Kano
Ƙwanƙwasa ɗakin Altaaf ya ji an yi, bai yi magana ba, baya jin zai iya ko da ya gwadawa shi yasa yayi shiru kawai. Ko waye in ya gaji da ƙwanƙwasawa zai tafi ya ƙyale shi ya ji da abinda yake damun shi.
“Altaaf…”
Zuciyar shi ya ji ta yi wani irin tsalle kamar zata fito ta bakin shi. Baisan lokacin da ya sauko daga kan gadon yana ƙarasawa ya buɗe ƙofar ba. Baba ne a tsaye ya raɓa Altaaf ɗin ya wuce cikin ɗakin yana samun waje gefen gadon ya zauna. Altaaf yana tsaye wajen ƙofar dake riƙe a hannun shi har lokacin. Ya kasa ko da motsawa balle yai ƙoƙarin rufewa ya koma ya zauna.
A tsawon rayuwar shi ba wai ya damu da Baba bane, asali ma komin shi Ammi ce, kuɗin kashewa, kayan sakawa, matsalar makaranta, ba zai tuna rana ɗaya da Baba ya ɗauki kuɗi ya bashi ba, ko ya bashi kaya a matsayin wannan shi ya siya mishi. In ma yana yi ɗin sai dai ko ta hannun Ammi hakan ke faruwa kuma bata taɓa faɗa mishi ba. Maganar data wuce minti sha biyar bata haɗa shi da Baba.
Da yana yaro ma ba komai bane a wajen shi sai mutumin da yake son takura shi, don wasu lokutan in ya zo fita da dare yana magana sai Ammi ta sa baki sai yayi shiru. Shi yasa yanzun da ya ji muryarshi ba ƙaramar girgiza yayi ba. Da ƙyar ya samu ya motsa jikin shi da yayi mishi nauyi ya rufe ƙofar. Shi ma gefen gadon ya samu ya zauna can nesa da Baba da ya sauke wani irin numfashi mai nauyi kafin ya soma magana.
“Bansan ta inda zan fara ba. Saboda sabon abu ne a wajena. Da gaske ne ba’a komawa baya a goge kuskure…”
Jinjina kai Altaaf yayi a hankali, don shi zai bada labarin hakan, shi zai faɗa ma mutane ba’a komawa baya a goge kuskure, da bai zo inda yake yanzun ba. Da yanzun kuskuren shi baya mishi barazana da komai daya gina bayan ya gane yayi hakan.
“Ina amsa sunan mahaifinka ne kawai, amma ban taɓa zame maka shi ba. Wannan kuskurena ne, bazan ɗora shi akan kowa ba. Duk da na sha gaya ma kaina ɗan Ammin shi ne fiye da yadda yake ɗanka… Ko ba komai ya kwanta a cikin ta, ƙaunar da ke tsakanin su abune da ba za ka taɓa fahimta ba…”
Ɗan jim Baba yayi, tunda ya dawo Ammi ta faɗa mishi abinda yake faruwa, kuskuren da yayi akan Altaaf yake danne shi. Ba yaune na farko ba kuma, tun yana Sakandire yake jin hakan, surutun mutane akan yanayin zaman su da Ammi bai taɓa damun shi ba. Daga kan ‘yan gidansu surutun ya fara, dangin ta kaf sun ɗauka don kuɗin mahaifinta ya aure ta, son da yake mata ya girmi komai, ya fi wanda yake ma su Altaaf. An kuma ce ƙaunar yara daban ce, amma da ta Ammi zuciyar shi ta fara buɗewa. Ci gaba yayi da faɗin,
“Amma hakan ba dalili bane ba, ina kallon duk abinda kake yi, ya kamata in tsawatar maka, in maka magana, ban yi ba. Na rasa wannan damar ba zata dawo ba, ban yi ƙoƙarin hanaka yin kuskuren da ka yi ba. Zan yi ƙoƙarin tayaka ka gyara shi iya yadda zai gyaru. Kana jina? Komai zai wuce In shaa Allah…”
Kai Altaaf yake ɗaga mishi yana jin wani irin yanayi da bai taɓa ji ba, baisan ya tallafin mahaifi yake ba, bai taɓa sani ba sai yanzun. Asalima baisan yana buƙatar mahaifi ba sai yanzun ɗin, Ammi ce komai nashi. Gyaran murya yayi a karo na ba adadi, kafin ya samu ya ce,
“Yanzun ba haka nake ba Baba… Wallahi na daina. Sosai na yi ƙoƙarin ganin kuskurena bai biyo ni ba… Na yi duk ƙoƙarina… Na daina tuntuni…”
Altaaf ya ƙarasa muryarshi na sauka can ƙasa, yana so wani ya yarda da shi ko yaya ne, don har ƙasan zuciyar shi yayi ƙoƙarin ganin A-Tafida bai biyo shi ba. Ya ɗauka ramin da yayi ya binne shi mai zurfi ne. Kai Baba ya jinjina mishi
“Za mu je ƙauyen gobe in Allah ya kaimu…”
Da sauri Altaaf ya ce,
“Za ku karɓo yaran?”
Kai Baba ya girgiza mishi.
“Babu tabbas, amma zanyi duk ƙoƙarin da zan iya saboda su, suna buƙatar dai-daito a rayuwar su ko yaya ne. Tabon kuskurenka mai girma ne, ba kai kaɗai zai ci gaba da bi ba Altaaf…”
Kai Altaaf ya jinjina, zuciyarshi na mishi wani irin nauyi. Yana jin yadda zai iya birkita duniyar duk wanda yai ƙoƙarin alaƙanta kuskuren shi da yaran shi. Miƙewa Baba yayi yana sa hannu ya dafa ƙafar Altaaf ɗin cikin son bashi ƙarfin gwiwa kafin ya fice daga ɗakin ba tare da ya sake cewa komai ba. Wayar shi Altaaf ya ɗauka yana kiran lambar Majida, har ta yanke bata ɗaga ba. Baisan me yasa ya kirata ba, kawai yana buƙatar wani abu ne da ba zai ce ko menene ba. Komawa yayi ya kwanta, ya rufe idanuwanshi ba don yana jin bacci ba.
*****
Inda an bi ta tashi ƙafafuwanshi ba za su taka Ƙauyen Kinkiba ba, su Baba su je su karɓo mishi yaranshi kawai, amma Baba ya ce dole sai an je da shi. Suna hanya ne yaima Wadata text cewar suna hanya ko zai same su acan. Majida ma text ya tura mata don ya kirata ya fi sau biyar bata ɗaga ba. Har cikin ranshi kuma yake jin rashin ɗaga wayar, babu yadda zai yi ne kawai.
Babu yadda Ammi bata yi da shi ba da suka ƙarasa ƙofar gidan su Nuwaira ya fito daga mota ya ƙi.
“Altaaf…”
Ammi ta sake kira a karo na babu adadi, shagwaɓe mata fuska yayi kamar zai yi kuka. Zatai ƙarya in ta ce bata kasa bacci ba a daren jiya, don har gari ya waye wani irin sama-sama take jinta. Ba zata ce ga asalin abinda take ji akan ƙaddarar da ke faruwa da Altaaf ba, tana kula da kallon da Baba yake mata jiya kamar laifinta ne abinda yake faruwa da Altaaf ɗin yanzun. In tambayar ta yayi ba zatai mishi musu ba. Amma kuma bata jin dana sani a ƙasan zuciyarta, batasan ko don Altaaf ɗin ya canza ba ne ba yanzun.
Abu ɗaya ta sani in za’a bata damar komawa baya, ba zata sake abu ɗaya akan yadda ta taso da Altaaf ba, bata dana sanin gatan da ta nuna mishi ko kaɗan, in zata iya mishi fiye da wanda take bashi a yanzun zata yi . Wannan kalar ƙaunar kawai ta sani. Yanzun ma da zata iya ɗauke mishi damuwar da take bayyane akan fuskar shi zata ɗauke ya samu sauƙi.
“Ammi don Allah ki barni…ba zan iya zuwa ba. Wallahi bazan iya ba…”
Altaaf ya faɗi ganin har lokacin Ammi na tsaye tana jiran amsar shi. Baba da ke tsaye yana jiranta ne ya ce,
“Ki zo mu je kawai…”
Bata yi musu ba, ta juya suka ƙarasa har ƙofar gidan.
“Ko za ki shiga?”
Da sauri Ammi ta girgiza kai, don tun shigowarsu ƙauyen fuskokin Nuwaira da kaf ‘yan uwanta ke dawo mata. In har ta tuna su haka, tana da tabbacin fuskarta bata ɓace musu ba.’ Yan kauye basu da hankali ta sani, ga gidadanci ya musu yawa, ba zata shiga ba, damar da Maman Nuwaira bata samu ba wancan karon yanzun ta samu, ko ta sheme ta da taɓarya ko ta sa kan icce ta faskareta da shi.
Daga nan bakin ƙofa Baba ya kwaɗa sallama, yana addu’ar Baban Nuwaira ya kasance yana gidan don komai ya fi zuwa musu da sauƙi. Idan ya ce yasan ta inda zai fara kawo maganar abinda suka zo ƙauyen Kinkiba ta dalilin shi zai yi ƙarya, amma tunda dai sun zo yana ji a jikinshi da ya buɗe bakin shi sauran maganganun za su fito suma. Sai da ya lumshe idanuwan shi cikin jin daɗin amsa sallamar da ya ji an yi cikin muryar da ta tabbatar mishi da maigidan ce, ba yaro ba. Ɗan gyara tsayuwar shi yayi yana jinjina ma Ammi kai alamar ‘Maigidan na nan’. Idanuwanta ta lumshe tana buɗewa, zuciyarta take ji ta soma dokawa da wani irin yanayi da ba zai fassaru ba.
Suna nan tsaye ƙofar gidan, Malam Bashari ya fito, Ammi ya fara kallo cike da mamaki yana tunanin inda ya taɓa ganin fuskarta, kafin Baba da ke tsaye ya miƙa mishi hannu, karɓa Malam Bashari yayi suka gaisa. Baba yana ɗorawa da faɗin,
“Wajen ka mukazo, maganar bata tsayuwa bace.”
Cike da mamaki Baba ya ce,
“To madalla, bari in ɗauko tabarma, ita saita shiga wajen iyalina.”
Ai bai ma rufe baki ba Ammi ta soma girgiza kai, bata ga dalilin da zai shigar da ita cikin gidan nan ba.
“Zamu zauna anan ɗin dai.”
Malam Bashari ya kalli Baba daya ɗauke idanuwa kawai, don yasan zai yi asarar maganar shi ne idan ya ce Ammi ta shiga cikin gida. Wucewa Malam Bashari yayi yana ɗauko tabarmi guda biyu ya dawo cikin soron gidan ya shimfiɗa tukunna ya zo yana ce ma su Baba su shigo daga ciki. Shigar kuwa suka yi suka cire takalman su suka zauna kan tabarmar da in da ace lafiya ne Ammi ba zata taɓa zama akanta ba, da atamfarta ‘yar dubunnai, amman yau ƙurar da ke jikin tabarmar ne ƙarshen abinda yake damunta.
Malam Bashari ma zama yayi kan ɗaya tabarmar yana zuba musu idanuwa, a lokaci ɗaya kuma yana ƙoƙarin gane inda yasan fuskar Ammi da take ta gyara mayafi tana ƙara ɓoye fuskar tata. Sake gyara zama Baba yayi a karo na babu adadi yana rasa ta inda zai fara.
“Na rasa ta inda zan fara magana, saboda maganar tana da nauyi sosai.”
Baba ya faɗi yana ƙara jin yadda maganar nan ba ta wasa bace, kunyar duniya kuma tana lulluɓe shi, don ya kasa saka ƙafafuwan shi a takalman mutumin da ke zaune nesa da su kaɗan, balle kuma yayi tunanin yadda ya ji lokacin da Altaaf ya keta mishi haddin yarinya. Zufa Baba ya ji tana tsattsafo mishi ta wajajen da baya tunani. Kasancewar Malam Bashari mutum marar hayaniya da yawan magana yasa ya bi Baba da kallo ba tare da ya iya furta komai ba. Baida abinda zai ce tunda su suka zo da niyyar magana da shi.
Baba kuwa Ammi ya kalla ko zata kawo mishi taimako, kai ta girgiza mishi a hankali, cikin wani irin sanyin murya ya ce,
“Akan ‘yarka ne”
Malam Bashari da ke zaune ya ji zuciyarshi ta yi wata irin dokawa, ba shi da wata yarinya da za’a iya zuwa ayi maganarta banda Nuwaira, ita kaɗaice yarinyar da ta rage mishi da ya riga da ya cire rai akan za’a zo ayi mishi magana akanta, ba dai a ƙauyen Kinkiba ba, duk da mutanen da suke zaune a gabanshi ko alama basu da ita ta cewa daga ƙauyen suke, bai kuma san wacce irin magana suka zo da ita ɗin ba, duk da haka zuciyarshi ci gaba da dokawa ta yi.
“Sunana Isma’il Tafeeda…”
Wannan karon yadda zuciyar Malam Bashari ta doka daban yake da kowanne lokaci, jin sunan Tafeeda ɗin ya zo mishi kamar dirar mikiya. Inda yasan fuskar Ammi na dawo mishi.Tabbas akan Nuwaira suka zo magana kamar yadda yai zato da farko. Baisan murmushin takaici ya ƙwace mishi ba sai da ya ji sautin shi cikin kunnuwan shi.
“Mahaifin Altaaf Tafeeda ko?”
Malam Bashari ya tambaya, yana ambaton sunan Altaaf ɗin da tsanar da Baba bai taɓa ji a muryar wani ba tunda yake. Ya kuma san tsanar da Malam Bashari yake ma Altaaf ɗin mai cancanta ce. Ammi da ke zaune ta gyara zaman mayafinta tana buɗe fuskarta sosai, tunda ya riga da ya gane su bata ga amfanin ɓoye fuskar da takeyi ba kuma. Hakan na sata faɗin,
“Yanzun bai kamata a ɓata lokaci ba, tunda an gane juna, na kuma tabbatar kasan maganar data kawo mu.”
Wannan karon dariya Malam Bashari yayi, ƙarfin hali irin na Ammi na bashi mamaki.
“Saikin faɗa na ji sai in fi tabbatarwa…”
Ya buƙata yana tsareta da idanuwan shi, don bai taɓa ganin kalar ƙarfin halinta ba, ya ga kaɗan daga cikinshi a ofishin ‘yan sanda, na yanzun ɗin ne ya bambanta, har da mijinta daya kwaso ƙafafuwanshi ya biyota suka zo mishi magana akan Nuwaira, yarinyarshi da sanadin ɗansu rayuwarta ta gurɓata ta fannin da babu abinda zai taɓa daidaitata, yadda duka mutanen ƙauyen Kinkiba suke yawo da zancenta a bakinsu kamar ita ta zaɓi abinda ya faru da ita. Yadda maza suka dinga faɗar da ta zubar da cikin da ta samu sanadin Altaaf da sun taimaka sun rufa mata asiri sun aure ta.
Sosai Malam Bashari yake ganin ƙarfin halinsu bayan kalar hargitsin da ɗansu ya jefa rayuwar ‘yarshi da ta sauran iyalanshi gaba ɗaya. Baisan suna ina a wannan lokacin ba, sai yanzun bayan shekaru huɗu har da wani abu, za su kwaso ƙafafuwan su suna tako mishi gida. Yasan sa’ar da suka ci ita ce Tawfiq ya riga da ya fita wajen aiki, don a kalar ƙunar zuciyar da Malam Basharin yake ji, baya tunanin zai iya hana Tawfiq yai ma mutanen dake zaune nesa da shi ɗibar albarka.
“Kan maganar yaran Altaaf ne.”
Ammi ta sake faɗi tana saka Baba rufe fuskarshi da duka tafukan hannayen shi, don kunyar da ya tsinci kanshi ciki ba zata misaltu ba.
“Kina ina?”
Malam Bashari ya ƙwala ma matarshi da take cikin gida kira, don wannan rashin hankalin na Ammi ya fi ƙarfin kanshi, ba zai iya saurara shi kaɗai ba, jikin shi har ɓari yake saboda ɓacin rai, cikin hanzari Zulai ta shigo soron gidan jikinta sanye da hijabi, duk da babu takalma a ƙafafuwan ta don yanayin kiran da Malam Basharin ya ƙwala mata tasan ba lafiya ba. Buɗe baki ta yi da niyyar tai mishi magana ta sauke idanuwanta kan Ammi da ta ƙara matsawa kusa da Baba sosai.
Cikin wani irin tashin hankalin da yake barazana da numfashin Zulai ta mayar da dubanta kan mijin nata da faɗin,
“Me matar can take anan? Me suka zo yi? Yadda suka gurgunta mana rayuwa bai isheta ba saida ta sake biyomu?”
Zulai ta ƙarasa maganar muryata na karyewa da kukan da ke shirin ƙwace mata. Ganin ‘yarta a kullum, tashi da ita a gida ba tare da sanin ko zata taɓa samun mijin aure da yara ‘yan gaba da Fatiha har biyu tashin hankali ne da ba kowacce mahaifiya zata fahimta ba, kullum kalar tsinuwar da take aika ma Altaaf da matar nan da take da ƙarfin halin zama a inuwar soron gidanta bata taɓa tunanin zata ganta tas haka ba, don tsinuwar ta isa ta tagayyara rayuwar su, duk da hanyoyin sakayya na Ubangiji suna da yawa, ba koyaushe sakayya take fara nunawa daga duniya ba, wata shari’ar sai a lahira.
“Ni kaina mamakin da nake yi kenan wallahi. Wai sunzo maganar yaran Altaaf ne.”
Malam Bashari ya maimaita ma Zulai maganar da Ammi ta yi. Ɗan dafe kai Zulai ta yi don alamar ciwon kai da yake san saukar mata.
“Waye Altaaf?”
Ta tambayi Ammi, tana kiran duk sunan Allah da yazo cikin kanta, don gab take da ƙarasawa inda Ammi take zaune ta afka mata da duka, ba ƙaramin ƙoƙarin ganin hakan ya faru take yi ba.
“Yaron wajena, nasan kin tsane ni, nasan ba kya son ganina yanzu haka, ki yarda da ni na zo nan ne kawai don yaran.”
Cewar Ammi iya gaskiyarta, don a fuskar Zulai take ganin tsanar da tai mata, ɗazun zuciyarta cike take da tsoro, amma yanzun babu wannan sam, don yaran Altaaf suka zo, batasan me yasa mutanen nan za su dinga kallon su kamar sun kashe musu wani abu ba, abinda ya faru ya riga da ya faru, su dukkansu ba za su canza wannan ba, yara suka zo karɓa don su samu rayuwa mai inganci, ta jima tana so ta ga Altaaf ya samu haihuwa, don ta gama tsara kalar gatancin da jikokinta za su samu, bata saka wannan biyun a ranta ba, don har suka shigo ƙauyen Kinkiba ba zata ce ga asalin abinda take ji ba.
Yanzun ganin wannan matar yasa ta jin son ganin yaran, tana so ta gansu ta ƙara tabbatar da yaran Altaaf ne, in hakan ya faru dole a bata jikokinta, don babu yadda za’ayi ta bari su taso cikin wannan akurkin gidan, jikokinta ba zasu taɓa tashi da gidadanci irin na ‘yan ƙauye ba. Don gashi nan tana ganin Malam Bashari da matarshi Zulai sun fara nuna mata. Zulai kuwa kallon Ammi take yi don tana da tabbaci matar na da ciwon hauka, ko da ya warke bai jima ba. Mai hankali ba zata dinga faɗar abinda Ammi take faɗa ba. Wata irin harara Zulai ta watsa ma Ammi da idanuwanta da suke cike taf da hawaye.
“Malam ka tashi mu koma ciki, ƙarya muke yi, tun a ofishin ‘yan sanda mun faɗa ƙarya muke yi, babu abinda ya haɗa ɗansu da Nuwaira. Bansan me kuma suke nema ba.”
Jinjina kai Malam Bashari yayi cikin yarda da maganar da matarshi ta faɗi, shirin miƙewa yakeyi Baba ya ce,
“Don girman Allah ku saurare mu…”
“Alhaji…”
Ammi ta fara, Baba ya ɗaga mata hannu
“Idan ba za ki min shiru ba Amina ki fita, don girman Allah ki koma mota…”
Shiru Ammi ta yi don yaune karo na farko da ta ji ya mata magana cikin irin muryar da yai mata yau. Hankalin shi Baba ya mayar kan Malam Bashari yana ci gaba da magana.
“Ku yi haƙuri don Allah…. Don Allah ku saurare mu tukunna.”
Hannu Zulai ta sa tana goge hawayen da suka zubo mata, wasu na sake fitowa da sauri, zuciyarta ciwo take yi, ƙirjinta yai mata nauyi, duk tsinuwar da take aika ma su Ammi tana haɗawa da addu’ar su wayi gari su gane kuskuren da suka aikata ma Nuwaira su dawo su gyara kaɗan daga cikin shi. Ko Nuwairan zata samu daidaito a rayuwarta, wahalar da ta sha mai yawa ce. Komawa Malam Bashari yayi yana zama, hakan yasa Baba sauke numfashin da baisan yana riƙe da shi ba.
“Kuskuren daya faru bazai gyaru ba, ba mun zo don zamu taɓa iya gyara abinda ya faru ba ne. Wallahi ko me za mu yi rashin adalcin da akai muku mai yawa ne…”
Baba yake faɗi zuciyarshi a jagule, bai tambayi me ya faru gaba ɗaya ba saboda baya buƙatar sani, yana da tabbacin su ne da rashin gaskiya ta kowacce fuska aka duba lamarin.
“Amman ku duba yaran nan, akwai abin dubawa a rayuwar su, na zo nan ne saboda suna buƙatar daidaito ko ya yake, tabon da akai musu abu ne da ba zai goge ba har abada.”
Cikin ƙunar rai Zulai ta ce,
“Tabon da ke tare da Nuwaira fa? Kana tunanin zai gogu?”
Da sauri Baba ya girgiza mata kai, gaba ɗaya duk wasu kalamai sun ƙwace mishi, baisan ko me yake faɗa yana bada ma’ana ba, don duk abinda ya zo bakinshi ne yake faɗa, magana yake shirin yi Malam Bashari ya rigashi da faɗin,
“Ku tafi don Allah. Gobe ku dawo, za mu yi shawara tukunna…”
Da sauri Ammi ta kalli Baba, kai ya ɗaga mata alamar su yi abinda su Malam Basharin suka buƙata, ko shi yana buƙatar ya ɗan huta daga wannan tashin hankalin, kafin su miƙe Zulai ta shige cikin gida abinta, Malam Bashari kuwa da idanuwa yake binsu Baba har suka tashi. Hannu Baba ya miƙa mishi don su sake yin musabaha kafin su fita, amma ko motsi Malam Bashari baiyi ba, haka Baba ya sauke hannun shi jiki babu ƙarfi suna saka takalman su suka fito daga gidan.
Altaaf da yake zaune cikin mota ya kafa ma ƙofar gidan idanuwa tunda su Ammi suka shiga zuciyarshi na dokawa kamar zata fito daga ƙirjinshi ta bisu ciki don tashin hankali ya buɗe murfin motar yana fitowa ganin su Ammi. Da sauri yake tambayar Ammi.
“Ina yaran Ammi? Kun karɓo su? Suna ina?”
Kallon shi Baba yayi.
“Allah ne kawai zai yafe maka yawan laifukanka Altaaf.”
Ya ƙarasa maganar yana wucewa ya shiga mota, maganganun Baba ya ji kamar an zuba mishi ruwan gishiri a ciwukan shi, don saida ya runtsa idanuwanshi sannan ya buɗe su kan Ammi da take tsaye. Hannun Altaaf ɗin ta riƙo, tana ganin yadda yai zuru-zuru.
“Sai gobe in shaa Allah. Za mu karɓo su, kana jina? Zan karɓo maka yaranka.”
Hannun Ammi da ke cikin nashi Altaaf ya dumtsa yana jinjina mata kai kawai. Tare suka ƙarasa wajen motar, ita ta buɗe mishi gidan baya ya shiga, ta mayar ta rufe, tukunna ta zagaya ta zauna itama. Baba ya ja motar.
“Ammi ɗan miƙo min wayata gata can…”
Altaaf ya faɗi a gajiye, wayar Ammi tasa hannu ta ɗauko mishi tana miƙa mishi, karɓa yayi yana lalubo lambar wayar Wadata ya kira ya kara a kunnen shi. Wadatan na ɗagawa ya ce,
“Kai yanzun zan fito, akwai abinda nake ƙarasawa ne.”
Muryar Altaaf ɗin can ƙasa ya amsa da,
“Ka bari kawai, mun gama, muna kan hanya ma. Su Ammi za su saukeni nan ɗin…”
Sai da Wadata ya amsa shi da faɗin,
“Ok tam ba matsala.”
Tukunna ya katse kiran yana sauke wayar daga kunnen shi .
“Ku ajiyeni a Zaria Ammi…”
Juyowa Ammi ta yi cike da damuwa ta ce,
“A wacce motar zaka dawo gida? Daka sani kamin magana sai mu ɗauko mota biyu Altaaf.”
Ɗan ɗaga mata kafaɗun shi yayi yana shagwaɓe mata fuska, shima baiyi wannan tunanin ba.
“Yanzun ya za’ayi to?”
Ta sake buƙata, baya son yawan magana a yanayin da yake jinshi.
“Ko Aslam sai in kira ya zo mu koma…”
Ammi bata ce komai ba, yana jin tana waya da Aslam ɗin tana fada mishi ya kamo hanyar Zaria yanzun, ko me yake yi ya ajiye ya taho. Lumshe idanuwan shi yayi yana jingina da kujerar sosai. Indai Ammi na kusa da shi, yana da tabbacin ko da komai bai mishi dai-dai ba, bazai taɓa shiga kowanne yanayi shi kaɗai ba, za su raba tare da ita. Nutsuwar da ke tare da hakan daban ce.
*****
Har ƙofar gidan Wadata su Ammi suka sauke shi tukunna suka juya, don n maigadin ma ya buɗe musu ƙofa, Altaaf ɗin ne ya ce su sauke shi a ƙofar gidan, ya ƙarasa shiga da ƙafafuwan shi kawai. A bakin ƙofa ya tsaya yana ƙwanƙwasawa, muryar Fatima ya ji ta ce mishi ya shiga, tukunna ya murza hannun ƙofar yana turawa tare da shiga da sallamar shi. Amsawa ta yi tana ɗorawa da,
“Altaaf…”
Murmushin ƙarfin hali ya ɗora kan fuskar shi.
“Matar Yaya. Ina kwana…”
“Lafiya ƙalau. Sannu da hanya…”
Murmushin ya sake yi.
“Sannu da gida.”
“Dee ya ce min tare kuke da Ammi.”
Kai ya jinjina mata.
“Ƙofar gida suka sauke ni suka wuce.”
Hararar shi Fatima take yi.
“Kai Altaaf rashin kirkinka babba ne.”
Sai lokacin yayi ‘yar dariya.
“Afuwan Matar Yaya, sauri suke yi ne wallahi shisa…”
“Ai shikenan, mu za mu je har gida mu gaishe su, ka ƙarasa ciki, yana dining area.”
Kai Altaaf ɗin ya ɗan ɗaga mata yana wucewa cikin gidan ya nufi inda wajen cin abincin yake. Wadata ya samu zaune yana karyawa, zagayawa yayi ya ja kujerar da ke kusa da shi yana zama tukunna ya ce,
“Yaya Imran…”
Yanayin yadda Altaaf ɗin yai magana ne yasa Wadata faɗin,
“Wallahi bazan zuba maka ba, ka ji na rantse… Gara in za ka ci ka taimaki kanka. ”
Jingina Altaaf yayi da jikin kujerar, muryarshi a shagwaɓe ya ce,
“Ba’a karɓo yaran ba fa, Ammi ta ce sai gobe wai.”
Sai da Wadata ya kurɓi shayin shi tukunna ya ce,
“Allah ya kaimu…”
Ware mishi idanuwa Altaaf yayi.
“Har yanzun ba za ka zuba min ɗin ba?”
“Ruwan shayi ne a hannuna Altaaf, kuma yana da zafi sosai…”
Wannan karon dariyar da Altaaf yayi tun daga zuciyarshi ta fito, sai da ya ɗauki plate ya buɗe abin saka abinci yana zuba soyayyar doya da ƙwan da ke cikinta iya yadda zai ishe shi, tukunna ya buɗe wani kwano ya zuba sauce ɗin kifi da ke ciki a gefe, tashi yayi yana ƙarasawa inda ƙaramin fridge yake ya buɗe, babu lemo ko ɗaya a ciki sai ruwa.
“Yaya Imran babu abin sha.”
Altaaf ya faɗi.
“Ruwan da ke ciki ya ƙare kenan?”
Wadata ya faɗi daga inda yake zaune, yana gutsurar doyar da ya ɗauka tare da taunawa.
“Abin sha fa na ce ba ruwa ba.”
“Uwarka ce wannan a ciki kenan?”
Dariya Altaaf yayi.
“Don Allah nidai…”
Ɗan juyawa Wadata yayi yana kallon shi.
“Babu tunda baka gani ba, wata yayi nisa, banda kuɗi.”
Robar ruwa ɗaya Altaaf ya ɗauko yana dawowa ya zauna, sannan ya ce,
“Ba wani wata yayi nisa… Nawa ake siyar da lemon?”
Hararar shi Wadata yayi.
“Inka fara tara yara za mu yi wannan maganar…”
Magana Altaaf zai yi Fatima da ta ƙaraso wajen ta sa shi yin shiru.
“In ƙaro muku doyar ne? Altaaf ina da zoɓo a kitchen, in haɗa maka?”
Da sauri Altaaf ya ce,
“Eh don Allah…”
Wadata kuma amsa ta yayi da faɗin,
“Ni dai na ƙoshi, sai dai ko Altaaf…”
Kai Altaaf ɗin ya girgiza mata.
“Akwai saura sosai a ciki… Zoɓon dai.”
Wucewa Fatima ta yi, Altaaf ya kalli Wadata.
“Don ba ka sona shi ne zaka bari in ci doya da ruwa…”
“Ka daina min surutu ina cin abinci…”
Wadata ya faɗi, amma Altaaf yayi kamar bai ji shi ba ma, sosai ya ci gaba da takura mishi ɗin, yana jin yadda nauyin da ke ƙirjinshi yake ragewa, ya kuma san Wadatan ya biye mishi ne don ya rage mishi damuwar da yake ciki. Yana jin daɗin yadda bai tambayeshi komai ba, yasan zai faɗa mishi da kanshi in ya shirya hakan. Ta kowacce fuska Wadata na da muhimmanci mai girma a rayuwarshi. Yanzun yake ƙara tabbatar da hakan.
G boy