Skip to content
Part 41 of 52 in the Series Alkalamin Kaddara by Lubna Sufyan

Kano

Aslam ya mayar da shi gida, saboda Ammi bata yarda da nutsuwar shi ba, har cikin harabar gidan Aslam ya ajiye shi tukunna ya buɗe motar ya fita ba tare da ya ce mishi komai ba, don ya ga alamar baya son yin magana, Altaaf ba zai gaji da jinjina ma hankali irin na Aslam ba, shi yasa yake jin kunyar shi matuƙa, ko baka zauna da shi ba, nutsuwar shi zata sa yai maka kwarjini matuƙa. Ya kai mintina biyar a ƙofar gidan a tsaye, yana neman ƙwarin gwiwar da zai shiga da shi amma ya rasa. Tunanin fuskantar Majida na rusa wani abu cikin zuciyarshi da baisan da shi ba. 

Yana tsaye a bakin ƙofar Majida ta buɗe daga ciki, sai da ya ɗan tsorata saboda bai tsammaci zata fito ba, atamfa ce riga da zani a jikinta, sai ɗankwalinta da ta ɗaura simple, murmushi tai mishi, fuskarta na mishi wani haske na ban mamaki yau. 

“Na ji kamar jirin mota, shi ya sanya na hito don na ga baka shigo ba.” 

Majida ta faɗi tana ɗorawa da 

“Mi ke damun ka?”

Dln yanayin shi da ta gani kamar babu nutsuwa a tattare da shi. Kai Altaaf ya iya girgiza mata yana takawa, hakan yasa ta matsa mishi ya fara shiga cikin gidan tukunna ta bi bayanshi har tsakiyar falon, a nan ya zare takalman ƙafarshi yana jin yadda Majida batai mishi maganar wuce mata da takalma har tsakiyar ɗaki ba. Ita kam bata ma kula da ya wuce da takalman ba, don yanayin shi kawai take nazari, bata san dalilin da yasa bugun zuciyarta yake ƙaruwa ba. Har ya zauna akan kujera kallon shi take, gefen shi ya bubbuga da alamar ta ƙarasa ta zauna. Bata yi musu ba ta ƙarasa tana zama. 

“Me kike yanzun?”

Altaaf ya tambaya. 

“Banyin komi, kai nike jira ka hiɗi mani abinda zan dahwa dama… Stew kurun na yi.” 

Kai Altaaf ya jinjina yana sauke wani irin numfashi mai nauyi. 

“Bansan ta inda zan fara ba.”

Ya ce muryarshi can ƙasa, zuciyarshi ta nutsu a cikin ƙirjin shi, kallon Majida yake yana jin yadda yake gab da rasa ta. 

“Tsoro hwa kake bani, kallon mi kake man haka?” 

Majida ta tambayeshi muryarta a karye. Hannunta ya kamo yana dumtsewa cikin nashi, yana jin yanayin siraran yatsunta da yake yawan tsokanarta akan rashin tsokarsu. 

“Ina gab da rasaki Majee… Bansan ya zan yi idan hakan ya faru ba.” 

Hanjin cikinta ta ji sun hautsina, cikin tashin hankali take kallon Altaaf ɗin. 

“Miye haka? Bani son irin wasan nan don Allah” 

Kai ya girgiza mata, ba wasa yake ba, zata fahimci hakan ba da daɗewa ba. 

“Majida…”

Ya kira ta da wani irin yanayi, wannan karon ita take girgiza mishi kai, bata san me yake shirin faɗa ba, amma bata son ji, ko ma menene bata jin tana son ji. 

“Kin san me yasa ba mu samu yaro ba har yanzun?” 

Daƙuna mishi fuska ta yi, don bata fahimci inda tambayar tashi ta dosa ba, basu samu yaro ba saboda haihuwa lokaci ne, nasu bai zo ba tukunna. Altaaf bai jira amsarta ba ya ci gaba da faɗin, 

“Saboda ni…ni ne dalilin da yasa bamu samu yaro ba. Majee ni ne nasa…” 

Kai ta sake girgizawa. 

“Tare da kai likita ya hiɗi mamu bamu da matsalar komi, lokaci ne kurun bai ba.” 

Wani irin murmushi Altaaf yayi da yake nuna damuwar da yake ciki ƙarara a fuskarshi. Bai taɓa tunanin ƙaddara zata juya mishi ta wannan fuskar ba, bai taɓa tunanin ko da Majida zata ci karo da A-Tafida shi ne zai bata labarin daga bakin shi ba, ko kaɗan bai hango faruwar hakan ba, amma me ya sani? Ba a ma ƙaddara shisshigi, rubutunta na da hargitsi da ya wuce tunanin kowane ɗan Adam. 

“Ba lokacin samun haihuwar mu ba ne bai yi ba. Ni ne na gama zubar da nawa yaran tuntuni…” 

Hannunta Majida ta fisge daga cikin nashi tanajin maganganun shi kamar saukar ruwan saman da babu hadari balle a tsammaci zuwan shi. 

“Ni ba mutumin kirki ba ne ba, ban taɓa tunanin rana irin ta yau zata zo min ba, tun farkon auren mu na san ban dace da ke ba Majida, bansan wane abin kirki na yi dana samu zaman aure da ke har wannan lokacin ba, wallahi ban sani ba da na koma na sake yi ko za ki ci gaba da zama da ni bayan kin ji me na aikata.” 

Bata san hawaye sun tarar mata ba sai da ta ji suna zubowa, ko motsin kirki bata son yi, numfashi ma a hankali take fitar da shi saboda tashin hankali, so take ta nutsu sosai, idan ta yi kamar bata wajen ƙila Altaaf ya daina magana, ya daina faɗar abinda fahimtarshi take mata wahala. Ko ƙoƙarin motsawa Altaaf bai yi ba, balle ya kai hannu ya riƙo ta, duk da hakan yake son yi fiye da komai. Yana kallon yadda katanga ta fara ginuwa a tsakanin su tun kafin ya fara faɗa mata komai. 

Sai dai ya riga ya fara, Ammi ta ƙara karfafa mishi gwiwa ya faɗa wa Majida kafin ta yi magana da Baba a karɓo mishi yaran shi, ko kowa ya barshi Ammi na tare da shi, ba zai ji duniyar ta mishi fili ba. Sai dai wajen Majida a cikinta daban ne, zuciyarshi har ta fara zafi da tunanin barin wajen da zata yi. 

“Bana jin ina da sauran rabon yara kuma… Idan goma aka rubuta min samu babu ko ɗaya…” 

Altaaf yake faɗi yana kasa gane muryarshi, jin shi yake wani irin sama-sama. Girman maganar na danne shi, da gaske ne in yara goma yake da rabon samu ya gama zubar da su da matan banza a waje. Wani irin tsoro yake ji yana ratsa shi, baisan yadda zai fara zaman kabari ba idan mutuwa ta riskeshi a yanzun.

“Halayena basu da kyau… Ko kaɗan halayena basu da kyau, da zan iya komawa baya in sake wasu abubuwan da na yi.” 

Banda numfashi babu abinda Majida take yi, don duk kalmar da zata fito daga bakin shi da yadda yake ruguza mata wani abu a tare da ita. Ba zata ce ga yadda akai take fahimtar abinda yake cewa ba, don ta rasa alaƙar da ke tsakanin Altaaf ɗinta da A-Tafida da yake bata labari. Kamar mutane ne masu banbancin da take da tabbacin ba ita kaɗai take gani ba, duk wani wanda zai ji labarin da yake bata ma zai yarda mutane ne daban daban. Wani irin nauyi ƙirjinta yake mata da bashi da alaƙa da yanayin yadda numfashin ta yake fita. 

Altaaf kam tunda ya buɗe bakin shi baya son ya rufe sai ya gama, baya son wani abu ya tsayar da shi ko yaya ne sai ya gama gaya mata komai, zufa yake ji har cikin rigarshi saboda tashin hankali, komai yake faɗa ma Majida daga farko har zuwa dirarshi ƙauyen Kinkiba, da yadda suka haɗu da Nuwaira, da yadda yaso ya siyeta da kuɗi ta ƙi, bakin shi bai soma nauyi ba saida ya fara gaya mata daren da ya canza gaba ɗaya rayuwar shi. Kasa furta kalaman yayi saboda nauyin su da yake ji fiye da lokacin da ya aikata su. Kokawa yake da maganar yana kallon yadda Majida ta nutsar da dukkan hankalinta a kanshi. 

Wannan karon hannun shi ya kai da nufin taɓa ta, yana kallon yadda ta matsa da saurin gaske, kamar ya miƙa mata miciji ko kuma takobi, ji yai kamar ta watsa mishi ruwan zafi, hakan yasa shi mayar da hannun shi kan fuskarshi yana goge zufar da yake ji a jiki, kafin cikin wata irin dakusasshiyar murya ya ce, 

“Fyaɗe nai mata.”

Runtsa idanuwanta Majida ta yi tana jero ‘Innalillahi wa inna ilaihir raji’un’ babu ƙaƙƙautawa, jikinta babu inda baya ɓari da tashin hankalin da ke ɗauke da kalmomin Altaaf ɗin, wasu irin hawaye na zubar mata kamar an buɗe fanfo, batasan ya ciwon zuciya yake ba sai yanzun nan da ya kamata, da duk sauran kalaman yadda Altaaf da Nuwaira suka yi bayan abinda yai mata na ƙara mata ciwon da take ji, batasan ta miƙe lokacin da ya gaya mata rabo ya gitta tsakanin shi da Nuwaira har na yara biyu ta sanadin fyaɗen ba, sai da ta ji Altaaf na faɗin, 

“Majida don Allah…. Wallahi ban sani ba… Bansan da yaran ba.” 

Idanuwanta ta ware kanshi, wata dariya mai haɗe da kuka na kubce mata, neman mijinta take a tare da shi ta rasa, neman mijinta da take so saboda yadda yasan darajar mace take yi, saboda yadda yake girmamata yana kare darajarta a matsayinta na ‘ya mace, yau ya ruguza komai, yasa ta ɗora ayar tambaya akan zamantakewar su gaba ɗaya. 

“Baka san mi ba? Bakasan da yaran ba? Altaaf mi kake son ce man?” 

Ta ƙarasa wani irin kuka na ƙwace mata, kai Altaaf yake girgiza mata. Juyawa ta yi zata wuce ɗaki, Altaaf ɗin ya tashi yana kamo hannunta da sauri, zuciyarshi yake ji tana wani irin dokawa kamar zata fito daga ƙirjin shi. Ya riga yasan abinda zai faru in har ta shiga ɗakin, kayanta zata haɗa ta barshi, baisan yadda zai yi ba in har ta barshi, baisan ta inda zai fara ba. 

“Majida…”

Hannunta take ƙoƙarin fisgewa amma ya ƙi sakinta. 

“Yanzun ne hwa lokacin da zan kwaɗa maka mari, a littahi ko fim haka ake yi, amma ni kau na kasa. Ka sakar man hannu kahin in nemo ƙwarin gwiwar wanke ka da mari wallahi.” 

Majida ta faɗi tana jin yadda ɗayan hannunta ke mata ƙaiƙayi da ta kwaɗa mishi marin da gaske. Hakan ya karanta cikin idanuwanta yasa ya sakar mata hannu babu shiri. Baya tunanin cikin kaso ɗari na mutuncin shi a idanuwan Majida akwai guda biyar da sukai saura, baya son ƙara zubar da shi gaba ɗaya, in ta mare shi ba za su iya komawa yadda suke ba, baya jin zata iya yafe ma kanta ya sani. Yana sakinta kuwa ta sa hannu tana goge fuskarta duk da wasu hawayen ne ke zubar mata sababbi, ɗakin su ta wuce yana bin bayanta da sauri. 

Akwati ta ɗauka babba tana buɗewa, har lokacin kuka take yi sosai, duka kayan da ke cikin akwatin ta juye kan gado tana buɗe wajen ajiye kayansu tana fara ɗibo kaya tana watsawa cikin akwatin. Altaaf baisan hankalin shi zai tashi fiye da yadda yake a tashe ba sai da ya ga da gaske kayan take haɗawa. 

“Inbalillahi wa inna ilaihir raji’un… Majee… Don Allah karki min haka… Karki tafi… Ki tsaya ki ji ni… Zan miki bayani wallahi. Na canza ba haka nake ba yanzun… Bazan iya komawa baya in sake komai ba. Bazan iya ba, amma yanzun na canza… Zanyi komai don in gyara ɓarnar da na yi.” 

Tsayawa ta yi tana kallon shi, mamaki bayyane kan fuskarta, da gaske in ya ci gaba da magana abinda ya fi mari ma zata yi mishi, bata son ganin shi ko kaɗan, zaluncin shi ya fi ƙarfin tunanin ta, tana buƙatar lokaci ita kaɗai ta tauna maganganun da ya faɗa mata ma tukunna ta yi tunanin wani abu, ganin ta tsaya da haɗa kayan yasa Altaaf sauke wani numfashi don ya ɗauka maganar da yake yi ta fara shigarta ne. 

“Kiyi haƙuri mu gyara komai tare…”

Ya ce yana ƙanƙance mata idanuwa yadda yakan yi duk idan ya mata laifin da ta yi mishi fushi. Hakan kuma kan sa ta murmushi sai komai ya wuce, ammanl wannan karin wani irin kallo ta yi mishi da ke fassara ‘Baka da hankali, ko kaɗan baka da hankali’ kafin hawaye su zubo mata ta juya tana ci gaba da janyo kayan ta watsa su cikin akwati, sabon zazzaɓi mai haɗe da ciwon kai Altaaf ya ji yana rufe shi, ya kasa magana saboda bashi da kalaman da zai yi amfani da su. Akwatin ya cika sosai don sai da ta rage wasu kayan da ta zo rufe akwatin. Tana gama zage zif ɗin ta sakko da shi dashi daga kan gadon tana soma jan shi da niyyar fita daga ɗakin. Altaaf ya bi ta yana riƙo akwatin. 

“Ina za ki je? Majida ina za ki? Baki tambayeni ba za ki fita?” 

Wani irin kallo ta watsa mishi da yasa shi girgiza kai yana faɗin, 

“Ki yi haƙuri, don girman Allah ki yi haƙuri kar ki tafi.” 

Wata dariya Majida ta yi tana fisge akwatin da duka hannayenta biyu tare da faɗin 

“In tai ina? Ka haukace ko? Ko shaye-shayen da ka ce man kana yi ne baka bari ba?” 

Maganganun ta zafi suke mishi har ƙasan zuciyar shi, amma zai jure, bai faɗa mata duka abinda ya aikata a baya ba sai da shirin cewa hakan zai faru, bai dai ɗauka jin maganganun daga bakinta zai taɓa shi har haka ba. 

“Kai man laihi in tai in barma gida? Wallahi baka da hankali, gidana ne Altaaf, kana jina? Gidana ne! Kai za ka hita ka bar man gidan tunda kai ka man laihi… Kai baka isa in tahi in bar maka gida ba, kai kaɗan, kana jina?! Kai kaɗan…” 

Ware idanuwa Altaaf yayi yana kallon ta don bai taɓa jin abinda yake shirin faruwa ya faru ba ko a litattafan Hausa balle kuma a fim, a ƙasa dai ta Najeriya kuma arewacin ta. Sai dai ko fina-finan ƙasar waje. Akwatin Majida tai cilli da shi tana faɗin, 

“Ka hita bani son ganinka… Wallahi ka tako man gida sai na fasa maka kai, kowa ya rako ka sai na fasa mai kai shima.” 

Kai Altaaf yake ɗaga mata, bai taɓa ganin ɓacin ranta irin na yau ba. Kama hanya yayi da niyyar fita Majida tai mishi wani ihu da ya sashi zabura yana juyowa. 

“Kai da kayanka ne bani son gani, ka ɗauki akwatin ku hita…” 

Kan dai Altaaf ya sake ɗaga mata yana kama akwatin da sauri, gani ta yi saurin bai mata ba, ta sa hannu tana fisge akwatin, ƙofar ta zo buɗewa Altaaf ya matsa gefe kafin ta gabje shi, waje ta wurga akwatin tana jawo kafaɗarshi shi ma, ya buɗe baki zai yi magana ta tura shi waje tana mayar da ƙofar ta rufe. A jikin ƙofar ta zame tana sakin wani irin gunjin kuka da yake fitowa daga zuciyarta. 

Ta ina zata fara da wannan bam ɗin da Altaaf ya sauke mata? Wa zata tunkara? Kuka take mai cin rai don bata san me ya kamata ta yi ba, ta kasa tsayar da nutsuwarta akan cewar Altaaf na da ‘yan biyu,’ yan biyu na gaba da fatiha. Tana jin wani irin abu ya mata tsaye a zuciyarta da yanayin sunan da ta kira yaran da basu da zaɓi da zama haka. Rashin adalcin Altaaf akan mahaifiyarsu da su kansu ɗin na sa ƙirjinta ɗaukar ɗumi. 

***** 

Gaban motar ya buɗe ya saka akwatin yana rufe ƙofar, tukunna ya zagaya yana shiga mazaunin direba. Sai lokacin ya kula mukullin yana jiki, Aslam ya barshi a jiki, kanshi ya ɗora a jikin abin tuƙin motar yana sauke numfashi, gaba ɗaya jikinshi a sanyaye yake jinshi. Komai ya cakuɗe mishi ta kowanne ɓangare, amma yana da hope akan Majida tunda bata bar gidan ba, in bata san ganinshi ne zai yi duk ƙoƙarin da zai iya na ganin bai nuna mata fuskarshi ba har sai ta huce ta saurare shi tukunna. Ya jima a haka yana saƙe-saƙen zuci, ji yake kamar ya fita ya shiga gidan ya ga halin da Majida take ciki, amma hakan ba zai taimake su ba. Don haka ya tattaro duk wani ƙwarin gwiwar da zai iya ya ɗago da kanshi yana janyo murfin motar ya rufe, tukunna ya murza mukullin motar ya tashe ta. 

Fita yayi daga gidan, baisan inda zai nufa ba don haka ya wuce gida kawai, ko Ammi idan ya gani zai ji ɗan sanyi-sanyi. Hakan kuwa aka yi, gida ya nufa yana parking ɗin motar ya fito daga ciki tare da zagayawa ya ciro akwatin shi tukunna ya nufi cikin gidan, ko sallama bai yi ba ya shiga cikin falon, ba kowa sai Barrah a zaune tana danna waya tana shan abinda baisan ko menene ba a cikin kofi. A hankali ta ɗago kanta daga wayar tana mayarwa kanshi. Akwatin da ke hannun shi ta fara kallo tukunna yanayin shi, taɓe baki ta yi tana yatsina fuskarta. 

“Kai kuma daga ina haka? Ina za ka da ƙaton akwati?” 

Numfashi Altaaf ya sauke. 

“Majee ta haɗa min kayana ta ce in bar mata gidan ta.” 

Daƙuna fuska Barrah ta yi tana tauna maganar da Altaaf ɗin ya faɗa kafin wata irin dariya ta kubce mata, kofin da ke hannunta ta ajiye tana ci gaba da wata irin dariya da ta tsaya wa Altaaf a maƙoshi, don ya duba maganar da yayi ko kaɗan baiga abin dariya a ciki ba, idan ba’a tausaya ma halin da yake ciki ba bai kamata a tusa shi gaba ana mishi dariya ba. 

“Don ubanki ni sa’anki ne? Meye abin dariya?” 

Ya buƙatar muryarshi a kausashe. Hannu Barrah ta ɗaga mishi tana dafe cikinta da ɗayan hannun nata. Dariya take sosai, da ƙyar ta iya ce mishi  

“Wai tsaya… Yaya da gaske kake? koro ka ta yi?” 

Kai Altaaf ya ɗaga mata, wata dariyar Barrah ta ci gaba da yi da ta sa Altaaf sakin akwatin da yake riƙe da shi yana takawa da nufin ƙarasawa inda Barrah take, yana neman inda zai juye abinda yake ji ne bata sani ba. Ihu Barrah ta yi tana miƙewa babu shiri, hakan yasa Ammi fitowa daga ɗaki dan taga me yake faruwa, da gudu Barrah ta ƙarasa bayan Ammi ta ɓoye tana ci gaba da dariya. Wata irin harara Altaaf yake watsa mata, in yai magana kuka zai yi, yana jin kukan ya zo mishi iya wuya. Saboda baiga dalilin da zai sa Barrah ta dinga mishi dariya bayan halin da yake ciki bana dariya ba ne ba. 

“Altaaf… Lafiya?”

Ammi ta tambaya, kai Altaaf ya girgiza mata har lokacin yana hararar Barrah. Wata dariyar Barrah ta sake kwashewa da ita. 

“Anty Majee ta koro shi daga gida… Yaji yayi ko sakin shi ta yi ne ma bai dai gama faɗa min ba…” 

Barrah ta ƙarasa maganar tana sake kwashewa da dariya. Kallon Altaaf ɗin Ammi ta yi tana jin zuciyarta ta mata wani iri da halin da yake ciki, don ita ta san dalilin da zai sa Majida ta koro shi, Barrah ce bata sani ba, tunda ya bar gidanta kuma ta shiga ɗaki ta kwanta don zazzaɓi take ji ya rufeta, tunani take tunda ya fita daga gidan na lokacin da rayuwar Altaaf ɗin ta gurɓata haka bata sani ba, tunanin inda ta yi kuskure take yi ta rasa. A karo na farko a rayuwarta da batasan ta inda zata tunkari babansu Altaaf da maganar yaran da Altaaf yake da su ba, tunanin hakan kawai na sa kunya marar misaltuwa tana lulluɓeta. 

Bata son ziyarar inda zuciyarta take son kaita ko kaɗan, zata bi komai ɗaya bayan ɗaya. 

“Altaaf…”

Ammi ta kira cikin taushin murya wannan karon, baisan ko yanayin muryarta ba ne ko kuma menene yasa wasu irin hawaye masu ɗumi suka zubo mishi ba, hannu ya kai yana goge su, amma ga mamakin shi nuna mishi suka yi basu san wannan ba, nuna mishi suka yi sun yi shekaru suna neman hanyar fitowa wani abu ne yake riƙe da su. 

“Yayaa…”

Barrah ta kira tana ware idanuwa ganin da gaske kuka Altaaf yake yi, kanshi ya saddar ƙasa yana sa hannu tare da goge hawayen da ke zubar mishi, amma kuka yake sosai har tana ganin hakan ta yanayin jikin shi, fitowa ta yi daga bayan Ammi tana ƙarasowa inda Altaaf ɗin yake a tsorace ta riƙo ɗayan hannun shi. Tunda take bata taɓa ganin hawaye a idanuwan shi ba ballantana kan fuskarshi, ɗagowa yayi ya kalleta.

“Ni ba mutumin kirki ba ne Barrah…”

Ya ƙarasa wasu hawayen na zubo mishi, tun lokacin da yaima Nuwaira abinda yai mata yake neman hawaye ko zai samu sauƙi amma ya rasa su, haka lokacin da Wadata yace baya son ganin shi, da lokacin da yai ma Ashfaq abinda yai mishi, da duk wani lokaci bayan ya gane yayi kuskuren da ba duniyarshi kawai zai taɓa ba har lahirarshi. Kuka yake yau na abinda ya rasa, kuka yake na yadda zaɓukan da yayi a rayuwarshi suka jefa kokwanto a cikin lahirarshi. Kuka yake na komai da komai, Barrah bata san me ya kamata ta yi ba, hannun Altaaf ɗin ta kama tana janshi ta zaunar da shi kan kujera, tukunna itama ta zauna, duka hannuwanta tasa ta dumtse nashi hannun a ciki. Ranƙwafawa Altaaf yayi yana ɗora goshin shi akan hannuwan nata. Wani irin kuka yake da Barrah ke ji har ƙasan zuciyar ta. 

“Yaya mana… Don Allah ka daina. Ko menene zai yi dai-dai…” 

Ɗagowa Altaaf yayi yana girgiza mata kai, komai na danne shi lokaci ɗaya. Muryarshi a dakushe saboda kukan da yake ya ce, 

“Ba zai gyaru ba… Barrah na yi ɓarnar da ba zata gyaru ba…” 

Kai ta girgiza mishi ita ma. 

“Babu abinda baya gyaruwa Yaya… Babu…”

Kafaɗa Altaaf ya ɗan ɗaga mata, yana ganin komai dishi-dishi da hawayen da ke cike da idanuwan shi. 

“Ina da yara guda biyu… Twins…”

Hannun shi da Barrah ta sake dumtsewa ne kawai reaction ɗin da ya nuna mishi cewar maganar da yayi ta girgiza ta, amma yanayin fuskarta bai canza ba. 

“Ba abinda zai canza… Kowa zai ce musu shegu saboda ni.” 

Sai lokacin Barrah ta ce, 

“Yaya…”

Kai Altaaf ya ɗaga mata yana jin a duniya babu marar adalci irin shi. Ta yaya ma zai bar Kinkiba bai taɓa tunanin ya rayuwa zata kasance ma Nuwaira ba, ba zai ce ya manta ta gaba ɗaya a tsayin lokacin nan ba, amma rayuwar da ya samu tare da Majida ta sauƙaƙa mishi abubuwa sosai, ta sa shi jin komai zai wuce mishi in dai suka samu yara, rayuwarsu zata cika, zai manta da bayanshi gaba ɗaya. Ashe rubutun da alƙalamin ƙaddara yai mishi daban da abinda yake tunani. 

“Basu yi komai ba…laifukana suna taɓa mutane da yawa…” 

Numfashi Barrah ta sauke, ta kawo ma ranta abubuwa da yawa, ciki har da cin amanar Majida da Altaaf zai iya yi, amma bata taɓa hasko mishi yaran gaba da fatiha ba. Ko kaɗan bata hango mishi wannan ba, yanzun kuma da ya faɗa bata san abinda zata ce ba. 

“Ki ce wani abu…”

Altaaf ya faɗi idanuwan shi cike taf da hawaye. 

“Me kake so in ce?”

Barrah ta buƙata muryarta na rawa, don ita ma tana jin kamar zata yi kukan. Ɗan ɗaga mata kafaɗu Altaaf yayi hawayen shi na zuba yana jin yadda suke fitowa da sauƙi. 

“Nima ban sani ba.”

Numfashi me nauyi Barrah ta sauke, bata tsani Altaaf ba, amma za tai ƙarya in ta ce bata tsani halayen shi da take zargin yana da su ba tun da can, amma kuma kowa zai shaida auren Majida ya canza shi gaba daya. Yayi wata irin nutsuwa tunda ta shigo rayuwarshi, duk da daga ita har Aslam basu tsammaci zaman Altaaf ɗin da Majida zai kawo inda yake yanzun ba tunda ba sonta yake ba, kuma haƙuri ya mishi ƙaranci. 

“Wacece? Maman yaran?”

Barrah ta tambaya

“Nuwaira, yarinyar nan ta ƙauyen Kinkiba…”

Ware idanuwa Barrah ta yi cikinta na ƙullewa da wani irin tashin hankali, tana tuno tashin hankalin da aka yi a lokacin. 

“Yarinyar da…”

Ta fara tana kasa ƙarasa furta kalmar saboda nauyin da ta yi mata a baki. Kai Altaaf ya ɗaga mata yana zame hannunshi daga cikin nata ya haɗa su duka biyun ya dafe fuskarshi da su, hawayen takaicin rayuwar da yayi da zaɓukan shi. Ammi kuwa tunda ta ga sun zauna dama ta juya ta koma ɗaki abinta, don a karo na farko bata san me ya kamata ta yi ma Altaaf ɗin ba. Suna zaune a wajen shiru an rasa wanda zai fara magana suka ji sallamar Aslam, Barrah ce ta iya amsawa, Altaaf kuwa fuskarshi ya sake rufewa cikin hannuwan shi kunyar duniya tana lulluɓe shi. 

Kallon su Aslam yake yanayin su na sanar da shi akwai wata matsala. 

“Me yake faruwa? Yaya…”

Aslam ya buƙata yana kallon su da wani irin yanayi, kai Altaaf yake girgiza ma Aslam ya kasa magana, ya kuma kasa buɗe fuskarshi, ba zai iya haɗa idanuwa da Aslam ba, idan zai iya ci gaba da ɓoye ma Aslam rayuwarshi ta baya zai bada komai don haka ta faru, ciki kuwa har da yaran da yake ji kusa da zuciyarshi fiye da komai a yanzun. Don basu kai darajar gudun zubewar kimarshi a idanuwan Aslam da yake yi ba. 

“Bana so in tambaya tun ɗazun saboda na ga kamar kana buƙatar lokaci ne, kuma babu kyau yawan tambaya. Amma wallahi banda nutsuwa tun ɗazun. Har Islamiyya na je amma na kasa koyar da komai saboda zuciyata na tare da kai…in ma ba zaka iya faɗa min ko menene ba na ji, amma ka ce min wani abu… Ka ji … Don Allah.”

Kukan da ya ƙwace ma Altaaf da maganganun Aslam ɗin mai sauti ne ya gauraye wurin wannan karon. 

“Oh Allah na…”

Aslam ya faɗi yana ƙarasawa ya zauna yana riƙo Altaaf ɗin da faɗin, 

“Yaya ka daina… Ko menene zai yi sauƙi. Addu’a za ka yi ba kuka ba.” 

Sosai Altaaf ɗin ya kwantar da kanshi a jikin Aslam ɗin yana karɓar comfort ɗin da baya jin ya cancanta ya samu daga wajen Aslam, amma kamar ko da yaushe yana da son kanshi. 

“Ana karɓar addu’ar me laifi ne Aslam?”

Altaaf ya faɗi da ƙyar. Cikin tashin hankali Aslam ya ce, 

“Subhanallah… Yaya me kake faɗa haka?”

“Hmmm…”

Altaaf ya faɗi yana ɗagowa daga jikin Aslam ɗin tare da miƙewa har lokacin ya kasa haɗa idanuwa da Aslam. 

“Addu’ar kowa na ƙarɓuwa indai yayita da yaƙini da kuma miƙa lamurranshi wajen Ubangiji…” 

Kai kawai Altaaf ya ɗaga mishi yana shirin wucewa. 

“Yayaa da gaske nake… Ina za ka je kuma?”

Ba tare da ya juyo ba Altaaf ya ce, 

“Ɗaki…”

“Karka je kana wasu kalar tunani Yaya… Ka zauna bazan ƙara tambayarka ba.” 

Aslam ya faɗi cike da kulawa. Altaaf na jin wani iri yadda duk ya saka su cikin damuwa. A hankali ya juyowa kanshi a ƙasa ya ce, 

“Aslam ina jin kunyarka… Sosai ina jin kunyarka… Don Allah karka tsaneni ko ka ji me na yi…” 

Cike da rashin fahimta Aslam ya ce, 

“Ta ya zan tsaneka? Saboda me zan tsaneka Yaya? Ko me ka yi ba zan taɓa tsanarka ba.” 

Ɗan murmushi Altaaf yayi. 

“Karka yanke hukunci sai ka ji… Barrah zata faɗa maka.” 

Da sauri Barrah ta ce, 

“Yayaa…”

Idan yana son Aslam ya ji me yake faruwa ya faɗa mishi da kanshi, yadda yake jin kunyar Aslam haka ita ma take jin kunyarshi, ko Ammi da kanta tana ganin kimar Aslam. Kuma ma ba labarin ta ba ne na Altaaf ne shi ya kamata ya faɗa. Kallonta Altaaf ɗin yayi da idanuwan shi yake roƙon ta, kai ta girgiza mishi. 

“Bazan iya ba Barrah… Bazan iya ba wallahi.” 

Altaaf ya faɗi, ɗan sauran ƙarfin da yake ji tafiya zai yi gaba ɗaya idan ya ce zai gayama Aslam abinda yayi, ba zai iya fuskantarshi ba, baya so ma ya ji idan yana wurin. Numfashi Barrah ta sauke tana ɗaga ma Altaaf ɗin kai. Ba zai iya magana ba, don haka sai ya wuce abin shi, ɗakin Barrah ya nufa don bai da ƙarfin komawa ya tambayi ina mukullin ɗakinshi yake, ƙofar ya tura yana kullewa daga ciki don baya son kowa ya dame shi, kan gadonta ya kwanta yana rufe idanuwanshi, sigari yake so ko da kara ɗaya ne ya busa ko zai samu ɗan sauƙi, lumshe idanuwanshi yayi yana ayyana riƙe karan sigarin ya kunna mishi wuta ya ja yana busar hayaƙin da ke tafiya da kaɗan daga cikin damuwar shi.

<< Alkalamin Kaddara 40Alkalamin Kaddara 42 >>

1 thought on “Alkalamin Kaddara 41 ”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×