Skip to content
Part 27 of 52 in the Series Alkalamin Kaddara by Lubna Sufyan

Har kofar aji wadata ya kai shi yana parking din motar, ba ko yaushe Altaaf yake zuwa da motarshi makaranta ba, sun fita yawo da ita akan zuwa makaranta. Yauma yasan wadata ya kawoshi ne don ya tabbatar ya halarci dukkan darussan shi na ranar. Jakarshi ya ɗauka yana murɗa hannun ƙofar motar da nufin fita Wadata ya ce,

“Altaaf ka tsayar da hankalinka kan karatunka, don Allah ka…”

Wani numfashi mai nauyi Altaaf ya sauke yana girgiza kanshi, kafin ya katse Wadata da faɗin,

“Da matata ce kai tsakanin jiya da yau da tuni na sake ka wallahi… Bana so a dinga maimaita magana ɗaya… Yana juya min kai…”

“Za ka ci ubanka A-Tafida.”

Wadata ya faɗi yana hararar shi, ya ga alamar maganganun shi ta kunnen dama suke shigar Altaaf ɗin suna fita a na haggu. Zaman Altaaf a makaranta na da muhimmanci a wajenshi. Don yana jinshi kamar ƙanin shi da suka fito ciki ɗaya, zuciyarshi ba za ta yi mishi daɗi ba in aka koreshi daga makarantar sam. Dariya Altaaf ya yi yana buɗe murfin motar.

“Ka zauna a aji kuma.”

Wadata ya ce.

“To Ammi.”

Altaaf din ya amsa, Wadata na kai mishi dukan da bai same shi ba, don ya riga ya fice daga motar yana dariya. Aji ya shiga yana ɗan ɗaga wa wanda suka haɗa ido da shi kai, kusan kowa a ajin yana magana da shi, matan nema duk yadda suke binshi bai cika kula su ba, yana da dokoki a harkarshi, ko kusa da ƙirjinshi baya bari mace ta je balle kuma ta shiga zuciyarshi. Sannan dare ɗaya ne da wahalar gaske ta sake na biyu tare da shi.

Shi yasa ya ma kanshi alƙawari babu wani abu da zai haɗa shi da duk yarinyar da suke aji ɗaya da ita, saboda yasan matsala za’a samu. Zai dinga ganinta kullum a aji, zata liƙe mishi, abu ne kuma da baya so. Ko Anisa da ke zuwa gidansu abinda yasa suke tare har yanzun don alaƙarsu bata wuce nishaɗi ba, itama kuma hakan ne a nata ɓangaren. Wadata ya hana shi zama ƙarshen aji, don haka ya ja kujera a layi na biyu ya zauna. Ya so zama darasin safen amma zuciyarshi na kan Safara Auwal.

Yana so ya je ya ga ya take, me yasa aka ce mishi ita. Me take da shi da sauran matan basu da shi. Miƙewa tsaye ya yi yana leƙawa ko Wadata bai tafi ba, ba don yana tsoron shi ba, sai don yana ganin girmanshi bai kuma san dalili ba, ko don ta ɓangarori da dama yana mishi yanayi da Ashfaq ne, ko don kuma yan jinshi kamar yayan da bai samu ba. Tunanin Wadata akanshi na da muhimmanci.

Ganin baya nan yasa shi ɗaukar jakarshi ya rataya a hannu ɗaya, yarinyar da ke zaune a gabanshi da ya sha gani a ajin, don indai za su haɗa idanuwa sai ta mishi murmushi a kunyace, samunta bazai mishi wahala ba, kuma tana da kyau, amma kasancewarta ‘yar ajinsu ya sa katanga a tsakaninsu, ko sunanta bai sani ba, littafin da ke gabanta da biro a ajiye ya ja yana rubuta registration number ɗinshi a sama tare da faɗin,

“Ina da abu mai muhimmanci da zan yi. Ki rubuta min attendance…”

Ya ƙarasa maganar yana mata murmushin karɓar lamba a hannun yan mata, kai ta ɗaga mishi idanuwanta cike fal da kunya cikin yanayin da ya sashi dana sanin zuwanta a ‘yar ajinsu, da ya bi duk wata hanya ya rabata da wannan kunyar da take tare da ita. Wucewa yayi yana fita daga ajin. Ismail ya hango ɗan ajinsu yana ƙoƙarin kafe mashin ɗinshi da sauri ya ƙarasa.

“Ismail ka saukeni wajen ‘yan computer science mana.”

Ɓata fuska Ismail ya yi da ke nuna Altaaf ɗin ya balain shiga rayuwarshi amma babu yadda zaiyi, bai ma jira amsarshi ba ya hau bayan mashin ɗin. Dole Ismail ɗin ya kai shi ya juya. Dubawa ya yi ko zai ga wanda ya sani, don ɗalibai ne suke ta hada-hada, wasu na shiga aji, wasu na tsaye suna hira, wasu na danna wayoyinsu. Wani gaye ya hango da ba zai tuna sunanshi ba amma sun sha haɗuwa wajen party. Hannu ya ɗago ma Altaaf ɗin, shima yana ɗaga mishi tukunna ya ƙarasa inda yake suna gaisawa.

“Safara Auwal fa?”

Altaaf ya tambaya, kallon ‘Meye haɗin ka da ita’ yake mishi, bai sauke nashi idanuwan ba, bai kuma faɗa mishi dalili ba don ba damuwarshi bane wannan a ganin Altaaf ɗin. Sai da ya yi kamar ba zai amsa ba tukunna ya ce,

“Yanzun ta wuce ita da ƙawarta, za ka gansu ɗaya da niƙab ɗaya babu. Marar niƙab dine ce Safara.”

Kai Altaaf ya jinjina ya wuce ba tare da ya ce komai ba. Duba su Safara yake tayi,e har ajinsu ya shiga amma bai ga kalar kwatancen da akai mishi ba, ya fito kenan ya hango su, hijabai ne a jikinsu har ƙasa daga ita har ƙawarta. Mu’amala da mata yasa shi komin hijab ɗin da ke jikin mace indai tana tafiya akwai yanayin da yake nuna mishi tana da ƙira me kyau ko bata da shi. Safara na cikin matan da suke kamar allin rubutu (chalk). Fara ce amma fuskarta batai mishi ba tun daga nesa, bai ga wani abu tattare da ita da zai sa Abdul ya zaɓe ta ba.

Saida suka tako gab da shi tukunna ya kula da kamala da nutsuwar da ke tattare da fuskarta. Yanayi ne da yake gani a fuskar Aslam, ya sha kallon tashi fuskar ko zai ga wannan kwarjinin amma bai gani ba, sai ya fi alaƙantashi da cewar mutanen da Islamiyya ta shiga jikinsu ne kawai za ka ga hakan, mutanen da basu waye ba. Wannan yanayin ne a tare da Safara, musamman da ta yi murmushi, sai ya ji kamar gabanshi ya faɗi. Har sun wuce shi ya ce,

“Assalamu Alaikum.”

Juyowa suka yi a tare, ƙawar Safara ɗin na amsawa. Safara kuma tana kallonshi da mamaki a fuskarta, da alama bai yi kalar da ta zaci sallama zata fito daga bakinshi ba, duk da ƙananan kaya ne a jikinshi sai hularshi hana sallah (Face cap) da ya saka baƙa, tunda takalmanshi ma baƙaƙe ne.

“Sannunku. Don Allah ko Ahmad Ayoob ya zo? Inata kiran wayarshi a kashe… Kuma ina sauri ne saboda ina test.”

Ya ƙarasa maganar a gajiye, yana tabbatar da ya ɗora yanayin gajiya da kuma ƙosawa da su bashi amsa ya bar wajen. Don har da duba agogon hannunshi yana ɗan jan guntun tsaki.

“Aikam bansan wani mai sunan nan ba, bansan ko Fatima ba.”

Safara ta faɗa cikin wata irin murya mai sanyin gaske. Shi ma sunan daya fara zuwa bakin shi ne ya faɗa, ita ma Fatima kai ta girgiza alamar a’a.

“Na gode… Na bar ku cikin aminci.”

Altaaf ya faɗi yana wucewa ba tare da ya juya ba. Murmushi yake wa kanshi. Aslam ke yawan faɗar haka, yasan akwai hankali a tattare da kalaman shi yasa ya faɗa musu yanzun ma. Ya kuma san ko babu komai ya bar musu tunanin cewa shi ɗin mutumin kirki ne.

* * ***

A department ɗinsu Safara ya samu wani yaro ya biyashi kuɗi ya bashi lamba kuma, ya dinga ganar mishi me Safara take yi, ina da ina take zuwa. Ya kuma faɗa mishi duk idan ta fita ya bita ya ga ina ta je zai sake biyanshi wasu kuɗin. Don haka hankalin shi a kwance yake, duk wani motsinta ana sanar da shi. Ba sauri yake ba, yana da lokacin da zai ɓata akanta ko don ya nuna wa Idris shekaru kawai zai nuna mishi. Don ranar ana kiranshi aka fada mishi Safara da ƙawarta za su je wajen cin abinci yasa aka bi mishi ita. Ya ji daɗin zuwa da yayi da mota ranar don haka bai wani jima ba ya isa wajen.

Yana shiga ya hango su a zaune, ruwan roba ne kawai a gaban Safara. Da alama ƙawarta ce kawai za ta ci abinci, cikin ƙasaitar shi ya taka har ya isa table ɗin da suke, sallama yai musu tukunna ya ja kujera ya zauna. Idanuwanshi na kan wayarshi, amma yana jin yadda idanuwansu ke yawo a kanshi. Don abu ɗaya suke ɗauka, ya zauna tare da su ne don yai musu magana ko ya roƙe su lambar waya. Sai dai abinda basu sani ba ya banbanta da sauran mazan da suka saba cin karo da su. Tunda ya zauna bai saka idanuwanshi a fuskar kowacce a cikinsu ba.

Daya gama danne-dannenshi da waya, lemo yasa aka kawo mishi na roba, ya saka abin zuƙarshi a ciki yana jingina bayanshi da kujerar sosai tukunna ya fara zuƙa a nutse, fuskarshi da wani yanayi da za ka rantse dole akai mishi ya zauna a wajen. Sam ya ƙi ko kallon gefen su Safara, yana dai kallon yanda ƙawarta ke wasa da cokali cikin abincin da aka kawo mata, da alama zamanshi a wajen ne ya hanata ci, matsalarta ce wannan, dankali ma ya tambaya in akwai akace mishi eh, yasa aka kawo mishi da ƙwai.

Earpiece ya saka duka kunnuwanshi biyu yana haɗawa da wayarshi. Ba wani abu yake saurare ba, amma yadda ya nutsu yana cin dankalin za ka ɗauka baisan abinda yake faruwa a wajen duniyar ba. Ƙawar Safara ce ta kalleta da faɗin,

“Kamar na taɓa ganin shi.”

“Idan yana jinki kuma fa?”

Safara ta tambaya a kasalance. Girgiza mata kai yarinyar tayi.

“Baki ga abune a kunnuwanshi ba.”

Dan taɓe baki kawai Safara ta yi tana ɗaukar robar ruwanta ta buɗe ta sha, don zaman Altaaf ɗin yasa ta ji maƙoshinta ya bushe. Akwai wani abu a tattare da shi tun ranar farko data ganshi da yake faɗa mata ta yi nisa da shi sosai, har a ƙasan zuciyarta take jin wata ‘yar ƙaramar murya na faɗa mata ta tashi ta ruga, ta tabbatar akwai tazara mai nisa tsakaninta da Altaaf. Ba kuma kyawun shi bane yasa hakan, wani abune daban da ba za ta ce ga asalinshi ba.

“Wasu mutanen suna da kyau.”

Ƙawar ta faɗi muryarta can ƙasa.

“Allah ya shiryeki Asiya.”

Cewar Safara. Sunan ƙawarta kenan, Altaaf ya faɗi a ranshi. Daman don ya ji hirarsu shi yasa ya saka earpiece a kunnenshi. Ko a fuskarshi ba zaka ga alamar yana saurarensu ba.

“Me nayi? Yana da kyau ko ke in zaki faɗi gaskiya kinsan yana da kyau.”

Kallonta Safara ta yi.

“Eh yana da kyau. Amma yaro ne.”

Dankalin da Altaaf ya ɗauko da cokalin ya kasa kaiwa bakin shi, da duk wani abu yake son ɗaga idanuwanshi ya kuma sauke su cikin na Safara, ya sa ta ga yadda idanuwanshi kaɗai sun isa su saka ta tsarguwa, ko bai girmeta ba za su zo shekaru ɗaya amma take kiranshi da yaro, bata cikin kalar matan da zai bi fiye da sau ɗaya, in ba don game ɗin nan ba ko kallo bata ishe shi ba, bayan jerin matan da ke son ya kula su.

Yana jin yadda sukai shiru don yanayinshi ya nuna yanajin su, wani murmushi yayi yana ɗan gyara zaman earpiece ɗin a kunnenshi ɗaya, kamar wani abu da yake saurare ne ya ɗauke mishi hankali. Kafin yasa dankalin a bakinshi. Wani irin numfashi mai sauti Safara ta sauke da yasa Asiya yin dariya.

“Kin ɗauka ya ji ki ko? ‘Yar rainin wayau.”

“Ni dai ki yi sauri mubar wajen nan…”

Safara ta faɗi muryarta a ɗan tsorace. Wani abu na faɗa mata Altaaf yana jinsu. Shi kam dankalin ya ajiye don bawai yana jin yunwa bane ba dama, ya ƙara zuƙar lemonshi sosai tukunna ya ja kujerar baya yana miƙewa. Zuwa yayi ya biya kuɗin shi, ya wuce yana fita daga wajen ba tare da ya kalle su ba, za su zaci zai biya da su ne, don samari da yawa za su yi hakan. Shi kuma baya cikin kalar samarin. Hidimarshi ta ranar ya ci gaba da yi.

A sati biyu rana ku ɗai-ɗai yake tsallakewa bai je wajen da aka ce Safara tana nan ba, baya zuwa kullum ne saboda yana son ta saba ganinshi, ta kuma dinga dubawa ko zata ganshi, yana son barinta da tunanin haɗuwarsu ba da niyyarshi ba ne (coincidence) ko kuma da binta yake yi duk inda take zuwa. Don duk haɗuwar da za su yi ita kaɗai ko da Asiya don ya kula kamar ita kaɗai ce ƙawarta, zai musu sallama sannan ya ci gaba da hidimar shi kamar ba su dame shi ba.

Yauma wani shago da ake photocopy ya bi su, dama zai cire wani assignment da Ruma ya taya shi yi. Kamar ko yaushe sallama yai musu yaci gaba da hidimar shi. Yana jin yadda suke ta kallonshi, hankalinshi na kan assignment ɗin da ake cire mishi don yana faɗa wa wanda yake mishin sunanshi da abubuwan da zai saka a cover page ɗin. Ji yai an damƙar mishi wuya ta baya.

“Ouchhhh”

Ya faɗi yana daƙuna fuska tare da riƙo hannun da yake bayan wuyanshi tukunna ya ɗago yana sauke idanuwanshi kan fuskar Wadata da yanayin shi ke nuna ran Altaaf ɗin zai ɓaci in ba shi da wani babban dalili na zuwa wajen.

“Me kake yi anan?”

Wadata ya buƙata, murza wuyanshi Altaaf yake yi yana wani shagwaɓe fuska.

“Inda ka kashe ni waye zai amsaka?”

Harararshi Wadata ya yi, yadda yake ta murza wuyan za ka ɗauka wata shaƙa Wadatan yai mishi.

“Assignment nake cirewa.”

Ya faɗi yana turo laɓɓanshi, inda wani namijin ne yayi ba Altaaf ba abin zai ma Wadata wani iri, amma Altaaf ne, kaɗan ne cikin aikinshi, sangarta na wa mata kyau, wannan karon ta fi zama dai-dai da Altaaf.

“Babu inda zaka cire a kusa da ku sai ka zo nan?”

Ƙanƙance idanuwa Altaaf ya yi, baisan yadda Wadata ya taimaka mishi ba, don yanzun hankalin su Safara na kansu gaba ɗaya.

“Akwai layi nikuma ina sauri shi yasa.”

Hararshi Wadata ya yi, bai yarda ba, duddubawa yayi don ya ga matan wajen, amma bai ga kalar da Altaaf zai biyo ba, duka basu da wani abin a zo a gani, duk da kowacce a cikinsu hankalinta na kan Altaaf ɗin, yana da kyau ne da yake jan hankalin su, gashi kaya na matuƙar karɓar jikinshi, sai dai duk yadda suke kallon shi duk sirara ne. Altaaf baison siririyar mace sai dai su haƙura. Tukunna ya yarda da gaske assignment ɗin Altaaf ya zocirewa.

“Yaya Wadata.”

Altaaf ya faɗi muryarshi ɗauke da dariyar da yake son yi, yana kallon yadda Wadata ya ware idanuwa cikin tsananin mamaki kafin ya kwashe da dariyar da ta fito da ta Altaaf ɗin shima.

“Yau nine na zama Yaya? Ni?”

Wadata yake faɗi yana ci gaba da dariya. Altaaf ɗin ma dariyar yake.

“Yanzun ban taɓa ce maka Yaya ba? Yi haƙuri laifina ne, Yaya Wadata ko Yaya Imran wanda duk kake so.”

Girgiza kai Wadata yake yi yana ci gaba da dariya.

“Me kake so Altaaf?”

“Sai ina son wani abu ne zan ce maka Yaya? Haba mana, yanzun in wani yaji zai ɗauka bana girmamaka ne.”

Murmushi Wadata yake yi.

“Ka gama mu tafi A-Tafida… Dramar ka tafi ƙarfina.”

Dariya Altaaf ɗin ya yi ya bayar da kuɗinshi ya karɓi assignment ɗin yana zagayawa gefen Wadata.

“Assignment ɗin math za kai min.”

Kai Wadata ya girgiza mishi.

“In dai koya maka ka yi da kanka.”

Sosai Altaaf ya matsa kusa da Wadata yana jingina kanshi jikin kafaɗar Wadatan.

“Haba Yaya?”

Hankaɗe shi Wadata ya yi.

“Za ka ci ubanka yanzun nan wallahi.”

Dariya Altaaf ɗin yayi yana saƙala hannunshi cikin na Wadata ya maƙale shi sosai.

“Ni ne fa, don Allah.”

Tafiya suke a hakan Wadata na ƙoƙarin ɓanɓare hannunshi daga riƙon da Altaaf ɗin yai mishi.

“Wallahi ranka zai ɓaci in baka sake ni ba.”

“Ka ce za kai min to.”

Ɗan tsayawa Wadata ya yi yana watsa wa Altaaf ɗin hararar da ba aiki take yi akanshi ba.

“Ba za ka sake ni ba saina kwaɗa maka mari?”

Buɗe baki Altaaf ya yi cikin mamaki.

“Yanzun fuskar nan me kyau kake tunanin mari? Kana da imani kuwa Wadata?”

Hannunshi Wadata ya ɓanɓare yana hankaɗe Altaaf ɗin.

“Wuce don Allah. Ka tafi ka ƙyale ni.”

Yake faɗi yana dana sanin shiga shagon ma, don hango Altaaf ɗin ya yi ya ɗauka mata ya bi ko wata shiriritar ya je yi bayan yana da darasi. Da yasan assignment zai cire da bai je ba, gashi nan yanzun ya addabe shi, Altaaf na takura mishi ba kaɗan ba. Ko me zai mishi kuma baya jin haushi, yanzun ma dariya yake yi.

“Ka tafi na ce Altaaf.”

Wadata ya maimaita, takardun hannunshi Altaaf ya matse a tsakanin ƙafafuwanshi yana tallabar fuskarshi da hannuwanshi tare da ƙyafta idanuwa.

“Ka tabbata baka son ƙara ganin fuskar nan me kyau?”

Dube-dube Wadata yake yi don ya ma manta ba a gida suke ba, ganin babu abinda zai iya jifan Altaaf ɗin da shi yasa shi takawa don ya kai mishi duka, hakan Altaaf ya gani ya zare takardunshi yana riƙewa a hannu tukunna ya ruga yana dariya. Murmushi kawai Wadata ya yi, a gaban kowa Altaaf zai yi yarintarshi kamar duniyar babu wani abu da ya fi yin abinda yake so muhimmanci.

*****

Zuwa yanzun duk wani waje da Safara take zuwa Altaaf ya sani, don lokuta da dama kafin ta je shi yana wajen, sai dai su sames hi a gurin, in suka haɗa ido sukan yi mishi sallama ita da ƙawarta, kamar yadda in shi ya same su yakan yi musu sallamar. Yauma yasan zasu zo wajen cin abinci, don haka yana bakin wajen, har sai da ya hango su tukunna ya shiga ya samu waje ya zauna. Yana zama suna shigowa, idanuwansu akanshi suka fara sauka. Shima nashi idanuwan ya kafa musu, musamman Safara, ɗan murmushi ta yi mishi da bai da alama da na nishaɗi.

Bai kuma daina kallonta ba, har ta samu waje ta zauna, yana kallo ta sauke nata idanuwan, wayarta ta ɗora akan teburin tana jujjuyata, lokaci zuwa lokaci takan ɗago kai, da sun haɗa ido take saurin mayar da shi ta duƙar. Bai motsa daga inda yake ba har sai da aka kawo musu abinci, yauma ruwa kawai aka ba Safara, bai taɓa ganin ta ci wani abu a wajen ba, Asiya dai take rakowa. Miƙewa ya yi yana gyara zaman hularshi tukunna ya taka har teburin su ya ja kujera ya zauna. Idanuwanshi na kan Safara. Sallama ya yi musu, wannan karon Asiya ce kaɗai ta iya amsa mishi, ko inda take bai kalla ba.

“Me yasa kike bina?”

Ya tambaya a kasalance, kallon da yake wa Safara tana jin kamar idanuwanshi sun yi rami a fuskarta, tambayarshi kuma na zo mata a bazata, don sai da ta ɗago tana ware mishi idanuwa cike da mamaki, kai ya ɗaga mata yana ƙanƙance idanuwa.

“Yes, me yasa kike bina? Duk inda zan je sai na ganki.”

“Malam ban gane muna binka ba? Me yasa zamu…”

Asiya ta fara faɗi, Altaaf na katseta ta hanyar ɗaga mata hannu ba tare da ya kalleta ba. Idanuwanshi na kan Safara ya ce,

“Ban kira da ke ba, ita na ce.”

Ya ƙarasa yana nuna Safara da hannu, yana kallon yadda ya takurata, ga kunya cike da fuskarta. Ya kuma ƙi daina kallonta.

“Ni ba binka nake ba.”

Ta faɗi muryarta can ƙasa, kai Altaaf ya girgiza.

“Bina kike yi…in ba haka ba, me yasa duk inda naje saina ganki? Me kike so?”

Asiya ta buɗe baki da mamaki tana kallon ƙarfin hali irin na Altaaf, ranta ma ya soma ɓaci, don duk ganinshi da take ba ƙaramin kyau yake mata ba. Yanzun ya nuna mata bai ma kula da ita ba, Safara kawai yake gani, yadda ya ɗaga mata hannu yasa kunya ta kamata ba kaɗan ba. Duk da mutanen kusa da su basa jin me suke cewa, suna kallon su. Musamman matan da gaba ɗaya hankalinsu na kan Altaaf.

“Me kike so?”

Ya tambaya yana ɗan ɗaga kafaɗun shi, murmushin takaici mai sauti ya suɓuce wa Safara. Yana da kyau ba za ta yi ƙarya ba, amma ko soyayya za ta yi ta san Altaaf ba sa’an soyayyarta ba ne, za ta yi aure har da yara kafin ya fara tunanin yin aure. Lokacin ta na da muhimmanci a wajenta, ba za ta iya ɓata shi akan Altaaf ba.

“Ba binka nake yi ba. Babu kuma abinda nake so.”

Ta fadi muryarta a daƙile. Murmushi Altaaf yayi yana ɗan murza agogon hannunshi. Kamar Safara ba ta yi magana ba ya ce.

“Bazan iya soyayya da ke ba. Kin sani ko? Level 1 nake yanzun.”

Wannan karon ita ta buɗe bakinta cikin mamaki. Bai bari tagama mamakin ba ya ɗauki wayarta yana faɗin,

“Amma zan iya zama abokinki. Ko don yadda kika dinga bina.”

Lambarshi ya saka a wayar yana kira tata lambar ta shiga tashi, tukunna ya kashe yana mata saving ɗin sunan shi da Altaaf Ismai’l kawai, tukunna ya tura mata wayar gabanta yana ɗorawa da,

“Altaaf Ismai’il. In kina son ganina kira kawai za ki yi ba sai kin sha wahala bina ba.”

Ya ƙarasa maganar da yanayin wasa yana mata murmushi tukunna ya tura kujerarshi baya yana miƙewa.

“Na barku cikin aminci.”

Ya faɗi yana cire hularshi tare da kwantar da sumar kanshi ya sake mayar da hular tukunna yasa hannuwanshi cikin aljihun rigar hood ɗin da ke jikinshi ya wuce yana jin yadda suke binshi da kallo. Hakan kuma yake so, wani irin murmushi yake yi, shi ba sa’an Idris bane ba. Jiya ma da suka haɗu sai da ya ce Altaaf ɗin ya bar wajen tunda su ba sa’anninshi bane ba. Ko lamba ya kasa karɓa a wajen Safara. Idanuwa da suka haɗa da Wadata ya girgiza mishi kai ne ya hana shi fasa bakin Idris. Duk da ya fishi girma yana da tabbacin bai yi rigimar da yayi ba, bai kuma da kalar zuciyarshi.

Gida ya wuce don bai jin yin darasin yammacin. Yana shiga su dukansu suna nan falo zaune, kaji ne a gabansu cikin ledoji sai lemuka, Wadata da system da takardu da alama karatun da baya gajiya da yi yake yau ɗin ma. Sai Jamal na danna waya. Yaks kuma hankalinshi na kan kajin da yake ci. Sallama yayi musu yana saka su duka juyawa suna kallonshi.

“Au sai na ji kamar anyi sallama…”

Jamal ya faɗi yana maida idanuwanshi kan wayarshi.

“Nima wallahi”

Cewar yaks. Dariya Wadata ya yi yana faɗin,

“Sallama ce mana…amma ba Altaaf ba ne.”

Kallonsu Altaaf yake yi, shi ma baisan sallamar ta suɓuce mishi ba, ya riga ya saba ne saboda su Safara.

“Me kuke nufi? Sallama na yi mana.”

“Yaushe ka fara sallama in za ka shiga waje?”

Yaks ya tambaya.

“Ina sallama mana…ina yi.”

Kai Jamal ya jinjina.

“Kana nufin yo! Ko yane? Ko kuma yunwa nake ji wallahi.”

Murmushi Wadata ya yi.

“Ko jikina na min ciwo.”

“Ko ku faɗa min dalilin da yasa nake zuwa makaranta.”

Yaks ya ƙarashe musu, don su ne sallamar Altaaf kullum. Yau ne karo na farko da ya yi musu cikakkiyar sallama.

“Me yasa kuke min hakane wai? Har da kai Yaya Wadata?”

Tari Yaks ya soma saboda lemon daya bi mishi ta wata hanyar.

“Yaya wa?”

Yaks ya tambaya. Dariya Altaaf yake yi.

“Ka bar ɗan iskan yaron nan. Wallahi ya raina ni.”

Wadata ya faɗi yana girgiza kanshi.

“Yaya Yakubu…”

Wannan karon su duka suke dariya. Rabon da Yaks ya ji wani ya kira sunanshi haka har ya manta.

“Karka sake”

“In sake me? Cewa Yaya Yakubu?”

“Wallahi kamar wani tsoho mai mata huɗun nan. Maza babanku bai duba maka ba. Yakubu fa? Yakubu.”

Jamal yake faɗi yana dariya. Harbi Yaks yakai mishi da ƙafa.

“Kaima ai Jamilu ne don ubanka. Wai Jamal…”

“Wallahi ƙarya kake. Jamal sunana.”

Hannu Altaaf yake ɗaga musu.

“Ku yi shiru. Yunwa nake ji ni.”

“Ina ruwan surutun mu da yunwarka?”

Wadata ya tambaya.

“Yay…”

“Idan ka ƙarasa wallahi sai dai ka fita ka nemo abinda za ka ci a gidan nan yau. Har gobe ma.”

Shirun Altaaf ya yi yana murmushi don yasan Wadata. Da gaske ba zai barshi ya ci duk wani abu da za su shigo da shi cikin gidan ba. Gashi ya fi ƙarfinshi, babu yadda zai yi da shi. Don haka ya rufa wa kanshi asiri yana zagayawa ya zauna. Wadata ya kalleshi da faɗin,

“Ka tashi ka wanko hannunka. Allah kaɗai yasan inda ya taɓa.”

“Inda ya taɓa mai tsabta ne…da…”

Pillow din kujera Wadata ya jefa mishi.

“Zauna ka ci…yi zaman ka.”

“Meye don na faɗa maka inda ya taɓa?”

Altaaf ya tambaya yana turo laɓɓanshi

“Bana son ji…”

“Wai da…”

Miƙewa Wadata ya yi, hakan na sa Altaaf ɗaga hannayenshi duka biyun tare da cewa,

“Na yi shiru wallahi…”

Duk da haka sai da Wadata ya harbeshi a baya tukunna ya wuce zuwa kitchen dama zai wanke hannunshi da ya ɓata ne. Dawowa yai ya zauna. Yana assignment ɗinshi suna hira sama-sama. Da Altaaf ya gama cin abinci ɗaki ya wuce shi ma ya watsa ruwa tukunna ya fito ya kwanta don bacci yake ji.

*****

Sai da satin ya ƙare wani ya shigo bai je inda duk za su haɗu da Safara ba. Bai kuma kira lambarta ba. Ya dai yi saving ɗinta. Yasan tana jira ta ga ko zai kira ko da kuwa ta goge lambar daga wayarta, duk wata baƙuwar lamba da za’a kirata da ita zata ɗauka saboda tana tunanin shi ne. Sai da yai kwana bakwai cif da karɓar lambar bai kira ba. Ranar da dare ya shirya tsaf. Su Wadata ma basa nan, yasan kuma suna gidansu Abdul, da alama sun fara game ɗin, don yanzun kusan kullum suna can.

Yana shiga gidan su Abdul kuwa ya same su, kiɗan da ke tashi na shigarshi, soma takawa ya yi, dama kwana biyu ba aiba. Wadata ya hana kawo party gidansu sai an gama jarabawa. Sosai yake takawa za ka rantse shi kaɗai ne cikin ɗakin, yana rawar ya ɗauko wayarshi yana ɗaga wa Abdul tare da yin murmushi. Ware idanuwa Abdul yayi cike da tambayar da ke fassara ‘Ka karɓo?’ kai Altaaf yake ɗaga mishi yana ci gaba da rawarshi. Remote Abdul ya ɗauka yana kashe kiɗan.

“Da gaske ka karɓo?”

Abdul ya tambaya, wajen na yin shiru, idanuwan kowa kan Altaaf din. Dariya Idris ya yi.

“Ya dai siya a wajen wani”

Wani kallo Altaaf ya watsa wa Idris ɗin

“Ba laifina bane don baka da ƙarfin halin karɓar lamba a hannun mata sai dai ka siya… Ba kuma laifina bane don ka zo a mummuna…”

Dariya suke yi banda Idris da ya miƙe, Abdul na riƙo shi.

“Barshi ya ƙaraso mu gama abin nan yau don Allah.”

Cewar Altaaf don sosai yake so ya gyara wa Idris ɗin zama. Kai Abdul ya girgiza wa Altaaf ɗin yana faɗin,

“Ba siya yayi ba. Na sa John ya bishi.”

Daƙuna fuska Altaaf ya yi. Abdul na ɗaga mishi kai.

“Game ɗin mu na da muhimmanci. Ba kuma ma son cheating…”

Waje Altaaf ya samu ya zauna. Lambar Safara yai dialing yana sakawa a speaker tukunna yai musu alama da su yi shiru. Sai da ta kusan yankewa tukunna ta ɗaga. Cikin sanyin muryarta ta yi sallama. Amsawa Altaaf ya yi tashi muryar a ƙagauce kamar bashi ya kirata ba. Bai tambayi ya take ba don mata irinsu lallami ba zai yi aiki ba, sun riga da sun saba da hakan.

“Baki faɗa min sunan ba. Bansan dame zan ajiye lambarki a wayata ba”

“Hmm…”

Safara ta faɗi daga ɗayan ɓangaren, tana nuna mishi alamar bata goge tashi lambar ba. Shiru ya yi bai sake cewa komai ba

“Hello…”

Safara ta faɗi daga ɗayan ɓangaren jin shirun yayi yawa.

“Ina jinki. Sunan za ki faɗa min.”

Sai da ta yi jim kamar ba za ta ce wani abu ba tukunna ta ce,

“Safara Auwal.”

“Na barki cikin aminci.”

Altaaf ya faɗi yana kashe wayar. Ihu wajen ya ɗauka gaba ɗaya. Abdul na dukan Altaaf ɗin a kafaɗa. Idris ya kalla yana faɗin,

“Furfura ce a fuskarka? Oh tamoji ne ashe, shekararka nawa wai?”

Kallon ‘ka matso kusa ka ga abinda zai faru’ Idris yake ma Altaaf ɗin. Dariya Altaaf yake yi

“Bana haɗa ƙashi da tsofaffi. Kafin ka shafa min muni.”

Hannu Idris ya kawo ma Altaaf ɗin. Wadata ya janye Altaaf gefe yana kallon Idris.

“Bansan me ya tsare maka ba. Ban taɓa maka magana akanshi ba saboda ina ɗauka kawai iya baki ne. Ranar da hannunka zai taɓa jikinshi zai zama ranar da za ka yi babban kuskure.”

Cikinsu duka babu wanda baisan Wadata ba. Bashi kaɗai ba ma, duka makarantar sun san Wadata, sun san abinda zai iya sa a aikata. Idanuwan Idris da suke cike da tsoro Altaaf yake kallo, kafin ya tashi yana kwantar da kanshi a kafaɗar Wadatan.

“Yaya Wadata…”

Hankaɗe shi Wadata ya yi har ya faɗa kan kujera. Dariya Abdul yake sosai kafin ya kalli Altaaf yana faɗin,

“You are in. Welcome to the game”

“Abdul…”

Wadata ya kira cike da kashedi.

“Ya cika sharuɗɗan Wadata. Ka yi haƙuri.”

Cewar Abdul. Numfashi Wadata ya sauke.

“Karka bari ya shiga karatunka…”

Hannu Altaaf ya ɗaga yana ma Wadata salute. Yau a sama yake jinshi, ko bakomai ya cakar da idris. Hakan ma kaɗai ya mishi daɗi, kuma sai ya tabbatar shi ya ci game ɗin su na wannan shekarar, gyara zamanshi ya yi yana kwanciya sosai cikin kujerar.

‘Yan matan ABU ku fara neman wajen ɓoyewa.’

Ya faɗi a cikin zuciyarshi yana lumshe idanuwanshi. Kiɗan da suka sake kunnawa yana shigarshi a hankali.

<< Alkalamin Kaddara 26Alkalamin Kaddara 28 >>

1 thought on “Alkalamin Kaddara 27”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×