zata je wajen aiki. Ranar farko ne kawai ta yi kuka sosai, amma sauran ranakun haka zata bita da ido har bus ɗin da take ciki ko adai-daita sahu ta wuce da ita. 

Duk wani muhimmanci da zata bata ta riga ta gama bata shi tuntuni, alƙawari ne tai wa kanta, Mama ba zata taɓa ƙwace mata nutsuwa da daidaiton da ta samu yanzun a rayuwarta ba. Jawwad ne ya kasa haƙura har yanzun, mai sunanta ma in ya ji sai yanayin fuskarshi ya canja. Tana shiga gida ko tsayawa ta ji me su Jawda ke faɗa bata yi ba, don sallama ma a tsakiyar falo ta yi ta, ɗakin Jawwad ɗin ta wuce kanta tsaye tana ƙwanƙwasawa. Tasan yana ciki kuma ba bacci yake ba. 

“Yaya Jawwad ka buɗe nasan ba bacci kake ba.”

Izzat ta faɗi a ƙagauce tana ci gaba da ɗukan ƙofar kamar zata karyata. Ta ɗaga hannu zata sake dukan ƙofar kenan ta ga ya buɗe yana kallonta 

“Menene?”

Ya faɗi rai a ɓace, wucewa ta yi cikin ɗakin tana samun waje ta zauna. Juyawa ya yi ya kalleta, ko ya ce ta fita ba zata fita ba, ya fi kowa sanin halin Izzat, taurin kaine ta fishi nesa ba kusa ba. Don haka ya ƙarasa gefen gadonshi ya zauna. 

“Ka ganta ko?”

Izzat ta tambaya, ɗan daƙuna fuska Jawwad ya yi kafin ya ware idanuwanshi, ma’anar tambayarta na zauna mishi, kafin ya yi dariyar takaici. 

“Kin ganta kenan? Kin san bara take yi? Izzat tun yaushe kika sani?” 

Ɗan ɗaga mishi kafaɗa ta yi. 

“Za ai wata biyu dana fara ganin ta.”

“Shi ne baki taɓa tunanin ya kamata in sani ba?” 

Jawwad ya faɗi ranshi a ɓace fiye da yadda yake tun safe, zuciyarshi har wani zafi take yi kamar zata fito daga ƙirjinshi. 

“Saboda me baki faɗa min ba?”

Ya buƙata yana tsareta da idanuwanshi, da mamaki Izzat take kallon shi, ta rasa dalilin da zai sa ya damu har haka, me sanin zai mishi? Maman da ta watsar da su saboda abin duniya, da ta yanke alaƙa da su, halin da take ciki ba matsalar Izzat bane, bata kuma ga dalilin da zai sa ya zama matsalar Jawwad ɗin ba. Ta gode wa Allah da Jawda bata da hankalin tuna abinda ya faru, wannan kawai kwanciyar hankaline a wajenta. 

“Bashi da wani amfani ne. Banga dalilin da yasa zaka damu ba. Me yasa zaka damu da ita Yaya?” 

Kallon mamaki Jawwad yake wa Izzat ɗin, duk yadda take magana kamar bata damu da Mama ba yana karantar ƙaryar hakan a cikin idanuwanta, alaƙa ta ɗa da mahaifa abu ne mai wahalar fahimta, bai ce ya damu da Mama ba, bai ce ya tsaneta ba, saboda bata cancanci ko da hakan ba a wajen su, amma kuma ganinta yau ya hautsina duk wani abu a tare dashi. 

“Ina son sani saboda yau ganinta ya hargitsa min komai… Da kin faɗa min zan dinga fita da sanin zan iya ganinta.” 

Girgiza mishi kai Izzat take yi, tana jin yadda wasu hawayen baƙin ciki suke ciko mata idanuwa. 

“Bai kamata ace tana da wannan muhimmanci ba…ba zamu bata wannan muhimmanci ba.” 

Take faɗi tana ƙoƙarin tarbe hawayen don bata so su zubo ko kaɗan. 

‘Sau uku ina gwada zubar da cikin ki, gara Jawwad na so samun shi dama, ke, marwan da Jawda duka bakwa cikin tsarin rayuwata, wallahi ban tsara rayuwata da ku ba.” 

Maganganun Mama da ko a mafarki Izzat take yawan jinsu ne suka dawo mata yanzun ma, hakan ya ba hawayen da take tarbewa damar zubowa, da sauri ta sa hannu ta goge su, jakar da ke rataye a kafaɗarta tun shigowarta ta sauke, sai lokacin ta kalli ƙafar Jawwad ɗin da ke naɗe da tsumma, ƙasa ta sauko ta kama tsumman ta warware a hankali, yankan da ta gani ya shiga sosai yana ƙara jagula mata lissafi. Jawwad na kallonta ta ɗauko allura daga cikin jakar, tana kuma ci gaba da fito da abubuwan da take buƙata. 

Runtsa idanuwa ya yi yana ganin yanayin halin da Mama take ciki a zuciyarshi, ƙirjinshi na nauyi kamar an ɗora mishi dutse, duk ƙoƙarin da yake yi na ƙinyin tunaninta, ko sauran ‘yan uwanshi da ya yi kewa, lokuta da dama sukan yi mishi kutse cikin tunanin shi, zafin da yake ji a ƙafarshi na ɗauke mishi hankali daga wanda yake faruwa a zuciyarshi, yana saka shi buɗe idanuwanshi babu shiri. Ɗinke ciwon Izzat take yi muryarta can ƙasa ta ce, 

“Ka yi haƙuri ban faɗa maka na ganta ba, ko ba komai ta tsara rayuwarta da kai ya kamata ka sani…” 

“Izzat…”

Jawwad ya kira a tausashe, maganganunta na tsaya mishi. Kamar bata ji ya kira sunanta ba ta ci gaba da magana. 

“Kai kaɗai ne kake da muhimmanci a wajenta tun farko, kai kaɗai take ganin kana da wani amfani…” 

Girgiza mata kai Jawwad yake yi, baya son inda tunaninta yake shirin mayar dasu duka. 

“Izzat….”

Ya sake kira yana roƙonta da muryarshi da ta yi shiru ta bari, ɗinkin ta ƙarasa tana ɗaurewa tare da datse sauran zaren, kafin ta ɗago, hawaye masu ɗumin gaske na zubo mata. Shi yaso ta mayar da su ko’ina ne ma, bayan duk abinda Mama tai musu, yasan yadda ta jima tana ganin ko a makaranta babu wanda ya wuce ta a karatu, yadda a rayuwa ta yau da kullum take yin ta da son nuna wa duk wanda yake kusa da ita tana da amfani, haihuwarta da Mama ta yi ba a banza bane ba. 

Ƙoƙarinta yasa aka dinga mata tsallaken aji, lokaci ɗaya ta gama karatun sakandire da Jawwad ɗin, ta karanci Midwifery, saboda tanason ganin masu ciki a kullum, tana son ganin yadda rayuwarsu ta yau da kullum take kasancewa, tana son ta dinga tuna ƙoƙarin da Mama ta yi mata na ɗaukar ciki da naƙudarta da a tsawon rayuwar da ta yi tare da su take goranta mata sau ba adadi a rana. Jawwad yasan abinda Mama taima rayuwarta, amma yana son bata muhimmanci. 

“Saboda me Yaya? Kai ka faɗa min ba zamu sake bari ta taɓa rayuwar mu ba… Me yasa kake son bari ta taɓa taka?” 

Numfashi yake ja da sauri-sauri yana fitarwa, yana jin yadda yake maimaita wa kanshi maganganun da Izzat ta yi yanzun kullum da safe, amma basu zauna mishi ba, sun ƙi zauna mishi sam, Mama tana taɓa rayuwarshi duk da bata cikinta. Miƙewa Izzat ta yi, hawayenta na sake zuba, tana fahimtar yadda inhar ciwukan Jawwad ba su warke ba, zai ci gaba da fama mata nata ne, kayayyakinta ta tattara tana ficewa daga ɗakin. 

Yana kallonta bai yi ƙoƙarin hanata ba, don yasan bashi da abinda zai faɗa mata, kwanciya ya yi yana lumshe idanuwanshi, nutsuwa yake son samu ko ya take. 

“Ki ƙyale mu haka, don Allah ki ƙyale mu haka.”

Ya furta a hankali da wani irin ciwo da yake ji a ko ina na jikinshi. Kafin ya gyara kwanciyarshi yana soma karanto duk ayar da ta zo cikin kanshi, a tare da hakan ne kawai yake da tabbacin samun nutsuwa. 

Kano

Ya manta ranar ƙarshe da ya zauna waje ɗaya haka. Duk kuwa kalar ciwon da ya ji ko baibar asibiti ba zai fita wajen asibitin ya sha iska, wannan ne karo na farko da harsashi ya huda jikinshi, ba kuma abu bane mai sauƙi sai yanzun yasan hakan. Ko tashi zaune zai yi sai ya ji shi har cikin ranshi. Tun ɗazun da Tariq ya tafi daga asibitin yake neman wayarshi amma baya ɗagawa. Hankalinshi ba zai kwanta ba sai ya ji halin da yake ciki. 

Sake kira ya yi a karo na babu adadi, har ta kusa yankewa tukunna Tariq ɗin ya ɗaga yana yin shiru ta ɓangaren shi. 

“Tariq…”

Ashfaq ya kira kamar mai son tabbatarwa ko Tariq ɗin ne ya ɗaga wayar ko ba shi bane ba. 

“Ina ji.”

“Inata kira baka ɗauka ba.”

Jim Tariq yayi kafin ya ce, 

“Sai yanzun na gani.”

Rasa abinda zai faɗa wa Tariq ɗin ya yi, maganganu ne a ƙirjinshi da baisan ta yadda zai fara fito da su ba, don fitar su na nufin ya rasa control ɗin da yake da shi akan su, yana kuma nufin buɗe wasu shafuka da ya zaɓi su zauna a rufe har abada. 

“Yayaa…”

Tariq ya kira muryarshi cike da wani yanayi. 

“Tariq ina jinka”

Ashfaq ɗin ya amsa, yana jin numfashin da Tariq ɗin ya sauke ta cikin wayar kafin ya ce, 

“Na karya alƙawarin mu.”

Baisan amsar da ta kamata ya ba Tariq ɗin ba don haka ya yi shiru. 

“Na faɗa maka maganganu ɗazun ko?”

Tariq ya tambaya cike da dana sani a muryarshi. 

“Ka dawo asibitin, ka zo mu yi magana”

Ashfaq ya faɗi. 

“Ina cikin asibitin Yaya. Bansan ya akai ban fita ba. Ina nan tun ɗazun.” 

Kai Ashfaq ya jinjina

“Ka zo to, yanzun fa.”

Ya ƙarasa yana katse kiran ba tare da ya ji amsar Tariq ɗin ba. Ruwa kawai ya ɗauka ya sha, yana ajiyewa ya ji an turo ƙofar tare da yin sallama. A hankali ya amsa, yana kallon Tariq ɗin har ya shigo ya ja kujera ya zauna, yana ƙin yarda ko fuskar Ashfaq ya kalla, kunya yake ji, abinda ya jima bai ji ba, yana ƙoƙari wajen ganin bai koma rayuwarshi ta baya ba, amma akwai wahala sosai, kullum jikinshi kamar ana tsotse mishi jini yake ji, kanshi kamar zai tarwatse, numfashi ma wahala yake mishi ba tare da ƙwayoyi, cocaine ko syrup ba. 

Kowacce rana a wahalce yake yin ta, maganin tarin baya mishi, indai baya haɗa da wani abu bane baya kaishi duniyar da yake son jinshi, ya wa kanshi kaɗan sosai. Kuma a tsawn rayuwarshi bai taɓa shan wani abu a gaban Ashfaq ba, yaune karo na farko da hakan ya faru, shi yasa yake jin nauyin Ashfaq ɗin. 

“Na san baka daina ba Tariq, na sani.”

Ashfaq ya ƙarasa muryarshi can ƙasan maƙoshi, duk da baya shan komai yana mu’amala da masu sha ko da yaushe, da ya kalleka yake ganewa. Idanuwan Tariq kawai in ya gani yana sanin ya sha wani abu ko bai sha ba. 

“Yayaa….”

Tariq ɗin ya fara, Ashfaq na katse shi da, 

“Ina son baka haƙuri kan abubuwa da dama, amma bazan iya ba, akwai abubuwan da ban cancanta ka yafe min su ba, ban ma da ƙarfin tunanin su ballantana in roƙe ka akan su.” 

Wani abu Tariq ya ji ya tokare mishi zuciya, saboda yasan abinda Ashfaq ɗin yake magana akai, yasan abubuwan da suka shafi Yasir ne da Arfa, su biyu ne abubuwan da Ashfaq yake tsoron ziyarta ko a tunanin shi, kanshi Tariq ya girgiza yana ƙoƙarin raba shi da tunanin su shima, saboda babu abinda hakan zai yi banda saka shi son ya sha abinda zai ji sun ɓace mishi ɓat. Jin Ashfaq ya yi shiru, hakan yasa Tariq faɗin, 

“Ba lallai ka yarda ba, amma na ganshi, wallahi na ga Yaya Yasir.” 

Numfashi Ashfaq ya sauke, idan Tariq na jin ya ga Yasir ne ba zai ja maganar ba, ba zai ƙara musa mishi ba, zai barshi akan cewa ya ga Yasir ɗin, duk kuwa yadda tunanin hakan ke shirin rusa mishi katangun da ya yi wa zuciyarshi da Yasir. Da sauri ya ce, 

“Altaaf ya kirani”

Hakan yasa Tariq ðagowa babu shiri yana kallon Ashfaq ɗin 

“Ya kirani.”

Ashfaq ya sake faɗi, wata ‘yar dariya mai sautin takaici Tariq ya yi. 

“Me kuma yake so? Me yake nema?”

Ɗan ɗaga mishi kafaɗa Ashfaq ya yi, don ba wai zai faɗa wa Tariq ɗin abinda Altaaf ya ce bane, ya yi amfani da zancen Altaaf ɗin ne don guje wa maganar Yasir. Girgiza kai kawai Tariq ya yi cike da takaici, gara ma shi yana zumunci da su Hamna har yanzun. Baya tunanin banda shi akwai sauran wani da suka haɗa jini da shi a rayuwar Ashfaq, ya jima da datse zumunci da kowa. Yaune karo na farko a shekaru da dama da yai mishi maganar Altaaf. 

Ya kuma gane abinda yasa hakan. 

“Yaushe rabon da mu yi magana mai muhimmanci Yaya? Yaushe rabon da hakan ya faru? Tunda ka ɗauko shi ka shigo da shi rayuwar mu kamar zai iya maye mana gurbin da muka rasa, ko don sunan su ya zo ɗaya?” 

Lumashe idanuwanshi Ashfaq ya yi yana buɗe su, abinda yake ƙoƙarin guje wa ne yake shirin faruwa. Tariq ba zai bar maganar nan ba, ƙaddara ta shigo da Yasir rayuwar shi, bai ɗauko shi don ya maye mishi gurbin Yasir ɗin da ya rasa ba, duk da in zai faɗa wa kanshi gaskiya zai ce hakan yaso yi amma bai faru ba, wajen Yasir yana nan da fili a zuciyarshi da babu wanda ya kusanta ballanta ya samu wajen zama. Turo ƙofar da aka yi ne ya tserar da shi daga tambayoyin Tariq da bai shirya amsawa ba. 

Juyawa Tariq yayi ya ga Yasir ne. Dariya ya yi yana miƙewa, 

“Yanzun nake maganar ka.”

Da idanuwanshi Yasir yake tambayar Ashfaq ɗin me yake faruwa kafin ya mayar da idanuwanshi kan Tariq ɗin. 

“Ina wa Yaya maganar yadda ya ɗaukoka don ka maye gurbin Yaya Yasir ne.” 

Numfashi Yasir ya sauke, yana jin tsanar shi a muryar Tariq ɗin kafin ya ganta cikin idanuwanshi, abu ɗaya ya sani akan Yasir ɗin da yake magana, ya ɓace shekaru da dama da suka wuce ba’a ganshi ba, kuma daga bakinsu ya ji har an mishi sadakar mutuwa, bayan hakan baisan sauran labarin ba, kamar yadda baisan abubuwa da dama na rayuwar Ashfaq ta baya ba. Saboda Ashfaq yake ɗaukar duk wani laifi da Tariq ɗin zai ɗora mishi. Ya kuma fara gajiya da hakan. 

“Bana cikin yanayin jin shirmenka Tariq.”

Yasir ya faɗi a gajiye yana tura ƙofar ya shigo cikin dakin. 

“Au shirme nake yi kenan?”

Tariq ya tambaya ranshi a ɓace, ba zai ce ga lokacin da ya fara tsanar Yasir ba, kawai ya fara ne, ba shi da wani dalili mai muhimmanci, ba shi ya shigo rayuwarshi ba, Ashfaq ne ya janyo shi, ba shi yace Ashfaq ya dinga gaya mishi sirrikanshi da Tariq ɗin waɗanda bai sani ba, duka laifin na Ashfaq ne, amma ba zai iya kallon idanuwan Ashfaq ya gaya mishi haka ba, ba zai iya tsanar Ashfaq ba, shi yasa ya zaɓi ya tsani Yasir, ya zaɓi ya raba ciwon da yake ji tare da Yasir ɗin. 

Zama Yasir yayi yana kallon Ashfaq, yana son nuna mishi da yai wa Tariq ɗin magana, da gaske yake ba shi da lokacin shirmen shi, yana da abubuwa da suka fi yarintar Tariq ɗin muhimmanci. 

“Tariq ya isa haka.”

Ashfaq ya faɗi a tausashe. Dariya Tariq ya yi cike da rashin yarda da abinda ya faru yanzu nan, da yadda Ashfaq ya zaɓi Yasir sama da shi. Girgiza kai kawai ya yi yana ficewa tare da doko ƙofar kamar zai karyata, numfashi Ashfaq ya sauke, kafin Yasir ya ce, 

“Ka dai-daita matsalarka da Tariq…na gaji da yadda yake gaya min maganganun da ya kamata ya faɗa maka, na gaji sosai.” 

Shiru Ashfaq ya yi, bai da abinda zai ce, ta wannan ɓangaren yanada rauni sosai, ba zai iya fuskantar Tariq ba. Yasir yasan ba magana zai yi ba don haka ya ce, 

“Bansan tsautsayin da ya sa ka harƙalla da su Seyi ba wallahi. Mugu ya kira ni ðazun in kana nan in ce maka ka ɓace na wani lokaci.” 

Hannu Ashfaq yasa yana murza goshin shi da yake jin alamun ciwon kai. In har mugu ya kira, yana da tabbacin rayuwarshi Seyi yake nema, in ba Allah ne ya ƙaddara mishi ƙarar kwana nan kusa ba zai yi duk ƙoƙarin shi na ganin bai tafi da wuri ya bar Tariq ba. 

“Meya kamata inyi?”

Ya tambayi Yasir din

“Ko maganin wu ƙa babu a jikinka amma ba ka tunani kafin ka yi abu.” 

Yasir ya faɗi ranshi a ɓace, jinjina kai Ashfaq ya yi cike da yarda da maganar Yasir ɗin, lokuta da dama shi ne ƙwaƙwalwar shi, ba dkn shi ba da tuni rayuwar Ashfaq ɗin ta salwanta. Ko yaushe wani abu zai faru sai Yasir ya tuna mishi da yadda yake fama da shi akan ya shirya kanshi ya ƙi. Ba zai sha komai ba, rayuwarshi daga ciki a hargitse take, babu abinda bai canja ba, idan akwai abinda yake dashi da bai canza ba shine jikin shi, yana jin ciwuka, suna yin jini suyi raɗaɗi har ma ya yi jinya, suna kuma yin tabo da yake gani a kullum. 

Bazai taɓa canja hakan ba, ya rabu da abubuwa da dama ciki har da mutuncin shi da tausayi, daga ranar da wani zai ɗaga mishi wuqa taƙi kamashi zai rabu da sauran humanity ɗin da ke tare da shi, zai ƙarasa jin banbancin da ke tsakanin shi da sauran mutane. 

“Bazan iya ba Yasir, bazan iya rabuwa da wannan ɓangaren a tare da ni ba, ina buƙatar inga mutum ne ni wasu lokuta.” 

Kallon shi Yasir yakeyi, sannan ya ce, 

“Sai ka zubda jini ne zaka tabbatar mutum ne kai?” 

A hankali Ashfaq ya ɗaga mishi kai, ba lallai ya fahimta ba ya sani, amman shikam yana buƙatar hakan. 

“Baka da hankali Faq. Kasan haka ko?”

‘Yar dariya Ashfaq ya yi, shi da hankali sun yi hannun riga da jimawa. Girgiza kai kawai Yasir ya yi. 

“Bari mu ga me zai faru daga yau zuwa gobe…” 

Kai Ashfaq ya jinjina, yasan Yasir zai kula da komai, zai gyara kuskuren da ya yi. Shiru ya yi yana jiran ya ji Yasir ɗin ya mishi wani bayani daban kuma. 

“Meye kake kallona?”

Yasir ya buƙata. Girgiza mishi kai Ashfaq ɗin ya yi yana jin zuciyarshi na motsawa cikin wani yanayi da ya zame mishi baƙo, kafin Yasir ya ce, 

“Oh, kai ni ban samu lokacin zuwa wajen mahaukaciyar nan ba.”

Numfashi Ashfaq ya sauke.

“Na faɗa maka sunanta Nudra, ba mahaukaciya ba ce.” 

“Na jika da farko ai.”

Yasir ya faɗi cike da rashin kulawa, sai yanzun ma ya tuna ya wa Ashfaq ɗin alƙawarin zuwa ya dubata, ya yi abubuwan da suka fi haka muhimmanci ne, kuma ma dai abin bai faɗo mishi ba sai yanzun. Zai yi ƙarya in ya ce baya son jin menene haɗin Ashfaq da ita, ko tana cikin rayuwarshi ta baya da Yasir ɗin bai sani ba, kuma baya jin akwai sunanta a takardar Ashfaq da itama baisan ta mecece ba har yanzun. 

“Za a kaimata wani abu ne?”

Yasir ya tambaya, yana son samun wani ƙarin bayani akan yarinyar, don in ya tambaya kai tsaye Ashfaq ba zai taɓa faɗa mishi ba, yana da tabbacin ɓoyayyun sirrikan Ashfaq ko zuciyarshi ya buɗe a kulle zai samu wasu wajajen. 

“A’a kawai dubata za ka yi, ka faɗa mata banda lafiya ne shi yasa. Kuɗin abincinta bai isa ƙarewa ba.” 

Kallon mamaki Yasir yake mishi, yana jin ƙara son sanin alaƙar shi da Nudra ɗin da har ya iya cire kuɗinshi ya bayar a sai mata abinci. Duk muhimmancin kuɗi a wajen Ashfaq. Tambayoyi yake gani fal a fuskar Yasir ɗin, murmushi yayi 

“Karka tambaye ni komai don Allah.”

Hararar shi Yasir ya yi. 

“Kana magana kamar in na tambayeka zaka faɗa min ne.” 

Dariyar dai Ashfaq ya ƙara yi, yarda da mutane abu ne mai matuƙar wahala a wajenshi, ya yarda da Yasir da rayuwarshi, amma banda abubuwa irin hakan, daga kan Altaaf ya daina ɗaga burinshi akan kowa. Wata hirar suka kama yi da bata shafi sirrikan Ashfaq ɗin ba.

<< Alkalamin Kaddara 20 Alkalamin Kaddara 22 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×