Bayan Wasu Shekaru
Inda ance ma Altaaf zai kai lokacin nan a makaranta zai ƙaryata. Don an kori mutane da yawa, baya buƙatar takardun makaranta ya sani, bai taɓa tunanin aikin gwamnati ba, kasuwanci yake son yi, Ammi kuma na nan bai da matsala. Amma yana buƙatar zama a makaranta, ya kuma san dalilin hakan Wadata ne. Da bai koya mishi yadda zai zauna ya yi karatu ba da hakan bai faru ba.
Yanzun gashi yana shirye-shiryen jarabawar gama aji uku. Shekara ɗaya ta rage mishi ya gama tunda fanninshi shekara huɗu. . .