Skip to content
Part 32 of 52 in the Series Alkalamin Kaddara by Lubna Sufyan

Lagos

Tunda Omeed ya fita daga gidan ya ɗauko Sayrah daga makaranta bata fito daga ɗakin baccin ta ba sai yanzun, bata kula ta ɗauko hijab ɗinta a hannu ba sai da ta zo zama. Ajiyewa ta yi kan kujera tana kallon agogo, sosai yamma ta yi, tasan zasu iya kaiwa magriba ma su Omeed basu shigo gidan ba saboda yanayin cunkoson garin Lagos. Wannan ba damuwarta bane ba, zuciyarta ta kasa daina bugawa tunda ta tura saƙon nan. Bata san ko ya je ko bai je ba, saboda bata tsaya duba hakan ba ta goge. 

Har wani zazzaɓin tashin hankali ne ya rufeta, don saida Omeed ya bata magani yai tsaye ya ga ta sha tukunna ya fita, cewa yai ta kwanta karta fita ko ina, amma ta gaji da zaman ɗakin, tunani da tsoro ya haye mata, in har Rafiq bai samu saƙonta ba, bata zaton tana da ƙarfin zuciyar sake tura wani, yanzun haka gani take kowanne lokaci Omeed zai iya gane abinda ta yi , lumshe idanuwanta ta yi tana haɗiye wani abu da yai mata tsaye a maƙoshi. 

“Yaya don Allah ka zo, komai zai iya faruwa in ba ka zo ba.” 

Ta faɗi muryarta cike da rauni, sabon zazzaɓi na sake saukar mata. Har a ƙasusuwanta take jin gajiya da zama da Omeed ɗin, tana jin inya sake ɗaga mata hannu mutuwa za ta yi kawai saboda yadda ta gama gajiya, kamar abinda yai mata da safiyar ranar ne ya ƙure gaba ɗaya haƙurinta, kamar dama can hakan take jira yadda ta gaji da zama da shi ya haɗar mata waje ɗaya. Miƙewa ta yi ta ɗauko ruwa mai sanyi a fridge ɗin falon tana dawowa ta zauna, ta buɗe robar ruwan kenan bata kai da sha ba ta ji an ƙwanwasa ƙofar, jikinta na ɓari ta ajiye robar tana rufewa tare da rugawa kitchen, kofi ta ɗauko ta ajiye. 

Omeed in yana son dukanta yana neman dalili komin ƙanƙantarshi, zai iya cewa ta san ba tsafta ba ne shan ruwa daga jikin robar, sai da ta ɗan tsaya na ‘yan daƙiƙu tana neman nutsuwa ko ya take tukunna ta taka zuwa ƙofar, tana ji aka sake ƙwanƙwasawa. Mukullin da ke jiki ta fara murzawa tukunna ta buɗe, Rafiq ta fara gani a tsaye, sai Fawzan daga gefenshi. Wani irin numfashi ta ja tana fitar da shi da dukkan ƙarfinta, bangon wajen ta dafa saboda ƙafafuwanta da take ji suna barazanar kasa ɗaukar nauyinta. 

Sun ga saƙonta, Rafiq ya ga saƙonta kuma ya zo, sosai take jan numfashi tana fitarwa kamar wadda ta yi gudu mai nisan gaske, bata san idanuwanta sun cika da hawaye ba sai da ta ji sun zubo. Hakan yasa Rafiq da tunda ta buɗe ƙofar idanuwanshi suke kanta, daga bandejin da ke goshinta zuwa shatin yatsu na alamun mari da yake kwance a fuskarta, sannan akwai ƙananun ciwuka a fuskarta, da wani sabo a gefen leɓenta na ƙasa, zuwa wuyanta da hannuwanta inda suke buɗe da shatin duka ne na belt. Baisan me yake ji ba, saboda babu kalaman da za su misalta yanayin. 

Bai iya yin komai ba ko da yaga relief ɗin da ke fuskar Zafira har sai da ya ga hawaye sun zubo mata tukunna ya riƙo hannunta da ke jikin bangon. 

“Zafira… Zaf…”

Ya kira muryarshi can kasa, yana jin ramar da ke hannunta da ya riƙe, sassauta riƙon yayi kar ya ji mata ciwo, wani irin kuka ne ya ƙwace ma Zafira, sai yanzun take jin komai na dawo mata sabo, daga ranar da Omeed ya fara dukanta har zuwa ranar. 

“Yaya…Yaya don Allah karku barni, wallahi zai kashe ni, na kasa haƙuri…Yaya na kasa… Na daure kar in baku kunya… Na kasa… Don Allah karku barni…” 

Zafira take faɗi tana wani irin kuka kamar zata shiɗe. Riƙota Rafiq ya yi a jikinshi maganganun ta na saukar mishi cikin kunnuwa da wani irin yanayi, yana jin yadda yai failing ɗinta a matsayin Yaya, yacda bai bincika kan rayuwar aurenta bayan anyi shi ba, yadda ya ɗauka komai na tafiya dai-dai a rayuwarta. Fawzan kam tsaye yake kamar an dasa shi, balle da ya ga kukan da Zafira take yi, baisan abinda ya kamata ya yi ba. 

“Zafira…”

Shi ne abinda Rafiq ya iya faɗa, kafin ya ɗago ta daga jikinshi yana riƙe hannunta ya miƙa ma Fawzan. 

“Yana ina?”

Ya tambayeta muryarshi can kasa, kai ta girgiza mishi ta kasa magana saboda kukan da ya ci ƙarfinta. 

“Yana ina Zafira?”

Rafiq ya maimaita, tana hauka ne in tana tunanin ba zata faɗa mishi inda Omeed yake ba, saboda bai ga wanda zai iya raba su ba duk faɗin garin Lagos. Sai ya faɗa mishi dalilin daya sa ya aurar mishi ƙanwa in yasan halin dabbobi zai nuna mata, dole zai faɗa mishi dalilin da a matsayin shi na namiji zai ɗaga ma mace hannu ko da ba Zafira bace ba, akwai abubuwa da yawa da Rafiq yake jin ba zai iya ɗauka ba a rayuwar shi. Dukan mace na ɗaya daga cikin su, ko addini bai haramta hakan ba babu tunani a cikin shi. Yanayin da ke fuskar shi Zafira take kallo, kafin ta tuna cewa ko wane lokaci Omeed zai iya shigowa, wani irin dokawa zuciyarta ta ci gaba da yi. 

“Yaya mu tafi… Don Allah mu tafi.”

Ta faɗi tana kallon Rafiq ɗin, don tasan akwai matsala idan Omeed ya zo, bata son ƙara minti ɗaya a cikin gidan. Kai Rafiq yake girgiza mata. 

“Ina son ganin shi”

Ya faɗi a taƙaice, juyawa tayi ta kalli Fawzan. 

“Ya Fawzan kace mishi mu tafi… Don Allah mu bar gidan nan, wallahi in ya dawo bazai yi kyau ba… Ka ji… Mu tafi.. Don Allah ku tafi dani…” 

Ganin yadda ta firgice yasa Fawzan kallon Rafiq ya ce, 

“Yaya mu tafi kawai…”

Kai Rafiq yake girgiza musu, babu inda za shi bai ga Omeed ba, yana son jin dalili, yana son ganin da idanuwan da Omeed zai kalle shi bayan ya ci amanar da suka danƙa mishi. Ganin Rafiq ɗin baida alamar motsawa yasa Zafira rushewa da wani irin kuka, wannan karon tare yake da wani irin tsoro, basu san Omeed ba, ko kaɗan basu sanshi ba, sai dai in gawarta suke son fita da ita daga gidan ba ita ba, amma bata tunanin zai bari su ɗauke ta. 

“Zai kashe mu, Omeed zai kashe mu duka Yaya…” 

Zafira ta faɗi da wani yanayi a muryarta da yasa Rafiq kallonta. Kai ta ɗaga mishi hawaye na zubo mata. 

“Mu tafi Yaya…”

Baisan ko kukan da take bane, ko yanayin da ya gani cikin idanuwanta yasa shi ɗan ɗaga mata kai, alamar su tafi ɗin, zai kaita inda zata samu nutsuwa ya barta da Fawzan, zai dawo ya samu Omeed, saboda har lokacin ya kasa fahimtar abinda yake ji, ko meye zai fahimta bayan ya ga Omeed. 

“Hijab ɗina.. Yana kan kujera.”

Ta ce muryarta a dakushe, Rafiq da kanshi ya shiga cikin falon ya ɗauko mata Hijab ɗin, Fawzan ya taimaka mata ta saka saboda yadda jikinta yake ɓari, har suka soma takawa ta kasa yarda cewar ita ce zata bar gidan Omeed ba tare da izinin shi ba yau, waige-waige take yi, don gani take kamar zai ɓullo ko wanne lokaci, tana kuma da tabbacin su ukun babu yadda za su yi da shi. Sosai ta sake riƙe hannun Fawzan kamar zata koma cikin jikinshi ta ɓoye ma Omeed. 

Bata sake rikicewa ba saida suka zo gate, maigadi take kallo ko zai hana su fita, hakan yasa ta ƙara maƙalewa jikin Fawzan, lafiya ƙalau suka fita daga gidan, sai fatan dawowa lafiya da maigadin yai mata wanda bata amsa shi ba, tana ganin su ƙofar gidan ta ji iskar da ta shaƙa ta banbanta da ta cikin gidan Omeed, motar da ke ajiye ƙofar gidan Rafiq ya nufa, baya ya buɗe musu ita da Fawzan suka shiga, tukunna ya zagaya gaba yana shiga don driver ɗin daya kawo su yana ciki dama. 

Suna barin asibiti da Fawzan tun a Abuja yasan yana buƙatar taimakon Daddy, bai kira ba text kawai yai mishi da faɗin, 

‘Za mu je Lagos ni da Fawzan, zamu ɗauko Zafira, wani abu na faruwa a gidanta Daddy, karka hanani don bazan jika ba wannan karon. Ba amincewarka nake tambaya ba, taimakon ka nake nema.’ 

Ya kai mintina goma da tura saƙon, har yana tunanin Daddy bai gani ba, kafin ya dawo mishi da amsa ɗauke da wata lamba. 

‘Ka kira shi, ka faɗa mishi sunanka zai muku duk abinda kuke buƙata. Zan yarda da kai wannan karon, ka samu bayanin yi mun kafin in dawo.’ 

Hatta hotel ɗin da zasu kwana an kama musu kafin su iso, da direba tare da motar da za su yi zirga-zirga da ita, a ƙasa irin Najeriya idan aka ce maka abu ba zai yiwu ba ne to ba ka da farcen susa ko baka da doguwar ƙafar da zata tsallaka da kai akan ko menene. Yanzun ma direban ne ya jasu yana nufar hanyar hotel ɗin da aka kama musu. 

***** 

Suna shiga hotel ɗin, a falon Fawzan ya zaunar da Zafira ya wuce ya buɗe fridge ya ɗauko mata ruwa ya bata, karɓa ta yi ta buɗe ta shanye kusan rabi tare da maida numfashi, kallon shi ta yi yana samun waje ya zauna kusa da ita, tukunna ta kalli Rafiq da yake tsaye yana kallon ta, ɗan murmushin ƙarfin hali tai mishi dan sai yanzun ne hankalinta ya ɗan kwanta. 

“Zafira…”

Rafiq ya kira, akwai wani irin yanayi tare da murmushin da tai mishi daya sa zuciyarshi matsewa, yanayinta kawai in ka kalla tana cikin matan da suke da rauni ta fannin sanyin halayya, baisan yadda wani zai kalli Zafira yai mata faɗa ba ballantana har ya ɗaga hannun shi ya dake ta, sai yanzun yake jin wani irin ɓacin rai marar misaltuwa, jikinshi har ɗumi yake ɗauka saboda ranshi da yake baci. Gefenta ya ƙarasa ya zauna, ya maida numfashi ya fi a ƙirga kafin ya iya cewa, 

“Tun yaushe? Yaushe ya fara dukan ki Zaf?”

Muryarta cike da rauni ta ce, 

“Bazan tuna ba, satika bayan bikin mu ina jin.” 

Runtsa idanuwa Rafiq yayi yana buɗe su. 

“Me yasa baki faɗa min ba?”

Idanuwanta ta ji sun ciko da sabbin hawaye, tunanin ta faɗa ma wani bai zo mata ba, saboda tana ganin sirrinta ne, tana ganin da lokaci Omeed ɗin zai daina, kuma ba wai bata mishi laifi bane ba. 

“Ba haka kawai yake dukana ba Yaya… Ina mishi laifi…” 

“Zafira…”

Wannan karon Fawzan ne ya kira ta da wani yanayi a muryarshi. 

“Babu laifin da ya cancanci duka daga wajen miji, babu, saki ne ya halatta ba duka ba…” 

Ya ƙarasa yana jin kanshi ya fara ciwo saboda damuwa, shi yasa yake duk iya ƙoƙarin da zai yi na guje ma ɓacin rai, don matsala yake ja mishi ba ƙarama ba. Yanzun ma hankalin shi ya kwanta ne tunda sun ɗauko ta, ko menene ya zo ƙarshe, don yasan Rafiq ba zai taɓa bari ta koma ba. 

“Me yasa? Me yasa baki faɗa min ba tun farko?” 

Rafiq ya sake tambayarta, kuka ta fara yi maimakon amsar tambayar da yai mata, Fawzan ne yake lallashin ta, Rafiq kuwa miƙewa ya yi yana nufar ɗaya daga cikin ɗakunan baccin don ya yi alwala, sallolin da ya rasa sun mishi tsaye a rai, in ya gabatar da su zai fi samun nutsuwar magana da Zafira, Daddy na son bayani ne, yana da bayanai masu tarin yawa da zai mishi, ciki har da na yadda za su kwashe kayansu su bar gidan kafin su bari yaima Aroob kalar auren da yai ma Zafira. 

Yana idar da sallolinshi ya fito daga ɗakin, su Zafira na zaune inda yabar su, babu wanda ya motsa. Fawzan ya kalla. 

“Sallah Fawzan…”

Kai Fawzan ɗin ya ɗan ɗaga mishi yana mikewa, a hankali Rafiq ya ƙarasa ya samu waje ya zauna gefen Zafira, a nutse yake kallonta.

“Ya kamata wani a cikin mu ya tambaya, don baki buɗe baki kin faɗa mana akwai matsala a auren ki ba bashi zaisa mu ɗauka komai na tafiya dai-dai ba. Ki yi haƙuri ban zo da wuri ba saida kika kira ni.” 

Kai Zafira take girgiza mishi tunda ya fara magana, tasan halin Rafiq, zai ɗauki laifin rashin dai-daiton aurenta ya dora akanshi ne gaba ɗaya. Ba laifin kowa bane ba, ƙaddararta ce ta zo da haka. 

“Ni ce ban kira ka ba Yaya, ka ce kiranka kawai zanyi zaka zo. Ka yi hakuri ban kira da wuri ba.” 

Baisan abinda zai ce mata ba, komai yake ji ya tarar mishi waje ɗaya, duniyar sama-sama yake jinta, hannun shi ya miƙa mata tasa nata a ciki. 

“Ba za ki koma gidan shi ba, daga ranar da ya ɗaga miki hannu ya kamata auren ku ya ƙare, lokaci yayi yanzun.” 

Kai ta jinjina mishi tana jin kamar ya ɗauke mata wani ƙaton dutse daga ƙirjinta. 

“Ina son in yi sallah Yaya.”

“To. Nima bari in kira su Nuri.”

Ya amsa yana sakin hannunta, miƙewa ta yi daga wajen, shi kuma yana ɗaukar wayarshi da ke gefe, lambar Nuri yake lalubowa kafin ya danna kira ya kara a kunnenshi. Bugu ɗaya ta ɗaga. 

“Rafiq, ina ta jira ku kira ni, lafiya dai ko? Zafira ɗin fa?” 

Nuri take tambaya cike da damuwa. Cikin sanyin murya Rafiq ya amsa ta da faɗin, 

“Alhamdulillah, tana tare da mu. Dukanta yake Nuri, Omeed dukan ta yake yi.” 

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…”

Shine kalmar da Nuri ta faɗi tana ci gaba da maimaitawa, sai da Rafiq ya ji ta yi shiru tukunna ya cigaba da magana. 

“Baya gidan sa’adda muka je, mun ɗaukota ne kawai. Amman ina son komawa in ji dalili…” 

Zai rantse Nuri ta girgiza kanta duk da baya ganinta. 

“Babu amfanin da komawar za ta yi, ku taho gida kawai, kana Jina.” 

Kai ya ɗaga mata. 

“Rafiq…”

Nuri ta kira daga ɗayan ɓangaren tana ɗorawa da, 

“Ba laifinka ba ne…”

Numfashi ya sauke mai nauyi.

“Ki gaya wa Aroob.”

Ya faɗi muryarshi can ƙasa. 

“Ka kula da kanka…”

Nuri ta ce kafin ta kashe wayar. Saukewa ya yi daga kunnenshi yana zame jikinshi cikin kujerar, lumshe idanuwa ya yi ba tare da yasan tunanin daya kamata ya yi ba. 

Kano

Tunda ya zo asibitin yau ne karo na farko da ya fito daga ɗakin shi, ya gaji sosai da kwanciya, amma tafiyar da ya yi daga ɗakin zuwa wajen na sa numfashin shi barazanar ƙwacewa, dole ya samu cikin kujerun hutawar da ke wajen ya zauna, yana maida numfashi tare da dafe kafaɗarshi da yake jin tana raɗaɗi kamar zata faɗo. Sosai ya jingina bayanshi da kujerar yana kalle-kalle, wasu ya hango sunyi parking ɗin mota, maza biyu suka fara fitowa daga gidan bayan sai mace daga mazaunin direba, da wani namijin kuma, kulolin abinci ne a hannun su da ledoji. 

Da alama dubiya suka zo, yana kallon yanda suke dariya, da alama wani abin suke faɗi, sunyi nisa da shi ba iya juyo su zai yi ba, kafin ya ga macen ta kaima ɗaya daga ciki duka ya kauce yana dariya, akwai wani abu a tare da nishaɗin da suke yi da baisan lokacin da yake buɗe mishi wani abu a ƙirjinshi ba, su ma da haka suke cikin nishaɗi, kafin komai ya canza da rasuwar Baban su. A hankali tunani yake fisgarshi… 

***** 

Hisham ne yaro na farko cikin yara huɗu na Tafida, shi kaɗai ne kuma Allah yasa ma albarka a sana’arshi ta siyo motoci da yake daga Cotonou zuwa nan gida Najeriya, har ma da mai da shinkafa yakan shigo da su, ya fara ne ƙarƙashin wani uban gidanshi a hankali har ya samu ya zama yana harkar shi kaɗai duk da zumunci bai yanke tsakaninshi da uban gidan nashi ba. Matarshi kuma uwar ‘ya’yanshi Nusaiba tun irin soyayyar nan ta yarinta suke tare. 

Don unguwar duk babu wanda bai sansu tare ba, marainiya ce don ko sanin mahaifinta bata yi ba, aurensu yazo mishi da bazata, duk da soyayyar da suke yi, ba haka suka tsara ba, da shekaru ƙasa da sha shidda ya aureta bayan rasuwar mahaifiyarta. Allah kuma ya albarkace su da samun yara har guda biyar. Don ma sun jima Allah bai kawo rabonba. Mazansu huɗu sai autarsu mace, Amjad, Ashfaq, Yasir, Tariq sai Arfa. 

Ba zaka kira su da masu kuɗi ba, amma idan ana lissafa masu rufin asiri na unguwar ta Bachirawa za’a haɗa da Hisham a cikinsu. Ba tun daga kan ‘yan uwanshi da suke gida ɗaya ba, harta’ yan unguwa kan yaba da halayen shi, mutum ne shi da Allah bai ma rowa ba, ko yaro ya gani yana tangaririya a unguwa ba makaranta zai yi magana da iyayen ya ji dalili, yakan taimaka iya ƙarfinshi. Sosai ake ganin mutuncin shi a duka unguwar, ake kuma jinjina ma ƙoƙarin kyautatawar da yake a zamanin da ake ciki na kowa kanshi ya sani. 

*****

Wanke-wanke Nusaiba da suke kira da Mama take yi a tsakar gida, tana kuma yin karatun Qur’ani cikin qira’a mai sanyaya zuciya. Amjad yai sallama, sai da ta idar da ayar da take yi tukunna ta amsa mishi. 

“Sannu da gida.”

Ya faɗi da murmushi a fuskarshi, hannunshi riƙe da takardun makaranta, don lokacin ya samu gurbin karatu a jami’ar Bayero da take nan garin Kano, yana aji ɗaya inda yake karantar fannin magunguna da aka fi sani da Pharmacy. 

“Yawwa, kaine da sannu Amjad, sai yanzun? Allah ya sa ka ci wani abu.” 

Murmushin dai ya sake yi wa Mama, kamannin shi da Babanshi na ƙara fitowa sosai, baka raba fuskarsu da fara’a ko da yaushe, har sanyin halin na Babanshi ne. Kafin a hankali ya girgiza mata kai. 

“Allah ya shiryaka, ka wuce kitchen ka zuba abinci, akwai macaroni da miya, shi muka ci da rana, yanzun kuma tuwo na yi miyar Kuɓewa ɗanya.” 

“Tuwon dai Mama…”

Wannan karon ita ta yi murmushin, dama Tariq ta ajiye ma Macaronin don ba shiri yake da tuwo ba, ko me za’a zuba a ciki kuwa, wani lokacin sai ta yi fada sosai ya ga ranta ya ɓaci tukunna zai dinga ci fuska babu walwala. Sai da Amjad ya wuce ɗaki ya ajiye takardunshi tukunna ya nufi kitchen ya zubo tuwon, kujera ya janyo ya zauna daga nesa da Mama ya soma ci. 

“Kinsan Allah ko Mama? Rabon da ki yi tuwo mai daɗin wannan tun lokacin da na yi ciwon cikin nan…” 

Dariya Mama ta yi, ta buɗe baki za ta amsa shi sallamar da Ashfaq yayi ta katse ta, jikinshi da uniform ɗin Islamiya ruwan ƙasa masu haske, murmushin daya kwace ma Mama wannan karon daban ne, ba don bata jin sauran yaranta ba, ba kuma don Ashfaq ɗin yana kama da ita kamar an tsaga kara ba, sai don akwai shaƙuwa mai ƙarfin gaske a tsakaninsu fiye da sauran yaran nata. Bata gama amsa Sallamar ba ya watsa ma Amjad wani irin kallo. 

“Yaya kana zaune take wanke-wanke.”

Cewar Ashfaq yana ƙarasawa ya raba litattafanshi a jikin bango ya tsugunna yana jan robar wanke-wanken gabanshi 

“Yanzun fa na dawo daga makaranta.”

Amjad ya faɗi. 

“Ko yanzun ka dawo.”

“Baka ga ina cin abinci ba ne?”

Juyawa Ashfaq yayi ya kalle shi. 

“Abincin zai iya jira. Ba kai niyya ba ne ba.”

Yanayin muryar Ashfaq ɗin yasa Amjad ya ji kunya ta kamashi. 

“Lallai yaron nan, faɗa za kai min? Kamar ban girmeka ba.” 

Ashfaq bai kula shi ba, dariya Mama take musu. 

“Ka barshi na kusan gamawa.”

Ta ce wa Ashfaq ɗin da ya girgiza mata kai, dama tasan ba tashi zai yi ba, ko bata bar mishi ya wanke duka ba tare za su yi, in yana nan duk wani aiki tare suke yi. Yanzun ɗin ma sai da suka gama tas, shi ya kwashe kwanonin, Mama kuma ta wanke wajen tukunna ya wuce ɗaki ya sake uniform, fitowa ya yi da su a hannu yana ɗauko bokiti. 

“Me za ka yi?”

Amjad da har lokacin bai ƙarasa cin abincin ba ya buƙata. 

“Wanki.”

Ashfaq ya amsa shi a taƙaice, baya son yawan tambaya, bai cika son surutu marar dalili ba kuma. 

“Ko karin gugar babu abinda yayi ballantana su yi datti.” 

Amjad ya faɗi, ko mace ba zata nuna ma Ashfaq tsafta ba, ko kaɗan baya son ganin datti, hakan yaita haɗa su faɗa, dole aka ware mishi ɗakinshi shi kaɗai. Ba mai zuwa sai ta kama, kafin ya balbale mutum da faɗanshi da baya ƙarewa. Lokuta da yawa Amjad kan ji kamar Ashfaq ɗin ne babba, in gaskiya ta kama baya shakkar ya faɗa mishi ita ko da ranshi zai ɓaci kuwa. Dama yasan da wahala ya samu amsar tambayar da ya yi, don haka ya miƙe da kwanon da ya gama cin abinci zuwa kitchen. Yana fitowa Yasir da Tariq na yin sallamar da basu jira amsar ta ba suka ci gaba da hirarsu. 

“Na faɗa maka dama ai, nifa na fi son Malam Haris, Allah wannan kafin ya kai Aya ɗaya numfashi na ya fara sama-sama.” 

Yasir ya faɗi, dariya Tariq yake sosai. 

“Ni kuma ina son mutumin, karatun shi na min yanayi da na Sheikh AbdulBasit…” 

Wani irin kallo Yasir ɗin yai wa Tariq 

“Ka taɓa ganin ina jin AbdulBasit? Karatun shi ya min slow…” 

Ɗagowa Ashfaq ya yi don ya shanya rigar shi kamar an ce ya sauke idanuwanshi kan Yasir, ya ga rigarshi a jikin Yasir ɗin. 

“Yasir rigata ce a jikinka ko? Me yasa ka raina ni? Ko don kana ganin girmanmu ɗaya?” 

Dariya Yasir ya yi. 

“Haba Babban Yaya..”

Tsaki kawai Ashfaq ya ja, don yana ganin girman Yasir ɗin ne shi yasa yai shiru, kuma shi kanshi yasan ba iya mishi faɗa yake ba, kusan shi kaɗai yake taɓa mishi kaya a zauna lafiya, ƙarasa shanya kayan Ashfaq ya yi yana ɗauke bokitin daga wajen. Su kuma Tariq da Yasir suka wuce cikin gidan, Amjad Ashfaq ya kalla da ke tsaye har lokacin. 

“Menene?”

Ashfaq ya buƙata. 

“Math ɗina za ka duba min.”

Amjad ya amsa yana kallon Ashfaq ɗin. 

“Waye ya ce na iya?”

“Ban ce ka iya ba nima, duba min kawai za ka yi.” 

Kai Ashfaq ya ɗaga, kusan kowa a gidan ya kwaso math ɗinshi sai ya nufo shi dashi, yanzun ne zai shiga aji shida, mutane da yawa kan ce lissafi na musu wahala, amma bai taɓa ganin wahalar hakan ba, asalima duk wata gasa da ta danganci lissafi da za’a yi a makarantar su da shi ake zuwa, kuma basu taɓa rashin nasara ba. Hakan yasa suke shiri da malamin lissafinsu, don yanzun haka ya bashi kyautukan litattafai da suka girmi ajin da yake, sukan yi tare kuma. 

Falo suka nufa, nan suka baje suna yin assignment ɗin da misalin da akai ma su Amjad a aji kawai ya nuna ma Ashfaq ɗin ya gane yadda zai ɓullo wa abin. Mama na zaune tana kallon su da Arfa kwance a jikinta, har aka kira sallar Magrib, kafin su tashi sallamar Babansu ta cika falon, su dukansu suka miƙe da farin cikin ganin su. 

“Dama Baba na hanya?”

Sannu da zuwa sukai mishi suna karɓar kayan da ke hannun shi, tare suka fita masallaci su ukun, a hanya ne Baba yake ce ma Amjad, 

“Ya karatun kuwa?”

“Alhamdulillah Baba, lissafi ne kawai yake bani matsala.” 

Murmushi Baba ya yi. 

“Kai da kake da Ashfaq, ya lissafi yake maka haka?” 

‘Yar dariya Amjad ya yi. 

“Kamar ya ara min kanshi in dinga tafiya da shi ajin lissafin haka nake ji wallahi.” 

Wannan karon Baba ne yai dariya, dai-dai gittawar wani mai mashin ta kusa da Amjad, duk da a gefen hanya suke, sai da ya taɓa mishi kafaɗa da yanayin tuƙin gangancin da yake yi, ba don Ashfaq da ya janye shi ba, sosai da ya ji mishi ciwo, a fusace Ashfaq yake faɗin, 

“Wanne irin rashin hankali ne wannan? Kuma fa ko juyowa bai yi ba, daya ji maka ciwo fa? Sannu…” 

Murmushi Amjad yake yi, musamman da Ashfaq ɗin ya kamo hannunshi yan dubawa don ya tabbatar bai ji ciwo ba. 

“Ashe kana sona haka baka nuna min?”

Amjad ya faɗi yana saka Ashfaq ɗin sakin hannunshi tare da watsa mishi hararar da ta saka shi yin murmushi da dukkan haƙoranshi. Ɗan ture shi Ashfaq ya yi, yanayin ƙaunar dake tsakanin su na sa zuciyar Baba cika da alfahari. 

***** 

“Faq!”

Yasir ya kira a karo na babu adadi, yana haɗawa da taɓa kafaɗarshi tukunna ya ɗago. 

“Tunanin me kakeyi haka?”

Yasir ɗin ya tambaya yana zama kan kujera gefen Ashfaq. Kafaɗa Ashfaq ya ɗan ɗaga mishi, abinda yai saura daga zuciyarshi na yin nauyin gaske, rabon da ya bari tunanin shi yai yawo haka har ya manta. 

“Da ba haka rayuwar mu take ba Yasir…”

Ashfaq yai maganar can ƙasan maƙoshi, cak Yasir ɗin yake zaune, ko numfashi a hankali yake fitarwa, yana tsoron yin shi da ƙarfi kar Ashfaq ɗin yai shiru don ba ko da yaushe yake magana kan rayuwarshi ba, yau na ɗaya daga cikin ranaku ƙalilan da Yasir yake tunanin zai ƙara sanin wani abu akan rayuwar Ashfaq ɗin ta baya, ba zai yi ruining ɗin lokacin ba. 

“Ba masu kuɗi bane mu, amma akwai nutsuwa a tattare da rayuwar mu, babu ƙunci, babu duhu a cikinta, kafin alƙalamin ƙaddara ya canza mana komai…” 

Ashfaq yake faɗi da wani nisantaccen yanayi a muryarshi don ji yake kamar rayuwarshi ta baya da ta yanzun banbancin shekaru dubu ne a tsakanin su saboda nisan da yake jin sun mishi, kafin ya ci gaba da magana, 

“Ina neman inda haske yake ko yaya ne, bana ganin komai a cikin kaina sai duhu… Yadda komai zai canza a ƙaramin lokaci na ban mamaki…” 

Numfashin da Yasir yake fitarwa a hankali ne kawai zai faɗa maka yana wajen a zaune. Hannuwa Ashfaq yasa yana dafe kanshi tare da mayar da numfashi, sosai yake kokawa da kanshi, yana mayar da ƙofar da ta buɗe mishi tunanin rayuwarshi ta baya ya rufe gam tukunna ya buɗe fuskarshi yana kallon Yasir ɗin. 

“Za ka ci wani abun ne?”

Yasir ya buƙata, don a idanuwan Ashfaq ɗin ya fahimci ba zai sake wata maganar da ta danganci rayuwarshi ta baya ba, sai kuma wani lokacin, kai Ashfaq ya ɗan jinjina, halayyar rashin son jin ƙwaf da bin diddigin da Yasir baya mishi ne yasa yake da kusanci da rayuwar shi har haka. 

“Lemon zaƙi za ka siyo min da balangu, sai coke.” 

Kai Yasir ya daga

“Bari in siyo in dawo to…”

Hannu Ashfaq ɗin ya miƙa mishi yana kamawa ya taimaka mishi ya miƙe. 

“Nima bari in koma ɗaki kawai… In ka zo ina can.” 

“Okay.”

Cewar Yasir yana wuce wa, shima Ashfaq ɗin ɗaki ya koma abinshi.

<< Alkalamin Kaddara 31 Alkalamin Kaddara 33 >>

2 thoughts on “Alkalamin Kaddara 32  ”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×