Kinkiba
Har ya kunna mota da niyyar juyawa ya hango su, baisan hannun shi ya kai kan murfin motar har ya buɗe ba sai da ya ji iska ta dakar mishi fuska, gaba ɗaya zuciyarshi neman fitowa take daga ƙirjinshi ta ƙarasa wajen shi, jikinshi ko ina ɓari yake, so yake ya ƙarasa inda suke, musamman da ya ga wadda ta fito da su ɗin sun miƙe hanya.
"Yara na..."
Ya furta zancen da yake a zuciya, bai taɓa sanin kusanci irin wannan ba tunda yake a rayuwar shi, da duk wani abu da yake. . .