Turare ya fesa wa jikinshi, yana sake duba kanshi a mudubi.
“Na gode Baba da jininka ya fi na Ammi ƙarfi a kaina.”
Altaaf ya faɗi yana saka ƙaramin comb cikin sumarshi ya taje, ba sai kowa ya faɗa mishi ba yasan yana da kyau, yana kuma ji da kyawunshi saboda yana tasiri sosai akan mata, mutane da yawa kance babu me kyawunshi duk a cikin yaran Ammi, kuma yasan gaskiya suke faɗa. Duk hasken fatar Ammi su Aslam suka ɗauka, shi kam har duhunshi da tsayin irin na Baba ne. Comb ɗin ya saka cikin aljihun wandon uniform ɗin.
“Altaaf takwas ta wuce fa.”
Ammi ta kira daga falon, a kasalance ya duba agogon da ke ɗaure a hannunshi, takwas da kusan mintina ashirin, baya son karatu, bai taɓa ko da sha’awar karatu ba, har a zuciyarshi yake jin mutanen da basu da tudun dafawa a rayuwa ne kaɗai suke buƙatar mayar da hankali akan karatu, amma kuma da yawan mutane za su yi mamaki idan ya ce yana son makaranta. Yana kuma son saka uniform, don makaranta na bashi wani nishaɗi na ban mamaki. Jakarshi ya ɗauka akan gado yana ratayawa a kafaɗa tukunna ya fito.
“Ko in saukeka makarantar ne, na ga lokaci ya ja sosai.”
Ammi ta ce tana kallon ɗan nata cike da alfaharin yadda da duk rana yake ƙara girma yana zama cikakken matashi. Shagwaɓe fuska ya yi.
“Da kin sai min mota da haka bai dinga faruwa ba…Ammi kamar ni sai a ga kin kaini makaranta sai kace dai Anam.”
Dariya Ammi ta yi, tana da nufin siya mishi mota, amma ta fi so ya gama sakandire in zai je jami’a tukunna, tunda ba halin motar bane bata da shi, tana tsoronshi da mota yanzun ko don lafiyarshi.
“Ni har yanzun kamar Anam ɗin nake ganinka ai.”
Dafe ƙirjinshi ya yi dai-dai zuciyarshi yana girgiza wa Ammi kai. Dariya ta sake yi, ƙaunar da take wa Altaaf ba zata misaltu ba.
“Ka ci wani abu kafin ka fita.”
Ta umarta, wajen dining ɗin ya ƙarasa yana ɗaukar wainar ƙwai ya cika bakinshi da ita.
“Ka samu wajen zama… Sau nawa zan ce ka daina cin abinci a tsaye haka.”
Hannu kawai Altaaf ya iya ɗaga wa Ammi saboda bakin shi a cike yake da wainar ƙwai da dankali, shayin da ke cikin cup da yasan ba zai wuce wani ya rage ba cikin su Aslam ya ɗauka yana kurɓa don ya kora abinda ke bakin shi. Da ƙyar ya haɗiye yana yamutsa fuska tare da wani irin matse bakinshi kamar ya sha abu mai ɗaci, ba son shayi yakeyi ba dama, balle kuma hutacce. Dariya Ammi take mishi, yasa hannu yana riƙe maƙoshin shi.
“Ammi dariya kike?”
Ya faɗi har lokacin yana yamutsa fuska.
“Ka zo ka tafi makaranta.”
Wainar ƙwan ya sake turawa a bakinshi, tukunna ya goge hannunshi kan abin gogewar da ya gani yana kama hanya, bakin shi a cike yake faɗin,
“Sai na dawo Ammi.”
Kafin ta amsa ma ya fara buɗe ƙofa.
“Allah ya tsare, kuɗi fa?”
Hannu ya ɗaga mata kawai yana ficewa, don akwai sauran kuɗi sosai a hannunshi, abokan da yake yawo dasu duk kuɗi ba matsalarsu bane, ko wani abu aka siya mutum ɗaya zai biya wa kowa, kafin shi ya samu ya biya ana jimawa, shi yasa kuɗin sukan kwana biyu a hannunshi. Da ƙafafuwanshi yake takawa saboda baya jin hawan komai, in ya ji ya gaji ya hau mashin. Wayarshi ya ji tana vibrating a cikin jaka, ya juyo da jakar ta gabanshi yana lalubawa ya fito da ita.
Yadda Ammi ke fitar dashi kunya na mishi daɗi, cikin abokanshi ya riga kowa riƙe waya saboda tsadarta. Dubawa yayi ya ga Nazir da suke kira Naz ne tukunna ya ɗaga.
“A-Tafida kana gidan uban wa?”
Murmushi Altaaf yayi yana amsawa da,
“Gidan Aminu.”
Yana jin dariyar Naz ɗin daga ɗaya ɓangaren.
“Ubana kenan?”
“Oh shi ne ubanka daman?”
Altaaf ya faɗi yana tsayawa wani shago da yasan ana siyar da sigari. Kuɗi ya zaro a aljihunshi yana miƙa wa mai shagon
“Guda biyu zaka bani.”
Ya ce ya ɗora da,
“Kun shiga makaranta ne?”
“Tun ɗazun fa. Anty Halima ce a gate yau.”
Ɗan ware idanuwa Altaaf yayi da wani murmushin nishaɗi a fuskarshi, tun kafin ya ƙarasa yana jin alamun makarantar zata yi mishi daɗi ba kaɗan ba.
“Gani nan zuwa yanzun.”
Ya faɗi yana sauke wayar daga kunnenshi tukunna ya zari sigarin kara ɗaya a hannun maishagon yana faɗin,
“Ka ajiye min da canjin zan amsa gobe.”
A wajen mutumin ya karɓi lighter ya kunna sigarin, yasan Altaaf ɗin don yawanci kullum da safe in za shi makaranta sai ya siya yake wucewa. Nan ya tsaya zuƙa biyar masu ƙarfi yai mata yana yarda ƙarshe ya take. Hayaƙin ya bulbulo ta baki da hanci tare da sauke numfashi, hannuwanshi ya haɗa ya murza waje ɗaya yana jin alamun sanyi daya fara shigowa. Yana yin gaba ya tare mashin ya hau zuwa makarantar su da ke Na’ibawa.
Yana sauka daga mashin kuwa ya hango taron ‘yan latti da aka jera ana duka, kamar yadda Naz ya faɗa ne, Anty Halima ce, sai ɗan ajinsu Rabi’u da yake taya ta, tunda ‘yan aji shida suna jarabawar fita ne wato WAEC, cikin ajinsu aka bada riƙon ƙwaryar muƙaman, Rabi’u kuma shi ne shugaban ɗalibai. Hankalin Altaaf kwance ya shiga cikin makarantar.
“A-Tafida”
Wani yaro ya faɗi, yana saka duka ɗaliban da ke wajen suka juyo, murmushi Altaaf yai musu yana ɗan ɗaga musu hannu, baya tunanin akwai wanda baisan shi a makarantar ba, har ‘yan primary, don yadda yake zama a ɓangarensu ma baya zama a nashi. Akwai wani abu tattare da yara da yake nutsar da shi, kuɗin shi sun fi tafiya wajen sai musu ƙananun lemuka ko alewa, don haka suna sonshi sosai. Kusan duka makarantar haka ne, wanda basa sonshi kuma suna tsoron shi, shi da abokanshi su jaka kwana suyi maka dukan tsiya ba wani abu bane ba.
Inka kai ƙararsu ma hakan ne zai sake faruwa da kai, kuma babu wanda zai bada shaidar an yi a gabanshi saboda tsoron su Altaaf ɗin. Wucewa ya fara yi hankalin shi a kwance Anty Halima ta sha gabanshi.
“Altaaf Isma’il Tafida”
Ta kira cikakken sunanshi a kausashe, bata fi wata biyu da fara koyarwa a makarantar ba, amma tana ganin yadda Altaaf ɗin yake taka duk wata doka ta makaranta, yake abinda yake so, yadda yake da dokoki nashi na kanshi a cikin makarantar da har malamai suke kiyaye taka su. Abin na bala’in ɓata mata rai. Ita bata tsoron yaron kamar yadda ta ga sauran malaman na yi, musamman mata Hausawan, don ita Bayarabiya ce girman Kano. Dama tana jiran irin yaune ta nuna mishi ɗalibi ne shi kamar kowa.
Juyowa Altaaf ya yi a kasalance yana sauke numfashi.
“A-Tafida. Ba saikin wahalar da bakinki ba.”
Dariya sauran ɗaliban suka yi, Anty Halima na watsa musu harara kowa yai shiru. Hankalinta ta mayar kan Altaaf
“Baka san ka yi latti bane? Ko baka ga sauran ɗaliban na karɓar hukunci ba?”
Take tambaya cikin harshen turanci, yanayin halin ko a jikina da Altaaf ɗin yake nunawa na ƙara kunna ta.
“Shi yasa kika ga ina sauri zan je aji. Banga haɗina da sauran ɗalibai da hukuncin da suke karɓa ba.”
Ya amsa yana sauke idanuwanshi cikin nata, yaso ya ɗan yi wasa ne a yi dariya a wuce, amma ta soma ɓata mishi rai, ba kuma ya so ranshi ya ɓaci, in ranshi ya ɓaci matsala za’a samu, yana tunanin bata ji haka daga sauran malaman ba.
“Kneel down.”
Anty Halima ta faɗi, tana karɓar bulalar da ke hannun Rabi’u da yake girgiza mata kai idanuwanshi cike da tsoro, sauran ɗaliban da ke wajen ma ware idanuwa suka yi cikin mamaki. Altaaf kuwa kallonta yake kamar wanda yake ganin ƙaho ya fito a saman goshinta, kafin dariya ta suɓuce mishi, tabbas ta samu matsala in tana tunanin ko a tsaye zata iya taɓa shi ballantana kuma shi gwiwarshi ta taɓa ƙasa, wannan sai lokacin Sallah ne kawai yake faruwa.
Ko da yana primary in za su yi mishi jibgar duniya ba zai yi ba. Bulalar ta ɗaga zata zabga mishi ya riƙe yana fincikewa daga hannunta.
“Indai ba kyau na yi miki da safen nan ba ki matsa min in wuce.”
Altaaf ya faɗi yana jin haƙurin shi na gab da ƙarewa, Anty Halima bata san lokacin da ta zabga wa Altaaf mari ba, dai-dai ƙarasowar su Naz don wani ne ya same su a aji yake faɗa musu ga Altaaf can a bakin gate da Anty Halima. Kallonta Altaaf yake yi, kafin ya mayar kan hannunta da ta sauke, sannan ya ɗaga nashi yana taɓa kuncin shi da ranar ne karo na farko da wani abu ya taɓa su. Naz da yake yafi su zafin rai yayo kanta da sauri, Altaaf yasa hannu yana janyoshi baya.
“Wannan ne kuskure babba da kika taɓa yi a shekarun haihuwar ki.”
Altaaf ya faɗi yana juyawa tare da jan Naz da yake watsa wa Anty Halima harara suna nufar gate, Salim, Ruma, da Kaigama suna bin bayansu, Ruma da asalin sunanshi Kabir sai Kaigama da nashi sunan Ahmad, amma da waɗannan sunayen ake kiransu.
“Saboda me baka barni na kwaɗa wa matar nan mari ba ne?”
Naz yake tambayar Altaaf ɗin rai a ɓace, girgiza mishi kai Altaaf ya yi.
“Maganar zata kai gida, bana so ka sami matsala da Maigidanku.”
Jinjina kai Naz yayi, cikinsu Altaaf ne kaɗai bashida matsala da babanshi don maganar wani laifi da ya yi ya je gida, ko a makarantar shi ne dalilin da yasa ba’a sallamesu ba har yanzun, saboda shugabar makarantar suna yin kasuwanci tare da Ammin Altaaf, abinda kuma yake so shi Ammi take mishi ciki har da barmishi abokanshi a makarantar da yake. Yanzun kam ko haɗuwa ta yi da su cikin makaranta da murmushinta zata dinga faɗin,
“Shekara me zuwa kamar yanzun kuma kun gama.”
Yanayin muryarta na yin kamar ta janyo shekarar su gama su bar mata makarantar ta.
“Kasan dai matar nan ba zata tafi haka kawai ba ko?”
Kaigama ya faɗi da muryarshi da take a buɗe ko da yaushe saboda wiwi. Girgiza musu kai Altaaf ya yi.
“Zata bar mana makarantar ne bayan ta kunyata anan, sannan tayi wa Ammi bayani a office ɗin ‘yan sanda.”
Dariya Ruma ya fara yi. Altaaf na faɗa musu abinda za su yi. Cikin makaranta suka koma, wannan karon Anty Halima bata ce musu komai ba, don ta ɗan tsorata da yanayinsu. Aji suka koma suna samun malamin lissafi a ciki. Aliyu da yake zaune kusa da Fatima don nan ne wajen zamansu bencin gaba tunda suna cikin masu ƙoƙarin ajin, kallo ɗaya Altaaf yaima Aliyu ya tashi daga wajen don baya son tashin hankali. Zama Altaaf ɗin yayi yana kashe wa Fatima ido ɗaya.
Dariya ta yi, tana da ƙoƙari sosai, ita ce shugabar ɗalibansu ta yanzun, ta fi kowacce mace burge Altaaf ɗin saboda bata jin magana itama, don dai tana maida hankali kan karatun ta fiye da su ne kawai. Dariyarta tasa malamin lissafin juyowa.
“Altaaf na ga hankalin ‘yan ajin gaba ɗaya yana kanka, ko zaka taimaka mana da darasin yau ne.”
Dariya aka yi gaba ɗaya, Altaaf ɗin ma dariya ya yi.
“Uncle wannan lissafin sai ku.”
A cikin malaman yana ɗaya daga cikin malaman da Altaaf ba zai iya kwashe wa albarka ba, tunda baya shiga gonar su. Gaisuwa ce kawai tsakaninshi da su. Ko yana tare latti baya ce musu komai. Akwai sa’adda ya tare latti yasa ɗalibai shara, Ruma ya ɗauki tsintsiya shima, sukaita mishi iskanci ya ce musu kunyar malamin yake ji sosai, da suka wuce su duka sai ya ji basu kyauta ba.
“Tunda ba zaka bamu gudummuwa ta wannan fannin ba, ko zaka ƙyale min sauran ɗaliban?”
Jinjina kai Altaaf yayi yana ɗan murmushi, kafin malamin ya ci gaba da darasin shi, hannu yasa ya murza kuncin shi, bawai marin ya mishi zafi bane, kawai kuskurenta hannun da ta ɗaga mishi da babu wanda ya taɓa yin hakan. Idanuwanshi ya lumshe yana barin marin ya ɓata mishi rai har zuwa lokacin da malamin lissafin zai bar ajin. Yana fita Kaigama ya miƙe yana faɗin,
“Za’azo tambayarku akan Anty Halima. Amsa ɗaya ce kawai, duk inta shigo zata fita tana cewa Altaaf ya bita office. Ba zai wahala ba ko?”
Kallon Kaigama ‘yan ajin suke da mamaki. Fatima ce ta kalli Altaaf
“Kace min zata bar makarantar nan? Bana son matar wallahi ta cika sa ido.”
Gira Altaaf ya ɗaga mata.
“Me za ki ban in na ce miki zata bar makarantar?”
Babu kunya balle tsoron wani Fatima ta rungume Altaaf ɗin na tsawon ‘yan daƙiƙu tukunna ta sake shi tana murmushi a kunyace.
“Woo…”
Ya faɗi yana dariya tare da ranƙwafawa ya sumbaci Fatima a kuncinta ya ɗago yana kashe wa Ruma ido, don shi yake son Fatima ya kasa gaya mata ne, shi yasa ko da wasa Altaaf ɗin bai nufeta ba duk da tana burgeshi, yanzun ma yayi hakane kawai din ya kunna Ruman daya baro inda yake zaune yana shaqo wuyan Altaaf ɗin ya miƙar da shi.
“Ruma kashe ni zakai?”
Altaaf ya faɗi yana ture shi, wasu cikin ajin na kallon su suna dariya, wasu kuma suna kallon su cike da tsanar halayensu amma basu da yadda za su yi. Ficewa suka yi daga ajin suna raka Altaaf har wajen office ɗin Anty Halima, tana ciki kuwa da alama tana duba takardun yara ne. Sai da suka duba suka ga babu kowa sai su kaɗai tukunna Altaaf ya tura ƙofar office ɗin ya shiga.
A hankali ta ɗago da kanta ta ganshi a tsaye, sai da gabanta ya faɗi, murmushi yayi yana kallon rigar uniform ɗinshi data sha guga kafin ya kama gaban yana daƙuunawa, sannan ya riƙeta daga wuyan da duka hannunshi yanaja, maɓallai huɗu suka fita da ƙarfi.
“Me kake yi?”
Anty Halima ta tambaya tana miƙewa.
“Da me ya yi kama?”
Altaaf ya amsa yana takawa har inda take, hannunshi yakai yana shirin taɓata ta matsa tana faɗin,
“Altaaf meye haka wai? Fitar min daga office kafin ranka ya ɓaci.”
Ido ɗaya Ruma ya kashe ma su Naz don shi ne laɓe ta wajen window, da sauri suka fita suka tattaro student na aji huɗu da uku, sannan suka buɗe ƙofar office ɗin, lokacin Altaaf yakai Anty Halima bango tana ta kawo mishi duka ta ko’ina, ihu students suka fara yi da ya janyo hankalin sauran malaman suka fito don su duba ko lafiya, Altaaf ya koma gefe yayi tsaye, Anty Halima kuwa gaba ɗaya jikinta ɓari yake yi, ta kasa tsaida tunaninta akan abinda yake shirin faruwa, yau student ɗinta ne a cikin office ɗinta yana neman taɓata, wace irin rayuwace haka.
Sai da aka kora ɗaliban aji tukunna aka tusa Anty Halima da Altaaf zuwa office ɗin Principal don jin me ya faru. Tana ganin su da Altaaf sai da gabanta ya faɗi.
“Me ya faru?”
Ta tambaya da sauri. Malamin Chemistry ne ya ce,
“Shi ne muka zo su yi bayani, ihun ɗalibai muka ji muka fita muma.”
Anty Halima da har lokacin take jinta a hargitse Principal ta kalla
“Ya akayi?”
Saida Anty Halima ta kalli Altaaf tukunna ta mayar da hankalinta kan Principal tana faɗin,
“Bansan meya faru ba kawai na ga ya shigo min office yana… Yana…”
Ta soma inda-inda saboda nauyin kalmar da take shirin faɗa, ga malamai da yawa a tsaye, ta ina zata fara faɗin wannan wulaƙancin da Altaaf yai mata, batasan hawayen baƙin ciki sun tarar mata ba sai da ta ji zubowarsu. Ganin haka yasa Principal faɗin,
“Altaaf Isma’il…me ka yi kuma?”
Ɗan ɗaga kafaɗa Altaaf yayi a kasalance.
“Ta faɗa miki nata ɓangaren tukunna, idan kuka gama ɗora min laifi sai in yi nawa bayanin.”
Numfashi Principal ta sauke. Kanta haryar fara ciwo, sosai ta gaji da Altaaf a makarantar ta, babu yadda zata yi ne kawai shi yasa.
“Anty Halima ki faɗa mana me ya faru?”
Ta kasa magana, banda hawayen baƙin ciki babu abinda yake zubar mata, duk da ba aure gareta ba wannan ba ƙaramin cin mutunci bane. Wani numfashi Altaaf ya sauke yana cewa,
“Ba zata iya faɗa ba saboda tana jin kunya.”
“Ka kiyaye harshenka Altaaf.”
Wani malami da bai san me yake koyarwa ba ya faɗi, ko inda yake Altaaf bai kalla ba, saboda ba shi da lokacin shi. Don haka ya ci gaba da faɗin,
“Indai zata shigo aji ta gama darasinta sai ta ce in bita office, ban ɗauki abin da komai ba sai da fara cewa tana sona…”
Cikin wani sabon tashin hankali Anty Halima take kallon Altaaf.
“Wallahi ƙarya yake… Ƙarya yake wallahi.”
Take faɗi, cikin idanuwa Altaaf yake kallonta.
“Wanne ɓangare ne ƙarya? Kince kina sona na ce kin min tsufa? Haushin jiya kin ce in je office ɗinki ban je ba saboda na gaji da faɗa miki kin min tsufa har marina kika yi yau da safe a gaban students da yawa.”
Dafe kai Principal ta yi, malamai da yawa Anty Halima suke kallo, mamaki bayyane a fuskokinsu.
“Yanzun office ɗinki naje in ce in baki ƙyale ni ba zan kawo ƙararki kika tashi kika cakumeni kina ƙoƙarin kissing ɗina…”
“Altaaf!”
Principal ta kira cike da kashedi, tana rasa ta inda zata fara, kallonta yayi yana murmushi.
“Ki kalli gaban rigata mana, har maɓallai ta cire min don na ƙi tsayawa…ba…”
Miƙewa Principal ta yi tana faɗin,
“Fita Altaaf, fitar min daga office yanzun nan.”
Sai da ya kalli Anty Halima da tashin hankali yake bayyane a fuskarta yai mata wani murmushi tukunna ya juya cikin ƙasaita yake takunshi yana barin office ɗin. Yana fita wayarshi ya ɗauko daga aljihu yana kiran Ammi, ɗagawa ta yi tana faɗin,
“Hello Altaaf?”
“Ammi don Allah kizo makaranta yanzun.”
Ya ƙarasa maganar da damuwa a muryarshi.
“Lafiya dai ko? Me ya faru? Me akai maka?”
Wata sabuwar damuwa da ɓacin rai Altaaf ya tattaro yana wani irin sauke murya ya ce,
“Kinga dai yanzun karatuna na saka a gaba ai ko Ammi? Wata Antynmu ce ta saka min ido haka kawai, ko yaushe ta shigo ajin mu sai ta ce in bita office, wai tana sona ne Ammi, na ce bana so ta ƙyale ni bata ji ba.”
Cikin ƙaraji da tashin hankali Ammi ta ce,
“So kuma? So fa Altaaf, malamar taku?”
Shagwaɓe murya ya yi.
“Kunya na ji sosai shi yasa ban iya faɗa wa kowa ba, jiya ta ce in sameta office banje ba, Ammi yau har marina ta yi a gaban ɗalibai saboda ta ji haushi, yanzun na je office ɗinta in ce in bata ƙyale ni ba zan kai ƙara kawai ta zo … Ta zo tana fara taɓa ni.”
“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…”
Ammi take faɗi tana ƙarawa, murmushi Altaaf yake yi jin yadda ta ruɗe.
“Ammi ki zo don Allah, ni gida nake son tafiya, kowa ya sani a makaranta kunya nake ji.”
“Ka yi haƙuri ka ji, yanzun zan taho…bani minti sha biyar.”
Ammi ta faɗi tana katse kiran, sauke wayar Altaaf ya yi daga kunnenshi, yana taɓa kuncin shi, bata gama biyan marin da ta yi mishi ba, da kanta sai ta tsugunna ta bashi haƙuri, inda yasan zai samu su Naz ya ƙarasa, suna ganinshi suka fara ihu.
“Amman fa ta kamu wallahi.”
Ruma ya faɗi yana dariya.
“Baku da matsala.”
Altaaf ya faɗi cike da isa da jin kanshi. Sannan ya samu waje ya zauna.
“Yanzun saura me?”
Kaigama ya tambaya.
“Sauran zuwan Ammi da ‘yan sanda.”
Duka Ruma yakai ma Altaaf a kafaɗa.
“Maza Ammi ta yi wallahi.”
“Haba ai yadda take take ma Altaaf a wajen maigida yana kasheni”
Naz ya fadi
“Wasu lokutan inajin dama na zo a gidansu.”
Dariya Altaaf ya yi, son da yake ma Ammi mai yawa ne. Yana jin daɗin yadda ko abokanshi suke faɗin tana burgesu. Aikuwa suna nan zaune sai ga motarta ta shigo makarantar, tana fitowa ta wuce office ɗin Principal, miƙewa Altaaf yayi yana faɗin
“Drama ɗin nan ba zata wuce ni ba.”
Bin bayanshi su Ruma suka yi, suna laɓewa wajen wata bishiya da ke kusada office ɗin Principal ɗin, shi kuma kai tsaye ya shiga office ɗin, lokacin da Ammi ke faɗin,
“Saiki faɗa min ‘yan iska kika tara a matsayin malamai, har ana shirin lalata min yaro…”
“Ki saurareni mana Hajiya Amina, don Allah ki zauna a yi maganar nan a nutse, bincike muke yanzun haka.”
Girgiza kai Ammi take yi, fuskarta cike da masifa tana kallon Principal ɗin.
“Ammi…”
Altaaf ya kira da sanyin murya, yana sakata juyowa ta sauke idanuwanta kan fuskar Altaaf ɗin, tana dubawa ko zata ga shatin hannun ‘yar iskar malamar da ta marar mata fuskar yaro. Kafin ta maida idanuwanta kan rigarshi da take a yamutse, maɓallan duk yawanci sun fita daga gani kasan da ƙarfi akai kokawa aka tsinkasu, runtsa idanuwanta ta yi zuciyarta na tafasa.
“Ki kalli yaron nan, ki kalli yanayin shi, shi ne kike faɗa min bincike kuke yi? Bazan yarda ba, babu yadda za’a yi ƙoƙarin lalata min yaro in ƙyale, tana ina? Ina malamar take, wallahi ‘yan sanda ne za su raba mu.”
Ammi take faɗi, miƙewa Principal ɗin ta yi tana zagayowa ko Ammi zata fahimceta, don maganar ‘yan sandar nan ta ɗaga mata hankali, za’ai wa makarantarta baƙin fenti ne.
“Don Allah Hajiya Amina ki zauna mu yi magana, korarta ma zamu yi wallahi, amma bai kai da saikin ɗauko ‘yan sanda ba.”
Girgiza kai Ammi ta yi.
“Kora kawai kike tunanin ta isa? Ta isa hukuncin laifin da ta aikata? Ki tattaromun kuɗaɗena in cire yarona daga wannan tambaɗaɗɗiyar makarantar kafin a lalata min shi.”
Cikin wani sabon tashin hankalin Principal ɗin take kallonta, abubuwa da yawane za su faru in suka samu matsala da Ammi, don lokacin data kawo Altaaf daga aji huɗu suna kiciniyar buɗe ɓangaren, ita ta haɗa su da yayanta da ke aiki a hukumar ilimi, komai yazo mata da sauƙi gashi tana ƙaruwa da Ammi, don tana ɗaukar kaya na maƙudan kuɗi a wajen Ammi ta ɗora ribarta ta siyar. Babu yadda batai da Ammi ba amma fur ta ƙi yarda, saida ta tattaro mata malaman makarantar aka haɗu anata bata haƙuri.
Ƙarshe dai Anty Halima da kanta ta zo ta tsugunna a gaban Ammi tana kuka tana bata haƙuri, don Principal ta ce mata ‘yan sanda Ammi zata ɗauko mata, ta kuma san sarai halin rashin adalcin ƙasar mu da muke ciki, mai kuɗi a aljihu shi ne da gaskiya, don haka ta ɗauki laifin da bata aikata ba.
“Ni kikai wa laifi?’ Yar iska marar kunya, ke yanzun tsofai-tsofai da ke, malamarshi, babu tsoron Allah kike shirin far masa a cikin makaranta?”
Ammi take faɗi tana watsa ma Anty Halima harara tare da dunƙule hannu tana ɗirka mata wani duka.
“Munafuka, da kin lalata min yaro…”
“Ku yi haƙuri, don girman Allah ku yi haƙuri.”
Anty Halima take faɗi, bata taɓa ganin bala’i irin wannan ba tunda take, dama a dangi ana mata surutun ta ƙi yin aure, wannan maganar in ta kai gida ta shiga uku da surutu. Wajen Altaaf ta juya tana soma roƙonshi don ta ga alama komai a hannunshi yake, numfashi ya sauke yana kallon Ammi a shagwaɓe.
“Ni dai Ammi mu tafi gida, a bar maganar nan, wallahi kunya nake ji.”
Kallon shi tayi tana buɗe baki zatai magana, ya taɓare fuska yana katse ta,
“Ammi don Allah mu tafi, ki ƙyaleta kawai.”
Kai Ammi ta jinjina har lokacin zuciyarta na tafasa, Principal ta kalla.
“Ki tattaro min kuɗina na faɗa miki…Altaaf wuce mu tafi.”
Wucewar suka yi, Ammi na kallonshi tana tambaya ko lafiyarshi dai.
“Ammi mana…”
Altaaf ya faɗi yana nuna mata da so yake kar maganar ta sake haɗa su , kunya yake ji, hannunshi ta kama tana riƙewa kamar ƙaramin yaro, suna nufar mota, su Ruma ne suka ƙaraso suna gaisawa da Ammin, tukunna ta zagaya ta shiga mazaunin driver, ido ɗaya Altaaf ya kashe ma su Ruma da suke dariya ƙasa-ƙasa tukunna ya buɗe motar ya shiga, yana musu nuni da hannunshi cewar za su yi waya. Ammi taja motar suna nufar gida.
*****
Tunda suka koma gida da Ammi ya shige ɗakin shi ya cire uniform ɗin ya sake kaya ya kwanta, ya fi shan taba akan komai, syrup ma yana sha ne in yana son yin bacci ya kasa, yana da syrup kwalba daya a jakarshi shi ya ɗauko ya kwance, ɗagawa ya yi zai sha kuma ya fasa yana miƙewa, wani wando da yake nan kan gado ya janyo ya cire kuɗi yasa a aljihun wandon jikinshi yana fitowa. Bai ga Ammi a falo ba, don haka kawai ya fice abinshi yana fita daga gidan gaba ɗaya.
Canjinshi ya biya ya karɓi sigari da su yasa a aljihunshi tukunna ya hau mashin zuwa unguwarsu Ashfaq, yasan dai yana makaranta an kusan tashi, kuma daga makaranta gida zai yo, mashin na sauke shi ya bashi kuɗin shi ya shiga babban soron gidan, yana karya kwanar da zata kaishi ɓangaren su Ashfaq ɗin. Da sallama ya shiga, Mama ta amsa mishi daga kitchen yana ƙarasa shiga cikin gidan sosai.
“Altaaf.”
Ta faɗi cike da fara’a, shi ma murmushin yake, akwai yanayin kwarjini a tattare da Mama da yake sakata shiga ranka lokaci ɗaya, ko da suna gidan duk kyarar da sauran suke mishi bata taɓa canja mishi fuska ba, takan yi mishi faɗa kamar yadda take wa su Ashfaq, amma maimakon ya ɓata mishi rai sai yasa jikinshi yai sanyi, saboda akwai ƙauna da kulawa a tattare da duk faɗanta.
“Mama. Ina wuni.”
“Lafiya kalau. Ka yi wuyar gani, jiyan nan nake tambayar Ashfaq kana ina.”
Ɗan sosa kai ya yi, yana jin rashin kyautawarshi, yana kuma shigowa unguwar sosai su yi zamansu a waje shi da Ashfaq ɗin.
“Wallahi ina nan.”
“To madalla, ya wajen su Amina.”
“Suna lafiya Mama.”
Altaaf ya amsa. Jinjina kai ta yi.
“Ka shiga ciki ka zauna mana. Ashfaq ɗin dai bai dawo ba tukunna amma nasan yanzun zai dawo.”
Shiru Altaaf ɗin ya yi, yana jin nauyinta haka kawai da yasa shi faɗin,
“Nima bana jin daɗi ne shi yasa ban je makaranta ba.”
Don yasan ko da bata tambaye shi ba a ranta zata yi tunanin haka kawai ra’ayi yasa shi ƙin zuwa makaranta. Bai damu da duk abinda mutane za su ce ko su yi tunani akanshi ba, amma ita da Ammi yana so a idanuwansu kawai ya samu nagarta ko ya take.
“Allah sarki. Haka ake ta fama, zafin nan ne da bai gama wucewa ba, ayi sanyi yau ayi zafi gobe. Mutane nata fama…Allah ya ƙara sauƙi.”
“Amin thumma amin.”
Altaaf ya amsa a sanyaye. Da alama girki ta gama don kwanonin data ɓata ne ta tattara tana fito da su tsakar gida don ta wanke. Bokitin ruwa ta cika zata ɗauka shima, Altaaf ɗin ya ɗaukar mata ya kawo mata kusa da kwanonin.
“Sannu. Ka shiga ka zauna mana, ɗakin Ashfaq ɗin a buɗe yake na sani…”
Wucewa Altaaf yayi yana cire takalminshi a ƙofar ɗakin don yasan halin masifar Ashfaq ɗin, ɗakin a gyare yake tsaf, musamman katifar, zanin kamar ba’a kwantashi ba.
“Neat freak.”
Altaaf ya faɗi a fili yana gyara labulen don Ashfaq zai ce ƙudaje sun shigo mishi ɗaki, sannan ya kwanta. Ɗakin ba wani girma gare shi ba, da store ne, suna da ɗakinsu ciki da falo kullum sai yai ta faɗa da su Amjad akan ya gyara ɗakin sun ɓata, dole aka bashi nashi daban. Mama ce ta yi sallama tana ajiye mishi wani kwano me kyau ta ɗora plate akai sai pure water da cokali, ta fice abinta. Tashi zaune Altaaf ya yi saboda ƙamshi da ya cika mishi hanci, tuwon shinkafa ne ya tuƙu, sai miyar taushe da naman rago, sai ƙamshin man shanu.
Daman yayi kewar abincin Mama masu daɗin nan, zama ya gyara ya ja abincin gabanshi ya fara ci. Sallamar Ashfaq ya ji ya shigo gidan yana wa Mama sannu da gida. Yana jin tana faɗin,
“Ashfaq daga dawowarka, don Allah ka barni in ƙarasa wanke-wanke na, sauran tukunyar nan kawai.”
Da alama wanke-wanken yake shirin karɓar mata, duk da haka bai shigo ɗakin ba sai da ya kwashe mata kwanonin ya mayar mata kitchen, da sallama ya ɗago labulen, Altaaf ya haɗiye lomar daya kai bakinshi tukunna ya amsa,
“Ka tuna da ni kenan.”
Ashfaq ya faɗi yana wucewa cikin ɗakin ya rataye jakar makarantarshi. Amsa shi Altaaf zai yi ya sake cewa,
“Baka je makaranta ba?”
Yanayin maganar cike da tuhuma.
“Na je mana.”
Altaaf ya amsa yana ƙarasa cinye tuwon ya ɗauki nama ɗaya ya saka a bakinshi
“Ka gudo kenan.”
Kai Altaaf ya girgiza mishi,
“Me ya faru to? Ko don manta kawai babu wani amfani.”
“In baka labarin abinda ya faru dai.”
Altaaf ya faɗi yana murmushi, ƙafa Ashfaq yasa yana ture Altaaf da take baje akan katifarshi.
“Bana son ji, matsa in wuce ni kam.”
“Allah saina baka labari, wata malama ce dama…”
“Zan bar maka ɗakin Altaaf. Ka ƙyale ni yunwa nake ji.”
Ashfaq ya ƙarasa yana ficewa, abinci ya zubo ya dawo ɗakin yana samun Altaaf ɗin ya kwanta. Gefen katifar ya zauna yana ajiye abincin ya soma ci.
“Syrup zan sha in kwanta in yi bacci da, sai na taho nan.”
Altaaf ya faɗi da wani nisantancen yanayi a muryarshi, yana sane da rayuwarshi daban take da ta mutane da yawa. Yana kuma sane da lalacewa yake ƙara yi kullum rana, ya rasa dalilin da yasa hakan baya damun shi. Lokuta irin yau dai yana jin son ya faɗi duk wani abu da yake yi ba dai-dai ba ko zai ji son bari. Shiru Ashfaq yayi yana ci gaba da cin abincin shi don yasan bawai gama magana Altaaf ɗin yayi ba.
“Nayi sanadin korar wata malama daga makarantar mu bayan ta ɗauki laifin dana ɗora mata, amma kuskuren nata ne, ta ɗaga min hannu, ko Ammi bata ɗaga min hannu Ashfaq, na kuma ji daɗi, zuciyata ta yi sanyi…”
Altaaf ya ƙarasa maganar yana lumshe idanuwanshi. Fuskar Anty Halima da yanayinta na saka mishi wani nishaɗi, babu yadda za’ayi ta mareshi ta tafi a banza. Abincin Ashfaq ya ƙarasa cinyewa yana tattara kwanonin da wanda Altaaf ya ci ya fita da su tukunna ya dawo.
“Ka tashi ka yi sallar Azahar, lokaci har ya wuce.”
Ashfaq ya faɗi don yana da tabbacin Altaaf bai yi sallah ba.
“Ba za kai min faɗa ba, club zan je anjima acan zamu kwana.”
“Ka tashi ka yi sallah.”
Ashfaq ya amsa. Buɗe idanuwanshi Altaaf ya yi a kasalance, ko baiji rashin kyautawar abinda yayi ba, in Ashfaq ɗin yai mishi nasiha yana jin kamar akwai yiwuwar zai shiryu nan gaba.
“Ka daina zaton zan shiryu ko?”
Altaaf ya tambaya da wani yanayi a muryarshi.
“Ka yi Asuba?”
Ashfaq ya amsa maimakon amsa tambayar da Altaaf ɗin yai mishi.
“Na yi Asuba.”
Altaaf ya ce a taƙaice yana mayar da idanuwanshi ya lumshe.
“In bacci za ka yi ka yi Azahar tukunna.”
Idanuwan Altaaf a rufe har lokacin ya ce,
“Zan haɗa inyi da la’asar idan na tashi.”
Waje Ashfaq ya samu ya zauna
“Faɗa ko gaya maka inda kake tafiya da rayuwarka ba dai-dai bane baya shigarka Altaaf. Shi yasa na ce ka tashi kayi sallah, baka sallah akan lokaci ta ya halayenka za su gyaru? Ko yaya ne in ka tsare Sallah zaka yi faɗa da shaiɗan akan wasu abubuwan.”
Shiru Altaaf ya yi yana jin Ashfaq ɗin ba wai bayajin shi ba. Kawai jikinshi yayi nauyi bazai iya tashi yai sallah ba, kanshi ma yake ji yayi wani dum da baccin da yake son yi. Don haka ya sake gyara kwanciyarshi yana rufda ciki.
“In ba za ka yi sallar ba ka gyara kwanciyarka, babu kyau wannan kwanciyar…idan mutuwa ta…”
“Don Allah ka yi shiru Ashfaq…. Na gyara.”
Altaaf ya faɗi yana gyara kwanciyarshi, baya so ana kiran mutuwa in yana nan, ko kaɗan baya so. Girgiza kai kawai Ashfaq yayi yana zame jikinshi ya kwanta tare da yin pillow da gefen katifar. Su dukkansu bacci ne ya ɗauke su.
Madalla