Kano
Ba zata ce ga yadda aka yi suka je Kano ba, bata san tunanin me take yi a hanya kafin su isa ba, ta dai san ta ƙirga bishiyoyi har lissafi ya ɓace mata. Haka idan ta ce ga yadda akai ta nuna ma Isah hanyoyin da zai kaisu unguwar Bachirawa ta yi ƙarya. Numfashi ma yinshi take yi kamar an jona mata batira a jikinta da suke taya ta numfashin ba tare da ta yi wani ƙoƙari ba. Bata sake shiga hargitsi ba sai da ta ganta a ƙofar gidansu tukunna, ta ɗauka washegarin auren su da Rafiq zata dawo, haka ta saka ma ranta, batasan ya akai yanzun da hakan ya faru bayan watanni yake saka ta cikin wani irin yanayi ba.
Tana fitowa daga mota kanta tsaye cikin gida ta yi, Isah ne ma ya dinga ɗauko akwatinan ta yana ajiyewa bakin ƙofar gidansu da ta yi tsaye ta kasa ɗaga ƙafafuwanta balle ta shiga. Sallama Isah yai mata da faɗin shi zai wuce, kai kawai ta iya ɗaga mishi, jakarta na maƙale a kafaɗarta ko da take cikin mota ma bata sauketa ba daga Abuja har suka ƙaraso Kano. Bata san lokacin da ta ɗauka a tsaye bakin ƙofayba, ƙafafuwan ta ta ji sun soma rawa da alamar gajiya.
Hamna ce ta fito daga ɗaki, ware idanuwanta ta yi cike da mamaki tana kallon Tasneem ɗin kamar wadda ta ga fatalwa, ba kaɗan ba take mamakin ganinta.
“Yayaa.”
Ta kira cike da rashin yarda har lokacin na cewa Tasneem ɗin ce tsaye a bakin ƙofa. Wasu irin hawaye masu ɗumi Tasneem ta ji suna tarar mata cikin idanuwa, ko kaɗan bata yi tunanin su Hamna ba, kanta kawai take tunani tun da ta fito daga gidan Rafiq, bata yi tunanin me zata ce ma su Hamna ba, ya zata fara musu bayanin mutuwar aurenta cikin watanni da basu wuce uku ba? Wane dalili zata faɗa musu? Wani sabon tashin hankali ta ji ya sake rufeta, ƙirjinta na ɗaukar ɗumi sosai, ji take kamar ta ciro zuciyarta ta ajiye ta a gefe ko zata ɗan samu sauƙi.
Tana kallon Hamna da take takowa har ta ƙaraso inda take, fuskarta da muryarta ɗauke da sabon mamaki ta ce,
“Lafiya dai? Me ya faru? Na ganki da kaya… Me ya faru?”
Yanayin yadda Hamna ta ƙarasa maganar kamar ta karya wani ɓangare na zuciyarta yasa hawayen da take ta ƙoƙarin tarbewa suka zubo wasu na biyo su da sauri. Riƙo ta Hamna ta yi tana faɗin,
“Azrah! Beena!”
Da sauri su biyun suka fito daga ɗakin suma, ganin Tasneem ɗin yasa su ƙarasawa inda take tsaye ita da Hamna, Azrah na faɗin,
“Me ya faru? Ya na ga Yaya? Innalillahi wa inna ilaihir raji’un… Kuka take yi… Me ya faru Hamna?”
uryar Hamna na rawa ta ce,
“Nima ban sani ba, ku shigo da kayan.”
Ta ƙarasa tana jan hannun Tasneem da ke wani irin kuka suna nufar hanyar ɗakinsu. Dai-dai fitowar Ummi daga ɗaki fuskarta a kumbure da alamar bacci ta tashi ko gama wartsakewa bata yi ba. Murza idanuwa ta yi tana sake buɗe su da faɗin,
“Tasneem?”
Janta Hamna ta yi don bata so ta tsaya, tasan halin Ummi zata iya faɗa mata wata maganar da zata ƙara ɓata mata rai fiye da wanda take ciki. Hannunta Tasneem ta ƙwace daga na Hamna tana takawa zuwa inda Ummi take tsaye. Runtsa idanuwa Tasneem ta yi fuskar Abba ta dawo mata da murmushin shi da yanayin ƙoƙarin da ya yi akan su, tarbiyarsu da duk wani haƙƙin su da Allah ya ɗora mishi, sannan abubuwan duk da suka faru bayan rasuwar shi na dawo mata, yadda Ummi ta kasa sauke haƙƙinsu da ke kanta, yadda ta gaza a matsayinta na mahaifiya, yadda ita ce silar komai da ya faru da Tasneem ɗin saboda bata damu da yunwarsu ba ma ballantana sauran abubuwan da za su buƙata a matsayinsu na ‘yaya mata. sannan ta buɗe idanuwanta kan na Ummi tana jin abinda bata son furtawa game da ita na mata yawo.
“Tasneem me ya faru?”
Ummi ta tambaya a tsorace, don ta ga akwatinan Tasneem ɗin da su Sabeena suka shiga da su ɗakin su, tana kuma kallon kukan da Tasneem take yi da yadda idanuwanta suke kumbure suna nuna alamar ba tun lokacin take kuka ba.
“Wani abu ne ya samu Rafiq?”
Ummi ta sake buƙata, cikinta na murðawa saboda tashin hankali, in rasuwa ya yi bata tunanin zata taɓa yin suriki irin shi, ko jikinta da suturarta aka kalla ansan tana cikin rufin asiri mai yawan gaske ma kuwa. Don hidima ta dubu goma yanzun ta fi ƙarfinta, ko lokacin da Abba yake aiki farko-farkon auren su bata cikin daula irin yadda take ciki a yanzun. Rafiq suriki ne da ba zata taɓa samun irin shi ba. Tana ta addu’a ƙanin shin da suka taɓa zuwa suka gaisheta tare ya ga Hamna ko Azrah ya ce yana so shima, in hakan ta faru kakarta ta yanke saƙa kenan. Ƙila ma su kwashe su dukan su su koma Abuja da zama.
Tana da shirin tura su hutun ƙarshen zangon da za’a yi a satin su je can gidan Tasneem ɗin, yanzun gashi ta dawo da alamun matsalar da Ummi bata san ta inda zata fara gyarata ba tun kafin ta ji wacce iri ce. Muryata a tausashe wannan karon ta ce,
“Ki min magana mana Tasneem, wallahi hankalina a tashe yake…me ya faru?”
Hannu Tasneem ta sa tana goge fuskarta, tare da jan wani irin numfashi a wahalce kafin ta haɗiye yawu tana yin murmushin da yake cike da takaici.
“Me ya ɗaga miki hankali Ummi? Tunanin na baro gidan daula ko? Hanyar samun kuɗinki ta tsaya. Ko ba shi kike tunani ba?”
Girgiza kai Hamna ta yi fuskarta a daƙune ta ce,
“Shi ya sa na ce mu wuce ɗaki kawai Yaya kika ƙi jina… Ki zo mu tafi don Allah.”
Kallon Hamna da ke tsaye Ummi ta yi, banda gaisuwa babu abinda yake haɗa su, ko turowa aka yi ana kiranta a waje tai mata magana kai tsaye take cewa babu inda zata fita, in Ummi zata yi faɗan duniya tashi take ta bar mata wajen. Ko ta ci gaba da danna waya kamar ma bada ita take ba, don Rafiq ya sai musu wayoyi manya tun kafin auren shi da Tasneem. Rabon da ta ce ta ɗaga hannu zata daki Hamna tun ranar da ta riƙe hannun tana faɗin,
“Ban miki komai ba Ummi, ina miki duk wata biyayya da Musulunci ya ɗora min duk da ba kya min duk wani abu da Musulunci ya ɗora miki, karki dake ni don na ce bazan fita wajen mutumin can ba, don ko na ce miki ɗan iska ne ba zai dameki ba in dai zan fita in dawo da kuɗi…”
Ta saki hannunta ta wuce, ranar ko baccin kirki bata yi ba, saboda maganganun Hamna sun tsaya mata ba kaɗan ba, daga ranar kuma bata sake matsa musu su fita zance ba, in sunyi niyya su fita, in basu yi niyya ba kuma shikenan. Ko idanuwa suka haɗa da Hamna sai ta ga yadda ta tsaneta, bata kuma san yadda zata yi ta goge hakan ba duk da yadda yake mata ciwo kamar me. Don haka bata ce komai ba, hankalin ta ma ta mayar kan Tasneem kawai.
“Ya sakeni Ummi!”
Ware idanuwa Ummi ta yi cike da tashin hankali, Hamna na jan wani irin numfashi, Azrah kam hawaye ne suka cika mata idanuwa. Sabeena ce ta samu ƙarfin halin faɗin,
“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…”
Wani murmushin Tasneem ta sake yi tana ci gaba da kallon Ummi da fuskarta ta yi wani haske kamar jinin da ke jiki ya koma wani waje saboda tashin hankali.
“Na faɗa miki idan aurena ya mutu a daren farko ke ce, ke ce Ummi, tun a daren ya mutu bai faɗa min ba ne sai yau. Kin rasa surikin da kike mafarkin samu Ummi, bazan yafe miki ba kamar yadda Abba ma ba zai yafe miki ba…”
Tasneem ta ƙarasa wani irin gunjin kukan da yasa Hamna ƙarasowa ta riƙota a jikinta na ƙwace mata, kuka take da soyayyar Rafiq da take da tabbacin har ƙarshen rayuwarta ba zata taɓa samun kalarta ba, kuka take na rashin Abban ta yau, don tasan da yana da rai hakan ba zai taɓa faruwa ba, ba zai taɓa sakata cikin yanayin da zata zaɓi duniya akan lahirarta ba, ba zai taɓa barinta da zaɓin kare lahirar ƙannenta ta watsar da tata ba, ba zai bar mata tarbiya da duk wata ɗawainiya ta ƙannenta ba balle har ta samu damar zaɓar gyara ɓarnar da take tunanin zata faru da wata ɓarnar da ta yi mata sanadin rasa Rafiq yanzun.
Kuka take na tarin laifukan da zaɓukan da ta yi suka haifar mata, laifukan da tasan ko su Azrah ba za su yafe mata ba, don ta ɓoye a bayansu ne ta yi zaɓukan da tasan inda ta nemi shawararsu za su zaɓi zama a zigace da yunwa da ta siyar da mutuncinta ta ciyar da su da haram. Gara ita, rayuwa ta bata zaɓin kauce hanya ko akasin hakan, amma ita bata basu zaɓin ciyar da su da haram ba. Ba kuma zata iya yafe ma kanta wannan laifin ba, balle ta yi tunanin za su yafe mata. Muryar Ummi na rawa ta ce,
“Tun ranar da kika faɗa min maganganun nan nake tunanin su Tasneem, na rasa me nai miki da za ki ce idan aurenki ya mutu ni ce sanadi, na rasa…”
Ɗagowa Tasneem ta yi daga jikin Hamna tana dariya duk da kukan da ta yi saboda ta kasa yarda da abinda kunnuwanta suke jiye mata, kallon Ummi take yi tana so ta tabbatar mata da cewa da gaske take nufin kalaman da ta yi. A hankali Ummi ta ɗaga mata kai, da gaske take yi ta yi tunani sosai, sai ta tsayar da cewar rashin yi mata kayan ɗaki da duk wani abu da ya kamata ace ankai ma mace a lokacin aurenta ne yasa ta yi maganar, don tasan yadda dangin miji suke, za su yi mata gori su ce Rafiq ne yayi komai. Amma in za su yi adalci ai sun san basu da hali ne shi yasa. Sai gashi auren ma bai mutu ba sai yanzun, bata san me yasa Tasneem zata ce ita ta kashe mata aure ba.
“Da gaske baki san me kika yi ba Ummi?”
Wannan karon a ƙufule Ummi ta ce,
“Don Ubanki in na sani zan ce ban sani ba ne? Ke ya kamata ki fara min bayanin abinda kikai ma bawan Allahn nan insan ta yadda zan fara kiranshi in bashi haƙuri ki koma ɗakinki bawai ki tsare ni da wasu shirmen maganganu ba.”
Dariyar Tasneem ta sake yi, wasu sabbin hawayen na ƙara zubo mata, muryarta na wani irin sarƙewa saboda ɓacin rai take faɗin,
“Baki taɓa damuwa da me za mu ci ba tunda Abba ya rasu, za ki iya fita daga safe har dare, baki taɓa damuwa da inda za mu je ba, matsalarki kawai kuɗi Ummi, abin duniya shi ne kawai matsalar ki… Za ki iya satika baki san me muka ci ba, in ma ganin mu kika yi da abinci ba kya tambayar inda muka samo ko ya akai muka samo…”
Hamna da ke kuka ta katse Tasneem da faɗin,
“Don Allah Yaa Tasneem ki ƙyale ta… Ba zata jiki ba… Kina ɓata lokacinki ne.”
Kai Tasneem take girgiza ma Hamna, ta gaji, tana jin idan bata amayar ma Ummi duka abinda yake cikinta ba mutuwa zata yi, baƙin cikinta da na rabuwa da Rafiq sun mata nauyin ɗauka a waje ɗaya, gara ta fitar da na Ummi ko zata yi numfashi mai sauƙi. Don haka ta ci gaba da magana tana kuka.
“Idan kuɗi kika gan ni da shi burinki in ƙara samo wanda suka fi su yawa. Baki tambayeni dalilin da yasa na bar aikatau ɗin da na samu ba… Ummi faɗa kikai ta min na miki baƙin cikin cin nama da abincin da Abbana bai taɓa kawo miki irin shi ba. Da kin kula sosai da kinga canji a jikina da yanayina gaba ɗaya… Amma baki damu ba…Wallahi ranar na yi tunani sosai akan meye akan dalilin da yasa kika haife mu tunda ba mu dame ki ba… Sosai na ji dama a bani damar sake mahaifiya Ummi… Da na zaɓar mana wata daban…”
Numfashi Tasneem takeyi a wahalce saboda zuciyarta da take ji kamar ana hura mata wuta a cikinta, musamman da fyaɗen da Haidar yai mata ya dawo mata sabo, da yadda yaune karo na biyu da zata furta ma wani faruwar hakan bayan Rafiq. Amma ta gaji sosai, ta gaji da riƙe abubuwa da yawa a cikinta ita kaɗai.
“Da kin tambaya dana faɗa miki ɗan gidan yai min fyaɗe Ummi…”
Riƙe bakinta Hamna ta yi tana ƙoƙarin mayar da ihun da yake shirin ƙwace mata, kafin ƙafafuwanta su fara rawa, Juyawa ta yi ta kalli Azrah da take girgiza kai tana wani irin kuka mai ɗaga hankali. Hannuwa Hamna take miƙa ma Azrah da ta ƙaraso tana kamata, don ji take faɗuwa zata yi kowanne lokaci, numfashinta ma baya fita dai-dai da wannan maganganun da Tasneem ta yi da ta ji su kamar saukar hadari, jikin Azrah ta faɗa suna durƙushewa a wajen, Sabeena kuwa ɗaki ta shige tana faɗawa kan katifa tare da fashewa da wani irin kuka, don ita a rayuwarta sam bata son ta ga ko wasu da bata sani ba suna kuka, balle kuma ‘yan uwanta.
Ummi kanta numfashinta kaɗan-kaɗan yake fita, ta yi tsaye inda take kamar an dasa bishiya, murmushi Tasneem ta yi tana kai hannu ta goge hawayen fuskarta, duk da wasu ne suke sake zubowa.
“Baki tambaye ni inda na samo kuɗin da na biya a asibiti lokacin da Hamna ta yi hatsari ba… Karɓa kawai kika yi Ummi, tun lokacin ya kamata in faɗa miki jikina na ba wa Alhaji Madu ya ban kuɗin… Haka jerin kuɗin da na ci gaba da samu ina ciyar da ku, banda su Hamna da nai wa ƙaryar aiki na samu don su kaɗai suka damu da yadda nake samun kuɗi, da yadda nake wuni a waje idan na fita… Ke kam lokacin kika fara nuna min soyayya saboda ina kawo miki abin duniya…”
Numfashin dai Ummi take fitarwa, shi ne kawai alamar da take nunawa ta cewar bata ƙame ta zama gunki a wajen ba.
“Ban taɓa kawo ma raina aure ba, don nasan rayuwar da nake yi ita halinki zai jefa su Hamna, ba zan iya kallo su lalace saboda kin kasa zamar mana uwa ba. Haɗuwa ta da Rafiq ne hasken farko da na gani tun rasuwar Abba, sai dai na gama zubar da mutuncina a waje…. Na sami namijin da yake sona Ummi, amma kin turani halakar da ban gane da wuri ba sai da lokaci ya ƙure min…”
Sauka daga jikin Azrah, Hamna ta yi tana rarrafawa ta kama bango ta miƙe tana wucewa ɗaki, Azrah ma bin bayanta ta yi. Su dukkansu ba za su iya jin maganganun da Tasneem ɗin take faɗa ba.
“Ya sake ni ne saboda ba zai iya zama da ni bayan na gama zubar da mutuncina a waje ba. Ko yaya ne da kin taimaka min Ummi, ko yaya ne da banyi zaɓin da na yi ba… Da aurena yana nan. Bazan iya yafe miki ba, baki saka ni inyi zaɓin da na yi ba, amma sanin ke ce silar hakan na rage min nauyin zunubaina…”
Tasneem ta ƙarasa maganar tana runtsa idanuwanta tare da buɗe su, wani irin tari da ta kwana biyu bata yi irin shi ba yana sarƙeta, ci gaba ta yi da yi kamar zata shiɗe, don sai da ta dafa bango tana tsugunnawa, kallonta kawai Ummi take yi, kafin ta zame tana zama a wajen ta zauna. Tasneem kuwa cikinta ta dafe, tana ƙoƙarin samun nutsuwa ko yaya ne, in ba Allah ne ya rubuta mata mutuwa a lokacin ba, tana roƙo da fatan yin rayuwa ko da zuwa lokacin da zata haifi abinda ke cikinta ne, tana da tarin zunuban da take son ƙara neman yafiyar Allah akan su, tana kuma son samun ƙarin mutum ɗaya bayan su Azrah da zai taya ta addu’ar Allah ya yafe mata.
Duk da yadda take ji ɗin a yanzun kamar ta mutu ne, amma tana numfashi saboda yaron da ke jikinta, don bata jin akwai sauran wani abu da zata numfasa domin shi, ciki kuwa har da su Azrah, komai na duniya ya gama fita daga ranta. Hannunta ta goge a jikinta don jini ya ɓata shi na tarin da ta yi, nan wajen ta bar Ummi tana shigewa ɗaki wajen su Azrah da ta samu sun haɗe jikinsu waje ɗaya kan katifar suna wani irin kuka.
Ummi kuwa maganganun Tasneem ke mata yawo, gaskiyar su na zauna mata, tunda Tasneem ta furta kalmar an yi mata fyaɗe Ummi ta ji zuciyarta na rabewa tana kasuwa gidaje daban-daban, ciwon na kaiwa ko ina na jikinta, siraran hawaye masu ɗumi ne suke zubo mata. Wani irin ƙunci da batasan daga inda yake zuwa ba ya taso mata yana baibaye duka duniyarta. Ko da Abba ya rasu bata san tashin hankali irin wanda take ciki a yanzun ba, tana jin labarin fyaɗe a gidajen radio da wajen iyayen yaran da hakan ya faru da su. Ko da wasa bata taɓa tunanin yadda suke ji ba. Balle ta misalta ita yadda zata ji in hakan ya faru da ita.
Ta ga yadda rayuwar su Ashfaq ta ƙarasa tarwatsewa bayan an yi wa Arfa fyaɗe ta rasu, ba za tai ƙarya ba, sun bata tausayi don sanadin hakan ne yasa suka bar gidan gaba ɗaya. Amma bata taɓa tunanin yadda suka ji ba sai yanzun, bayan ƙuncin da take ciki idan aka bata bindinga zata harbe ko waye ya taɓa mata Tasneem ta wannan sigar, runtsa idanuwan ta ta yi tana tsanar kanta da wani irin yanayi. In har abu mai girma haka zai samu ‘yarta bata ko kula ba, ita kanta Tasneem ɗin bata ji ta yarda da ita ta zo ta faɗa mata ba bata jin ta cancanci zama mahaifiya.
Sauran maganganun take tattaunawa, sai yanzun take gane dalilin da yasa Hamna ta tsaneta, ita da kanta ta tsani kanta, kuma ba ita akaima kalar laifukan da ta yi musu ba, da gaske ne Abba ba zai taɓa yafe mata ba, zai yafe mata dukkan laifukan da ta yi mishi da yana da rai, amma banda na banzatar mishi da yara. Numfashi Ummi ta ja tana jin kamar ta farka daga wani irin dogon bacci, ba su kaɗai ta yima laifi ba, har da Abba, duka rayuwar aurenta ce bata riƙe da daraja ba, da kuma duk wani abu da ya zo tare da auren.
“Na shiga uku…”
Ta faɗi zuciyarta na fara wata irin dokawa kamar zata fito daga ƙirjinta. Yadda lokaci ya ƙure mata take gani, bango ta kama tana miƙewa, da gudu ta ɗauki buta tana zagayawa banɗaki don cikinta ya kaɗa. Tana da tabbaci babu abinda zai hanata dakuwa a hannun mala’iku saboda laifukanta masu girma ne, tana tsoron mutuwa, amma bata taɓa jin tsaronta irin na yau ba.
Tana fitowa ɗaki ta wuce ta kwanta kan gado tana jan mayafi ta rufe jikinta har kanta, sanyi take ji kamar wadda aka watsama ruwan ƙanƙara. Duk wani ɗibar albarka da ta yi wa Abba daga aurensu zuwa rasuwarshi ne yake dawo mata kamar an kunna fim.
Wasu irin hawaye ke bin fuskarta, bata jin ta yi kukan rasuwar shi yadda ya kamata, saboda ba wai rasuwar shi take ma kuka ba a wannan lokacin, ɗan abinda yake kawowa da zata rasa shi ne matsalarta. Yanzun kuma sosai take kukan rasuwar shi, take kukan yadda bata da tabbacin ya yafe mata laifukan da ta dinga yi mishi da ƙuncin data dinga saka shi, bata ma taɓa ganin laifinta ba balle ta yi tunanin ta bashi haƙuri.
“Ka yafe min… Don Allah ka yafe min.”
Ummi take faɗi tana ci gaba da wani irin kuka, duniyar duka ta haɗe mata waje ɗaya yau. Kafin abubuwan da ta dinga yi ma su Tasneem su soma saukar mata kamar ruwan sama, yadda akai su Hamna basu lalace ba yana bata mamaki, yadda akai baƙin halinta bai shafe su ba yana taɓa mata zuciya, da yanzun sun ajiye mata ‘yan gaba da Fatiha, wataƙila da tuni ta dawo hayyacinta. Allah kenan mai iko akan bayin Shi, yadda Ya fitar da yara kimtsatstsu kamar su Hamna daga jikinta, da yadda Ya kare su daga dukkan tura sun da ta yi don su faɗa halaka yana saka wani sabon tsoro rufeta.
Bata da ƙafafuwan da zata tsaya a gaban Allah a lahira ta amsa tambayoyin masu tarin yawa, kan amanar su Tasneem da haƙƙin Abbansu, tana sa rai akan rahmar Allah, amma hakan bai hanata kokwanto akan tata lahirar ba. Runtsa idanuwanta tayi gam tana jero duk wata addu’a da ta zo bakinta ko zata samu sauƙin abinda take ji.
*****
Kan gadon ta ƙarasa ta zauna itama, hannu ta sa tana dafa kafaɗar Hamna, hakan na sata ɗagowa, abinka da farar fata, fuskarta har ta yi ja saboda kukan da takeyi.
“Hamna…”
Tasneem ta kira, kai Hamna ta girgiza mata.
“Me yasa? Akwai zaɓuka da yawa…me yasa za ki mana haka? Kinsan me kika yi? Kinsan girman laifin da kika yi? Zan fahimta in kin zaɓi yin wasa da lahirarki Yaya, amma bazan fahimci wasan da kikayi mana da tamu lahirar ba, me yasa zaki raba zunuban da baki bamu zaɓi akan su ba da mu? Me yasa zaki ciyar damu da haram? Shekara nawa hakan ya ɗauka?”
Kuka Tasneem take yi kamar ranta zai fita, hannu Hamna ta sa tana goge fuskarta, cikin wani irin kuka take cewa,
“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un… Yaa Tasneem kin cuce mu duka… Wallahi kin cucemu duka… Me yasa baki faɗa mana ba? Wacce irin ƙauna ce haka? Wacce irin ƙauna kike mana da za ki saki tabbacin lahirarki akan mu? Kinsan babu taimakon da za mu yi miki, kin sani…”
Kuka ya hanata ƙarasawa, ji take kanta kamar zai rabe biyu saboda ciwon da yake mata, tana son ganin laifin Tasneem ɗin fiye da yadda take jin laifin ta, inda ta matsa ma Tasneem ɗin da tambaya kan kuɗaɗen da take samu da hakan bata faru ba, jikinta ya bata akwai abinda yake faruwa, yarda da Tasneem ba zata yi musu ƙarya ba yasa bata taɓa binta taga kalar kamfanin da tace musu tana aiki ba. Tunanin jikinta take siyarwa tana ciyar da su kawai na hautsina mata hanji, ji take kowanne lokaci amai zai iya ƙwace mata, aman kuma take son yi ko zata samu ta fito da wani abu daga cikin haram ɗin da ta ci.
Itama Tasneem ɗin kuka take yi sosai, bata da amsoshin tambayoyin da Hamna ta tsareta da su, ta buɗe bakinta ya fi a ƙirga amma banda gunjin kuka babu abinda yake fitowa daga cikin shi. Azrah ce ta ɗago tana faɗin,
“Sauran kuɗin da yake hannunmu sa’ada kika bar aikatau da kin faɗa mana, sai mu yi awara a ƙofar gida, ko dankali, ko ni da Hamna mu yi tallar wani abin, koma menene dai banda zaɓin da kika yi… Da kin faɗa mana a tare zamu nemo mafita… Me yasa kikai mana haka? Me yasa? Don Allah me yasa za ki yi mana haka? Kinsan me Abba yake ji a kabarin shi duk lokacin da kika haɗa shimfiɗa da wanda ba muharamminki ba?”
Wani irin numfashi Tasneem ta ja bisa tambayar Azrah, wani sabon tari na taso mata da yasa Sabeena ture su tana riƙo Tasneem ɗin tare da shafa bayanta cikin sigar son sauƙaƙa mata tarin da take yi, amma kamar ma ƙara mata shi take, juyawa Sabeena ta yi tana watsama su Hamna wani irin kallo, a ƙuruciyarta da tasowarta bata san wata uwa da ta wuce Tasneem ba, ba zata ce ga yadda ɗumin jikin Ummi yake ba, ba zata tuna ranar ƙarshe da ta ɗauke ta ba, amma zata tuna ranar ƙarshe da Tasneem ta goyata da girmanta tun daga unguwarsu har bakin titi da bata da lafiya.
Zata tuna ranar ƙarshe da ta yi bacci a jikin Tasneem, don ko daren ɗaurin auren Tasneem ɗin kan kafafuwanta Sabeen tayi bacci suna hira. Ba zata bari su Hamna su karasa kashe ta ba, cikin hargowa ta ce,
“Sai tambayoyi kuke mata… Da me kuke so ta ji? Ta yi zaɓuka marasa kyau… Kuka san lokacin da ta roƙi Allah yafiya?”
Kallon Sabeena suke data ke ɗaga musu hannu.
“Baku sani ba, kamar yadda ba ku san tayi duk laifukan da ta yi ba sai yanzun… Idan Allah ya yafe mata kuma fa? Ta ciyar da mu da Haram saboda tana jin bata da wani zaɓi da ya wuce hakan, in ba za ku yafe mata ba karku kasheta, don ni bazan yafe muku ba wallahi, bansan yadda zan zauna da Ummi a duniyar nan babu Yaya Tasneem ba… Bazan iya ba… Don Allah ku yi haƙuri… Don Allah…”
Sabeena ta ƙarasa cikin kukan da yasa nasu Hamna dawowa sabo, jikin Tasneem da tarin da take ya tsagaita Hamna ta ɗora kanta tana ci gaba da wani irin kuka.
“Ku yi haƙuri… Ku yafe min don Allah… Ku yafe min Azrah… Hamna ku yafe min…”
Tasneem take faɗi cikin kuka, su dukkan su huɗun magana na musu ƙaranci, duka jikinta suka kwanta suna wani irin kuka, ta zagaya hannuwanta ta riƙe su, tana ɗora kanta a bayan Sabeena, don tana buƙatar su fiye da yadda zata iya faɗa, kuka suke mai tsuma zuciya.