Baisan lokacin da ya ɗauka suna zaune cikin motar ba, ko da ya ji ta tashi motar sun fara tafiya bai buɗe idanuwan shi ba, ko motsi bai yi ba, sai da ya ji ta kashe motar tukunna ya buɗe idanuwan shi, ganin ta yayi ta haɗe kanta da abin tuƙin motar, kuka take sosai. Bai ce mata komai ba, kallon ta kawai yake yi yana jin kamar su yi musayar matsayi, ƙila idan yai kukan, hawayen shi suka zuba ya ji sauƙin abinda yake ji a cikin kanshi. Za su kai mintina goma zaune a cikin motar. Kafin a hankali ta ɗago tana saka hannunta ta goge fuskarta da harta kumbura saboda kukan da ta yi.
“Mu je?”
Rafiq ya buƙata, don babu inda zai barta, kai ta ɗaga mishi yana kallon hawayen ta na sake zuba. Murfin motar ya buɗe ya fita, ya zagaya yana buɗe mata. A gaba ya tusa ta har suka shiga falon gidan su.
“Daddy! Daddy!! Daddy!!!”
Rafiq yake kira yana ɗaga kanshi ko zai hango fitowar Daddy ɗin, bai kira Nuri ba saboda in hauka yake ba zata faɗa mishi ba, amma yasan Daddy ba faɗa mishi kawai zai yi ba, har asibitin mahaukata zai kaishi don nemar mishi magani. Shi yasa yake ƙwala mishi kira, yana so ya tabbatar daga bakin shi ne. Sai dai me, su dukan su ya hango suna fitowa daga ɓangaren su tare da tako matattakalar benen suna saukowa.
“Rafiq…. Lafiya? Me yake faruwa?”
Nuri ta faɗi tana kallon Rafiq ɗin bayan sun sauko cikin falon, kai ya girgiza mata, yana ƙarasawa ya kamo hannun Daddy ya kawo shi kusa da matar.
“Daddy kana ganin ta?”
Rafiq ya tambaya, yana so ya fara ji ko shi kaɗai yake ganin ta tukunna. Sai lokacin Daddy ma ya lura da ita, fuskarta yake kallo yana jin wani abu na kwancewa a zuciyar shi, kafin ya fisge hannun shi daga na Rafiq din yana matsawa baya cikin tashin hankali ya ce,
“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…”
Kamar wanda ya ga fatalwa, ƙafafuwan shi yake jin sun mishi sanyi gaba ɗayan su, kamar mai shirin faɗuwa yake matsawa daga kusa da ita, tunda Rafiq yake bai taɓa ganin Daddy ya rikice haka ba. Wajen Nuri ya ƙarasa yana ɓoyewa a bayanta da faɗin,
“Hafsatu ki fitar da ita daga gidan nan, me take yi?”
Hannun shi Nuri ta kamo tana girgiza kai, ita ma ta kasa yarda da matar da take gani a gabanta, Daddy take so ya tabbatar mata da cewar mafarki take, ya faɗa mata ba tashin hankalin da suka guje ma Kano saboda shi bane ya biyo su har Abuja duk tsawon shekarun nan, ba yanzun ba, ba zai yiwu ba ne ba, ba zata iya bari wani abu ya sake samun Rafiq ɗin ba. Zuciyar ta ba zata iya ɗaukar ya sake shiga cikin wani yanayi ba. Daddy ta saki tana rugawa ta riƙo hannun Rafiq ɗin tana ƙoƙarin jan shi. Kallon su yake da wani irin ruɗani shimfiɗe a fuskar shi, saboda bai taɓa ganin su a rikice irin yadda yake ganin su yanzun ba.
“Nuri… Me yake faruwa? Yayaa…”
Juyawa Rafiq yayi ya ga Aroob a tsaye da Fawzan na rufo mata baya. Don gidan ne baya musu daɗi su dukkan su, shi yasa ma sukai zaman su a falon sama suna kallo suka ji kamar muryar Rafiq ɗin, Aroob ta taso ta leƙo daga saman benen ta gansu shi ne ta tabbatar ma da Fawzan ɗin, kafin su dukan su suka sauko ƙasan don ganin me ke faruwa. Zafira kuwa bacci take yi.
“Nima ban sani ba, abinda nake so su Nuri su faɗa min kenan.”
Rafiq ya faɗi yana kallon fuskar Nuri da har lokacin bata daina ƙoƙarin jan shi ba, yayi tsaye ne kawai yana kallon ta, don babu inda za shi in ma haukan yake sai sun tabbatar mishi tukunna.
“Babu abinda yake faruwa, Fawzan ku koma ciki, Rafiq mu je kaima…”
Nuri take faɗi muryarta na rawa, Daddy ta kalla daya taimaka mata, cikin shi da ke yamutsawa ya dafe yana samun waje a ƙasa kan kafet ya zauna yana wani irin mayar da numfashi da yasa Fawzan da Aroob suka ruga wajen shi.
“Daddy!”
Suka faɗi a tare, hannun shi Fawzan ya riƙo yana ƙoƙarin duba shi, idanuwan Aroob cike da hawaye take faɗin,
“Wai me yake faruwa da mu haka ne? Me yasa ba zamu ɗan huta ko kaɗan ba ne ba…”
Ta ƙarasa maganar hawayen na zubo mata, juyawa ta yi tana kallon matar da ke tsaye tana wani irin kuka, matar da ta fahimci tana da alaƙa da koma menene ya rikita su Daddy haka, miƙewa ta yi tana ƙarasawa inda matar take tsaye tana haɗe hannayenta duk biyun da alamar roƙo.
“Don Allah ki tafi, koma menene ki tafi kawai…bama buƙatar wani sabon abu… Ban san ko kin buɗe bakin ki ba, amma ki kalle su, don Allah ki tafi.”
Aroob ta ce tana tsare matar da idanuwan ta, kai Rafiq yake girgiza ma Aroob.
“Ki barta, Aroob ki barta fa, tunda ba ni kaɗai nake ganin ta ba, akwai abinda yake faruwa…”
Hannun shi ya ƙwace daga riƙon da Nuri tai mishi yana ƙarasawa wajen su Aroob, hannun matar ya kama yana janyo ta har tsakiyar falon.
“Yayaaa….”
Aroob ta kira don bata taɓa ganin shi cikin yanayi irin na yau ba, ko kulata bai yi ba, Nuri yake kallo bayan ya saki matar .
“Ba za ki ɓoye min wannan ba Nuri, ki faɗa min ko menene yake faruwa….ina jin na san matar nan duk tsawon rayuwa ta, ba sai kun faɗa min ba, na ga kuma kun gane ta, wacece? A ina na santa?”
Kai Nuri take girgiza mishi, tana jin numfashin ta na mata barazana, tsugunnawa ta yi daga tsayuwar, wasu hawaye masu ɗumin gaske na zubo mata, kai take girgizawa tare da kai hannu tana dafe goshin ta saboda jirin da take ji yana ɗibar ta, sake komawa ta yi ta tsugunna, kafin ta zauna kan kafet ɗin gaba ɗayan ta, Daddy da Fawzan yake famanl yi ma sannu take kallo cikin tashin hankali don bata san me ya kamata ta yi ba, shi ma kallon da yake mata cike yake da ruɗani. Hakan yasa ta rarrafawa inda yake don bata jin zata iya miƙewa. Bata damu da su Rafiq da suke tsaye ba, kanta ta ɗora jikin ƙafafuwan Daddy tana sakin wani irin kuka.
Hannun shi Daddy ya ɗora kan bayan ta, yana ɗago kai ya kalli Rafiq da yake kallon su yana jiran wani a cikin su ya soma magana, ɗauke idanuwanshi Daddy yayi daga kan Rafiq yana mayarwa kan matar da itama kukan takeyi
“Ba zan rasa yarona ba, kina jina, ɗana ne wallahi, ɗan mu ne, ba zamu rasa shi ba kuma…”
Cikin rashin fahimtar maganganun Daddy su dukan su ukun suke kallon shi.
“Wane irin magana kake yi Daddy?”
Fawzan ya tambaya, Daddy bai kula shi ba, matar yake kallo.
“Shekara talatin da huɗu, wallahi bazai yiwu ba kin ji na rantse…”
Ya faɗi muryarshi a dakushe, yana jin wani abu ya mishi tsaye a ƙirji ya tokare mishi zuciya yasa iska bata kai mishi inda ya kamata. Hannu ya miƙa ma Rafiq, kallon hannun Rafiq yake yi, hakan yasa Daddy faɗin,
“Please… Rafiq…”
Roƙon da Daddy yayi da yanayin muryar shi yasa Rafiq ɗin saka hannun shi cikin na Daddy ɗin da yake ji yana kyarma. Numfashi mai nauyin gaske Daddy ya sauke yana runtsa idanuwan shi ko zai samu nutsuwa, ba zai iya rasa ɗanshi ba, yasan yana ƙaunar yaran shi gaba ɗaya, rayuwa bata taɓa gwada shi ta fannin da zai yi kokwanto akan hakan ba, yanzun ya sake sanin girman son da yake ma Rafiq da tunanin zai iya rasa shi, ko sa’adda ya samu hatsari bai shiga yanayi irin na yanzun ba.
“Ɗana ne kai Rafiq…babu abinda zai canza hakan, kana jina? Ɗana ne kai! Kar wanda ya faɗa maka wani abu akasin hakan ka yarda.”
Cikin tashin hankali Fawzan ya ce,
“Daddy wai me yake faruwa ne haka? Waye zai ce ba ɗanka ba ne ba? Wani ya ce ba ɗanka ba ne ba?”
Ko kallon shi Daddy baiyi ba, hankalin shi kacokan yana kan Rafiq ɗin yana so ya ga ya tabbatar mishi da cewar ko me wani zai faɗa bazai canza cewar shi ɗin ɗanshi bane ba. Amma nisantaccen yanayin da yake gani cikin idanuwan Rafiq ɗin na tsorata shi, kafin a hankali Rafiq ya zare hannun shi daga cikin na Daddy duk yadda yake ƙoƙarin ganin hakan bai faru ba.
“Rafiq…”
Daddy ya kira a tsorace, kai Rafiq ya girgiza ma Daddy, zuciyarshi ta yi luf cikin ƙirjin shi, ji yake kamar an tsoma shi cikin ruwan ƙanƙara, don baya jin jini na kai kawo a jikin shi.
“Me yake faruwa, ina son sani.”
Ya furta muryar shi na fitowa da wani yanayi da yasa shi daƙuna fuska. Kallo ɗaya Aroob taima Daddy ta san kome zai fito daga bakin shi ba abu bane da su dukan su suke son ji, da sauri ta riga shi magana da faɗin,
“Don Allah Daddy, karka ce komai, kar ka yi magana.”
Numfashi Daddy yake ja yana fitarwa da sauri sauri.
“Ku yi haƙuri, don Allah ku yi haƙuri…”
Ya ƙarasa a karo na farko tunda ya mallaki hankalin shi da ya ji hawaye sun cika mishi idanuwa. Hakan yasa Fawzan faɗin.
“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…”
Zuwa yanzun ita kanta matar ta tsugunna saboda kukan da ya ci ƙarfinta, Nuri ce ta ɗago daga jikin Daddy fuskarta ta yi ja saboda kukan da ta yi, Daddyn ta dafa tana miƙewa, inda Rafiq yake zaune ta ƙaraso tana saka hannuwan ta duk biyun ta tallabi fuskar shi, sai lokacin ya sauke wani numfashi da baisan yana riƙe da shi ba, kanshi ya tsugunno yana haɗa goshin shi da na Nuri, kafin ya ɗora hannuwanshi kan nata da ke riƙe da fuskarshi, idanuwan shi ya lumshe yana neman comfort ɗin da yasan Nuri ce kaɗai zata iya bashi.
Raɗaɗi yake ji a ko ina na jikin shi, har wajajen da bai taɓa sanin za su iya mishi ciwo ba ma yau ciwo suke mishi. A yadda yake ɗin ya ce,
“Nuri ki faɗa min, idan ban sani ba ba za mu taɓa wuce wannan yanayin ba, na gaji sosai, don Allah, wallahi na gaji sosai… Ki faɗa min kawai…matata da yarinya ta sun rasu, ko tuna su na kasa yi, bana jin akwai abinda zai kai haka muni…”
Yana jin ta sake matsa hannuwanta a jikin fuskarshi, idanuwanta a rufe suke gam yana kallo, amma hakan bai hana hawayen ta zuba ba.
“Nuri…”
Ya kira a hankali, muryar shi can ƙasa, don saida yai zaton bata ji ya kirata ba kafin ta bude idanuwan ta cikin nashi yana kallon yadda zuciyarta take a karye ta cikin su da yanayin da yai mishi tsaye a tashi zuciyar.
“Ɗana ne kai Rafiq…ko me ya faru ɗana ne kai…”
Baisan me ya same su ita da Daddy da maimaita mishi kalaman nan yau ba, ko da yana buƙatar tabbaci daga wajen Daddy duk in sun yi faɗa, bai taɓa buƙata daga wajen Nuri ba, ƙaunarta kawai ta ishe shi tabbaci a kullum, ko waya a rana za su iya yin sama da goma, ko da yana gari kuwa, ko yana Kano ne ma, da shida ta yi sai ta kira shi ta ji me yake bai koma gida har lokacin ba, Nuri daban take a rayuwarshi, wajen ta da ƙaunarta daban suke da na kowa.
“Me yasa kike maimata min abinda na riga na sani Nuri? Kawai na tambayi me ya faru ne.”
Wasu hawayen ya sake gani sun zubo mata. Muryarta na rawa ta ce,
“Ina so ka riƙe su ne sosai Rafiq, yarona ne kai, ko me zai faru ɗana ne kai, kana jina? Ɗana… Ɗana ne kai.”
Ya ga alama ba tana tabbatar mishi ba ne, tana so ita ya tabbatar mata cewar ɗanta ne shi, hakan yasa shi ɗan ɗaga mata kai, saboda har lokacin goshin shi na haɗe da nata, bata kuma saki fuskarshi daga cikin hannuwanta ba. A hakan ta sauke wani irin numfashi tana lumshe idanuwan ta da faɗin,
“Yaa Allah…Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…”
Zuciyarta ke wani irin raɗaɗi, bata taɓa ɗauka yau zata same ta tana numfashi ba, shi yasa bata shirya mata ba.
“Rafiq ɗana ne kai…”
Ta sake maimaitawa, sauran kalaman da take son faɗi na maƙale mata, amma tana so ya fara jinsu daga bakinta ne, kafin ya ji daga na kowa.
“Ki bari in faɗa mishi Hafsatu, ki bari…”
Daddy da ke zaune ya faɗi cikin wani irin sanyin murya, kai ta girgiza tana riƙe fuskar Rafiq ɗin tana jin kamar ta mayar da shi cikin jikin ta ta ɓoye shi daga duk wani abu da zai same shi. Amma hakan ba zai yiwu ba.
“Hafsatu…”
Daddy ya sake kiranta, ta manta rabon da ta ji asalin sunan ta a bakin shi haka, a muryarshi yake faɗa mata gab yake da faɗa ma Rafiq don ya samar mata sauƙin abinda take ji, hakan yasa ta jan numfashi mai nauyin gaske kafin ta buɗe idanuwanta, zuciyarta take ji a bushe.
“Ɗana ne kai Rafiq…wallahi ban taɓa buƙatar haɗa jini da kai kafin in ji hakan ba…ɗana ne kai duk da baka fito daga cikina ba…”
Nuri take ƙarasawa tana wani irin kuka, a hankali kamar wanda ake zarewa kuzari Rafiq yake janye fuskarshi daga jikin ta Nuri, yana matsawa baya, yana raba gaba ɗaya jikin shi daga nata, maganganun ta na saukar mishi kamar hadarin gini, suna samun wajen zama a wajajen da suka rushe mishi abubuwan da baisan menene ba.
‘Ɗana ne kai duk da baka fito daga cikina ba.’
Maganganun da ke mishi yawo kenan, yana so su ƙarasa ɓangaren ƙwaƙwalwar shi da zata fahimtar da shi su. Amma hakan ya gagara, amsa mishi maganganun kawai suke ya daina jin duk wani sauti banda su.
“Nuri?”
Fawzan ya kira da wani irin tashin hankali, Aroob kuwa tunda Nuri ta buɗe bakinta take jin ƙafafuwanta na mata kyarma, kujerar da ke kusa da ita ta dafa tana buɗe bakin ta saboda iska ta daina shiga ko wucewa ta hancin ta, wani irin numfashi take ja amma iska ta ƙi wuce mata, ba Nuri ta haifi Rafiq ba, ba Nuri ta haifi Rafiq ba, shi ne abinda ke mata yawo a duk wata gaɓa ta jikin ta, duk da zuciyarta na gaya mata hakan bai canza komai na alaƙar su ba, amma bai hana jin duniyar na wulwula mata da yanayin da hakan zai ma Rafiq ba.
Duk tsawon shekarun nan me yasa basu faɗa mishi ya sani ya huta ba, sai yanzun, me yasa sai yanzun da yake fama da ɓacewar wani ɓangare na tunanin shi, in ba so suke su kashe shi ba, bata ga dalilin da yasa Nuri zata faɗa mishi ba ita ta haife shi ba yanzun. Tunanin da take yi shi Fawzan yake yi, banbancin shi ne kawai shi abin na mishi wahalar yarda, saboda ko da wasa bai taɓa ganin ko alamar da ke nuna cewar ba Nuri ta haifi Rafiq ba, ko a dangi bai taɓa ganin hakan ba, ya kuma san waye dangin shi na ɓangaren Daddy, in sun sani bakin su ba zai taɓa yin shiru ba.
Alamar da ke nuna cewar basu sani ba, idan basu sani ba ya za ayi hakan ya yiwuwa, Daddy bai da wata matar da suka sani bayan Nuri, kuma sun san ita kaɗai ce matar shi. Labarin da Fawzan ɗin kawai ya sani shi ne na cewar dangin Daddy sun so ya ƙara aure amma hakan bai faru ba, to taya zata ce ba daga cikin ta Rafiq ya fito ba, daga ina ya fito to, me yasa ba ma za su ƙyale Rafiq ɗin ya ji da ruɗanin da ke rayuwar shi ba, so suke su ga ya faɗi ne ko me.
“Nuri me kike cewa haka?”
Fawzan ɗin ya sake tambayar ta, kuka take sosai, tana kallon yadda ba Rafiq kaɗai kalamanta suka tarwatsa ba, har da su Fawzan ɗin. Aroob ta kalla da ke kokawa da numfashin ta, hakan na ƙara ma Nuri ciwon da zuciyarta take yi, bata ga abinda take jira ba, gara ta faɗi musu gaba ɗaya kawai, tana wani irin kuka mai cin rai ta ce,
“Ba mu muka haifeka ba….Rafiq ba daga jikin mu ka fito ba daga ni har Daddyn ku…”
Rafiq baisan yana shirin faɗuwa ba, sai da ya ji Fawzan ya riƙo shi tukunna, kafin wani irin duhu ya mamaye shi komai na mishi ɗif. Aroob ma da gudu ta ƙaraso tana taya Fawzan ɗin kama shi, numfashin ta baya fita yadda ya kamata, tasan kuma asthma ɗinta ne ya tashi, ga kukan da take baya taimaka ma hakan. Nuri take kallo.
“Ki kashe shi Nuri… In ya mutu sai ki huta gaba ɗaya…”
Take faɗi tana wani irin kuka, musamman da taga Fawzan ya kwantar da Rafiq ɗin da baisan duniyar da yake ba.
“Kin gani ko Nuri? Kin gani ko? Wallahi bazan yafe miki ba idan ya mutu… Yaya Fawzan…”
Cewar Aroob, girgiza Rafiq ɗin Fawzan yake yi cikin tashin hankali.
“Yayaa… Yayaa don Allah… Ka ji Yayaa…. Mu bamu damu da abinda Nuri ta ce ba wallahi… Don Allah karka yi haka…”
Numfashi Nuri ta sauke tana wucewa da ƙyar ta ɗauko ruwa, Fawzan ta dafa tana miƙa mishi, hannun ta ya ture yana girgiza mata kai, wasu irin hawaye masu ɗumi na zubo mishi, baya son taimakon ta, Rafiq yake so ya tashi, Aroob ya kalla da ta kwantar da kanta jikin Rafiq din tana kokawa da numfashin ta.
“Aroob…”
Girgiza mishi kai take yi, in so yake ya ce ta tashi ta ɗauko inhaler ɗinta sai dai asthma ɗin tai ajalin ta yau, don babu inda zata je, ba zata bar Rafiq ba.
“Ki karɓa Aroob.”
Fawzan ya faɗi yana goge hawayen shi, wasu na fitowa, inhaler ɗin da ke jikin shi ya miƙa mata, karɓa ta yi da sauri, gyara ma Rafiq da yai luf kamar bashi da rai kwanciya yayi. Fawzan baisan me yake faruwa da su ba, abu ɗaya ya sani in Rafiq ya tafi binshi zai yi, baya jin zai iya zama kuma. Hannun shi yasa a aljihu yana zaro wayar shi, bai ma san me yake ba, yana buƙatar yin magana da wani da yake wajen gidan, don ya ga alama su dukkan su da suke cikin shi sun samu matsala. Naadir yake kira, har sai da ta yanke bai ɗaga ba, sake kira yayi yana faɗin,
“Ka ɗauka Naadir….don Allah ka ɗaga wayar….”
Ɗagawar kuwa yayi, Fawzan na saka ta a speaker da faɗin,
“Ina ka je Naadir?”
“Wanka nake yi.”
Jinjina kai Fawzan yayi.
“Naadir ka ji Nuri ba, wai ba ita da Daddy suka haifi Yaya ba.”
“Fuska ta na wanke…da kumfa a jikina Yaa Fawzan, in wannan wasan ka kirani ina da abubuwa masu muhimman ci a gabana…”
Naadir ya faɗi cikin harshen turanci, kai Fawzan ya girgiza kamar Naadir na ganin shi.
“Ba wasa ba ne ba, haka suka ce…”
“Ƙarya ne.”
Naadir ya faɗi, hakan Fawzan yake son ji, wani yake son ya ƙaryata mishi dama.
“Na gode… Na gode Naadir.”
Wayar zai kashe Naadir ya ce,
“Ka bama Yaya wayar…”
“Baya numfashi…”
Fawzan ya amsa shi, yana jin shi kamar wanda aka saka ma battery, wani irin sama-sama yake jin shi.
“Zan taho jirgi na gaba dazan samu. Ka faɗa mishi idan ya tashi.”
“Yaya zai kashe mu in ka taho…”
Aroob ce tai maganar wannan karon, har lokacin numfashin ta na fita da shiga a wahalce .
“Bai dame ni ba.”
Cewar Naadir yana kashe wayar kafin Fawzan ɗin ya ce wani abu, aljihun shi ya mayar da wayar, yana juyawa ya karɓi ruwan da Nuri take riƙe da shi har lokacin bai damu da kukan da take yi ba, buɗewa yayi ya zuba a hannun shi, saida ya shafa ma Rafiq sau huɗu tukunna ya ja wani irin numfashi yana tashi a firgice, miƙewa Fawzan yayi yana kama shi, bai yi musu ba ya miƙe, ɗayan hannun shi Fawzan ya miƙa ma Aroob yana taimaka mata ta miƙe ita ma, jan su ya yi suna barin ɗakin gaba ɗayan su, baisan me yake damun Nuri ba yau, amma ba zai bari ta kashe mishi ‘yan uwa saboda hakan ba.
Daddy da ke dafe da kanshi Nuri ta kalla yanayin shi na janta zuwa shekaru talatin da biyar da suka wuce.
*****
Fitowa ta yi daga ɗakin baccin su tana samun shi zaune a falo yana duba jarida, hawaye masu ɗumin gaske suka zubo mata. Zagaye kujerar ta yi tana karɓar jaridar da ke hannun shi ta watsa ta gefe.
“Me yasa za kai musu ƙarya? Halin da nake ciki da danginka bai isheka ba ko? Almustafa me yasa zakai musu ƙaryar ina da ciki, Dada ce ta kirani yanzun tana min murna…”
Numfashi ya sauke yana kallon ta, murmushi yayi a gajiye, ta mishi wani irin kyau na ban mamaki, ba ko yaushe yake ganin ɓacin ranta ba, duk da yasan a shekaru uku da auren shi da yadda danginshi suka sako ita da shi a gaba akan batun haihuwa ba abu ba ne me sauƙi, sai dai ita da shi duk sun san ƙarin aure ba abu ba ne da zai yiwu a wajen shi. Hannu ta sa tana goge hawayen ta, hakan bai hana wasu fitowa ba.
“Ka ƙara aure mu dukkanmu mu huta ka ƙi, ya kake so in yi? Ya kake so in yi da ƙaryar nan da kai musu? Ina zan samo yaro yanzun?”
Hannun ta ya kamo duk da ƙoƙarin fisgewar da take, sosai ya rike ta yana sa karfi ya ja ta ya zaunar kan kujerar.
“Kin san banda ra’ayin mata biyu…kin isheni ke kaɗai, haihuwa lokaci ne, ko Allah bai bamu ba banda ra’ayin mata biyu, bansan sau nawa zan faɗa miki hakan ba.”
Yanzun kam kukan ta mai sauti ne, tana son shi, fiye da yafda dangin shi zasu taɓa fahimta, tunanin zata raba soyayyarshi da wata na neman saka mata ciwon zuciya. Amma gara ya ƙara aure indai hakan zai sa dangin shi su ƙyale ta ta zauna lafiya da shi. Tun kafin ya aureta ya faɗa mata burin shi na riƙe wani babban muƙami a Najeriya. Target ɗinshi gaba ɗaya akan siyasa ne, ya faɗa mata ba zai iya rikicin mata biyu ba, baya buƙatar wannan rabuwar hankalin.
“Na faɗa miki wajen aiki sun barni tafiya Jordan yin degree ɗina na uku, tare za mu tafi da ke l, shi yasa na ce ma Dada kina da ciki don su bari in tafi da ke babu wani tashin hankali…”
Matsawa ta yi tana kwanciya a jikin shi.
“Shekara ɗaya ne kawai koma bai kai ba, ya za mu yi idan mun dawo? Ya za mu yi? Ba za su haƙura ba.”
Numfashi ya sauke yana zagaya hannun shi a jikinta ya riƙe ta gam, sumbatar gefen kanta yayi tukunna ya ce,
“Za mu yi tunanin wani abun kafin mu dawo in sha Allah… Ki yarda da ni, komai zai yi daɗi.”
Lumshe idanuwan ta tayi, yarda da shi abu ne da bai bata zaɓi akan hakan ba. Daga ranar ne komai ya fara, daga tafiyar su Jordan ne komai ya fara.
*****
Bata ga tasowar Daddy ba, sai riƙetan da ta ji yayi a jikin shi, duka nauyin ta ta sakar mishi tana wani irin kuka da yake ji har ƙasan zuciyarshi. Matar da ke zaune ya kalla.
“Ki tafi don Allah… Ki bar address ɗinki, za mu nemoki in mun samu nutsuwa… Don Allah ki tafi… Kin yi abinda za ki yi na rana ɗaya ya isa haka.”
Kai ta ɗaga mishi, don bata jin ko ta yi magana sauti zai fito saboda kukan da take yi.
“Karki sa a ranki za ki ɗauke shi…. Zan yi shari’a da ke daga nan har wajen Nigeria akan hakan, ina tabbatar miki ba za ki taɓa yin nasara ba, ɗana ne, babu wanda ya isa ya karɓe shi.”
Murmushin ƙarfin hali ta iya yima Daddy, ko a ƙarancin shekarun Rafiq ta same shi bata da wani tubalin dafawa ta ce su bata shi, ballantana da girmanshi haka, ta mishi magana ne da ta ganshi saboda ta kasa jurewa, saboda tana so ya yafe mata ko zata yi bacci mai nutsuwa bayan tsawon shekarun nan, ta biyo shi gidan ba don ya karɓeta a matsayin mahaifiya ba, sai don ya yafe mata kasa zamar mishi hakan da ta yi. Iya ƙaunar da ke tsakanin su da Rafiq da ta gani ya tabbatar mata ko na minti ɗaya bai taɓa jin rashin ta ba, hakan ya mata daɗi a lokaci ɗaya kuma ya taɓa wani ɓangare na zuciyarta da ta kasa fahimta.
“Gida mai lamba 23, Wuse II, gidan Alhaji Dikko.”
Ta faɗi tana miƙewa, kai Daddy ya jinjina mata, yana tsayawa sai da ya ga ta fice daga gidan tukunna ya kama Nuri da ta yi luf a jikinshi suna wucewa sama.