Skip to content
Part 28 of 52 in the Series Alkalamin Kaddara by Lubna Sufyan

Bayan Wasu Shekaru

Inda ance ma Altaaf zai kai lokacin nan a makaranta zai ƙaryata. Don an kori mutane da yawa, baya buƙatar takardun makaranta ya sani, bai taɓa tunanin aikin gwamnati ba, kasuwanci yake son yi, Ammi kuma na nan bai da matsala. Amma yana buƙatar zama a makaranta, ya kuma san dalilin hakan Wadata ne. Da bai koya mishi yadda zai zauna ya yi karatu ba da hakan bai faru ba. 

Yanzun gashi yana shirye-shiryen jarabawar gama aji uku. Shekara ɗaya ta rage mishi ya gama tunda fanninshi shekara huɗu ne ba kamar na su Wadata da yake shekara biyar ba. Su sun gama yanzun. Amma babu abinda ya taɓa zumuncin su, sai ma ƙaruwa da ya yi musamman ma da Wadata, tunda har bikin gidansu da akayi sai da ya zo har Zaria. Ƙauna mai girma ce tsakaninsu da Altaaf ɗin. 

Duk da yanzun suna yawan faɗa da Altaaf akan halayyarshi. Wadata na gani lokaci yayi da ya kamata Altaaf ɗin ya rage abubuwan da yake yi l, su lokacinsu suna girma suna ragewa, amma a ɓangaren Altaaf ba haka abin yake ba, yana girma yana ƙara lalacewa. Yanzun babu wanda baisan A-Tafida a ABU ba. Kafin su Abdul su fita sai da suka koya mishi shan cocaine, wanda ba yadda Wadata bai yi ya daina ba amma ya ƙi. 

Gashi yanzun shi da mata abin sai hamdala. In har ya ƙyalla ido kan yarinya sai ya sameta yake zama lafiya. Bai damu kuma da duk hanyar da zai bi ba, kuɗi, yaudara, duk wadda ya ga za ta fi mishi sauri ita yake bi. Rashin mutunci duk girmanka baka wuce shi wajen Altaaf ba, ya biya kuɗi ai maka duka ba komai bane ba. Shi yasa kowa yake tsoron shiga harkarshi. Tun tafiyar su Wadata shi kaɗai yake zama. Gida ya kama mai ɗaki biyu a area ɗin. In wani ya kwanar mishi to mata ne, amma duk yadda kuke in namiji ne kai ba za ka kwanar mishi ba. 

Yanzun ma daga aji gida ya taho kanshi tsaye, a tsakiyar falo ya zare takalman ƙafarshi yana barinsu nan, jakar kan kujera ya wurgata, bayanshi ya dafe da duka hannuwa biyu yana yin miƙa, jikinshi yake ji yana ciwo, ya kuma san rashin motsa shi ne da bai yi ba kwana biyu, duka hutun ƙarshen mako a gida ya yi shi, daga bacci babu abinda yake yi, tunda waya kawai zai yi in yana son wani abin za’a siyo mishi a kawo har gida. 

Mukullin mota yake zarewa daga Aljihunshi ya ji an shigo, juyawa yayi yana jan ƙaramin tsaki ganin Mimi ce. 

“Inata kiranka a waya baka ɗauka ba. Na maka text na faɗa maka maganar na da muhimmanci…” 

A kasalance yake kallonta yana murza wuyarshi. 

“Shi ne za ki shigo min gida ba sanarwa?”

Ya tambaya yana ƙanƙance idanuwanshi. Baisan me yasa take da naci ba, duka sau nawa wani abu ya shiga tsakaninsu. Amma ta ƙi gane cewa mata kamar takalma suke a wajenshi, in sun mai zai siya ya saka na wani lokaci, daya gaji zai ajiye su ko bai hango sabo ba. Duk da shi ne namijin farko da wani abu ya shiga tsakanin su baya nufin ta takurashi haka. 

“Haba A-Tafida…”

Mimi ta faɗi idanuwanta cike taf da hawaye. Wani sauti Altaaf ya fitar can ƙasan maƙoshin shi, a gajiye yake ga yunwa yana ji, ba zai iya da wannan drama ɗin ba yanzun. Baisan me yasa kuka baya wa mata wahala ba, duk da ya saba gani, tunda hakan na yawan faruwa da shi, basu taɓa damunshi bane ba. 

“Kinga yanzun na dawo, jikina na min ciwo, kuma ina jin yunwa. Maganar ba za ta jira wani lokaci ba?” 

Kai ta girgiza mishi, tana sa hannu ta goge hawayen da suka zubo mata. Numfashi Altaaf ya sauke yana faɗin, 

“Menene?”

Buɗe baki ta yi za tai magana kuka ya ƙwace mata, ko motsawa bai yi daga inda yake ba ballantana yai yunƙurin lallashinta. Idanuwa ya kafa mata fuskarshi da nuna alamun ƙosawa, ta yi sauri ta gama kukan tai mishi bayani, yadda abubuwa masu muhimmanci da suka fi kallonta tana kuka. Sai da ta yi mai isarta tukunna ta ɗago muryarta na rawa ta ce, 

“Na yi ɓatan wata…”

Ta ƙarasa wasu sabbin hawayen na zubo mata. Kallonta Altaaf yake cike da rashin fahimta m

“Ɓatan wata kuma?”

Ya buƙata. Kai ta ɗaga mishi, tsaki ya ja. 

“Shi ne me to? Abinda za ki faɗa kenan kika sa na ɓata lokacina tun ɗazun? Bayan na faɗa miki yunwa nake ji?” 

Altaaf yake faɗi ranshi a ɓace, kuka ta ci gaba da yi sosai, juyawa yayi da nufin barinta a falon, inta gaji ta tafi, don bai san meye wani ɓatan wata ba. Yunwar da yake ji ma ba zata barshi wani dogon tunani ba. Ganin haka yasa Mimi saurin cewa, 

“Ina da ciki.”

Wata irin juyowa Altaaf yayi yana ware mata idanuwa, tunaninshi na yawo da abubuwan da suka faru tsakaninshi da ita, dafe kai ya yi. 

“Mimi baki da hankali? Ya akai haka?”

Dariyar takaici tayi

“Ni kake tambaya ya akai haka? Ni ce banda hankali?” 

“Kina da shi ne? Mimi kina da hankalin ne? Da kina da shi da kin je kin zubar.” 

Ware idanuwanta ta yi kanshi cike da mamaki kafin ta haɗe space ɗin da ke tsakaninsu tana ɗaga hannunta da nufin marinshi, riƙe hannun Altaaf ya yi yana mata wani murmushi da ba shi da alaƙa da nishaɗi. 

“Kuskurenki na farko yarda da ni, kuskuren da zaki yi na biyu shi ne ɗaga min hannu…” 

Kuka Mimi take yi, yana ganin tsanarshi a idanuwanta, cike da dana sani, ya saba gani ba baƙon abu bane a wajenshi. Zuwa yanzun bai san ciki nawa aka zubar mishi ba, ya soma bi a hankaline saboda Wadata, wasu da yawa sun ɗauka Yayanshi ne, sun kuma san office ɗin shi don ba ɓoyayye bane, sukan kuma je su gaya mishi. 

“Kije ki zubar, ko nawa ne zan baki, karki sake tako min cikin gida, yau ya zama ranar ƙarshe da zan sake ganinki…” 

Kai Mimi take girgizawa, Altaaf bai bata damar yin magana ba ya jata zuwa ƙofa yana buɗewa. 

“Da gaske nake kar in sake ganin ki, ki turo min account number ɗinki…” 

Ya ƙarasa yana turata, saura kaɗan ta faɗi, dai-dai lokacin da ya ga motar Wadata, ya kuma ganshi yana kan fitowa daga ciki. 

“Damn…”

Ya faɗi a ƙasan maƙoshin shi. Yana kallon Mimi da mamaki ya hanata ko motsi, ba zai tuna a yadda ya je mata ba, in tana ɗaukarshi mai mutunci wannan kuskurenta ne. Ta bar wajen kafin Wadata ya ƙaraso ne matsalarshi. 

“Mimi ki tafi… Don Allah kije zan kira ki mu ƙarasa maganar nan.” 

Altaaf ya faɗi yana tausasa muryarshi, ganin Wadata na takowa inda suke. Sai dai lokaci ya ƙure don har ya ƙaraso, kallo ɗaya yaima Mimi da yanayinta, sannan ya kalli Altaaf ɗin yana girgiza kanshi kawai. Hankalinshi ya mayar kan Mimi da faɗin, 

“Zaki yi tunani kala-kala yanzun. Amma guda ɗaya ne zai fi miki alkhairi, ki cire cikin nan ki ja bakinki ki yi shiru. In kina tunanin kai ƙara ne ba zai yi aiki ba in ba ki da wadataccen kuɗi kuma asirinki zai tonu… In kina tunanin ya aureki ne mafarki ne da ba zai taɓa faruwa ba…in zaki kira iyayenki ne kuma to, sai ki shirya haifo abinda ke cikinki…” 

Cike da tashin hankali Mimi take kallon Wadata. Kai ya jinjina mata. 

“Ba yadda za’a tabbatar da cikin shi ne ba’a gwada ba, sai kuma kin haifoshi hakan zai faru…” 

Muryarta na rawa ta ce, 

“Yasani wallahi. Shi ne na farko kuma shi kaɗai ne.” 

Ɗan ɗaga kafaɗa Wadata ya yi. 

“Shine na farko zan iya yarda. Amman shi ne kaɗai ne zai min wahala…” 

Kuka ya ƙwace mata, daga Wadata har Altaaf sun san bata da wata mafita. 

“Ki tafi gida. Ki aiko mishi account number ɗinki. Kina jina?” 

Kai ta ɗaga mishi tana wani irin kuka da Wadata yake ji har a ranshi. Duk abinshi baya son kukan mace, ɗaga mishi hankali yake yi. Musamman yanzun da yake ganin duka babu ranar abubuwan da suka yi a baya sai tarin zunubin da baisan ko shekarun da suka rage mishi a duniya sun isa ya wanke kanshi ba. 

“Kar in sake ganinki a kusa da gidan nan. Yau ya zama na ƙarshe. ” 

Yana ganin tsoro cikin idanuwanta da yanayin da yai maganar, don da ƙyar ta iya ɗaga mishi kai tana wucewa. Altaaf Wadata ya kalla, kallon da zai tsorata wasu mutanen da ba Altaaf ba, tunda yasan babu abinda Wadatan zai mishi. Duk da hakan bai hanashi turo laɓɓa ba. 

“Yaya Imran mana”

Ya faɗi, don tun yana kiran Yaya Imran ɗin da zolaya har abin ya zauna mishi. Tunda har a ranshi yake jin Wadata kamar Yayanshi. 

“Me na faɗa maka? Ka raina ni ko Altaaf? Banda mutunci a idonka, ina cikin mutanen da basu isa su faɗa maka magana ka saurara ba.” 

Shagwaɓe fuska Altaaf ya yi. 

“A waje za kai min faɗa yanzun?”

Kai Wadata ya jinjina yana juyawa, da sauri Altaaf ya riƙo hannunshi. 

“Yi haƙuri.”

Fisge hannunshi Wadata ya yi. 

“Haƙuri zai gyara abinda kayi? Ciki na nawa ne wannan a shekarar nan kawai? Sai ka samu wadda zata barshi ne za ka ci ubanka, sai ta haifoshi ta kawo maka.” 

“Allah ya sawwaƙe…”

Altaaf ya faɗi yana daƙuna fuska. Ta ina zai fara karɓar ɗan gaba da Fatiha, ya ce wa Ammi me? Don mutumin kirki take ganin shi, nutsatsen ɗanta da take alfahari da shi. Komai zai faru ya faru amma kar ya taɓa Ammi, mutane da yawa yasan za su yi mata Allah ya ƙara musamman wanda suke ganin ta lalata shi. 

“Meye na Allah ya sawwaƙe?”

“Shege fa? Haba Yaya Imran, ina son yara kaima ka sani, amma nawa…” 

Taɓe baki Wadata ya yi. 

“Waɗannan ɗin ba naka ba ne ba?”

“Eh amma ai na kirki, in na yi aure nake nufi.” 

Numfashi Wadata ya sauke. Sai ya ɗauka ya gaji da ma Altaaf faɗa, sai ma ya ce ba zai ƙara ba zai saka mishi ido sai ya kasa kuma. 

“Baka ji wallahi.”

Kai Altaaf ya ɗaga 

“Na sani… Zan daina ai, ka dinga min addu’a.”

Hararar shi Wadata ya yi, ƙarasawa Altaaf ya yi yana zagaya hannunshi akan kafaɗar Wadata. 

“Ka ga yadda yarinyar nan ta tsorata? Da za ta samin ciwon k…” 

Bai ƙarasa maganar ba saboda wani irin duka da Wadata yai mishi da gwiwar hannu a haƙarƙari yana sashi sauke hannunshi daga kafaɗar Wadata babu shiri, numfashin shi na tsayawa na wucin gadi saboda bai tsammaci dukan ba, kuma bana wasa Wadata yai mishi ba. 

“Sa’anka ne ni? Ka ɗauka na ji daɗin abinda ka sani yi ne?” 

Murza wajen Altaaf yayi, har lokacin ya kasa magana, iska ma ta baki yake shaƙarta, wuyan rigarshi Wadata yakama yana janshi cikin gida tare da wurgashi kan kujera. Sai lokacin ya iya cewa, 

“Kashe ni za ka yi? Ka karya min haƙarƙari”

Kai Wadata ya girgiza mishi. 

“Ban karya ba, amma nan gaba zan karya ɗin. Fita za mu yi tashi.” 

Da ƙyar Altaaf ya iya miƙewa yana dafe da haƙarƙarinshi har lokacin wajen zafi yake mishi sosai. Duk da ba lokacin Wadata yake mishi irin haka ba, na yau ya fi shigarshi fiye da koyaushe. Ko bai yi komai ba, in yana jin cin zalinshi haka yake mishi. 

“Allah sai Ya saka min.”

Altaaf ya faɗi ƙasa-ƙasa. 

“Magana kake yi?”

Wadata ya tambaya yana murmushi da duka haƙoranshi a waje. Kai Altaaf ya girgiza mishi yana wucewa ɗakin baccin shi, don sai ya watsa ruwa tukunna, gefen hannun kujera Wadata ya zauna, ganin Altaaf ya daɗe bai fito ba yasa shi ƙwala mishi kira. 

“Altaaf!”

“Gani nan zuwa. Abu nake nema.”

Altaaf ɗin ya amsa daga can cikin ɗakin, miƙewa Wadata yayi yana ƙarasawa ɗakin, tura ƙofar ya yi ya ji ta ƙi wucewa, don haka yasa ƙarfi yana turawa. Runtsa idanuwa yayi ya sake buɗe su, don yana son tabbatar ɗakin mutum ne ba kasuwar gwanjo ba. Kayane a baje ko ina na ɗakin, baifi sati da zuwa gidan ba, kuma ya shiga bedroom ɗin Altaaf ɗin, wannan kayan da alama sun kai wata biyu ko fiye da haka ana tarasu, ya jima bai shigo nan ɗakin ba shi yasa baigani ba. 

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un.”

Wadata ya faɗi, Altaaf da ke ɗakko kaya a wardrobe ɗinshi ya ɗago yana ware mishi ido, duk da yasan abinda yake magana akai. 

“Wani ya mutu ne?”

Ganin Wadata ba amsa shi zai yi ba yasa shi ci gaba da jawo kayanshi yana watsawa kan gado, akwai rigar da yake nema, sabuwa ce ma bai ko saka ba, ya rasa inda ya ajiye. Hakan ya tabbatar wa Wadata ba kayan dauɗa bane kawai a ƙasa, har da wankakku, don duk wanda Altaaf ɗin ya janyo bai mishi ba anan yake wurgarwa. 

“Ka daina jefar da kaya haka…”

“Ni banga rigata ba.”

Ya faɗi yana ci gaba da abinda yake yi, takalmanshi Wadata ya cire a bakin ƙofar yana faɗin, 

“Daina wahalar nema, ina me wankinka?”

Ɗan ɗaga kafaɗu Altaaf ya yi. 

“Ina nufin in kirashi, ban samu zama ba ne.”

Kai Wadata ya jinjina yana ajiye wayarshi gefen gadon Altaaf ɗin. 

“Babu inda za mu je…ɗakin nan za mu gyara.”

“Kai da wa?”

Altaaf ya tambaya. 

“Ni da waye a ɗakin?”

“Ni da kai, amma bance ina son gyarawa ba.”

Harara Wadata ya watsa mishi. 

“Bance ko kana so ko bakaso ba.”

“Wallahi yunwa nake ji, tunda safe rabona da inci wani abu.” 

Altaaf ya yi maganar kamar zai yi kuka. 

“Good. Sai ka daina ɓata lokaci ko za mu gama da wuri don ka ci wani abu.” 

Yadda yai maganar babu wajen gardama yasa Altaaf yin shiru. Ba don yana so ba suka gyara ɗakin, suna ware kayan dauɗar suka mayar da wanda basu da datti, basu fita daga gidan ba sai da Wadata yasa Altaaf ɗin ya kira mai wankin shi yazo ya ɗauka tukunna. 

***** 

“Wai kai ma aure za ka yi?”

Altaaf yake tambayar Jamal muryarshi ɗauke da mamaki. Don lokacin da Wadata ya faɗa mishi an kai kuɗin neman aurenshi bai yarda ba, sai da aka sa rana. Gashi yanzun sauran kwana biyu da yake rayuwar babu wahala. Kai Jamal ya ɗaga mishi yana murmushi. Yaks Altaaf ya kalla yana tambayar,

“Me yake damun su?”

Ɗan ɗaga mishi kafaɗa Yaks yai yana dariya. 

“Dariya za ka yi? Ba zaka faɗa mishi kaima ka kusa ba?” 

Jamal ya buƙata, hannuwa Altaaf yasa yana toshe kunnuwanshi tare da girgiza musu kai. 

“Bana son ji, ku duka kun samu matsala…duka nawa kuke da za ku yi aure? Kuna so ku tsufa da wuri ko? In fa kukai aure shikenan jin daɗi ya ƙare, ba zaku fita da mata ba, ba za ku…” 

Hannu Wadata ya ɗaga mishi. 

“Ya isa… Kai baka tunanin yin auren?”

Ware ido Altaaf ya yi. 

“Ba yanzun ba wallahi. Taɓ! kudai ku yi…wai ƙarfe nawa ne partyn nan? Jikina na min ƙaiƙayi.” 

Duka Jamal ya kai wa Altaaf ɗin da ya kauce yana dariya da faɗin, 

“Tunda kun tsufa ba sai ku bar mana ba. Nan da shekara mai zuwa su Yaya Imran an zama Baba.” 

Miƙewa Wadata yayi yana sa Altaaf ɗin tashi ya ruga. 

“Da ka tsaya ai, marar kunyar ƙarya.”

Dariya Altaaf yake yi. Party za su yi na bikin Wadata da babu mata, abokanshi ne na kusa da na nesa da za su haɗu don taya shi murna. Su Jamal ne suka haɗa mishi. Waje suka kama musamman don yin shagalin, nan gidan Altaaf sukai zamansu suna hira har sai da takwas ta yi suka shirya tukunna suka wuce wajen partyn. Sosai yaima Altaaf daɗi don an yi harkar girma yadda yakamata. 

Hidima suke babu kama hannun yaro har ranar dinner ɗin bikin. A karo na farko da Altaaf ya ɗinka manyan kaya, manyan shaddoji ne sosai, har babbar riga ya ɗinka na washegari ɗaurin aure. Yauma duk inda ya wuce idanuwan mata na kanshi, yasan yana da kyau ko da ba’a faɗa mishi hakan kullum. Shaddarshi ruwan ƙwai mai haske, gashi ta ɗinku, sai hula da takalmi da agogo kalar mai cizawa. Shi kanshi sai yake jin me yasa bai saka manya kaya tun can, don yadda ya ga kayan sun karɓeshi. 

Zaune yake, idanuwanshi na kan wata yarinya da take ta mishi murmushi tunda suka zo wajen, amma ya ƙi ya mayar mata, duk da fuskarshi a sake take, amma bata ga wajen mishi magana ba ne ba. Yana so ya tabbatar babu wadda ta fita kyau a wajen tukunna yai mata magana. Robar ruwa ya ɗauka yana kwancewa ya ji MC ɗin na ya kira sunanshi. 

“Altaaf Ismai’il Tafida da aka fi sani da A-Tafida zai bamu taƙaitaccen tarihin angon.” 

Ware idanuwa yake yi cikin mamaki, yana sauke su kan su Jamal, don ɗaya daga cikin su ne ya kamata ya ba da tarihin Wadata, su ne abokanshi, shi ƙanine, dariyar da ya ga suna yi ne yasa shi sanin da gangan suka yi haka. Wadata da ke zaune kusa da amaryarshi Maryam ya kalla. Kai ya girgiza mishi yana dariya, alamar shima bai san za su yi haka ba. Miƙewa Altaaf yayi yana takawa har wajen ya karɓi abin maganar daga hannun MC ɗin. 

Magana cikin taro ba matsalarshi bane ba, komin yawansu kuwa, abinda zai ce ne matsala. Murmushi yayi, yana ɗago abin maganar. 

“Babban abokin ango ne yakamata yayi ɓangaren nan. Yana da su har guda biyu bansan me yasa aka kirani ba…” 

Dariya aka ɗan yi. 

“Imran Hassan Engineer ne, yayi primary ɗinshi…” 

Ɗan jim Altaaf ya yi, kafin ya juya ya kalli Wadata. 

“A ina kai primary?”

Ya tambaya, dariya aka yi, Wadata kanshi dariya yakeyi. Kafin Altaaf ɗin ya yi murmushi. 

“Well ba shi bane abu mai muhimmanci, bana tunanin akwai abinda za ku yi da sanin tarihin karatun shi, duka zai kawo mu inda ya zama Engineer ne, don haka zan tsallake duk wannan abubuwan…” 

Ɗan jim Altaaf ya yi, har da safiyar ranar sai da yaima Wadata magana kan auren don a yadda ya ɗauki aure yanzun bai wuce takura ba. Sai dai me yanzun da yake tsaye, yana jin shi daban, yana jin yadda can ƙasan zuciyarshi yake farin ciki da inda rayuwa ta kawo Wadata ɗin, juyawa yayi ya kalle su shi da Maryam, ya kalli farin cikin da ke fuskokinsu, murmushi ya yi. 

“Bansan sa’adda rayuwa ta kawo ka nan ba Yaya Imran, banda abin ce maka ko mutanen da ke cike da wajen nan. Amma ina da abubuwa da yawa da zan faɗa wa Maryam…” 

Ware mishi idanuwa Wadata ya yi a wasance, hannu Altaaf ya ɗan ɗaga mishi. 

“Karka da mu ba zan faɗa mata yawan ‘yan matanka na makaranta ba, sirrinka na adane a zuciyata…” 

Dariya aka sake yi, Wadata nakai hannunshi a wuya yana yankawa, alamar zai kashe Altaaf ɗin. Dariya Altaaf ya yi, kafin fuskarshi babu alamar wasa ya soma cewa, 

“Karki duba rayuwar shi ta baya saboda ta riga da ta wuce, ki duba ta yanzun, yau, dai-dai lokacin nan, ki duba yadda ya zaɓi bude shafin rayuwarshi mai zuwa tare da ke. Shekaru biyu da suka wuce inda wani ya faɗa min ya hango ma Yaya Imran yau bazan yarda ba. Amma gashi yana faruwa, ke ce zaɓin shi, a ƙarshe ke ce zaɓin shi karki manta wannan…” 

Altaaf ya ƙarasa muryarshi na sauka, kafin ya ci gaba da faɗin, 

“Duk da bansan me ya faɗa miki kika zaɓe shi ba, na san bai kai sauran kyau ba.” 

Kai Wadata ya sake dafewa, Altaaf na haɗe hannayenshi duka biyu cikin ban haƙuri duk da dariya yake, har ranshi yake taya Wadata farin ciki don ƙaunarshi mai girma ce a zuciyar Altaaf ɗin. 

“Ina taya ku murna. Ku kasance cikin farin ciki. Na gode.” 

Altaaf ya faɗi yana miƙa wa MC ɗin abin maganar da ke hannunshi, tafi aka shiga yi wa Altaaf ɗin. Sannan ya koma wajenshi ya zauna. Haka abubuwa suka ci gaba da kasancewa har aka ƙare hidimar ranar. Su duka gidan Altaaf suka wuce bayan sun mayar da su Maryam da duk mutanenta gidajen su. Gaba ɗaya jikin Altaaf ciwo yake mishi. Ga wani irin bacci da yake ji, ko kaya bai iya sakewa ba haka ya kwanta. 

***** 

Sai yanzun Altaaf yake ganin dalilin da yasa Wadata ya auri Maryam. Tana da kirki ba kaɗan ba, wajen aikinsu ɗaya ita da Wadata, lokuta da dama sukan biyo su kawo mishi abinci kafin su wuce wajen aiki. A hankali Maryam ta zama mace ta huɗu da yake ganin ƙima, don yana jin kunyarta sosai, akwai wannan kwarjinin a tare da ita. Har aikenshi tanayi in za ta yi siyayya, kuma ya je mata, ko me yake zai ajiye ya je , abin har mamaki yake bashi. 

Yanzun ma shagon telanta ya je ya amso mata ɗinkunan da ta bayar. Yana shiga falon da sallama. Yanayin su ya gani da yadda Maryam take ɗauke da wata babbar jaka yasa shi faɗin, 

“Matar Yaya lafiya?”

Kamar yadda yake kiranta. Kai ta girgiza mishi. 

“Hajiya ta yo waya an yi rasuwa.”

Kan kujera Altaaf ya ajiye ledar da ke hannunshi. Cikinshi na ƙullewa, sam baya son ya ji zancen mutuwa. 

“Wa ya rasu?”

Altaaf ya tambaya cikin sanyin murya. 

“Ƙanin Daddy ne. Yanzun za mu wuce…”

“Mu je to”

Altaaf ɗin ya faɗi. 

“Kana da makaranta Altaaf, kwana za mu yi.”

“Shi ne me? Karka ce min ba zan je ba don wallahi ba saurarenka zan yi ba.” 

Kai Wadata ya jinjina mishi don yasan halin gardamar Altaaf ɗin. 

“Kaya fa to?”

“Akwai a motata, na karɓo wanki da safe, sai in ɗauka mu wuce.” 

Altaaf ya ƙarasa maganar yana juyawa ya fita daga ɗakin. Kaya ya ɗauka kala biyu, bai da buƙatar motarshi tunda za su tafi a ta Wadata ne. Don haka ya gyara parking ɗinshi sosai, tukunna ya wuce yana buɗe baya zai zauna, Maryam ta riga shi. 

“Matar Yaya.”

Ya faɗi a kunyace, don har ranshi yai niyyar bar mata su zauna a gaba ita da mijinta. 

“Ka wuce ka zauna Altaaf.”

Ta faɗi, kai ya ɗan ɗaga yana zagayawa ya buɗe motar ya shiga. Wadata ne ya shigo shima ya tayar da motar. 

“Ko ka kawo in tuƙa”

“Aiko ni kaɗai ne ma bazan baka ba…kai ɗin?” 

Dariya Maryam ta yi. 

“Me yasa? Don zai hutar da kai.”

Ta mudubin gaba Wadata ya kalli Maryam.

“Kin san gudun mutuwar da yaron nan yake yi da mota kuwa?” 

“Yanzun fa na daina. Wannan tun muna yara ne.” 

Tsaki Wadata ya ja kawai yana mayar da hankalinshi kan tuƙin da yake yi. Altaaf kuma na gyara zamanshi ya kwanta cikin kujerar sosai. 

“Ina za mu je?”

“Ƙauyen kinkiba.”

Wadata ya amsa shi a taƙaice, kai Altaaf ya jinjina yana maimaita sunan, hira suka ci gaba da yi jefi-jefi har suka isa ƙauyen. Akwai wani abu tattare da ƙauye da yake burge Altaaf da bai zai ce gashi ba. Gashi dai basu da wani kuɗi, amma akwai nutsuwa a tattare da yanayin su, tunda suka soma shiga ya juyar da kanshi yana kafe idanuwanshi ta glass ɗin motar yana kallon gari. 

A hankali Wadata yake tafiya saboda ramuka da yanayin damina ya bari, tun kamun su ƙarasa ya hangota tana soya wani abu da ba zai ce awara bace ko dankali. Sai wata budurwa a tsugunne kusa da ita da alama labari suke. Gefen fuskarta ya fara gani kafin ta ɗago tana dariya, dimple ɗinta duka biyun suka bayyana, fuskarta ɗauke da manyan idanuwan da sukai wa Altaaf ɗin tsaye. Ba fara bace ba, baƙa ce amma tana da wani irin kyau daya bashi mamaki. 

Bai taɓa zaton akwai me kyau kamarta a ƙauye ba, sai ma da suka matsa kusa yaganta sosai, akwai wani abu a tattare da dariyarta daya shiga wani waje cikin kanshi ya zauna. Fuskarta yake son tallaba cikin hannunshi tana dariyar nan, tunda yake a duniya bai taɓa jin son kusantar wata mace kamar haka ba a ganin farko, baisan ya ɗora hannunshi ta glass din motar bama kamar zai shafa fuskarta ta ciki da yake hangowa. Koda suka wuce wajenta glass ya sauke yana zira kanshi. 

“Altaaf uban me kake kallo? Ƙura zata cika min mota.” 

Wadata ya faɗi. Sai lokacin Altaaf ya dawo cikin hankalin shi, sama yayi da glass ɗin, bai ce komai ba, sai ya ji kamar jikinshi na ɓari, cocaine ɗinshi yake son shaƙawa ko zai ɗan samu nutsuwa, hannu yasa jikin aljihunshi yana jin alamar ledarta, suna zuwa zai ce a nuna mishi banɗaki don ya shiga ya samu ya shaƙa. Yana buƙatar yarinyar nan ta fita daga kanshi, kafin a samu matsala.

<< Alkalamin Kaddara 27Alkalamin Kaddara 29  >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×